Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wallahi Mami ban sani ba kawai kwana biyu bana jin dadi ne shi kuma Yaya Taheer rashin Khadeejah ne wallahi yana sonta sosai.


Shiru Mami tayi na dan wani lokaci sannan tace " to Allah ya sauwake.


Da sallama ya shigo cikin falon zaunawa saman kujera yayi yace "Mami lafiya dai ko"!?.



Ajiyar zuciya tayi tace "wallahi ina tausaya maka ne Amma insha Allah zaka samu mata tagari.


Murmshi yayi yace "babu komai ai Mami ni na bar ma Allah komai.


Cikin jin dadi tace "Alhamdulillah yanzun naji dadi haka Allah ya kawo.


Sallamar wata yar budurwa ce ta shigo cikin falon tana murmshi Ameera da ke zaune gefe muryar da tajiya ne da sauri ta dube kofar zaro ido tayi tace "Maryam yau ke ci gidan na mu da gudu taje ta rungume ta.


Cikin kunya tace "wallahi kuwa sake ni mu gaisa da Mami karasowa tayi tace "ina wuni Mami"!?.


Murmshi Mami tayi tace "lafiya klau ya gida naku ina Mamar ki"!?.


Sunkuyar da kanta tayi tace "suna lafiya tace ai gaishe da ku.


Muna amsa wa sosai.

Yaya Taheer ina yini cewar Maryam.


Baki ya saki yana kallon ta sai da Ameera tace "Yaya Taheer an gaishe da kai fa.


Murmshi yace "Alhamdulillah su mommy na lafiya dai ko"!?.


Cikin jin kunya tace "lafiya klau Yayan mu"tashi tayi suka wuce daki da ita da Ameera.


Kallon Mami yayi yace "wallahi ni dai yarinyar nan tayi mani sosai Mami.


Murmshi Mami tayi tace "to Alhamdulillah Allah ya tabbar muna da alkhairi.


Kiran wayar sa yayi yana duba wa sai ya ga sunan Suleiman dauka yayi yace "ya akayi ne dan uwa" da yake yanzun sun zama yan uwa.


Yana tuΖ™i yace "ina saman hanya fa zan shigo gari".


Da sauri Taheer yace "Haba dai kai dan uwa kace yau zamuyi babban bako"!?.


Dariya yayi sosai yace "insha Allah sai nazo ina kanwata masifafa"!?.


Dariya Taheer yayi yace "Ai kuwa kai da ita kun zama toom and jerry fa Allah daga ina sai gidan ka.


Kashe wayar sa yayi yana dariya yana tuΖ™in sa.


Kallon Mami yayi yace "Ι—an ki yana saman hanya zai shigo.


Kai masha Allah abu yayi kyau Allah ya kawo shi lafiya................


*TOPA SULEIMAN YA FADI TARKON SOYAYYAR AMEERA TAHEER KUWA SHIMA DAI YA FADA TARKON SOYAYYAR MARYAM KO YA ABUN ZAYA KASAN CE*πŸ€”πŸ€”πŸ€”πŸ€”πŸ€” 🀣🀣🀣🀣🀣🀣

*KU CIGABA DA BIBIYA TA DA SAMUN AMSA WANNAN TAMBAYOYIN*πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»


