Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

surutunsa ba ta tanka shi ba ze fice ne ya ƙyaleta. Se dai kafin ta yi aune se jinsa ta yi a kan gadon. Ta juya da sauri ta kalle shi, se ganinsa ɗin kuwa ta yi kan gadon.

"Damm!!" Ƙirjinta ya buga da ƙarfin gaske.

"Na shiga 3.." ta faɗa a kan laɓɓanta tana cigaba da kallansa. Ba tare da yace komai ba ya soma matsawa inda take. Ba ta san lokacin da ta yi baya ba muryarta har ta soma rawa tace

"Wai me ye haka ne kam?" Ta faɗa lokacin da wata ƙwalla ta ida tarar mata cikin idanu. Ƙiris take jira ta zubo. Cikin basarwa yace yana kafeta da idanunsa

"Ina so ne na duba ko lafiyar taki ƙalau, tun da kin ƙi ba ni amsa." Ya yi maganar still yana ƙara matsawa kusa da ita. Dab yake da haɗe tazarar dake tsakaninsu. Ba ta san lokacin da ta yi wani baya ba da sauri. Tana shirin sauka ya sanya hannunsa ya riƙota da sauri, ya yo baya da ita ya zamana ta faɗo kansa. Kawai se ta fashe da kuka. Cikin ƙarfin hali ta sanya hannunta ta riƙo na shi hannun tana girgiza kai ta soma faɗin

"Don girman Allah ka yi haƙuri ka ƙyale ni. Wallahi Allah lafiyata ƙalau.. Ka ƙyale ni don Allah.." ta faɗa hannunta riƙe da na shi da ta ƙi saki tun ɗazun. Be san sanda wata dariya mara sauti ta ƙwace masa ba. Wato duk tsiwarta matsoraciya ce ta ƙin ƙarawa. Gaba ɗaya ta rikirkice, jikinta na wani irin karkarwa kamar wadda ake shirin yankawa.

"Ban yadda ba.." ya sake faɗa yana ƙoƙarin zame hannunsa. Duk wani ƙarfinta ta saka ta sake riƙo hannun nasa da ƙyar ta iya buɗe baki tace

"Na haɗaka da Allah fa.." ta faɗa kamar ba Lulu ba. Saboda yanda hatta muryarta ta koma ta waɗanda za a tausayawa. Se a lokacin ya saketa yana sake riƙe dariyarsa ya sauka daga kan gadon. Yana sakin nata ta yi saurin komawa gefe ta takure waje ɗaya kamar me jin sanyi. Duk wani tsoron Gwanin da ta ji a ranar nan ya sake dawo mata sabo. Amma duk da haka da ta ga ya saketan se da ta saci kallansa ta jefa masa harara tana sake jan bargo ta lulluɓe ilahirin jikinta. Sarai yana lura da duk wani abu da take yi. Shi dai har yanzu ya kasa dena dariya saboda tsoron nan nata ya ba shi dariya ainun.


... Da sallama Baba Atine ta shigo ɗakin. Didi ta amsa sallamar da murmushi kan fuskarta.

"Sannu da zuwa Baba Atine.." Didi ta faɗa.

"Yawwah ɗiyata.." Ta yi maganar tana neman waje ta zauna. Suka gaisa cike da sabo.

"Ina kwana..?" Little ya faɗa yana kallan Baba Atinen. Hannu Baba Atine ta saka ta janyo Little ɗin da murmushi kan fuskarta tace

"Lafiya ƙalau yarona.. ka na lafiya..?"

"Ehh.." ya faɗa yana gyara zamansa a kan cinyarta.

"Kin shirya ne 'Yata?" Baba Atine ta tambaya bayan ta maida dubanta kan Didi. Ɗan ɓata fuska Didi ta yi sannan tace

"Ki yi haƙuri Baba.. kin ga yanzu nake so na shirya." Murmushi Baba Atine ta yi kana tace

"Ai babu koma 'yata. Bari kawai na ɗauki Areef mu je sashen Hajiya. Idan kin gama se ki iskemu a can."

"Tohm shi kenan.." Didi ta faɗa. Miƙewa Baba Atine ta yi hannunta riƙe da na Little.

