Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Saurin rufe mata baki yayi yace “Dad shine jikan naku bayason zumunci" dariya Dad yayi yace “kajimin ja'iran yara to naji kunyi ciki kunyi abin kirki amma fah zan kafa doka banason shan zaqi da shan abu me sanyi kada a illatamin jika" dariya sosai Mainah Abdu yayi yace “angama Dad" haka sukayita barkwancinsu daga qarshe sukayi sallama ya kamota yace “biyu jirginmu zai tashi yanzu daya saura minti takwas yakamata mu tafi kafin lkc ya qure" sama suka haura suka dauka sauran abubuwan da zasu buqata suka sauko suka fita driver yajasu zuwa airport sai birnin London.



*****



Saukar asuba sukayiwa birnin Landon kai tsaye motar SS Ambassador (SSAOP) sune sukazo daukarsu nanta Samha ta zama yar kallo yanda taga turawan suna girmama mijin nata mazansu da matansu kowa sai zuwa yake yana kwasar gaisuwa mazan su rungumeshi matan kuma su daga masa hanu su rungume Samha suna fada masa matarsa kyakkyawa ce nandanan taga ya daure fuska ya janyota jikinsa musamman da yaga mazan turawan sunata kallonta haushine yasashi shigar da ita mota ya dawo suka qarasa gaisawa ya shiga driven yajasu Suma sauran motocin suka take musu baya saida suka biya office dinsu ya fita ya shiga baifi minti goma ba ya dawo motar ta nufi wata unguwa dasu wani qaton gdane da yake cike da manyan bishiyoyi kamar gdan gona suka shiga driven yayi parking ya fito ya bude musu suka fita suka shiga ya danna code din door din ta bude suka shiga kawai saita saki baki komai na fasalin parlourn irin nasu ne na 9ja dagowa tayi ta kallesa ya kashe mata ido yace “komai na wannan gdan naki irin na gdanki ne na 9ja" ajiyar zuciya tayi tace “amma aikin me kakeyi anan My Abdul?" Murmushi yayi yace “meyasa kika tambayeni?"



Shiru tayi babu amsa yayi kissing dinta yace “tunda muka taho bakiyi bacci ba muje muyi wanka mu huta mayi komai daga baya" batayi mgn ba ya kamata suka hau sama ya bude musu qofa suka shiga sukayi wanka suka kwanta bai takura mataba saboda shima a gajiye yake saida sukayi bacci suka tashi sannan ya fita ya nemo musu abinda zasuci bai jima ba ya shigo ya tarar da ita a kwance ya dagota ya sauko da ita sukaci abincinsu bata wani jin dadinsa hakanan ta rinqa turawa shikam dake ya saba bai wani damu ba bayan sun gama ta koma ta kwanta shima ya dawo ya kwanta ranar yini sukayi suna baccin gajiya sai dare suka fita suka zaga garin London taga gari sosai sannan suka juyo suka dawo gda suna komawa gdan suka zube a kujerun parlourn.




Hakanan kwanaki sukayita turawa tafiya na miqawa har watanni cike da soyayya da tattalin juna watansu uku a garin London wanda yake tafiya daidai da watannin cikinta hudu da sati biyu a cikin lkcn ne kuma Samha ta rinqa fama da wani matsanancin ciwon ciki wanda tun abin yana iya boyuwa ita kadai har takai Mainah Abdu ya fara gane da matsala kuma abin baya tashi sai bayan Isha zuwa wayewar gari lamarin daya dagula lissafin ma'auratan saboda idan ciwon ya tashi kwana sukeyi basuyi bacci ba fita take daga hayyacinta tayita malelekuwa tana kuka tana kiran sunan Allah da sunan Mamy da Dad da sunansa sunje asibiti har sun gaji kullum cikin yi mata scarnning ake amma amsa dayace cikinta lfy qlau a cikin wata ukun cikin yayi girma sosai hakan yasa likitocin asibitin da take zuwa suka duqufa wajen ganin sun gano meke a cikinta amma Allah ya lullube abinsa hakanan dole suka qyaleta su dakansu suka bashi shawarar ya rinqa yi Mata na addininsu hakan kuwa akayi sosai ya duqufa wajen yi mata addu'o'i alhmdllh sai ciwon ya fara lafawa sai tayi kwanaki be motsa mata ba idanma ya motsa baya dadewa yakeyin sauqi.




