Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nasa yaji dadi yace


"To Allah ya tsare ya bada abin da aka je ne ma,

Amin suka ce ban da sitti da zuciyar ya ke a tunzure yama raina mata hankali tana magana yayi kunnan uwar shegu

Abba yace


"Zuwa ina?,

Ƙasa da kai tareek yayi yana jin wani ɗaci a zuciyarsa jine ya gangaro ta hancin sa da sauri jameel ya ɗauko mai tissue sai dai be ƙarɓa ba ya ɗauko farin
handkerchief ya goge sosai hankalin abba ya tashi yace

"Sannu Allah ya baka lafiya,


Runtsai idanuwansa yayi yace


"Amin Palestine zamu an aika mune a gun aikin mu,


Da sauri sitti tace


"Wallahi baka isaba so kake ka maida min da jika ƙaramar bazzawara to wallahi a hir ɗinga sai tasa kuka yanzu Ubaidu kana gani ɗanka na cimun mutunci kayi shiru wane besan cewa gun nan ko tsuntsu ya huce sai sun kashe garin yan ta'adda amma kai shiru ga hukuma da yazo ya zube min a gida,


Cikin ladabi yace


"Ji haƙuri sitti kinga ga yace agun aikin sune sannan zan sa ya ɗauke su,


Majina ta fyece tace


"Wallahi yaron ne me zuciyarsa kafuran farko ya rainani wannan Allah ne ya ragewa aya tsaƙinta be fito a arne ba yaro yawa jikokin Bature ko da yake inji ke juyashi ba mamaki dan yana da taurin zuciya,


inda take tareek be kallah ba be ma nuna mata yasan me take faɗi ba ya tashi yayiwa abba sallama mama Amina tace


"Amma tareek ka ganmu ko ai wani kallo da ya jefa mata sai ta nutsu domin tasan ƙaramin aikin sane ya fara hulli da duk kayan da yaci karo agarin haka kwanaki yayi mata karaya in abin nasa ya tashi yawa zaki yake komawa

fita yayi cikin sarsarfa Muhsin jameel ya ƙiran sa ya kai su airport filin tashi da sauka na malam aminu kano international airport tuni jirginsu ya tashi sai Palestine Muhsin ya dawo da motar gida



*_________BABA GANA ƘYARI FAMILY*



knocking ya Shiga yi cikin hausar ta mara fita tace


"NUR bana faɗa miki ba zan fito shine kika dawo,

gyaran murya babah yayi yace


"Ummin nur nine,

Jikinta a sanyaye ta taso ta buɗe kallo yabi ta dashi bayan ta matsamai tace


"Múndú máá,

shigowa yayi ya zauna cikin sakin fuska yace


"Yauwa Kú fárá ndá?,

murmushin karfin hali tayi cikin kulawa da soyayyar mijinta kuma uban ya'yanta tace


"Ndá kú sírè,


rungume ta yayi yace


"Kalmtum kiyi haƙuri kinji komai yayi zafi maganin shi Allah kamata yayi ki manta da abin da ya faru ko dan lafiyar ki,

Kuka tasa tace


"Yauwa naga ahalinsu kuma me kama dashi sai ta ƙara fashewa da kuka,


da kyar tayi shiru yace

"Wanke fuskar ki muje floor yaran duk sun damu,

tashi tayi ta shiga toilet murɗa fanfon sink tayi ta wanke fuskarta da showar jel me daɗin kamshi fitowa tayi tasa towel ta goge fuskarta ta dansa power dariya yayi yace


"Wow kin yi kyau,


Murmushi tayi hannunsu asarke da juna suka fito da sauri nur ta rungume ta tasaki kuka ummi tace



"Ki shiru dan Allah ai na fito kaina ne yake ciwo,

Nur tace


"To Allah ya baki lafiya,


Amin tace


Zama sukai azizi yace


"Ku tayani murna yau andawo da king of journalists kula da lafiyar sa ta dawo hannuna hakan ba ƙaramar nasara bace a guna na zama consultant doctor insha Allahu zan kawo karshen matsalar sa,


