Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kansa yayi yace " *innalillahi wa inna ilaihir raji un* to yanzun menene mafita kusan dole anemota ko yanzun ma haka my love mom tana cikin damuwa sosai fa.


Cikin tausayawa yace "insha Allah za, aganta ku cigaba da addu,a.


A bangaren khadeejah kuwa.


Yau kwana biyar da sace Khadeejah tunda aka sace ta har yanzun bata tashi daga bacci ba wani mutum ne ya shigo cikin dakin da ruwan sanyi dai dai inda take kwan ce ya watsa mata ruwan sanyi wata uwar firgita da tayi da sauri ta mik'e zaune jikinta sai rawa yake sannu ahankali ahankali ta bude baki tace "wai dan Allah menayi maku ne idan akwai abun da kuka bukata to ku fada mani takara she maganar cikin kuka da bakin ciki.


Wani mugun kallo ya bita da shi yace "ga abinci nan idan kina bukata kuma kada ki kuskura bakin ki ya furta fita daga cikin gidan.


Zaro idanuwanta tayi cikin tashin hankali kuka ta kara fashewa da shi ga wani kafurar yunwa da take ji.

Turo mata abinci yayi sannan ya fita daga cikin dakin kuka take mai ban tausaya sosai tana gani ya rufe dakin gaba d'aya.


A bangaren Hajiya kuwa.


Damuwa tayi mata yawa sosai har ciwon zuciya ya kamata a yau ne Alhaji muntaka wato Baban Khadeejah koda ya shigo cikin gidan sai yaji duk hankalin sa be kwana ba karasawa yayi gidan koda ya shiga cikin falon sallama yayi tunda ya shigo cikin be ji motsin kowa ba hankalin sa be kwana ba da sauri ya kara sa cikin dakin koda ya shiga ciki sai Hajiya ce ya hango kwan ce da alamar bata da lafiya.


Da sauri ya karaso kusa da Hajiya yace " Subhanalillah Hajiya lafiya meya ke damunki ne"!?.


Bude idanuwanta tayi tana kallon sa sai ta fashe da kuka sosai hankalin Alhaji yayi dubun tashi sosai yace " Hajiya ko baki da lafiya ne"!?.

Runtsi idanuwanta tayi saboda kuka yaci karfinta girgiza kan sa yayi yace "Am sorry kiyi hakuri ki fada mani abun da yake faruwa kinji "!?.

Ajiyar zuciya take ahankali ahankali sai da tayi shiru sannan ta bude baki tace "Alhaji an sace Shalelen ka"!?.


Wata zufa ce ta karke masa duk Ac da akwai Amman be hana zufa ta zubo masa ba yace "an sace ta kuma yaushe haka ya faru bani da labari"!?.

Muryar ta na rawa tace "yau kwana biyar kenan nima ban sani ba sai da yaro na ya fada mani yanzun haka suna ahanyar zuwa gidan nan bata rufe baki ba.


Bakin su dauke da sallama shigowa cikin falon sukayi kowa yana cikin damuwa sosai part din Hajiya suka wuce ciki koda suka karaso Alhaji ne Zaune ya buga tagumi karasowa su mommy sukayi zaunawa kusa da Hajiya tayi shi kuma ya zauna saman kujera yace "Daddy barka da zuwa dafatan kadawo lafiya"!?.


Ajiyar zuciya yayi yace " *innalillahi wa inna ilaihir raji un* yanzun kai yaro na har yau babu labarinta ne"!?.


Cikin damuwar da su daddy sukayi yace "har yanzun dai daddy babu labarin ta Amman insha Allah za,aganta mu cigaba da addu,a.

Hankalin Alhaji yayi dubun tashi sosai yace " to shike nan Allah ya baya muna ita.


Baki suka hada guri d'aya suka ce "Amin ya Allah.


Haka rayuwa ke tafiya gudu gudu sauri sauri yau Khadeejah watan ta biyu da sace ta su Hajiya sun bar ma Allah komai kullum cikin Addu,oi suke yau kwanan Captain kb biyar da koma wa America saboda Ana neman su da gagawa shiyasa ya koma Amman har yanzun ana neman Khadeejah sojoji kuwa ko ina an zuba su saboda nemanta.


