Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mommah ta ji ba. Dan haka ta kira Baba Atine.

"Atine ki samu ki kai min su ɗaki.. Ba na buƙatar a yi musu komai da kaina zan yi.. Yanzun nan zan shigo.." Mommah ta ƙare tana murmushi.

"An gama Hajiya." Baba Atine ta faɗa cikin girmamawa.

... Tuntuni yake lura da yanayinta, ya kuma kasa haƙuri, be san dalilin da ya sa ya ganta cikin matuƙar damuwa ba. Dan haka suna fita be bari ta shiga ɗaki ba ya yi saurin ƙarasawa inda take. Cikin damuwa yace

"Afaaf.." Dakatawa ta yi daga inda take, dan da ma ta lura da fitowarsa daga ɗakin, bayan Mommah ta sallame su, ya yin da ta ƙi barin Bad Man ya fita. Aikuwa kawai zama ya yi amma hankalinsa ba ya wajen, dan kuwa ya san dalilin da ya sa Mommahn ta ƙi barinsa fita, dan kar ya bi Didi ne. Wai shi da matarsa amma an hana shi ko da magana ne da ita. Ko kallanta ya yi se ya samu tsarabar kallan nan na Mommah na gargaɗi. Gaba ɗaya dai Mommah ta maida shi tamkar wani kwarto.

Kasa juyawa ta yi dan har lokacin ba ta ji ta koma daidai ba. Ganin ta ƙi juyowa ne ya sanya shi zagayawa ya tsaya a gabanta. Ya zuba mata idanunsa kamar wanda ze karanci abin da ke damunta. Sam ta kasa ɗaga ido ballantana ta kalle shi.

"Me ya faru Uhmm?" Ya tambaya cikin kulawa kuma a hankali kamar me raɗa. Hannunta ta kama ta shiga murzawa kaɗan, kamar za tace wani abu, se kuma ta girgiza kai kawai. Ta ɗaga ƙafa tana shirin tafiya ya riƙo hannun nata da sauri yana faɗin

"Ki faɗa min don Allah.." Yanzu kam ɗaga idanunta ta yi ta kalle shi. Se kuma ta janye da sauri. Har ga Allah wata irin kunyarsa take ji. Haka nan kawai take ji idan ta ɗore da sauyawar da ta yi a yanzu haka ze kawo ko dan ta fahimci waye shi ne. Duk da tun kafin sanin waye shi ɗin ta soma chanjawa amma yanzu ita dai haka take ji, ze yi tunanin dalilin chanjawarta kenan. Se da ta ja numfashi kafin ta buɗe baki cikin ƙarfin hali tace

"Don Allah Didi na jirana.." Ta yi maganar muryarta na rawa. Shi dai sam ya kaasa samun nutsuwar zuciya tun da ya ganta a irin wannan halin. Da alama kuma ba sanar da shi abin da ke damunta za ta yi ba. "Me ya sa har yanzun?" Ya tambayi kansa. Se ya sauke ajiyar zuciya yana sakin hannun nata. Ta yi amfani da wannan damar wajen saurin shigewa cikin ɗakin. Binta ya yi da kallo har ta shige ɗakin, kafin ya ɗauke kansa yana ficewa daga sashen.


.. Se da dare sannan Mommah ta samu suka zauna da en biyunta. Bayan ta fito daga ɗakin da baƙin da suka kwana suke ta tabbatar ba sa buƙatar komai, sannan ta dawo sashenta. A palour suka zauna, kamar kowanne lokaci yanzu ma se da ta soma tambayarsu lafiyarsu da kuma tambayar ko akwai wani abun, duka suka amsa mata da babu. Se suka ɗan cigaba da tattaunawa. Mommah so take ta yi shawara da Gwani a kan maganarsu Ummeey, se dai tafi so su yi maganar ne tare da Daddy. Shi kuma yanzu haka hutawa yake yi saboda yau ɗin da ya wuni gaba ɗaya be runtsa ko kaɗan ba.

