Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kansa saitin kanta cikin lallashi yace

"Ki yi haƙuri na miki wanka.. Za ki ji daɗin jikinki.." Wasu sabbin hawayen ne suka sake zubowa a kan kuncinta. Se ta shiga girgiza kai. Cikin ƙarfin hali ta buɗe baki da ƙyar tace

"Ka ƙyale ni.. Ka ƙyale ni.. Ka ƙyale ni.." Hannu ya kai ya shafi sumar kansa cikin rashin sanin abin yi. Bayan duk abin da ya faru kuma ba ya son sake zama silar sakata kuka. Se dai da za ta daure ta yi wankan ko da kanta ne za ta ji daɗin jikinta ko yaya ne. A hankali ta shiga buɗe idanunta da suka yi jaajir suka kuma kukkunbura saboda kukan da ta sha. A kansa idanunta suka sauka. Ta yi saurin rufe nata idanun kamar wadda ta ga wani dodo.

"Ka matsa ba na san ganinka." Ta sake faɗa da muryarta da ke a dashe. Se da ya sauke numfashi sannan yace

"Don Allah ki yi haƙuri ki dena wannan kukan.." Ya san ta ji shi, amma kuma ya san ba amsawa za ta yi ba. Ya san idan har ya ƙyaletan cigaba za ta yi da zama ba za ta tashi ba. Hakan ne ya sanya shi matsawa inda take ɗin ya sake saka hannunsa ya ɗagota ya sanyata cikin jikinsa. Ya lulluɓeta da duka hannayensa biyu. Duk wani ragowar kuzarinta ta saka dan tashi daga jikinsa, se sai ko kaɗan ta kasa. Da dai ta fahimci ba abin da za ta iya se kawai ta haƙura ta cigaba da kukanta da babu sauti se hawaye kawai. Wajen minti 20 suka ɗauka a hakan yana jin yanda take sauke numfashi a hankali. Tausayinta na sake ratsa shi, ji yake tamkar ya maidata ciki. Se dai da hakan ba ze yiwu ba se ya sake yi mata kyakkyawan masauki a jikin nasa. Se da ya tabbatar ta nutsu ta haƙura da ƙoƙarin tashin da take yi sannan ya miƙe. Ba tare da saninta ba ya ɗauketa kawai gaba ɗayanta se bandaki.

"Ni ka sauke ni.." Shi ne abin da take faɗa a hankali. Be kulata ba har se da ya kaita ciki. Ya kalleta a nutse lokacin da ta buɗe lumsassun idanunta dake cike da bacci. Ya san a yanzu ba ta buƙatar komai se bacci, idan kuma yace ze tsaya taimaka mata dan ta ji daɗin jikinta za a ɗauki lokaci, dan haka cikin taushin murya yace

"Ki yi wanka ki zo ki yi bacci.." Ita dai tana tsugunne kanta kife a kan cinyarta tana jin yanda gaba ɗaya jikinta ke amsa mata. Fita ya yi daga banɗakin ya nemi waje ya tsaya dan jiranta ta gama. Se dai har wajen minti 10 be ji motsin ruwa ba ko wani abu da ze nuna ta soma wankan ba.

"Ya ilahy.." ya faɗa yana dafe goshinsa. Har ga Allah ba ya so ya sake sakata kuka, ko kuma abin da ze sanya ta sake jin tsoronsa. Amma kuma ya ga alama dole se ya yi hakan, idan ba haka ba su shekara a wajen ba tare da ta yi komai ba. Kai tsaye toilet ɗin ya faɗa tana nan kuwa a inda ya barta. Babu ɓata lokaci ya saka hannunsa ya ɗagota a hankali ka da ya je ya jangwalowa kansa. Da ma ya lafiyar kura bare ta yi zawo. Be ɓata lokaci ba ya shiga yi mata wankan. Ita kam yau Lulu haukacewa ne kawai ba ta yi ba. Ga shi bakin tsiwa ya mutu, ga babu ƙarfin ƙwatar kanta. Se dai duk da haka wani ƙaramin yaƙin ma aka yi a wajen nan, duka dai ya jure ya kuma daure. Haka tana ji tana gani ya wanketa tass sannan suka fito. Zuwa lokacin babu laifi ta ɗan ji jikinta ya saki ba kamar ɗazun ba. Se dai har yanzun ji take kamar ba ita ba. Wata doguwar riga mara nauyi ya ɗakko mata ya ƙaraso inda take da niyyar sanya mata. Ta girgiza kai ba tare da ta ɗaga ido ta kalle shi ba. Hawayenta suka zuba a kan tawul ɗin dake ɗaure a jikinta. Cikin rawar murya tace

