Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

karatu a kano kuma Aliyu a kano yake zama kawai abar masa ita ya tafi da ita idan yaso tana ƙarasa karatunta sai ya dawo daita ko gurina ko gurinka please"


Shuru Daddy ya yi dukda ba haka yaso ba yaso ace ya raba auren dake tsakaninsu ta cigaba da karatunta a Abuja, amma shi kuma Uncle N ya yi hakane saboda zama yau da gobe yafi ƙarfin wasa dole a hankali yarinyar taza fara shigar masa rai har yaji yana son zama da ita.


"Ka amince ko baka amince ba?"

Daddy ya tambaya yana kallon Aliyu

"Babu komai in sha Allah zan riƙeta zuwa tayi graduation ɗin"


Okay Daddy ya ce sannan ya danna wayarsa not too long Mommy suka shigo itada Aneeserh, zama suka yi ta gaishesu sannan Daddy ya ce

"Daughter kinason zuwa kano ko?"

Da sauri ta gyaɗa masa kai dan ta ƙagu ta koma kano kodan ƙawayenta


"Tom zaki koma yanzu in sha Allah"

Murmushi ɗauke a fuskarta ta ce" thank you Daddy"


Yana nuna mata Aliyu ya ce

"Kinga wannan?"

Kallonsa ta yi sai kuma ta sunkuyar da kanta tana ɗaga masa kai alamar E

"Tom zaki koma gidansa da zama a kano ki ɗaukeshi matsayin Abbanki Aneeserh ki ɗauka duk abunda kike buƙata Abbanki zai yi miki sannan kuma mijin kine"


Da wani irin sauri ta ɗago kanta tana kallon Daddy jin furucin da ya yi, fashewa ta yi da kuka tana kallonta ta ce


"Daddy tsoronsa nakeji please ka barni anan"

Murmushi Mommy tayi tana riƙeta ita kuma tana cigaba da kukanta

"Kiyi haƙuri Aneeserh babu abinda zai sameki ki ɗauka shiɗin Abbanki ko kina tsoron Abbanki?" girgiza masa kai ta yi ya ce


"Toh shima karki ji tsoronsa in sha Allah kuma zan dinga kawo miki ziyara"

Gyaɗa kanta ta yi tana sake rushewa da kuka jikin Mommy, kallonta kawai Aliyu yake dan gani yake shine wanda yafi dacewa ya zubar da hawaye ba ita ba


"Aliyu kaji tsoron Allah cikin riƙon da zaka yiwa marainiyar Allah ka ɗauki Aneeserh matsayin ƴar cikinka ka kula da rayuwarta please banson mu samu saɓani akan rainon Aneeserh dan ni bama haka naso ba"


Okay Aliyu ya ce sannan ya miƙe jiki a sanyaye ya yi waje. Sosai suka yi mata faɗa da kuma kwantar mata da hankali har tayi shuru sannan Mommy ta ɗauketa suka koma ɗakinta.



Tunda ya koma ɗakinsa bai kula kowa ba ya yi kwanciyarsa itama Safeena sanin halinsa yasa bata wani damuba tayi kwanciyarta.


Wajejen ƙarfe 11am suka gama shiri da jirgin su ya kusa tashi, zaune take ɗakin Mommy gaban mudubinta bayan ta gama ƴar kwalliyarta dukda ba wani abun ta shafa ba daga powder sai lip gloose sai ta saka kwalli shikenan amma tayi wani sihiritaccen kyau dan Aneeserh nada jikin girma bazaka taɓa cewa batakai irin 18yrs ɗin nan ba komai nata irinna manya ne. Dafata Mommy ta yi tayi saurin kallonta sai kuma ta sunkuyar da kanta haka kawai taji tana jin kunyar Mommy, murmushi Mommy ta yi ta ce

"Aneeserh lokaci na shigewa zaku wuce"

Hawaye taji ya kawo idonta amma tayi sauri shanyewa dan tayi alƙawarin bazata sake zubarda hawayenta ha kamar yanda Mommy ta roƙa, kama hannunta ta yi sannan suka jero tare suka sakko.



Bai tsaya kallonta ba ya yi gaba suka bi bayansa itada Safeena dukda ita batasan mene ne yake faruwa ba, guards ɗinsa na tsaye suna jiransa ya shiga mota sannan suma suka shiga Mommy na ɗaga musu hannu suka bar gidan dan daman Daddy bayanan.