Murna suka taya shi ace zai duba mutun kamarsa yace


"Wallahi ummi jinsa nake kamar dan uwana ina jin tashin lafiyar sa ajikina,


Baba yace


"Allah yasa ya sami sauki,

Amin suka ce

Aeesar yace


"Kasan ɗazu mun haɗu da shi ina sane na faffadamai magana wallahi girman kai ne da shi,


Saurin dagowa aziz yayi yace


"Daman kai katada mai da ciwonsa gaskiya aeesar baka kyauta ba yana gudun mutane ne saboda ciwonsa da kuma gudun bakin jama'a,


*Zuciyar ummi ce tayi wani irin bugawa ta dafe kirjinta tace.....✍️*




*🌹 Perfectly Pen's ✍️✊*


*Our Ongoing Book's...✍️*

*1_SHIRYAYYIYAR ƘADDARA.*

*BY: Queen Kainaat.*


*2_RANAR BIYAN BUƘATA.*

*BY: Nainarh KD Nkd's.*


*3_DESTINY LOVE.*

*BY: Oum Yasmeen.*



*Mun Shirya tsaf domin kawo muku daɗaɗan littattafan mu masu cike da ilmantar wa faɗakarwa tunatar wa wa'azantar wa har ma da Nishaɗantar wa.💝*



*🔥Kada ki bari wannan tafiyar ya kasance ba tare dake ba. Don't Miss It Dearest sisters 🔥*




*DESTINY LOVE*


*OUM YASMEEN*



*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*


*PERFECTLY PEN*


*Ina ganin saƙon fatan alkairi ina godiya Allah ya bar zuminci*

https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k


Episode 18 *י"ח (Yod Chet) to 19י"ט (Yod Tet) "Tet-Shei" (ט-שי).*


Ta buɗe baki kenan za tayi magana wayar ta tayi ringing ɗauka tayi ta bar gun domin amsa kirana kafin ta dawo Aziz yabar part ɗin ta ya tafi nasu zama tayi akan luxury sofa ta zuba ta gumi ji tayi na zare mata hannu dago idanuwanta ta kalle sa murmushi ya sakar mata yace



"Ummin nur har yanzu wai yau she zaki dena wannan da muwar ne? wai yau she komai zai zamar miki jiki ne Please i begging you ki dena sawa ranki damuwa narasa yanzu me kike buƙata kin rabu da shi to wannan a bu zaki tuna na bakin ciki da ya faru a baya babu,

shiru tayi tana sauraran sa tabbas abin da ya faɗa gaskiya ne amma me isa wani lokaci ake damuwa da halin da yake duk kuwa ƙoƙarinta na tamanta da shi cikin rawar murya tace


"Insha Allah zan dinga kawar da maganar araina,

Tashi yayi yace


"Ko kefa ai haka nake so zo ki hada min ruwan wanka,

dafe kanta tayi tace


"Kaga shaf na manta da wannan dan Allah kai hakuri,


Murmushi yayi yace


"Bakomai babbar likita guda nasan sha'afa kikai Dr,

A kullum son mijinta ƙara huda zuciyarta yake dai dai da rana daya beta ɓa faɗa mata abin da ya shafi rayuwar ta tabaya ba yayi mata guri *Dr shattima Baba gana ƙyari* consultant dr abangaran. *neurology clinic* duk wata nasara da tasamu tofa sanadin sane



*QUEEN ALIYA INTERNATIONAL AIRPORT JORDAN*


Jirgin su acan ya sauka saboda *Yasser Arafat international airport baya aiki yanzu* shine airport ɗin palestine gama checking ɗin kayan su aka ƙarayi da duba biza ɗin su bayan sun fito wayar sa ya ɗauko ya fara duba internet domin binciken hotel mafi kusa da inda suke tunda a yanzu dare yayi baza su iya zuwa Palestine yanzu ba doba da yaƙin da suke ciki cin karo yayi da


*Kempinski Hotel Amman Jordan*

Ganin irin tsarin su tarar taxi yayi ya fada mai inda zai kai shi tuni mutumin dan ƙasar Jordan ya fada mai kudi da zai bashi shiga sukai inda ya bida su ta

