Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ku.



Kashe wayar yayi sannan ya kira doctor mintina 30sai gashi yashigo cikin dakin da sallama karasowa yayi yace "gani Alhaji.




Khadeejah har ta fara fita hayacinta saboda azaba allura doctor yayi mata sannan yace "gaskiya Ina baku shawara kuyi ma ƴar ku Aure idan har kuna son ta daina ciwo nan.




Murmshi daddy yayi yace "ai tana da Aure yanzun dai ga mijinta can kwan ce bashi da lafiya.



Doctor yace "Masha Allah Allah ya basu zaman lafiya gaskiya ina tayaku murna sosai.



Fita sukayi daga cikin dakin wuce wa part din Captain kb lokacin kwan ce yake saman gado yana rawar sanyi shigowa cikin dakin da sallama suka sannan ya duba sa yayi masa allura har da ta bacci sai ya dauke sa.



Ajiyar zuciya daddy yayi yace "Alhamdulillah yanzun dai komai zama normal ko"!?.



Doctor yace "insha Allah hannu ya bashi sukayi musabiha.



Khadeejah kuwa bacci take sosai sai Ameera tace "wai mommy haka take fama da shi ko lokacin da muna tare da ita tana yin sa sosai.


Hakane muna godiya sosai Allah ya saka maku da alkhairi cewar su mommy da Hajiya.



Bayan kwana biyu.


Su mommy da Hajiya da Mami ne Zaune saman kujera suna labari sai ga daddy yashigo cikin falon da sallama.



Amsa sallama sannu da zuwa sukayi masa.



Zaunawa yayi saman kujera yace "wai yaran nan suke"!?.



Mommy tace "suna daki".


Daddy yace "gaskiya ya kamata KABEER ya dauke matar sa ya tafi da ita gida nagaji da zaman da sukayi cikin gidan nan fa ciro wayar sa yayi ya kira captain kb sannan ya kashe ya kira Khadeejah sannan ya kashe wayar sa.



Shigowa Captain kb yayi da sallama karasowa yayi yace "barka ku da hutawa Hajiya.


Murmshi Hajiya tayi tace "yauwa yarona dafatan kaji sauki sosai.




Zaunawa yayi saman kujera yace "Alhamdulillah Hajiya.


Sallama Khadeejah tayi tace " ina kwana ku su Mommy"zauna tayi kusa da mommy .



lafiya klau muke ya jikin na ki"!?.


Alhamdulillah Hajiya cewar Khadeejah .


Gyara murya daddy yayi yace "Alhamdulillah KABEER ka dauki matar ka ku tafi gidan ku na G. R. A ga key nan.


Da sauri Khadeejah ta dago idanuwan ta duba daddy tace "daddy tun yanzun dan Allah kayi hakuri bata karasa ba ya daga mata hannu.


Daddy yace "Aa ƴ'ata bana son musu da ke ni dai Allah ya baku zaman lafiya kiyi masa biyaya duk abun da yace kiyi to kada kiyi musu kiyi abun da yace kinaji ko"!?.


Hawaye ne suka zubo mata ga kumatu kuka ta fashe da shi da sauri ta rungume Hajiya, rungume ta Hajiya tayi tace "kiyi hakuri wannan shine mafi alkhairi da ke yanzun kin zama babbar mace da kin haihu to kin zama uwa kiyi ma mijinki biyaya ki bisa sauda kafa dan Allah kada ki yarda wani yaji sirin ku da ke da mijin ki tashi ku tafi Allah ya baku zaman lafiya.


Tashi tayi tazo gurin mommy ita ma ta rungume ta tana bu buga bayanta tace "kiyi hakuri Auta ta wannan shine gatan ki yanzun ke ba budurwa bace kin zama matar wani wato matar Aure nasanki da tarbiyar mai kyau sosai Allah ya albarkar ce Auren ku.


Tashi yayi ya amsa key sannan yace " muna godiya sosai Allah ya saka maku da alkhairi tashi muje.


