Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi, se yake ji ina ma a ce Lulun mutuniyar kirki ce, wadda ta san darajar mutane musamman ma manyan da suka haifeta.

"Zan fa ɗauka na kai da kaina.." Ummeey ta katse shi da faɗin hakan. Se ya miƙe kawai yana sake yin murmushin, dan be ma san abin da ze ce ba. Ya ɗauki flask da cup ɗin ya wuce zuwa ɗakin nasa. Kamar ko da yaushe, yanzu ma haka da sallama a kan laɓɓansa ya shiga cikin ɗakin. Tana zaune a kan gadon ta rafka wani uban tagumi kamar wadda aka yiwa mutuwa. Fuskar nan kamar za ta kaiwa na kusa da ita duka. Ta cika ta yi famm, ƙiris take jira ta fashe. Kai tsaye inda take ɗin ya isa. Ya ajje su a gefenta kana ya sake ɗaukar abun buƙata ya fice daga ɗakin. Har ya gama abin da yake yi ba ta ɗago ta kalle shi ba, saboda yanda zuciyarta ke mata zafi, musamman a yanzun da tafi sarewa da zuwan Mami fiye da ɗazu. Ɗaga ido ta yi ta kalli abin da ya ajje ɗin, ta taɓe baki tana faɗin

"Allah ya kiyaye ni cin abincin gidan nan.. Ko mutuwa zan yi ba zan ci ba har se na koma gidanmu." Ta faɗa tana murguɗa baki kamar da wani a kusa da ita. Cigaba da zama ta yi, ba tare da ta bi ta kan abincin ba. Zuwa can dai da ta gaji se ta miƙe zaune kawai cikin nemarwa kanta mafita. Wayarsa da ta gani ajje ya sanyata ƙarasawa da sauri ta ɗauka ta duba lokaci. Ganin yanda lokaci ya ja ne ya sanyata maida wayar inda take, zuwa yanzu kam ta gama saddaƙarwa Mami ba zuwa za ta yi ba. Dan haka se kawai ta gyara zaman hijab ɗinta ta soma takawa dan barin ɗakin. Kafin ta ƙarasa fitowa daga ɗakin ta tsaya ta kalli gidan, ta sake kallan gidan. Se ta yi gefe da kanta tana faɗin

"Tuff.." ta faɗa kawai irin a iskancen nan ba tare da ta zubda komai daga bakinta ba. Yau ɗin da ta sake ganin gidan nasu se ta ji haushinsa ya ƙaru a cikin ranta. Kenan me yake taƙama da shi da yake ji da kansa, izza kamar wani ɗan gidan sarauta bayan shi ɗin ba kowa ba ne? Se taƙama da kyau da duk en makarantar sun shaida amma banda ita, dan kuwa ita dai ba ta ga kyan da ake faɗa ba. Mutum se Addini kawai, da nuna shi ɗin wani ne. Toh yau dai ga ta a cikin gidansu, ga ta a cikin ɗakinsa, ba ta ga wani abu da ze sa ya dinga ɗaukar kansa daidai da ita ba. Kawai se ta sake taɓe baki tana ƙarasa fitowa daga cikin ɗakin. Daidai lokacin da Ummeey ta kwashe sharar da ta yi a inda ta gama girki, murmushi ya suɓuce mata sanda ta ga Lulun na fitowa daga cikin ɗakin.

"Kin gaji da zaman koh?" Ummeey ta faɗa tana kallanta. Da sauri Lulu ta ɗaga kai ta kalleta, dan ba ta yi tsammanin ganin kowa a wajen ba. Ganin murmushi ne har lokacin a fuskar Ummeey ya sanyata yin yaƙe kawai, wanda kana ganin fuskarta za ka fahimci hakan.

