Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su Mami suke da ita da Ameera Mami ta fahimci wannan abu tace "tana tsoron mu ne kai ne zaka nuna mata abubuwa saboda yanzun kai ne ta sani tana karashe maganar tana kallon ta cikin tausayawa.


Rike mata hannu yayi yace "insha Allah Mami zo mu Zauna yana nuna mata wuri zama.


Rike take da shi sosai kada ya gudu ya barta zaunar da ita yayi saman gado yayi sannan shi ma ya zauna saman kujera.


Dariya Ameera ta kwal, 'kyale da ita sosai tace " Yaya Taheer yanzun ka zama mai raino hhhh.


Kallon ta yayi da alamar tambaya.


Tace "Yaya Taheer ko da gurin aiki zakaje to tare zakuje kuwa.


Mami tace "kwari ma kuwa kullum sai ka nuna mata abubuwa..


Kallon ta yana murmshi yace "insha Allah Allah ya bamu ladar taimako ...


Amin ya Allah suka ce.


Kallon su take Amma bata gane komai ba gashi tana jin yunwa tace "ni dai wallahy yunwa nake ji..


Zaro ido sukayi da mamaki da al,jabi Ameera tace "kai ke dama ba haushiya ce........



*HASSY SOJA CE*✍🏻✍🏻

*COMMENT AND SHARE*


🧑🏻‍✈️ *CAPTAIN KABEER* 🧑🏻‍✈️



*RUBUTAWA*


*HASSY SOJA ce*✍🏻


*MAMA NA DA BABA NA ALLAH YA JIKANKU DA RAHAMA YA SA ALJANNAH CE MAKOMARKU AMIN YA RABBI*😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

```BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM DA SUNA ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN'KAI GODIYA DA AMINCI SU TABBA GA ANNABI MUHAMMAD S. A. W ALLAH YA KARA MASA DARAJA AMIN```



*WANNAN LABARIN NAWA GAJERAN LABARI NE*😀😀😀😀😀😀

*WANNAN NOVEL DIN BA NA KUDI BANE RASHIN COMMENT ZAI SANYA YA KOMA NA KUDI YASIN*

*GARGA'DI*


*BAN YARDA WANI KO WATA YA SU JUYA MANI LABARI BA SAI DA IZINI NA YIN HAKA KUSKURE NE DAN HAKA SAI AKIYA YI*😎😎😎😎

*TO MASOYAN CAPTAIN KABEER GASHI NAN DAI ALLAH YA BANI IKON NAYI MAKU POSTING YAU DA MASU KIRA NA DA MASU MANI MAGANA TA PC NAGODE SOSAI DA SOYAYYAR DA KUKE MANI*😘😘😘😘😘😘😘💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻



*SADAUKAWAR GA MASOYANA AKO INA KUKE A AFADIN NIGERIA DAK KASASHIN WAJE WANNAN NAKU NE*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻


🅿️3️⃣6️⃣%4️⃣0️⃣


*_________________*🖊️

Zaro ido sukayi da mamaki da al,jabi Ameera tace "kai ke dama ba haushiya ce"!? 🤔

Kallon su tayi sai ta fashe da kuka sosai jikinta har rawa yake saboda yunwa da sauri yace "to ya isa zaki ci abinci ko"!?.


Share hawayen da suka zubo mata tayi tace "ai tunda zu nake jin yunwa".


Ayyah sorry sister kinji ko"!? Cewar Ameera da ke Zaune kusa da Mami.


Abinci ya zuba mata cikin pelta kallon ta yayi sannan yace "Alhamdulillah gashi nan har sai kin koshi.


Amsa tayi jikinta har rawa yake hannu baka hannu akushi har sai da ta kusan cinye wa sannan ta turo masa pelta tace "na koshi yanzun.


Cikin jin dadi Mami tace "to Alhamdulillah yanzun dai babu abun da yake damunki?.


Kallon Mami tayi tana magana mai makun tayi magana sai ta shareta tana kwan ce saman kafadar Taheer shi kuma latsar waya yake doctor ne ya shigo cikin dakin kallon su yayi sannan yace "Alhamdulillah yanzun bata da wata matsalar komai dai to masha Allah meka masa takarda yayi yace "wannan ta sallamar tane sai maganin da zaku siya mata kullum ta sha Allah ya bata lafiya.


Amin amin suka ce hada kayan sanyawa su sukayi sannan Ameera tace "to muje ko Yaya Taheer.


Mik'ewa sukayi sannan suka fita daga cikin dakin hannun sa rike da hannun khadeejah tafiya suke dai dai motar sa suka tsaya bude kofar motar tayi tace "Yaya Taheer ka bude mata ta zauna gaba.


Daga kan sa yayi ya turo wayar sa cikin aljihu sannan ya bude mata yace "to shiga ciki ki zauna ko".


Kallon sa tayi tace " A nan zan zauna"!?.