*Nassarawa G.R.A Kano state.*




*ANEESARH*

*💥Aneeserh Just The Beginning.*💥



*Story $ Writing By:*✍️📚


*N $ N.*


*🔥💫Nanameera $ Nainarh KD.🔥💫*



*Ep. Thirteen*



*Nassarawa G.R.A Kano state*




Sosai Yasmeen da ƙawayen ta Sabeera da Suhaila suka sha fira kafin daga bisani suka shiga haɗaɗɗen kitchen na Gidan suka shirya lafiyayyun girke girke kala kala domin Yasmeen kam ba baya ba wurin iya girki iri iri na zamani dana gargajiya yadda bata wasa da cikinta haka batayi sake wurin ƙin koyan girka lafiyayyun gaske ba, shiyasa kuwa ta kafa dafa a zuciyar mijin su Hydar ta wannan fannin.









Sai wuraren ƙarfe 2:30pm sannan Sabeera da Suhaila suka ma ta sallama suka tafi.










Yayin da ita kuma ta koma cikin Gidan, fara tattare plate's da suka yi amfani da su tayi ta kai kitchen ta wanke ta zuba kowanne a ma'ajinsa sannan ta dawo ta gyara palon da su Sabeera suka yi kaca kaca da shi kuma suka tsallake suka bar ma ta shi a Hakan, sai da ta gyara palon tsaf komai ya yi tsaf tsaf yadda ya kamata sannan kai tsaye Bedroom nata ta wuce, tayi wanka da Sallahr Azhur da bata samu tayi ba daga nan Bacci ɓarawo ne ya yi gaba da ita.





Sai wuraren ƙarfe 5:20pm ta farka tana salati sannan ta shiga Bathroom ta kuma yo wanka cikin ƙanƙanin lokaci ta shirya sauri sauri take yin komai domin shaf ta manta G.A ya ce da ita yau zasu dawo Kano, Sallahr La'asar tayi a gurguje sannan ta fito Palon Gidan.






Hango mutum tayi zaune saman Sofa 1sieter ta bata baya tana kallon gaban ta da alama system take sarrafawa.



"Hello."




Ta faɗa tana yin gaba ba tare da ta jira ta amsa ba domin ta gane Safeena ce.



"Hii."


Ita ma Safeena ta faɗa a taƙaice idanunta cikin system nata, dama haka suka saba babu Magana daga hello sai hi.



Kai tsaye part ɗin G.A ta nufa sallama ɗauke saman laɓɓanta ta ƙari sa shiga cikin Main Bedroom ɗin.


Hangosa tayi zaune In bedside saman Sallaya da alama ya idar, Addu'o'i yake yi.



Murmushi ta saki sosai takeson mijin mana General Aliyu sama da komai domin ya tara dukkan abin da mace zata so samu wurin mijin Aure.





Na farko dai ya kasance kyakkyawa ne shi ajin farko kuma fari ne fal sol, ya kasance murɗaɗɗen jiki garesa gunin burgewa gashi ya kasance adire yake ga kwarjini izza dama kuma yana da alaƙa da sarauta, ba koda yaushe General Aliyu ya cika son magana ba, sai dai sam baya da wulaƙanci amma baya ɗaukar raini sam ko kaɗan, yana son mai son sa ko'a wurin Aikin sa na Soja yabawa akeyi da nagartattun halayensa, gashi ma'abocin ibada sam Sallah bata wucesa kuma, Aliyu yana daga cikin Mazen kirki da suke wahalar samu cikin wannan Rayuwar a yanzu shiyasa Yasmeen take mugu mugun ƙaunar sa kamar ranta kuma yana bata kulawa daidai yadda ya kamata haka ma sauran matan sa babu wacce zata ce bata jindaɗin zama tare da General Aliyu duk da cewa duka ga irin Auren da suka yi, dukkan su Aura masa shi aka yi....



"Her Heart ka Kammala idar da Sallahr?."


Ta tambaya Ganin alamun da tayi.

Ba tare da ya yi magana ba, ya ɗa ga ma ta kai idanunsa akan nata.


"Sorry Please, ka dawo ina ta Bacci gajiya ne yasa, ina Fatan ka dawo Lafiya?."


Still ba tare da ya ce komai ba ya kuma jinjina ma ta kansa.