Kuka take sosai kamar ranta zai fita daƙwari ta sufa fita tare bude mata mota yayi saman ta shiga tana kuka zagayawa yayi ya shiga sannan yaja motar suka fita daga cikin gidan gudu yake sharawa saman titi kukanta har cikin ransa tsawa ya daka mata yace "dan Allah gafar can ki rufe mani baki kin cika mani kunne da baƙan kukan tsiya mtsss.


Dago jajan idanuwanta tayi tana hararar sa tace "to ina ruwan ka da ni ai wallahi an cuce ni da aka hadi ni da kai mugun kawai kuka ya subuce mata.


Parking yayi gefen titi saboda takaici yace "yasin idan baki rufe mani baki ba sai dai ki fitar mani daga mota.


Ko sauraren sa batayi ba haka tacigaba da kuka sannan tace "wallahi baka isa ba ai ba motar ka bace da zaka ce na fita.



Murmshin mugunta yayi yace "haka kika ce ko"!?.



Eh din wai ina ruwan ka da ni ne mtsss.


Gudu yake shararawa saman titi unguwar G. R. A suka shigo dai dai wani hadaden gida ne mai feenti gree horn yayi da gudu mai gadi ya bude masa shigowa cikin gidan yayi cikin gareji yayi parking sannan ya fito daga cikin motar ko da ta duba ya fita daga cikin motar sannan tace wallahi sai na kuya maka hankali fito tayi cikin gidan tashiga tundaga can ta hango sa zai shiga daki karasowa tayi ta duba gefen dakin green feenti dakin da gudu ta ture sa ta shiga ciki baƙin kofar dakin ta tsaya tace "wannan daki nawa ni kaje ka duba wan can"sannan ta rufe kofa.


Baki ya saki yana kallon ta da mamaki gefe d'aya ya kalla sai ya ga feenti fari da baki ne yace "Alhamdulillah kamar daddy ya sani wan can shine nawa karasawa yayi ya shiga cikin cire kayan jikin sa yayi sannan ya shiga toilet watsa ruwa yayi sannan ya fito daure da towel yana goge ruwan jikin sa jalabiyar sa fari ce ya sanya sannan ya kwanta bacci yayi gaba da sh.



khadeejah kuwa kwan ce take tana kallon sama tana ajiyar zuciya saboda kukan da tasha yau bacci yayi gaba da ita.


Misalin karfe 4:47 pm sannan ta farka tashi tayi ta shiga toilet ta watsa ruwa sannan ta fito bedroom ta bude ta dauko Abaya yellow ta sanya sannan ta feshe jikinta da turaruka masu kamshi sosai duk da batayi kwaliya ba tayi kyau sosai sannan ta fito daki saukowa tayi daga saman bene cikin falon ta karasa gaban ta yace dumm dumm hango shi tayi zaune saman kujera yana kallon tv BBC kamshin turaren ta ne ya dake hancin sa da sauri ya juya suna hada ido ya dauke idanuwan sa ya cigaba da kallon sa.


Karasowa tayi cikin falon zuciyar ta na bugawa da sauri sauri runtse idanuwan ta tayi sannan ta karasa gurin kujera tayi kujera d'aya ce sai zauna tana kallon gefen windo.


Captain kb ya daure fuska yace "ke ki saurareni da kyau sosai kada ki ce ban fada maki ba to daga yau zaki rinka gyara mani daki na sannan kuma ke zaki rinka yin mopping sannan kuma girki kullum da safe da rana da dare kuma bana son ƙazata ko kaɗan sannan kuma bana cin tuwo ko wane irin ne sai shinkafa da wake.


Sakin baki tayi tana kallon sa sai da ya gama fada sannan tace "ikon Allah yanzun kana nufe duk wannan uban aikin nice zanyi sa"!?.


Wani mugun kallo ya aika mata da shi.......



