Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

KARYA DA GASKIYA
Cigaban
TAFARKIN TSIRA
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi










BABI NA ƊAYA






Al'amarin da firgita gaba ɗaya jama'ar dake fadar kenan suka sha jinin jikinsu, a lokaci guda Fitinatul-Amir ya turɓune fuska tamkar an aiko mashi da WASIƘAR MUTUWA, kawa sai ya dubi waɗansu ZARATAN DAKARU dake tsaye a gefen shi cikin matuƙar fushi ya buɗi baki ya ce "Ya ku dakaru ina so ku yi hanzari ku bi sahun dakarun dake ɗauke da haraji ku tabbatar da cewa ba a sanya dukiyar sarki Madsur a cikin Baitul-Mali ba, kuma ku tabbatar da cewa kun kawo mini Madsur da tawagarshi cikin ƙoshin lafiya domin na yanke masu hukunci dai-dai da abin da suka aikata mani,


Na rantse da girman halarar tsafi na idan ku ka yi kuskure a wannan aiki da na baku sai KAIFIN TAKOBI ya sha jininku,


Kafin sadauki Fitinatul-Amir ya gama rufe bakinshi dakarun su kimanin dubu sun zare makamansu sun ruga izuwa wajen fadar suka bazama cikin gari wasu bisa dawakai wasu a ƙasa, domin farautar sarki Madsur.


A she a ɗazu lokacin da Fitinatul-Amir ke tattaunawa da yaro Usaiba, kuma abin da Usaiban ya faɗa ya tabbata bayan Fitinatul-Amir ya gudanar da bincike 'yan majalisa sun ji da kunnuwansu, nan take suka raya a cikin cewa haƙiƙa wannan yaro yakasance ɗan baiwa taban mamaki, wai shin ma mene ne alaƙar dake tsakanin su,


Amsar tambayar da suka kasa bawa kansu kenan, kawai sai suka zuba idanu domin su ga sakamakon da dakaru za su dawo da shi.


Al'amarin sarki Madsur da tawagarshi kuwa, lokacin da suka fice daga fadar Fitinatul-Amir, sai Madsur ya karanta ɗalasiman tsafi suka ɓace ɓat! Tamkar ba su taɓa wanzuwa ba, ba su bayyana a ko ina ba sai a fadar Madsur dake cikin babban birnin Hairul-Maswat,


Fadar yakasance makekiya da aka ƙarara da nau'ikan ababen more jin daɗin rayuwar duniya, a wannan lokaci fadar ta cika maƙil da jama'a makaɗa, mawaƙa tare da dukkan wani mai faɗa a ji, lokacin da sarki ya zauna bisa kan karagar mulki sai waɗansu irin tsala-tsalan 'yan mata kuyangi suka shigo fadar ɗauke da nau'ikan kayan ciye-ciye da tanɗe-tanɗe suka shiga raba wa jama'a, nan al'umma suka fara kimtsa cikinsu cikin nishaɗi da annashiwa, makiɗa da makawa suka fara aikinsu na raye-raye da kiɗe-kiɗe domin ƙara wa al'umma nishaɗi, shi kan shi sarki Madsur tashi ya yi daga kan karagar mulki ya cire alƙyabbarshi ya zauna cikin 'yan majalissa suka shiga yin walimar suna shewa da tafi, da yawa daga cikin al'ummar dake fadar ba su dalilin da ya sanya aka shirya wannan walima ba, domin tsawon shekaru sarki Madsur yana buƙata daga sharrin Fitinatul-Amir amma bai taɓa farin ciki tamkar yau ba, ana tsaka da wannan walima ne sarki Madsur ya karɓi wani kofi mai ɗauke da barasa a hannun wani hadimin shi ya kai bakinshi da nufin ya ƙurɓe ruwan, amma sai kawai aka ga ya yi jifa da kofin ya faɗi ƙasa ya tarwatse sannan ya miƙe tsaye zumbur yana mai kwarara wawan ihu da ya firgita baki ɗaya jama'ar dake fadar kowa ya shiga taitayin shi, tsawon daƙiƙa talatin yana kururuwar sai tsuke bakinshi gami da murtuke fuska tamkar an aiko mashi da WASIƘAR MUTUWA, Kawai sai ya durfafi inda karagar mulki take ya juya ya fuskanci al'umma fuskarshi har gyatsine take yi saboda tsananin fushi sannan ya buɗi baki cikin kakkausar murya ya ce "Ya jama'ata ku yi sani cewa bakomai ya sanya ni wannan baƙin ciki ba face lalacewar dukkan wani shiri nawa da na yi na mallakar dukiyar Fitinatul-Amir shugaban 'yan fashin duniya, kuma ba wani ba ne ya watsa shirin nawa ba face wani hatsabibin yaro mai ɗauke da hatimin takobin SAIFUL-ZAYYAD, matsawar yaron yana tare da Fitinatul-Amir ba za mu taba yin nasara akan shi ba, sannan yaron zai zamo ANNOBAR SARAKAI da matsafa gami da bokayen duniya, sai dai kash! Ana dara ga dare ya yi shi kan shi Fitinatul-Amir bai sani ba cewa yaron annoba ne a gare shi domin abin da ya daɗe yana farauta dare da rana domin ya hallaka shi ko ya cika muradin shi ya samun magaji.