"Ya asibitin kuwa? Me ke damunta?" Mom ta tambaya tana kallan Gwani. Hannu ya kai ya ɗan shafi gefen ƙeyarsa. Ya ɗan yi murmushi duk da gefe guda kuma hankalinsa na cikin ɗakin dan ganin ta inda za ta ɓullo. Cike kuma da fatan kar ya ganta kamar yanda ya ganta ɗazun.

"Mommah.." Ya faɗa yana dakatawa.

"Na'am." Ta amsa yana karantarsa. Kawai se ya yi ta maza ya maaze yace

"Wai tana ɗauke.. da.. juna biyu ne.."

"Kaiii!! Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!" Shi ne abin da Mommah ta soma faɗa lokacin da ya kai ƙarshen maganarsa.

"Allah Ubangiji Ya ɗayyiba, Ya kuma inganta.. Kai Alhamdulillah.. Allah Ka ƙarawa Annabi daraja." Mommah ta sake faɗa, farin cikin da take ciki sam ya kaasa ɓoyuwa a kan fuskarta. Yanda ya ga zallar farin ciki a fuskar Mommahn shi ne ya sanya shi sake jin daɗi. Ya kuma sake godewa Allah. Ita kam Mommah ba ta san wacce irin godiya za ta yi wa Allah ba. Ga danginta sun dawo cikin rayuwarta, ga kuma jika tana shirin samu nan kusa. Lallai Allah shi ne abun godiya.

"Congratulations bro.. Ashe na kusa zama uba." Bad Man ya faɗa kyakkyawan murmushi kwance kan kyakkyawar fuskarsa. Jinjina kai Gwani ya yi har lokacin fuskarsa ɗauke da ƙawataccen murmushi.

A ɗaya ɓangaren kuwa tashi Didi ta yi daga kan daddumar ta ninketa, sannan ta ajjeta a ma'ajiyarta kafin ta kalli inda Lulu ke zaune ta yi shiru, ta ƙurawa waje ɗaya ido kamar me tunani.

"Amma dai ba zazzaɓin ba ne koh?" Didi ta faɗa lokacin da ta zauna kusa da Lulu. Se a lokacin Lulu ta ɗaga kai ta kalli Didi, ba tace komai ba se turo baki da ta yi ta shiga ɓata rai kamar wadda aka ɓatawa rai.

"Kaii!! Toh me kuma ya faru?" Didi ta sake faɗa tana kallan nata. Ita Allah ma ya gani ba ta san ta ina za ta fara ba. Da wane idon za ta cigaba da kallan Didi idan tace mata ciki ne da ita? Taɓ ɗi jam. Daidai lokacin Mommah ta shigo cikin ɗakin. Ta ƙarasa ta nemi waje ta zauna tana kallansu su duka. Se da suka sake gaisawa da Mommahn sannan tace

"Afaaf.."

"Na'am.." Lulu ta amsa tana kallan Mommah. Murmushi Mommah ta yi kana ta soma faɗin

"Allah Ya yi miki albarka Afaaf, Ya inganta abin da ke cikinki, Ya kawo shi lafiya.. Ya kike jin jikinki yanzu? Babu abin da ke damunki dai koh?" Shiru ta yi bayan ta ɗauke kanta da sauri. Ba ta taɓa tunanin Mommahn ta sani ba, dan ba ta ɗauka Gwanin ze iya faɗa mata ba. Yanzu shi saboda rashin kunya da rashin ta ido Mommahn ya faɗawa wannan maganar Wannan abun kunya da me ya yi kama.

"Uhmmm?" Mommah ta sake tambaya. Se ta yi saurin jinjina kai har lokacin ba ta ɗaga kai ta kalli Mommahn ba, se hannunta da take murzawa a hankali.

"Toh ki kula sosai.. Idan ki na buƙatar wani abu ki sanar da ni. Afrah ki kula da er uwakki.. Allah Ya yi muku albarka." Ta ƙare yanzun tana kallan Didi. Se a lokacin Didi ta ɗauke kanta daga kallan Lulu da take tun ɗazu, ta yi murmushin yaƙe tana faɗin

"Toh.."

"Akwai abin da zan yi yanzu.. Bari na je."