A bangaren khadeejah kuwa.


Kwan ce take tana bacci ahankali ahankali ta fara bude idanuwanta koda ta bude su sai ta wani saurayi Zaune saman kujera ya daura kafa d'aya saman d'aya yana kallon ta yana murmshi.


Da sauri ta tashi Zaune tana kallon sa da mamaki sosai cikin ranta tace "kamar Suleiman"!?.


Bude baki tayi tana kallon sa tace "Suleiman dama kana raye"!?..............

*GA ALKAWARIN KU*πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚


*HASSY SOJA CE*✍🏻✍🏻

*COMMENT AND SHARE*



πŸ§‘πŸ»β€βœˆοΈ *CAPTAIN KABEER* πŸ§‘πŸ»β€βœˆοΈ



*RUBUTAWA*


*HASSY SOJA ce*✍🏻


*MAMA NA DA BABA NA ALLAH YA JIKANKU DA RAHAMA YA SA ALJANNAH CE MAKOMARKU AMIN YA RABBI*😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

```BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM DA SUNA ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN'KAI GODIYA DA AMINCI SU TABBA GA ANNABI MUHAMMAD S. A. W ALLAH YA KARA MASA DARAJA AMIN```



*WANNAN LABARIN NAWA GAJERAN LABARI NE*πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€

*WANNAN NOVEL DIN BA NA KUDI BANE RASHIN COMMENT ZAI SANYA YA KOMA NA KUDI YASIN*

*GARGA'DI*


*BAN YARDA WANI KO WATA YA SU JUYA MANI LABARI BA SAI DA IZINI NA YIN HAKA KUSKURE NE DAN HAKA SAI AKIYA YI*😎😎😎😎


*SADAUKAWAR GA MASOYANA AKO INA KUKE A AFADIN NIGERIA WANNAN NAKU NE*πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»


πŸ…ΏοΈ2️⃣6️⃣%3️⃣0️⃣


*________________*πŸ–ŠοΈ


Bude baki tayi tana kallon sa tace "Suleiman dama kana raye "!?.


Dariya yayi sosai sannan yace "kwari ma kuwa masoyiyata ai dama ban tunda ba ya zama za,ayi na mutu na bar masoyiyata ai bazai taba yuyuwaba ya karshe magana yana kallon ta.


Cikin da mamaki take kallon sa tace " kamar ya ban gane ba"!?.


Gyara zama yayi yace "ai bazaki gane ba tunda har yayanki ya wula'kanta ni saboda ke saboda da haka yanzun za,a daura maki Aure da ni shike nan kuma".


Cikin tashin hankali tace "dan girman Allah ka rufa mani asiri wallahi ban tashi Aure ba yanzun kaji ka fadi duk abun da kake so daddy na zai baka".


'Kwal,'kyale da dariya yayi sosai sannan yace " au kin dauka zanyi rabuwa da ke ne to bari kiji akan ki zan iya kashe kowa saboda ke, ke bar kiji ko mahaifina zanyi kashewa akan ki dan haka ki sanya ma zuciyar ki ruwan sanyi.


Kuka take sosai kamar ranta zai fita saboda tashin hankali har zazabi yaso ma rufe ta muryar ta na rawa tace "Suleiman dan Allah ka rufa mani asiri wallahi ba zan iya Auren ka ba".


Cikin bacin rai ya mik'e tsaye yace "wallahi tallahi ko mutuwa zakiyi sai na Aure ki dogon tsaki yaji ya fita daga cikin dakin da karfin gaskiya ya rufe kofar dakin.


Kuka take sosai babu mai lallashin ta har jikinta ya fara rawar sanyi zazabi mai zafi ya rufe ta.


Captain kb ne Zaune office yana rubuce rubuce sako ne ya shigo cikin wayar sa duba yayi sabuwar number ce ya gani koda ya bude sai yaga _HIMM NA SANI DOLE KAYI MAMAKIN GANIN SAKO NA TO BA, A ABUN MAMAKI BANE NI NE NA DAUKE KHADEEJAH RABIN RAINA DAN HAKA ZAN AURE NAN DA SATI D'AYA IDAN HAR KA ISA TO KADA KATAR DA AUREN MU NI SULEIMAN BY_ tashi tsaye yayi yana maimata sakon yace "lallai Suleiman kai dan iska ne da sauri ya kira daddy lokacin yana Zaune falo kusa da Hajiya ringing din wayar sa yaji daukowa yayi sai yaga yaro na yace "yaro na ya aiki"!?.


"Alhamdulillah daddy yanzun dai abun da yake faruwa shine yaron nan da na kora wanda yake zuwa gurin ta Ashe shine ya dauke ta kuma yace zai Aure ta nan da sati d'aya to kaji sakon da ya turo mani yanzun haka ma".


Cikin tashin hankali daddy yace " *innalillahi wa inna ilaihir raji un* yanzun dama shine ya sace ta Hajiya dake Zaune sai da ta zabura tana kallon sa ya cigaba cewa to yanzun menene mafita kasan dole sai an sanya sojoji ko"!?.


Kwari ma kuwa yanzun dai shine zan turo maka da number sannan zan turo ma yaro na da suke tsaron garin nan sai ayi bincike agano inda yake ".


Ajiyar zuciya yayi sannan yace "to Allah ya taimake mu ya bamu sa,ar kama sa".


Amin ya Allah suka ce.


Kashe wayar sa yayi sannan ya kalle Hajiya da take kallon sa tace "ganta ne Alhaji "!?.


Gyara zama yayi sannan yace "yaron da ya sace Shalele na shine Suleiman din na da yake zuwa gurin ta".


Zaro ido tayi tace "Suleiman kuma d'an dan Alhaji musa mai gidaje "!?.


Kwari ma kuwa dan haka ki cigaba da addu,a insha Allah sai naganta kinji ko"!?.


Ni fa shiyasa ban yarda da shi ba saboda daga gan sa bashi da tarbiya wallahi.


*A bangaren Captain kb kuwa*