"Mu je ki zauna a ciki kafin ki dawo.." Ummeey ta faɗa. Ji ta yi kamar ta rusa ihu, ko kuma ta zage ta juye kwandon rashin kirkin da ta kwaso, da kuma haushin rashin zuwan Mami da ya ƙara fusatata, take ji za ta iya yiwa duk wani na cikin gidan bore, ta yi musu da yaren da za su fi gane gida take so su maidata, ba za ta taɓa zama cikin gidan nan ba. Se dai yanda matar ta mata kwarjini ya sanyata kasa ƙoƙarin yin komai, se binta a baya da ta yi, duk da har lokacin zuciyarta tafasa take yi. Har ɗaki Ummeey ta kai Lulun, ta nemi waje ta zauna tana sake kallan cikin ɗakin. Ita har mamaki ma abin yake bata, yanda aka yi wanda ya tashi a gida kamar wannan ya kasance Gwani. Wanda a yanayinsa ko wani abun ƙaryarka ka iya fasalta muhallin da ya taso. Ta sake taɓe baki tana jin yanda zuciyarta ta sake yo kusa kusa. Fita Ummeey ta yi zuwa inda tukunyar girkinta take, ta zubowa Lulun dambun masarar da ta gama yinsa yanzun nan. Se da ta ɗebo mata ruwa a randa sannan ta shigo ɗakin ta ajje a gaban Lulun tace

"Ki ci kin ji ɗiyata.." Bin kwanon ta yi da kallo tana ji kamar ta yi fatali da shi, ita sam ba wannan ne a gabanta ba, burinta kawai ta ganta a gida. Ko ma ba a gida ba ne, ta dena ganinta cikin mutanen dake da alaƙa da Gwani.

"Na ƙoshi.." karo na farko kenan da ta yi magana. Murmushi Ummeey ta yi sannan tace

"A'ah fa.. ban yarda ba. Ki ci ko kaɗan ne idan ya so anjima se ki ƙara.."

"Allah na ƙoshi ni." Ta faɗa tana gyara zamanta. Jin Ummeeyn za ta sake cewa wani abu ya sanyata faɗin

"Na ci abinci ɗazu." Ta faɗa dan ba ta so Ummeeyn ta ƙara yi mata wata maganar a kan abincin, dan sake tunzurata take yi.

"Toh madallah.." Ummeey ta faɗa tana miƙewa dan ficewa daga ɗakin, wataƙila idan ta ga ba ta cikin ɗakin ta samu ta ci ko kaɗan ne. Runtse idanunta Lulu ta yi tana sauke numfashi da sauri da sauri. Haka ba dan ta so ba ta cigaba da zama cikin ɗakin kamar za ta rusa ihu.

Ya yi matuƙar mamaki lokacin da ya shiga ɗakin ya ga ba ta ciki. Mamaki ya kama shi, ka da dai a ce guduwa ta yi? Idan guduwa ta yi ina ta je kenan? Dan ya san dai ba za ta tunkari gida ba idan ta aikata wannan ɗanyen aiki. Ya ɗan fesar da iska daga bakinsa yana lumshe idanunsa. Shi kam ya haɗu da wahala, wannan wace irin mata ce? Miƙewa ya yi kuma da ɗan sauri kamar wanda ya tuna wani abu. Kai tsaye ɗakin Ummeey ya wuce.. A tsakar gida ya tarar da Ummeeyn tana kwashe kayan da ta gama wankesu ɗazu da safe. Da sauri ya ƙarasa ya karɓi kayan a hannunta yana faɗin

"Da kanki kuma Ummeey?"

"Babu komai Affan.. Ka dawo?" Ta faɗa da murmushi a kan fuskarta. Jinjina kai ya yi kana ya amsa da

"Ehh.."

"Ka kyauta da ka dawo yanzu ai.. Ka bar er mutane dama ita kaɗai? Ba ta saba ba se fitowa ta yi, yanzu haka tana ɗakina.."

"Ɗakinki?" Ya tambaya a mamakance. Jinjina kai Ummeey ta yi tana mamakin yanda ya yi tambayar cike da mamaki kamar wadda ta faɗi saɓo. Da sauri kuma ya basar kawai ya yi murmushi. Da sauri ya ƙarasa taya Ummeeyn ninkin, se da suka gama tsaff, sannan ya kwaso su duka zuwa cikin ɗakin nata. Tana zaune cikin ɗakin kamar wata munafuka se rarraba idanu take yi. Tunda ya mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa, ya ƙarasa cikin ɗakin ya ajje kayan, daidai lokacin da Ummeey ma ta shigo ta ajje na hannunta.

