Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganinsa batayi, kallaonta ya shiga yi from head to toe ya kalli fuskarta dukda ta sace amma shaidar tafin hannunsa tana nan raɗau a fuskar


"Ina kika shirya zuwa?"

Tambayar da ya yi mata kenan yana kafeta da ido, sunkuyar da kanta ta yi ta ce


"Makaranta zani"


Harararta ya yi ya ce" zoki shige ciki" ya faɗi maganar yana nuna mata hanyar parlon hawayene ya taru a idonta ta ce" dan Allah Abba yau test zamuyi kuma idan banyi ba malamin bazai sake yimin ba"



"Oh really?"


Sauri gyada masa kai ta yi ya ce" idan kika kuskura na ƙirga uku kina tsaye anan wlh sai ranki yayi mugun ɓaci shashasha kawai" tana riƙe bakinta gudun kada tayi kuka tashige cikin parlon da gudu ta koma sama tana zuwa ta waɗa kan gadon ta fashe da wani matsananincin kuka.




"Ina Aneeserh?"


"Tana bacci Mommy idan ta tashi zan kiraki sai ku gaisa" ok Mommy ta ce sannan sukai sallama. Ajiyar zuciya ya sauke dan bayason ko kaɗan aga gazawarsa wajen rikon yarinyar har sanda zai maida ita. Murmushi Yesmeen ta yi ta ce" wai dear yaushe zaka mayar musu da ƴar su?" kallonta ya yi sai kuma ya ce

"Daman akanki take bansani ba?"

Murmushi ta yi ta ce" kawai tambaya nayi yallaɓai"


"Tom babu ruwanki ko yaushe zan mayar daita koma anan zata ƙari rayuwarta" saurin kallonsa ta yi ta ce" Allah ya baka haƙuri mai da wuƙar".



Sai azhar sannan ta farka tayi wanka ta gabatar da sallah shiryawa ta yi cikin wata atampa super holland green da adon baƙi ta ɗaura ɗankwalinta tayi kyau abinta amma kwata-kwata zuciyarta babu annuri.



Zaune ta tarar dasu kamar dole sai an zauna atare saida ta kalli gefenta sannan taga G.A zaune ya tankwashe ƙafa ana ajiye abincin kala-kala gabansa, tsayawa tayi tana kallonsu da mamaki dan ita bata taɓa ganin wannan abun ba tashi sukai suma suka zauna kusada shi kowacce ta ɗauki plate ta zuba abinci, kallonta ya yi yaga ta juya zata koma sama ya ce

"Aneeserh!"

Juyowa ta yi ta kalleshi sai kuma ta ƙaraso gabansa ta tsuguna kanta ƙasa

"zauna kici abinci"

Kallonsa ta yi sai kuma ta ce"naƙoshi Abba" wani kallo ya yi mata daya sanya ta shiga nutsuwarta ya ce


"Zauna nace" bata kuma musu ba ta zauna daga gefe tana bin kowa da kallo haka kawai taji abincin na saka mata tashin zuciya musaman naman da tayi ido biyu da,


Abincin ya zuba mata yana kallon fuskarta ya ce"oyha take it" karɓa tayi amma batayi yunƙirin ciba ta ajiye gefenta ta cigaba da kallonsu saida ya gama cin abincin sannan ya kalleta yaga ko taba abincin bata yi ba


"Keee, ni sa'an wasanki ne?"

Girgiza masa kai tayi ya dauki abincin yana kallonta ya ce

"Open your mouth"
Sauke idanunta ta yi sai kuma ta buɗe bakin nata a hankali ya zuba mata abincin domin shi duk abunda zaku yi dashi baya lamuntar zama da yunwa dole sai kaci abinci. Haka ya cigaba da feeding ɗinta har ta ƙoshi dukda yanda zuciyarta ke tashi bata nuna masa ba saida suka gama ci, da gudu ta ƙarasa toilet bayan tashiga parlon tana zuwa ta hau kwara wani irin amai, duk abunda taci saida ta amayar dashi a hakama kamar ta amayar da hanjin cikinta saida tagama aman sannan ta zauna banɗakin tana sauke numfashi dakyar ta tashi ta wanke bakinta sannan ta fito daga banɗakin tana dafe bango saboda kanta dake juya mata. Tana shiga bedroom din ta kwanta nan da nan bacci ya dauketa.



