Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakiji abinci ba amma kince kina lafiya ko, ya yi miki kyau, zauna anan?."


Ya yi maganar yana ma ta nuni da kujerar dake gefansa.


Zama tayi a ɗar ɗar sannan ta fara buɗe food flasks dake jere a Dining ɗin tana neman abin da zai yi ma cikin ta daidai.



Ta gefan ido yake kallon ta sai dai bai kuma cewa komai ba. Haka ma sauran matan sa dake wurin. Ita dama Aneeserh yanzu ba surutu take so sosai ba, mayar da hankali tayi wurin cin abincin ta bil-haƙi.







𝐀𝐑𝐎𝐔𝐍𝐃 10:30 𝐀𝐌



Gajiya da zaman palon da tayi ne tsuru da ita yasa ta miƙe tsaye tana kallon sa ta ce.


"Abba na, na gaji zan koma Bedroom ɗina."


Ba tare da ya juya ya kalle ta ba, ya amsa ma ta da faɗin.


"Okay take care."



Bata ce komai ba ta juya ta koma zuwa Bedroom ɗin ta dama a takure take tun lokacin da ta kammala Breakfast nata taso ta koma Bedroom ɗin amma ya hanata da faɗin ta zauna a Palon tare da su nan ne yake faɗa ma ta kaɗan daga cikin tsarukan Gidan nasa, wai duk sati Ranar Jumma'a ke nan kamar yau, haka ake yi ba ya fita Office ko wani wurin sai dai zuwa Masallaci, bayan ya dawo kuwa yana gida tare da matan sa a Palo suna fira idan akwai mai wata maganar ma sai tayi anan, ita dai Aneeserh amsa masa kawai tayi a lokacin badan ta gama fahimtar abin da yake faɗa ma ta ba. Domin bata hayyacinta sama sama takejin ciwon mara na taso ma ta sai dai ta daure.


Tana shiga Bedroom nata ta garƙame da key, zama tayi gefan Bed idanunta na kallon ƙasa yayin da fara lulawa Duniyar tunani, Allah Sarki Baiwar Allah sosai takejin kewar Hajiya Aisha Mommy har dama His Excel. Uncle nata sai dai kewar iyayenta ya shanye wannan, shawara kawai ta yanke akan zata sama G.A da maganar ya taimaka ya sai ma ta waya ko dan ta dinga gaisawa da Mommy.






*IN BRIEFLY.*


Haka dai Rayuwar Aneeserh ta ci gaba da kasancewa a gidan General Aliyu Yayanta kuma miji a gare ta, cikin matan sa masu mabanbanta halaye, tsakanin ta dasu sai dai ido domin ko gaishesu ma da take yi da farko zuwa yanzu ta dena domin ta fahimci ba ƙaunar ta suke yi ba, tsakanin ta da uban gayyar wato G.A Gaisuwa kaɗai ke haɗasu wasu lokutan ma saita kwana ta wuni bata gansa ba, sai dai lokaci bayan lokaci Khaleepa yana kawo ma ta ziyara kuma sosai takejin daɗin hakan musamman ma lokacin da ya zo da matar sa har da Yaron sa ƙarami. Ta gefe guda kuwa duk yadda taso akan ta sama Aliyu da Maganar ya sai ma ta wayar kasawa tayi domin mugun tsoron sa takeji ga mugun kwarjini da yake ma ta, cikin sati guda da zuwan ta Kano komai ya kammala na komawar ta school cikin Iko da nufar Ubangiji Aneeserh ta fara zuwa School Driver yake kaita ya dawo da ita....






*💥Aneeserh Just The Beginning.*💥



*Story $ Writing By:*✍️📚


*N $ N.*


*🔥💫Nanameera $ Nainarh KD.🔥💫*





*ANEESERH*


*💥Aneeserh Just The Beginning.*💥



*Story $ Writing By:*✍️📚


*N $ N.*


*🔥💫Nanameera $ Nainarh KD.🔥💫*




*Ep-Sixteen*




Da sauri tashige ɗakinta tana riƙe mararta saboda wani azababben ciwo da take mata, kwanciya tayi ƙasan carpet ta baje kamar wata gawa hankali kuma ta fara kuka tana sake riƙeta dan ji take kamar ranar mutuwarta ce tazo

