Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace

"Jeki ki wanken toilet ,

Sum sum ta shige toilet......

**** Flash back

zuba ta gumi tayi har Aziz yazo bata san ya zo ba kura mata ido yayi cikin tsananin bugawar zuciya yace

"Ummi ... Me ya faru na ganki a nan ?,

Ɗagowa tayi ta  tatashi tace

"Aziz nan ba gun tambaya bane muje gida,

Ba yarda ya iya haka ya buɗe motarsa ya shiga wayar sa ya ɗauko domin kiran bakanike bugu daya ya ɗauka

da yake bashi da nisa daga inda suke nan da nan ya zo ya ɗauki motar ta su kuma suka huce gida

yana parking ta fito har tana harɗewa

a bubuwa sunwa kwakwalwar ta yawa gobe dole ta ziyarci gidan su ko za'a san inda take me yasa ta ɓoya bayan tasan ɓoyan tana tashin hankali ga rayuwarta

nur kade ta tarar a floor ta dama costom tana sha bowl ɗin hannunta ta ajiye ganin ummi ta taso da gudu ta rungume ta tace

"Ummi yau kuma da huri haka ba aikin kwana kike ba..?,

rungume yarinyar tata tayi sanyin idaniyar ta tace

"Ehwllh nur ,

cikin farin ciki tace

"To Barka da dawo wa addah ya kura tazo,

jimm tayi ta dubi yar tata tace

"Tana ina...?,

tsaki nur taja tace

"Ta gama fadan ta wai wallahi baba maza ya rako duniya ya tsa kina juyash....,

bata ƙarasa ba ummi ta ɗaga mata hannu tace

"Nur shikkenan nagane,

Ummi juyawa tayi tace

"Na'am aisar,

zama yayi a daya daga cikin royal sofa yace

"Ummi yunwa nake ji bazab iya cin abincin wannan yarinyar ba ,

dariya tayi ganin nur ta kwaɓe fuska yawa anmata bushara yau zata mutu tace

"Aikuwa auta a bagen girki zata iya karawa da kowa,

Aziz ne ya shigo yace

"Uhmm uhmm ummi yaufa abin yafi na kullum,

zaro ido tayi tace

Uhmm nidai komai auta ta dafa zanci,

ganin baba yana saukowa da gudu taje gunsa tasa kuka ƙarasowa yayi ya ruƙe mata hannu yace

"Yi shiru wa ya taɓan yar gaban goshina...?,

Azizi yace

"Baba abinci ta kwaɓa mana,

har suna haɗa baki da aisar....

ummi tace

"Wai shi abincin bashi da suna ne..? Kuna faɗi nasan wanda ta iya da wanda bata iya ba zan gane ku,

aisar yace

"Biski na mutan barno,

Pillow cases baba ya ɗauka ya cilla musu yace

"Abincin garin namu kuke kushewa ko tab yau ni da kune wato kunzama hausawa ko tab yau dole mu koma tushen mu,

dariya sukai suka shiga shashin su kowanne ya shiga bedroom ɗin sa.

nur ma dakin ta ta shiga ummi tafiya tayi tayi wanka tazo ta kwashi girki.....

KING Of JOURNALISTS MUHAMMAD TAREEK

Duk girman gadon bazai iya kwanciya da ita ba dan haka akwai wata kujera akan tayace ta kwanta

da yake ciki yake da jameel be ƙara fitowa floor ba addu'a yayi ya kwanta ya kashe fitilah tsorene ya kama abrar daƙin yayi duhu kuka ta fara tun tanayi a hankali har ta ƙara sauti

cikin bacci yaji wannan kukan nata ransa ne ta ɓaci ya tashi kunna fila yayi

cak ta saboda mugun kallon da yayi mata kwafa yayi

komawa ta yi ta kwanta domin yanzu wani bugun tsoronsa take ji Saboda abin da ya faru a toilet har yanzu zafi gun ke mata

Kashe fitilah yayi ya kwanta

karfe hudu ya tashi nafilah yayi har aka kira sallar asuba tashin ta ya fara yi

Kwanciya ta gyara kura mata ido yayi duk inda me kyau takai to abrar ta kai duba da irin jinsin da ta fito saurin kauda idonsa yayi sakamaƙon ƙirjinta da saman sa ya fito gun yayi ja ga shatin hannunsa rada rada a jikinta...