"Oh Her Heart!! menene yake damun ka haka ne ya naga idanun ka sun yi firi firi haka kamar wanda tunani yayima yawa menene ya faru a Abujan Allah ya sa dai Komai lafiya?."


Ta jero ma sa tambayoyin tana miƙe wa tsaye cikin sauri ta ƙari sa garesa ta zauna suna fuskantar juna ta kamo fuskar sa saman tafin hannunta.




*Aneeserh P.o.v.*


Kam tun bayan faɗa ma ta komai da Daddy ya yi wai wannan mutumin mai kama da Dodo a wurin ta shiɗin mijinta ne kuma zata kasance tare da shi a nan Kano bayan sun zo.

Komai ya dawo ma ta sabo cikin zuciyarta taji ta kuma kewar Ahalinta Abbanta, Ummin ta, Yaya Farouq nata da'ace duka suna nan tasan ba za'a taɓa bari ayi ma ta wannan rashin adalci ba.







Karo na farko da taji Daddy bai kyauta ma ta ba, akan me ma za'ayi tunanin haɗata da wannan mutumin wanda ta lura ma sam ba ƙaunar ganinta yake ba.


Kuma gashi wai har ma ta uku garesa, ita kuwa Aneeserh ina zata kai wannan ƙaddara haka na Auren sa.






Duk abin da take yi daurewa kawai take yi tana pretending domin kar Hajiya Aisha ta gane komai.


Tun barin Abuja da suka yi suka shiga jirgi har izuwa ƙari sowa nan Kano da suka yi ba ta kuma furta komai ba, kuma bata kuma cin komai a bakinta ba.






Domin koda suka ƙari so katafaren gidan na General Aliyu tsaban ruɗewan da tayi na ganin securities da uniform na soldiers yasa ko tsayawa kallon kyau da tsari da kuma haɗuwar Gidan ba tayi ba.






Da shigarsu palon gidan da ya gaji da haɗuwa sai ƙamshi ke tashi ta ko'ina ya juyo a bazata gareta yana kallon ta da rikitattun idanunsa, a lokacin tsaban tsoro kusan fitsari ne ya kusa Zubo ma ta, amma ta daure, tana sauraren umarnin da yake bawa Safeena da zuwa lokacin ranta yake a mugun ɓace domin kuwa a cikin jirgi Hydar ya sanar da ita komai, umarni ya bata akan ta kai Aneeserh zuwa Bedroom nata sannan ta bata duk Wani abu da take buƙata sannan ya yi gaba izuwa Up part nasa.






Yayin da Safeena badan taso ba, ta kai Aneeserh wani Bedroom dake cikin Palon ba tare da tayi ma ta bayanin komai ɗin ba da Hydar ya umurce ta, ta fito a fusace.







Aneeserh kuwa zubewa tayi saman gwawowin ta a tsakiyar ɗakin tana kuka mai tsuma zuciya kukan da babu mai rarrashin ta, ji take yau ne ta kuma tabbata marainiya a duniya, batasan haka rashin iyaye yake da zafi ba, tayi kuka sosai taba uku lada, har sai da ta gaji dan kan ta sannan ta haƙura.






Yanzu haka ma da kyar ta samu ta daddafa ta shiga bathroom tayo Alwala sannan ta fito da kyar ta yi Sallahr La'asar kana ta kuma zubewa saman carpet tsakiyar Bedroom ɗin tana kukan zuci domin zuwa lokacin hawayen ya dena ma fito ma ta sam, daga haka ne kuma Bacci da ya kasance ɓarawo ya yi gaba da ita....









*ABUJA*


"Humaira wai daga ina kike haka tun jiya Hydar ya zo sun kwana anan shi da Safeena, ɗazuma suka wuce Kano tare Aneeserh ke duk kina ina?."



Hajiya Aisha ce take jerowa Humaira waɗan nan tambayoyin, tun bayan barin su Aneeserh daga gidan babu daɗewa ita ma motar ta shigo gidan acewarta wurin Mijinta Aliyu tazo dama ya ce da ita Abuja zai fara zuwa before yaje Kano, shi ne fa yanzu Hajiya Aisha da Mijinta His Excel. Suka zaunar da ita a Palo Hajiya Aisha tana tambayar ta.



Ajiyar zuciya ta sauke tana Gyara zama saman carpet na Palon ta ce.


"Sorry Mommy and Daddy dama abin da yasa ban biyo Hayatie ba Oumun mu ce batajin daɗi acan Austaraliya, shi ne na wuce na duba jikin nata sai dai ma ta sama lafiya, eyya ban san har Hayatie ya bar nan ba.."