Har akayi sallar magriba bata fito ba kuma babu alamun tana ɗakin, shigowa ya yi bakinsa dauke da sallama yana kallonta da mamaki ganinta kwance tana bacci da alama ma batasan anyi sallah ba, tsaki ya yi sannaan ya ƙarasa gabanta ya taɓata ya ce

"Aneeserh!! Aneeserh"

Kasancewar batada nauyin bacci yasa tayi saurin buɗe idanunta nata murtsikesu harararta ya yi ya ce

"Bakida hankali ko?, bakisan lokacin da zaki kwanta bacci ba ko?"


Kalle-kalle ta shiga yi sai asannan tagane dare yayi ita kanta mamaki ta shiga yi domin baccin rana ba ɗabi'arta bace amma yanzu ta rasa meyasa take kwanciya kowane lokaci kuma bacci ya ɗauketa bai sake cewa komai ba ya juya ya fita ita kuma ta tashi ta shige banɗaki. Tana fitowa ta gabatar da sallar magriba tana jiran ayi isha'i, wata sabuwar yunwa taji ta ziyarceta dukda daman yau yini tayi bataci komai ba dan da safe bata ciba da rana kuma tayi amansa gashi kaf duniya babu abinda take sha'awar taci ji take komai ma ta tsaneshi kuma yunwar ta fara damunta. Kifa kanta tayi tsakanin cinyoyinta ta fashe da wani kuka na baƙin ciki kenan abincima bata isa ta ciba wannan wace irin ƙaddarace?, sallar isha'in da batayi ba kenan bacci ya sake awon gaba da ita..



*Aneeserh the begining of the manifestation*


*Written by N^N*

*Nanameera & Nainarh.*






*ANEESERH.*


*EP_Nineteenth.*



BY: N^N🤙




"One Month! One Month kaɗai suka rage mana ko mu nemo waɗanan files mu damƙa musu, ko kuma muyi rashin nasara mu rasa gaba ɗaya Dukiyar da take shirin zama namu."


Shiru tayi tana sauraren abin da take faɗa, har sai da taji ita ma tayi shirun alamar dai ta kammala sannan ta sauke ajiyar zuciya ta ce.






"Nifa ban gane miki ba sam, yanzu kina nufin na saka rayuwata a wala-wala ta hanyar shiga Bedroom ɗin Aliyu domin ɗauko files.. an ya ke uwa ta gari ce kuwa, wato baki damu ba idan Aliyu ya kamani ke nan ko, wai shin ita Dukiyar nan na abin da suka yi alkawarin bamu?.....

Kai a barshi a komai ya tafi normal na ɗauko files na damƙa miki ke kuma kin basu, ke nan wanene zai kasance dukiyar tana hannunsa ke nan kiyimin Bayani ko kuma na rusa Komai ta hanyar kin ɗaukowa sannan ki sani na bincika nasan inda suke kawai ɗaukowa ne bazan yi ba."





Cike da tsaban takaici take sauraren abin da Ɗiyar nata take faɗa har sai ita ma takai a ya sannan a fusace ta ce.


"Amma dai kin cika shashasha wacca batasan menene take yi ba wato ma kinsan inda suke tsayin kwanakin nan amma shi ne kikaƙi ɗaukowa ki kawo a kai musu mu sama kuɗaɗen nan, na gama fahimtar komai zuwa yanzu na fahimci ina ne kika dosa wato Hassada kikemin na abin da zan samu daga biliyoyin kuɗaɗen da zamu samu idan muka damƙa musu wannan files ɗin, an ya kuwa keɗin 'yata ce da na sani kece kuwa anya ba kin fara son General Aliyu ba ne?."