Ganin lokaci yana kurewa bata tashi ba ya fito har jameel ya ɗauro alwalah a toilet ɗin floor yace

"A'a ango har an fito ya kwanan amarya  yice ko anbimin kwanwa a hankali dan najin kukan ta jiy.........,

Ran tareek ne ya ɓaci yace

"Wallahi jameel ka kiyaye ni,

ruƙo hannunsa yayi yace

"Calm down big brother wallahi naji me kai mata,

Ahassale yace

"Uwar...k nayi mata,

kama baki yayi yace

"Wow yau tareek da zagi muje,

haka suka tafi jan tareek ya ɗin gayi da hira yana basar dashi masallaci suka shiga sai karfe 7:30 suka fito kai tsaye

Restaurant suka shiga inda sukai order abinci har sun fito kamar ance tareek juya mutumin da yayi shekara da shekaru yana nema ya gani tsohon me lefi amma kash har ya hau mota ya tafi number motar ya ruƙe

Domin hatsarine babba ya bi bayansa duba da irin ƙasar da suke akwai tsaro

Jameel yace

"Lafiya tareek naga kana kallon waccan motar..?,

hmmm bakomai mu tafi domin tareek besan yana aiki da D.A.S.S ba  shiyasa ma wayan nan sujojin Isra'ila suka so kashe shi

daga nan suka biya wani phone centre suka siyi waya sai 8:30 suka dawo hotel ɗin lokacin

Abrar taci kuka ta gaji suna buɗe ƙofa ta rungume jameel tasa kuka ran tareel ne ya ɓaci idanuwansa sunyi ja yawa garwashi janyota yayi ya kifa mata mar......✍️




*DESTINY LOVE*

          Daga alƙalamin

              *Oumyasmeen*

Watt pad @Aminaoumyasmeen

Arewabooke@oumyasmeen

          

             Perfectly pen's ✊

KING AND QUEEN WRITING CHAMBER👌✊

ABRAR=me tsoran Allah





Episode 55


TARÉÉK POV


Sai dai me yawa an ruƙe hannunsa ya kasa dukanta ita kuwa tuni ta firgita ya fashe da wani irin marayan kuka zama jameel yayi  be cewa tareek kala ba domin yana iya hango hutar kishi dake ruruwa a idanuwansa gwara inya huce yayi mai magana...

Shiga bedroom yayi wanka yayi tunani duk ya cin kunshe me zuciya gwara ya koma gida ko zai sami salama a zuciyar sa har ya fito be dena tunani ba shirya wa yayi cikin White t-shirt da blue jeans  sai ƙamshi yake zubawa wayar da ya siyo ya shiga sai ta mahimman abubuwa sa

Jameel ne ya shigo yace

"Malam kabar fa yarinya na jin yunwa,

ɗagowa yayi yace

"Bata take away ɗaya taci,

Juyawa yayi ya koma floor leda ɗaya ya ɗauko ya kawo ya kawo gaban ta ya buɗe mata tausayin ta ya kama shi

me lallashi take buƙata gashi Allah ya haɗata da miskilin miji

bata yi mai  musu ta amsa domin itama yunwa take ji komawa yayi ya zauna

tamkar me koyan cin abinci haka ta fara tsakurar sa bawai dan be dadi ba sai dai wannan ba cimar ta bace cimar garin Jordan dan ce

kaɗan taci ta barsa yago tissue tayi  ta goge hannunta  ta ɗauki lemo ɗaya ta fara sha ko rabi bata sha ba taji fitsari ajiye wa tayi ta shiga

bedroom ɗin da tareek yake ta shiga

Samunsa tayi yana kwance yana latsai latsan waya idanuwanta ne ya ciko da kwallah cikin sanyi murya tamkar ana busa sarewa tace