Turo ma yaron sa number yayi sannan ya kirasa ya fada masa komai da komai cikin girmamawa yace "insha Allah zamuyi bakin kokarin mu.


Kashe wayar sa yayi yana murmshin gefen baki sannan ya zauna saman kujera ya daura kafa d'aya saman d'aya yana tunani irin wulakancin da zasuyi masa idan suka kama sa.


Bayan kwana biyu da faruwar haka bincike ake sosai har gidan su anji aturo wata dattijor mata ko za,a dace sai dai taji labarin yana kaduna hotel yana hutawa ana take ta kira su ta sanar dasu duk abun da yake faruwa.


*A bangaren khadeejah kuwa*.


Zaune take kamar kullum addu,a take Allah ya fitar da ita cikin wannan dakin bude kofar dakin akayi wani katun mutune ya shigo cikin fuskar sa babu fari,a kaya ne a hannu sa ya jifa mata yace "ki sanya wannan kayan saboda yau ne za,a daura maki Aure da oga kuma kada ki kuskura bakin ki furta bazaki saka ba.


sannan ya fita daga cikin dakin kuka ta kara fashewa da shi sosai haka ta dauki kayan tana kuka ta sanya su duk da tana cikin damuwa sosai be hana fito da kyauwanta ba daure gashinta tayi da ribos bayan ta kamalah sai tayi ta kama zagayar dakin tana addu,a gajiya tayi da yawa guri ta samu sai ta zauna bata fi mintina biyar ba da zaunawa kasa ba sai wani ya shigo cikin dakin fuskar sa rufe karasowa kusa da ita yayi da sauri ta mik'e tsaye tace " bawan Allah lafiya"!? Tana zaro ido.


Bude mata fuskar sa yayi yace "Amma kiyi hakuri dan Allah nazo ne zan taimaka maki saboda kina bani tausaye yanzun ma haka babu wanda ya san halin da muke ciki".


Captain kb ne hankalin sa ya tashi sosai kira waya yake yace "Dan Allah kuyi sauri yau za,a daura masu Aure fa.


Cikin girma mawa yace "Sir yanzun haka muna saman hanyar zuwa inda yake kuma ba a hotel yake ba yana cikin daji zamuyi kokari insha Allah.


Jin jina kansa yayi yace " good " sannan ya kashe wayar sa kiran daddy ne ya shigo cikin wayar sa da sauri ya dauka yace "daddy antashi lafiya"!?.


Alhamdulillah yanzun dai muna saman hanyar zuwa inda yake insha Allah ki cigaba da addu,a Allah ya sa mudace.


Amin ya Allah Allah ya taimake mu ya sa mudace.


Gudu suke shararawa saman titi Khadeejah kuwa ajiyar zuciya tayi tana goge hawayen da suke zubo mata sannan yace "ki natsu sosai ki biyo baya na sai na nuna maki hanyar fita daga gidan nan.


Murmshi tayi ta biyo bayan sa sai ya leka sannan yace "karaso haka suka cigaba da sauri sauri har Allah ya taimake su ya kawo bakin get sannan yace "to kanwata kada ki tsaya ko ina idan kika mik'e sosai akwai titi na sani Allah zai haka ki da nagari ya kaiki gida.


Murmshi tayi saboda farin ciki sosai tace "na....... go.... de..... Sosai Allah ya saka maka da alkhairi.


Amin yace sannan ya jiya ya koma cikin gidan.


Khadeejah kuwa gudu take sosai sai da tayi nisa sosai sannan ta zauna tana ajiyar zuciya tace " Allah sarki Hajiya ta da mommy na da daddy na nasani kuna cikin tashin hankali kuka taci ta koshe sannan ta goge tace " yau insha Allah sai gida.


Lokacin motocin sojoji sun shigo cikin daji da sauri suka fito cikin moton Alhaji kuwa yana nan Zaune yana kallon su zagaye gidan suka sannan suka shiga cikin gidan halben bindiga suke sosai.


Hankali mutane gidan ya tashi sosai koda Suleiman ya bude daki sai yaga babu kowa aciki hankali sa yayi dubun tashi sosai kira mutane gidan yayi gashi hankalin su tashe ciki bacin rai yace "uban waye ya bude ma masoyiyata ta kofar dakin nan ta gudu.


Kowa sai cewa yake bashi bane cikin tashin hankali kuka ya fashe da shi bindiga ya dauko yace "wallahi zan kashe kugaba d'ayan ku be rufe baki ba sai aka ta'ka masu bindigogi soja d'aya shiga cikin dakin kayanta ya gani daukowa yayi yace"Sir ku dube kayanta.


Ogan su ya kalle sa yace "ina ka buye muna ita ka fito da ita kafin mu tafi da ku ya karshe magana cikin tsawa yana kallon sa ".


Kuka yake kamar wani karamin yaro yace "ta gudu wallahi.


Mik'ewa tsaye tayi ta cigaba da tafiya jiki babu kwari sosai haka cigaba tafiya bakin titi ta hango da sauri ta kara gurin ta gaji sosai sai nishi take tafiya take har ta iso bakin titi zata tsalaka bakin titi dai dai wata babbar mota tazo wuce wa ta buge ta Khadeejah ta fadi kasa some kanta ya buge kasa sai jini yake zuba sosai.............



*HASSY SOJA CE*✍🏻✍🏻

*COMMENT AND SHARE*



πŸ§‘πŸ»β€βœˆοΈ *CAPTAIN KABEER* πŸ§‘πŸ»β€βœˆοΈ



*RUBUTAWA*


*HASSY SOJA ce*✍🏻


*MAMA NA DA BABA NA ALLAH YA JIKANKU DA RAHAMA YA SA ALJANNAH CE MAKOMARKU AMIN YA RABBI*😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

```BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM DA SUNA ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN'KAI GODIYA DA AMINCI SU TABBA GA ANNABI MUHAMMAD S. A. W ALLAH YA KARA MASA DARAJA AMIN```



*WANNAN LABARIN NAWA GAJERAN LABARI NE*πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€

*WANNAN NOVEL DIN BA NA KUDI BANE RASHIN COMMENT ZAI SANYA YA KOMA NA KUDI YASIN*

*GARGA'DI*


*BAN YARDA WANI KO WATA YA SU JUYA MANI LABARI BA SAI DA IZINI NA YIN HAKA KUSKURE NE DAN HAKA SAI AKIYA YI*😎😎😎😎


*SADAUKAWAR GA MASOYANA AKO INA KUKE A AFADIN NIGERIA WANNAN NAKU NE*πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»


πŸ…ΏοΈ3️⃣1️⃣%3️⃣5️⃣

*________________*πŸ–ŠοΈ



Mik'e wa tsaye tayi ta cigaba da tafiya jiki babu kwari sosai haka cigaba tafiya bakin titi ta hango da sauri ta kara gurin ta gaji sosai sai nishi take tafiya take har ta iso bakin titi zata tsalaka bakin titi dai dai wata babbar mota tazo wuce wa ta buge ta Khadeejah ta fadi kasa some kanta ya buge kasa sai jini yake zuba sosai..