"Ɗiyata tashi ku je, ai ma kin yi ƙoƙari. Zama kai ɗayan nan ba shi da daɗi sam.." Kamar jira take yi se kuwa ta miƙe zumbur, har tana riga shi yin gaba. Da mamaki ya ɗan kalleta se kuma ya maida dubansa kan Ummeey. Yana shirin cewa wani abu tace

"Ɗauki abincin nan ka tafi mata da shi.. Ba taci komai ba tun zuwanta ɗakin nan, ina ga ko kunya take ji. Ka sakata ta ci ko da kaɗan ne."

"Toh" ya amsa da hakan yana ɗaukar abincin.

Ƙarasawa ya yi ya ajje abincin inda ya ajje na ɗazu. Ga mamakinsa komai da ya shigo da su ɗazun duk suna wajen, babu alamar ma an taɓa su. Hakan na nufin kenan babu abin da ta ci tun jiya? Juyawa ya yi ya kalleta inda take tsaye wajen bakin ƙofa. Idanunta sun cika fall da ƙwallar baƙin ciki, haushi da abubuwa da dama. Yana shirin ɗauke kansa ya ji muryarta tana faɗin

"Ka sake ni gidanmu zan koma. Ba na sonka.. Kuma ai ba a aure dole." Tsayawa ya yi yana kallanta, cike da ganin ƙoƙarinta na iya tsayawa gabansa tana faɗar hakan. Se da ya ɗan yi murmushin gefen baki sannan yace

"Saki kike so?" Cikin sauri ta amsa da

"Ehh. Saboda ba na sonka, ba na sonka, ba na sonka.." Ɗan runtse manyan kyawawan idanunsa ya yi, duk da shi ɗin ma ba sonta yake ba, amma tabbas ya ji zafin waɗannan kalaman nata ainun, ya ji zafinsu fiye da zaton me tsammani. Shi kansa ba dan wasu abubuwa ba da babu abin da ze hana shi sawwaƙe matan. Se dai kuma tana nuna kamar umarni take ba shi, daga kuma lokacin da ya bi umarnin nata ya saketa ya zama lusarin namiji kenan, ya zama sokon namiji wanda mace kan iya sarrafa shi. Dan haka se ya ɗan ciji lips ɗinsa da ɗan ƙarfi kafin ya watsa mata idanunsa, se ya soma matsowa zuwa inda take fuskarsa a haɗe fiye da yanda take a da. Se da ya zo dab da ita sannan ya dakata ya ɗauki hannayensa duka biyun ya saƙala a ƙirjinsa sannan ya zuba mata idanunsa masu matuƙar kyau da kwarjini. Yanda ta gan shi kusa da ita ne sosai ya sanyata ɗan ruɗewa, ta ji ƙirjinta ya wani irin bugawa duk da rashin kunya da tsiwar da take ji amma ganinsa kusa da ita ya sanya ta ɗan ji tsoro. Se kawai ta maaze ta ɗan gyara ƙafarta saboda yanda ta ji har ita ma rawa take yi kamar wadda ke shirin ƙin ɗaukarta. Cikin dakakkiyar muryarsa ya soma faɗin

"Waye ya faɗa miki ni sonki nake yi? Ko ki na tunanin hakan ne?" Se ya girgiza kansa cike da takaicin halayen Lulun yace

"Ki dena yaudarar kanki.. Ina zaune, ba tare da na nema ba aka ba ni aurenki.. Dan haka ki dena wani fiffiƙa ki yi ƙoƙarin kwantar da kanki ƙasa dan cigaba da zama da ni.. Saki kuma idan har ba ni na ga dama ba, za ki cigaba da zama ne cikin gidan nan har se lokacin da na yi niyyar sakinki. Idan kuma a hannunki yake maza ɗauki takadda ki rubuta ki tafi da ita.." Yana kaiwa nan ya dakata. Wani irin tafasa zuciyarta ke yi sanda maganganun ke sauka cikin kunnenta. Se ta shiga sauke ajiyar zuciya da sauri sauri, wani irin kukan baƙin ciki na taso mata. Cikin ɗaga murya ta buɗe baki da iya ƙarfinta ta soma faɗin cikin kuka