Wannan ta wucce sai kuma wata ta bullo idan ya fita ya barta a gdan ita kadai sai ta rinqa firgita tana zabura ita kadai amma daya dawo sai komai yayi sauqi wannan dalilin faduwar gaban yasa duk ta rinqa ramewa sai uban ciki a gaba ramar tata tana mugun damun Mainah Abdu lamarin razana Abdu yakeyi sosai wannan dalilin yasa daqyar ya rufa wata shida a qasar England suka kamo hanyar dawowa gda itace sukayi waya da mamy ta fada Mata sun kusa dawowa yaga sanda sukayi wayar amma baiji me Mamy tace ba da asuba jirginsu ya sauka Mansoor ne yazo ya daukesu zuwa gdansu shi kansa Manson saida yayi mamakin girman cikin nata wata bakwai amma daqyar take daga qafarta yana rirriqeta yana Mata sannu suna tsayawaya fita ya bude mata ya tallafo cikinta yace “sannu My Aysha insha Allah idan kinzo haihuwa baby bazai wahalarmin dakeba" takawa suka rinqayi tanayi masa murmushinta suka isa corridoor din dazai shigar dasu parlourn yasa mukulli zai bude ita kuma ta daga qafarta ta taka saman tiles kawai sai taji mararta da bayanta sunyi wata muguwar riqewa batasan sanda tayi qasa ba da sauri kawai sai taga jini yanabin qafarta ta dago ta kalleshi ta saki qara tace “My Abdul jini wayyohh!" Juyowa yayi a sukwane ya tsuguna a gabanta gumi yana keto masa yace “jij...jini Aysha wayyoh kinga zuba yakeyi mene hakan ya zamuyi".......





*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[2/18, 8:27 AM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_AD_*



*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*




*36*




Qwarara jinin yaci gaba dayi hankalin Samha yana qara gushewa tashin hankalin Mainah Abdu yana qara nunkuwa idanunsa suna qara qanqancewa Manson ne da yake cikin mota yaga tsugunnan yayi yawa kasancewar har lkcn akwai duhun dare lkcn 5:43am baya iya hango asalin abinda yake faruwa fita yayi daga motar ya nufesu da sauri kawai sai ya cambala qafarsa cikin jinin da yake zuba da sauri yakai kallonsa qasa ganin jinine yake malala ta jikin matar aminin nasa shikuma ya saki baki yana kallonta harta fara jijjiga yasashi baisan sanda ya sunkuce ya juya a sukwane ba ya nufi mota cikin tashin hankali sai lkcn Mainah Abdu ya dawo hayyacinsa shima ya miqe yana jiri zuciyarsa na bugawa da qarfi daqyar ya iya qarasa motar saboda 50 50 yake gani shiga yayi Manson yaja a guje suka fita daga gdan Amir's hospital suka nufa yanda suka shiganne yasa hankalin kowa ya dawo kan motar wadda number motar kawai take nuna ta waye Mainah Abdu 4 haka number take da sauri duk wasu manyan ma'aikatan dake asibitin sukayo cahh a motar sunayin parking aka bude tare da dorata a wani gado saboda jijjigar da takeyi idanunta duk sun juye shiga akayi da ita emergency room aka fara checking dinta.