Dai dai wannan lokacin Hajiya na Zaune taji gaban ta yace dumm dumm dumm jikinta ya soma rawa tace " *innalillahi wa inna ilaihir raji un* waya ta bude ta kira Alhaji lokacin hankalin su atashe kira ringing din wayar sa yaji daukowa yayi duba sai yaga sunan Mommyn Shalele da sauri ya dauka yace "Hajiya".


Baki na rawa tace "Alhaji kun ganta ne"!?.


Ajiyar zuciya yayi sannan yace "Am sorry Hajiya bata gida yace ta gudu.


Kuka ta kara fashewa da shi tace "wallahi Alhaji jikina ya bani tana cikin matsala wallahi gabana faduwa kawai yake ta kara she maganar cikin kuka.


Cikin tausayawa yace " A'a ki daina fadar haka insha Allah tana cikin koshin lafiya.


Wallahi Alhaji jikina ya bani akwai matsala kuka ta kara fashewa da shi.

Runtse idanuwan sa yayi yace " *innalillahi wa inna ilaihir raji un* Allah kayi muna maganin abun da bamu iya ma kanmu ya Allah kasa y'ata tana cikin koshin lafiya.


Kashe wayar yayi yace "inshaAllah za,aganta.


Hajiya kuwa kuka take sosai sannan ta tuna da mommy da sauri ta kira ta lokacin mommy na Zaune ta buga tagumi ringing din wayar ta taji sai ta duba sunan Hajiya taga cikin sauri ta dauka tace "Hajiya an ganta ne"!?.


Kuka take sosai muryar ta na rawa tace "Ba,a ganta ba wai ta gudu ta kara she maganar cikin kuka.


*Innalillahi wa inna ilaihir raji un* to yanzun menene mafita Hajiya"!?.


Wallahi ina ji ajikina tana cikin matsala sosai wallahi mommyn KABEER.


Ajiyar zuciya tayi hawaye na zubo mata tace "zamu cigaba da addu,a insha Allah za,aganta kuma wannan dan iska yaro wallahi sai my son ya masa hukunci sosai yanzun dai kin san baki da lafiya ko"!?.


Ajiyar zuciya take ahankali ahankali tace "Eh mana kuma zamu cigaba da addu,a shi kuma wallahi yarda ya sanya mu kuka shima haka uwayen sa zasuyi.


Hakane Allah ya bayana muna ita.


Amin ya Allah.


Da sauri drivern yaja burki parking yayi ya bude motar ya fito masha Allah dan saurayi ne shima yar uwar sa ta fito cikin motar cikin tashin hankali d'aya ya aza hannuwa saman kai yace "na shiga ukku na Ameera kashe yar India.


Kuka ta fashe da shi da sauri suka Kara sa gurin kwan ce take cikin jini sosai durkusawa tayi tana kallon ta tace "Yaya Taheer mu dauke muje da ita Asibity mana aduba muna ita.


Cikin kankana lokaci ya dauke ta ya rungume Ζ΄ar India cikin mota ya sanya ta sannan yace "Ameera ki shi muje Asibityn.


Da sauri ta mik'e tashiga cikin mota ai kuwa ya ba mota wuta gudu yake shararawa saman titi Allah dai ya kai su lafiya da sauri mai gadi ya bude masu sannan ya shigo cikin asibity parking yayi yana kokarin bude motar sai ga wasu nurse sunzo wuce da sauri Ameera fito daga cikin motar tace "dan girman Allah ku taimaka muna ga wata marar lafiya mun kawo.