*HASSY SOJA CE*✍🏻✍🏻

*COMMENT AND SHARE*



πŸ§‘πŸ»β€βœˆοΈ *CAPTAIN KABEER*πŸ§‘πŸ»β€βœˆοΈ



*RUBUTAWA*


*HASSY SOJA ce*✍🏻


*MAMA NA DA BABA NA ALLAH YA JIKANKU DA RAHAMA YA SA ALJANNAH CE MAKOMARKU AMIN YA RABBI*😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

```BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM DA SUNA ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN'KAI GODIYA DA AMINCI SU TABBA GA ANNABI MUHAMMAD S. A. W ALLAH YA KARA MASA DARAJA AMIN```



*WANNAN LABARIN NAWA GAJERAN LABARI NE*πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€

*WANNAN NOVEL DIN BA NA KUDI BANE RASHIN COMMENT ZAI SANYA YA KOMA NA KUDI YASIN*

*GARGA'DI*


*BAN YARDA WANI KO WATA YA SU JUYA MANI LABARI BA SAI DA IZINI NA YIN HAKA KUSKURE NE DAN HAKA SAI AKIYA YI*😎😎😎😎


*SADAUKAWAR GA MASOYANA AKO INA KUKE A AFADIN NIGERIA WANNAN NAKU NE*πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»


πŸ…ΏοΈ7️⃣1️⃣%7️⃣5️⃣


*_________________*πŸ–ŠοΈ

Kai masha Allah abu yayi kyau sosai Allah ya kawo shi lafiya cewar Mami da take murmshi.


Amin ya Allah dama kwana biyu yana kira yace mani zai shigo sai dai yanzun Allah yayi zuwa nai.



Jin jina kai Mami tayi tace "haka ne Allah dai ya kawo muna shi lafiya.


A bangaren Suleiman kuwa yanzun ya shigo kaduna kuka kawai yake shararawa saman tit cikin i unguwar tudun wada ya shigo kiran wayar Taheer yayi yace "ina shigo cikin tudun wada fa.


Ok babu damuwa gani nan fitowa kaji rani yanzun cewar Taheer.

Kashe wayar sa yayi yana jiran sa ko mintina biyar beye ba sai gashi ya isko gurin da yake ya fada masa motar da shigo Taheer yace "kaga gida can fa kai kullum sai na fada maka"!?


Hararar sa Suleiman yayi yace "ban sani ba tuΖ™in motar yayi dai dai get din gidan sai yayi horn da sauri mai gadi ya bude masa shigowa cikin gidan yayi samu guri yayi sannan yayi parking kashe motar yayi bude masa kofar motar Taheer yayi yace "to fito mana Mami na jiranka.


Fitowa yayi daga cikin motar yana murmshi sannan ya bashi hannu sukayi musabiha.


Cikin gidan suka wuce da shigowa cikin falon yayi da sallama Taheer yana dariya yace "uhm Mami ga surukin kinan ya iso.


Da sauri Suleiman yake kallon Taheer da mamaki yace "kamar ya fa"!?.


Murmshi Mami tayi tace "Suleiman sannu da zuwa ansha hanya ko"!?.


Sosa kai yayi da key din sa yace " Yauwa Mommy na same ku lafiya"!?.


Lafiya klau ya daddyn naka yana klau ko"!?.


Yace "a gaishe ku.


Muna amsa tashi ka zauna mana.


Saman kujera ya zauna yana watsa da key din sa yayi kusan mintina 30 sannan yace "wai har yanzun banga Ameera ba ko ta fita ne"!?.


Dariya Taheer yayi yace "Alhamdulillah yanzun gashi nan ya fada da bakin sa.


Kallon sa yayi yace "Himm ba haka bane to wai ma ko haka ya akayi ne"!?.

Dariya Mami tayi tace "ni indai Ameera ina tana son shi ai shike nan sai ayi yar gida kawai.


Duk kunya ta kasa shi yace "wasa nakeyi fa Mami.

Ai ko da gaske kake yi mun baka shike nan cewar Taheer yana murmshi kwala ma Ameera kira yayi.

Zaune suke suna labari kira ta tayi anayi shi ya sanya ta tace "ina zuwa dan Allah kiyi hakuri Yaya Taheer na kira na".

Murmshi maryam tayi tace "wai ni ai yanzun gida zani je fa".


Bata fuska tayi tace "ni dai gaskiya ba yanzun ba bar nadawo"da sauri ta fito daga cikin daki tana murmshi hango su Mami da Yaya Taheer tayi sai taga wani hadaden saurayi zaune karasowa tayi tace "gani.


Kallon sa yayi sannan yace "uhm ga Yayan ki nan yazo yace duk yau be ganki ba.

Kallon sa tayi sannan ta zauna kusa da Mami tace"Yaya Taheer waye dan Allah.


Suleiman yace "ni ne mana ko baki gani ne ba ne"!?.

Harara ta watsa masa tace "Au dama kai ne kazo"tabe baki tayi tana kallon sa kasa kasa tana hararar sa.

*A bangaren Khadeejah kuwa*



washe gari da rana shinkafa da wake ta girka masa lokacin yana aiki sai da ya kamala sannan ya fito daga cikin dakin falo ya nufa wata hadader kula ce ya gani karasowa yayi gurin Khadeejah kuwa tana kwan ce saman kujera tana kallon tv kamshin turaren captain kb tajiya shine zuciyar ta take bugawa da sauri sauri *Innalillah wa inna ilaihir raji un* cikin ranta tace "wai meya ke faru da ni ne mtsss.


Da sauri Captain kb ya daure fuska yace "ke tashi zaune".


Turo masa baki tayi tana kallon kasa kasa tana hararar sa tace "ni wallahi nagaji yanzun fa na gama gyaran daki da girki fa.