"Toh Mommah.." Shi ne abin da Didi ta faɗa, da ma ta ƙagu Mommahn ta fita daga ɗakin. Aikuwa kamar ta sani ɗin se ta fice daga ɗakin. Maida fuskarta yanda take Didi ta yi ta ƙurawa Lulu ido. Duk da yanda gefe guda wani farin ciki ke neman danne ɓacin ranta, ta yi fatali da hakan, ta ƙi bari ya yi tasiri a kanta.

"Ciki ne dake Lulu shi ne ba ki faɗa min ba?" Didi ta faɗa har cikin muryarta ɓacin rai na bayyana. Da sauri Lulu ta ɗaga kai ta kalleta jin muryarta da ke ɗauke da fushi. Se ta yi saurin girgiza kai tace

"Ba haka ba ne Didi.. Ba ƙin faɗa miki na yi ba."

"Ya ishe ni.. Ni babu abin da za ki faɗa min." Didi ta faɗa bayan ta ɗaga mata hannu. Ta miƙe, dan idan ba ta yi wasa ba farin cikin na dab da danne ɓacin ran gaba ɗaya. Riƙo hannunta Lulu ta yi tace

"Don Allah ki yi haƙuri Didina.. Wallahi ba haka ba ne.. Kin ga ni fa Allah.." Se kuma ta yi shiru. Harara Didin ta jefa mata kafin tace

"Allah me..?"

"Toh ni kunya nake ji, na rasa ta ina zan fara faɗa miki.. Haka kurum.." Ta ƙare tana turo baki. Yanzu kam haƙura ta yi ta sheƙe da dariya sosai har da toshe baki. Daidai lokacin da aka turo ƙofar ɗakin. Duka suka ɗaga kai suka kalli wadda ta turo ƙofar ɗakin. Sanye take cikin wata haɗaɗɗiyar doguwar riga, ta yafa yalolon mayafinta da ta yi amfani da shi wajen rufe gashin kanta. Hannunta ɗauke da tsadaddiyar wayarta da take dannawa. Idanunta ta kai cikin ɗakin daidai lokacin da suma suka kalleta.

"Oh.. yi haƙuri fa.." Ta faɗa a ɗan yatsine tana sakin ƙofar bayan ta watsar da su. Ba ta jira sun ce komai ba ta yi gaba tana taɓe baki. Kallan juna Lulu da Didi suka yi. Haka nan kawai se su ka ga abun wani iri. Kamar irin da gangan ta yi hakan.

"Wace wannan ɗin? Me ye hakan ta yi? Ni fa ba ba na son rashin mutunci." Lulu ta faɗa fuskarta a haɗe. Sanin hali ya sanya Didi faɗin

"Ke babu fa komai. Ƙila akwai wadda take nema ne, ta yi kuskuren zuwa ɗakin nan.." Didi ta ƙare tana murmushi duk da ita ma ta fahimci wani abun..


✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO75*


... Kusan a tare Mommah da su Lulu suka fito daga ɗaki. Dukkansu shirye cikin shiga me kyau, wadda ta yi matuƙar dacewa da su. Kaya iri ɗaya Lulu da Didi suka saka, sun sake fitowa a en biyunsu sakk. Se dai Lulu sosai take sake murjewa, ta ƙara wani shahararren kyau. A palour suka tarar da Iftihal da ke zaune kan kujera, t.v na ta aikinta ya yin da idanunta ke kan wayarta tana dannawa. Murmushi ta yi lokacin da ta ɗaga kanta ta kalli Mommah tace

"Barka da wannan lokaci.."

"Barka dai.. Ki na lafiya?" Mommah ta faɗa tana murmushi.

"Alhamdulillah." Ta amsa tana maida dubanta kan waya. Kamar yanda ba ta kallesu ba haka su ma babu wanda ya kalleta. Takaici ya kamata, su ba su san ita ɗin tana da bambanci da su ba ne? Ba su san ita ɗin wace ce ba? A hankali ta ɗaga kai ta watsa musu wani banzan kallo, daidai lokacin da Lulu ta ɗaga kai. Se kuwa kallan ya sauka a kan fuskarta, da ta jefa mata wani kallo da ya fi nata muni da manyan idanunta masu kyau kafin ta watsar da ita. Haushi takaici suka sake rufe Iftihal. Lallai dole ne ta koyawa yarinyar nan hankali.