*HASSY SOJA CE*✍🏻✍🏻

*COMMENT AND SHARE*



🧑🏻‍✈️ *CAPTAIN KABEER*🧑🏻‍✈️



*RUBUTAWA*


*HASSY SOJA ce*✍🏻


*MAMA NA DA BABA NA ALLAH YA JIKANKU DA RAHAMA YA SA ALJANNAH CE MAKOMARKU AMIN YA RABBI*😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

```BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM DA SUNA ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN'KAI GODIYA DA AMINCI SU TABBA GA ANNABI MUHAMMAD S. A. W ALLAH YA KARA MASA DARAJA AMIN```



*WANNAN LABARIN NAWA GAJERAN LABARI NE*😀😀😀😀😀😀

*WANNAN NOVEL DIN BA NA KUDI BANE RASHIN COMMENT ZAI SANYA YA KOMA NA KUDI YASIN*

*GARGA'DI*


*BAN YARDA WANI KO WATA YA SU JUYA MANI LABARI BA SAI DA IZINI NA YIN HAKA KUSKURE NE DAN HAKA SAI AKIYA YI*😎😎😎😎


*SADAUKAWAR GA MASOYANA AKO INA KUKE A AFADIN NIGERIA WANNAN NAKU NE*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻


🅿️5️⃣6️⃣%6️⃣0️⃣


*_________________*🖊️
Su Mami ne suka shigo cikin falon da sallama, sallamar Mami ce ya sanya kowa ya juya yana kallon su.


Khadeejah ce tace "ku karaso ciki mana Mami.


Karasowa sukayi sannan suka fara gaishe gaishe zaunawa saman kujera su Mami da Ameera da Taheer sukayi shiru sukayi.


Hajiya ce ta dauko wayar ta ta kira daddy tana gama fada masa ko minti biyar beyi ba sai gashi ya shigo cikin falon da farin ciki sosai kallon falon yayi sai yaga ciki da mutane da gudu Khadeejah taje ta rungume daddy tana kukan farin ciki tace "Daddy na gani nan nayi kewarka Ashe zan kara ganinka "!?.


Rungume khadeejatu yayi sosai sannan yace "Allah sarki y'ata Ashe kina kusa da mu Alhamdulillah Allah kai ne abun godiya.


Su Mami da Ameera da Taheer da Suleiman hawayen tausaye suke basu taba ganin irin wannan kulawar ba sai ga Khadeejah.


Jawo hannuta yayi yace "muje mu Zauna ko"!?.


Daga masa kai tayi sannan sukaje suka Zauna saman kujera d'aya daddy ne yace "Alhamdulillah Allah shine abun godiya Mommyn Shalele kin ga yarki tadawo ko "!?.


Cikin murna suka "Eh gashi nan tazo tare da wandin da suka taimaka mata.


Sai yanzun ya kula da Captain kb Zaune kusa da Hajiya mamaki da al,jabi ya kamashi yace "ikon Allah kai yarona yaushe kadawo"!?.


Murmshin gefen bakin sa yayi yace "daddy nima yanzun nadawo ma, ƙasa ne.


Daddy yace " ina barawon y'ata ne ko yana can kun baro ne"!?.


Khadeejah kuwa jikinta sai rawa yake sosai saboda taji an ce wanda ya sace ta sai taga Suleiman ya mik'e tsaye tace "Suleiman waya kawo ka gidan mu har cikin falon.


Suleiman kuwa jikin sa ya soma rawa yataso durkusawa yayi gaban su mommy da daddy Hajiya yace "kuyi hakuri dan Allah wallahi shairin shed'an da son zuciya yana kuka.


Mommy tace "to shike nan Allah ya yafe mu baki d'aya.


Suka ce" Amin ya Allah.


Suleiman kuwa kuka yake sosai kamar wani karamin yaro tashi yayi yazo gaban Khadeejah, Khadeejah kuwa gaban ta sai faduwa yake rike hannuwa daddy tayi sosai tana kuka Suleiman yace "dan girman Allah Khadeejah kiyi hakuri ki yafe mani sanadin ki na sha wahalar da bantaba tunane zan sha ba ki yafe mani.