"Ka ba ni zan saka.." Babu musu ya miƙa mata. Gaba ɗaya ma se ya bar wajen dan ya ba ta damar sakawa a nutse. Se kuwa a lokacin ta iya saka rigar daidai lokacin da ta lumshe idanunta wasu sabbin hawaye na kawowa a kan fuskarta saboda yanda take jin jikinta. Tana gama sakawa ta kwantar da kanta kan gadon. Lura da hakan ne ya sanya shi ƙarasowa dan gyara mata kwanciyar. Tana ganinsa ta yi saurin tashi zaune a tsorace. Da tana da ƙarfi da tashi za ta yi ta bar wajen. Se dai ba za ta iya ba.

"Yi kwanciyarki.. Babu abin da zan miki.." Ita dai ba ta kwanta ba, ba kuma ta ɗaga ido ta kalle shi ba. Ganin da ya yi idan be bar wajen ba ba za ta kwanta ba ya sanya shi matsawa daga wajen. Se da ta dena jin motsinsa sannan ta ɗaga kumburarrun idanunta ta kalli wajen. Ganin da ta yi ba ya wajen ne ya sanyata jan jikinta da ƙyar ta haye kan gadon, ta kwanta duk da a tsorace take.. Duk da jikinta babu daɗi amma da yake baccin na kanta cikin ƙanƙanin lokaci kuwa ya yi awon gaba da ita. Se a lokacin Gwani ya sauke wata ƙatuwar ajiyar zuciya yana faɗin

"Alhamdulillah.." Ya ƙare yana fesar da iska daga bakinsa. Se ya ƙarasa ya lulluɓa mata sabon bargon da aka zo mata da shi cikin kayanta. Dan ya san za ta ji daɗinsa. Ya yin da ya koma gefe ya zauna kawai yana kallanta cike da tausayi, da kuma wata irin ƙauna.



... A nutse take takowa cikin ɗakin kai se ka rantse tana sane take irin wannan takun. Se dai sam ba haka ba ne, tsananin yanda nutsuwa da kuma tarin kamala wanda ya kasance a tare da ita tuntuni shi ne ya haifar da hakan. Ko wannan kaɗai na ɗaya daga cikin abin da ya sa Mom ke kishi da Mommahn. Musamman idan suka shiga taro, yanda Mommahn ke kereta a kan kowacce kalar shiga ta yi. Duk kuwa da yanda za ta aro wata uwar izza ta yafawa kanta, hakan ba ya hana mutane nuna sun fi yin Mommahn ba. Saboda ita tana yin komai nata ne very classy. Babu garaje kuma babu nuna ita wata ce. Yau ɗin ma tun da ta ɗaga ido ta mata kallo ɗaya ba ta sake kallan inda take ba. Saboda yanda wani kishi ya zo ya tirniƙe mata ƙirji. Haushin Mommahn na sake kamata. Ta wani haɗe rai tana maida dubanta kan Dad dake zaune kan kujerar dake kusa da tata. Cikin ladabi Mommah ta kalli Daddy bayan ta sakar masa murmushi tace

"Barka da wannan lokaci Yallaɓai"

"Yawwah Barka dai Rankiyadaɗe."