Maganar tayi garesu cike da tsantsan ladabi tana ƙasa da kanta.






Cike da mamaki His Excel... A karo na farko da ya yi magana a wurin ya ce.


"Ai dama ita Oumun taku bata da lafiya shi ne bata faɗa ba, an tura Doctor?."



"To Mun gode Allah tunda kince jikin nata ya yi sauƙi ina fatan kowa yana lafiya acan ɗin?."


Cike da ladabi ta kuma amsawa Hajiya Aisha da tayi maganar daga ƙarshe da faɗin.


"Eh duka suna lafiya, sun ce ma a gaishe ku."


"Yauwa Toh muna amsawa kam."



"Toh Mommy and Daddy zan wuce zuwa Kano ɗin banason dare ya yi min ban ƙari sa ba."



"Toh Humaira Dan Allah a kula kinji kuma ko mai zaki tarar a gidan ki daure koda bai miki daɗi ba kinji Ɗiyata?."






Kallon Hajiya Aisha Humaira take yi da mamaki na jin abin da ta faɗa sai dai ta daure ta amsa da cewa.


"Tohm shikenan Insha Allah."


Sallama suka yi sannan ba tare da bata lokaci ba. Driver ya wuce da Humaira zuwa Airport da zata hau Jirgin komawa Kano.


Yayin da Hajiya Aisha da mijin nata suka ci gaba da tattaunawa akan wannan lamarin.








Dama Humaira da Mahaifiyar ta sun kasance Ahalin Abokin His Excel... Ne wanda ya kasance ya rasu da daɗewa sakamakon 'yan damfara da ya samu suka masa Babbar cuta cikin kasuwanci da suka haɗa hannu gaba ɗaya Dukiyar sa ya rasa, sanadin haka ciwon zuciya da hawan jini yasa ba tare da jan lokaci ba ya rasu.
Sosai matar sa ta shiga cikin wani mummunar hali na rashin sa, saboda ita ɗin marainiya ce ba ta da kowa, hasalima a gidan marayu mijin nata ya ɗaukota suka yi Aure.
Ganin irin tashin hankalin da Ahalin abokin nasa suka shiga ne kuma ba shi da Burin sake Aure domin Matarsa ta ishe sa, yasa His Excel... Ya Aurawa yaron sa Aliyu Aishatul Humaira ɗiyar abokin nasa ta shiga matsayin ta Biyu domin lokacin an daɗe da Aura masa Yasmeen.
Daga nan ne kuma ƙannen ta maza biyu da mace guda ya fita dasu Austaraliya suna karatu shi ne ita ma Mahaifiyar tasu ta ce zata bisu kawai can ɗin ta ci gaba da kula da tarbiyyar yaran ta, dama kuma bata da kowa.
Ba da ɓata lokaci ba His Excel... Ya amince aka shirya Komai, mahaifiyar Humaira da ƙannen ta suka wuce Austaraliya.
Yayin da Humaira take gidan Aliyu matsayin matar sa ta Biyu....


*WANNAN KE NAN. IN BRIEFLY!!!*



*PRESENT.!!!!*




*ANEESERH*


*💥Aneeserh Just The Beginning.*💥



*Story $ Writing By:*✍️📚


*N $ N.*


*🔥💫Nanameera $ Nainarh KD.🔥💫*



*Ep-Fourteen*

Da sassafe ta tashi ta shirya ta saka kayanta amma kuma batasan mene ne abunda zatayi ba dan kwata-kwata tsoron sauka ƙasa take, tana nan zaune har kusan ƙarfe sha ɗaya ganin babu wanda yazo nemanta kuma ga yunwa data fara damunta yasa ta mike jiki babu ƙwari ta sauko duk ta koma asalin Aneeserh nta marainiya, zaune ta samesu suna taɓa hira wani matashin mutumne wanda aƙalla bazai shige shekarun G.A ba kuma sosai suke kama dashi kana gani ko ba'a faɗa maka ba kasan ɗan'uwansa ne, murmushi Khaleepa ya sakar mata yana kallonta ta sunkuyar da kanta ahankali ta ce

"Ina kwana?"