"Didi se mun dawo." Little ya faɗa yana ɗaga mata hannu bakinsa kamar ze faɗo dan dariya. Duk saboda za a fita.

"Toh Little.." ta ba shi amsa ita ma tana ɗaga masa hannu. Daga haka Baba Atine ta ja hannun Little ɗin suka fice daga ɗakin. Hango Bad Man da ya yi kafin su fice daga ɗakin ya sanya shi sakin hannun Baba Atine ya tafi da gudu wajen shi. Ita sam ba ma ta lura da Bad Man ɗin ba. Dan haka da sauri tace

"Areef!!" Dakatawa ya yi daga inda yake. Ya ɗaga idanunsa ya sauke su kan Baba Atine da yake da tabbacin ita ce ta kira sunan shi. Daidai lokacin kuma da Little ya riƙo hannunsa yana faɗin

"Uncle.." Se a lokacin Baba Atine ta lura da shi. Cike da girmamawa ta ƙaraso kanta a ƙasa tace

"Barka da wannan lokaci Yallaɓai.."

"Barka.." Ya amsa a taƙaice. Se ta maida dubanta kan Little tace

"Taho mu tafi.." Maƙe kafaɗa ya yi yana wani cuno baki lokaci ɗaya kuma yana sake riƙe hannun Bad Man ɗin da kyau. Sauke idanunsa Bad Man ya yi a kansa yace

"Me ye sunanka?"

"Areef.." Murmushi ne ya wanzu a kan fuskarsa jin da ya yi sunansu iri ɗaya. Karon farko kuma da ya ji yaron ya burge shi. Se ya saka hannunsa ya riƙo shi, daidai lokacin da ya maida dubansa kan Baba Atine yace

"Ki je kawai.." Babu musu ta amsa da

"Toh Rankayadaɗe.." Daga haka ta fice daga ɗakin. Shi ma ficewa ya yi daga ɗakin har lokacin hannunsa riƙe da na Little. Kai tsaye parking space ya wuce inda yake da tabbacin Kaseem na jiransa. Aikuwa yana tsaye hannunsa sarƙe a ƙirjinsa yana jiran fitowar Bad Man ɗin. Tun daga nesa yake sake buɗe idanunsa yana kallan yaron da ke hannun Bad Man. Har dai zuwa lokacin da suka kusa ƙarasowa.

"Laaa!!" Little ya faɗa yana kallan Kaseem bayan ya dakata. Se kuma ya ƙarasa da gudu ya rungume shi. Tabbatar da lallai wannan ɗin Little ne ya sanya Kaseem saka hannu ya rungume shi. Kafin ya buɗe baki yace

"Areef.. Ya na ganka a nan?"

"Wajen Didi na zo.." Ya faɗa bayan ya ɗago yana kallan Kaseem ɗin.

"Didi kuma?" Kaseem ya faɗa cike da mamaki. Cike da mamakin dai Bad Man ke kallansu. Se dai hakan be nuna ba a kan fuskarsa. Tambayar da ke ta masa lugude cikin kai ita ce ta sanya shi gyara tsayuwa yace yana kallan Kaseem

"Da ma ka sansu ne?" Se da ya kalli Bad Man ɗin sannan ya soma faɗin

"Ehh.. na sansu sosai.. Musamman ma yayar tasa. Dan mun yi soyayya da ita a da, amma Allah be yi zan aureta ba. Se dai kuma a yanda na sani yanzu haka ta yi aure shi ya sa ban fahimci maganar Areef ba." Harɗe hannayensa a ƙirji Bad Man ya yi yana kallan Kaseem kamar me son gano wani abu daga kan fuskar tasa. Kaseem na shirin sake yin magana Bad Man ya katse shi da faɗin