Saboda haka da nan zuwa kowanne lokaci zai iya kawo mana FARMAKIN BAZATO domin ɗaukar fansa, saboda haka wajibi ne a gare ni na gudanar da bincike mai zurfi domin tunkarar duk wani ƙalubale da zai iya biyo wa baya, sannan akwai buƙatar a daren yau a shirya tawagar dakarun kar-ta-kwana".


Lokacin da sarki Madsur ya zo nan a jawabin shi sai ya taka da ƙafafunshi ya durfafi ƙofar da za ta sada shi da gidan sarauta, cikin hanzari waɗansu ZARATAN DAKARU ma'abota baƙaƙen sulken yaƙi suka mara mashi baya har sai da suka ƙule izuwa cikin ƙofar sannan jama'a suka watse kowa ya kama gaban shi, zukatansu cike da matuƙar bargaba domin sun san cewa gwabzawa da Fitinatul-Amir tamkar mutum ya sayi ajalin shi ne kuɗinshi.


Wannan shi ne abin da ya faru da sarki Madsur a lokacin da ya bayyana a fadarshi, bayan ya miƙa haraji ga shugaban'yan fashin duniya sadauki Fitinatul-Amir.






Lokacin da dakarun sadauki Fitinatul-Amir suka fice daga fada sai suka kasu rukuni biyu, kaso na farko suka durfafi hanyar da zata sada su da Baitul-Mali, na biyun kuwa suka bi sawun tawagar sarki Madsur, rikuni na farko sun riski dakarun dake ɗauke da harajin sarki Madsur, sai suka garzaya baki ɗayan su suka dawo izuwa fada, bayan sun gurfana gaban sarki sun kwashi gaisuwa sai Fitinatul-Amir ya dubi shugaban dakarun fuskarshi a murtuke babu annuri tamkar an watsa mashi garwashin wuta a kan ta cikin kakkausar murya ya ce " Ya kai Huzlaif haƙiƙa da a ce wani acikin ku ya yi kuskure an sanya duniyar sarki Madsur a Baitul-Mali da ɗayanku ba zai tsira da rayuwar shi ba, bayan tafiyar ku na gudanar da bincike bisa halarar tsafi na na gani cewa sarki Madsur ya ɓace tare da tawagarshi yanzu haka yana birninshi, saboda ina so ka shirya dakarun yaƙi domin kai farmaki izuwa ga sarki Madsur kafin wayewar gari ina so a hallaka duk wata halitta koda kiyashin birnin ba na so a bar shi a raye"


Koda Fitinatul-Amir yazo dai-dai nan azancen shi sai ya mayar da duban shi ga wani garjejen ƙato ma'abocin kwarjini, ƙasumba da gemu baƙaƙe siɗik daga cikin jerin 'yan majalisar shi ya ce da shi "Ya kai dirkar birnina kai ne za ka jagoranci wannan kai FARMAKIN BAZATO ka tabbatar da an zartar da komai yadda ya dace"


Koda gama faɗin hakan sai sarki Fitinatul-Amir ya miƙe tsaye tsam! Daga kan karagar mulki ya durfafi ƙofar da zata sada shi da gidan sarauta cikin hanzari waɗansu ZARATAN DAKARU suka rufa mashi baya har sai da suka ƙule izuwa cikin cikin ƙofar sannan fadar ta watse kowa ya kama gaban shi, inda ace mutum zai ga yadda fadar ta yi watan! Sai ya rantse ya ce wata halitta bata taɓa wanzuwa a fadar ba.


