Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi ya sa ma na zo na sanar da kai." Sauke numfashi Daddy ya yi kafin yace

"Ku barta ta shigo." Cikin girmamawa ya amsa da

"An gama Sir." Daga haka ya juya. Ƙarasawa Daddy ya yi ya jingina da motar da za su shiga. Da ma tuni Mommah ta ƙarasa jikin motar.

"Rankiyadaɗe bari na ganta se mu wuce." Daddy ya faɗa yana kallan Mommah.

"Babu damuwa." Ta ƙare tana murmushi. Bayan wajen minti 3 se ga mutumin nan na ɗazu ya ƙaraso, bayansa wata mata ce me matsakaicin tsawo. Baƙa ce wuluk, irin baƙin nan da wahala ke kawo shi dan har wani dabbara-dabbara fuskarta ta yi. Kayan jikinta kansu sun yi wani iri, alamar sun daɗe a jikinta. Ban sani ba ko dalili kenan da ya sa kallo ɗaya suka mata na mahaukaciya. A ido ma tabbas ta yi kama da masu taɓin hankali. Se dai yanayin yadda take tafiya ya sani tantamar an ya kuwa mahaukaciyar ce? Daga Mommah har Daddy kallanta suke yi. Ita dai Mommah sanin da ta yi ba ta santa ba ya sanyata ɗauke kai daga kan matar ta maida kan Daddy dan ganin yanayinsa. Tana ƙarasowa matar ta zube a kan ƙafafunta tana fashewa da wani irin kuka irin me fitowar nan daga can ƙasan zuciya. Zare sunglasses ɗin da ke idanunsa Daddy ya yi yana kallan halittar da ke gabansa cike da tsananin mamaki. Mutumin na ida juyawa matar ta soma faɗin

"Don girman Allah Alhaji ku yafe min kai da Sa'adah, ku yafe min don Allah ko na samu na ga daidai a al'amurana. Ku taimaka min don Allah.." Cikin lokaci ƙanƙani bugun zuciyar Mommah ya ƙaru, wato ko daga bacci ta tashi ta ji muryar nan ai ta shaida wace ce, ballantana kuma ba hakan ba ne. Hajiya Salman ce ta dawo haka? Hajiya Salman ce ta sauya ta zama kamar almajira? Ina gayun nata? Ina en uwanta? Tambayoyin da Mommah ke ta yi wa kanta kenan tana cigaba da kallanta. Shi kansa Daddy ya yi matuƙar shiga mamaki ganin wannan ɗin Mom ce. Runtse idanunta Mommah ta yi lokacin da ta ji Mom ɗin ta cigaba da faɗin

"Na san na zalunci rayuwarku.. Musamman ma ke Sa'adah, na cuce ki, na raba ki da 'ya'yan da kika haifa saboda son zuciyata. Se dai yanzu da nake a gabanku a duƙe wallahi da gaske nake na tuba, na yi nadama. Kowa ya juya min baya, ban sani ba ashe dan ina tare da kai ne ake nuna ana ƙaunata, na ɗauka idan na je wajensu bayan sakina da aka yi za su karɓe ni, se na ga ashe abun ba haka ba ne. Makiyya ce kaɗai take tare da ni har ila yau. Se dai mijinta ya ƙi yarda in zauna masa a gida. Ban san yanda zan yi ba, na rasa mafita, hakan ne ya sa na fara fita nemarwa kaina abin da zan ci. Kalli yadda rayuwa ta juya min baya, waɗanda suka sanni a baya ma yanzu ba sa gane ni ɗin ce. Rayuwa ta yi min juyin waina, ji na nake kamar ba a raye ba. Don Allah ku ji tausayin halin da nake ciki ku yafe min." Ta ƙarasa maganar tana sake fashewa da kuka. A hankali Mommah ta saka hannu ta buɗe ƙofar motar da suke kusa da ita, tana shirin shiga ta ji Daddy ya riƙo hannunta. Dalili kenan da ya sanya ta dakatawa se dai har lokacin ba ta ɗago kanta ba, dan kuwa idanunta sun tara ƙwalla sosai, tuna abubuwan da suka faru kawai take yi. Tuna irin tsantsar zaluncin da Mom ɗin ta mata take yi. Se take ji kamar tsayawa ma ta cigaba da saurarar neman yafiyar da take ɓata lokaci ne. Kallanta Daddy ya yi ya girgiza mata kai dan son bata ƙwarin gwuiwa. Ta girgiza kai tana ƙoƙarin maida ƙwallar idanun nata. Maida dubansa kan Mom Daddy ya yi, kamar ba ze ce komai ba se kuma yace