"Wayyo Ummina!! Wayyo Abbana!! Wayyo Yayana wlh mutuwa zanyi wayyo Allah cikina na shiga uku zan mutu"


Abinda Aneeserh ke furtawa kenan tana sake rushewa da kuka har lokacin sallar magrib ya yi tana nan ta kasa tashi. Fitowa ya yi dan tafiya masallaci kamar wanda aka yiwa dole ya ƙarasa jikin ƙofar apartment ɗin nata, tura ƙofar ya yi bakinsa ɗauke da sallama yana ƙarewa ɗakin kallo. Hangota ya yi kwance daga gefe kamar wata matacciya da mamaki ya ƙarasa yana kallonta dan batasanma ya shigowa ba

"Keeee!"

A firgice ta ɗaga kai ta kalleshi sai kuma ta sake fashewa da sabon kuka tana miƙo masa hannunta ta ce" Abbana ka taimakeni zan mutu cikina zai cire" ɗagota ya yi ya jinginata ƙirjinsa yana kallon fuskarta wacce duk ta kwaɓa da kuka ya ce" lafiya?" cikin kuka ta ce "cikina ne yake ciwo zan mutu kuma" girgiza kansa ya yi danshi a ganinsa shirmene irin nata wanda ta saba ya miƙe yana kallinta ya ce" tashi tsaye" kwaɓe fuska ta yi zata fashe da kuka ya ce" idan kika yimin kuka sai na zaneki, tashi nace" kujera ta kama ahankali kamar wata mai ciki ta miƙe kallon inda ta tashi ya yi kafin ya yi mata magana ta tafi tayi baya luuuuuu kafin ta ƙarasa ƙasa ya riƙeta yana kallonta bai ɗauka period take ba dan shi iya zatonsa ma tayi ƙarama da period, rasa yanda zai yi da ita ya yi gashi lokacin sallah na shigewa tsaki ya yi sannan ya ɗauketa kamar Baby ya shige Bathroom ɗin da ita, saida ya yi mata wanka lokacin ta farfaɗo ya bata kaya da pad ta saka sannan ta sake kwanciya.


Fita ya yi ya koma wani ɗaki wanda yake kamar chemist ya ɗauko allura da drip ya fito, a hanya Yesmen ta ganshi tana kallon abin hannunsa ya ratsa ta gefenta ya yi wucewarsa dan yasan yanzu saita saka shi magana har sannan Aneeserh na kwance sai kuka take ya shiga ɗakin wata kyakyawar tsawa ya daka mata ya ce

"Kimin shiru shashasha kawai ko yau kika fara haila da zaki dameni" haɗiye kukanta ta yi saboda yanda ta tsorata da tsawar gashi dai Allah shine shaidarta akan irin ciwon da takeji amma shi ko ajikinsa bazaka taɓa cewa yarinyar ta raɓeshi ba ko sau ɗaya bai cemata sannu ba har ya gama ɗaura mata drip ɗin da allurar, ita kanta ta yi mamakin irin dauriyar da tayi har ya yi mata allura batayi kuka ba ya kwashe kayansa ya yi waje lokacin kusan ƙarfe 7:06 dole ya koma ɗakinsa ya yi sallar acan.




Wajejen ƙarfe goma ya shigo domin cire mata drip kwance ya tarar da ita har sannan kuma bata daina kukanba tsaki yayi sannan ya zauna gefen gadon yana kallonta ya ce" miƙe zaune" bata yi musu ba ta kama fuskar gadon ta miƙe zaune ta jingina da jikin gadon miƙe mata plate ɗin hannunsa ya yi ya ce"ci" batayi musu ba ta karbi abinci ta buɗe Jallof rice ce sai peppersoup ɗin offals da aka watsa akai sai kaza kusan rabi, kallon abincin ta tsaya yi ya ce" kee jiranki fa nake" ahankali ta fara ɗiban abincin tana kaiwa bakinta ko loma uku batayi ba ta kauda kanta tana ajiyewa kan bedside drawer ɗin, wani banzan kallo ya yi mata ya ce" i'm play with you?" girgiza masa kai tayi kafin ya sake magana ta fara yunƙurin amai, da mamaki yake kallonta dan bai gane wannan abun nata ba bai kai ga taɓuka komai ba ta fara kwarara masa amai anan inda take



Shuru G.A ya yi yana kallon ikon Allah har ta gama aman sannan ya kaita banɗaki ta wanke bakinta ya gyara wajen, wani zazzaɓine ya rufeta jikinta ya fara kakkarwa ya ce"fita muje" bin bayansa ta yi suka fita daga ɗakin



Bedroom ɗinsa ya shiga ya ɗauko car key ɗinsa sannan ya yi gaba tana biye dashi abaya har suka isa parking lot ɗin gidan, guards ne suka taso ya ɗaga masu hannun ya buɗe mata motar ta shiga sannan shima ya zagaya ya shiga ya bar gidan...