"Eh mana"

Shiga cikin motar tayi sannan shima ya zagaya ya shiga ciki su Mami kuwa dama sun dade da shiga cikin motar fita yayi daga cikin Asibity gudu yake shararawa har ya iso bakin get din gidan su masha Allah gidan irin masu hali ne babu karya ya hadu sosai.


Horn yayi wa mai gadi da gudu yazo ya bude masa get shigo cikin gidan yayi cikin gareji yayi parking sannan suka fito daga cikin motar cikin gidan suka shiga acikin palon kuwa zazaunawa saman kujera sukayi ya Zauna saman kujera d'aya kusa da shi ta zauna ta rike sa sosai.


Dariya Ameera kayi kasa kasa tace "Yaya Taheer kana da aiki gabanka yasin kuwa".


Yace "to ya zanyi dole na rike ta Amma insha Allah zan rika nuna mata abubuwa.


Mami tayi murmshi tace "wannan gaskiya ne yauwa ka kira Amina kuwa"!?.


Shiru yayi sannan yace "A'a Mami inaso sai zani gida sai na fada mata saboda kin san bakin kishi gareta wallahi.


Cikin tausayawa tace "hakane gaskiya Allah dai ya rabaku lafiya.


Ameera tace "Himm ai wallahi kishi har na hauka take da shi kai ni dai ba yar uwar sa ba to bata yarda mace ta rabe sa ba Allah dai ya kyauta.



_*Asalin labarin*_


Alhaji muntaka shine Babba sai Mommy ita ce Auta adakin su da Alhaji buzu da Hajiya dakin su guda Auren zumunci akayi masu Alhaji muntaka ya Auri Hajiya shi kuma Alhaji buzu ya Auri mommy rana d'aya akayi bikin su kwana atashi babu wuya gurin Allah ya shekara goma da Auran su Mommy ce ta haifi shin talelen jariri yaro ranar suna ya ci sunan sa KABEER haka suka cigaba da rainon kb har ya kai shekara tara ciwo ciki yayi sanadin rasuwar sa kowa ya shiga cikin damuwa da tashin hankali suka shiga bayan rasuwar mahaifin Kabeer sannan aka haife jaririya fara ce sosai Allah yayi mata kyau sosai ranar sunan yarinyar taci Sunan KHADEEJAH haka suka cigaba da raino.


Har wani shekaru goma kb yana karatu kasar India.


Khadee kuwa tana kusa da gida lokacin ta kara girma haka ita ma aka sanya ta school sosai take karatu.


Bayan wasu Shekaru abubuwa sun faru har da shiga Aikin soja da kb yayi cikin ikon Allah samu CAPTAIN KABEER gida kuwa suna cikin farin ciki sosai komai yana tafiya dai dai.


Khadeejah kuwa ta grima dan yanzun shekarar ta goma sha biyar aduniya har ta gama second school yanzun tajona jami,a ta tafi gurin Shopping ta shiga cikin shagon turaren wuta turaren jiki da coconut milk siyaya mai yawa tayi tazo acire kudi sai akace "hello sauraniyar ta dafata dai kina lafiya"? Da sauri najiyo ina kallon sa murmshi yayi yace "yes ni dai Sunan SULEIMAN ni ka d'aya ne ga mahaifina kuma bani da mommy dan ta dade da mutuwa kuma muna da dukiya sosai so dafatan zaki soni"!?.


Baki na saki ina kallon sa ya bani da dariya sosai dai na share kawai nace "am sorry ni bana kowa number bale kai daga zuwanka".


Da sauri yace "haba dai beauty kada kiyi mun haka mana ok to nawa zan baki ki bani number ki"!?.


Khadee tace "bana bukatar Namiji kusa da ni tana fadar haka da sauri ta fita daga cikin shagon motar ta shiga ta rufe da sauri tabar gurin.


Biyar ta yayi daga baya dai dai get din gidan su yayi parking kallon sa yace "yes na gano gidan nan ai kuwa kullum sai nazo gidan gurinki kuwa tafiyar sa yayi lokacin.


kullum sai Suleiman yazo gurin ta tun bata fitowa har takai tana fitowa tana fada da shi saboda haushi yake bata ranar ta zaune sai kiran Mommy ya shigo wayar ta dauko tayi ta dauka tace "Assalamu Alaikum barka mu da yamma mommy na ".


Cikin jin dadi mommy tace " Amin wa,Alaikum sallama barka dai Auta ta yaushe, zaki shigo ne"!?.


Dama inason zuwa nayi sati biyu gurinki bari na gyara yanzun zan shigo insha Allah.