"Ki tashi ki je, da ma kowa ya yi na gari ai kansa. Abin da kika aikata sakayya ce ke bibiyarki. Ki kuma gode wa Allah da ya haska miki zuwa neman yafiya wajen wadda kika aikatawa laifin. Don haka ki tashi ki je, sannan kuma kamar yadda na faɗa miki ba na buƙatar sake ganinki cikin gidan nan." Daga haka Daddy ya soma ƙoƙarin shiga motar.

"Don Allah Alhaji ku yafe min. Ka saka baki Sa'adah ta yafe min, kar ku bar ni cikin taraddadi domin Allah.." Mom ta faɗa tana ji kamar ta saka ihu ko za ta ji sauƙin abin da take ji.

"Ba ki ce komai ba..?" Daddy ya faɗa yana kallan Mommah da ta zauna cikin motar. Girgiza kai Mommah ta yi tace a sanyaye

"Ba ni da abin cewa.."

"Kin yafe mata?" Daddy ya tambaya yana kallanta sosai. Da sauri ta girgiza kai kafin tace

"Ba na ji zan iya yafe mata Yallaɓai.. Ni kaɗai na san abin da nake ji a cikin zuciyata. Don Allah mu bar maganar." Sauke numfashi Daddy ya yi, tabbas ya san abin da take ji, ya kuma san tana da gaskiya. Se dai shi kansa duk fushin da ya ɗauka da Mom ɗin yau da ya ganta se da ya ji tausayinta. Dan haka cikin rarrashi yace yana kallan Mommahn.

"Tabbas abun da ciwo, a cuce ka kuma a zo a baka haƙuri.. Se dai ki sani ko Allah ma muna masa laifi kuma ya yafe mana. Ko da ba ki duba komai ba ki duba hakan, ki kuma duba yadda ta yi nadama.. Ba ina nufin ku cigaba da alaƙa ko wani abu makamancin haka ba, a'ah.. Kawai dai ina so ne na ji kalmar yafiyar daga bakinki. Ki yi haƙuri ki yafe mata ɗin." Runtse idanunta Mommah ta yi, kusan minti 1 da gama maganar Daddy ba tace komai ba. Se zuwa can tace a sanyaye.

"Allah Ya yafe mana gaba ɗaya."

"Ameen.. Allah Ya miki albarka, Ya ƙara raya zuri'a, Ya albarkaci yaran nan." Ba ta iya amsawa a fili ba se komawa da ta yi ta jingina da kujera. Daddy ya fita daga cikin motar. Har lokacin Mom na nan a gantale, har kuma lokacin ta kasa cire rai a kan yafiyar Mom ɗin.

"Kin yi sa'a Allah Ya saka mata tausayi a cikin zuciyarta, bayan abubuwan da kika aikata mata, se ga shi ta yafe miki.." Da sauri ta ɗaga kai ta kalli Daddyn, ba ta taɓa tunanin haka ne ze fito daga bakinsa ba. Da gaske Mommahn ta yafe mata? Da gaske ta yafe duk laifin da ta mata?. Maganar Daddy ce ta katse mata tunani lokacin da ya cigaba da faɗin

"Se dai fa ki sani, yafe mikin da ta yi ba shi ne ke nufin cigaba da bibiyarmu ba. Tun da kin samu abin da kike so, ina so ki yi nesa da mu, ki je ki cigaba da rayuwarki." Ita zancen yafiya ma kaɗai da ya mata ai ya ishe ta, ko bayan nan ya faɗi wani abun ai ba za ta damu ba tun da dai Mommahn ta yafe mata.