Daya daga cikin likitocin ne ya fito ya dubi Abdu da yake durqushe dafe da kansa duniyar gaba daya juya masa takeyi ya dafashi yace “matarka da abinda ke cikinta suna buqatar taimakoka cikin wannan lkcn bai kamata ka bata lkcnka cikin tunanin abinda bazai fissheka ba jinin da take zubarwa yayi yawa daqyar dai an samu ya ragu dole saidai ayi mata teather a cire abinda ke cikinta muna buqatar jini leda hudu" dagowa yayi ya busar da wata iska me zafi Manson yariga yasan halinsa idan ya shiga tashin hankali komai ma qwace masa yake yanda yake huci kadai ya isa ya nuna mawa wanda yasan ahlin gdan sarautar bashi kadai bane cewa Manson yayi “muje ayi duk abinda daya dace" binsa sukayi suka shiga Lab din saida ya fada gwada na Samha yaga group din jininta sannan ya gwada na Mainah Abdu irin jinin nanne dazai iya bawa kowa hakan yasa aka diba har leda biyu amma kafin nan saida aka nemi wani a freezer irin na Samha aka jorner mata shikuwa Manson fadu zuwa tayi daidai da qasa dan jinin nasu irin daya ne da Samha leda daya aka diba a jikinsa.




Wani daki aka rakasu wai su huta shikam gogan qeqashe qasa yayi yace shi matarsa kawai yakeson gani babu yanda Dr din zaiyi dashi dole ya qyaleshi suka shiga tare tana kwance kamar gawa sai cikinta kawai da yake motsi tayi wani fyau da ita ta dashe ga inda duk ta cije lebenta na har harshenta ta datse har yanzu ma haqoranta na cikin harshenta bakinta sai jini yakeyi shafa cikinta yayi idanunsa nayi masa gizon abubuwa da yawa ciki harda fuskar fulani Hadiza da Hajiya Lubabatu dama mutane da yawa da bazai iya tantance fuskokinsu ba juyawa yayi ya fita da sauri daidai lkcn da iyalen gdansu sukazo fulani Amina Mai martaba da Dr Hasina shidai kawai bin kowa yakeyi da kallo batare da yana fahimtar ko kalma daya da suke fada masa ba.




Yananan zaune cikin wannan yanayin mai wuyar fassarawa aka fito da files dinta likitan ya miqa masa yace “Kayi signing zaa shiga da ita teather room munyi iyakar yinmu mugano meye ke a cikinta mun kasa" baiyi mgn ba sai karbar files din da yayi yasa hanu ya miqa masa Mai martaba ne yasa hanu a matsayin mahaifinta saboda Dad yana Abuja sunyi waya yace duk abinda ya kamata ayi mata kafin ya iso Dr Hasina itace a matsayin Mamy saboda koda aka kirata ma domin sauke haqqinta na uwa aka fada mata murmushi ma tayi tace “Allah ya kyauta Amina may be idan na gama uzurirrika na zuwa jibi nazo idan kuma ta Allah ta kasance to dama lkc muke jira" tana fadin haka ta kashe wayarta tana dariya.
Wannan abu ya gigita duniyar fulani Amina tare dasa mata kokwanto akan cikar hankalin Hajiya Lubabatu haka aka fito da Samha aka shiga da ita dakin teather miqewa Mainah Abdu yayi zaibisu Mai martaba da yayansa Mainah Abubakar suka riqeshi ya kuwa girgijesu zai wucce daqyar Mainah Farooq daya shigo yanzu ya riqeshi ya hanashi gaba ya hanashi baya dama idan yana cikin wannan yanayin shi kadai ne yake iya control dinsa yanke jiki yayi zai fadi saboda juwar data debeshi amma sai sukayi maza suka riqeshi suka shigar dashi dakin da Mansoor yake kwance saboda shi tunda aka dauki jininsa yake jiri hakanne yasashi shiga dakin ya kwanta.