Watsa mata mugun kallo yace " wasa nake da ke ne tashi zaune nace"cikin masifa.


Tashi zaune tayi idanuwan ta sun cika da hawaye sai gan gara suke.

Tabe baki yayi sannan ya zauna saman kujera ya daure kafa d'aya saman daya fuskar sa babu rahama yace "zuba mani abinci naci".

Shiru tayi masa tana wasa da yatsinta wata irin tsawa ya daka mata sai ta tashi zata gudu saboda tsoro sai zaro ido tayi tace"to" durkusa kasa ta zuba masa lemon juice sannan ta zuba masa shinkafa da wake ta mike masa.


Binta yayi da mugun kallo yace "me kike nufe da ni ne halama ce maki akayi ni rago ne da zaki ta dirka mani wake da shinkafa to bashi nake so ba ki tashi maza da sauri ki daura mani yan ball.


Kuka ta fashe da shi sosai tace "haba dan Allah kayi hakuri bata karasa ba ya daga mata hannu yace "bashi nace kiyi ba dole yan ball zakiyi mani dan har kina son zaman lafiya a cikin gidan kuwa kuma sannan wannan abinci ke zaki cinye sa" yana gama fadar haka yayi kwan ce yar sa saman kujera ya lumshe idanuwan sa.


jiki babu kwari haka ta mik'e ta wuce kitchen ta daura masa abincin da yake so tana kuka tana girki kusan mintina 50 sannan ta fito da kula acikin kitchen kawo masa tayi tace "gashi nan nagama.


Shiru yayi mata kamar mai bacci haka yayi mata sai da ya ga alamun tagaji har ta fara kuka sannan yace" uhm saman kai na zaki ajiye sa ko yayi bude idanuwan sa yayi yana kallon tv.


Jikinta rawa yake sosai gashi kanta yana ciwo sosai sannan ta ajiye masa abinci har ta mike zata wuce sai taji yace "kina nufe ni zan zuba mani abinci ko yaya"!?.

Dawowa tayi ta zuba masa yan ball sannan tace "gashi nan".



tashi zaune yayi yace "ci na gani kin san dole sai da haka kada ki zuba mani guba naci na mutu maza ci abinci nan"yana daure fuska.


Dafe kanta tayi tace "na koshi wallahi".

Murmshin mugunta yayi yace "ko ki ci ka nayi maki dure da kai na.


Tana jin yace haka da sauri ta sanya hannunta ciki tana ci tana yatsinar fuska tace "to na koshi fa"!


Kallon ta yayi yace "haka ake cin abinci ne"!?.


Tashi tayi tana hawaye tace "to ai na koshi ne".


kallon ta yayi sama da kasa yace "ke banson iskan ci zauna ki ci abinci so kike ace bani ci da ke kenan"!?..


Idanuwan ta suka ciki da hawaye tace "to ai na koshi wallahi kuma ai bana jin yunwa".


Tabe baki yayi ya cigaba da cin abincin sa hankali kwan ce ita kuma Khadeejah wuce daki tayi saboda kanta yana mata ciwo koda ta shiga fadawa tayi saman gado tana kuka mai cin rai sai da zazzabi ya fara rufe ta sannan tayi shiru har bacci ya dauke ta.


*A bangaren Suleiman da Ameera kuwa*


Zaune yake yana kallon ta da mamaki yace "Ameera.


Har cikin ranta taji kiran suna ta yatsin fuska tayi tace "gani fa".


Gyara zama yayi sosai da yake babu kowa cikin falon yace"kin ga yanzun na gyara halayena ya kamata ki bani dama na nuna maki soyayya da kauna".


Zaro ido tayi tace "tabba Allah ya sauwake ni ba zanyi soyayya da mugu ba gaskiy.


Dan marairaice mata yayi yace "haba Ameera sai ka ce ba musulmaba kada ki manta bawa yana ma Allah laifi kuma sannan ya roΖ™isa kuma yayafe masa dan Allah kiyi hakuri ko khadeejah da nayi wa wannan abun, shairin sheΙ—an ne kuma ta yafe mani ya kamata ace kin yafe mani ke ma".


Shiru ta na dan wani lokaci sannan tace " to shike nan babu damuwa Allah ya yafe muna baki d'aya.....


Amin ya Allah cewar Suleiman.


*A bangaren Taheer kuwa*


Zaune yake cikin motar da shi da Maryam kallon ta yayi yace "Maryam na san zakiyi mamaki jin abun da zan fada to ba abun mamaki bane alkhairi ne yazo da ni.


Sunkuyar da kanta kasa tayi tana wasa da hannunta tace "to Allah ya sa muji alkhairi.


Murmshi yayi yace "Amin ya Allah Inason ki kuma so bana wasa ba kuma ni Auren ki zanyi nasani kina da wani saurayi Amma.


Da sauri Maryam ta kalle Taheer cikin idanuwan sa taga hango irin son da yake mata ajiyar zuciya tayi tace "Alhamdulillah dama nima ina jiran wannan rana da zaka furta mani so kuma ni amince dari bisa dari .


Taheer yace "Alhamdulillah Ashe akwai ranar da zaki aminci mani wai halama dama kina so na ne"!?.


Rufe fuska tayi tana dariya tace "eh mana ko kana mamaki ne"........





*HASSY SOJA CE*✍🏻✍🏻

*COMMENT AND SHARE*




β€πŸ§‘πŸ»β€βœˆοΈ *CAPTAIN KABEER*πŸ§‘πŸ»β€βœˆοΈ



*RUBUTAWA*


*HASSY SOJA ce*✍🏻


*MAMA NA DA BABA NA ALLAH YA JIKANKU DA RAHAMA YA SA ALJANNAH CE MAKOMARKU AMIN YA RABBI*😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

```BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM DA SUNA ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN'KAI GODIYA DA AMINCI SU TABBA GA ANNABI MUHAMMAD S. A. W ALLAH YA KARA MASA DARAJA AMIN```



*WANNAN LABARIN NAWA GAJERAN LABARI NE*πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€

*WANNAN NOVEL DIN BA NA KUDI BANE RASHIN COMMENT ZAI SANYA YA KOMA NA KUDI YASIN*

*GARGA'DI*


*BAN YARDA WANI KO WATA YA SU JUYA MANI LABARI BA SAI DA IZINI NA YIN HAKA KUSKURE NE DAN HAKA SAI AKIYA YI*😎😎😎😎


*SADAUKAWAR GA MASOYANA AKO INA KUKE A AFADIN NIGERIA WANNAN NAKU NE*πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»


*LAST PAGE*πŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”š


πŸ…ΏοΈ7️⃣6️⃣%8️⃣0️⃣


*_________________*πŸ–ŠοΈ

Rufe fuska tayi tana dariya tace "eh mana ko kana mamaki ne"!?.


Murmshi yayi sannan yace "kwari ma kuwa dole nayi mamaki mana.


Himm ai ba abun mamaki bane alkhairi ne saboda lokacin da Ameera suke zuwa gurina babu abun da ban sani ba game da kai Yaya Taheer wallahi ni tun lokacin da naganka na kamu da sonka Amma sai dai kashi wata tarigani.


Jin jina kai yayi yace "to meyasa baki fada mani kina sona ba"!?.


Dariya Maryam tayi tace "Haba dai nace inasonka kuma tabba ai bazan iya fada maka ba saboda mu mata muna da al, kunya fa nace ni fa ko cewa nayi wallahi ko soyayyar zata kashe ni to ban fada wa kowa ba sai sirin zuciya ta .