Dafe kanta tayi ita fa batasan takura a rayuwarta komai da take yi sai tayi ra'a sam ta tsani naci wallahi.


"Na fasa."!


"Kin fasa me?."!!



Ta tambaya da sauri tana Gyara riƙon da tayi ma wayar cike da faɗuwar gaba ta ci gaba da cewa.


"Ke Humaira karfa muyi haka dake domin ƙarshen abin nan bazai ma kowa kyau ba muddun kika ce kin fasa dauko files ɗin nan...."!



Katseta tayi da faɗi a fusace.



"Yes haka nake nufi na fasa ɗaukowa kiyi abin da zakiyi akai sannan da kike magana akan ƙarshen abin bazai yi kyau baz kece zata kwaɓe ma domin ni ina cikin kariyar Aliyu da kalma ɗaya tak zan yi amfani koda ya gane gaskiya ya kasa aikata Komai a gareni Simple ina faɗa masa Ina ɗauke da cikin sa, ma kaɗai ya wadatar."




A gigice irin na fusata da kalaman ɗiyar tata, ta miƙe tsaye har wayar tana ƙoƙarin faɗuwa daga hannunta bakinta har kumfa take fitar wa cike da Bala'i ta ce.


"Ke Humaira amma yau na tabbatar da kin cika mara ƙwaƙwalwa ki saka Ido a yau ba sai gobe ba zan saka a shigo har cikin Gidan a gaban shi Aliyun yana ji yana gani za'a ɗauki waɗanan files a tahomin dasu har nan Austaraliya. Tabbas na lura kin fara manta Wacece ni..."




"A'a ina ga kece dai kika manta Wacece Humaira da alama kin manta da basira ta da shawara ta aka yi amfani wurin kashe mai Gidan ki da muke pretending a matsayin shi ne mahaifina bacin cewa ni ɗin ɗiyar shege ce ke kanki da kika haifeni bakisan wanene ubana ba...."😳



Shiru tayi tana shafa kanta tare da furzar da iska daga bakinta idanunta a rumshe da alama abin yana damun zuciyarta sai dai tana ƙoƙarin dannewa.




"Ina saka Ido domin ganin ta yadda wasan naki zaki ɓullo ina jiran zuwan Gaggan 'yan ta'adda na Duniya domin ɗaukar waɗannan files."




Tana fitar da huci cikin ɓacin rai ita ma ta bata amsa da faɗin.


"Ki saka Ido zan baki mamaki zan kuma nuna Miki na daɗe cikin Duniyar ta'addan ci ba'akan kashe mijina da ba shi ne farau ba na fara ta'addan ci ba kuma ba zai zama ƙarau ba."


"Ina jira kuwa..."



Tayi maganar tare da katse kiran ƙitt......





Banda huci babu abin da take fitarwa tana tuna kalaman mahaifiyar nata Zazzafar iska ta kuma fitarwa sannan ta zura wayar In her Trouser pocket, p-cap dake kanta ta Gyara ta sauko da shi ta rufe fuskarta sannan ta ɗauki face mask ta saka, zura hannayenta tayi cikin Aljihun rigar sanyi dake jikinta bayan ta saka wasu Boots na ma ta a ƙafafunta, fitowa tayi daga Bedroom ɗin, kamar yadda tayi tsammani babu kowa a palo dama kuma Aliyu ya fita shi da Safeena. Direct Master Room nasa na musamman da babu mai shiga kaf cikin su sai shi ɗaya ta shiga.
Ta fara lalube laluben ta inda zata ɗauko su domin ta ɗan shiga confusing saboda bata gansu a wurin da ta san suke ba, lokaci guda garin neman files ɗin tayi kaca kaca da Room ɗin har takai ga ta cire mask dake fuskarta ba tare da ta sani ba. Tana ci gaba da neman ta wurin da suke.