Runtse idanuwan ta tayi tace "Allah ya kara maka kai bacewa kayi ba sai ka Aure ni ko mutuwa zanyi ba to yanzun gashi nan an koya maka hankali.


Ameera tace "Himm ikon Allah dama kai ne kayi sanadin bugewar y'ar India tabba yasin da na sani da nayi maka ila kuwa tana hararar sa.


Suleiman kuwa kallon Ameera yake sai yaji kamar ya kama dukanta saboda haushi.


Khadeejah tace "dan girman Allah ni dai ka tashi bana son ganka.


Murmshi daddy yayi yace "A'a bazayi haka ba shike nan kice kinyafe masa tunda ya tuba.


Turo baki tayi tana bu buga kafafuwanta tace "ni dai Uhm uhm uhm uhm uhm uhm uhm uhm uhm bazanyi ba saboda wata rana zai dawo.


Daure fuska Captain kb yayi yace "ke baki da hankali ne kina gaban mutane zakiyi muna abun da kika saba ko"!?.


Turo baki tayi tana hararar sa ƙasa ƙasa tace "Allah ya kara masa.


Dariya mommy tayi tace "A'a fa Auta ta ban sanki da haka ba fa.


Turo baki tayi tace "to shike nan Allah ya yafe muna baki d'aya.


Dariya Hajiya tayi tace " ikon Allah wato sai da mommyn ki tayi magana sannan ikon Allah wannan soyayya haka.


Tabe baki Captain kb yayi yace "ai dama nasani halin ta wai ita Shalele wallahi mommy ke zaki lallata ta da shagwaba mtsss ace mutum ya girma be san ya girma ba.


Murguda masa baki tayi tace "eh din ina ruwanka da ni daga zuwa na sai masifa nima ai nayi masifar tana hararar sa.


Kallon su kowa yake sosai da mamaki.
Captain kb yace "ai shiyasa nace maki baki da hankali yarinya kina abu sai kace wata Babba kuma ni Yayanki ne dole ki bani girma na.


Tabe baki tayi tana hararar sa tace "tabba Allah ya sauwaka ni fa yanzun na wuce da saninka dube sai dan Allah wai ko mata baya da ita hhhh.


Cikin jin haushi yace "haka ne to ai ke ma baki isa Aure ba kin gani ko mun zama d'aya gwarowa kawai.


Dariya Hajiya da mommy sukayi Hajiya tace " sannu ku Tum and jerry kun dawo kenan kowa ya nuna halin sa ku wai dan Allah ko kunyar mutane bakuje ba"!?.


Su har Allah sun manta da akwai mutane acikin falon wata kunyar ta kama Captain kb da khadeejat kamar su shige cikin ƙasa sun kuyar da kan sa yayi yace "Am sorry Hajiya na manta ne.
Dariya suka bushe da ita saboda abun ya basu dariya sosai.


Daddy ne ya gyara murya yace "A'a babu wani idanuwan ku sun riga sun rufe da masifa ne yanzun dama akwai magana mai muhimmaci kowa ya saurane da kyau.


Kowa yayi su gaban Khadeejah yake faduwa sosai da sauri sauri Captain kb kuwa gaban sa yake faduwa da sauri sauri *Innalillah wa inna ilaihir raji un* shine abun da suka maimata wa.
Khadeejah cewar daddy.


Gaban ta yace rasss tunda take da daddy be taba kiran sunata ba sai yau topa Yau magana ce mai muhimmaci zai fada mani bakin ta na rawa tace "Naam daddy.


KABEER cewar daddy.


Gaban sa yace dumm dumm yace "Naam daddy.
Daddy yace "ni waye agurinka"!?.


Sunkuyar da ƙasa yayi yace "kai Mahaifina ne.


Ajiyar zuciya daddy yayi yace "to ina leman wata alfarma agurinka.


Kallon daddy yayi yace "daddy babu wata alfarma da zaka ne ma aguri na narasa baka ni dai kawai daddyka fada mani wallahi Allah ko wuta kace na fada zan fada.