Sakin labulen tayi sannan tayi kwafa wato har zai fara nuna musu banbanci a tsakaninsu wlh kam da sake ta furta aranta sannan ta koma ta kwanta, sai kusan ƙarfe 11pm sannna suka dawo gidan lokacin har bacci ya ɗauketa dalilin allurar da likita ya yi mata, a hannunsa ya ɗauketa tamkar wata Baby ya ashiga cikin gidan, zaune ya samu Safeena da Yeemen suna hira amma bazaka ce ga hirar da suke ba, kallo ɗaya ya yi musu ya shige ciki suka bisa da kallo baki sake saida ya haye sama sannan Yeesmen ta ce


"Kin gani ko wlh ya mayar damu ƴar iska"

Taɓe baki Safeena ta yi bata ce koma ba. Master bedroom ɗinsa ya shige da ita ya kwantar da ita kan haɗaɗɗan royal bed ɗin nasa na alfarma karo na farko kenan da wani ya kwanta akai bashi ba.




Aneeserh bata farkaba sai wajen ƙarfe 3:30am lokacin yana zaune kan dadduma bayan ya idar da salloloinsa, zama ta yi tana kallonsa har ya gama sannna ya kalleta ya ce" lafiya?" girgiza masa kai ta yi ya ce" ya yi sauƙi marar?" hawayene ya zubo fuskarta ta ce" zafi ya kemin Abba" tasowa ya yi ya zo wajenta ya tsaya yana kallonta ganin duk ta rame daga yammaci zuwa sannan


"Ki kwanta zai saida duka"

"Fitsari zan yi Abba"

Kama hannunta ya yi ya kaita banɗakin sannan ya fito tana gamawa ta fito ta sake kwanciya nan da nan bacci ya ƙara ɗauketa.




*Washe Gari.*


Kallonta ya yi har ta karaso ta tsuguna ta gaishesa sannan ta ce" Abba zan tafi makaranta" "kinji sauƙi?" gyaɗa masa kai tayi ya ce" toh zauna ki fara breakfast sannan" zama ta yi kan kujera sannan ya miƙo mata plate mai ɗauke da soyayyen kwai sai chips agefe


"Ki saka sugar kaɗan" gyaɗa masa kai ta yi sannan ya cigaba da cin abincinsa ɓakinciki ne yasa ta miƙe fuuuu ta bar wajen ya bita da kallo sannan ya taɓe baki.


Tana gama cin abincin ta kalleshi ta ce"Abba nagama" ɗago kansa ya yi daga kan wayar hannunsa y ce" kije ki kwanta zuwa gobe sai ki tafi makarantar" hawayene ya kawo idonta ta ce" dan Allah Abba ina son naje please" girgiza mata kai ya yi zata sake magana ya ɗaga mata hannu yana nuna mata hanyar ɗaki ya ce" je ki" tashi tayi jiki asanyaye ta koma part ɗinta




Tana shiga ta zauna kan kujera ta fashe da kuka sai da ta yi mai isarta sannan ta kwanta nan da nan bacci ya yi awon gaba da ita.






****

Tsaki ya yi ya ce" nifa ba haka nake ba Khaleepa wlh bazan iya haƙura na zauna da wannan yarinyar ba ai yazama abun kunya kenan duk abokai na su dinga ganinta ace matata ce ko?"