Dariya yayi sosai sannan yace "gaskiya Ina Ashe ina matata kusa da ni Allah sarki yanzun sai nayi ta biyu da ke".


Cikin shagwaba tace "ni uhm uhm uhm uhm uhm uhm Allah bazan zauna da kishiya.


Zaro ido yayi yace " kina nufen bazaki Aureni ba kenan ko"!? .


Da sauri Maryam kallon sa tace "ni wallahi ba haka nace ba ni fa nafi son na zauna da ni da mijina mu sha soyayya fa"da sauri ta rufe fuska tana dariya.


Taheer yace "Alhamdulillah Alhamdulillah yanzun nasamu mata Allah ya nuna muna lokaci lafiya mu sha soyayyar mu.


A bangaren Suleiman kuwa yanzun komai yana tafiya dai dai Ameera ta amince da soyayyar sa wata irin soyayya yake nuna mata sosai yanzun Auren su saura kwana biyu biki.


*A bangaren Khadeejah kuwa*


ko ina da ko ina ta gyara sosai sannan kuma girki kullum sai ta canza kalar abinci yau ma ta gama girki kusan mintina 50 tana zaune falo tana chat da Ameera kamshin turaren captain kb tajiya shine zuciyar ta take bugawa da sauri sauri cikin kafin hali tacigaba da chat voice Ameera tayi mata tace "Amarya kina kamshi wai Yaya Captain kb ne ko ya koma America"!?.


Zaunawa yayi saman kujera ya daure kafa d'aya saman daya fuskar sa babu rahama yana kallon tv Amma duk abun da take yana kallon ta ta gefen idonsa itama sai tayi mata voice tace "wallahi lafiya klau muke yana gari be koma ya su Mami da Yaya Taheer "!?.


Koda ta dago idanuwan ta sai cikin nashi da sauri ta daura idanuwanta ta cigaba da chat Captain kb yace "ke zubo mani coffee zan sha.


To kawai taci da shi sannan ta tashi ta wuce kitchen coffee ta hadu masa sannan ta fito daga cikin kitchen falo ta nufa a hankali koda ta karaso guri tace "gashi" ta mika masa kenan ya dago hannu Ashe be amsa ba kawai ta saki coffee ya zube mata kafafuwa sai kofin ya fashe kasa ihu ta saki ta fadi kasa tana kuka sosai hankalin sa ya tashi sosai yace "Subhanalillah sannu da sauri ya dauko ruwan sanya yazo ya zuba mata yana goge mata kafafuwanta yana mata sannu kallon sa take hawaye na zubo mata ga kumatu kuka ta fashe da shi sosai tace "wayyo Allah na wayyo Mommy wayyo Hajiya wayyo daddy wayyo kafafuwa na kuka take sosai.


Har cikin ransa yake ji yace "Am sorry Khadeejah kina iya tafiya"!?.

Kuka tana girgiza masa kai duk ya rude da sauri ya dauketa kamar ya dauke jaririya rontsin idanuwan ta tayi ta turo kanta cikin kirjin sa shiga cikin dakin ta yayi saman gado ya daura ta yana mata sannu sannan yace "Am sorry mekike so yanzun"!?.


Girgiza masa kai tayi tana hawaye tace "to ai na koshi wallahi".


Murmshi yayi yace "sannunki kinji Allah ya sauwake bari na kira doctor yazo ya duba k ko da allura ce sai yayi maki".


Kara fashewa da kuka tayi tace "ni dai wallahi bana son allura.


Shiru yayi sannan ya juya ya fita daga cikin dakin falo ya nufa ya zauna saman kujera ya lumshe idanuwan sa sannan ya kira d'aya daga cikin sojojin sa ya turo masa kudi yayo masa shopping .



binsa tayi da kallo sai da ya fita daga cikin dakin sannan tayi ajiyar zuciya tana gyara kwan ce tana jin radadi konewar da tayi mintina 30sai gashi yashigo cikin dakin da sallama hannun sa rike da leda mai zane sai ya rasa me zai ce mata kawai yace "Amma Khadeejah tashi ki sha wannan sannan ya juya ya fita daga cikin daki tashi zaune tayi tana tunani wai yaushe Yaya captain kb ne ya canza ta lura kwana biyu ya canza ko lafiya oho jawo ledar tayi sannan ta bude ayaba da lemo ne acikin da apple sai madara koma wa tayi ta kwanta bacci yayi gaba da ita.