Abdul Hamid Shouman Street,

Har hotel ɗin kuɗin suka bashi kallo daya zakai wa hotel ɗin kasan luxury hotel ne jameel yace


"Tareek hotel ɗin nan daga gani zai kuɗi,

kallon sa yayi yace


"Uhmm na riga nasai ticket a website ɗin su na biya komai,

Kai jameel ya daga mai kai tsaye reception suka nufa key aka basu da number dakin wani mutun ne ya raka su suna shiga ya ajiye travel bag ɗinsa yar gidan Louis Vuitton

ya nemi gu ya zauna akan luxury bed ɗin dakin jameel kuwa toilet ya shiga domin yayi wanka yayi alwala yayi sallah dan jin ana kiran sallah isha da yake garin musulmai ne arnan basu da yawa


wanka yayi ya ɗauro alwalah bayan ya fito tareek ya shiga fitowa yayi ɗaure da towel Jin na knocking bell kallon

jameel yayi sai akai sa'a jameel ɗin shima shi yake kallo dan karamin tsaki yaja ganin jameel beje ya buɗe ba dariya sosai jameel ke kunshe wa cikin dan daga murya yace


"Am nace ango an bugon ƙofa jika ka buɗe ko amaryar yace ta biyo mu saboda in kai zaka iya jurewa ita ba lalle ta iya ba,

takaici ne ya turnuke tareek jura jallabiya yayi ya buɗe asalin dan ƙasar Jordan sa'eed m hammad ya miƙo mai basket food karɓa yayi yamai godiya

a kan Centre table ya dubi jameel yace


"Anya kuwa wannan zan iya ci jibi fa abinci?,

Wani shegen murmushi tareek yayi ya ɗauke kai dayan plate ɗin ya buɗe wata takar da ya gani bayanin abincin abin da yaga ansa

Falafel an hada shida chickpeas sai Fattet Hummus ganin duk basu da wani tashin hankali zai iya ci ya dubi jameel yace

"Kai ɗauki wannan saboda Ni ba dan chaina bane ba zanci shi ba kai ina ga zaka iya ci,

ya nuno mai wani Warak Enab and Kousa Mahsh anyi hada shi da

stuffed grape leaves and zucchini, filled with rice and ground meat kallon sa yayi yace


"Tom shikkenan aini kasan daga chaina kagan ni ka ɗauko ni,



Prayer mat ya shinfida ya tada kabbarah ganin abin da yayi ya saki wani murmushi ya bude ya ɗibi rabi ya barmai ga wani hadaddiya juice zama yayi yaci ya ko shi sannan ya shiga toilet lokacin kuma tareek ya idar addu'a yayi sosai sannan ya janyo basket food ya fara zuba abin da zai ci kaɗan ya tsakura ban yayi mai rashin dadi ba a'a sai dan haka yake

bayan ya gama ci ya wanke bakin sa ya sa pyjamas farare tas da su system ɗinsa ya janyo domin insha Allah bazai huce sati biyu ba zai dawo so yake yayi abin da zaiyi ya gama yabar ƙasar tsaki yaja ganin jameel ya fara wannan shegiyar wayar tasa dan dagowa yayi ya zare medical glasses ɗinsa yace

"Malam ka ishe nifa,

dan zare wayar jameel yayi daga kunnen sa yace

"Uhmm baka san dadi soyayya bane shiyasa kake faɗin haka in baku gaisane?,

cikin gatsai yace

"A'a babarta zaka bani mu gaisa ba ita ba,

Cikin tunzura shi yace


"Dan Allah ai kuwa ina da number ta ,

Tsaki yaja ya ɗauki system ɗinsa ya koma floor

*KANO ZOO ROAD*


Sai Safa take na mawarwa wani irin takaici ne ya tukare mata zuciya Bily da sauri ta ɗago ta dubi wacce ta shigo zama tayi a daya daga cikin kujerun da aka tanadar domin zaman customer yace


"Bily tunanin me kike haka?,

Wacce ka kira da bily ta ci abaya milk colour an ammata ado da golding stone anmata kalbar attachment kana kana ta zubo su a jiyar zuciya ta sauke tace