"Ni ne mijin nata.." Ya faɗa cikin basarwa. Ɗaga ido Kaseem ya yi ya kalli Bad Man irin kallan mara hankalin nan. Duk da be san Bad Man ɗin na shaye shaye ba amma tabbas yau yana da yaƙinin ya sha wani abu. Ta yaya ma shi ɗin ze kasance mijin Afrah? Ta yaya ma hakan za ta faru? Cigaba da masa kallan tuhumar nan ya yi yana jira ya sake jin wani abu ya fito daga bakinsa. Se dai shi ma ɗin kawai kallansa yake yi ba tare da yace uffan ba. Daidai nan Didi ta fito daga sashensu sanye cikin doguwar riga da hijab ɗinta madaidaici. Ta yi wani shahararren kyau kamar wadda ta kwashe awanni tana shiryawa. Kamar wanda aka ce ya ɗaga kai yana ɗagawa kuwa idanunsa suka sauka a kan Didin da ke cigaba da takawa. Haka nan kawai ya ji zuciyarsa ta buga. "Ka da fa a ce da gaske Bad Man ɗin yake masa?" Ya tambayi kansa cike da fargaba. Haka nan kawai ta ji ido na yawo a kanta. Duk se ta ji ta tsargu, dan haka ta ɗaga kanta dan ganin me kallan nata. Cikin sakannin da basu wuce 5 ba suka yi 4 eyes ita da Kaseem. Babu shiri ta dakata a inda take zuciyarta na soma gudu. Kawai se aka shiga kallan kallo tsakaninsu, kowa da abin da yake saƙawa a ransa..


✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO56*

___ A hankali Bad Man ya ɗaga idanunsa ya kalli inda Kaseem ɗin ke kallo, dan shi sam be san da wanzuwar Didi a wajen ba. Se kuwa idanunsa suka sauka a kan Didi wadda zuwa yanzun ta sauke idanunta daga kan Kaseem ɗin. Ya yin da shi kam Kaseem ko gezau har zuwa lokacin idanunsa na kan Didin. Wato lokacin da Bad Man ya maido da dubansa kan Kaseem. Haka nan kawai ya ji ransa ya sosu, ba kuma dan komai ba se dan yanda ta kasance matar aure. Duk da shi dai ya san ba sonta yake yi ba, amma kuma abin da Kaseem ɗin yake yi sam be dace ba. Ya kuma zama dole ya taka masa burki tun kafin ya ƙarasa fusata shi. Ya ɗan runtse idanunsa kafin ya buɗe su. Cikin takun nan nasa ya soma takawa zuwa inda Didi take. Ba tare da ta lura da hakan ba. Se kawai tsintar shi ta yi dab da ita kamar wanda ke shirin rungumeta. Cike da fargaba ta yi saurin yin baya a ranta tana jin haushin kanta da ta tsaya kallan Kaseem ɗin. Yanzu idan ya ganta da wane ido za ta kalle shi? Duk da ta san be ɗauketa matsayin matarsa ba amma ko babu komai hakan da ta yi be dace ba. Sake matsawa ya yi kusa da itan, daidai lokacin da ƙirjinta ya wani irin bugawa ta ji ina ma ƙasa ta tsage kawai ta shige da dai wannan mutumin yace ze hukuntata. Ba ta yi tsammani ba se jin tattausan hannunsa ta yi a tsintsiyar hannunta ya riƙe da ƙarfin gaske. Ba ta san lokacin da ta ɗaga kai ta kalle shi ba. Ya watsa mata wani kallo da ba ta taɓa ganin ya yi kalarsa ba. Duk se ta sake jin jikinta ya yi mugun sanyi har ba ta san lokacin da ta tara ƙwalla cikin idanunta ba. Ba tare da yace komai ba ya sake riƙe hannun gam yanda ya san za ta ji zafi. Aikuwa se da ta runtse idanunta tana ji kamar ta fashe da kuka. Se ya soma takawa zuwa sashensu. Ba tare da ya sake kallan inda Kaseem ke tsaye ba suka shige cikin ɗakin. Se a lokacin ya saki hannun nata sannan ya juya da niyyar ficewa. Se kuma ya juyo ya kalleta kamar wanda aka wa dole yace

"Idan na sake ganin ƙafarki a wajen sashen nan za ki ga abin da zan miki.." Ya ƙare yana yin ƙwafa. Be jira tace komai ba ya fice dan zuwa ya ji da Kaseem. Hannunta ta riƙe tana ji kamar har yanzu be saketa ba saboda zafi. Ta kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka. Duk haushin kanta ya ƙi sakinta. Tuna abin da ya faɗa ne ya sanyata wucewa ɗakinta ba tare da sake tunawa da inda za ta je ba.