A hankali yakai hannu domin buɗe ƙofar da key. Ya yi mamaki gwarai jin ƙofar da ya yi a buɗe, silently ya fara takawa yana shiga Room ɗin yayin da yake ƙare masa kallo da mamaki ganin wasu muhimman files zube a ƙasa....



A firgice ta juya gaba ɗayanta jin alamun taku kuma coridor da take ake tunkarowa gadan gadan......





"Na shiga uku na Mommy ki taimakamin Aliyu ya kashe ni, na shiga uku na Ni Yasmeen Mommy ciki! Ciki Yarinyar can take da shi, wayyo ni Yasmeen zuciyata zata buga Mommy ji nake kamar na kashe ta Aliyu bai kyauta min."


A firgice ta miƙe tsaye daga zaunen da take jin yadda ɗiyar nata take kuka tare da kiran ta shiga uku.


"Ke Yasmeen wai menene yake faruwa, kiyimin Bayani yadda zan fahimta Please menene ya faru da Aliyu?."



Cikin sheshsheƙar kuka hawaye kace kace Yasmeen ta ci gaba da faɗin.



"Mommy Aliyu ne...."



"Aliyu ya yi me??."


Ta tambaye ta jin ta kasa Ƙarisawa, da kyar ta iya saita nutsuwar ta tana fyace hanci ta ce.


"Ciki Aliyu ya yi ma wancan kucakar Yarinyar Mommy bazan iya jurewa ba domin dana bari wata ta haifawa Aliyu yaro bani ba, gwara na ƙona gidan nan gaba ɗaya mu mutu har da shi Aliyun domin hakan zai fi min da ganin Ranar da wata mace ba Ni ba zata haihu tare da Aliyu zama da kishiyoyi ma da ya ya na haƙura balle azo ga batun haihuwa."



Ɗifff wutar jikinta ya dakata da jin abin da Yasmeen ke faɗi da kyar ta iya tambayar ta.


"Yasmeen wai ciki na haihuwa kike nufin Aneeserh take da shi?....."





Cikin baƙin ciki da sake jin wani kukan yana zuwa ma ta ta ce.


"Eh Mommy Aliyu yaci amana ta ya yiwa Yarinyar cikinsa ciki...."😳




"Alhamdulillah. Madallah da faruwar haka daga ƙarshe dai Her Excellency da His Excel... Zasu sama jika nan kusa, gaskiya ya kamata a ce Ni ce zan fara sanar da su wannan kyakkyawar albishir."



Ɗifff kuka da jan macina tare da Ruwan Bala'i da Yasmeen keyi ya dakata chakk sakamakon jin abin da mahaifiyar nata take faɗa. Cikin rashin yarda da abin ta buɗe baki da kyar ta iya cewa.


"Mommy Hamdala ma kikeyi bayan faɗa miki wannan mummunar labari da nayi?..."



"E, mana Hamdala nayi kuma zan ci gaba da yi sannan ba tare da ɓata lokaci ba zan sanar da His Excel wannan Kyakykywar Labarin..."



"Ba zai yiwu ba. No! No way!! Bazan taɓa yarda ba, saina kashe ta tabbas yau ɗin nan sai na hallaka Aneeserh da ita da yaron dake cikin ta su mutu gaba ɗaya. Sai dai duk abin da zai biyo baya ya daɗe bai faru ba komai ta fanjama..."



Yasmeen tayi maganar a fusace tare da cilli da wayar gefe guda tana fitar da huci gadan gadan ta nufa kofar fita daga Bedroom ɗin.



"Hello! Hello!! Hello Yasmeen!!! Na roƙeki da ki dakata kada kiyi wannan mummunar aikin domin ƙarshen ba zai mana kyau ba daga mu iyayen ki har ke..."