"Abbu Abbu ta nuna mai hanyar toilet,

ɗagowa yayi ya zuɓa mata ido bece mata komai ba ƙasa tayi danata idon dan bazata iya kallan sa ba ta fara wasa da hannunta

haushi ne ya ishi tareek abu kaɗan kuka yawa me takaba bawai ya fahimci me take nufi a'a kawai shigar da ita zai komai ma zata yi tayi wannan shagwaɓar da sangarta ta ishe shi....

ajiye wayar yayi ya sauko daga luxury bed ɗin ya kama hannunta har toilet yawa me ciwon baki yace

"Taking care  taking,

a wannan karan taji me yace dan haka ta ɗaga mai kai tayi har wanka zatayi


To bayan ta fito tasa kaya duk yana dakin saidai hankalin sa ya kanta lokaci zuwa lokaci yakan ɗago ya kalle ta gamawa yayi ya fara haɗa kayansu dake komai yayi mata ta internet

yau sai Nigeria ƙasar mu ta gado garin shugaba jagaba

Fitowa yayi tana biye dashi jameel ma ya shirya kullo dakin jameel yayi sukai kaiwa me kula da dakuna

Tesxi suka hau har airport ta kai su bincikar kayansu akai da vizar su basu sami wata matsala ba suka shiga jirgi

Wajan tareek da abrar ɗaya jameel na bayan su baccine yayi a won gaba da ita   a jikin tareek ta kwanta magazine ya ɗauka ya fara karantawa har Allah ya kawo su kano suka sauka a

AMINU KANO NTERNATIONAL AIRPORT

checking kayan su akai bare idanuwa abrar tayi tana kallon ikon Allah ruƙe tareek gam tayi tsoron wayan nan bakaƙen mutanan take 

Tun ɗazu wanda zai ɗauke su yazo dan gaka ana gama binciken su

suka shiga Mota yau sai gidan

BN NADER


GADAN ƘAYA J.R.A

Juyowa driving yayi yana kallon abrar mamakine fal a zuciyar sa ko ina wayan nan mutanen suka samo wannan yarinya..? lalle yau a kwai tashin hankali a gidan nan dama basa rabo dashi to gawa ni nan ya rakito musu sabo fil

ganin ba me bashi amsa ya mai da hankalin da kan titi har suka iso horn yayi me gadi ya buɗe parking yayi fitowa sukai

Kallon ko ina abrar take yawa wacce ta warke daga cutar makanta

jameel ne ya dube SA yace


"TAREEK wanne bayani za kaiwa su abbie naga ko a jikin ka ?,

Haɗe girar sama data ƙasa yayi yace

"Wanne bayani kuma..? akan me ..? zan musu bayani..,

murmushi jameel yayi daman yasan za arina shashin aunty Ayesha suka nufa cikin tana zaune a floor da sauri ta tashi jin sallamar su tace


"sannun ku da zowa na neme ku har na gaji bata lura da yarinyar dake hannun tareek ba ,

Hmm kawai jameel yace domin sun ga mutuwa ido da ido zama jameel yayi tareek ya shigo hannunsa ruƙe da na abrar yawa wata doluwa ta saki baki tana kallon sa kasa haƙura tayi yana zama tace

"Tareek wace wannan....?,

gyara zama yayi yace


"Ga a jiyarta zan miki bayani,

Yana fadar haka ya tashi har ya fara tafiya ya tsaya yace

"Duk abin da take buƙata ki faɗamin in baki kuɗi ki siyo,

daman tasan za'arina shi mutum ne da ba'a sanin cikin sa ba kuma yason shishshigi da shigar mai rayuwa tace