Runtse idanunsa Kaseem ya yi lokacin da ya ga hannun Bad Man a kan na Didi. Shi kenan ashe da gaske yake kenan? Ya aka yi hakan ya faru? Me ya sa aka hana shi auren Didin aka kuma aurawa Bad Man? Ko dan ya fi shi arziƙi ne mahaifinsa sananne ne cikin garin Kano? Ko kuwa Areef ɗin ya fi shi wani abun ne da ake buƙata a wajen namiji? Me ya sa aka masa haka? Shin ba su san waye Areef ba? Ko kuwa sun ɗauka yanda mahaifinsa yake haka shi ma yake? Ashe da ma auren da kwanaki Bad Man ɗin ya yi Afrah aka aura masa? Ta yaya hakan ta faru? Ya dai san Areef ɗin ya fi shi kyau, arziƙi da wasu abubuwan da dama. Se dai kuma a wannan fannin yana ganin shi ne ya dace a ce ya samu Didi ba Bad Man ba. Dan kuwa idan dai har hali ne na gari ya san ya fi Bad Man ɗin. Ɓacin rai da baƙin ciki babu abin da ba su sanya zuciyarsa ta kawo ba. Ya kasa haƙura, ya kuma kasa dannewa. Gani yake kamar amanar shi aka ci. Aka raba shi da wadda yake so aka ɗauka aka bawa wanda sam be cancanta ba. Ba tare da Bad Man ya kalle shi ba ya soma ƙoƙarin buɗe ƙofar mota.

"Malam ka tsaya ka min bayanin abin da ke faruwa mana.. Ya aka yi haka? Zuciyata na dab da bugawa." Kaseem ya ƙare yana kallan Bad Man. Kallan Little Bad Man ya yi ya miƙa masa hannu a hankali yace

"Let's go.." Babu musu Little ya tafi da sauri wajen nasa. Ganin da gasken motar ze shige ba tare da ya tanka masa ba ya sanya shi faɗin

"Ka ƙi ce min komai.. Hakan na nufin ba ka da gaskiya kenan.." Se a lokacin sannan Bad ya dakata. A nutse ya ɗaga kansa ya dubi Kaseem. "Me yake nufi da ba shi da gaskiya?" Ya tambayi kansa. A fili kuma se cewa ya yi

"Duk yadda ka ɗauka haka ne.." Kansa Kaseem ya dafe. Da ma ya san halin Bad Man ɗin, ba lallai ne ya samu amsar tambayar da ya masa ba. Se dai kuma har ga Allah ze so ya ji yanda aka haihu a ragaya. Ta yadda hakan ta kasance. Wai Areef shi ne mijin Afrah. Kawai se ya juya a matuƙar fusace ya haye motarsa ya figeta da ƙarfin gaske. Ba tare da ya kalli inda Bad Man da Little ke tsaye ba ya sake baiwa motar gudu ya bar wajen. Taɓe baki Bad Man ya yi daidai lokacin da ya kalli Little da ke faɗin

"Me aka yi wa Uncle?" Se da ya ɗan yi murmushin gefen baki kafin yace

"Ba shi da lafiya.." Rashin sanin amsar da ze bayar ne ya sanya shi yin shiru kawai. Daga haka suka faɗa cikin motar. Kai tsaye Bad ya tashi motar suka fice daga gidan kamar ko yaushe ba tare da ya bi ta kan mutanen Daddy ba.



... Tun da ya ji labarin rufe gidan Ladi hankalinsa ya ƙi kwanciya. Musamman idan ya tuna tona mata asiri da ya yi ya san idan ta ɓaɓe mata za ta iya ambatar sunansa. Haɗa kayansa yake yi cikin wata bagco dan kuwa ko me ze faru yau ba se gobe ba ba ze sake kwana cikin garin Kano ba. Daidai yana ida haɗa kayan aka turo ƙofar ɗakin. Ya ɗaga kai da sauri abinka da mara gaskiya.

"Huuu Bad.. Ashe kai ne.." ya faɗa yana sauke ajiyar zuciya.