Murmushi Khaleepa ya yi ya ce" shikenan tunda haka ka zaɓa amma idan nine kai haƙura zanyi na tabbata akwai abinda su Daddy suka hango wanda kai baka hangoshi ba" ɗaga kafaɗa ya yi ya ce" ni wannan bai dameni ba kawai banason abu banaso period"



Da gudu Sabeer ya tawo ya rungumeshi, ɗaga shi sama ya yi yana dariya ya ce" my boyy ka ɓuya" dariya Sabeer ya yi ya ce" ba Daddy bane yaƙi kawoni kullum idan nayi masa magana sai yace sai anyi hutun school" kallonsa Aliyu ya yi ya harareshi ya ce"rabu dashi yau ko yana so ko baya so sai muntafi tare" murmushi ɗauke afuskar kyakkyawan yaron ya ce" thank you Abba"




Fashewa ta yi da sabon kuka ganin irin yanda jinin jikinta ke tafiya abanza ita bata taɓa irin haka ba arayuwarta, tayi amfani da pad aƙalla guda biyu daga dare zuwa yanzu duk ta zuge ta rame. Ana idarda sallar magriba suka shigo gidan da kallo Sabeer ya bi duk matannasa yana ganin Humaira ya tafi da gudu ya rungumeta murmushi ta yi ta ce" oyoyo Love sai yau?" " wlh Aunty sai yau Abba ya tawo dani da Dad ya hanani" ok ta ce sannan ta riƙe hannunsa suka shige part ɗinta shikuma ya haye sama.



Har ya yi gaba sai kuma ya dawo ya buɗe ɗakin ya shiga, durƙushe ya tarar da ita gefen gado


"Wai ke har yanzu baki ji sauƙi ba?"

Hawaye na gangarowa kan kuncinta ta ce.


"Ciwo yake min sosai Abba."

Tsaki ya yi sannan ya juya ya fita dan ɗauko ma ta magani.



https://chat.whatsapp.com/J3EAYvZGXUxKkXHsRRvrpS


_Innocent Girl_
*ANEESERH.*


BY
AMEENAH I IBRAHEEM
(Nanameera)
And
KHADEEJARTH SABI'U YAHYAH
(Nainarh KD)


*EP_Seventeen.*



*IN BRIEFLY.*


Haka dai Rayuwar Aneeserh Baiwar Allah ta ci gaba da kasancewa a cikin gidan General Aliyu Yayan ta kuma Mijinta da take kiransa da Abbanta a koda yaushe kuma ta ɗauke sa a matsayin hakan.


Ta ci gaba gudanar da Rayuwarta a cikin gidan tare da matansa uku kuma wacce halinta ya bambanta dana 'yar uwarta kaf cikinsu Yasmeen ce take mugu mugun takurawa Aneeserh cikin zamanta a gidan, tsakaninta da Humaira sai dai kallo dan bata cika zama a gidan ba ma tana fita Office. Yayin da ita kuma Safeena babu ruwanta da kowa sai dai taci tasha ta kwanta a palo ta yi kallo tahau online aikin ta ke nan a kullum ko girki ma ba ita keyi ba 'yar aiki take yi ma ta duk Ranar da ya kasance ita ke da girkin.


Aneeserh ta ci gaba da zuwa school nata tana fafata Karatu Yayin gefe guda kusan duk sati sau uku zuwa huɗu take waya da su Mommy da Uncle nata His Excel...




*Wannan Ke Nan...*



*Abuja, Nijeriya.*



Da mamaki ta kuma kallonsa a karo na biyu da jin abin da ya kuma faɗa cike da takaicin raina ma ta da yakeon yi ta ce.






"Saima suna na kuma Kaduna State nake ni ce make-up artist ta Gidan Hajiya Aisha nake yiwa aiki kuma ni ba 'yar aiki bace domin duk wata Dubu ɗari Biyar nake ɗauka a matsayin salary nawa, kaga ko nafi ƙarfin 'yar aiki, sannan kuma ni ba Yarinya bace domin shekaruna Ashirin da Biyar ehee."





Tayi tana murguɗa masa baki kaɗan domin ta lura wannan mutumin akwai rainin wayo da yawa akan mai ma zai kama ya kira ta da 'yar aiki kuma Yarinya ai ba za ta lamun ta ba shiyasa ta saki jiki ta yi masa bayani idan ya fahimta ruwansa.





Kama Hanya ta yi zata bar wurin sai dai a bazata taji ya riƙo hannunta ko kafin ta yi wani yunkurin ya janyo ta zuwa cikin Garden.