Kwantar dashi sukayi Mai martaba ya zauna a gefensa ya kalli Manson yace “Mansoor wai meye sanadin faruwar hakanne?" Miqewa yayi t zauna yace “lfy qlau na daukosu daga airport muna hirarmu har tana tsokanata tunda naqi aure idan ta haihu zata bani yarta ta fari na aura kawai na kaisu sun fita zasu shiga Mainah yanata zuba mata sannu kawai sai ganinsu nayi a tsugunne ganin tsugunon yayi yawa ne yasani fita ina zuwa naganta cikin wannan yanayin jini yana zuba a jikinta kamar famfo" numfashi Mai martaba yaja yace “Allah shine ya barwa kansa sani" “nasan komai kuma zan fallasa komai ka kira Dad ka fada masa kada ya taho a mota ya biyo jirgi kuma ka fada masa ya taho shi kadai kada ya taho da excourt dinsa ko daya" kallonsa Mai martaba yayi yace “meyasa gagarabadau?" Idonsa a lumshe yake kamar wanda yake bacci yace “kawai nidai nace ka fada masa haka banason tambaya idan lkc yayi zaka sani" saqo Mai martaba ya turawa dan'uwannasa haka kuwa akayi har ya fito zai hau mota ya fasa ya sallami kowa ya dauki mota shikadai ya tafi filin jirgi saida yaje sannan ya kirasu yace azo a dauki motarsa.





Goma a palace hospital tayi masa shima dai tambayar da yakeyi kenan “ya akayi hakan ta faru amsar da Abdallah yabawa Mai martaba shima ita ya bashi dole haka suka qyaleshi.
2:30pm aka gama Mata CX din cikin nasara suka fito Mata da zaratan yaranta maza guda uku dukkansu rayayyu duk da kasancewarsu guda ukun amma sunyi mamakin girmansu sosai hakanan aka sanyasu a Incurbetoor wayyohh Allah kuzo kuga murna gurin iyalan ne shikuwa Abdul da aka fada masa dagashi har Mai martaba da Dad sujjada sukayiwa lillahi rabbulsamawatih wal ardih suna qara miqa gdyrsu ga Allah yana miqewa kuwa kafin wani ya ankara ya fice daga dakin duk yanda likitocin sukaso hanashi yaqi hanuwa dole saida suka kaishi dakin da take kwance har yanzu kamar gawa bata ko motsi ya zuba mata ido yana hawaye yana roqon Allah ya bata lfy ta shayar masa da yayansa juyawa ya kumayi aka kaishi inda yaran suke ya qura musu ido ya kalli wannan ya kalli wannan yana murmushi yanda suke motsi abin gwanin ban sha'awa yana rayawa a ransa wadannan duk nasane sune fulani Hadiza da Hajiya Lubabatu suke yunqurin salwantar masa dasu dama uwarsu tabbas qiris ya rage rabon yarannan yayi kisa kuwa.





Daqyar ya fita daga dakin yana waiwayen yayansa da daidai da daidai saida kowa yaje yagansu Dr Hasina kuwa batasan sanda ta rungume Mainah Abdu ba tana hawaye tana cewa “ina roqon Allah ya azurtani da haihuwa nima kamar yanda ya azurtaku dasu don Allah Mainah kabani su ni zan dawo ma gdanku nake kula dasu" murmushi yayi yace “idan muka samu wasu zan baki amma wadannan bazan iya nisa dasu ba babban rabone daga Allah" Dad ne ya kira Mamy ya fada mata abinda yake faruwa saboda tsabar tashin hankali batasan sanda ta qunduma uwar ashar ba tace “yan uku Gidado Aishan ce ta haifi yan uku ya akayi ta haifesu?"…………









*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[2/18, 8:07 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_AD_*



*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*




*37*







Mamakine ya cika Dad yace “bangane ba wannan wacce irin tambaya ce?" Kit ta yanke wayar ya juya ya kalli mutanen dake gurin ga mamakinsa sai yaga Mainah Abdu yayi murmushi ya juya ya fice daga dakin gda ya wucce ya hadowa Samha kayanta kamar yanda fulani Amina da Dr Hasina suka fada masa.