To shike nan babu damuwa Allah ya kawo ki lafiya cewar mommy.


Amin amin kashe wayar tayi da gudu ta shiga cikin dakin Hajiya lokaci Zaune take tana kallon da sallama ta shigo cikin dakin.


Amsa mata sallama tayi tace "au ashe ma har kintashi"!?.


Yatsine fuska tayi sannan tace "Eh wallahi Hajiya ina son gudu yau hijira zanyi".


Kallon ta take tace "uhm to shike nan babu damuwa yau zaki guje mu kenan ko"!?.



Murmshi tayi tace"laaaa ba haka bane Hajiya sai nadawo da gudu ta fita daga cikin dakin.


Koda ta shigo cikin falon mommy lokacin tana cin naman kaza da hollandia yoghurt da sallama ta shigo.


Dagowa mommy tayi cikin farin ciki tace "A'a Ashe da gaske Auta ta take to shike nan karaso gurin ki ci ragin Mommyn ki".


Murmshi tayi tace "sannu da hutawa mommy na dama kwana biyu kullum sai nayi mafarkin ki wallahi zaunawa tayi kusa da mommy.


Ayyah to gani Auta dafatan dai Hajiya tana lafiya da Yaya na"!?.


Lafiya Qlau cewar khadeejah.


A yau ne *CAPTAIN KABEER* zai dawo Nigeria gyara gyaran gida ake khadeejah kuwa ko da ta fito cikin dakin sai ta hango mommy zaune ta ci kwaliya kamar ba ita ba kamshin turaren ta ne ya game falon shine ya tabbar mata da cewar Auta ta ta fito lokaci waya take da kawayen ta tana cewa "haba dai best yanzun dai yaushe zaki shigo ne"!?.


Karaso gurin tayi tana kallon mommy tace "best zamuyi magana anjima insha Allah.


"Good morning mommy na".


Mommy tayi murmshi tace "my Auta morning kin tashi lafiya"!?.


Khadeejah tace "Alhamdulillah naga sai gyaran gida ake yi lafiya"!?.


Murmshi tayi tace "Yayanki zai dawo Nigeria yau din nan insha Allah.


Gabanta yace rasss wani fargaba ya shigeta gabanta yace dumm dumm jikinta ya soma rawa tace "yau kuma mommy na "!?.


Kallon ta mommy tayi tace "Auta ta lafiya kike kuwa"!?.


Waskewa tayi tace "lafiya Qlau mommy na ina tunani wani abu ne shiyasa.


Mommy dai tace "Himm to Allah ya sa zatayi magana kenan sai kira Waya ya shigo lokacin mommy ta duba sunan my son ta gani dauka tayi tace "missyou my son.


Captain kb yace "miss you my love mom dafatan kina lafiya"?.


Lafiya Qlau har kun iso kenan ko"!? cewar mommy.


dariya yayi yace "Eh wallahi gani nan cin mota ne ok mommy mun iso bakin get.


Kashe wayar tayi tace "tashi muje Yayan ki ya iso.


Mik'ewa mukayi jikinta babu kwari haka suka fito waje motoci suka shigo cikin gidan dai dai inda mommy take tsaye sukayi parking.


Kusan mintina 30 sannan ya fito daga cikin motar kallon gidan yayi sannan karaso gurin mommy yace "miss you my love mom.


Bude masa hannunwa tayi tace "missyou my son rungume sa tayi cikin jin dadi sosai.


Hada ido yayi da Khadeejah ta watsa masa harara sannan tayi magana kasa kasa tace " dube sa dan Allah sai kace karamin yaro mtss.


Sakin mommy yayi yace "my love mom wannan yarinyar fa yana mata mugun kallo.


Juyawa tayi tace "Au kanwarka ce fa Auta ta ce har kamanta da ita ne"!?.


Dafe kansa yayi yace "ok ke baki iya gaisuwa bane"!?.


Wuce cikin gidan mommy tayi tana murmshi jin dadi yau d'anta yadawo gida.


Dariya tayi masa sosai sannan ta daure fuska tace "ban iya ba gaisuwa ni ko mutum ban gani ba bale na gaishe da shi .


Karasowa gurin yayi dai dai numfashin sa yana tafiya tare da nata yace "yaushe kika iya rashin kunya ne"!?.


Jikinta yaso ma rawa tace "mallam meye haka wai kake nufi ne"!?.


Karasowa yayi kamar zai rungume ta yace "abun da kike nufe shi ne ke damunki ne? arayuwa dole ki bani girma na fa.


Jikinta har rawa yake sosai tace "ni dai babu abun da nake nufi ka bani guri na ce".


Murmshin gefen bakin sa yayi yace " kada ki kuskura na ganki da wani mutum ko saurayi dan baki isa Aure ba saboda ban tashi maki Aure ba yanzun sannan yayi gaba abun sa.