Misalin 3:39 sannan ta falka daga bacci ruwa ta watsa sannan ta gyara cikinta sosai sannan ta dauko rida da skit na atamfa mai ratsin ja da baki kayan sunyi mata kyau sosai sannan ta feshe jikinta da turaruka masu kamshi sosai duk da batayi kwaliya ba tayi kyau sosai sannan fito daga cikin dakin falo ta nufa a hankalin kujera ta biyu ta zauna lokacin babu kowa cikin falon ya fita wayar ta dauko saman d'ayar kujera duba chat din da suke da Ameera tayi voice biyu taga misalin karfe 12:00 pm kun nawa tayi tana sauraro tace " Khadeejah yau saura kwana biyu biki na da Yaya Taheer dan Allah ki shigo please my sister.


Da sauri ta kira ta lokacin Ameera tana zaune da kawayen ta rigging din wayar ta tajiya da sauri ta duba suna my sister tagani dauka tayi tace "my sister dazu nayi maki magana fa.


Ajiyar zuciya khadeejah tayi tace"wai da gaske kike ko wasa"!?.


Ameera tace "wallahi da gaske nake da ni da Yaya Taheer fa sai dai kin zo dan Allah ki fadawa Yaya captain kb please.


To shike nan babu damuwa Allah ya kawo shi lafiya cewar Khadeejah.


Amin ya Allah yayi tafiya ne"!?.


Wallahi ban sani ba kawai ban gan shi ba bata rufe baki ba sai gashi ya shigo cikin falon da sallama.


To gashi nan ma ya shigo cikin falon ina tunani daga masallaci ya fito.


Dariya Ameera tayi sannan tace "ikon Allah ke bazaki tashi kije ki tarbesa ba topa dama haka kuke soyayyar.


Dogon tsaki tayi tace "ban son iskan ci fa to sai anjima kawai.


Da sauri Ameera tace "Afuwa my sister sai kinzo.


Kashe wayar ta tayi tana bata fuska karasowa yayi gurin Khadeejah yace "ya jikin"!?.


Dago idanuwan ta dube sa tace "Alhamdulillah naji sauki".


Zaunawa yayi saman kujera yace "Masha Allah Allah ya tsare gaba.


Amin tace da shi daga nan babu Wanda yace komai haka suka cigaba da zauna tunani take ta ina zata fara tace "Amma dan Allah inaso zanje biki"!?.


Be kalle ta ba Amma yana jin Abun da take fada shiru yayi sannan yace "ke da baki da lafiya zaki ce wai zakije biki to bikin waye"!?.


Idanuwan ta suka ciki da hawaye tace "to ai biki Ameera ne zan tafi.


Kallon ta yayi sama da kasa yace "wai ke yaushe zakiyi hankali ne wai"!?.


Kuka ta fashe da shi sosai tace "haba danAllah kayi hakuri kabari naji daga shi bazan kara zuwa ko ina ba.


Share ta yayi yana jin kukanta har cikin ransa yace "dan Allah kiyi mani shiru please zaki sanya mani ciwon kai.


Da gudu ta wuce dakin ta tana kuka kamar ranta zai fita har bacci ya dauke ta.


Dafe kansa yayi yace "wallahi wannan yarinyar zata sanya mani ciwon ka ko dan taga ni ina tausaya mata ne mtsss aikin banza kawai.



Sai bayan isha'i sannan ya shigo cikin falon Amma be ganta ba sai sai ya fara tunani fushi take da shi fa sannan ya wuce dakin ta koda ya shiga cikin dakin zaune take tayi tagumi da sallama karasowa yayi gurin Khadeejah yace "to shike nan babu damuwa yaushe ne biki.


Da sauri Khadeejah ta dago idanuwan ta dube sa tace "gobe nake so na tafi saura kwana biyu bikin.