Karaso gurin sukayi da sauri sauri ya taimaka masu aka shiga da ita Emergency taimakon gagawa kayi mata Taheer da Ameera hankalin su tashe kallon sa tayi tace "gaskiya ya kamata mu fadawa Mami abun da yake faruwa.


Ciro wayar sa yayi ya kira Mami lokacin tana zaune palo tana karatun jarida ringing din wayar ta taji sai ta duba sunan Taheer ta gani cikin ranta tace "ko lafiya ko dai har sun dawo ne " kiran ya katse kara shigo yayi karo na biyu sannan ta dauka tayi tace "har kun dawo ne"!?.


Cikin tashin hankali yace "Mami wallahi muna cikin tashin hankali wata yar India ce na buge ta da mota yanzun haka muna asibity ya kara she maganar cikin kuka.


Sakin jaridar hannunta tayi tana maimata *innalillahi wa inna ilaihir raji un* to yanzun da sauki ko"!?.


Zayayi magana sai ga doctor ya fito daga emergency ameera tace "doctor ya jikinta"!?.


Cire glass din sa yayi yace "Am sorry gaskiya ta samu matsala saboda kanta ya bugu kasa koda ta tashi bazata gane yan uwanta ba sai ta dauki dan wani lokaci kafin ta dawo normal.


Zaro idanuwan sukayi yace "doctor yanzun kana nufin tayi losing din memory ta"!?.


Kwari ma kuwa sai yanzun bacci take saboda nayi mata allurar bacci zaku iya shiga cikin dakin ku ganta Amma ban da hayaniya please ya karashe magana yana tafiya.


Mami kuwa duk abun da aka fada acikin kunnuwanta tace " Allah sarki yar mutane Allah ya baki lafiya zamu cigaba da kulawa da ke insha Allah.


Koda suka shiga cikin dakin kwan ce tana bacci alamar tana jin ciwo ajikinta zaunawa kusa da ita Ameera tayi tana kallon ta tace "Yaya Taheer kaje gida sai ka gyara sannan kazo da Mami saboda hankalin ta ya kwanta.


Ajiyar zuciya yayi sannan yace "insha Allah bar naje gida daga nan zamu muyo mata shopping.


"Yauwa na sani Mami ya tayo muna abinci kuma akwai nama na da na,aje sa kazo mani da shi dan Allah tana kallon sa.


Jiyowa yayi yace "insha Allah sai nadawo sannan ya fita daga cikin dakin....


Kallon ta take sosai tace "ikon Allah dama India wa na zuwa Nigeria Allah mai iko.



*A bangaren captain kb kuwa*


Duk abun da yake faruwa yaron sa ya fada masa komai da komai yace "wallahi tallahi ko mutuwa zai yi to sai dai ya mutu Amma maganar hakuri babu ta inaso kazo mani da shi america yau yau dina bana so ku bata mani lokaci .


Cikin gamsuwa yace "ok Sir insha Allah yau yau zamu shigo da shi.


Kashe wayar yayi yace "baka san waye Captain kb ba Amma yau zaka gane waye ni lelo yake saman kujera ya daura kafa d'aya saman d'aya.


*A bangaren khadeejah kuwa*.


Taheer ne da Mami cikin mota tafiya suke sosai shopping sukayi sannan suka dawo asibity parking yayi yana kallon Mami.


Budewa tayi tace "muje mana kayi Zaune.


Fitowa yayi daga cikin motar kullon abinci ne ya dauko dai dai kofar dakin yayi tsaye yace "gashi nan Mami bar na amsa waya.


Amsar abincin tayi tace "to shike nan babu damuwa shiga cikin dakin tayi har yanzun bata falka ba daga bacci ba Zaune ta same Ameera tayi tagumi sallamar Mami tajiya.


Amsa sallama tayi tace "Sannu da zuwa Mami bar na baki guri ki zauna.


Kallon yarinyar take sosai tana jin son yarinyar har cikin ranta tace "Allah sarki yarinyar kykkyyawa ce Allah ya baki lafiya zamu cigaba da kulawa da ke.


Zaunawa saman kujera tayi karfe 4:00pm ta fara bude idanuwanta kallon dakin take sosai Ameera ce ta da ke Zaune ta lura da tashin ta da sauri tace "Mami ta bude idanuwanta.


Mami tace "sannu baiwar Allah ya jikin naki"!?.