"Na gode sosai, na gode, na gode, Allah Ya saka da alkhairi. Na gode. Don Allah ka yi wa Hajiya godiya, Allah Ya saka mata da alkhairi, na gode." Shi ne abin da Mom ta yi ta faɗa kamar za ta aro baki.

"Ki gode wa Allah.." Daddy ya faɗa. Daga haka ya juya ya shige cikin motar. A sukwane ta miƙe haka tana ji tana gani duk daular nan da a da take ciki, ta fice ta bar gidan. Har juyawa take ta kalli gidan da zarar ta yi nisa. Da ta san rayuwa za ta juya mata baya haka, da tun farko ta zauna a matsayin wadda ba ta da ɗa, tun da ga Mommah nan duk da a da da ake tunanin ba ta da komai hakan be rage ko kaɗan daga soyayyar da Daddy yake mata ba. Ko da kuwa Daddy ya faɗi ya mutu za ta samu kuɗi. Se dai da yake a lokacin sheɗan ke ta ingiza ta, ba ta taɓa kawo hakan ba. Ita burinta kawai duk dukiyar ta zamo tasu. Wannan shi ne kaɗai burinta. Ashe ba ta san ranar danasani na nan zuwa ba. Se ga ta ta zo a kurkusa babu daɗewa da tonuwar asirinta. Ba ta san lokacin da kuka ya ƙwace mata ba. Ta saka gefen hijab ɗinta tana goge hawayen. A haka ta fice daga tanƙamemen layin gidan na Alhaji Matawalle.



... A karo na barkatai ya sake kallan Didi da ke zaune a kan kujera, ta ɗora kanta a kan kujerar ta yi shiru kamar me tunani. Se da ya ƙarasa abin da yake sannan ya miƙe. A nutse ya ƙarasa ya zauna dab da ita yana kallanta. Kafin ya saka hannunsa ya riƙo hannunta. A hankali ya furta

"Wai ɓacin ran na mene ne? Me ke damun Babyna?" Ya ƙare yana zuba mata idanunsa. Lumshe idanunta ta yi fuskarta a narke kamar wadda ke shirin yin kuka. Ta girgiza kai jiki a sanyaye.

"Ni ma ban sani ba." Ta faɗa da iya gaskiyarta, dan ba ta san ainahin abin da ke damunta ba. Ita dai kawai ta tashi da ɓacin rai.

"Ko dai Babyna ne?" Ya yi maganar yana ɗora hannunsa a kan cikinta da ya ƙara girma sosai. Kallan hannun nasa ta yi na tsawon sakanni kamar me nazari, se kuma ta girgiza kai tana kai hannunta ta ɗora a kan nasa hannun lokaci ɗaya tana lumshe idanunta. Murmushi ya yi kafin yace

"Yawwah ko ke fa.." Daidai lokacin ta buɗe idanunta

"Wajen Lulu zan je.." Ta faɗa bayan ta ɗora idanunta a kan fuskarsa. Cike da mamaki yace

"Lulu kuma? Me ya faru?" Girgiza kai ta yi tana ƙoƙarin miƙewa tace

"Ni dai wajenta zan je.. Ina so in ganta." Da sauri ya miƙe, ya riƙota sosai yana sake tambayarta lafiya?

"Ba komai, so nake na ganta." Amsar da take ta ba shi kenan. Shi dai abun mamaki yake ba shi, se ka ce wadda za ta fara ganin Afaaf ɗin yau? Anya kuwa? Ko dai akwai wani abun da ya faru ne be sani ba? Ganin da ya yi ta ƙi ba shi haɗin kai ne ya sanya shi janta cikin jikinsa ya rungume. Ya ɗora hannunsa duka biyu a bayanta, cikin rarrashi yake faɗin

"Ki nutsu! Ki nutsu Uhmm?" Da sauri sauri numfashinta ke fita tamkar wadda ta yi tsere. Zuwa can kuma se ya koma fita daidai. Ya sauke numfashi daidai lokacin da ta ɗaga kai ta kalle shi.

"Wajen Lulu zan je." Ta sake faɗa tana kallansa.

"Iko sai Allah." Ya faɗa yana ƙura mata idanunsa.