Baki saki tana kallon sa hawayen bakin ciki suka zubo mata da sauri ta goge hawayen koda ta dago sojoji ne tsaye cikin gidan da sauri ta wuce cikin gidan.


Daki tashige ta rufe ta fashe da kuka sosai kamar ranta zai fita.


Bayan ya shiga cikin dakin sa wanka yayi sannan ya fito ya sanya farar jalabiya sannan ya fito falo Zaune ya hango mommy Amma bega khadeejah ba tabe baki yayi ya karaso gurin mommy ya Zauna saman kujera yace "washii na gaji sosai wallahi.


Cikin kulawa tace " ai dole yanzun dai kaci abinci.


Ajiyar zuciya yayi sannan yace "ina wannan yarinyar tazo ta zuba mani abinci.


Kallon sa mommy tayi sannan kwala mata kira tayi tace "Auta ta kizo ina falo.


Khadeejah kuwa tana daki taci kuka sosai har ta koshi toilet tashiga ta wanke fuskar ta sannan ta fito kiran mommy ne ya shigo cikin waya bata dauka ba sai dai ta fito falo hango shi tayi Zaune yana latsar wayar sa karaso gurin tayi tana kallon mommy tace "gani mommy na


Mommy tace "yauwa Auta ta ki zuba ma Yayan ki abinci ina zuwa tashi tayi ta wuce cikin dakin.



Jitayi kamar takama dukan sa saboda bakin ciki da takaici kamar ta hade zuciyar ta ta mutu saboda haushi.


Pelta ta dauko ta cika masa abinci sannan ta ajiye gaban sa ta mike tsaye zata wuce sai taji muryar sa yace "ke gidanku haka ake ba mutum abinci halama nayi maki kada da irin ki ne"!?.


Kallon ta jifa masa tace " ai ga alamome nan nagani tunda baka da hannuwa da zaka ci abinci.


Kallon ta yayi yace "ke wasa nake da ke ne to maza ki dauke abinci nan ki cinye sa.


Murguda masa baki tayi tace "sannu sarkin huta to ba zan ci ba ko nayi maka kama da mai jin yunwa ne".


Wata irin tsawa ya daka mata idanuwan sa sukayi jajaru yace "zo nan".


Jikinta yaso ma rawa tace "Allah sai dai ka kashe ni Amma bazan zo ba.


Mik'ewa tsaye yayi da gudu khadeejah ta shige daki ta rufe tana ajiyar zuciya tana mamakin irin halin na.


Shi kuma mamakin rashin kunyar ta yake dogon tsaki yaji.


Wata rana Captain kb yazo gaida Hajiya sai yaga mutum tsaye bakin get parking yayi sannan ya fito yana kallon sa yace "kai daga ina"!?.


Washe baki Suleiman yayi yace "nazo gurin matar da zan Aura"..


Tsawa ya daka masa yace "Babu wata matar ka anan daga yau duk sannan na kara ganinka sai na karya maka kafafuwa kaji ko"?.


Cikin rawa jiki yace "dan Allah kayi hakuri wallahi ba zan iya rayuwa babu ita ba.


Kiran sojoji yayi yace "kun ga wannan dan iskan yaro duk ranan da yakara zuwa gidan ko sai nayi maganinku afusace ya shigo cikin gidan..


Yace "wallahi sai na dauki fansa.


*Dawowa labari*


*A bangaren Captain kabeer kuwa*



Zaune yake yana aiki ga laptop turo kofar office din kayi be dago idanuwansa ba ya cigaba da aikin sa.


Sir gashi tare muke da shi cewar wani soja.


Kashe laptop din sa yayi sannan ya mik'e tsaye ya fito waje sojan yana biye da shi.


Durkushi yake kasa yana kuka sosai har da majina idanuwan sa sunyi kumburi sosai.


Kallo d'aya yayi masa ya dauke idanuwan sa gurin yace "ku kai sa gidan horo.


Dagowa yayi ya kalli fuskar Captain kb babu rahama yace "dan Allah oga kayi hakuri wallahi ba zan kara ba dauke ta ba.


Ko inda yake be kalla ba juyawa yayi ya koma cikin office haka suka dauke sa suka tafi da shi gidan maza.............



*To masoyan CAPTAIN KABEER gashi nazo nayi maku posting din asha karatu lfy*
😁😁😁😁😁😁

*HASSY SOJA CE*✍🏻✍🏻

*COMMENT AND SHARE*



*CAPTAIN KABEER*



*RUBUTAWA*


*HASSY SOJA ce*✍🏻


*MAMA NA DA BABA NA ALLAH YA JIKANKU DA RAHAMA YA SA ALJANNAH CE MAKOMARKU AMIN YA RABBI*😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

```BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM DA SUNA ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN'KAI GODIYA DA AMINCI SU TABBA GA ANNABI MUHAMMAD S. A. W ALLAH YA KARA MASA DARAJA AMIN```



*WANNAN LABARIN NAWA GAJERAN LABARI NE*😀😀😀😀😀😀

*WANNAN NOVEL DIN BA NA KUDI BANE RASHIN COMMENT ZAI SANYA YA KOMA NA KUDI YASIN*

*GARGA'DI*


*BAN YARDA WANI KO WATA YA SU JUYA MANI LABARI BA SAI DA IZINI NA YIN HAKA KUSKURE NE DAN HAKA SAI AKIYA YI*😎😎😎😎


*SADAUKAWAR GA MASOYANA AKO INA KUKE A AFADIN NIGERIA WANNAN NAKU NE*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻


🅿️4️⃣1️⃣%4️⃣5️⃣


*_________________*🖊️

Ko inda yake be kalla ba juyawa yayi ya koma cikin office ya cigaba da aikin sa haka suka dauke sa suka tafi da shi gidan maza.


Kuka yake yana magiya Amma basu saurara masa ba cikin gidan suka shiga da shi mutane ya gani kamar bayi aikin wahala kawai suke babu Wanda ya damu da su can gefen wani ya hango an dukan sa kamar jaki hankalin sa ya tashi sosai yace " dan Allah ku taimake ni zanyi fitsari"!?.


Wani katun soja ne yazo da bulalar sa katuwa yace "oga aiki zayayi ne"!?.


Sojan yace "eh shine wanda ya sace kanwar Sir".