"Ifti ko za ki bi mu ne..?" Mommah ta faɗa tana murmushi. Se da ta sake watsawa Lulu harara sannan ta girgiza kai kafin tace

"A'ah.. zan zauna a nan.. Se kun dawo." Ta ƙarasa maganar tana soma danna wayarta.

"Babu damuwa?" Mommah ta sake faɗa cikin kulawa.

"Eh babu.." Se a lokacin sannan Mommah ta kalli su Didi tace

"Mu je.." Ta bi su da kallo sanda suka fice ɗin, a ranta tana jin daɗin hakan, ko babu komai ta san mazan gidan za su shigo sashen ba tare da sanin Mommah ta fita ba. Ita kuma dama irin wannan damar take so. Se dai abin da ba ta sani ba Mommahn tare suka fita da su Gwani gaba ɗaya, dan za su je su gaida su Ummeeyn ne kafin su baro su Mommahn a can. Da farko da ba ma tare za su je da su Lulu ba, se dai Mommah ta san duk lokacin da ba ta gidan Areef kan iya amfani da wannan damar wajen zuwa wajen Didi. Shi ya sa ƙafarta ƙafarsu.


.. "Yallaɓai lafiya na ganka haka?" Mommah ta faɗa tana kallan Daddy. Se ya yi murmushi kafin yace

"Abin da zan tambayeki kenan kika riga ni. Ko dai kin saka damuwa ne cikin ranki?" Girgiza kai Mommah ta yi kafin tace

"A'ah.."

"Idan ma dai damuwar abubuwan da suka faru ne, toh ki kwantar da hankalinki tun da komai ya warware. Idan kuma komai ya sake lafawa se ku je ku ziyarci dangin mahaifinku." Jinjina kai Mommah ta yi cikin na'am da zancen Daddyn sannan tace

"In Sha Allah.. Amma kuma Yallaɓai ka kautar da tambayar da na maka." Rufe idanunsa Daddy ya yi kamin ya buɗe. Be san ta ina ze fara ba, har yanzu ya kasa mantawa da abin da Mom ta aikata. Zuciyarsa har yanzu ta kaasa samun sukuni. Ban da wannan babu abin da ke damunsa.

"Kar ka ki wani damu. Babu abin da ke damun mijinki." Ya ƙare cikin barkwanci. Dariya Mommah ta yi cikin ranta tana fatan Allah Ya yaye musu damuwarsu gaba ɗaya. Se suka ƙarasa wajen motar duk suka shiga. Areef da ke zaune a wajen zaman driver ya ja motar suka fice daga gidan.

Sosai Ummeey ta ji daɗin ganinsu cikin gidan, musamman da ya kasance dukansu ne suka zo. Dan haka babu ɓata lokaci ta shiga hidima da su. Lokacin da suka je, sun samu Abeey zaune a kan tabarma da pillow a bayansa. Ba ya jin daɗi, se dai kamar ko yaushe nunawa yake tamkar babu abin da yake damunsa. Se dai da yake Gwani ya san hali hakan ne ya sanya shi ƙarasawa kusa da shi yace

"Abeey ko dai ba ka jin daɗi ne?" Lalubo murmushi ya yi ya wanzar a kan fuskarsa kafin yace

"Kar ka damu.. Babu abin da ke damuna. Ciwo ne dai irin na yau da kullum da ka riga ka san shi."

"Shi kenan kuma?" Gwani ya sake tambaya. Se ya jinjina kai yace

"Ehh In Sha Allah.." Ya faɗa cike da tabbatarwa. Dan da gaske a lokacin ba ya jin komai, se dai da ciwo sosai ya kwana. Da safen nan ne dai kuma se ya ɗan ji sauƙi. Bayan wani lokaci Bad Man da Gwani suka yi sallama da Mommah da Abeey saboda zuwa da za su yi aike da Daddyn ya musu.

"Toh ku gaida gida Allah Ya tsare.." Ummeey ta faɗa tana murmushi.