"Okay ya sunan ta...?,

fita yayi yayin da jameel ya bishi be bata amsa ba

Kafin ta ankara abrar ta fita tana kuka ta bisu tana Abbu Abbu Abbu da sauri Aunty Ayesha ta bita amma ina gudu take

bata luraba ta bige sitti ruƙota sitti tayi chak jameel ya tsaya banda tareek dama ranta a ɓace yake da tafiyar su yan zun nan hafsa ta sanar mata da dawo war su shine ta zo ta wanke su tas sai ga abin da ta ci karo da shi

janyota tayi ta sharara mata mari ta dubi jameel tace

"Kai ina ɗayan takadirin yake  wannan kuma a ina ku ka samota....?,

Sosa ƙƴeya jameel yayi yace

"Uhmm sitti kenan ,

hassala zuciyarta tayi ganin suna shirin raina mata hankali  shi dayan ya gudu shi kuma ga amsar da ya bata

maida kallon ta gun Aunty Ayesha tayi tace

"ke ina kika samu wannan tana zaune a gidan nan ban sani ba ...?,

gaban aunty Ayesha ne ya tsananta bugu tasan tujarar sitti bata ƙarewa bakinta narawa tace

"Nima yanzun nan tareek ya ban amanarta,

Ihu sitti tasa sakamakon cizo da abrar ta gartsa mata ta zuba a guje ta bi inda taga sunyi sitti tace

"Innalillahi shikkenan tareek ya dawo mana da jikar aljanu da mayu irin wannan kyau haka to wallahi ba zata saɓo ba ke Aishatou kiramin kowa na gidan nan ya zo babban flooe dole yau wannan aljanar ta barmin gida ,

Jikin Ayesha be yayi sanyi tace

"To ,

Kallon sama da kasa sitti take mata tace

"Lafiya kike gyaɗa kai yawa wata gaɗangaruwa ko bazaki bane...? ni inje,

girgiza kai Ayesha tayi tace

"Zani sitti,

harara sitti ta bita dashi tace

"Wallahi yau tareek sai ya san faɗa dani ba daɗi ba ya rainani ba..

Besan ni baƙar fura bace faɗan ibilisai

dole yau safna ta tareek a shashinsa ni anya kuwa ba yarsa ce wannan ba kai biri yayi kama da mutum ya zauna yaƙi aure to wallahi bazan yarda shege ya kara zamar mi a gida ba ,

Inteesar ce ta zo hucewa turus tayi ganin sitti na zuba tujara tace

"A'a sitti lafiya kike magana ke kaɗai...?,

da sauri ta ɗago yace

"Yar nan zancen zucine ya fito fili yau ran kowa na cikin gidan nan sai ya ɓaci,

Taɓe baki inteesar tayi tace

"Me ya faru sitti..?gutsuramin kafin a fara faɗan ibilisan da naji kina magana...,

Sarai sitti tasan inteesar ba kunya ce da itaba yanzunan zata mai da ita abokiyar wasan ta ita kuma ta tsani raini tace

"Uwarki ce ,

Zaro ido tayi tace

"Sitti nayi nan da alama kenan aljanun gidan nan sun fara taɓa ki ,

Wani uban ashar ta bulmulu tace

"Ke inteesar wallahi kike yaye ni wanne aljani aini naci dubu sai ce to ,

Zaro Ido inteesar tayi tace

"Wallahi sitti yi shiru kar yau su hanaki bacci Ni dai nayi nan tayi gaba,

Tsorone ya kama sitti domin bata manta buga kanta da suka dinga yiba da ta shiga toilet aikuwa itama bara tayi wa kanta kiyamul laili

floor ta takoma ta harɗe kafa ɗaya kan ɗaya dan wallahi yau me rabata da tareek sai Allah ..

💨💨💨 Flash back

Ji yayi an rungume shi  kuka take juyowa yayi ya rage tsayin sa ya kura mata ido ga shatin hannun sitti a fuskarta raɗa raɗa

abin ka da farar fata hannu yasa ya share mata hawaye ya ruƙe hannunta suka fara tafiya har shashinsa buɗewa yayi ya shiga