Da fara'arsa y ce" lpylao sannunki"


Shuru ta yi dan bai sake cemata komai ba kuma har sannan ko kallonta Aliyu bai yiba bare tayi tunanin zai kulata ganin haka yasa Khaleepa ya ce" zauna manaa Aneeserh" batayi musu ba dan daman ta gaji ta tsayuwar ta zauna ɗan nesa dasu sai asannan G.A ya ce" tashi kije ki karɓi abinci" ya yi maganar batare ya kalli inda take ba, jiki babu ƙwari Aneeserh ta miƙe ta tafi duk sai ta baka tausayi bayan ta shiga kitchen ɗin Khaleepa ya ce


"Gaskiya kada kace zakayi treating ɗinta hka coz batada laifi kuma ance a warware auren so dan Allah kamar yanda Daddy ya faɗa ka kula da'ita kaji" harararsa ya yi ya ce" ai sai ka sani na kula da itan ko ni nace su auran min ita? Me zanyi da wannan ƙaramar yarinyar" murmushi Khaleepa ya yi ya ce" kawai dan bakason auran yarinya ne amma ni banga aibun wannan yarinyar ba she's cute kuma ga hankali wlh ƙarshema tafi waɗannan gantafalfallun matan naka amfani" tsaki Aliyu ya yi sannan ya ce" kai ka sani" daidai nan Aneeserh ta fito hannunta riƙe da plate sai ɗan mug ɗin tea tana rarraba idanu dan ganin inda zata zauna bata damesu ba, ganin haka yasa Khaleepa ya ce" zo ki zauna mana Aneeserh" ok ta ce sannan ta dawo wajen da take da ta zauna tana ɗan satar kallon G.A ta fara cin abinci ahankali dan ba daban yunwar da takeji ba da haƙura zatayi.




Yesmeen ce ta fito tana kallonsu ta ce" sannuku da hutawa" "yawwa" suka amsa mata kallon Aliyu ta yi ta ce


"Wai dear wannan yarinyar fa naga kuna kama?"


Shuru Aliyu ya yi mata dan yasan halin surutunta, kwaɓe fuska ta yi ta ce" i'm.asking you"


"Ajiya aka bani ita kuma matata ce so becarefull" dafe ƙirjijta ta yi tana kallonsa baki buɗe ta ce" what!?"


Miƙewa ya yi dan daman yasan ita ce zata kawo masa ruɗani ya ce

"Abinda kikaji na faɗa haka maganar take babu ruwanki da ita ok?"

Yana gama faɗin haka ya kalli Aneeserh wacce tayi shuru sai kallonsu take ya ce" tashi ki koma ɗaki" batayi musu ba ta tashi ta wuce shikuma ya yi hakane saboda yasan halin Yesmeen ɗin, banda huci babu abinda take harma wannan ƙaramar yarinyar zai aura wato tunda su sun gaza bari asake sabon zubi tana wannan tunanin bata lurada sanda suka fita daga parlon ba saida ta ɗago zata yi masa magana taga wayam basu nan kwafa tayi sannan ta haye sama.




Aneeserh kam nan parlon ta zauna tagama cin abincinta dan daman ta takura zama tare dasu ɗin, bugun ƙofar da tajine yasa ta kalli ƙofar amma bata yi tunanin buɗewa ba, sosai Yesmen take bugun ƙofar zuwa sannan kuma Aneeserh ta fara tsorata da bugun kawai ta kifa kanta a cinyoyinta ta fashe da wani irin raunataccen kuka, duk rashin iyaye shine abinda ya jefata cikin irin wannan rayuwar kwata-kwata bata ganin zamanta dasu Excel matsayin cigaba musamman ma zamanta gidan G.A tabbas akwai wata ƙaddarar data kawota cikin irin wannan gidan kuma matsayin matar gidan, wani irin mahaukacin bugu Yesmeen takewa ƙofar duk Aneeserh ta ruɗe hakan yasa ta miƙe jikinta na rawa ta ƙarasa bakin ƙofar tana sake tabbatar da ita ake bugawa. Kwafa kawai ta yi sannan ta bar ƙofar ɗakin ganin ba'a buɗe ba.