"Za ka iya kama shi.." Bad Man ya faɗa yana yin nuni da Hero. Babu ɓata lokaci wanda suka shigo tare da Bad Man ya saka hannu ya riƙo Hero. Waro ido Hero ya yi. Kar fa ya je har ta kwaɓe da shi tun kafin ya bar cikin garin nan? Ya tambayi kansa. A fili kuma se ya kalli Bad Man yace

"Haka za mu yi da kai Abokina? Me na maka? Na ɗauka ko me ye ya shiga tsakanina da kai kai me iya rufa min asiri ne?" Ko nuna ya ji abin da ya faɗa ma be yi ba se ficewa daga cikin ɗakin da ya yi. Hero ya yi iya ƙoƙarinsa wajen ganin ya ƙwace kansa, se dai da yake mutumin ƙwararre ne wajen kama masu laifi kuma kakkaura ya sa ko gezau be yi ba, a haka har ya fitar da Hero daga cikin ɗakin.

.. Ɗaga kai Little ya yi ya kalli Bad Man lokacin da ya shigo cikin motar. Murmushi kawai ya sakar masa ya maida dubansa kan wayar Bad ɗin da ke hannunsa ya cigaba da dannawa. Yana shirin tayar da motar wayarsa ta soma ruri. Se ya dakata ba tare da ya kalli wayar ba. Kamar ba ze kulata ba se kuma a nutse ya saka hannu ya karɓi wayar da Little ɗin ke miƙo masa yana faɗin

"Ana kiranka.." Kai tsaye duba me kiran ya yi. Sam be yi tsammanin ganin kiran Mom ɗin ba. Se dai kuma numberta ke yawo a saman screen ɗin wayar tasa.

"Mom..!" Ya faɗa yana dafe kansa dan ya san zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi..




Asslm.

A cigaba da min uzuri kar ku ga ba kwa samun Update kullum. Ba ni da lafiya ne. Kawai dai daurewa nake yi a hakan nake samu na yi. Toh ranar kuma da jikin ya ƙi min daɗi shi ne ranar da za ku ga ban yi Update ba. Saboda haka a yi manage da wannan dan wallahi da ƙyar na yi.



✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO57*


___Daga can ɓangaren Mom tace

"Ina ta kiranka ba ka ɗauka ba?"

"Ba na kusa ne Mom." Ya faɗi hakan kansa na kallan waje.

"Ohk toh yanzu ka na ina ne? Ka taho nan ɗin ne? Ko kuwa ka zaɓi inda za ka je." Numfashi ya ɗan zuƙa kana ya fesar da shi a lokaci guda. Yace

"Mun yi magana da Daddy.. Ya ce babu inda zan je."

"Oh my goodness! Wai kenan ni yanzu ba zan iya saka ɗana ya yi wani abu ba? Fisalillahi.. iyeee??" Ta ƙare a zafafe, dan babu ƙarya ta fusata. Shiru ya yi dan be san me ze ce mata ba. Se dai kuma ba ya so ta sake masa magana a kan barin ƙasar, dan haka yace

"Amm kar ki damu Mom, zan shawo kansa. Ba se kin sake kirana ba. Ina isa ko ma ina ne zan kira ki." Sauke ajiyar zuciya Mom ta yi sannan tace

"Toh shi kenan. Ka kula da kanka dai tun da ba na kusa."

"Umhum." Ya amsa da hakan yana ajje wayar. Daga haka ya tayar da motar suka bar wajen.


... Fitowarta kenan daga ɗakin Abeey, hannunta ɗauke da flask me nutsatstsen kyau. Se ta ji an yi sallama. Ta ɗaga kai ta kalli me sallamar daidai lokacin da take amsawa. Murmushi Fatima ta yi tana ƙarasawa inda Ummeeyn take. Cikin girmamawa tace

"Barka da wannan lokaci Umma.."

"Barkanki dai yarinya.. Kin zo lafiya?" Ta tambaya bayan ta maida mata da martanin murmushin.

"Ehh Alhamdulillah.."