Ok babu damuwa Allah ya kaimu Amma kwana biyu kawai zakiyi saboda nima tafiya zanyi.


Da sauri ta rungume sa tace"ina godiya sosai Yaya captain kb Allah ya saka da alkhairi.


Zaro ido yayi yace ""Amin ya Allah to sakeni.


Da sauri ta sake sa wata kunya ce ta kamata girgiza kai yayi yace "to ki hada kayanki da wuri saboda driver zai kai ki.


To shike nan babu damuwa yana fita daga dakin ihu tayi cikin farin ciki tana tsalle tsalle saman gado tace"uhm yau zanyi kwana farin ciki", saukowa tayi saman gado ta dauko akwati kala biyar ta zuba ciki sannan ta rufe.


Washe gari tunda asuba tayi wanka ta gyara sannan tayi masa lafiyayin abinci mai rai da lafiya ta ajiye masa saman dani table wani Soja ne ya shigo cikin falon yace "madam idan kin gyara ki fito muna jiranki.


Kallon sa tayi tace "ok shiga cikin ka dauko akwai na.


ok madam akwatin ta ya dauko sannan ya fito daga falon ita kuma Khadeejah wuce dakin sa da sallama lokacin zaune yake da kayan sojoji yana aiki amsa mata sallama yayi ya cigaba da aikin sa.


Karasowa tayi tace "Yaya captain kb ina kwana"!?.


Lafiya klau har kin gama gyara wa ne"!?.


Eh mana gashi nan har afita da kayana.


Kudi ya dauko yan ban duri ban duri yace "gashi nan kiyi masu tsaraba.


Amsa tayi tace "nagode sosai Allah ya biya"har tajuya sai taji muryar yace" Amma ina tunani daga bari dai kawai ki zauna cikin shiri kawai Allah ya tsare.


Amin ya Allah sannan ta fita daga cikin dakin waje ta nufa koda ta shiga cikin motar sai garin kaduna.



A bangaren Ameera kuwa gobe ne za,a daura masu Aure gida ya ciki da mutane misalin karfe 2:00pm sai wayar Ameera ta fara rigging da sauri ki dauka tace " har kin iso ne"!?.


Khadeejah kuwa tace "eh gamu nan cikin gidan mana.


gudu Ameera ta fito daga cikin dakin ta fito waje mota black ta gani da sauri ta karasowa gurin ta bude mata mota tace welcome back my sister dafatan kinzo lafiya"!?


Murmshi Khadeejah tayi tace " uhm Amarya zamani lafiya klau alhamdulillah.


Wani soja ne ya fito daga cikin motar yace "ina kwana Hajiya"!?.


Murmshi Ameera tayi tace "Alhamdulillah Amma muje daga cikin mana.


Mai gadi yazo nan cewar Ameera.


Da sauri yazo yace" gani Hajiya.


Yauwa wannan sojan da shi da driver zaka nuna ma dakin baki kaji ko sannan suka wuce cikin gidan.


Bayan sun shiga cikin falon sannan aka biyo ta da akwatin ta kawar Ameera ta amsa akwati aka shiga da shi cikin dakin bayan Khadeejah ta gaishe da Mami sannan suka koma daki zaune sukayi Ameera tace "Allah mai iko yau gashi kin zo biki na.


Dariya Khadeejah tayi tace " uhm wannan waye sace zuciyar ki haka ne"!?.


Ajiyar zuciya tayi sannan tace "wallahi nima kai na banyi tunani zanyi Aure yanzun ba ko da yake komai na Allah ne ( littafin Ummu ihsan) kin san ko waye"!?.


Gyara zama Khadeejah tayi tace " Aa sai kin fada.



Bakuwa bane face Suleiman kuma wanda kika sani cewar Ameera tana kallon khadeejah.


Zaro ido tayi tace"Suleiman kuma wanda ya sace ni"!?.


Kwari ma kuwa Khadeejah kin san bazanyi maki karya ba ko wallahi su Mami da Yaya Taheer suka sanya ni gaba shiyasa.



Ajiyar zuciya khadeejah tayi tace "ikon Allah to Allah ya bada zaman lafiya.

Amin ya Allah.


Rigging din

Please Login or Register in order to submit comment