Jin jina kansa yayi yace "to Alhamdulillah"sai ya kalle Khadeejah yace "Khadeejah ni waye agurinki"!?.


Bakin ta na rawa tace "kai mahaifina ne Daddy.


Ajiyar zuciya daddy yayi yace"inda har ni mahaifinki ne to kuma ki dauke ni mahaifinki to na yanke maku hukunci da ke da Yayanki na Daure maku Aure ya din nan.


Dafe kirjinta tayi hawaye na zubo mata bakin ta na rawa tace "Dan Allah daddy kada kace wannan mugun ka Aure mani ni dai ko mai gadi ka Aure mani zan Aure sa Amma dan Allah kaje maganar Aure na da *CAPTAIN KABEER* daddy kara fashewa da kuka tayi jikinta na rawa.


Idanuwan Captain kb sukayi jajaye sosai har zazzabi ya soma rufe sa yace "Daddy dan Allah kayi hakuri tunda bata son zama da ni.


Girgiza kai daddy yayi yace "ke Khadeejah Ashe ban isa da ke ba Ashe akwai abun da zan fada ki nuna mani ban isa da ke ba to shike nan tunda haka kika ce kai kuma KABEER na riga na yanke maku hukunci tunda kayi mani biyaya Allah yayi maka albarka futt ya wuce part din sa.


Tashi Captain kb yayi jikinsa babu kwari sosai fita yayi daga cikin falon kansa kamar ya rabe gida biyu part din sa ya wuce.


Kuka Khadeejah take sosai ta sauri ta mik'e taje gurin Hajiya tace "Hajiya kina jin abun da daddy yace ko kuka take sosai.


Rungume khadeejat tayi tana bu buga bayanta tace ""A'a Shalele na ban san ki da rashin kunya ba kin san daddyn ki be taba ɓata maki rai ba fa kuma ki tuna tun sanda kira jaririya har kika girma duk abun da kike so to shine akeyi agida to yanzun bazaki duba kiyi masa biyaya ba"!?.


Dagowa tayi tana share hawayen da ke zubo mata tace "wallahi na hakura zanyi masa biyaya idan har zai ji dadi sosai farin cikin sa shine nawa bar na bashi hakuri.


Murmshi Hajiya tayi tace "Yauwa Allah yayi maki albarka.


Wuce part din daddy tayi can ta hango sa zaune saman kujera yayi shiru yana tunani da Sallama tashigo cikin dakin jikinta babu kwari gurin sa ta karasa ta durkusa ƙasa tace "dan Allah daddy na kayi hakuri ka daina fushi da ni ni na aminci da da Auren sa zanyi maka biyaya idan har zai sanya ka farin ciki kuma daddy ko wuka kace na dauko na yanke kai na zanyi bale Aure.


Murmshi yayi yace "ni ai bana fushi da ƴata ina alfahari da tarbiyar ki dan haka babu komai Allah yayi maki albarka.


khadeejat tace "Amin ya Allah daddy na to kayi dariya mana cikin shagwaba take cewa.


Dariya sannan suka fito falo yana rike da hannun ƴata suna labari suna dariya.


Su mommy kuwa ba karamin farin ciki sukayi ba Taheer kuwa kamar ya hade zuciyar sa ya mutu saboda baƙin ciki da takaici Ameera ma bata ji dadi ba Amma cikin ranta tace "Allah ya baka wata Yaya Taheer.


Suleiman kuwa wasu hawaye ne suka zubo masa cikin ransa yace "da yanzun ni ne na Aure ta shike nan.... ...



*HASSY SOJA CE*✍🏻✍🏻

*COMMENT AND SHARE*



‍🧑🏻‍✈️ *CAPTAIN KABEER*🧑🏻‍✈️



*RUBUTAWA*


*HASSY SOJA ce*✍🏻


*MAMA NA DA BABA NA ALLAH YA JIKANKU DA RAHAMA YA SA ALJANNAH CE MAKOMARKU AMIN YA RABBI*😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

```BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM DA SUNA ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN'KAI GODIYA DA AMINCI SU TABBA GA ANNABI MUHAMMAD S. A. W ALLAH YA KARA MASA DARAJA AMIN```



*WANNAN LABARIN NAWA GAJERAN LABARI NE*😀😀😀😀😀😀

*WANNAN NOVEL DIN BA NA KUDI BANE RASHIN COMMENT ZAI SANYA YA KOMA NA KUDI YASIN*

*GARGA'DI*


*BAN YARDA WANI KO WATA YA SU JUYA MANI LABARI BA SAI DA IZINI NA YIN HAKA KUSKURE NE DAN HAKA SAI AKIYA YI*😎😎😎😎


*SADAUKAWAR GA MASOYANA AKO INA KUKE A AFADIN NIGERIA DA ƘASASHIN WAJE WANNAN NAKU NE*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻


🅿️6️⃣6️⃣%7️⃣0️⃣


*_________________*🖊️

Wani mugun kallo ya aika mata da shi yace "wasa nakeyi da ke ni ko na taba wasa da ke to bar kiji wannan gidan ba gidan hutawa bane aiki dole kiyi sa kuma ko da wasa kika fadawa su mommy da Hajiya wallahi sai na kakarya maki kafafuwa na cire maki hauru.


Kuma sannan na bindige ki shike nan ki mutu babu ruwa na afusace ya fita daga cikin falon sai masallaci saboda lokacin sallah azzhur yayi kuka Khadeejah ta fashe da shi tashi tayi ta shiga kitchen kayan tagani green masu kyau sosai tsaye tayi tana kallon su komai ya buge ta.



Buhuhuwa shinkafa tagani da taliya da wake da indomie komai akwai kuna gs tayi ta daura ruwa acikin tukunya sannan ta rufe wake ta debu ta gyara sosai sannan ta wanke sa ta zuba wanken cikin ruwan kanwa tazuba ciki da maggi minti biyar sai tukunya ta tafasa shinkafa ta wanke ta zuba sannan ta rufe fitowa tayi tana tunani ina zataga yaji dawowa kitchen tayi sai ta bude wata loka can ta hango sa daukowa tayi tace "yauwa bar na gyara yajin kafin nagama girki.


Taushi da maguguna da kayan kamshi daka shi tayi sosai sannan ta zube sa cikin yar ruba ko da ta duba shinkafa tayi sannan ta dauke ta zuba mai guda sannan ta soya bayan ta kamala ta kashe gs sannan ta zuba shnkafa da wake cikin kula ta rufe dauko kular tayi ta kawo masa falo ta ajiye sa kowa ma kitchen tayi ta dauko yaji da mai suma ta kawo falo ta ajiye masa.


Dakin sa ta wuce ta gyara sosai sannan ta fito daga cikin dakin zata wuce part din ta sallamar sa tajiya amsa masa tayi Amman bata kalle sa ba dakin ta ta wuce ta gyara sosai sannan ta shiga toilet ta watsa ruwa sannan ta fito da daure da towel tana goge ruwan jikinta riga da wando ta sanya sannan ta feshe jikinta da turaruka masu kamshi sosai duk da batayi kwaliya ba tayi kyau sosai sannan tayi kwan ceyar ta daki tana tunani duniya.



Captain kb kuwa koda ya shigo cikin falon kamshin turaren wuta mai dadi yake falon zaunawa saman kujera yayi yace "washii bar na kira Hamza ko yaushe zamu koma.


Koda ya duba sai taga kular abinci da kwai da kayan miya da yaji da mai kallon kayan yayi sosai tabe bakin sa yayi ya kira hamza yace " hello yaushe zamu koma america"!?.


Hamza yace "Sir kai da kayi Aure ka bar kagama cin amarci sannan.


Cikin bacin rai yace "wai kai hamza yaushe na fara wasa da kai ne"!?.


Hamza yace "Sorry Sir bazan sake ba insha Allah.


Kashe wayar sa yayi yana kallon tv BB kwala mata kira yayi yace "ke yarinya kina ina ne"!?.


Kwan ce take tana kallon sama kiranta taji anayi da sauri ta fito daga cikin dakin ko dankwali babu saman kanta karasowa tayi ta duba gefen ta bata komai ba har zata juya sai taji yace "wai ke bada ke nake ba ne "!?.