"Wayyo Hajiya Aisha zoki taimakeni wayyo ni kwartt....."😳


Cikin sauri ya kai hannunsa ya toshe ma ta baki cikin zaro ido da Magana ƙasa ƙasa ya ce.


"Ke baki da hankali ko wato ni ne ma zaki kira da kwartt......"🤨


Shiru ya yi ba tare da ya ƙari sa ba.



"Ni ka sakeni, ka ƙari sa faɗa mana in ba hakan ba mai zai sa ƙaton gardi kamar ka mara mata ka janyo budurwa kamar Ni cikin nan wurin."



"Bazan sake ki ba ɗin."


Kuka ta saka masa ta ce. "Saboda me?."


Murmushi ya yi yana ɗan sassauta riƙon da ya yi ma ta ya ce.


"Ko ki nutsu da kyau na faɗa Miki abin da ke Zuciyata ko kuma mu ci gaba da kasancewa a haka muga wanda zai gaji."







Sanin halinsa da ta yine da kuma tuna cewa Hajiya Aisha tana neman ta domin zuwa anjima zata fita zuwa wurin taron auren wata ɗiyar ƙawarta kuma ita ce zata ma ta make-up kamar kullum yasa Saima ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce.


"To na nutsu ai."



"Good Girl."


Ya faɗa sannan ya umarce ta da ta zauna.



Tana zumɓura baki ta zauna saman ɗaya daga cikin Chairs na hutawa dake garden ɗin, sannan shima ya zauna gefanta kaɗan.


"Ki Aure ni."



Ya faɗa lokaci guda kuma babu alamar da wasa ya yi maganar a gare ta.


Kallon amma dai baka cikin hayyacinka take bin sa da shi tsaban mamaki ma ta kasa ta ce masa Komai.


Da sauri ta miƙe tsaye har tana tuntuɓe ta fi ce daga Garden ɗin ko waigen sa ba tayi ba, yayin da ya bita da kallo yana lumshe ido. Yarinyar tanason wahalar da zuciyarsa gashi baisan ya nema abu ya rasa ba a Duniya tun tasowarsa har izuwa yanzu.






"Saima lafiya kuwa kika shigo kamar wacce aka koro?."



Tana sauke haki na gudun da tayi ta zauna a sofa tana faɗin.


"Babu Komai Her Excellency kawai dai na ɗan tsorata ne sakamakon ganin snake da nayi a garden gashi kuma ya gudu."


Ta faɗa hakan ba tare da ta kalla Hajiya Aisha ɗin ba dan gudun karta ganota.



"Ayya, snake kuma zuwa anjima zan saka securities su duba bai kamata ana samun irin su a Garden ba."



"Ai gaskiya kam ya kamata a gaggauta dubawa a fitarda shi daga Gidan nan domin hatsari ne ga 'yan mata iri na."




Tayi maganar tana ɗauke idanunta akan Jay da shigowar sa Palon ke nan.



"Akan menene ake magana haka naji ana cewa a fita da shi?."



Juyawa Hajiya Aisha tayi tana kallon sa da mamaki ta ce.


"Jay! Yaushe kuma ka shigo Gidan dama kana Nijeriya?."



Ta jero masa tambayoyin lokacin da yake zama saman Sofa 2 sieter ya kalleta sannan ya bata amsa da faɗin.



"Yanzu Yanzu na shigo fatan na sameku lafiya?."


Ya ƙari sa maganar yana kashewa Saima da ta saki baki tana kallon sa ido.



"Ah Hajiya Ina ga kizo mu fara make-up ɗin tun yanzu lokaci fa yana ja."



Saima tayi maganar lokacin da Hajiya Aisha ta buɗe baki da niyyar ta yi masa wata maganar. Ajiyar zuciya Hajiya Aisha ta sauke ta ce.



"Dama ai kece kika tsaya jan lokacin yanzu tunda kin shigo sai a yi kawai."






*Kano, Nijeriya.*






Watannin Aneeserh Biyu ke nan a Garin Kano zuwa yanzu sosai ta saba da Khaleepa da kuma Matarsa Hafsat da Yaron su.


Zamanta da G.A kuwa ba'a ce komai ba, domin sai ta kwana biyu ma basu haɗu da shi ba sai dai idan taji tanason magana da su Hajiya Aisha ne shi ne zata nemesa da maganar, idan yaga dama ya bata wayar ta kirasu su gaisa, wasu lokutan kuwa idan yanajin tsiya hana ta yake yi sai dai taci kuka ta gode Allah.