"Na rantsai da Allah akwai tashin bama bamai nucy wai safna ita zata ha'ince ni,

wacce ka kira da nucy ta ja tsaki tace


"ba daman na fada miki yar akuya ce ba kin kasa fahimta ba dai tayi aure ba to wallahi sunan auran matatce,


zama tayi tace


"Nucy ai ko baki faɗi haka ba daman sunan sa kenan amma sai na nuna mata darasi wallahi ,

dariya nucy tasaki ta ajiye jakar ta ta ciro wata kwalba ta bude ta sha sannan ta mai da ta rufe tace


"An bamu kwangila amma fa akwai hatsari sosai,

Gyara zama tayi domin jin bayanin kawarta ta ba ko sallama babu wani matashi ya shigo yace


"Hy guys,

Bily ce ta tashi tsaye tace


"Tafida kazo a daidai lokacin da nake tsananin bukatar ka wallahi wallahi wallahi sai dai kowa yayi prison,

kallon tara saura kwata yayi mata yace


"To yar bala'i lafiya kike mana baƙin fata,


Idanuwanta ne suka kaɗa sukai ja bakin ta na rawa tace


"Tafida nucy wallahi inban same shi ba mutuwa zanyi,

Tsaki tafida yayi domin sunsan ta tsuneyar gizo ba ta huce ta koƙi yace


"Amma ke anyi jaka wallahi yanzu haka kike cewa zaki tona kinsan dai gidan yari ba gidan ubanki bane ko ?,


sulalewa tayi a ƙasa abin duniya ya ishe ta sun kasa fahimtar ta tabbas ta yarda da cewa so ƙaddara ne duban su tayi tace


"Ku tashi zan rufe shagona,


Nucy ce ta matso kusa da ita tace


"Haba my friend gaskiya tafida ya fada miki ke kinsan hukuncin mu yan zuma wani aiki na kawo muku in zaku yi,

zama tafida yayi ya washe baki yace


"Allah nucy amma fa ba irin waccan ba domin wallahi sai bayan nayi nake dana sani,

Tashi tsaye tayi ta kama ƙugu ta dafa shi tace


"Bukatar maji hajji sallah kasar nan da kake gani wallahi kuɗi sune rayuwa tafida ko ita wannan jakar saboda ganin family ɗinsu na da kuɗi shiyasa tayi haka amma wallahi inta san wata bata san wata ba ba'a shiga gona ta in kƴale saina da tsai kafafun mutun sannan in fasa kwai duk wacce za ai saidai ayi,

Murmushi tafida ya saki hannu ya bata suka tafa suka saki shewa bily kuwa tun dazu tana zaune tana ji me suke faɗi amman fa wallahi shirinta yafi nasu kwantanɓauna zata yi musu


*BN NADER FAMILY*

1:30

Dare ne ya tsala baka jin motsin kowa sai na tsuntsaye a hankali take sanda har ta sami nasarar fita daga shashinsu kai tsaye gun masu gate ta nufa kuɗi ta ciro a jakarta ta basu nan da nan suka buɗe mata ƙofa wata baƙar mota ce tun dazu tana tsaye tana jiranta da sauri ta shiga akuje motar ta fisga har suna kokarin bugewa Allah ya rufa a siri sai da sukai tafiya meni sa sai gasu a wani kata faran gida horn sukai me gadi ya buɗe

parking yayi ta fito tana sanye da mini skirt da armless kirjinta duk a waje ga wani uban takalmi da ta sa fitowa yayi daga shi sai boxer sai wata t-shirt ga uwar sarka a huyansa shiga ciki sukai ba me magana kowa sai huci yake wata hamshaƙiyar mace ce tana sanye da strength gown sai taunar chingum take tana kar kaɗa ƙafa juyowa tayi ganin sun shigo budurwar da ta fito daga family ɗin nan ta sami gu ta zauna saurayin nan kuwa fita yayi ya jawo musu kofa cikin isa wannan hamshakiyar matarnan tace......