Itakuwa Mamy tana kashe wayarta wayar fulani Hadiza ta kira tana dure duren ashariya tace “wannan ma ai iskanci ne yama zaayi ace Aisha ta haihu har yaya uku Ina wlh bazai taba yuwuwa ba dole saidai a sake lale yaya uku fa Hadiza" gaban fulani Hadiza ne yabada wani rass tace “kutmar ubancan yaya uku kuma duk na Abdu ne yayansu ne yaushe ma akayi auren da har zaace an haihu?" Katseta tayi da cewa “qyaleni Hadiza wannan bokan ya ruguzamin shirina gaba daya wai ba cewa yayi zai turo aljani ya tsinkar mata da jini ba kuma yasawa mijin mantau harsai jininta ya qare ta mutu yayanta su mutu kowa ma ya huta idan yaso saimu waiwayi waccan karfar matar uban nata da tasa ya aura to meyasa yayimin haka..." katseta fulani Hadiza tayi da cewa “tabbas an samu akasi wannan shegiyar yarinyar ta zame mana matsala kamar yanda kafirin mijin nan nata ya zamemin wlh na rasa ya zanyi da zuri'ar Amina musamman Abdu duk inda na biyu da sauri na shi saina tarar a guje ya kereni kawai mu zuba musu ido ni Ina ganin zaifi Lubabatu na fara tsoron yaron nan wlh har guba nabawa Abdu a Apple yaci amma bai mutu ba sai baqar wuya da yaci ya tashi..."




Katseta Mamy tayi tace “kinga dakata kada ki kashemin gwiwa nayi rantsuwa da nonon uwata kamar yanda na batar da Maryam uwar Aishatu na mantar da duniya labarinta iyayen da suka haifeta ma suka manta da ita na rabata da yarta Aishatu tun kafin a yanke mata cibiya na kadata duniya na dauki Aishatu na riqe naci kashinta naci fitsarinta nayi wahalar shekara ashirin da ita batare da ku kanku kunsan banice na haifeta ba sannan na juya qwaqwalwar ubanta ya manta da matar dana aura masa yayi auren sirri da ita ta haifa masa Aisha duk dan cikar burina guda daya tak a duniya to shakka babu wannan dalilin kadai ya isa yasa na shafe labarin Aishatu da yayanta harma da tsinannen la'anallahun yaron nan da yake amsa sunan mijinta idan zaki bini mu tafi tare ki biyoni Idan kuma gabanki ya fadi tun yanzu to ki kwanta ki huta amma ki sani ni Lubabatu takenane yar sa'a haba haba Hadiza nice fah maza nawa na kashe before nazokan uban Samha to wlh da Gidado da Aisha da tsinannun debabbun yaran nan guda uku da mijinta wato Abdu gaba dayansu rayuwata a tafin hanunsu take wannan ma kuskuren aikine kawai a yau zan diro Katsina kuma a yau saina aika yarannan lahira zan hada baki da likita a kashemin shegiyar yarinyar kowa ya huta dama qawata Barira tace min dan hakinnan dana Raina wato Samha idan nayi wasa saita tsonemin ido"




Kashe wayar tayi a fusace ta figi mayafinta ta watsa wayoyinta a jaka ta fice daga gdan a mugun guje har dakawa driven duka take tana cewa ya qara gudu so take cikin minti talatin taganta a Katsina
Allah ne kawai ya kaisu Katsina lfy tana zuwa kai tsaye palace hospital tasa driven ya wucce yana zuwa yayi parking ta fito a mota har tana gurgudewa ta shiga a guje tana shiga kafin takai shikuma Mainah Abdu yana fitowa karo sukayi kowanne yaja baya da sauri bude idonsa yayi tarr a kanta itama shi take kallo cikin wani matsanancin baqin ciki da taketa qoqarin dannewa tanason yin mgn murmushi yayi ya rigata cewa “kin iso kenan dama nasan zakizo kuma kedin nake jira saidai kuma kin makara My Aysha da yayana duka yanzunnan suka daga daga qasar nan zuwa wata qasar zaa kulamin dasu har zuwa lkcn da zasu samu kansu sannan mu dora wasan dake yanzu muka fara kada ki janye nima bazan janye ba nida dake zanga cikakken dan halak"