"Toh ka sake ni mana ka huta.. Ni ka sake ni na faɗa maka ba na sonka. Ba zan iya zama da kai ba har abada.. Ba na sonka." Kafin ta cigaba da maganar ta soma ƙoƙarin zubewa a wajen tana kuka wiwi. Tana shirin sake faɗar wasu maganganun dan sake baƙanta masa, da tunzura shi ya saketa, hakan ne ya sanyata ƙoƙarin sake ɗaga murya dan maganar yanzun tafi shigarsa se ji ta yi ruff, an rufe mata baki da wani abu da ta kasa gane meye saboda tsabar taushinsa. Ni kaina ba zan iya cewa ha lokacin da ya riƙota ba. Se kawai ganinta na yi a hannunsa. Hannunsa ɗaya ya saka shi ne a bayanta ya riƙota dab da jikinsa, yayin da ɗayan hannun nasa da shi ya yi amfani wajen rufe mata bakin, dan ba ya buƙatar duk wani abu da ze faru Ummeey ta san da shi, saboda baya son ɓata mata farin cikin da ya gani a tattare da ita tun bayan auren. Musamman kuma tun zuwan Lulu gidan. Yanda ta buɗe idanu a razane cikin matuƙar ruɗewa ya sanya idanunta sauka a kan fuskarsa, sanda shi ma nasa idanun ke kan fuskarta a haɗe, dan hatta da idanunsa se da suka chanja colour. Cikin kausashshiyar murya me cike da gargaɗi yace

"Keee!!" Ya faɗa har lokacin tana kan hannunsa, ɗayan hannun nasa kuma na kan bakinta. Ita sam ba ma fahimtar abin da ya faɗa ta yi ba, se ƙoƙarin tashi da take yi ƙirjinta na wani irin bugawa. Ga shi ta kasa cewa komai, ga shi ta kasa aikata komai, hakan ne ya sanya ƙwallar da ta taru cikin idanunta damar zubowa a kan fuskarta tana sake yunƙurin miƙewa cike da ƙarfin hali..

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO31*

___"Ba ki da hankali? So kike ki nunawa kowa rashin kunyarki? So kike kowa ya fahimci ba kya amfani da tarbiyyar da iyayenki suka miki? So kike ki sake nuna min da gasken ke fitsararriya ce?" Gwani ya ƙarasa faɗa yana kallan cikin idanunta ransa a mugun ɓace. Ba ta san sanda ta runtse idanunta ba, jin ƙoƙarin miƙewar da take yi ya faskara ya sanyata haƙura kawai se ruwan hawayen dake ambaliya daga idanunta. Ga shi kuma ya hanata cewa komai saboda rufe bakinta da ya yi, ballantana ta yi amfani da bakin wajen yin rashin kunyar da ta saba. Se dai kamin ta ida tunanin ta sake jiyo kausassar muryarsa yana faɗin