Da sauri ta mik'e zaune jikinta sai rawa yake sosai tana zaro ido direwa tayi saman gado tana girgiza kan ta tana kuka bude kofar dakin akayi Taheer ne ya shigo cikin dakin da sallama.


Dagowa tayi tana kallon sa da gudu taje ta rungume sa tana kuka sosai.


Zaro idanuwan sukayi yace "Mami lafiya dai"!?.


Kallon kallo suke tace "ta tsorota ne shiyasa tana ta tashi daga bacci.


Rike sa tayi sosai tana kuka hankali sa yayi dubun tashi sosai yace " menene"!?.


Nuna masa take su Mami da ke tsaye kallon su, su Mami suke da ita da Ameera Mami ta fahimci wannan abu tace "tana tsoron mu ne kai ne zaka nuna mata abubuwa saboda yanzun kai ne ta sani tana karashe maganar tana kallon ta cikin tausayawa.


Rike mata hannu yayi yace "insha Allah Mami zo mu Zauna yana nuna mata wuri zama.


Rike take da shi sosai kada ya gudu ya barta zaunar da ita yayi saman gado yayi sannan shi ma ya zauna saman kujera.


Dariya Ameera ta kwal, 'kyale da ita sosai tace " Yaya Taheer yanzun ka zama mai raino hhhh.


Kallon ta yayi da alamar tambaya.


Tace "Yaya Taheer ko da gurin aiki zakaje to tare zakuje kuwa.


Mami tace "kwari ma kuwa kullum sai ka nuna mata abubuwa..


Kallon ta yana murmshi yace "insha Allah Allah ya bamu ladar taimako ...


Amin ya Allah suka ce.


Kallon su take Amma bata gane komai ba gashi tana jin yunwa tace "ni dai wallahy yunwa nake ji..


Zaro ido sukayi da mamaki da al,jabi Ameera tace "kai ke dama ba haushiya ce........



*HASSY SOJA CE*✍🏻✍🏻

*COMMENT AND SHARE*




πŸ§‘πŸ»β€βœˆοΈ *CAPTAIN KABEER* πŸ§‘πŸ»β€βœˆοΈ



*RUBUTAWA*


*HASSY SOJA ce*✍🏻


*MAMA NA DA BABA NA ALLAH YA JIKANKU DA RAHAMA YA SA ALJANNAH CE MAKOMARKU AMIN YA RABBI*😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

```BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM DA SUNA ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN'KAI GODIYA DA AMINCI SU TABBA GA ANNABI MUHAMMAD S. A. W ALLAH YA KARA MASA DARAJA AMIN```



*WANNAN LABARIN NAWA GAJERAN LABARI NE*πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€

*WANNAN NOVEL DIN BA NA KUDI BANE RASHIN COMMENT ZAI SANYA YA KOMA NA KUDI YASIN*

*GARGA'DI*


*BAN YARDA WANI KO WATA YA SU JUYA MANI LABARI BA SAI DA IZINI NA YIN HAKA KUSKURE NE DAN HAKA SAI AKIYA YI*😎😎😎😎

*TO MASOYAN CAPTAIN KABEER GASHI NAN DAI ALLAH YA BANI IKON NAYI MAKU POSTING YAU DA MASU KIRA NA DA MASU MANI MAGANA TA PC NAGODE SOSAI DA SOYAYYAR DA KUKE MANI*πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»



*SADAUKAWAR GA MASOYANA AKO INA KUKE A AFADIN NIGERIA DAK KASASHIN WAJE WANNAN NAKU NE*πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»


πŸ…ΏοΈ3️⃣6️⃣%4️⃣0️⃣


*_________________*πŸ–ŠοΈ

Zaro ido sukayi da mamaki da al,jabi Ameera tace "kai ke dama ba haushiya ce"!? πŸ€”

Kallon su tayi sai ta fashe da kuka sosai jikinta har rawa yake saboda yunwa da sauri yace "to ya isa zaki ci abinci ko"!?.


Share hawayen da suka zubo mata tayi tace "ai tunda zu nake jin yunwa".


Ayyah sorry sister kinji ko"!? Cewar Ameera da ke Zaune

Please Login or Register in order to submit comment