"Barka da wannan lokaci.." ta ƙare tana kallan Mom. Se da Mom ta wani ɗauke kai kamar wadda wata er aiki ta gaisar sannan tace a yatsine

"Barka.." Sarai Daddy ya lura da yanda ta amsa ɗin amma ya share. Dan ba ya so ya taso da wata matsalar kuma a yanzu haka. Mommah ba ta damu da yanda Mom ɗin ta amsa ba ta nemi waje ta zauna ba tare da ta sake kallan inda Mom take ba. Se a lokacin sannan Daddy ya buɗe baki yace

"Toh kin ji Abokiyar zamanki za ta je ganin likita? Ina fatan dai kun yi sallama?" Daddy ya ƙare maganar yana kallan Mommah. Se ta girgiza kai tana murmushi tace

"A'ah ban sani ba. Allah Ya tsare hanya."

"Ameen in da gaske kike.." Mom ta faɗa tana sake kautar da kai.

"Salma!!" Daddy ya faɗi sunanta gatsal. Wanda ba kasafai ya saba faɗar sunan kowaccensu ba. Se dai abin da Mom ɗin ta faɗa ya sanya shi faɗin hakan. Dan ya fahimci abin da take nufi..

"Na'am.." Mom ta amsa da hakan tana kallan Daddy dan ba ta yi tunanin ya ji abin da ta faɗa ɗin ba. Se dai yanayin yanda ya kira sunan nata ne ya sanyata fahimtar ya ji abin da ta faɗa. Ita dai Mommah nunawa ma ta yi kamar ba ta ji abin da ta faɗa ba.

"Tashi kawai ki je.. Allah ya tsare.. Idan kin sauka a Abujar za mu yi magana."

"Toh. Zan kiraka kuwa Rankayadaɗe da zarar na sauka" Ta ƙare tana miƙewa gami da sakarwa Daddyn wani murmushi. Ya maida mata martanin murmushin sannan yace

"Bari na musu magana su kai ki.."

"A'ah Yallaɓai.. Ni da nake da ɗa me ye kuma zan buƙaci driver?" Ta faɗa tana satar kallan Mommah da ko kallanta ba ta yi ba.

"Ba jiya kuka yi da shi za ki je ba? Ka da kuma ki same shi busy.." Se da ta juyo sosai sannan tace

"Ni fa na haifi abuna Yallaɓai.. Da ma ban haifa ba ne se na ji wani abu.. Amma ko yanzu na ce ya min abu ai shi me min ne.. Idan ma na ce zan nemi wani bayan ga ɗana ai ma kamar na butulcewa Allah kenan bayan ya ba ni wanda zan saka ya min ba se na nema ba.." Ta tsaya a nan. Lura da ta yi Daddy ya ɗauki wayarsa da aka kira ze amsa ya sanyata ɗorawa da faɗin

"Ko ba haka ba ne Hajiya Sa'adah..?"

"Uhmm.." Mommah ta faɗa tana murmushi. Dan duk wani take taken Mom ɗin ta fahimceta. Tun da ba yau ne karon farko da take mata irin haka ba. Tun tana damuwa yanzu ma har ta dena damuwa. Ta samawa kanta salama.

"Tun da na haifa dole na yi alfahari da shi, na kuma godewa Allah da be yo ni juya ba." Ta yi abin da ko yaushe da shi take amfani wajen son ganin ta ƙunsawa Mommahn baƙin cikin da ze hanata bacci. Dan ta riga ta san da wannan ɗin ne kaɗai take iya ƙuntatawa Mommahn. Yanzun ma haushi ta bata shi ya sa ta yi amfani da wannan damar wajen ƙuntata mata ita ma. Kafin Daddy yace komai ta yi saurin ficewa daga ɗakin dan ta san idan ba ta yi hakan ba dole yace wani abun. Idan ma yanzun be yi magana ba toh ta tabbatar wani lokacin ze yi. Ita dai tun da ta zubar da abin da ke ranta ai shi kenan..

MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO53*

___Se da ta gama shiryawa tsaff cikin doguwar riga me kyau. Ta sanya baby hijab ɗin da ya kasance mahaɗin rigar. Ba ƙaramin kyau ta yi ba, kamar wadda ta tsaya ta ɓata lokaci me tsayi tana shiryawar. Neman waje ta yi ta zauna a gefen gadon. Ita dai har ga Allah ta saka a ranta ba za ta sake shiga ɗakin nan nasa ba ko mene ne kuwa. Gefe guda kuma har yanzu ba ta fidda ran tsamo shi daga wannan mummunar ɗabi'a ta shi ta shaye shaye ba da yaddar Ubangiji. Se dai kuma ba ta fatan sake shiga ɗakin nasa. Ji take tamkar ta sanarwa da Mommah abin da ke faruwa ko ta taimaka mata da shawarar yanda za su ɓillowa lamarin. Amma sam se ta ji hakan be kwanta mata ba. Da so samu ne har ta cimma burinta ma ba su sani ba. Tafi minti 10 zaune a hakan, kamar ba za ta tashi ba se kuma ta miƙe ta fice daga ɗakin. A daidai lokacin da ta kusa kitchen ɗin shi kuma ya fito daga cikin ɗakin. Shi ma ya yi matuƙar kyau kamar ko yaushe. Ji ta yi kamar ta koma kawai ta haƙura da shiga kitchen ɗin. Se dai kawai ta maaze ta ɗan runtse idanunta lokacin da take ƙoƙarin gifta shi. Ba zaka ɗauka za ta gaishe shi ba se dai cikin sanyin muryar nan tata tace

"Ina wuni?" Ba tare da ta jira amsarsa ba ta yi wuff ta faɗa kitchen. Duk da be yi niyyar amsa gaisuwar tata ba, amma kuma se ya bi bayanta da kallo yanda take ta wani sum sum da kai kamar munafuka ko kuma wadda ta ga wani dodo. Ya ɗan ja ƙaramin tsaki yana girgiza kai sannan ya ƙarasa ficewa daga ɗakin.


... Wayarsa da ta yi ƙara ya ɗaga kai ya kalla. Ya ɗan sake buɗe idanunsa a kan wayar sannan ya miƙe. Cikin nutsuwa ya yi sallama bayan ya kara wayar a kunnensa. Daga can ɓangaren aka amsa sallamar tasa sannan aka ɗora da

"Malam Affan mu jiraka ne bayan Sallah?" A nutse ya ɗaga kansa ya kalli Lulu da ke kwance tana baccin da yanzun ba wani daɗinsa take ji ba. Hakan ne ya sanya sam ya ƙi yin nauyi. Daga zarar ta soma se ta farka a tsorace kamar wadda ake tsoratawa.

"A yi min afuwa Malam ba zan samu damar zuwa ba.."

"Toh subhanallahi.. ina fata dai lafiya." Malam Ahmad ya faɗa dan ya san tun da Gwanin yace ba ze je ba ba ƙaramin uzuri ne ya taso masa ba.

"Ehh.. In Sha Allah.." Shi ne abin da Gwani ya faɗa yana sake maida dubansa kan Lulu.

"Toh shi kenan.. Babu damuwa."

"Ina godiya.." Gwani ya faɗa ba tare da ya jira komai ba ya ajje wayar. Kai tsaye ya sake komawa inda ya tashi ɗazun. Ya sake zama yana cigaba da kallanta cike da tausayinta. Saboda duk da yanda take cikin bargo amma hakan be hana shi ganin yanda take ta mutsu mutsu ba alamar kwanciyar ta ƙi mata daɗi. Daidai lokacin aka soma kiraye kiraye a masallaci. Se ya miƙe a nutse ya faɗa toilet ya ɗauro alwala kana ya fito. Ya riga ya san ko da magana ya yi mata ba lallai ne tana da ƙarfin da za ta iya tashi ita ɗaya ba tare da taimakonsa ba. Hakan ne ya sanya shi ƙyaleta kawai ya fice daga ɗakin. Kamar ko yaushe tare suka fita masallacin da Abeey wanda yanzun jikinsa ya sake yin kyau. Kai ba za ka taɓa cewa ma ba ya da lafiya ba.

Da mamaki Abeey ya kalli Gwani lokacin da ya miƙe dan barin masallacin daga idar da Sallahr Asuba, bayan hakan ba ɗabi'arsa ba ce.

"Har za ka wuce ne Affan?"