"Ameen Ummeey.." In ji Gwani. Se ya maida su amsa kan Abeey yace

"Abeey.." Kallansa Abeey ya yi kafin yace shi ma da murmushin a kan fuskarsa

"Allah Ya tsare hanya yarana."

"Ameen Allah Ya ƙara lafiya. Yau babu karatu ne Abeey?" Gwani ya yi maganar duka a lokaci ɗaya. Girgiza kai Abeey ya yi kafin yace

"A'ah akwai.. Amma Abbati ne ze gabatar yau ɗin.. In Sha Allah se zuwa gobe zan fita." Addu'a Gwanin ya sake yi, kafin ya bi bayan Bad Man suka fice daga gidan. Ko a gidan Ummeey su Didi ba su matsa daga kusa da Mommah ba har se bayan da su Bad Man suka bar gidan sannan ta barsu suka shiga ɗaki. Se a lokacin sannan Daddy ya gyara zama, bayan ya sauke ajiyar zuciya yace

"Wato da ma mun zo ne mu sake godiya a kan abin da aka mana.. Muna sake godiya, Allah kuma ya saka da alkhairinsa. Se kuma magana a kan ragowar abubuwanku da ke hannuna.."

"Godiyar ta isa haka Yallaɓai.." Abeey ya faɗa yana murmushi. Hannu Daddy ya saka ya ciro keys daga aljihunsa ya ajje su a gaban Abeeyn sannan yace

"Waɗannan mukullan na gidaje ne guda biyu.. se kuma motoci guda biyu.. Waɗannan kuma kuɗi ne a ciki, se dai abin da nake so ka sani ba ni ne na baku ba. Ba kuma ita mahaifiyar yaran nan ce ta baku ba.. har yanzun dai daga cikin kyaututtukan da abokaina suka muku ne. Ina fatan ba za ku ce a'ah ba." Girgiza kai Abeey ya yi kafin ya soma faɗin

"Haba.. Wannan se kace kuna neman biyanmu abin da muka muku ne? Mun yi haka ne don Allah ba don komai ba.. Ba kuma dan a biya mu ba.. Saboda haka don Allah ka riƙe waɗannan kayan sun yi yawa. Waɗanda muka karɓa ma Allah Ya amfana." Girgiza kai Daddy ya shiga yi.

"Wato Malam har abada ba za mu taɓa iya biyanku abin da kuka mana ba.. Su kansu ba sun yi hakan ne dan su biyaku ba, se dan kawai su nuna farin cikin abin da kuka mana. Se kuma abu na gaba.. Mun duba na duba, Mun ga me ya kamata mu yi muku da ze sa ku shiga makamancin farin cikin da muka shiga dalilin wannan abun alkhairin da kuka mana. Shi ne muka yanke shawarar biya muku aikin Hajji ku je ku sauke farali.. Amma don Allah kar ku ce a'ah. Bayan ita ma ina so don Allah ku faɗa min idan da akwai abin da kuke so ko mene ne shi ku faɗa min, ni kuma In Sha Allah zan samar muku shi idan dai har be fi ƙarfina ba." Kallan Daddy Abeey kawai yake yi cike da mamakin abubuwan da ke ta fitowa daga cikin bakinsa. Makkah? Su yau su ne ake faɗin za a basu kujerar Makkah? Shin da gaske ne ko kuwa dai mafarki ne? Lallai Allah me yadda ya so. Lallai Daddy mutum ne har da rabin mutum. Wato shi ne kuma bayan duk wannan abubuwan yake tambaya idan akwai abin da suke so? Su kuwa me za su buƙata bayan irin wannan tarin alkhairan da Alhaji Matawalle da makusantansa suka masa? Kuka kawai Ummeey ta fashe da shi, dan ta rasa me ma za tace ita kam. Wannan abun alkhairin har ya yi yawan da ta kaasa furta komai.

"Haba.. ki dena kukan nan haka mana.." Mommah ta faɗa tana kallan Ummeey. Girgiza kai kawai Ummeeey ta yi ba tare da tace komai ba. Dan har i zuwa lokacin ta rasa me za tace. Godiya sosai Abeey da Ummeey suka musu cikin matuƙar farin ciki. Har lokacin ganin abun suke kamar mafarki. Kafin su tafi Daddy ya shigarwa da Abeey maganar da yake da ita.