Hango sa tayi zaune saman kujera ya daure kafa d'aya saman daya fuskar sa babu rahama karasowa tayi tace "gani.


Captain kb yayi kamar be ganta ba sai da tayi mintina 30sai yace "kina nufe me"!?.


Cikin rashin fahimta tace "kamar ya fa"!?.


Harara ya aika mata da ita yace "ban sani ba wai ke yaushe zakiyi hankali ne wai"!?.


Turo masa baki tayi tana kallon kasa kasa tana hararar sa tace "ni wallahi ina da hankali na"!?.


Duk abun da take yana kallon ta ta gefen idonsa murmshi yayi yace "sannunki da hararar ta kinji".


Da sauri Khadeejah ta dago idanuwan ta dube sa tace "yaushe kuma na harare ka"!?


Karya zanyi maki kenan ni dai kizo ki zuba mani abinci.


Jiki babu kwari haka ta durkusa kasa ta zuba masa abinci ta mike masa sannan ta zuba masa lemon juice tace "to gashi nan" har ta mike zata wuce sai taji yace "kina nufe ni zan cinye wannan abinci ko yaya"!?.


Bata fuska tayi tace "ni fa na koshi wallahi kuma ai kai kace na zuba maka"!?.


Tsawa ya daka mata yace "zauna ki fara ci saboda kada ki zuba mani guba naci na mutu maza ci abinci nan"ya daure fuska.


Jikinta har rawa yake sosai kuka ta fashe da shi tana cin abinci kamar tana cin magani luma biyu tayi dakar da sauri ta mike da gudu ta wuce dakin ta tana kuka binta yayi da kallon ya tabe baki ya cigaba da cin abincin sa.


*A bangaren Suleiman kuwa*


Koda ya koma gida daddyn sa kawai ya isko kuka yake sosai yace "daddy Ashe akwai abunda zani nema na rasa samun sa Ashe duk abun da nake ba dai dai bane to yanzun na gane gaskiya.


Kallon sa daddyn sa yayi sannan yace "my son ina kashiga cikin duniyar nan munyi nemanka amma bamu samu labarin ka ba.


Labari ya fara bashi tun daga farko har karshe yace "yanzun nayi nadama kuma insha Allah bazan kara ba.


Cikin jin dadi daddyn sa yace "Alhamdulillah Allah mungode maka da kagane gaskiya to yanzun sai kane ma matar da zaka Aure shike nan nima son naga jikana.


Share hawayen sa yayi yace "insha Allah kacigaba da yi mani addu,oi Allah ya bani tagari.



Amin ya Allah cewar daddy.


kwana biyu da faruwa haka kwan ce yake saman gado yana bacci mafarki Ameera yake suna zaune gefen ruwa suna soyayya har da Aure da sauri ya tashi zaune yana mamakin mafarkin sa dafe kansa yayi yace "Alhamdulillah yanzun dai ita zan koma wa Allah ya sa ta soni.


Tashi yayi ya shirya cikin manya kaya kamar wanda za, a daure wa Aure ya sha kyau sosai fitowa yayi falo daddy ne ya iske zaune yana karatun jarida gaishe da shi yayi sannan yace "daddy zan shiga cikin gari.


Washe baki yayi yana jin dadi yaron sa ya shiryu yace "Alhamdulillah Allah ya taimaka ya sa adace.


Amin ya Allah cewar Suleiman.


Fita yayi daga cikin falon sai gurin da motoci ya dauke d'aya daga cikin motoci ya shiga ya fita daga cikin gida.


*A bangaren Taheer da Ameera kuwa*


Bayan sun koma gida komai yana tafiya lafiya klau kullum sai Ameera tayi waya da Khadeejah da kuma kawarta maryam har tace zata shigo.


Zazzune suke saman kujera da Mami da Ameera kallon ta Mami tayi tace "wai lafiya kwana biyu da ke da Yayan ki sai ahankali wai me yake faruwa ne"!?.


Ajiyar zuciya Ameera tayi tace "ni kai

Please Login or Register in order to submit comment