Zaro ido sukayi da mamaki da al,jabi katun sojan yace "kutttt kace nama ne gasashi ai kuwa zaka ci ubanka zamu koya masa hankali.


Jikin sa ya soma rawa yace "kuyi hakuri wallahi shairin shed'an ne"!?.


Sojan yace "yanzun sai shed'an ya taimake ka tunda da sani nai ku wuce da shi kawai "sannan ya juya ya fita daga cikin gidan mazan.


Watsa masa dorinar yayi sai da ya fadi kasa some ruwa masu sanyi ya watsa masa ajiyar zuciya Suleiman yayi yace "Ashe mafarki ne nake".


Can yaji ance ba mafarki ne kake ba fa.


Zaro ido yayi shi har ga Allah ya dauka mafarki ne yake kuka yake jikin sa na rawa yace "dan girman Allah oga kayi hakuri bazan kara ba.


Kara watsa masa yayi sai da yasaki firsari a wandon sa da gudu ya shiga cikin gurin dai dai gurin dutsi yayi tsaye yana kuka har da majina yaji an ce "kalle wannan dutsin kagan shi ko"!?


Daga kai yayi yace "eh na gashi".

Dariya yayi sosai sannan yace "shi ne zakayi aiki gurin inaso ka fasa mani shi gaba d'aya da kagama shike nan ka gama da wannan aikin.


Shiru yayi cikin ransa yace "yanzun shike nan nazama dan wahala sanadin Khadeejah gashi ban iya aiki ba kuma gashi an ce da nagama wannan shike nan afili kuwa yace "yanzun da nagama wannan shike nan gida zan koma"!?.


Daure fuskar sa yayi yace "yaushe nayi da kai haka to aiki yanzun ka sanya hannu kuma kana murnar zuwa gida salon kacigaba da iskan ci ko to ba yanzun ba wuce ka cigaba da aiki yaro.


Kuka yake sosai idanuwan sa har sunyi kumburi haka ya karasa gurin jikinsa babu kwari sosai guduma ya dauka kamar ya fadi saboda nauyi.


Captain kb kuwa Zaune yake yana kallon su duk abun da suke yana gani murmshin gefen bakin sa yayi yace "Am sorry yaro ka shigo hannu" video ya turo ma su mommy da daddy.


*A bangaren su Mommy kuwa*


Zaune take sai taji wani sako ya shigo cikin wayar ta taji sai ta duba sunan my son tagani video ne tagani tana budewa wahalar da Suleiman yake sha ita tagani dariya mommy tayi tace "wannan shine dai da kai kiran daddy ya shigo cikin wayar ta dauka tayi tace "Yayana kaga abun da ya dace da shi ko"!?.


Gyara zama yayi sannan yace "wallahi kuwa abun yayi kyau sosai ai Hajiya tana kallon sai tayi dariya tace "Allah ya kara masa.


Labari suka cigaba da yi abubuwa suka mata ayi masa sannan sukayi sallama.


Hajiya kuwa share hawayen ta tayi tace "Allah sarki y'ata ko tana cikin wane hali Allah ne masa Allah ya sa tana cikin koshin lafiya.


Kwantawa tayi saman gado sai bacci yayi gaba da ita.


Koda daddy ya shigo bacci ya sameta tana yi cikin tausayawa yace "insha Allah y'ar ki zatadawo maki nada badadewa ba in Allah ya yarda" sannan ya fita daga cikin daki.



*A bangaren khadeejah kuwa*


Yanzun ta fara sakin jikinta da su Mami yau ma kamar kullum Zaune take tana kallon tv da sallama Taheer ya shigo cikin falon Ameera ce sai Khadeejah kallon sa Ameera tayi tace "Yaya Taheer ina kwana".


Kallon ta yayi yace "Ashe kuna cikin falon lafiya klau ina Mami"!?.

Tana ciki bari nakira ta cewar Ameera.


Zaunewa yayi Saman kujera ya daura kansa yace " yar India yau babu magana"!?.


Turo baki tayi tace "to ba tunda kashigo nake maka sannu da da zuwa Amma ko kallona bakayi ba.