"Daga yau.. duk ranar da kika sake yunƙurin yi wa wani a cikin gidan nan rashin kunya wallahi zan kawar da mutuncin mahaifinki da nake gani, na saɓa miki.. Hatta bakin rashin kunyar da kike taƙama da shi zan gurje shi ne ko da a jikin bango ne, yanda ba za ki sake yunƙurin aikata hakan ba. Shashashar yarinya.." Ya ida faɗa yana ɗan fesar da numfashi saboda yanda ya ji kansa ya sara da ƙarfin gaske. Se kuma ya janye hannunsa daga kan bakinta sannan ya saketa a hankali, ba tare da jiran komai ba ya fice daga ɗakin hannunsa dafe da kansa. Zubewa kawai ta yi a wajen tana fashewa da kukan takaici. Ai koma mene ne ya faru Abba ne ya janyo mata, ita ya za ta yi da rayuwarta ne? Me za ta yi ta ji daɗi, ta fita daga wannan ƙuncin da ta shiga a cikin gidan nan. Mami tace mata za ta zo su san abin yi, amma har yanzu ba ta zo ba. Shin guduwa ya kamata ta yi ko mene ne? Ta ɗauka rashin kunyarta za ta yi tasiri a wajen Gwanin, ganin cewar ba ya son raini, ba ya kuma ɗaukarsa, ta ɗauka cikin ƙanƙanin lokaci za ta fusata shi ya saketa, se dai ba ta ga alamar hakan ba. Toh ita kam ya za ta yi da rayuwarta?. Kawai se ta kifa kanta a ƙasa duk da kukan da take hakan be hanata sauke ajiyar zuciya ba cikin rashin sanin abin yi. Jin yanda ƙamshin jikinsa ke cigaba da tashi a jikinta ne ya sanyata sake fusata, se ta cigaba da rusar kukanta lokacin da ta miƙe dan tuɓe kayan ko za ta rabu da jin ƙamshin turaren nasa da a wajenta ba shi da maraba da ɗoyin tutu.

Se da ya ɗan tsaya na tsawon minti 2 sannan ya wuce ɗakin Ummeeyn. Kallansa ta yi cike da mamakin ganin yanayinsa tace

"Affan lafiya kuwa?" Ta tambaya cike da kulawa. Se da ya yamutsa fuska, dan be yi tunanin ma ɓacin ran nasa ya bayyana har kan fuskarta ba, sannan yace

"Kaina ke ciwo Ummeey.. Amma zan sha magani.."

"Toh gwara dai ka sha.. Ka kalli har yanayinka ya chanja.."

"Tohm.." ya faɗa yana gyara zamansa, sannan ya ɗora masa

"Ummeey.. maganar kayan nan dama nake so mu yi dake ɗazun. Ya ba ni kayan, ya kuma ce zan iya juya su har zuwa lokacin da nake so.. Se na maida masa da kuɗinsa.." Cikin farin ciki Ummeey tace

"Kai Masha Allah.. Masha Allah.. Allah ya sa a fara a sa'a. Allah ya saka masa da alkhairi ya ƙara masa arziƙi.."

"Ameen Ameen.." ya amsa a nutse.

"Kun yi maganar da Abeeynka?" Girgiza kai ya yi yace

"A'ah Ummeey na ga yana buƙatar hutu ne kin ga ba ya wani jin daɗi.. So kuma na ga yana bacci ne shi ya sa na bari se ya farka se na faɗa masa."

"Toh madallah.." Ummeey ta faɗa cike da farin ciki, dan babu ƙarya ta ji daɗin wannan al'amari sosai.



... "Rankiyadaɗe wata magana na zo da ita.. Se dai ban san yanda za ki ɗauketa ba.." Atine ta faɗa kanta a ƙasa.

"Toh.. Ikon Allah.. Faɗeta mu ji.. Allah dai ya sa lafiya.." Mommahn da ke sanye cikin wani haɗaɗɗen lace ɗinkin buba da ta matuƙar karɓar jikinta kasancewarta me ɗan jiki haka dai ba can ba. Ta yi ɗaurin ture ka ga tsiya wanda ya matuƙar zaunawa cass a kan fuskarta da duk da yanayin shekarunta hakan be hana zallar kyawunta fitowa zam zam ba. Kai se ka ɗauka er shekara talatin da wani abun ce zaune a wajen, ta faɗa tana kallan Atinen. Gyara zama Atine ta yi, bayan ta sauke ajiyar zuciya tace

"Dama a kan maganar Areef ne da matarsa.."

"Tirƙashi.. wani abu ya faru ne bayan zuwanki sashen?" Da sauri Atine ta girgiza kai tace

"A'ah Rankiyadaɗe, babu abin da ya faru.. kawai dai ina so ne idan da dama mu shiga cikin lamarin ko dan ceto rayuwar auren waɗannan yara.." Girgiza kai Mommah ta shiga yi tana murmushin yaƙe.