"Shi kenan mu je na raka ki." Wata ajiyar zuciya ta sauke tana yin gaba. Ya bi ta da kallo. A kan laɓɓansa ya furta

"Rigima dai kawai." kafin ya girgiza kai yana murmushi lokaci ɗaya yana bin bayanta.


A ɗaya ɓangaren kuwa zaune take a kan kujerar, se dai kusan fiye da awa ɗaya kenan bayan wasu mintuna ta kan kama ƙugu ta riƙe tana runtse idanunta. Kwata-kwata ta kasa zama a kan kujerar. Ita kaɗai ta san azabar da take ji. Wani irin ciwo take ji kamar za ta mutu. Ciwon da yake zuwa bayan wasu mintuna. Se ta ɗauka ta dena ji se ta ji wanda ya fi na da. Daidai lokacin Gwani ya shigo cikin ɗakin. Ya kalle ta sosai yana nazarinta. Ƙarasawa ya yi ya zauna a kusa da ita.

"Me ya faru?" Ya tambaye ta a karo na babu adadi. Saboda tun jiya yake ganinta wani iri. Da zarar ya tambaye ta se tace babu komai. Girgiza kai ta yi kafin tace komai irin ciwon da take ji ya sake dawowa. Hannunsa da ke gefenta ta dafe da ƙarfi tana runtse idanunta. Girgiza kai take tana sauke wahalallen numfashi cikin wata irin azaba da take ji. Ƙanƙame hannun nata ya yi cike da tsoro yake kallanta. Bayan wajen minti 1 ta koma sauke ajiyar zuciya. Idanunta sun yi muzu-muzu, duk ta yi wani yaɓe-yaɓe.

"Ko dai haihuwar ce?" Ya tambaya yana kallanta. Girgiza kai ta yi ta kalle shi da lumsassun idanunta tace

"Ina ganin juyi ne kawai.." Ta faɗa da muryarta da ta shige ciki saboda wahala. Shi dai haka nan kawai ya ji be yi na'am da hakan ba, ya dai yi shiru yana cigaba da nazarinta. Kanta ya ja ya kwantar a kan kafaɗarsa. Duk da jinta take kamar ba a hayyacinta ba hakan be hana ta kwantawa ɗin ba ta yi shiru a ranta tana fatan Allah Ya sa kar ciwon ya dawo. Se dai addu'ar tata ba ta karɓu ba, dan kuwa ba a ɗauki lokaci me tsayi ba ciwon da ya fi na ɗazu ya taso mata. Yanzu kam ruƙunƙume shi ta yi kamar za ta ɓalla ƙirjinsa ta shige. Cikin galabaita muryarta na rawa take faɗin

"Wayyo Allah na.. zan mutu.. Wayyo Allah na.." Abin da take iya faɗa kawai kenan, cikin lokaci ƙanƙani hankalin Gwani ya tashi. Ai babu shiri ya janyo wayarsa ya danna kiran Mommah. Mommah da ke tare da Yaya Amina a lokacin ta ɗauki wayar.

"Mommah Afaaf ba lafiya." Shi ne abin da ya faɗa ko sallama be iya yi ba.

"Ya salaam! Kuna cikin gidan ne?" Mommah ta faɗa.

"Ehh.." Ba ta ce komai ba ta katse wayar. Ta kalli Yaya Amina tace

"Tashi maza mu je.. Afaaf ba lafiya, ina kuma tunanin haihuwar ce.."