Lokacin da aka garƙame da azababban yaƙi tsakanin Musulmi da kafurai sai yaƙin ya zamo abin tsoro ga kowa ne ɓangar, kabbarta musulmi haɗe da ihu da kururuwar kafurai gami da ƙarar karafniyar ƙarafa da haniniyar dawakai ta cika dodon kunne, rundunonin biyu suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA, sassan jikkunan bil'adama suka dinga shawagi a sama suna zubowa ƙasa tamkar ana ruwan su ne daga saman, JINI DA ƘASA suka cakuɗe waje guda.


A ɓangaren manyan GWARAZAN JIYA kuwa sarki Rayyan da Lamsarul-Azlam sun wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama na gaban kwatance sai da sa'a ta shuɗe a cikin wannan hali ɗayansu bai samu nasarar lakutar jikin abokin gwamin shi ba,


Wohoho! Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce kyan faɗa a kwana a na yi, kuma inda babu ƙasa nan ake gardmar kokawa, koda gwarazan biyu suka fahimci cewa sun kasa yin nasara ta hanyar amfani da makaman yaƙin su sai kawai suka yi jifa da makamansu suka ja da baya domin a gwada 'yar Kashi, suka ruga izuwa kan juna ya yin da ya rage saura taku goma tsakanin su sai suka dako wawan tsalle sama suka kaiwa juna huri suka naushi fuskokin juna, sannan suka diro ƙasa, koda kowanne su ya shafa hancinshi sai ya ji jini na zuba, kawai sai suka ruguntsume da sabon artabu, suka wanzu suna naushi da bugun juna hannu da ƙafa tamkar waɗansu ifritai.






Mu haɗu a babi na biyu domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari


Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe






ƘARYA DA GASKIYA
BABI NA UKU
Rubuta Labari
Mansur Usman Sufi
Sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071