"Wato da so samu ne.. da duk gidajen se ku saka haya a ciki.. Zan saka a gina muku wani gidan a kusa da nawa se ku dawo nan ku zauna." Daddy ya faɗa cike da fatan su amince da hakan. Dan kamar hakan se ya fi musu. Ko babu komai sun zama kusa da juna kenan. Musamman da yanzun ya fara tunanin sakawa a ginawa Gwani da Bad Man gida su ma duk a kusa da nasa, dan ba ya so iyalansa su rabu.

"In Sha Allah se a yi hakan." Abeey ya faɗa. Murmushi Daddy ya yi yace

"A'ah fa Malam shawara na bayar.. Kuma yanzu haka tafiya za mu yi idan ka yi shawara se ka sanar da ni. Idan kuma akwai unguwar da kake son zama ne a ciki duk se ka sanar da ni."

"In Sha Allah." Abeey ya faɗa jikinsa a sanyaye. Har lokacin yana jinjina irin alkhairansu Daddyn a gare su.



.. A ɓangaren Bad Man jira kawai yake yi su Mommahn su dawo. Se dai sam se be san lokacin da suka dawo ɗin ba. Dan haka kai tsaye sashen Mommahn ya wuce, cikin zuciyarsa yana sake mamakin wannan lamari. Abu se kace wanda aka jefa, gaba ɗaya ya bi ya chanja tamkar ba shi ba. A kan mace ne yake ta wannan abun se ka ce almajiri. Se dai zuwansa sashen Mommahn ma se ya yi danasanin zuwa. Dan kuwa yana shiga ya yi daidai da fitowar Mommah daga ɗakinta kenan. Ta kalle shi dan ba ta tsammaci shigowarsa ba.

"A'ah.. Areef.." Ta faɗa tana kallansa.

"Na'am Mommah.. Ashe kun dawo?" Ya ƙare yana ɗan babbasarwa. Kallansa ta yi sosai yanda ta ga yana ta wani ɗaɗɗauke kai ya sa ta fahimce shi. Ta girgiza kai tana murmushi a kan laɓɓanta ta furta

"Za ka gane kurenka ne." A fili kuma se tace

"Ehh.. mun dawo.. Ƙaraso ka zauna mana.. Ko dai akwai wani abun ne?" Ta tambaya lokacin da ta ƙaraso cikin ɗakin. Girgiza kai ya yi kafin yace

"A'ah fa.. babu wani abu.. Kawai na zo na duba ne ko kun dawo." Ya ƙare yana maida hannayensa cikin aljihun wandonsa yana sake basarwa. Murmushi Mommah ta yi, duk wani take-taken Bad Man ɗin ya nuna abin da ke ransa. Wato se bayan ya gama wahalar da su sannan ze dawo ya ɗauka ze sameta ne cikin sauƙi. Kamar yanda ya yi wasa da su su ma se sun yi wasa da zuciyarsa. Ganin yanayin Mommahn kamar yau ɗin za ta ba shi goyon baya ya sanya shi faɗin

"Mommah don Allah.." Se da ta sauke numfashi kafin ta katse shi da faɗin

"Kaa ga in dai dan yarinyar nan ne kar na sake ganin ƙafarka cikin sashen nan. Idan wajena ka zo ka zauna a first palour zan fito mu gaisa. Ba za ka kuma shiga ɗakina ba har se na mayar musu da 'ya." Be fahimci abin da zancenta na ƙarshe ke nufi ba, hakane ne ya sa be ba shi muhimmanci ba. Se hankalinsa ya karkata a kan maganarta ta farko. Kenan ba ze din ga ganinta ba? Yana shirin cewa wani abun se nemar Mommah ya yi a wajen ya rasa, dan idan ta cigaba da kasancewa wajen tausayin ɗan nata ka iya sakawa ta janye maganarta.