"Ni za a janyowa baƙin jini Atine.. Ba na son abin da ze janyo na dinga shiga maganarsu ita da ɗanta musamman ma dai a yanzu.. Saboda haka ki barsu idan Allah ya yadda da kansu za su shirya kansu ba tare da saka hannun kowa ba.." Shiru Atine ta yi na tsawon sakanni, kafin tace

"Rankiyadaɗe kin san bauɗaɗɗen hali irin na Areef. Idan dai har ba shiga cikin lamarin nan muka yi ba mahaifiyarsa ba za ta taɓa nuna masa daidai ba."

"Toh mu bar su mana su yi abin da suke so Atine.." Mommah ta faɗa a hankali, se dai ita ma har cikin ranta da za ta samu dama da ta yi wani abun a kan auren Areef ɗin. Saboda tun zuwan Didi ta ji ta kwanta mata a rai sosai. Ba ma ita kaɗai ba, ita kanta Atine yarinyar ce ta burgeta, hankalinta da nutsuwarta komai abin burgewa ne.

"Ko da wannan ze kasance abu na ƙarshe da za ki sake shiga a kan Areef.. toh ki yi mana Hajiya. Ba don kowa ba se don Allah.." Shiru Mommah ta yi, kamar ba za tace komai ba se kuma can tace

"Shi kenan.. Allah ya taimaka.."

"Na gode sosai Hajiya.. Allah ya ƙara girma.." Atine ta faɗa cikin farin ciki, wanda har cikin muryarta se da farin cikin ya bayyana.

"Ni ma shishshigi na yi Atine.. Amma dai Allah ya ga zuciyarmu.. Allah ya taimaka.."

"Ameen.." Atine ta faɗa tana miƙewa, bayan ta yi wa Mommahn sallama ta fice daga ɗakin. Binta da kallo Mommah ta yi kamar me nazarin wani abu, se kuma daga baya ta dawo da dubanta cikin ɗakin tana sauke ajiyar zuciya.

Kai tsaye part ɗin Didi ta wuce, daidai lokacin da Bad Man ya tura ƙofar wani ɗaki ya shiga. Se da ta kalle shi sannan ta girgiza kai ta wuce ɗakin da Didi ke ciki. Kamar yanda ta batta tana zaune a kan dadduma tun bayan da ta idar da Sallah. Gaba ɗaya jinta take wata iri kamar ba ita ba. Har kuma lokacin ji take kamar mafarki take yi, za ta farka ta fahimci hakan. Se kuma ta yi ƙoƙarin tunanin Kaseem se ta tuna idan kuma da gaske ne an yi aurenta ba mafarki take yi ba fa? Hakan ne yake sanyata basar da tunanin nasa ta cigaba da zama kawai tana tunanin da yanzun ya zame mata aboki.

Duk wani motsinta tana lura da shi, yanda take komai a nutse a kuma sanyaye ya sa ta ƙara burgeta. Se da ta gama abin da za ta yi sannan ta kalli Atinen kamar jiya tace

"Baba ba za ki kwanta anan ɗin ba?" Girgiza kai ta yi tana buɗe ido daga inda take zaune

"Rufa min asiri Afrah.. Ina ni ina kwana tare da matar masu gida?" Ta faɗa tana murmushi. Ita kam Didi matar burgeta take yi saboda yanda take da barkwanci da kirki. Dan tun jiya ta fahimci hakan, mace ce me kirki.

"Kai Baba.." Didi ta faɗa tana neman waje a kan gadon ta zauna. Ganin tana ƙoƙarin kwanciya ne ya sanya Atinen faɗin

"Wai ni kam ba aure ne ya kawo ki gidan nan ba..?" Ta faɗa sanda ta ƙaraso kusa da gadon ta zauna tana kallan Didi. Shiru Didi ta yi kawai tana kallanta. Ganin haka ne ya sanya Atinen faɗin

"Tun zuwanki gidan nan kin ga mijin naki?" Shirun dai Didi ta sake yi, se kuma can ta girgiza kai a sanyaye.