"Toh subhanallahi! Mu je.." Yaya Amina ta miƙe ta soma yafa mayafinta da ke ajje. Tare suka fita da Mommah. Kai tsaye sashensu Gwanin suka wuce. Lulun na kwance kane-kane a jikin Gwanin, dan zuwa lokacin har ta soma fita daga hayyacinta. Ciwon ke dawo mata a kai a kai babu tsayawa. Yaya Amina ce ta ƙarasa ta kamo Lulun da taimakon Gwani. Suka fito palour riƙe da ita. Se a lokacin sannan Mommah ta ƙarasa ta karɓi Gwani. Se faman jerawa Lulun da duk wata alamar wahala ta gama bayyana a tattare da ita sannu suke. Lulun da a yanzu ko ganewa ba ta yi. Daidai lokacin da suka fito daga sashen Areef da Didi suka ƙaraso bakin sashen. Gaba ɗaya idanunsu suka ɗaga suka ɗora a kansu Mommahn. A kan er uwarta idanunta suka soma sauka. Ƙirjinta ya wani irin bugawa, a take jikinta ya soma ɓari, zazzaɓin da ya so rufe ta tun ɗazu yanzu ya samu damar soma rufeta. Cikin ƙanƙanin lokaci cikinta ya yi wani daƙiƙin juyawa. Ba ta damu da hakan ba, halin da ta ga er uwarta ciki ya sanya ta mantawa ma da abin da ke cikin nata. Ba ta san lokacin da ta fincike hannunta daga cikin na Areef ba. Cikin azama kamar babu komai a jikinta ta saka kai zuwa wajen Lulun da take hangowa riƙe a hannunsu Mommah da alama ba ta cikin hayyacinta. Se dai cikin rashin sa'a ba ta kula da abin da ke gabanta ba, ta yi tuntuɓe, kafin kace me ne wannan ta faɗi a wajen. Tsautsayi ya sa ta faɗi a kan cikinta. Wani azababben zafi da tun da Ammi ta haifeta ba ta taɓa jin irinsa ba ya ziyarceta. Dalili kenan da ya sanya ta kai hannu kan cikin nata tana sakin wata ƙara cikin matsanancin azaba.

"Baby..!!!" Ya faɗa cikin ɗaga murya yana kallanta lokacin da yake durƙushe a wajen. Mommah da Yaya Amina cikin matuƙar tashin hankali suke kallan abin da ke faruwa. Kusan a lokaci guda suke sauke salati. Ga Lulu a hannunsu wadda suke dab da shigar da ita cikin mota, ga shi babu damar su zo su taimakawa Didi. Da sauri Mommah tace

"Maza ɗauke ta ka saka a mota." Inaa, shi ba ji yake ba, gaba ɗaya a hankalinsa na kan Didi da ke hannunsa, wadda take a kwance kamar babu rai a tattare da ita.

"Areef!!" Gwani ya faɗa yana dafa kafaɗar Areef ɗin. Se a lokacin sannan ya iya ɗaga jajayen idanunsa ya kalli Gwani.

"Ɗauke ta ka saka a mota mu wuce asibiti." Kamar wanda ya farka daga bacci, se ya maida dubansa kan Didi. Cikin azama ya miƙe ya saɓe ta se cikin mota. Ko driving kasawa ya yi, se sakawa ya yi ɗaya daga cikin drivers ɗin gidan ya tuƙa su. Yana baya hannunsa ɗauke da Didi da zuwa lokacin ta farfaɗo se dai kwata kwata ya kasa fahimtar abin da ke damunta. Cikinta kawai ta riƙe tana kuka gami da sallallami. Shi dai ya san cikinta be isa haihuwa ba ballantana yace ko haihuwa ce. A'ah toh me ya samu cikin? Kar dai wani abun ne ya same shi? Ya tambayi kansa har lokacin idanunsa na kan Didi

A tare suka isa asibitin. Babu ɓata lokaci aka karɓe su. I zuwa lokacin gaba ɗaya sun yi laushi sun yi tuɓus. Duk wahala ta gama jigata su. A harabar haɗɗɗen asibitin duk suke zaune, waɗanda ke a tsaye suna tsaye. Dan zuwa lokacin har Ummeey ta iso. Abun da ya bawa kowa mamaki shi ne lokacin da aka sanar musu da cewa ita ma Didi haihuwar ce ta taso mata gadan-gadan.

"Haihuwa kuma?" Areef ya tambayi kansa bayan jin abin da aka faɗa ɗin.