BABI NA UKU




Lokacin da ya rage saura kamu biyu kafin addar ya ratsa wuyan yaro Usaiba, kwatsam! Bazato babu tsammani sai jaruma Rusayyat ta bayyana a daf da inda yaro Usaiba yake kwance, tana shirye cikin gagarumar shigar yaƙi a kwiɓin cinyoyinya tana ɗauke da Waɗansu zaratan takubba.
Kafin Fitinatul-Amir ya yi wani yunƙuri uwar gidanshi ta shammace shi ta gabza mishi wawan naushi a ƙeyarshi. Saboda ƙarfin naushin sai da Fitinatul-Amir ya wuntsila addar dake hannunshi ta faɗi can gefe guda amma sai ya turje ya ja ya yana mai gyara tsayuwar shi.
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin shi da uwar gidanshi, duk wannan abu dake faruwa akan idanuwan Jama'ar fadar yake gudana. Ya yin da suka ga cewa Rusayyat ta shirya fito-na-fito da Fitinatul-Amir sai suka cika da matuƙar mamaki suka ce tabbas Rusayyat ta yi wauta ainun, amma masu iya magana na cewa idan ka ji makaho ya ce ayi wasan jifa to ya ji ya taka duste!
Fitinatul-Amir ya buɗe baki cikin kakkausar murya mai tattare da matuƙar fushi ainun lokacin da idanuwanshi suka canza launi izuwa shuɗi ya ce "ya uwar 'ya'yana haƙiƙa kin ci amana kuma kin bani kunya da kika tseratar da rayuwar maƙiya na bayan cewa kin san ba zan taɓa cimma burina na samun haihuwa ba face na hallaka yaro Usaiba, shin bakya farin ciki da nawa farin cikin, ina mai tabbatar miki da cewa a yanzu zan yanke maki hukunci dai-dai da laifin da kika aika mini, bayan na aika rayukan Usaiba da 'yar uwarshi Hairat izuwa barzahu...,
Kafin Fitinatul-Amir ya kammala rufe bakinshi Rusayyat ta tari numfashi tana mai bushewa da dariyar mugunta sannan daga bisani ta turɓune fuska da SAƙON MUTUWA ta ce "Haƙiƙa ranar wanka ba a ɓoyen cibi! Ya mijina ka yi sani cewa ja da baya ga rago ba tsoro ba ne face shirin artabu, koda da daƙiƙa ɗaya a rayuwata ban taɓa jin ina ƙaunar ka ba a cikin zuciyata kawai dai ina yi maka biyayya saboda na cimma burina na ɗaukar fansa akan amininka wato attajiri Kulbus, a halin yanzu ina so ka sani cewa ɓuyan da wannan ƙwanwa ke yi a bayan kare ya zo ƙarshe"
Lokacin da Rusayyat ta zo dai-dai nan azancen ta sai ƙwallar takaici da baƙin ciki ta zubowa Fitinatul-Amir, gashin jikinshi ya mimmiƙe kuma wani tiririn ɓakin hayaƙi ya dinga fita daga sassan ƙofofin hancinshi da bakinshi, kawai sai sanya hannunshi ya keta alƙyabbarshi gida biyu ya yi wurgi da ita da ita gefe take waɗansu jajayen sulken yaƙi suka bayyana a jikinshi masu matuƙar kwarjini, kai idan ka gan shi a cikin wannan hali sai ka yi tsammanin cewa wani ifritu ne, kawai sai Fitinatul-Amir ya zare wata sharɓeɓiyar takobi a gadon bayanshi ya falfala da azababban gudu a izuwa kan Rusayyat yana ihu da kururuwa mai firgita DANDAZON MAYAƘA a FILIN DAGA, tsinin takobin yana kartar ƙasa yana tayar da wata kariyar walƙiya.
Al'amarin da ya ɗimauta jama'ar dake fadar kenan suka shiga guje-guje da ifice-ificen TSIRA DA RAYUKA.
Koda ganin hakan sai Rusayyat ta yi koyi da shi ta hanyar zare takobinta ta ruga gare shi domin tarar juna,
Wohoho! Haƙiƙa KARON MAZA sai GWARAZAN JIYA kuma ranar bikin farar kaza balbela ba abar gayya ba ce, tabbas idan BABBAR GIWA ta fito FILIN FAMA babu wanda ke fitowa ya yi GABA DA GABA da ita face GOGA SHA FAMA da sha gwagwarmaya a DAULAR MAYAƘA.
Inda ace mutum yana tsaye a wannan waje lokacin da waɗannan taurari biyu ke yin shirin KARON BATTA dole ya ɗimauce ya tabbar da cewa inda babu ƙasa nan ake gardmar kokowa.
Lokacin da rage tazarar dake tsakanin su bata huce taku huɗu ba sai kowannen su ya daka tsalle sama suka kaiwa juna hari, cikin matuƙar zafin nama suka sanya takubbansu suka kare wani tartsatsin wuta ya tashi, sannan suka dira ƙasa bisa diga-digansu cikin gwaninta, suka shiga kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA irin ta MAZAJEN DUNIYA.
Kaico! Haƙiƙa artabun gwani da gwani daɗin kallo gare shi, ana fara wannan ɗauki ba daɗi ne mutane suka fara gane kuren su, domin su Fitinatul-Amir sun fara hargitsa fadar, duk sa'adda ɗaya daga cikin gwarazan biyu ya kai wa abokin gwamin shi hari idan ya kauce, duk abin da takobin ta sauka a kan shi sai ka ga ya tarwatse ya yi bindiga ya yi kan jama'a koda kuwa gini ne,
Nan fa suka ci-gaba da gudun tsira da rayukansu hatta 'yan majalisar sarki da su aljani Lattul-kifas cika wandunansu suka yi da iska domin dai ina amfanin baɗi babu rai.
A wannan lokaci babu abin da kunne ke ji ƙarar karafniyar takubba gami da ihu da kururuwar jaruman, sai da rabin sa'a ta shuɗe ana wannan ɗauki ba daɗi babu ɓangaren da yake da RINJAYE, al'amarin da ya fusata su kenan bisa ganin cewa suna artabun ne cikin matuƙar zafin nama da ƙwarewa.
Abin da su duka biyun ba su sani ba shine bakomai ya sanya ɗaya su ya gaza yin nasara ba sai domin saboda takubban dake ɗauke da su an sana'anta su da sinadarin tsafi guda ɗaya,
Lokacin da Fitinatul-Amir ya fahimci wankin hula zai kai shi dare kuma kimar shi za ta zube a idanun talakawan shi ace uwar gidanshi ta gagare shi. Koda kammala tunanin hakan sai kawai ya shammaci Rusayyat ya gabza mata wawan naushi a fuska. Saboda matuƙar ƙarfin naushin sai da ta yi sama tamkar an janye ta da ƙugiya sannan daga bisani ta faɗo ƙasa tim a matuƙar galabaice, kafin ta yi yunƙurin miƙe wa tsaye Fitinatul-Amir ya sake gabza mata wani naushin a fuska take ta langwaɓe ƙasa sumammiya, hanci da bakinta na yoyon jini.
Koda samun wannan gagarumar nasara sai Fitinatul-Amir ya bushe da dariyar farin ciki sai da ya yi ta ishe shi sannan ya murtuke fuska tamkar an aiko mishi da sakon mutuwa, kawai sai ya durfafi inda Usaiba ke kwance ya yin da ya isa sai kawai ya ɗaga takobinshi domin ya sare mishi wuya.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai wata irin shirgegiyar mikiya ta bayyana ta saman rufin fadar ta mangare Fitinatul-Amir ya faɗi ƙasa, kafin ya yi yunƙurin miƙewa tsaye, mikiyar ta sanya faratan ƙafafuwanta ta ɗauki yaro Usaiba da Rusayyat ta tashi sama ta ratsa ginin fadar tamkar yadda danshi ke ratsa ƙasa ta ɓaci bar! Tamkar bata taɓa wanzuwa ba.