Shiru tayi sakamakon gane Yasmeen ta daɗe da katse kiran da tayi dafe kanta tayi cike da damuwa tare da tashin hankali cikin rashin abin yi...






Daɓas taja da baya tare da zama irin na 'yan bori saman Bed ɗin tana tuna kalami da taji Yasmeen ke faɗa tuna maganar Yasmeen ɗin na ƙarshe da take ikirarin hallaka Aneeserh ne yasa ta miƙe tsaye cikin sauri ta ɗauko Wayarta ƙoƙarin kiran lambar Aliyu take ta faman yi sai dai kuma a kashe ta gwada ta gwada har ta gaji, cikin sauri ta fito daga Bedroom ɗin nata da sauri ta nufa hanyar Bedroom ɗin Aneeserh dake Up ɗin domin tanada tabbacin nane Yasmeen ta nufa ko'a mutu ko ai rai.....





*ANEESERH.*

*EP.20.*

*END OF BOOK ONE.*



*AFTER SOME HOUR'S.*


Ji ya yi gaba ɗaya ji da ganinsa kamar ba daidai suke ba. Kara kallon Doctor dake kwararo masa bayani kawai yake yi cike da al'ajabi da rashin abin faɗa, da kyar ya iya saita kalaman bakinsa ta hanyar faɗin.



"Pregnancy and Aneeserh ita ce ke ɗauke da shi tsawon three Months ba tare da na sani ba ikon Allah ke nan that's very amazing, Masha Allah tabbas godiya ta tabbata ga Ubangiji maɗaukakin sarki da ya bani ikon ganin wannan kyakkyawar Ranar a Rayuwata.."


Maganar ya yi tare da miƙe wa tsaye daga inda yake, saitawa ya yi sannan ya yi sujadar shukur yana daɗa miƙa godiya ga Ubangiji.



Da kallo Doctor tare da Khaleepa suka bisa Yayin da Khaleepa yake baki a sake cike da ruɗani da kuma sarkakiya da wannan lamarin ya je fa sa.





*Few minutes later.*



Fitowarsu ke nan daga harabar hospital ɗin Khaleepa ya kallesa da kyau yana nazari tare da imagine chakwakiyar dake gaban su.




"Aliyu wai da gaske ne Aneeserh Yarinyar da kake raino ce da juna biyu tsawon three Months wannan lamarin fa akwai ruɗani yanzu baka tunanin irin hukuncin da His Excel... Zai yanke idan ya sama wannan Labarin?."




Dakatawa da tafiyar ya yi, yana shafa sumar kansa ya jingina da motar su bayan sun suka ƙari sa wurin da take a fa ke.



"Tabbas ina tunanin abin da zai biyo baya idan Daddy ya sama labari sai dai bani da zaɓi ne."



Jinjina kai Khaleepa ya yi da jin amsar da ya basa.



Yana shirin ƙara furta wani wani abu wayar G.A tayi ƙarar shigowar kira. Picking ya yi ba tare da ya ce komai ba.
Yayin da Khaleepa ya zuba masa ido.




Annashuwar dake ɗauke saman fuskar sa ne ta ɗauke ɗifff. Baya ya yi kamar wanda juwa ya ɗiba yana mai kallon wayar hannun nasa tare da nazarin kalaman da Doctor yake faɗa masa sam ya rasa a wani matakin zai ajiye su.




Da sauri Khaleepa ya ƙari sa wurin sa tare da riƙo sa yana tambayar sa abin da ke faruwa.


Kallon Khaleepa yake yi kamar yau ce Ranar da ya fara Ganin sa.




"Wai Aliyu menene yake faruwa ne, me aka faɗa maka ne da ya saka ka shiga wannan yanayin lokaci guda?."


Khaleepa ya tambaya yana mai fata ba abin da yake zargi ne ya faru ba.



"Khaleepa, Safeena ce.. Safeena..."!