Tashi Zaune yayi yana kallon ta yace "haba dai kanwata kodai kinyo fada da Auntyn ki ne"!?.


Muryar Ameera yajiya tace"himm waye zai kara zuwa gidan ka ai wallahi mu da gidan ka ko ba yanzun ba.


Kallon su yake sosai lokacin Mami ta shigo cikin falon tace "A'a Taheer yanzun ka shigo tana kokarin zaunawa kusa da ita.


Yace "eh wallahi wai me yake faruwa ne kanwata fushi take da ni"!?.


Tabe baki Mami tayi sannan tace "matar ka bata fada maka wani abu ba ne"!?.


Girgiza mata kai yayi yace "eh babu abun da ta fada mani kawai dai na sameta tana ta bakar masifa Amma ban tambaye ta ba.


Himm wai meya sa Amina bata da hankali ne su Ameera ne suka je gidan ka zagi kala kala take ma baiwar Allah nan wai wallahi sai ta kashe ta duk sannan ta ganku tare da ita.


Dafe goshin sa yayi sosai sannan yace " *innalillahi wa inna ilaihir raji un* wai yaushe zata rage haukar kishi ne haukar ta zata hanani nayi Aure ko yayi wallahi Mami da ina da wata budurwa da sai na Aure ta nagaji da haukar Amina wallahi.


Cikin kulawa Mami tace "hakane Allah ya baka ta gari ko nima inaso naga jikoki na wallahi.


Ameera tace "ga yar India nan aka Aure ta.


Da sauri Mami tace "A'a kada ayi haka saboda baku sani ba ko tana da Aure sannan ke Ameera kada ki sake wannan maganar dan Allah.


Ajiyar zuciya Taheer yayi yace "wallahi kuwa nima abun da nake tunani kullum sai nayi tunani ko tana da Aure gashi inason sosai har cikin raina.


Kallon su Khadeejah take Amma bata gane komai ba tace "wai lafiya kuke kuwa naga kun shiga cikin damuwa ne"!?.


Kallon soyaya yake aika mata da shi da sauri ta dauke idanuwanta gurin.


Mami tace "wallahi kuwa Yayan ki ne yana cikin matsala sosai saboda matar sa bata barin sa yayi Aure ko budurwa bata yarda ta rabesa ba.


Khadeejah tace "to Allah ya sauwaka Allah ya shige masa gaba.


Gaba d'aya suka ce" Amin ya Allah.


*A bangaren Daddy kuwa*


Mommy da Hajiya Zaune gurin d'aya gyara zama daddy yayi yace "to Alhamdulillah yanzun ke Hajiya ina mai baki hakuri akan abun da zan yanke.


Kallon sa suka kowa yana son yaji abun da zai fada.


Hajiya ta kalle mommy tace "Alhaji kayi magana mana ka sanya mu cikin duhu fa ko ba gaskiya ba"!?.


Mommy tace "wannan gaskiya ne Yaya kayi muna bayani.


Gyara murya yayi yace "Abu na farko shine mu dauke wannan abun amatsayin kadara.


Jin jina kai sukayi suka ce "wannan haka yake.


"Sannan kun ga yanzun bamu san inda Shalele take ba Amma ina tunani tana cikin koshin lafiya.


"Hakane insha Allah muna tunani haka".


Jin jina kai yayi yace "masha Allah abu na gaba shine inaso na hada Shalele da yarona Auren Zumunci kamar yarda akayi muna inda tadawo sai afada mata nasani zasu muna biyaya insha Allah.


Wasu hawayen farin ciki ne suka zubo masu mommy da Hajiya da sauri mommy tace "Allahu akbar yanzun dai ka nufin da Auta ta da my son zasuyi Aure kenan.


"Kwari ma kuwa cewar daddy.


Share hawayen ta Hajiya tayi tace "to kuna gani zasu amince kuwa saboda nagani basu shan inuwa d'aya"!?.


Mommy tace "nima dai abun da nake tunani kenan kullum ciki fada kamar kaji".


Daddy yace "zasu shirya ai saboda babu wanda zai kalle su insha Allah sai munyi alfahari da wannan Aure.


Hajiya tace "to

Please Login or Register in order to submit comment