Lokacin da waɗannan dakaru suka yi arba da abin da zakanyar ta yiwa gimbiya Aslaima sai suka zare makamansu suka yi ɗauki kan ta aka kacame da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini daban al'ajabi. Dakarun suka wanzu suna kai mata sara da suka cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance, ita kuwa ta dinga zille da zame wa gami da mayar da martani da yakushi da ciwo, duk wanda ta bangaza daga cikin su sai ka ga ya yi sama tamkar an janye shi da ƙugiya sannan ya faɗo ƙasa ko shurawa bai yi ba.
Nan fa ya zamana cewa yawan dakarun ya zamo a banza domin zakanyar ta zame masu tamkar ANNOBA ƊARI, duk inda ta sanya a gaba sai dai ka ga suna faɗuwa ƙasa matattu, kafin shuɗewar rabin sa'a ta maishe su gawa babu ɗayan su da yake raye, sannan ta farma kuyangin dake tare da gimbiya zubar da su ƙasa matattu.
Koda samun wannan gagarumar nasara sai zakanyar ta yi wani irin mahaukacin gurnani tana mai daga ƙafafuwanta na gaba sama tana buga su a ƙasa, sannan daga bisani ta daka wawan tsalle domin ta turmushe gimbiya Aslaima ta kai ranta izuwa barzahu.