Zuwa lokacin Yasmeen ta fara saukowa akan kishin da take gwadawa akan Aneeserh gane cewa da tayi da gaske Aneeserh bata gaban mijinta General Aliyu, zuwa lokacin tunaninta ya koma ne akan yadda zata raba sa da gaba ɗaya matan nasa cikin sauƙi ba tare da Asirin ta ya tuno ba.😳🙄


Humaira kuwa ta ɓangaren ta sosai suke shiri ita da Mahaifiyar ta akan yadda zasu sace wasu files na wurin aikin sa masu matuƙar muhimmanci a wurin Aliyu wanda akan hakan ne kaɗai Burinsu zai cika.


Safeena kuwa wannan 'yar daɗi Miji ce duk abin da Aliyu yakeso ita ma shi take so, haka ma abin da yaso tofa wannan abun baya burgeta sam, shiyasa shima yake ji da ita bata da Hayaniya bata da gulma barta da son jiki kawai da rashin iya girki.



A cikin wannan taƙin ne Aliyu ya yi tafiya zuwa ƙasar Paris sannan bai faɗa musu ga adadin kwanakin da zai yi ba, sannan kuma da Safeena ya tafi kuma Hakan ba ƙaramin fusatar da zuciyar Yasmeen ya yi ba, kawai daurewa ta yi ta nema ƙawayen ta Sabeera da Suhaila domin su bata shawara.







Aneeserh sanye take cikin Riga Top white Mai gajeren hannu sai kuma wando jeans crazy white and black color ta ɗaure dogon gashin kanta da ribbon tayi packing ɗin sa a tsakiyar kanta ba tare da ta saka hula ba, fitowarta ke nan daga Garden hannunta ɗauke da guava da alama bishiya ta hau ta tsinko.


Murmushi tayi hango Umaru mai bawa flower's Ruwa da tayi, kaf cikin ma'aikatan gidan tafi shaƙuwa da shi, sakamakon sunan Yayan ta Umar da yake da.


Cikin sauri ta ƙari sa wurin sa cikin washe baki ta ce.


"Barka dai Yayana aiki kaketa sha ne haka kawo na tayaka bawa flower's ɗin Ruwan."


Tayi maganar tana ƙoƙarin karɓar abin bawa flower's ɗin Ruwan dake hannunsa.


Kallon ta ya yi yana Murmushi ya ce.



"A'a dai ƙanwata na huta ce ki fa, kije ki ci guava da kyau ki barni da aikina anan."


Murmushi tayi tana faɗin.


"Kai Yaya Umar to shikenan na tafi sai anjima."



Tayi maganar tana juyawa domin shiga cikin palon gidan, sai dai jin ta yi karo da Mutum ne ta bugi faffaɗan ƙirjin sa, yasa ta ɗa go kanta da sauri cikin zare ido take kallon mutumin dake gaban ta....








*ANEESERH*

*Ep-18*


Da sauri tayi baya tana kallonsa tayi zilli gidi-zilli gidi da'ita batareda yace komai ba ya kama hannunta ya hau figarta har cikin gidan, tsabar yanda ta tsorata ko kuka ta kasayi yana zuwa ya yi wurgi da'ita a parlon yana mata Wani mugun kallo, tsayawa sukai suna kallonsa dan ce musu ya yi wajen Khaleepa zashi, hannunsa yasa ya ɗagota batayi auneba taji ya wanketa da wani kyakkyawan mari dan har saida taga stars a fuskarta, kasa yin kuka tayi ta koma baya tana riƙeda kuncinta tana sakin ajiyar zuciya cikeda bala'i yake cewa


"Wato ke mara hankali ko?, ke ga mahaukaciya ko?, ba kisan mene ne yake miki ciwo ba uban wane ya baki damar fita daga cikin parlon nan har kitafi kina hira da maid?"



Shuru Aneeserh tayi dan sai a sannan tagane laifin data aikata jikinta sai rawa yake


"I'm talking to a daft?"