*DESTINY LOVE*





*AREWABOOK@oumyasmeen*



*Episode 20-30*




*___________________________*




tashi tayi ta juya baya tace


"Ƙar ki sake a haɗa abiki dake a cutar da shi wallahi in hakan ta faru baza kiji dadi ba ,

A dan har zuƙe safna tace


"ke wacce da har zaki dinga shinfiɗan doka,

Ƙas tayi da chingum ta saki kwai yace tush tace


"Au allah doka ma nake kafa miki ko ki sake inji wani abu ya faru da shi wallahi saina fasa bara gurɓin kwai da kuka ajiye kowa yaji warin sa ,

Da sauri safna ta ɗago ta kalle ta saidai me har ta shiga ciki tsaki safna ta ja ta miƙe ta fita a waje ta sami wanda ya ɗauko ta buɗe mirfin mota tayi ta shiga shima shiga yayi domin ya mai da ita gida yace


"me tace miki?,

tsaki taja tace


"Waini wannan tsohowar kilakin zata yiwa bara zana me ta ɗauki kanta ne ?,


ɗauke kansa yayi ya maida kan titi yace


"Hmm a zuri zuwa rafi wata ran tulu zai fashe ,


Cikin rashin fahimta tace


"Nazeer me kake nufi wallahi basa hannu na hassalima ban san wanda ya kashe bahijjah ba me tayi min da zan kashe ta?,


yan sanda ne suka tsare motar su suka hasske su da ƙatuwar fitilah ɗan dube dube sukai sannan suka sallame su godiya tayiwa Allah sauke ta yayi ta shiga gida kai tsaye shashin sitti ta shiga samin sitti tana kai wa tana komowa tana ganin safna tace


"bar san ɗannar dan uba ...ki ina kika je?,

da sauri ta ɗago agaban ta na tsananta bugu inda inda ta fara cikin ɗaga murya sitti tace


"Da kata safna da auran ki kina fita tun yau she kika fara fita kinsan irin shirin da nayi har wa yancan hukumar suka bar gidan nan anya kina so auran ki da tareek ya ɗore?,



Zama tayi tace


"Sitti ki hakuri,

kai sitti ta girgiza ta shiga bedroom ɗinta


wata gigi tatciyar ƙara su kaji karar da ta ɗinga amsa kuwa a estate ɗin abin ka da dare da sauri safna ta shiga ɗakin sitti akan gadon sitti ta zauna tace


"Wallahi sitti lamarin gidan ya fara ban tsoro ko baki ji abin da naji ba ,

sitti da tun ɗazu cikin ta ke murɗawa anya kuwa gidan lafiya yake lamarin fa ya fara huce gona da iri a kullum karar nan daɗa matsowa take tashi tayi ta ɗogara sanda ta nufi toilet tana shiga

ƙofar toilet ɗin ta rufe tana ta kawo huta kala kala tana ɗauke wa ihu take ba me jinta gashi ta rasa hanyar fita

safna kuwa ihu tasa Sultan ne ke tsaye a gabanta ɗakin yayi duhu bata ganin komai sai Sultan kuka tasa amma ba me jin ta can kuma abin ya lafa komai ya dawo dai dai kamar an hur go da sitti haka ta fito kallon safna take da jikinta duk duka kallon kallo a ka shiga tsakanin sitti da safna kowa da abin da yake saƙawa sun kasa magana gumine ya wanke sitti an kashe Sultan wata ranfa abin nan kanta zai dawo tabbas dole ta takawa abin birki


*Shashin mom hafsa*



Cikin bacci ta ji futsari ya matsaita buɗe ido tayi ido hudu sukai da Sultan ƙara ta kwallah ta fara tashin mijinta Abdulkarim ko motsi be ba ihu take ji tayi an fella mata mari cikin tsawa yace


"Ja bakin ki kiyi shiru,


Ruƙe bakin ta tayi da hannunta batt ya ɓace tashi uncle Abdulkarim yayi yace


"Lafiya nake jin wari ?,

Zaro ido momhafsa tayi ƙara mai maita tambayar sa yayi cikin rawar murya tace


"Kashi nayi wallahi yau ido hudu nayi da sultan,

Tsaki uncle Abdulkarim yayi yace


"Nasifa anya kuwa lafiyar ki kalau ki rasa a inda zaki yi sai a nan har da futsari?,