BABI NA HUDU




Lokacin da ya rage saura kamar kamu uku zakanyar ta dira a kayan gimbiya Aslaima ba, kwatsam bazato babu tsammani sai aka ga wani kyakkyawan saurayi ya yi firar burgi daga cikin duhuwar bishiyun dajin, sanye yake cikin fararen tufafi, a kwiɓin cinyarshi ta dama yana ɗauke da salkar ruwa, a gadon bayanshi kuwa yana rataye da wata sharɓeɓiyar takobi, kallo ɗaya zaka yi mishi ka tabbatar da cewa ya cika GWARZON MAYAƘI mai ƙarfi na Allah ya isa, babu wata 'ya mace mai hankali da za ta yi tozali da shi face ta kamu da matuƙar ƙaunar shi.
Cikin baƙin zafin nama saurayin ya daka wawan tsalle ya dira a daf! Da inda gimbiya take ya gabzawa zakanyar naushi a wuya take wuyan ya karye ji kake ruƙus ƙas! Zakanyar ta faɗi ƙasa rikica ko shurawa ba tayi ba. A dai-dai wannan lokaci ne boka kaddad da dakaru dubu suka ruga izuwa wajen ɗauke da miyagun makamai, koda suka ga abin da yafaru sai suka yi turus! Cikin matuƙar fushi boka kaddad ya dakawa kuyangi tsawa da su kaiwa gimbiya Aslaima ɗauki, cikin hanzari inda take domin aiwatar da umarnin da aka yi masu.
Boka kaddad ya dubi gawarwakin dakarun dake zube a ƙasa, sannan ya mayar da duban shi ga saurayin fuskarshi a murtuke babu annuri cikin kakkausar murya ya ce "ya kai wannan saurayi yi maza ka sanar da ni abin da ya faru da gimbiya kafin na yanke maka hukunci dai-dai da abin da ka aikata, kuma wane ne kai?
Koda jin wannan tambaya sai murmushi mai taushi ya suɓuce wa saurayin da ya ƙara bayyana kyawun fuskarshi, sannan ya dubi boka kaddad ya buɗi baki a karo na farko ya fara magana cikin wata irin zazzaƙar murya ya ce "ya kai wannan dattijo kayi sani cewa ba ni da masaniyar abin da ya wakana tsakanin zakanyar da gimbiya ba sai dai kawai na jiyo kururuwar ta ne kuma na fahimci tana buƙatar taimako shine na kawo mata ɗauki,
Game da tambayarka ta farko kuwa ita ce suna na jarumi MUHASSIN IBN SHA'ABAN na fito ne daga nahiyar larabawan yamma a wani birni da ake kira da Madinatul-yusra, domin yaɗa addini na na bautar Ubangijin talikai a faɗin duniya.
Koda jarumi Muhassin yazo dai-dai nan azancen shi sai dakarun dake wajen suka cika da matuƙar mamaki ainun jin Muhassin ya ambaci Ubangijin talikai.
Boka kaddad kuwa sai ya murtuke fuska tamkar an aiko mishi da SAƙON MUTUWA ya dubi Muhassin babu annuri a tare da shi cikin kakkausar murya ya ce "naji dukkan bayanin ka kuma na fahimci cewa ba kayi yunƙurin cutar da sarauniyar kyawawa ba, saboda haka sai ka kama gaban ka bamu da buƙatar wani dogon jawabi",
Har Jarumi Muhassin ya buɗi baki da nufin ya sake furta wani abu sai boka kaddad ya ɗaga mishi hannu yana nuni da ya tafi ya basu waje.
Amma sai aka ga gimbiya Aslaima ta miƙe tsaye tsam! Tamkar babu wani rauni a tare da ita ta dubi Muhassin fuskantarta cike da wani irin ƙayataccen murmushi mai ɗimauta zuciyar duk wani ɗa namiji, cikin tattausan murmushi mai daɗi tamkar sarewa ta ce "ya kai wannan saurayin ma'abocin kwarjini da taimako ka yi sani cewa kai ne mutum na farko da taɓa ceton rayuwata a lokacin da nake gaɓar mutuwa, duk da kasancewar a halin yanzu ina ɗauke da cutar makanta amma idanuwana suna iya ganin ka, saboda ina neman wata alfarma a wajen ka da ka biyo ni izuwa gagarumar tafiyar mu ta nemo mini maganin lalurata, na yi maka alkawarin bayan mun samu nasara zan sanya mahaifina ya baka duk wani abu da kake buƙata da ya danganci sarauta ko dukiya.
Koda gimbiya tazo nan azancen ta sai gaba ɗaya jama'ar dake wajen suka cika da matuƙar mamaki, daga can sai ya ci gaba da cewa "idan har ka na tantama akan abin da na faɗa bari na bayyana maka surar ka da tufafin dake jikinka.
Nan take Aslaima ya shiga bayanin sura da tufafin Muhassin. Tana kammalawa mamaki ya turnuƙe kowa kuma suka fahimci cewa Aslaima kallon haƙiƙa ta yi mishi ba labari ta ji ba.
Nan fa mamaki ya turnuƙe kowa domin tun da gimbiya ta makance koda aljani bata taɓa gani ba, amma ga shi yanzu tana iya ganin bil'adama, shin mene ne ya sanya idanun nata iya jarumi Muhassin suke gani? Ko kuwa ƙarfin sihirin shi ne ya sanya hakan?
Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan.
Shi kuwa boka kaddad koda ya ji abin da gimbiya ta furta sai zuciyarshi ta buga da ƙarfi tsoro ya kama shi ainun, ya ce a ran shi shin ya aka yi gimbiya take iya ganin Muhassin bayan cewa na wa'adin sihirin da na yiwa idanunta bai ƙare ba, haƙiƙa akwai lauje cikin naɗi, amsar tambayar da ya kasa bawa kanshi kenan.
Shi kuwa Jarumi Muhassin koda ya ji gimbiya ta ce tana iya ganin shi nan take ya fahimci cewa matsalar aiki ne sihiri, domin kuwa da makanta da gaskiya ba

Please Login or Register in order to submit comment