"Ehh Abeey.." ya ba shi amsar a taƙaice.

"Toh Allah ya tsare.."

Duk da ya fahimci abin da Abeeyn ke nufi, ya ɗauka ko ze wuce inda za su haɗu ne su wuce wajen musabaƙar amma hakan be hana shi amsawa da "Ameen" ba. Kawai se ya fice daga masallacin kai tsaye ya koma gida. A inda ya barta a nan ya sameta. Ya saka hannunsa a hankali ya ɗan yaye bargon. Da yake lokacin idanunta a buɗe suke se ta yi saurin warosu sosai daidai lokacin da ta sanya hannayenta duka biyun ta riƙo bargon.

"Ki tashi ki yi Sallah.." Ya faɗa cikin taushin murya dan ma ka da ta yi tunanin umarni yake bata tace za ta yi tsiwar tata, duk da dai ya ga alama babu bakin yinta. Amma duk da haka yau ɗin komai ze mata ya fi so ya yi cikin rarrashi, tun da ya san laifinsa ne.

"Ni ka fita ka ƙyale ni.." ta faɗa da dashashshiyar muryarta da har zuwa lokacin ba ta koma daidai ba har kuma lokacin ba ta buɗe idanunta ba.

"Shi kenan.. zan fita amma ki tashi ki yi Sallahr.." Ya faɗa kai ba za ka taɓa cewa Gwani ne wannan ba. Ba tace komai ba duk da ta ji abin da ya faɗa ɗin. Bayan wajen minti 10 ta soma ƙoƙarin miƙewa dan tashi ta yi sallahr. Sake runtse idanunta ta yi saboda azabar da ta ji lokacin da ta zauna ɗin daidai lokacin da sabbin hawaye suka zubo a kan kuncinta. Sabon haushin Gwanin na sake kamata. Ji take kamar ta yi ta ihu ko za ta ji sauƙin abin da take ji. Haka dai ta daure, a daddafe ta shige banɗakin ta ɗauro alwala ta fito. Ko da ta fito kaasa tsayawa ta yi ta yi sallahr a tsaye, se zaunawa ta yi ta miƙata. Ko minti 3 ba ta ƙara zaune kan daddumar ba ta miƙe ta sake komawa kan gadon ta yi kwanciyarta tana share hawaye.



... "Tun da ka faasa zuwa wajen musabaƙar kasuwar ma kuma ba za ka je ba?" Se da ya kai hannunsa kan kwantacciyar sumar kansa sannan yace

"Ummeey ba na jin zuwa ne yau ɗin.."

"Ba ka jin zuwa kuma? Ko dai ba ka jin daɗi ne?" Ta tambaya tana karantar yanayinsa.

"A'ah Ummeey.." Sake ƙura masa idanu Ummeey ta yi. Dan ta san ƙarya ba halinsa ba ne. Duk yanda aka yi lafiyarsa ƙalau amma kuma akwai dalilin da ya hana shi fita yau ɗin.

"Lafiya kuwa Affan?" Ta ƙare maganar a sare. Dan ya kwantar mata da hankali ya sanya shi yin murmushin da ya ƙawata fuskarsa sannan yace

"Ummeey.."

"Ina Afaaf..?" Ta katse shi da wannan tambayar. Duk se ya ji jikinsa ya yi sanyi. Dan har ga Allah ba ya so Ummeey ta san abin da ya faru dan be san da wane ido ze kalleta ba. Ya yin da ita kuma Ummeey tsoranta ɗaya ka da zazzaɓin da ya kwantar da Lulu a asibiti yanzu ma shi ya rufeta. Shi kuma dan gudun kar ya tayar mata da hankali ya sanya shi ƙin faɗa mata. Dan ta riga ta saba yanzun kullum Lulun kan fitowa bayan Sallahr Asuba ta gaidata, har ma ta zauna ta tayata wasu ayyukan. Se dai yau sam ba ta ganta ba. So ta ɗauka ma ko bacci ne yau ɗin ya riƙeta. Se dai kawai kuma a yanda ta ga Gwanin ya sa hankalinta ya kaasa kwanciya.