Hawaye ne ke sunturi a idanuwanta shi tayi fak a fuskarta ihu tasa agigice haushi ne ya kama hanya uncle Abdulkarim ya tashi yace


"Wallahi ki gaggawar gyara gun nan ɗakin ya bari ya koma nasa momhafsa kowa ta shin hankali take ciki kafin safiya ta ci uban duka hafsa ce shigo hannunta ruƙe da waya ga earphone a kunnan ta da sauri ta ƙara sa gun mom ɗinta tace


"innalillahi mom lafiya?,

kuka mom ta fasa tace


"Hafsa ina cikin tashin hankali jiya fatalwar Sultan ce ta zomin Wallahi ita duk tayi min haka,


tunanin Hafsah ta shiga yi tace


"Mom fatalwa kuma kai haba wannan duk zancan kune ai wannan camfine bara inje in kira sitti,

bata jira me zata ce ba ta tafi kiran sitti sallam tayi jin shiru ta ƙarasa bedroom ɗin ta me zata gani ganin su tayi duk sun zuba ta gumi jikin safna rudu rudu da duka cikin sauri tace


"Sitti me ya sami safna?,


Harara sitti ta watsa mata tace


"Uwarki ce ta same ta ,


Bakinta ta taɓe tace


"Sitti ga mom dinna can ba lafiya wai fatalwar Sultan ta gani ai bata ƙara ba ta tuntsure da dariya ganin su sitti sai zare idanuwa suke

Ta shi sukai sai shashin mom hafsa ganin yana yin da safna take mom hafsa tace


"Kuma tazo muku ne?,


zama sitti tayi ta lula duniyar tunani kar fa agoge ya mai maita kansa tab akuwa akwai matsala bayan anyi sulhu da su momy amina ce ta shigo da yake hafsa ta faɗa mata tace


"Sitti ga wani shirme da hafsa take sheda min wai fatalwar Sultan ta dake aunty nafisa da safna?,


ɗago ido tayi ta kalli momy amina tace


"Usaina nima nan bata kyale niba wallahi daman tun da aka haifi yaran nan nasan ba mutun bane dan Allah jibi idonsa kamar yana gani tar amma baya gani,

hannu hafsa ta sarke ta jingina da bango tace


"Haba sitti kuma yawa wasu hajilai aljanune suke so suhi wasa da tunaninku amma wacce fatalwa zancan rashin ganin Sultan daga Ubangijin ne bayarda baya iya yi ,

Ahar zuƙe safna

"Da halla can rufen mana baki ke kin kuwa san ido biyu mukai da Sultan kema Allah ya nuna miki fiye da abin da muka gani,


Ganin sunyi nisa basa jin kira tabar ɗakin ta nufi nasu da yake ɗakin yan matan gidan yana shashin aunty aysha dakine ƙato kowa da gadon sa da yake yau talata duk sun tafi makaranta sai ita da basma da sun gama zana jarabawar shiga aji uku na secondary wato a.s.s


tana shiga tace


"Basma kinji wani zance wai fatalwa ce tazo wa su sitti,

ɗan ya tsuna fuska basma tayi ta tashi zaune tace


"Fatalwa kuma?,


Kai Hafsah ta jinjina mata alamun eh ajiyar zuciya basma ta saki tace


"Duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka ta juya ta kwanta aunty Ayesha ce ta shigo tace


"Hafsa basma zo muyi breakfast,

tashi sukai suka hau kan dining ba kajin karar komai sai ta chocali




*Jordan*

Tun da asuba suka tashi suka shirya yau sai Palestine treval bag ɗin su jameel ya ɗauka da sauran kayan su suka fito tareek ya miƙa mukullin ɗankin su kai tsaye mota suka shiga ta kai su gaɓar kogin Jordan da Palestine daga nan jirgin ruwa suka shiga aka tsallakar da su amma hanyar na da hatsari domin ansawa wajan nan takunkumi na hana shige da fice sosai suke keta ruwa wani ɗan waje suka samu bayan sun isa kasar suka sauka suka biya me jirgin ruwa

waya tareek ya ɗauko ganin babu network ala dole ya haƙura ya maida tafiya sukai menisa tukun na suka fara tarar da tantin mutane a dan nesa ƙaɗan da kogin ɗagowar abrar kenan.....