A tsawace ya yi maganar dan duk saida suka tsorata yanda idanunsa suka sauya kala shine zai nuna maka irin ɓacin ran da yake ciki, kwafa ya yi sannan ya kalleta ya ce" na fuskanci ke yanzu kika fara iya naki haukan to zanyi maganin duk rashin hankalin da kike famada wlh idan baki nutsu ba ruwa sai kin gagara sha cikin kwanciyar hankali a gidan nan shashasha mara hankali kawai" yana gama faɗin haka ya juya ya yi fitarsa. Sai a sannan ta fashe da wani irin kuka tana shafo fuskarta domin ita tunaninta fuskar fashewa tayi da kallo suka bita kowacce ta kama gabanta dakyar Aneeserh taja jiki ta haye sama tana riƙe da fuskarta



Kallonsa Khaleepa ya yi ya ce

"G.A what's wrong with you naga ranka a ɓace?" kwafa Aliyu ya yi bai ce komai ba kuma daman yasan ba lallai ya magantuba, murmushi ya yi ya ce" kodai kaida ƴar rainon taka ne?" tsaki ya yi ya ce" kasan Allah nan bada jimawa ba zan mayarda yarinyar nan dan idan ina ganinta tana yimin wani abu wallahi wataran saidai a ɗauki gawarta sabida yanda nakejin haushinta bataji ko kaɗan yarinya kamar sheɗaniya" girgiza kai Khaleepa ya yi ya ce


"Dan Allah ka dinga sakawa zuciyarka haƙuri i know zamada yarinya akwai ƙalubale amma tunda har ta dawo wajen naka kuma bazata ƙara kwanakin da tayi abaya ba dan Allah kayi haƙuri yanzu fa third term suka shiga kwata-kwata four months akeyi kuma yanzu sunyi 2months kaga idan kayi haƙuri nan bada jimawa ba zata koma hannun Daddy ta cigaba da rayuwarta karka manta yarinyar nan marainiyace kuma batada wasu shekaru dole sai kana haƙuri"


Furzar da iskar bakinsa ya yi ya ce" bazaka gane bane bakasan halinta bane dan badakai take zaune ba wlh inaga da tuni ka koreta saboda halinta" murmushi Khaleepa ya yi ya ce" ni ka kawomin ita mu zauna tare" harararsa ya yi ya ce" ba haka nake ba"



Tanajin ana kiran sallar magrib amma ta kasa tashi tayi sallah saboda wani zazzaɓi ya rufeta jikinta sai rawa yake dakyar ta lallaɓa ta mike lokacin anfara kiran isha'i tana dafe kanta saboda wani ciwo da yake mata ta shiga banɗakin, a daddafe ta idar da sallar ta jingina da jikin gado ta rushe da wani irin kuka mai tsuma zuciya tabbas rashin iyaye masifane bata taɓa tunanin haka zata kasance da rayuwarta ba bata taɓa tsammanin rabuda da iyayenta a wannan lokacin ba sannan ta ɗauka matsalar ta kau bayan ta hadu da His excellency ashe sannan ne matsalar zata fara tana zaune nan har kusan ƙarfe 9pm lokacin yunwa ta fara damunta ga kuma tsoronda take ji karta sauka taje ta tarar da G.A yana ƙasan dan taji sanda ya dawo gidan. Daga ƙarshe haƙura tayi da abincin ta linke daddumar ta ajiye sannan ta kalli fuskarta jikin dreesing mirror ɗin dake maƙale a ɗakin sosai fuskarta ta yi wani Ja ta kumbura duk shaidar yatsu akanta taɓa fuskar ta yi hawaye na zirarowa kan kuncinta ta tafi ta kwanta tana lumshe ido wasu zafafan hawaye suka shiga sakko mata haka har bacci ɓarawo ya saceta.






Da safe bayan tagama shirin makarantarta ta sauka dukda yanda take jin jikinta babu daɗi, gabantane ya faɗi ganinsa da tayi zaune kan kujera yana operating laptop Safeena na zaune gefensa dakyar ta ƙarasa sakkowa tana tafiya kamar mara gaskiya har takai bakin ƙofar


"Keeeee!"

Da sauri ta juyo ta kalleshi taga ya kafeta da ido ta sunkuyar da kanta tana wasada fingers ɗinta har batasan sanda ya iso gabanta ba hucin mutum kawai taji tana ɗaga kai suka haɗa ido dauke nata tayi dan ko san

Please Login or Register in order to submit comment