"Toh madallah.." Daga haka se shiru ya wanzu na en wasu sakanni. Kafin Fatima ta katse shirun da faɗin

"Umma Afaaf na nan?" Se a lokacin sannan Ummeeyn ta gane wace Fatiman. Don kuwa tun ɗazu take ƙoƙarin lalubo wace ce ita ta kaasa.

"Tana ciki.." Ummeey ta faɗa har lokacin da murmushi kan fuskarta. Se ta miƙe daidai lokacin da take furta

"Yawwah na gode.." Daga haka ta wuce ɗakin Lulun. Kasancewar ƙofar a ɗan tokare take kawai ya sanya ba ta tsaya ƙwankwasawa ba, kai tsaye ta tura ƙofar ta shige bakinta ɗauke da sallama. Kamar daga sama ta jiyo muryar Masoyiyarta. Se kuwa zumbur ta yi saurin tashi zaune.

"Oyoyo Masoyiya.." ta faɗa har cikin ranta tana jin wani irin farin ciki. Ƙarasawa Fatima ta yi ta rungumeta tana faɗin

"Masoyiyatah matar aure.." Ta faɗa tana murmushi. Hannu Lulu ta saka ta ture hannunta bayan ta jefa mata harara tace

"Ke dai haka za ki ƙare.."

"Oho dai.." Fatima ta faɗa tana dariya. Neman waje ta yi ta zauna gefen Lulun.

"Ya mu'allim ba ya nan ne..?" A niyyarta ta buɗe baki tace "Oho masa" Se dai kuma a karo na farko ta ji be kamata har yanzu ta din ga bari Fatiman ta san yanda zamansu da Gwanin ke kasancewa ba. Don haka se ta jefa mata harara tace

"A'ah ga shi a bayana.." Dariya Fatima ta yi sosai har da tsintsirawa.

"Wai Masoyiya me ye haka ne? Wannan maganganu da ki ke ta yaɓa min. Ko dai ba ki yi farin cikin zuwana ba..?" Ta ƙare tana langaɓar da kai gefe.

"Ke Allah kuwa a'ah Masoyiya.. Na ji daɗi fiye da yanda ki ke tsammani."

"Shi ya sa ma na ga har kin kawo min ruwa." Fatima ta faɗa tana jefa mata harara.

"Toh yi haƙuri.." Ba tare da ta jira amsar Fatiman ba ta miƙe cike da takatsantsan gudun kar Fatiman ta fahimci wani abun. Ta wuce wannan ƙaramin ɗakin ta ɗauko ɗaya daga cikin jug ɗinta me shegen kyau. Fita ta yi daga ɗakin zuwa tsakar gida. A nan ta samu Ummeeey. Ta yi ƙasa da kai dan har yanzu ba ta dena jin kunyarta ba. Se dai ta maaze kawai tace cike da nutsuwar da tafi wadda ta sameta a kwanakin baya.

"Ummeey.."

"Na'am Afaaf.. kin samu kin fito kenan?" Se kawai ta yi yaƙe ba tare da tace komai ba. Ganin da Ummeeyn ta yi idan dai har ta tambayi Lulun jikinta kunya take bata ya sanyata ƙin tambayarta a yanzun.

"Ruwa za ki ɗiba ne?" Ummeey ta tambaya tana kallan jug ɗin hannunta. Se ta jinjina kai tana faɗin

"Ehh baƙuwa na yi."

"Kawo na ɗibar miki cikin randa dan na san yanzu haka ya yi sanyi." Da ma ita ma abin da ya fito da itan kenan, don ta san randar Ummeeyn akwai ɗaukar sanyi. Har tana shirin miƙa mata jug ɗin se kuma ta ga kamar hakan be dace ba. Dan haka se kawai ta yi murmushi tace

"A'ah Ummeey ki bar shi zan ɗibo.." Murmushi Ummeey ta yi tana bin Lulun da kallo lokacin da ta wuce wajen randar ta buɗe ta ɗiba.


Sauke numfashi Lulu ta yi lokacin da ta zauna a kan gadon tace tana miƙawa Fatima Jug ɗin

"Ga shi ki sha ki ƙoshi.."