Kai tsaye company ɗinsa na motoci suka shige bayan sun shiga cikin office ɗin Khaleepa ya ce" yanzu ya zakayi da yarinyar?" jingina ya yi da kujera ya ce" zuwa ta kammala karatunta zata zauna wajena tana ƙarasawa zan mayar masa da'ita dan ni babu abinda zanyi da yarinyar kamarta dan da nayi aure da wuri toh da tabbas na haifi kamarta"



Tuntsirewa ya yi da dariya harda buga table ya ce" ai mace bata kaɗan wlh tuni zata saka ka fita hayyacinka" tsaki Aliyu ya yi ya ce" banza mahaukaci kawai"

"E, naji wlh shawara ka gwadata ka gani amma tayi ƙarama da yawa kar ashiga haƙƙinta"

Tsaki G.A ya yi sannan ya ɓalle water bootle ya fara sha, saida ya kusa shanyewa sannan ya ajiye yana yin gyatsa ya ce


"Alhamdulillah, kai kuma na dawo kanka wlh koda desire zai kashe ni babu abinda zanyi da wannan yarinyar ni kallon ƴa nake mata bawai matata ba"


Girgiza kai Khaleepa ya yi ya ce" Allah ya bamu rai da lafiya"


"Ameen"



Sai kusan 10pm sannan convey ɗinsa suka shigo, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta bar jikin benen ta koma ɗaki. Babu kowa a parlon ya shigo kai tsaye ya shiga vip part ɗinsa wanda ko matan nasa babu wacce ta taɓa shiga shi kaɗai yake mu'amala awajen, yana gama shirin baccinsa ya fito cikin wasu pyjamas farare ƙal sunyi matuƙar amsar jikinsa musamman yadda duk wata hallita ta jikinsa ta fito ana gani tar,kai tsaye apartment ɗin ya nufa bai tsaya wani bugu ba ya saka key ya buɗe ɗakin. Bata cikin parlon hakan yasa ya shige cikin bedroom ɗin.



Zaune ya tararda ita tayi tagumi kana gani kasan cikin damuwa take sosai, dafata ya yi tayi saurin kallonsa tana bude idanuwanta,


"Kukan me kika yi?"

Sunkuyar da kanta ƙasa tayi bata ce komai ba ya ce" keee i'm talking to a daft?" girgiza masa kai tayi ta ce


"Dan Allah dan Annabi Abba ka mayar dani wajen Mommy banson zama anan"


Numfasawa ya yi sannan ya ce" wani abun akayi miki?"

Girgiza masa kai ta yi ya ce" then banason rigimar banza kin ci abinci?"

Girgiza masa kai tayi nanma ya ce" why?"


"Banajin yunwa kuma ni banason shinkafa"

Sakar baki ya yi yana kallonta jin irin nata rainin hankalin ya ce" sai ki kwana da yunwa" daga haka ya juya ya fita a ɗakin.


Kwanciya tayi kan gadon ta sake fashewa da kuka dan Allah ya gani tana jin yunwa kuma batason cin shinkafar shiyasa ma bata ciba, rumtse idonta ta yi jin yadda yake murɗa mata saboda rashin sabo da zama da yunwa tana wannan halin har Bacci ya yi awon gaba da ita.



𝐀𝐍𝐄𝐄𝐄𝐒𝐄𝐑𝐇.

*_𝐄𝐩.Fifteenth_*



*💥Aneeserh Just The Beginning.*💥



*Story $ Writing By:*✍️📚


*N $ N.*


*🔥💫Nanameera $ Nainarh KD.🔥💫*




*_𝐄𝐩.Fifteenth_*






𝐖𝐀𝐒𝐇𝐄 𝐆𝐀𝐑𝐈.



𝐀𝐑𝐎𝐔𝐍𝐃 6:50𝐀𝐌.



A hankali ta tura ƙofar Bedroom ɗin ta shiga, bakinta ɗauke da sallama ƙasa ƙasa ba tare da ta jira an amsa sallamar ba, ta cusa kanta ta shiga cikin Bedroom ɗin gaba ɗaya.


Zaune ta hangota saman Stool na Dress Mirror tana fuskantar Mirror da alama bata daɗe da fitowa daga bathroom ba domin bathrobe ne sanye a jikin ta.



"Wa'alaiki Salam lafiya dai na ganki a ɗakina da wannan sassafiyar ina fatan dai lafiya?."



Safeena ta faɗa Hakan ba tare da ta juya ta kalla Yasmeen da ta shiga Bedroom ɗin ba.



"No, akwai dalilin zuwa na, domin haka kawai bazan shigo Bedroom ɗin ki ba har sai da Dalili."



"Okay Tohm Ina sauraren ki."



Zama gefan Bed tayi tana Gyaran murya ta ce.