DESTINY LOVE



Arewabooks@oumyasmeen

Pinterest www.oumyasmeen.com



Chapter 31-40



Kura musu ido tayi da sauri ta tashi idanuwan ta na zubda hawaye ganin sa take kamar abbun ta da sauri ta tashi ta zaga ya dai dai inda taga sun tsaya ba zato ba tsammani yaji an rugumesa da sauri ya kalli wacce ta rungume sa kuka tasaki tace

"Abbuna abbu,

zaro ido taréêk yayi yayin da jameel ya saki dariya ganin yarda tarêēk ya zaro ido kai kace wata halitta ya gani yace


"Haba tareek ka rarrashe ta mana kana ganin tana kuka beautiful baby girl,


da sauri tareek ya saki baki yana kallon jameel yace


"Kana da hankali kuwa ? daga ganin yarinya jibi fa jikin ta duk datti zata ɓata min kaya ,



Sakar baki abrar tayi ganin basa Arabic ko Hebrew ko roman kallon su take yawa taga sabuwar halitta ihu zazzirah tayi ganin wasu mutane a kusa dasu ihun da ya janyo hankalin sauran mutanan taruwa suka kafin su tareek su ankara su gudu sun za gaye su wani tsoho yace

"منو انت؟ (Minno inta),


I card tareek ya fito da shi ƙarɓa tsohon yayi ya fara dubawa tuni matasan cikin su sun ɗauko sanduna suna jiran cewar jalaluldeen dan murmushi yayi yace


"Are You Journalist?,


kallon abrar yake da ta kasa barin jikinsa yace


أنا صحفي (Ana sahafi

jalaluldeen yace


"من أي مكان أنت؟ (Min ay makan inta?)




Raba abrar yayi da jikin sa ta sa kuka ta ƙara ruƙunkume sa yace

أنا من نيجيريا (Ana min Nijiria)


zubar da makamansu sukai hannunsa jalaluldeen ya kama yace


"Me ya kawo ku nan?,


duban sa tareek yayi yace


"Kamar yarda na fada maka da farko mu yan jarida ne na kasar Nigeriya munzo daukan rahoto akan abin da ke faruwa a nan ƙasar,


sosai jalaluldeen ya gamsu da bayanin tareek yace


"Bisimilah zamu baka gu ku zauna kuyi abin da ya kawo ku ku gama ku koma kasar ku amma da sharadin muka kama ka da wani abu na cutarwa a garemu tofa kashe ku za muyi mu musulmai ne bama zalunci ba muyar da ayi mana ba ko wannan faɗan daka ganin fin karfin mu akai,

jameel yace


"Insha Allahu zamu kiyaye muma musulmene,


Masha Allah jalaluldeen yace yayin da kowa ya koma gurinsa samin sukai suka zauna yayin da abrar ta kwanta a jikin tareek cike da tausayi jalaluldeen yace


"Wannan yarinyar abar tausayi ce mahaifinta amini nane a yanzu bata da kowa ba ko wanne lokaci muke samin abinci ba sama da shekar arba'in ba musan mene kwanciyar hankali ba ana kashe mu yawa kiyashi yara ƙanana sun zama marayu tun da abun nan ya faru ina lura da yarinyar nan yau ne ta sami lokacin yin bacci,


Dan ya mutsa fuska yayi domin shi bega abin da ya hada shi da labarin yarinyar nan ba duban sararin samaniya talaluldeen yayi yace



"Ɗana dan Allah wata alfarma nake nema a gunka ko wanne lokaci muna cikin bara zanar Isra'ila nima balalle in rayu ba inaji ajikina ko basu kashe mu na yunwa zata hallaka mu dan Allah da Manzonsa zan baka aurar abrar ka ruƙeta amanah kazama gatan ta bata da kowa in yan uwan mahaifiyar ta su kasan tana raye to tabbas zasu kashe ta .....,


da sauri ya ɗago kyawawa idanuwan

Please Login or Register in order to submit comment