Wuccewa yayi ya barta a gurin a tsaye sororo cikin tsananin tsoro da mamaki saida yaje qarshen gurin sannan ya juyo yace “na barki lfy surukata" ji tayi kamar ya qara caka mata mashi a zuciyarta juyawa tayi a salube ta fice daga asibitin ta kira driven ta yazo ya sake daukanta daganan gdan sarautar ta nufa tana zuwa ta shiga sashinsu ta bude bangarenta ta shiga ta fada saman kujera a zafafe zuciyarta na tafasa ta jima a zaune ta rasa sanin abinyi miqewa tayi ta shige dakinta ta Kira wayar qawarta bugu biyu ta daga tace “akwai babbar matsala Barirah" nanta zayyane mata komai aikuwa ta qunduma uwar ashar tace “lallai kin sake yaron nan ya rainaki har kika bari yake iya caka miki mgn haka meyasa bazaki haukata shege ba yabi duniya Lubabatu matsawar kika qyale Mainah Abdu tare da Samha burinki bazai taba cikaba kina kallo fah ciwon cikin da mukasa aka tura mata da qarfin addu'ar sa ya tarwatsashi ya dawo kanki kikayi kamar zaki mutu saida mukaje boka ya karyashi duk wani sihiri da zamu tura mata indai ya fahimta kanki yake dawowa saboda haka yanzu shi yakama mu fara kawarwa kawar da wadannan yan tayin yayan da uwarsu yafi komai sauqi" ajiyar zuciya tayi tace “bantaba sanin kanki naja ba sai yau tabbas Abdu shine barazanata kuma matsalata shi yakamata na fara kautarwa daga doron qasa sai yayansa da matarsa subi bayansa amma tayaya zai tabu mutumin da aljanu ma tsoronsa sukeyi kinaji fah Boka Jegus daya kira aljaninsa zai turawa da tsinanniyar matar tasa a lalata cikin jikinta a gabanki aljanin yace bazai iyaba saboda sukansu aljanu suna tsoron hatsabibin mutum irin Abdu nifa inajin tsoron ko ya gane banice na haifi Samha ba saboda yanda yakemin baya nuna ya daukeni da muhimmanci ga wata shegiyar sara tashi ya gama cin mutunci na sannan yace min surukarsa"




Murmushi Barirah tayi tace “haba Lubabatu saikace bake ba Ina surukarki Aishatu mahaifiyar mijinki Gidado? Ina Umar Dandoki mahaifin mijinki? Ina mahaifiyar Samha Maryam matar da kika aurawa mijinki auren sirri yayi zaman aure da ita yayi Mata ciki har aka haifi Samha kika karbeta a matsayin yarki ta cikinki batare da kowa ya sani ba kuma kika batar da uwarta a duniya tsayin shekara ashirin babu labarinta? Lubabatu wadannan tunda suka shigo gonarki kin batar dasu kinga bayansu sarki Hassan baban Abdallah shine kadai ya gagareki to akanme zaki karaya akan wannan qaramin alhakin?"




Kamar tayiwa Mamy allura ta miqe tace “tabbas wannan haka yake dolene dukiyar Gidado da duk wasu kadarorinsa su zama mallakina dole ne na gyara dammara yaqi bazan taba sarayar da burina ba" saurin katseta tayi tace “amma fah saikin nutsu tun farko kikayi sakaci mijin yarki ya rainaki da kika nuna qiyayyarki a fili Lubabatu baacin naman maqiyi cikin sauqi saboda haka ki koyi boye qiyayya kuma ki koyi juriya ki dake ki shiga cikin hidimar haihuwar nan ayi dake kija Samha a jiki magungunan mata irin namu na Shuwa hada Mata a ciki zaki rinqa zuba mata asirin da aka baki tanasha yana ratsata ki mallaketa sosai ta yanda ko cewa kikayi ta kashe mijinta bazatayi miki musu ba in yaso ma hanya me sauqi saiki sanyata ta kasheshi da hanunta yanda babu me zarginki kinga riba biyu kenan dukiyar Mainah Abdu ta zama ta matarsa da yayansa to da daidai saiki aika yayan nasa sannan ki aika Gidado daganan sai itama Samha tabisu wannan itace way mafi sauqi da zamubi"