"Bacci take Ummeey.."

"Har yanzu?" Ta sake tambaya tana cigaba da kallansa. Se kawai ya sauke ajiyar zuciya, jin da ya yi babu hanyar fita. A hankali yace

"Ba ta jin daɗi ne shi ya sa ba ta fito ba tun ɗazun."

"Subhanallahi.. Haba Affan.. Yanzu ɗiyar tawa ba ta da lafiyar da har ta hanata fitowa shi ne ba ka faɗa min ba ina nan a zaune. Bari na duba gaskiya idan zazzaɓin ne se dai mu sake zuwa asibiti." Ta faɗa lokacin da ta gama miƙewa a kan ƙafafunta.

"Ummeey ai tana samun sauƙi ma.." Gwani ya faɗa dan gudun ka da Ummeeyn tace za ta dubata. Duk da ba ta taɓa shiga ɗakin ba tun bayan aurensu. Amma a yanda ta damu da Lulun ya san sarai za ta iya shiga ɗakin.

Tun da aka yi bikinsu Gwanin Ummeey za ta iya cewa ba ta sake shiga ɗakin ba se yau ɗin. A nutse ta yaye labulen ɗakin ta shiga. Gwani kam kasa motsawa ya yi daga inda yake. Se cigaba da tsayawa da ya yi a wajen kamar wanda aka dasa.

Yanda ta ganota lulluɓe cikin bargo ya sanyata sake fahimtar da gasken zazzaɓin ne ya sake rufeta. Dan haka da sauri ta ƙarasa tana faɗin

"Afaaf.." Ƙirjinta ne ya buga lokacin da ta ji kamar muryar Ummeey cikin ɗakin. Sake maimaita sunanta da Ummeyn ta yi ne ya sanyata sake tabbatar da lallai Ummeeyn ce. Hannu Ummeey ta saka ta ɗan ɗage bargon ta wajen fuskarta. Hakan ya bata damar ganin idanunta da suke a kumbure.

"Ya salaam.. Sannu.." Ta faɗa cikin tausayawa. Ba ta iya buɗe baki tace komai ba saboda yanda dabara ta ƙare mata. Ta kasa buɗe idanunta dan ba ta san da wanne ido za ta kalli Ummeeyn ba. Saboda ji take kamar ko ba ta faɗa mata ba tana kallan idanunta za ta fahimci abin da ya faru. Lura da idanunta biyu ya sanya Ummeey matsawa kusa da ita ta yi amfani da hannunta wajen ɗagota.

"Ai ba a zauna a gida haka ba lafiya ba." Ummeey ta faɗa tana ƙarasa ɗago Lulu da ta kaasa ko yunƙuri ballantana ta ƙwaci kanta. Zuwa lokacin gaba ɗaya jikinta ya gama yin mugun tsami. Dan haka ba ta san lokacin da ta saki ƙaramar ƙara ba lokacin da Ummeeyn ta ida zaunar da ita a kan gadon. Ba tare da Ummeey ta fahimci wani abun ba tace

"Daure ki tashi ki shirya mu je asibiti.. Ai ba a zauna haka ba." Ta ƙare tana sake taimaka mata dan ta miƙe. Se dai zuwa lokacin ta ɗan tsaya tana karantar Lulun. Sam ta rasa me za tace. Ta kasa buɗe baki tacewa Ummeeyn ta barta lafiyarta ƙalau. Se a lokacin sannan ta buɗe idanunta, se dai har lokacin ta gaza furta komai. Ta kuma kasa ɗaga ido ta kalli Ummeeyn. Taimaka mata Ummeey ta yi suka soma tafiya dan ita a niyyarta a maidata asibiti su ƙara dubata. Lokaci ɗaya kuma tana sake karantar Lulun. Se dai ko tafiyar second 10 ba su yi ba Ummeey ta dakata. Ta ɗan sauke ajiyar zuciya sannan ta komar da Lulun ta zaunar da ita a kan gadon. Idanun Lulu a runtse suke gaba ɗaya tun lokacin da suka fara tafiya. Har kuma yanzun ba ta buɗe su ba. Ba tare da Ummeey tace komai ba ta fita daga ɗakin. A inda ta bar Gwani a nan ta same shi. Ba tare da ta kalle shi ba tace