"Wai baki da labarin abin da yake faruwa ne a gidan nan?."


"Kamar ya ya ke nan, kiyimin Bayani yadda zan gane Please idan kuma ba haka ba ga hanya nan ni banason gulma wallahi da kike gani na ."




"Dalla Malama kema ai kinsan bana gulma ɗin, kawai dama faɗa miki zan yi wancan Yarinyar Aneeserh take ko wacece to matar Aliyu ce ba ƙanwar sa ba. Yes na faɗa Miki ne saboda idan baki sani ba ma ki sani Aha."



Yasmeen ta ƙari sa maganar tana kuma lura da yadda Safeena ta zaro ido cike da mamaki na maganganun ta ga dukkan alamu dai batasan da maganar ba sai wannan lokacin.



Murmushin gefan fuska Yasmeen tayi tana karkaɗa ƙafa ba tare da ta ce komai ba, yayin da Safeena ta kasa taɓu ka komai, kawai dai ta zuba ma ta ido ne tana kallo.











*ANEESERH P.O.V.*


Tun Bacci da ya ɗauke ta jiya da dare ba ita ta kuma farkawa ba har sai safiyar yau da ta kasance Jumma'a sannan kuma kwanakin ta na biyu ke nan a gidan General Aliyu Yayan ta kuma Mijinta.



Zama ta ci gaba da yi saman Sallaya tun bayan idar da Sallahr Asuba da tayi, sannan tayi azkhar nata kamar Kullum.







Tanajin yadda cikin ta ke faman ƙugi na yunwa amma ta kasa ta tashi balle ta nemawa kanta abin da zata saka a bakin sallati sai faman zare ido take yi tana ƙara tabbatar wa da lokacin period nata kwanakin sun kusa shiga tunda take a Rayuwarta sau ɗaya ta taɓa yi kuma baizo ma ta, ta sauƙi ba domin sosai tasha Azaba, shiyasa har batasan tunawa da lokacin domin ita kaɗai tasan kalar wahalar da ta sha na ciwon mara.






"Wayyo ni Aneeserh ya ya zan yi da rayuwata ke na?."


Tayi ma kanta tambayar da babu mai bata amsa.


Shiru tayi yayin da take sauraren bugun zuciyarta cikin Rashin abin yi daurewa kawai tayi sannan ta miƙe tsaye da dabara, folded na sallayar tayi sannan ta mayar da shi ma'ajin sa ba tare da ta cire hijabin Sallahr dake jikinta ba ta kama hanya, murɗa handle ɗin ƙofar tayi sannan ta buɗe ta fita gaban ta bai dena bugawa ba.





"Ke Aneeserh kike ko, come here."


A firgice ta juya tana kallon saitin wurin da ta jiyo Muryarsa mai cike da amo da ya yi ma ta magana.


Taɓe baki tayi cike shagwaɓa kamar mai shirin fashewa da kuka ta fara tafiya a hankali har ta ƙari sa Dining Room ɗin taja tunga ta tsaya yayin Mutanen dake Dining ɗin suka bita da kallo.

Sosai Humaira take ɓoye dariya domin lamarin sosai yake bata dariyar wai wannan 'yar halittar dake gaban su ita ce Mata ta huɗu a wurin mijin su G.A. lallai kam da alama iyayenta sun gaji da ita ne Tabbas, ta ayyana hakan a ranta tana kuma kumshe dariya.



Yayin da banda ido babu abin da Safeena take bin Aneeserh da shi.


Ita kuwa hamshaƙiya Yasmeen zuba mata ido kawai tayi tana so taga ta yadda Yarinyar zata moru ƙarama da ita ban da abin iyayen Aliyu ma abin da su suka kasa ne wannan kucakar zatayi, qwafa kawai taja cike da takaici.😒






"Hey you, how are you feeling today?."




Cikin rawar baki kaɗan ta amsa masa da faɗin.


"Am Okay Abba na."🤨


Da mamaki matan Aliyu suka kalleta jin sunan da ta kira sa da shi, sai dai babu wacca ta iya cewa komai, Murmushi kaɗan da bai bayyana ba, ya yi domin yana lura da Reacted na kowa, mayar da kallon sa ya kuma yi kan Aneeserh sannan ya ce.


"No, you're not okay, kinji abinci ne?."


"A'a, ban ci ba."


Ta basa. amsa.


"Okay,

Please Login or Register in order to submit comment