"Yawwah ko ke fa." Ta faɗa tana karɓa. Se kuma ta ɗora da

"Wai ba ki da lafiya ne?" Da sauri Lulu ta kalleta cike da mamakin abin da ta faɗa ɗin

"Me ki ka gani?" Ta yi ƙarfin halin faɗin hakan.

"Ganinki na yi kamar ba ke ba. Kin zama shiru shiru.. Ke kin dai koma kamar Didi." Sauke ajiyar zuciya ta yi tana ɗan lumshe idanunta. A fili kuma se ta harari Fatiman tace

"Oho miki dai."

Hira sosai suka sha kasancewar sun kwana biyu ba su ga juna ba. Fatima na sake jin daɗin yanda Lulun ta sauya kamar ba ita ba. Babu laifi ta ɗan jima a gidan. Se dai kamar yanda ta yi wa Ummanta alƙawari ba ta wuce hakan ba. Don haka lokacin da ta gama shiri se ta kalli Lulu tace

"Toh ni zan tafi.. Se haɗuwa ta gaba." Ba dan Lulu ta ji daɗi ba ta buɗe baki za ta yi magana Fatima tace

"Laaa Masoyiya na manta ban faɗa miki ba. Kin san da wa na haɗu ɗazu kuwa?" Girgiza kai Lulu ta yi kana ta amsa da

"A'ah.."

"Mutuniyarki Abida.." ta ƙare tana taɓe baki. Kallanta Lulu ta yi, cikin mamaki tace

"A'ah da ma ba ku na haɗuwa kullum a Islamiyya ba.?"

"Waaa..? Abidar? Tun yaushe aka koreta ke kam? Har babansu fa se da ya daɗe yana zuwa makarantar wai ashe duk a kan halin Abidar ne. Se daga baya kuma ya dena zuwa." Shiru Lulu ta yi na tsawon sakanni masu ɗan yawa. Ashe ma an kori Abidar daga Islamiyyar?

"Ai gwara haka.. Allah Ya shirya." Lulu ta faɗa.

"Ameen. Uhmm kin ga wucewata Masoyiya bye.." ta faɗa tana juyawa.

"Na gode sosai Masoyiya. Don Allah ki gaida min da Umma."

"Za ta ji." Ta ƙare maganar lokacin da ta gama ficewa daga ɗakin. A tsakar gida ta tarar da Ummeey da kuma Gwani da shigowarsa kenan. Cikin girmamawa tace

"Barka da wannan lokaci Ya mu'allim."

"Barka dai Fatima." Gwani ya amsa da hakan yana miƙewa tsaye daga zaunen da yake kan tabarmar da Ummeey ta ke kai.

"Toh Ummeey na tafi.." Fatima ta faɗa tana kallan Ummeey.

"Toh a gaida mutanen gidan."

"Za su ji In Sha Allah." Daga haka ta fice daga gidan.


... A karo na barkatai ta sake kallan agogon ɗakin da ya nuna ƙarfe 8 na dare daidai. An ya kuwa Little ɗin na sashen Mommah? Ko dai ya taho shi ɗaya be gane hanya ba ya yi wani wajen? Ta tambayi kanta tana miƙewa tsaye. Ita dai har ga Allah hankalinta ba ze taɓa kwanciya ba idan ba ta ga Little ɗin ba. Miƙewa ta yi a nutse ta fice daga ɗakin. Daidai ta zo fita ta tuna da gargaɗin da ya mata ɗazun. Se ta dakata tana ji kamar ta fashe da kuka. Ta fi ƙarfin minti 10 tsaye a wajen ba tare da ta sake yunƙurin yin komai ba. Se kuma a hankali ta juya da niyyar komawa.

"A'ah Rankiyadaɗe." Ta jiyo muryar Baba Atine. Se ta juyo da sauri cike da jin daɗin ganinta. Don ko babu komai ta san ita ta fita da Little. May be ma yanzun ta dawo mata da shi ne. Se dai se ta ga Baba Atinen ita ɗaya ba wani Little.

"Ina Areef ɗin.. Ko ya yi bacci ne?" Baba Atine ta tambaya tana murmushi.

"Ai ba ya nan Baba."

"Ba ya nan kuma?"

Please Login or Register in order to submit comment