... Washegari haka sirr ya wuni be sanyata cikin idanunsa ba. A hankali ya saukar da ƙafarsa ƙasa daga kan gadon da yake. Ya lumshe idanunsa lokaci ɗaya yana cusa hannayensa duka biyun cikin sumar kansa. Gaba ɗaya al'amarinsa neman taɓarɓarewa yake yi. Mace na neman saka masa hauka. Ji yake kamar ya fita ko ma ina ne ya nemo wani abun ya zo ya bankawa kansa ko ze ji sauƙi. Se dai wani ɓangaren na zuciyarsa ya ƙi yin na'am da hakan. Daga zarar ya raya hakan se Mommah ta faɗo masa. Zazzafar iska ya fitar daga bakinsa yana miƙewa. Ya ɗauki rigarsa da ke gefensa ya zura, ya saka haɗaɗɗen tsadadden takalminsa ya fice daga ɗakin. Abin da be taɓa tsammata ba, se ga shi a bakin sashen Mommahn ya hangeta. Daga nesa ya sake buɗe idanunsa yana fatan ba idanunsa ke gizo ba, ko kuma er uwatta ce ya gani. Se da ya ɗan sake matsawa ɗin kuwa sannan ya tabbatar da tabbas ita ɗin ce. Ya lumshe idanunsa ya buɗe, kana da sauri ya ƙarasa inda take. Ya sha gabanta lokacin da take ƙoƙarin shigewa sashen. Dakatawa ta yi tana jin jikinta ya yi sanyi. Ita kam wannan mutumin ta shiga uku da shi. Ba ta iya ɗaga ido ta kalle shi ba, se yin shiru kawai da ta yi tana jira ta ji yau kuma da me ya zo. Da so samu ne su yi wata maganar ba wannan ba, se dai ba ya so Mommah ta gan shi ballantana tace ba ya jin magana. Hakan ne ya sanya shi tamke fuskarsa kamar yanda ya saba a da idan ze mata magana. Dan gani yake hakan ne kaɗai ze sa ta ji maganar da ze mata.

"Ki kawo min Coffee.. Kar ki kawo min maganar Mommah dan ba karɓa zan yi ba. Ina nan ina jiranki a ɗakina, kar kuma ki sake ki sanarwa da Mommah." Ba ta san me ya gani ba ita dai ta ga ya yi saurin bi ta baya ya bar wajen. Se da ta ji maganar Mommah na faɗin

"Daughter.. lafiya?" Sannan ta yi saurin girgiza kai tana faɗin

"A'ah Mommah babu komai." Ta ƙare tana ƙaƙalo murmushi a kan fuskarta. Daga haka suka wuce cikin ɗakin tare da Mommahn.



... Ya fi minti 30 yana zagaye cikin ɗakin, yana jiran shigowar Didi. Dan ya saka a ransa ko me za ta yi yau cikin ɗakin za ta kwana ko ya samu ya fanshe kallanta da be samu ya yi ba jiya da yau. A karo na barkatai ya sake kallan agogo ya duba lokaci, har lokacin babu ita babu dalilinta. Har bayan Sallahr maghrib shiru babu Didi babu alamunta. Kenan me ta cigaba da zama ta yi a sashen Mommah? Ko dai Mommah ta san ya sakata aikin nan ne? Ko kuma ita ta sanar da Mommahn? Ya kaasa haƙuri har ga Allah zuciyarsa azalzalzalarsa take yi, hakan ne ya sa ya miƙe kawai ya fice daga ɗakin zuwa sashen Mommah. A madaidaicin palourn da za ka fara tararwa kafin ka kai ga ainahin palourn Mommah ya sameta tana shirin shiga palournta. Se ya dakata yana ji kamar ya koma, se dai kawai ya basar yace

"Barka da wannan lokaci Mommah.."

"Barka dai Son.." Mommah ta amsa da hakan.

"Amma kamar na ce maka ka dakata da shigowa ɗakin nan idan ba na nan koh?" Ɗaga idanunsa ya yi ya kalli Mommahn a narke ko da hakan ze sa ta ji tausayinsa. Yace a sanyaye

"Ki yi haƙuri Mommah.. ba tare da saninki ba na sakata kai

Please Login or Register in order to submit comment