"Juyo min ruwan zafin da ke kan wuta ka kawo min.." Daga haka ta juya ciki. Be fahimci ta gane abin da ya faru ba ne. Dan haka kai tsaye wajen wutar ya nufa kamar yanda ta umarta ya juyo cikin bokiti ya kai mata har cikin banɗaki. Be jira wani abu ba ya fice daga ɗakin. Se da ta shiga banɗakin ta haɗa ruwa sannan ta fito. A nutse ta kalli Lulu tace

"Maza tashi ki je ga ruwa can na haɗa miki ki yi tsuguno ciki.. Idan ya huce akwai wani a gefe se ki chanja da shi sannan ki yi wanka In Sha Allah za ki ji daɗin jikinki.." Ɗaga idanunta Lulu ta yi ta saci kallan Ummeeyn. Ƙirjinta ya buga da ƙarfi. Kar dai ta san abin da ya faru. Ita kam idan haka ne ta shiga 3 ta lalace.

"Tashi kin ji?" Ummeey ta katse mata tunanin da faɗin hakan. Wai duk dan idan Ummeeyn ba ta fahimci komai ba kar ta gane. Hakan ne ya sanyata aro duk wani jarumta ta miƙe cike da ƙarfin hali ta wuce banɗakin. Ummeey ta yi murmushi lokacin da Lulun ta shige banɗakin a fili ta furta

"Allah sarki!!" Daga haka ta cigaba da zama cikin ɗakin.

Kamar yanda Ummeey ta umarceta hakan kuwa ta yi. Cikin ƙanƙanin lokaci ta ji jikinta ya yi mata daɗi kamar ba shi ne ɗazun take jinsa kamar ba nata ba. Ta ɗauki mintuna masu yawa a ciki kafin ta fito sanye da hijab ɗinta. Har lokacin kanta na ƙasa ta ƙarasa ta zauna a kan gadon. Riga Ummeey ta miƙa mata mara nauyi tace

"Saka wannan se ki kwanta ki samu ki yi bacci.." Ji take kamar ta ɗora mata da bayani a kai, se dai ko babu komai ita ɗin sirikarta ce. Kuma a yanda take ta sum sum da kai ta san ba ta so kowa ya san abin da ya faru. Dan haka ita ma Ummeeyn se ta basar kawai cikin hikima dai ta cigaba da yi mata magana.

"Ya kike jin jikin naki?" Ummeey ta tambaya dan ita har zuwa yanzun tana ɗaukar Lulun ne a matsayin ɗiyarta. Wata irin kunya da takaici su ne suka taru suka mata dirar mikiya. Ta kasa ko da ɗaga ido ne ta kalli Ummeeyn. Idanunta na kawo ƙwalla tace a sanyaye

"Alhamdulillah.."

"Toh madallah.. ki cigaba da yanda na faɗa miki har zuwa lokacin da jikinki ze koma daidai." Sam Ummeey ba ta damu da yanda Lulun ke cigaba da ƙunshe kai ba kamar ba ita ba. Ta cigaba da mata magana cikin hikima. Ba Ummeey ce ta bar ɗakin ba se da ta tabbatar Lulun ta kwanta har ta soma bacci sannan ta fito. A ƙofar ɗakinta ta samu Gwani. Tana neman waje za ta zauna tace

"Ka samu ka siyo mata wani abun da za ta ci idan ta tashi.. Yau ɗin wainar gero zan yi. Na kuma san ba lallai ta mata daɗi ba."

"Toh Ummeey.." Ya ƙare yana miƙewa. So yake ya tambayi Ummeeyn se dai yau ɗin wata irin kunyarta yake ji kamar wata sirikarsa. Se dai ya maaze kawai yace

"Ba sai an je asibitin ba Ummeey?"

"Ehh ba se an je ba.." Ummeey ta

Please Login or Register in order to submit comment