Jameel ma shigowa yayi ya tsaya a bakin kofa yace

"Tareek ni na tafi gida yanzun nan hibbah ta kirani hajiya ba lafiya,

Juyawa yayi yace

"Okay Allah ya bata lafiya,

Amin yace ya fita komawa yayi ya rufo kofar sa

abrar kuwa zama tayi har bacci ya fara ɗaukanta iya gajiya ta gaji

jingina yayi da jikin kofa

" baya tsoran sitti saboda in da sabo ya saba amma fa mahaifinsa shi zata tusa a gaba da tujarar ta bakuma ya tsoron kowa yasan abrar matarsa ce amma me ai tayi ƙanƙanta da ace babba ce ko dan ya baƙantawa sitti zai zauna da ita suyi zaman aure amma wannan fa da ko kanta bata gama sani ba tabbas yana buƙatar mace amma bashi da ra'ayin tara mata har hudu ga safna matar shige ga abrar wacce ƙaddara ta haɗasu ko me sitti za tayi ba zai taɓa rayuwar aure da safna ba

yana kƴamatar zina yana ƙin meyinta

alkawari yayi saidai su gaji sunemi saki amma bazai taɓa hada shinfiɗa da itaba....

tsaki yaja lokacin da yakalli a gogo ya ɓata lokaci yana tunani a gurguje ya  shiga bedroom ɗinsa ya cire kaya

ya shiga toilet wanka yayi ya ɓata lokaci yawa wata mace fitowa yayi ɗaure da towel ga wani a hannunsa yana tsane kansa besan da ta shigo bedroom ɗin ba

ya zame towel ɗin dake ɗaure a ƙugunsa wata irin yar ƙara abrar ta saki

da sauri ya maida   towel ɗin idonsa ne ya kaɗ'a yayi ja yanzu yarinyar nan zata raina shi ta gansa ba kaya 

Tsawa ya daka mata ya nuna mata kofar fita da sauri ta fita har tana tuntuɓe

Cikin sauri ya shirya cikin T-shirt red colour an yi rubutu da baƙi ansa Gucci...

tuni ta haskaka farar fatar sa jeans yasa black colour expensive spray ya ɗauko ya  feshe jikin sa  agogo ya ɗauko Rolex ya ɗaura

Ji yowa yayi ana buga kofar sa yawa ba gobe da  saurin fitowa yayi ya buɗe kallo ɗaya yayiwa salim ya nutsu yace

"Kazo abbie na kiranka yana floor sitti,

juyawa yayi batare da yace me komai ba ya kulle kofar

tsaki salim yaja yaso ace yaga wacce sitti take cewa ya kawo ashe shima ya kawo mata me fuska biyu sai ya nuna shima na Allah ne ko da yake dan zina yaƙi zina....

Yana rufe kofar ya nufi wata glasses door zogeta yayi sai ga takalma jere sunfi hamsin ɗauko wani slippers yayi Black colour da yarin ja yasa kallon ta yayi ta haɗa kai da gwuiwa

ba abin da yaki jini irin kuka da zata gane da ta dena gashi bajin hausa take ba balle yayi mata gunta ya je ya ruƙo hannunta domin in ya barta zata kara wani kukan ne ta rikita mai lissafi

ya kullo shashin sa sai da sukai tafiya me nisa tukun na ya isa shashin sitti baƙin sa ɗauke da sallama ya shiga kowa na zaune duk wanda ya ke kwana a cikin estate ɗin ya hallara agun duk sun zauna ita shugaba tana tsakiya ransane ya ɓaci

shiga yayi ya zauna a ɗaya daga cikin Luxury royel chairs ɗin dake tabkeken floor ƙasa yayi da kansa

kowa kallo yabi abrar da shi mamakine ya kusan kar mom amina  ina ya samo wannan balarabiyar tab a kwai kura haka ta ayyana a ranta sitti ce zuciyar ta takai har huya tace

"Kai rasa kunya ɓeran tanka kowa kai yake jira ina kasamo wannan aljanar me idon mage,

ido huɗu sukai da abrar ƙara rukunkume tareek tayi domin tsoran matar ya shigeta haɗe rai yayi abbie da shi ma yake son sanin ko wa wace wannan duk da yayi shedar ɗan nasa bazai taɓa aikata abin da sitti take faɗi ba yace

"Tareek ina ka samo wannan ba ce min kayi ba aiki aka tura ku to ya akai ka dawo da yarinyar nan ....?,