"Ka kwantar da hankalinka, hakan ba abun damuwa ba ne, da ma hakan kan iya faruwa.. so ba sabon abu ba ne." Yaya Amina ta faɗa wa Areef bayan ta dafa kafaɗarsa. Shi dai jinta kawai ya yi. Hakan ne ya sa be ce komai ba se jinjina kai da ya yi. Cikin ƙanƙanin lokaci kowa ya duƙufa wajen addu'a tare da fatan Allah Ya sauke su lafiya. Bayan shuɗewar awanni masu yawa ana fafatawa, ana ta gwagwarmaya, cikin ikon Allah, se ya ba su sa'a Lulu ce ta soma haifo santalelen ɗa namiji ƙato da shi. Ko minti 2 ba a yi ba Didi ma ta dire nata ɗa namijin, se dai shi be kai girman na Lulu ba. Kowannensu kawai bajewa ta yi a kan gadon jiki a matuƙar mace. Tabbas babu ƙarya sun sha wahala sosai, sun kuma jigata gaba ɗayansu.

"Alhamdulillah!" Mommah ta faɗa lokacin da ta jiyo kukan jinjiri daga cikin ɗakin. Dukkansu suka juyo suna kallanta. Ta jinjina kai lokacin da ƙwallar farin ciki ta taru a cikin idanunta.

"Tabbas wata ta haihu a cikinsu.." Mommah ta faɗa murmushin ya ƙi barin fuskarta. Se dai kafin ma ta sake cewa komai ko wani yace komai kukan wani jaririn da be kai wancan ba ya sake karaɗe wajen. A karo na biyu ta sake faɗin

"Alhamdulillah! Alhamdulillah.." Ta faɗa idanunta a lumshe. Dukansu kuma se hankalinsu ya koma kan ɗakin. Babu daɗewa midwives guda biyu suka fito daga cikin ɗakin kowaccensu ɗauke da Baby ɗaya lulluɓe cikin fararen tausasan towel, wanda suke cikin kayan da Ummeey ta taho da su, dan tashin hankali ya hana su ɗaukar komai na haihuwar. Gaba ɗayansu suka miƙe, har rige-rigen karɓar yaran ake yi. Areef ne ya yi nasarar saka hannu ya karɓesu su duka biyun, hannunsa har wani rawa yake yi. Cike da zumuɗin ganinsu ya ɗan yaye towel ɗin dan ya ga fuskarsu. Bacci ƙaramin ke yi hankalinsa kwance, yana sauke numfashi a hankali. Ɗayan kuma wanda shi ne babban idanunsa biyu yana ɗan wawurar bakinsa alamar abinci yake nema.

"Kin gan shi Maama, daga fitowarsa har ya san abinci.. Ko da me yake ci?" Ya ƙare tsantsar farin cikin da yake ciki na bayyana a cikin muryarsa. Duka Mommah ta kai masa tana faɗin

"Ja'iri." A hankali Gwani ya miƙa hannunsa dan karɓarsu, dan shi kansa ya ƙagu ya ga yaran. Se da ya sake zame towel ɗin ya sumbaci goshin kowannensu kafin ya miƙa masa.

"Alhamdulillah!" Shi ne abin da Gwani ya sake faɗa yana kallansu, tsantsar farin ciki na bayyana a kan fuskarsa. Be ƙara minti 1 ba ya miƙawa Mommah yaran, dan su ma su samu damar ganinsu. Ta karɓa cike da farin ciki da kuma zumuɗin ganinsu a hannunta. Haka aka yi ta sanyawa yaran albarka, har zuwa lokacin da aka maida su su ma aka kwantar, musamman ma ɗan Didi da jikinsa babu ƙwari Sosai. Su ma masu haihuwar aka kai su ɗakin hutu.

"Wannan kam kamarsa ɗaya da Affan lokacin yana ƙarami." Ummeey da ɗan Lulu ke hannunta ta faɗa tana kallansa. Kallanta Mommah ta yi, abin da take ƙoƙarin ganin ta manta ya dawo mata. Ta girgiza kai murmushin nan da aka cewa ya fi kuka ciwo na wanzuwa a kan fuskarta. Ita da ta haifa kwata-kwata ba ta san ya yake ba a lokacin yarinta ballantana har ta kai ga ɗorarwa. Ba da ban akwai mantuwa ba, zuciyar mutum kuma ta musulunci ce ba, da babu abin da ze sa ta yafewa Mom.

Cikin ƙanƙanin lokaci haihuwar en biyun Mommah ya baza cikin dangi, har ma da abokan arziƙi.