Wata uwar guda Mamy ta saki tace “Ahayyehhh nanaye saini Lubabatu duniya makwantar rikici kinyi taki kinyi ta yaro kuma nayi tame qaramin qarfin aminyar Barirah qulle qulle tabbas kin kawo shawara wannan abu anyi an gama rayuka shida zasu sheqa barzahu kuma duk bazasu wucce shekaran nan ba nagaji da zaman dukiyar nan a hanun Gidado dole ta dawo hanuna sannan shima wannan qaramin alhakin da aljanu ke tsoro to zamu gwabza dashi kamar yanda yace shege ka fasa ni Lubabatu na haifu cikin Jummala mai alagidigo kuma saina nuna masa shine shege ta hanyar aikashi barzahu amma wani hanzari ba gudu ba kinsan kamar yanda boka Jegus ya fada fah dole aiki bazai tafi ba sai an dorawa Gidado jinyar da bazai warke ba idan ba hakaba akwai matsala" dariya sosai Barirah tayi tace “kin damu da Gidado qaramin alhaki ki qyaleshi wannan shine yafi komai sauqi tunda yana kwana dake kema kinada matsala kinsani boka Jegus ya fada miki su irin Gdan sarautar nan basa tabuwa sosai saita hanyar matansu saboda Allah yayisu jarababbu ki bude masa kawai ya rinqa ci wannan qaurace masan da kikeyi kanki kikeyiwa illah shima wannan shegen yaron me qananun idanu kamar idon bura dole saidai mu fara binsa ta gindin matarsa don da ganin idanunsa akwai jaraba cikinsu"





Haka suka yini suna saqa da mugun zare hardai suka cimma matsaya yanzu damuwar Mamy itace ina su Samha suke wacce qasa aka kaita ita da yaranta tasan dai ko giyar wake tasha bazata taba iya tarar idanun hatsabibin mutum irin Mainah Abdu ta tambayeshi ba gashi tun safe take kiran wayar Dad yaqi dagawa saboda ba qaramin tashin hankali ta jefashi ba najin yanda hankalinta ya tashi dajin cewa yarsa ta haifa masa jikoki har uku ba dake layinsa International ne tunda suka sauka a qasar Egypt din yake ganin kiranta amma yaqi dagawa dashi da Dr Hasina ne sai fulani Amina da Mai martaba shikam danme da bin diddigin tsiya Mainah Abdu cewa yayi ya wakilta Dr Hasina amana akan yayansa da matarsa zaiyi wani aiki wanda yake na dole ne amma very soon zai shigo shima kulawa shugaban qasane yabawa Dad jirgi sukayi tashin gaggawa zuwa qasar Misran suka sauka a wani babban asibiti me suna Raudhatul Haqq kulawar da ake bawa Samha da yan ukunta ta musamman ce, kwananta biyu a asibitin ta fara motsawa amma bata bude idonta ba yaran kuma har yanzu suna cikin Inquivetoor anaci gaba da kula dasu saidai a fito dasu a basu abincin da magunguna a gyarasu a mayar dasu su fulani Amina sunga abu Abdu kiran Dad yace masa shifa kafa kada a rinqa jagwalgwala masa yaransa shima yananan zuwa a kwana na hudu ya diro qasar da magrib ya jima yana kallonta kafin ya tashi ya koma gurin yaransa mamakin girman da suka qara a cikin kwanaki hudun yakeyi sosai sai wutsil² sukeyi haka yasa aka fito masa dasu ya rinqa daukansu yanayi musu addu'a yana tofa musu yana hawaye tare dayi musu huduba Muhammad Ahmad da

Please Login or Register in order to submit comment