Safna ce ta shigo yawa an hankaɗo ta wani irin kallon tsana take jifan abrar da shi tamkar dirar miƙiya kamar an ɗiga mata dalma a zuciyar ta da kunnan ta numfashin ta yake kai kawo bata da cutar asma amma a yau fa ta kamu da cutar saboda da numfashin ta dake sama da ƙasa ga bugun zuciya jiiiyi yace......✍️

*_🤔tab akwai kurafa me zai faru gaba to nidai ba ruwana ku yayyafawa safna ruwa 🤗 nayi nan🚵_*


*DESTINY LOVE*


Daga alƙalamin

*Oumyasmeen*


Watt pad @Aminaoumyasmeen

Arewabooke@oumyasmeen




Perfectly pen's ✊


KING AND QUEEN WRITING CHAMBER👌✊

Duk meson ci gaba ya shiga link ɗin nan ku yi following ɗina domin samun ci gaba da zarar na ɗora ku danna min VOTE ngd



https://www.wattpad.com/1466636040?utm_medium=link&utm_content=share_published&utm_source=android




Episode 56-57

ƙasa yayi da kansa yace


"Mata tace basu labarin abin da ya faru yayi


Tuni gun suka ɗauki salati ban da safna da ta zube basu sani ba kuka sitti tasa ta fyace majina tace


"Ubaidullah kaji abin da ɗanka kake faɗi ko baka fasa mai baki ba saboda ya raina ni na zaɓa mai mata shine yaje ya kwaso mana farar fata baya hudiya wallahi bazata zauna min a gida ba...,



ɗago da runannun idanuwansa yayi ya kafe sitti da su jin kalamanta na karshe a hankali ya buɗe baki yace


"Sitti kin manta baya....? me ya faru

Hmmm ya saki wani muskilin murmushi yace


"Gurin da nake zaune da kuɗina na siya da gumina na gina da kofar shi ba a cikin gidan nan take ba sai da uncle yayi min magana na tushe kofar na shigo da ita yanzu ma ina da yancin mai da ita inda take zama da ita ba gudu ba jada baya....,


Salati sitti ta saki tace


"Kana ji ɗanka yana gasan magana kayi shiru.... Ko to wallahi dani kuke zance kuma yau ɗin nan safna zata tare a gidansa,

dafe kai salim yayi yaushe tareek ya auri safna be sani ba itama bata faɗamai ba lallai akwai kura yanzu ainiyin wasan zai fara wato ko ta wanne fanni tareek ya fishi shida ma yake shege tab jajar ubannan.....


alhaji Ubaidullah ya gyara zamansa yace


"Muhammad kar in ƙara jin bakin ka sannan yau ka tattara kayan ka guri ɗaya safna zata tare,

Ɗago hajayen idanuwansa yayi ya dubi mahaifinsa sai a kai sa'a suka haɗa ido da uncle nasir girgiza mai kai yayi ya na yimai alama yabi umarnin mahaifinsa cije lips ɗin sa na ƙasa yayi motsa lips ɗin sa yayi yace


"To,


Alhaji Abdulnur da Alhaji Abdullah ransu be soba da sitti ba takori tareek ba musanman alhaji Abdullahi da suke yar tsama yana da gidan yin robobi to chemical ɗin yana cutar da al'umma sai aka kai shi ƙara gidan Radio


shine ya jagoranci shirin har cin hanci ya bashi akan ya danne abin amma yaƙi haka shugaban gidan Radio ya bashi umarni kar ya yaɗa shirin yaƙi ya yaɗa dan haka ya salame shi shine yanzu Alkhairi radio ta ɗauke shi aiki



gyara zama yayi yace


"Allah ya ja da ranki sitti amma wannan yarinyar mece makomar ta a gidan nan gaskiya bazai yuhu ba kin haɗa ƴa'ta da tareek amma banyi magana ba duk da irin tawayar da yake da ita be gani ba ya kara ɗauko wata gaskiya baza ta saɓo ba ...,

wani irin numfashi tareek ya fesar me huci fuskarsa tayi ja riƙe hannun gujerar sitti yayi gam har hannunsa na jini saboda ruƙo da yayi


kurawa kahunsa ido yayi ko kiftawa bayayi besan lokacin da ya ture Centre table ɗin dake gan bansa ba

jikake tararatsar ga bada sautin tush a binka da glass da sauri mom hafsa da mom amina suka takure gu ɗaya sun san halin haukan tareek zai iya daukan mutum yayi hulli dàshi miƙewa yayi ya riƙe hannun abrar ya fara tafiya


Wallahi tareek kakiyaye ni wannan fadan dani kake faɗar sitti

Chak ya tsaya juyawa yayi ya kalleta ya saki muskilin murmushi gaban mom amina ne ya waɗi domin ita kaɗe tasan murmushin sa ba alkairi bane akwai.....

wata a ƙasa tareek wani irin juyayyan mutum ne ba hago gane inda ya dosa sai Allah zakai abu ya nuna tamkar be gaban ka ba besan me kake ba....

Amma yana lura da komai bawai be ganka bane aa iya takune mutumin dake faɗa da gwamnati dole tasan abin da yake nufi kafin komai ya jagule mata


Tafiaya ya fara sitti ta saki salati be juyaba.....

Mom hafsa kuka tasa lokacin da tayi arba da safna a xube tace


"Wayyo Allah kunga zai kashe min ya' wallahi taji abin da yace,


da sauri su salim suka zagaye ta hajiya karima kuwa tashi tayi ta taɓe baki dan ita bata ga abin kirata a wannan maganar ba bata shafe ta ba ...


a hankali suka zare jikin su aka bar salim da alhaji Abdullah da mom hafsa sai sitti watsa mata ruwa sukai ta saki wani marayan kuka....

Rarrashin ta sitti ta fara shiru tayi bawai dan ta haƙura bane a'a da kudiri da yawa a zuciyar ta karan bana shike .... maganin zomon bana ..




Flash Back




Kofar shashinsa ya tura ya shiga ya kullewa ya buɗe kofar floor sa

da gudu abrar ta hau kan kujerar be biya ta kanta ba ya ɗauko system ɗin da yana aiki fitsari ne ya matsai ta gashi bata san inda toilet yake ba tashi tayi ta tsaya a gaban sa ɗago kansa yayi jin alamar tsayawar mutum sai yanzu ya tuna ko wanka batayi ba miƙewa yayi ya ja hannun ta suka fita har Shashin anty aysha yana zuwa yace


"Ga tanan ki riƙe ta duk kukan da zata yi haka zata gaji ta haƙura,

Dariya anty Ayesha tayi tace


"To mijin mace biyu angama na lura gudun yar'tawa take aikuwa zan baka mamaki wata ran sai ka haɗani da Allah inbaka ita,

zaro ido yayi yace


"Never...,

Hmm kawai aunty Ayesha tace riƙe ta tayi ya fita kuka tasa ko juyawa be ba ya tafiyar sa basma basma


Dasauri basma ta fito tace


"Aunty gani...,

gyara riƙon da tayiwa abrar tayi tace


"Kullemin kofa,

To tace mata ta kullo ko arzikin kallo abrar bata samu ba a gun basma saima wani baƙin ciki da ya tukare mata ƙawon zuciya....,





Maitama Abuja JB club


Kallon kowa take ɗaidai... tun da ta shigo gun ta zauna ba abin da tasha duk kuwa da kayan motsa bakin da aka cika mata gabanta da shi buƙatar ta kawai taga wanda tazo gani ko wanne minti yana bugawa ne tare da zuciyar ta agogon dake manne a hannun ta take dubawa lokaci zuwa lokaci takan ja tsaki ....


baƙin glass ne manne a fuskar ta dan haka ba zaka gane ko wace ba ga facemask da tasa wani mata shine yazo ya raɗa mata magana a kunne


da sauri ta tashi tafiya take cikin yanga yawa me tausayin ƙasa duk kuwa da tsoron dake fal a zuciyar ta bata san ko yau ma baza ta sami ganinsa ba bata san ko zai

Please Login or Register in order to submit comment