.. "Abbansu ba zan iya haƙura ba.. Don Allah ka bar ni na je." Ammi da tun da ta ji labarin haihuwar en biyun nata ta kasa sukuni. Da ma tun da aka ce mata suna asibiti ta so zuwa, Abba ne yace ta bari tun da su Mommah suna wajen. Yanzu kam duk se ta kasa haƙuri, gaba ɗaya burinta ya tafi a kan ta je ta ga 'ya'yanta, ta kuma ga jikokinta. Murmushi Abba ya yi dan shi kansa yana so ya ga 'ya'yansa da kuma jikokinsa.

"Shi kenan je ki shirya ki fito mu je."

"Ina godiya Abbansu." Ammi ta faɗa tana murmushi. Lokacin da suka isa asibitin Lulu da Didi na ɗakin hutu. Bayan da Abba ya gama ganin jariran Ammi ce ta karɓesu ta riƙe a hannunta. Se take ji tamkar ranar da ta haifi su Lulu ne. Ƙaunar yaran na ratsa kowacce gaɓa ta jikinta. Abun kamar a mafarki wai yau ita ce ke riƙe da 'ya'yan Didi da Lulu. Lallai da ma aka ce idan da rai da rabo.

"Allah Ya albarkaci rayuwarku." Ta faɗa murmushi na wanzuwa a kan fuskarta. A hankali ta juya ta kalli en biyun nata da ke ta baccin wahala, duk sun yi zuru-zuru. Ƙwallar da ta ji a cikin idanunta ne ya sanyata saka hannu ɗaya ta ɗauke ta. Tausayinsu ya kamata, tabbas yaranta sun yi ƙoƙari, yau ɗin sun ƙara sanin tabbas sun girma.

"Allah Ya ƙara muku lafiya." Ta faɗa a hankali.

Cikin dare aka sallame su, bayan an ba su shawarar yadda za su kula da ɗan gidan Didi da be cika watanninsa ba. Haka suka ɗunguma zuwa gida cikin matuƙar farin ciki. Kai tsaye gidan Ammi aka wuce da masu jegon har ma da mazajensu da yau ɗin suke cikin farin ciki mara misaltuwa. Da ma tuni Ammi ta gama gyara inda za su zauna. Hakan ne ya sa kai tsaye can ɗin suka nufa.



.. "Ban taɓa kawo miki haihuwa a kusa ba Dear.. Se ga shi wai yau ɗin kin haihu.. Na kuma zama uba! Ikon Allah!" Areef ya faɗa dan tabbas abun ya ba shi mamaki ainun.

"Ni kaina ban kawo hakan ba." Didi ta faɗa tana gyara zamanta. Da sauri ya miƙe yana faɗin

"Zaman ne be miki ba?" Girgiza kai ta yi kafin tace bayan ta yi murmushin da ya fi kama da na yaƙe, saboda har lokacin ba ta dawo daidai ba.

"A'ah fa Babe.." Be yadda ba se da ya gyara mata zaman sosai kafin ya koma ya zauna, daidai lokacin da yake faɗin

"Yau na sake tabbatar da ƙaunar da ke tsakanin en biyu." Murmushi Didi ta yi tana tuna abubuwan da suka faru.

"Allah Ya raya mana, Ya ƙara miki lafiya ke da Babynmu." Ya faɗa yana hango fuskar Babyn da ya baro yanzu cikin ɗaki. Ɗan ajje numfashi ya yi kafin ya gyara zama yace

"Wato idan na tuna yanda auranmu ya kasance se na dinga mamaki sosai. Ikon Allah ne kawai ya haɗa mu, ban da shi babu wanda ya isa ya haɗa mu. Idan na tuna farkon ganinki da na yi da kuma yanda abubuwa suka soma faruwa tun bayan nan.. Ashe ban sani ba haɗuwa da ke ne silar zuwana gidanku. Da na haƙura da marin da Afaaf ta min da ban haɗu da ke ba. Se yanzu na gane ashe rashin haƙuri ma wataran yana da rana." Ya ƙare yana wani murmushi. Tura baki ta yi kafin tace

"Kai dear rashin haƙurin?"

"Ehh mana, ba gashi ya haɗa

Please Login or Register in order to submit comment