"Amma shi ne kike zaune? Ba ki taɓa zuwa kin ga a wane hali yake ba? Kuma ga shi kina ƙoƙarin sake kwana a cikin ɗakin nan dan kawai shi be neme ki ba?" Se ta dakata anan tana ɗan girgiza kai sannan ta ɗora da

"Ke yarinya ce Afrah, ba za ki gane abin da nake son nuna miki ba. Amma dai ba wannan ba, kawai tashi ki je ɗakin mijinki ko da gaishe shi ne ki yi ya san dai kin tuna da shi, idan ya so na san zuwa gobe za ki koma can ɗin ma gaba ɗaya, tun da dai ba kya cigaba da zama cikin ɗakin nan ba bayan shi mijin naki yana cikin wani.."

"Baba.." ta faɗa sanda fuskarta ta wani irin narke kamar za ta yi kuka. Ƙoƙarin faɗa mata take yi ita sam ba ma ta san shi ba, ba ta san yanda aka yi auren ba, amma Atine ta katseta da faɗin

"Maza tashi kin ji 'yata.. Kar ki min gardama kin ji?" Ta faɗa tana matsawa kusa da ita ta riƙo hannunta dan miƙar da ita.

"Amma Baba don Allah.."

"Ki yi abin da na ce kin ji?" Atinen ta sake faɗa tana kallanta lokaci ɗaya tana lumshe mata idanu, dan bata ƙwarin gwuiwa a kan abin da take faɗa. Shiru Didi kawai ta yi, tana ji kamar ta rusa ihu, ba ta so ta sake yiwa dattijuwar matar musu, se dai abin da ta sakata yi ɗin ba ƙaramin abu ba ne. Tun da ita dai ba ta san mutumin ba, ba ta taɓa ganinsa ba, ba ta san waye shi ba. Dan har yanzu ita ba ta fahimci wanda aka aura mata ba. Idanunta cike da narkakkiyar ƙwalla ta juyo ta kalli Atine sanda take faɗin

"Ki saka mayafi mana.." Girgiza kai ta yi da sauri, dan ta kasa cewa komai. Se dai ganin Atinen na ƙoƙarin sake cewa wani abu ya sanyata faɗin

"Don Allah Baba ki bar ni da hijab ɗin.." ta faɗa muryarta a raunane.

"Shi kenan.. Hakan ma kin yi kyau sosai.." Atine ta faɗa tana sake feshe Didin ta wani daddaɗan turare me sanyin ƙamshi.

"Mu je na raka ki.." Atine ta faɗa tana yin gaba. Se da suka fito sannan Atine ta ƙarasa dinning, ta ɗakko wani haɗaɗɗen ƙaramin jug na coffee. Se ƙananan cups guda biyu su ma mallakin jug ɗin. Ta miƙa mata tana faɗin

"Yawwah.. riƙe ki gani.. Ki samu ki kai masa wannan na san ze ji daɗi.." Hannu Didi ta saka ta karɓa har lokacin jikinta a matuƙar sanyaye. Atine ta nuno mata ɗakin da ta ga Bad Man ya shiga tace

"Toh je ki 'yata.. Yana ciki.." Kallan ɗakin da Atinen ta nuna mata Didi ta yi, jikinta har rawa yake yi, dan haka kawai ta ji fargaba na kamata. Kawai se ta runtse idanunta sannan ta buɗe, a hankali ta soma takawa zuwa ɗakin hannunta ɗauke da coffee ɗin..



A yi manage da wannan. Shi ma dan masu Comments na yi.😐

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO32*


___ Cigaba ta yi da tafiya har lokacin tana jin yanda jikinta ke rawa. Ta ɗan dakata na tsawon minti guda tana kallan ɗakin kamar me son ganin abin da ke cikinta. Se kawai ta yi shahada ta cigaba da takawa. Dakatawa ta yi sanda ta ƙarasa bakin ƙofar, ta ɗan lumshe idanunta tana ji kamar ta fashe da kuka. Se dai kawai ta sake yin shahada ta ɗaga hannunta ta shiga knocking na ƙofar. Yana zaune a kan er ƙaramar kujerar dake gefen gado sanye cikim riga mara hannu da wandon da yake dab da gwuiwarsa se dai be ƙarasa kan gwuiwar tasa

Please Login or Register in order to submit comment