"E, Safeena menene ya faru da ita ɗin menene Doctor yace akan lamarin ta?."



Cikin fitar hayyaci ya kalla Khaleepa kamar yadda shima ɗin shi ne yake kalla.



"Safeena ta rasu sanadin daɓa ma ta wuƙa da Yasmeen tayi.... Na rantse ba zan bar Yasmeen ba tun da har ta kashe rai nima sai na kasheta kowa ya huta ai kishi ba hauka ba ne."


Ya yi maganar a fusace tare da nufar mota domin buɗewa sai dai dakakkiyar murya mai cike da amo ce da ta daki dodon kunnen sa cikin tsawa yasa shi dakatawa chakk....



"Ina ne zakaje kuma menene abin da zakayi?."


Chak ya dakata ba tare da ya iya buɗe motar Ba, bare ya shiga yayin da salon bugun zuciyar sa ya ƙaru fiye da baya.



A firgice Khaleepa ya juya domin ganin wanda ya yi maganar da kuma son tabbatar da zargin sa akan Muryar da yake ji.


"His Excellency Oh Allah komai ya caɓe."


Ya yi maganar cike da tashin hankali yana kallon yadda His Excel... Yake bin Aliyu da wani mugun kallo na ka ci amana.


"Ta ina?."

Shiru Aliyu ya yi ba tare da ya ce komai ba kuma bai cire hannunsa saman murfin motar Ba.


A fusace His Excel.. ya kuma daka masa tsawa da faɗin..


"Nace ta ina ne ko baka ji nane?."



Da kyar ya iya harhaɗo kalaman bakisan ta hanyar faɗin.


"Please Daddy zan yi maka Bayani Please.."!


"Au ba zaka faɗa min tana ina ba ke nan?."






Ganin lamarin yana neman ya yi tsauri ne yasa Khaleepa ya yi saurin tarar Daddy daga ƙoƙarin ƙari sawa wurin Aliyu da yake yi gadan gadan.



"Ayya. His Excellency kayi haƙuri Aneeserh tana lafiya tana ciki ta sama Bacci ne And ita kuma Safeena Allah Ubangiji da ya halicce ta kuma yafimu son ta ya karɓa abin sa sanadin 'yar hatsaniya da ta shiga tsakanin ta da Yasmeen. Safeena tana ƙoƙarin kare Aneeserh shi ne cikin rashin sani Yasmeen ta daɓawa Safeena ɗin wuƙa a ciki yanzu haka ma tana Headquarter. Please Daddy ina mai haƙuri a duka waɗan nan abubuwan babu hannun Aliyu ko laifinsa..."




Shiru His Excellency ya yi da alama ba ƙaramin taɓasa maganganun Khaleepa suka yi ba, lokaci guda ya ɗimauce tare da shiga tashin hankali da jin wannan mummunar labarin ke nan dai da gasken Iyalin Yaron sa sun tarwatse.


Yayin da cikin sauri ko tsayawa kuma sauraren abin da Khaleepa zai kuma faɗa Hajiya A'isha batayi ba, tun lokacin da ya faɗa Address na Ward da Aneeserh take ta nufa ciki Saima da suka taho tare tana mara ma ta Baya...




*END OF BOOK ONE.*


BY: N^N🤙


_Am nace ba Innocent Girl Reader's daga nan fa Book 1 da yake free ya ƙare. Zamu shiga Book 2 is Paid book kamar yadda aka faɗa da farko so duk masu buƙatar ci gaba da karantawa sai ku biya kuɗin 500₦ ne kacal karku bari a baku labari fa kuma dai kun san ya ya tafiyar take Aneeserh 🔥💃💖👑_



______

*Account Name: Hauwa lawan.*
*Account Number: 9086030007.*
*Bank Name: Opay digital service.*

*Sannan sai ki turo evidence of payment ta waɗan nan Countacts_08081129487 or 0908 603 0007 via WhatsApp Only*


___________________✍️🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥













An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment