Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zulumi lkc zuwa lkc yana share hawaye.





Sai wajen azahar sannan Samha allurar baccin ta saketa ta fara bude idonta a hankali tana qarewa dakin kallo sauke idonta tayi akan Rahmah dake kallonta tana sharar hawaye sai lkcn abubuwan da suka faru suka fara dawo Mata hanunta take qoqarin dagawa amma ta kasa sai wani kuka me sauti data saki cikin kuka tace “da gaske ne ko Rahmah da gaske ne Abdul ya kawar min da budurcina da gaske ne ya ketamin haddi innanillahi wa Innah ilaihirraji'un wayyoh Mamy wayyoh Dad Allah ka isarmin ka cuceni Abdul ban mori komai a tarayyata dakai ba sai baqin ciki Allah ya isana......."





Tana mgnr tana kuka me tsuma zuciya daidai lkcn da Abdul din ya shigo dakin ya zuba idonsa akanta cike da tsananin kunyarta kawai sai ya juya saboda qunan da zuciyarsa takeyi bazai iya jure kallon Samha ba wata muguwar kunyarta yakeji da tsoron irin kallon da zatayi masa sarai yakejin tsoron kalamanta saboda yasan bazai tabajin masu dadi ba ya cuceta cutar da har abada bayajin wani zai kumayi mata irinta ciwo da radadin abun bazai taba gogewa a ranta ba baitaba jin haushin kansa irin yau ba bau taba tsanar kansa irin yau ba ya tsani rayuwarsa a matsayinsa na azzalumi Samha ta dade tana fada masa burinta akan budurcinta yaqi yarda da ita qarshe ma harshi da kansa yake fada mata bazai aureta a matsayin budurwa ba saidai ya aureta a matsayin bazawara ashe shine azzalumin dazai karya mata quduri “Allah ya isanki Samha Allah ya saka miki me zan baki dazai goge laifina a gurinki mezan baki a matsayin fansar budurcinki.....” tabashi yaji anyi ya juyo da sauri ganin Mansoor da Khamal yasashi share hawayen idonsa Khamal yace “ya kamata ka sanarwa likitan data karbeta tayi mata wasu dabarun da ciki bazai zauna ba inajin tsoron kada rabone yasa hakan ta faru bisa jagorancin Azzaluman abokanka Ja'afar da Nasir......"





*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[2/13, 8:51 AM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_AD_*



*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*




*21*



Kallonsa yayi baki sake murya na rawa ya shaqeshi yace “me...me kakeso kacemin kanada masaniya akan abinda ya faru kenan?" Janye hanunsa yayi daga wuyansa yace “ita qaddara ta riga fata wlh a gabana suka shirya plan dinnan jiya ina qoqarin zuwa na sanar dakai sai babata ta kirani a waya na koma gefe ina amsa waya bayan shigowar Nasir ya kawo maka lemon da suka zuba qwayoyin qara qarfin sha'awar me suna Signature da Vigor na gama waya na biyoshi da sauri amma kafin nazo harya fito daga dakinka yana murmushi yana cewa “kiyi hqr Samha yau zakisan namijin gaske yau zakiji abinda akeji badon komai ba saidon kankaro miki da darajarki tabbas barna ce zamu hada amma wannan barnar gyara ce wannan hanyar ce kadai zaki tsarkaka daga zargin da wannan shashashan masoyin naki yake miki"





Dafe kansa yayi yana kiran “innanillahi wa Innah ilaihirraji'un" mugun juya masa kansa yakeyi yanajin wani jiri yana daukarsa ya durqushe a gurin yace “Allah kabimin haqqina kai kadai zaka fitar dania gurin yarinyar nan" yanda zuciyarsa take tafasa yasashi tashi ya shiga motarsa ya tafi gda yaje ya kwanta shi dama ba lfy ce ta isheshi ba wani zazzabi ya rufeshi yana kuka kamar qaramin yaro yanata Istigfari yana rawar sanyi yana kuka mecin rai baisan da wanne ido zai kalli Samha ba idanunsa sunyi qananu su kalli tsabar idonta suce zasu bata hqr dole ya barta tayi masa duk hukuncin da take ganin ya dace dashi.




Itakuwa Samha takurawa Rahmah tayi akan dole sai sunbar asibitin a yau takeson barin garin Katsina ta tsani garin fiye da yanda ta tsani kanta a yau Allah ya isa kuwa Abdul yashata tafi cikin tifa hakanan kan dole Rahmah taje ta kira likitan tazo ta sake dubata Dr Hasina mutuniyar kirki me kishin yan'wanta mata haka ta rinqa tattalin Samha da bata hqr harda hawayenta tana fada mata jinta takeyi kamar yarta ta cikinta daqyar ta samu ta rarrasheta amma saida tayi mata alqawarin zatabar asibitin da ita ita kuma tace “tunda kunce service kukeyi anan iyayenku baanan sukeba to saidai kubini gdana ku zauna idan kinji sauqi saiku koma gdanku" badon Samha taso ba hakanan sukabi Dr Hasina gdanta anan taci gaba da kula da Samha sosai tare da bata shawarwari musamman da ta fada Mata auranta saura wata uku.




Satinsu biyu a gdan kullum Rahmah da Aunty Hasina cikin lallashin Samha suke saboda kullum cikin kuka take tana fadawa Allah ya saka mata abinda Abdul yayi mata tsanarsa takeji aduk wata gaba ta jikinta duk sanda ta tuna barnar da yayi mata takanyi tur dashi taji dama baa rubutoshi a cikin qaddarorinta ba a cikin sati na ukune sukaso barin gdan Dr Hasina amma ta hanasu ta zaunar da ita tana tambayarta tana cewa na hango wata matsalar yata kasalarki tayi yawa ya kamata ki shirya muje a dubaki kada muyi gyaran gangar auzinawa itadai Samha bata kawo komai ba ta shirya cikin wata blue din gown tayi rolling da dankwalin duk da ramar da tayi tayi kyau sosai amma har yanzu tafiyarta bata koma normal ba Dr Hasina tace a qalla zata iya daukan wata biyu kafin ta koma daidai hakadai take dan daddaburawa.




Suna zuwa asibitin Dr Hasina ta shigar da ita Lab tace taje tayo fitsari ta kawo mata taje tayo ta kawo mata ta debi jininta ta bawa ma'aikatan Lab din suka fita suka tafi office din Dr Hasina suna shiga motar Abdul tana shigowa asibitin yayi parking yaci gaba da bincikensa kamar yanda ya saba duk wani kalar hauka saida Abdul yayishi a asibitin lkcn daya dawo Dr Hasina ta sanar dashi iyayen Samha sunzo sun tafi da ita a lkcn shaqer Dr Hasina yayi yace “kika barta akanme zaki bari su tafi da ita ban nemi yafiyarta ba ban nemi afuwarta ba sannan ban fada mata sirrin zuciyata ba meyasa kika bari ta tafi tana fushi dani Dr ki taimakeni don Allah wlh sonta zai kasheni bansan inason Samha ba sai yanzu wlh bayin kaina bane magani abokaina suka zubamin kawai saboda na lalata rayuwarta na lalata tawa don Allah ki... Dr kice ta dawo muyi aure nasan tana sona..."




Duk da zafinsa da Dr Hasina takeji saida ya bata tausayi amma tayiwa Samha alqawarin bazata taba sanar dashi tana gurinta ba dole ta waske ta qwace daga hanunsa tace “toni mene bawa ma a ciki" zubewa yayi a gurin yana kuka me ban tausayi yace “kina cikin list kema ban yarda dake ba waima kinsan wayeni da zanke fada kina fada to ki tambayi kowa waye Mainah Abdu a masarautar Katsina" saida gaban Dr Hasina ya fadi amma dole ta dake ta zube tace “kayi hqr ranka ya dade banida wata masaniya a game da patient dinka an kirani gda akan nazo yarona babu lfy na fita da niyyar zanje na dawo nazo na tarar sun gudu...."





Daga mata hanu yayi yace “sakacinki ne koma mene" tun daga ranar kullum sai yazo asibitin yayi zagayensa sannan ya fita har tambayar Dr Hasina yayi wai bata bada saqo a bashi ba baisan inda zai nemeta ba kuma yanason ganinta ya fadawa me martaba aika² da yayi mata yace ya kawo masa ita tayi Istibra'ih a gdan sarautar sannan ta koma gdansu su nemi aurenta" jikin Dr Hasina a sanyaye tace “kayi hqr kaci gaba da addu'a idan rabonka ce zaka sameta amma ni banida wata masaniya game da patient dinka" tana fadin haka ta juya ta shiga wani daki da zata duba patience dinta saboda gudun kada ta shiga office ya biyota aikuwa tana tafe yana binta yanayi mata magiya daqyar ta bashi hqr akan zata tayashi binciken inda zai samu Samha hakanne yasashi hqr ya tafi.




Ajiyar zuciya tayi tace “qaraqaqa qaqa ya kamata ta bawa Samha hqr karta bari wannan damar ta wucce ta ta lura ba qaramin so Yariman masarautar tasu yakewa yarinyar ba" haka ta koma Lab ta karbi gwajin abindai da take zargin shine gabanta ya fadi sosai tace “ciki? Na shiga uku ni Hasina wai meyasa indai aka samu irin wannan cases din zaiyi wahala ciki be shiga ba?" Kallonta Dr Mabaruka tayi tace “bangane ba" ajiyar zuciya tayi saboda Dr Mabaruka batasan da case dinba kuma tasan surutunta da neman sunanta tsaf zata nemi Abdul ta fada masa, murmushin yaqe tayi ta nufi bangaren saida magani ta siyo wasu qwayoyi na zubar da ciki ta wucce tana zuwa “bata fadawa Samha qullin dake cikinta ba saida ta bare magungunan guda uku ta bata tasha sannan tace juya nayi miki allurar nan Emergency ce yanzu zata baro dashi wannan magungunan na rage zafin ciwon marar da zaki iya fuskanta ne" cikin kuka tace “Aunty Hasina kina nufin cikin Abdul ne a jikina..." Rufe mata baki tayi tace “karki wani damu cikin yan mintina zai fita daga jikinki tunda ba qwari yayi ba cikin sati uku ai ruwane nafiso ki zama normal Samha banason na barki da tabon abunnan daya faru ko kadan shiyasa kikaga na dage wajan nema maki mafita" tana kuka ta juya Dr Hasina tayi mata Allurar sannan tace “ba wani wahala zakisha ba dan ciwon marane kadan da baifi na period ba inma yafi kadanne" tashi sukayi suka tafi suka shiga mota tun kafin su isa gdan cikinta ya fara hautsinawa suna zuwa gdan ta shige ta kwanta a daki bayan tayi sallar azahar lkcn ne Dr Hasina take basu lbrn yanda sukayi da Abdul yau itadai batace komai ba amma tayi alqawarin ko ita Dr Hasina bazata bawa asalin address din gdansu ba so take suyi rabuwa ta har abada ita da Abdul ta tsaneshi tsana mara misali ko sunanshi bata qaunar taji wani ya ambata.




Ciwon marar be matsanta mataba sai dare cikin ikon Allah sai jini amma da dan qarfinsa hamdala Dr Hasina tayi tace “kinga kin tsarkaka bakida wani tabo na fyade a tare dake amma da ace na barku kun tafi lkcn da kika nace saikin tafi dinnan da yanzu ma baku gane da cikin ba sanda zaku gane yayi qwarin da idan aka tabashi zaa shiga hurumin ubangiji sai kuma ayi daban kwalo laifi cikin laifi amma kinga yanzu baikai lkcn da idan an zubar zaace anyi kisa ba" itadai Samha ciwon mararta bai barta tace wani Abu ba saida Aunty Hasina ta sake yi mata Allurar relief sannan ta samu dama dama ta miqe ta shiga bathroom ta sake gyara jikinta ta dawo ta kwanta Dad ne ya kirata yake fada Mata ya dawo daga Brazil din da yaje gobe zaizo ya ganta takuwa sanya masa kuka tace ita ta gama service yasan yanda zaiyi kawai Allah sarki Alh Sa'ad take yace Mata an gama indai kudi zasu iya to tagama service"




Washe gari kuwa da wuri ya gama yimata komai ya sanar dasu yarsa batada lfy shiyasa hakanan dai dake a 9ja ne aka yi duk me yuwuwa ya kirata yace yaje gdanta batanan ta kwatanta masa inda take yazo ya ganta ya rinqa latsata kamar rago yana magana cikin tashin hankali “Pretty na meye ya ramar dake haka ciwo kikayi baki fadawa kowa ba Mamynki tace idan ta kiraki bakya dagawa kina fushi da ita meyasa" fadawa tayi jikinsa tace “Dad yanzu nayi uwa a duniya amma Mamy bata sona ni Ina tantamar itace ta haifeni Dad duk wata kulawa da iyaye suke bawa yayansu Mamy bata bani tsayin sati biyu bata kirani taji lfyta ba bayan tasani duk safiyar duniya ina kiranku mu gaisa amma batayi tunanin meye yasa bana kiranta ba sai cikin satinnan sannan ta kirani wacce irin uwace wannan da bata damu da halin da amanar da Allah ya bata take ciki ba?"




Qara rungumeta ya qarayi yana bubbuga bayanta yace “kema Lovely kinsan halin Mamynki ki qara hqr kwana nawa ma ya rage ku rabu kema ki tafi naki gdan jiya mukayi waya da Mus'ab yake neman alfarmar a rage tsayin lkcn bikinku saboda tafiyarsa ta kama cikin watan da zamu shiga so naso nace masa aa saboda wani badaqala data taso a gdanmu nan Katsina akan aurenki da Mainah Abdu kamar yanda dokar gdan yake bama ba da aure a waje matsawar munada zaratan samari a cikin gdanmu so bandai san ya zamuyi dasu ba amma inasonki da Mus'ab baby naso mu wucce nakaiki kiga yan'uwanki amma wani kiran gaggawa ya sameni daga shugaban qasa saboda haka zamu wucce yanzu muje ku fara shirye² itadai batayi mgn ba saida taji yanayi mata rada a kunne yana cewa “me kikeso ayiwa likitanki na kula dake da tayi?" Ajiyar zuciya tayi dake daga ita saishi tace.




“mijinta ya mutu shekara bakwai bata da da saboda mijinta baya haihuwa haya takeyi a wannan gdan gashi gdan ma ya tsufa da yawa ka siya mata gda kuma kayi mata wani abu a cikin gwabnati sannan idanma zaka aureta zanyi farin ciki Dad tasan sirrin da Mamy na bata saniba a kaina kuma inada yaqinin zata riqeni amana ko babu ran Mamy na tanada sauqin kai sosai"







*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[2/13, 2:55 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_AD_*



*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*




*22*




Kallonta Dad yayi yayi murmushi yace “meyasa kikace na aure ta pretty?" Kawar dakai tayi tace “saboda ta cikemin gurbin da mamy na ta kasa cikemin Dad ina buqatar uwar da zata dauki lamarina da muhimmanci duk da nasan baa taba sakewa tuwo suna Mamy itace mahaifiyata amma zan samu kulawa ta wasu bangarorin" mikewa yayi ya ruqo hanunta yace “zan duba yuwuwar hakan Pretty farin cikinki nafi buqata fiye da komai tayi murmushi daidai lkcn da Aunty Hasina ta shigo da kayan abinci ta ajiye tace “yadai naga kun miqe Samha badai har tafiyar ba" ajiyar zuciya tayi tace “na gde da kulawarki gareni kece mutum ta biyu da bazan taba mantawa dake ba Aunty" murmushi tayi ta janyota jikinta wasu hawaye suka zubo mata tace “inajinki kamar yata ta cikina Samha koda kin tafi kada ki manta dani don Allah ki daukeni uwa a gareki kinji" ta juya ta kalli Alh Sa'ad tace “Alh zaka daukemin yata bazanso hakaba saidai dan babu yanda zanyi kaine me iko akan komai" sukayi dariya dukkansu sannan sukaci abincin Samha tana bawa babanta abincin a baki shima yana fata soyayyar tsakanin uban da yarsa tayi mugun burge Dr Hasina taji dama ahlinta ne haka.




Bayan sun gama cin abincin Dr Hasina da Rahmah suka rakasu tsohon gdan Samha suka debi kayanta sannan sukayi sallama suka tafi ita kuwa Rahmah tayi uwa Dr Hasina cewa tayi bazata zauna anan ita kadai ba dole sai gdanta ta koma.
Sai dare sosai suka shiga Abuja dake tafiyar mota ce suna zuwa Samha ta tarar gdan babu kowa wai Mamy ta tafi Maiduguri yar yayarta ta haihu dakinta ta shige tayi kwanciyarta duk sanda ta tuna yanzu itafa ba budurwa bace sai tayi kuka kamar ranta zai fita ta qara jawa Abdul Allah ya isa.




Haka kwanaki sukayita tafiya saida Mamy tayi sati ta dawo lkcn Samha ta qara warwarewa cima me kyau ga kulawar mahaifinta har tayi qiba tayi shar da ita babu abinda takeyi saidai tayi wanka taci abinci tayi sallah a cikin kwanakin ne Dr Mus'ab ya kirata sau daya yake fada mata zaizo zasuyi wata mgn akan shirye²n bikinsu tunda Dad ya yarda an sauko dashi yanzu haka bikin saura sati uku lkcn da yazo ta jima a daki a kwance kafin tayi qarfin halin miqewa ta fito a garden suka zauna suka gaisa tun daga yanayinta ya fahimci akwai damuwa a tattare da ita ya kalleta sosai yace.





“Nazo da tawa damuwar kuma sai na fahimci kamar taki tafi tawa Samha meye yake faruwa ne kusan sati hudu kenan banajinki a yanayin dana saba jinki kin daina sakin jiki dani kin daina bani kulawa sai na kiraki sau uku baki dagaba meyene?" Hawayen da take boyewa ne suka gangaro mata tace “bansan wanne kallo zakayimin ba idan na fada maka ainihin abinda ya faru Mus'ab rayuwata taqi tafiya kamar yanda ta kowa take tafiya Mus'ab Abdul yayimin tabon da bazai taba gogewa a zuciyata ba na tsaneshi Mus'ab na tsani Abdul wlh na tsane don Allah Mus'ab ka janyewa aurena" dagowa yayi ya kalleta da sauri yace “kamar ya na janyewa auranki Samha?" Cikin kuka tace “ina nufin ka hqr dani kace da Dad ka fasa aurena wlh nafi buqatar rayuwa ni kadai bansan irin kallon da zakayimin ba duk ranar daka fahimci nidin ba budurwa bace wani ya lalata min budurcina ta hanyar zalumci Mus'ab don Allah kace ka fasa..." Rufe mata baki yayi memakon taga alamun bacin rai ko damuwa a tattare dashi sai taga yayi murmushi yace “abinda yasa kike qara burgeni kenan Samha qarya bata cikin tsarinki wlh tun washegarin ranar da abin ya faru aka turomin saqo da wata number da yake nunamin abinda ya faru dake a ranar saida nazo Katsina haka na gama bulayi na ban samu ganinki sai bayan na gaji na koma na kama hotel ina hutawa sannan saqo ya kuma shigowa wayata akace min dama kayi hqr Samha tayi maka nisa Samha a cikin saqon har gargadina akayi cewa kada na kuskura nace zan aureki ke matar Yariman Katsina ce sannan aka qara tabbatar min cewa harma cikinsa gareki kuma yanason kayansa nayi qoqarin bayyanawa Dad wannan saqon sai kuma naga rashin dacewar hakan saboda ya kamata ace ya zama sirrin mu saboda mune zamu rayu tare kodan rufuwar asirin yayanmu amma wani abu nima da yake damuna har yasa na sauko da aurannan namu Samha Hajiyata tace saidai na aureku ku biyu keda yar qawarta bama wannan ba Samha abu daya dana boye miki shine inada mata da yarana biyu...."





Dagowa tayi da sauri cikin tsananin mamaki tace “kana da Mata harda yara biyu amma Sir baka taba fadamin ba meyasa ka boyemin hakan..." Saurin katseta yayi da cewa “aa ba haka bane lkcn dana fara neman auranki banida mata mun rabu da ita so wata uku kenan data dawo gdana itama Hajiya ce tasa na dawo da ita wai a cewarta dana auro mata ke da muka hadu ADANDI gara na da Maryam matar data nemi kasheni kawai saboda taga hotonki a wayata".....




_Kuyi hqr da wannan sisters_ 🙈🙈





*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[2/13, 8:26 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_AD_*



*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*




*23*




Miqewa tayi ta nufi cikin gdan yayi saurin shan gabanta yace “ki fahimceni Samha kada kiyi fushi saboda gudun irin wannan yasa na boye miki gsky" tsaya ta saurareshi ba ta shige gdan daidai lkcn da Dad da Mamy suke sakkowa daga sama Dad ya tareta da sauri yace “lfy meye ya faru Aishatu?" Cikin kuka tace “na hqr da dauren Dad wlh bazan aureshi ba Dad ya yaudareni ya munafurceni dama Abdul ya fadamin Mus'ab yana boyemin wasu abubuwa Dad kabashi kudinsa don Allah Dad kada ka takuramin na aureshi...."



Riqeta Mamy tayi tace “Waime yake faruwa ne meye ya faru tsakaninki da Mus'ab din?" Cikin kuka tace “yanada aure Mamy kuma wai mu biyu zaya aura yanzu Dad Mamy Mus'ab bashida gsky" wata uwar zabura Mamy tayi tace “yana da Mata kuma ku biyu zai aura kambu wannan rashin mutuncin ba anan ba wlh bazai yuwu ba" shikam Dad zama yayi yana nazarin abun bai iya cewa komai ba ya miqe ya fita ya tarar da Mus'ab a tsaye ya kama hanunsa yace “Aishatu tazomin da wani zance na yarinta Mus'ab mene gskyr lamarin nan?" Sunkuyar dakai yayi alamun rashin gsky ya fara sosa kai yana zayyano masa kamar yanda ya fadawa Samha gwauron numfashi Dad ya ajiye ya jinjina kai yace “shikenan kaje zan nemeka"




Yana fadin haka ya juya ya shiga gdan lkcn Samha ta shiga daki so Mamy a tsaye tanata huci ta tareshi tace “ya kukayi dashi?” ajiyar numfashi yayi yace “abinda ke akwai kenan" kallonsa ta kumayi da sauri tace “kawai ka mayar masa da kudinsa tunda dama gobe ake shirin kawo lefe sai kawai ya hada ya kaiwa waccan din amma yata bazata iya wannan auren ba Mata biyu ita ta uku ina laifinma daya ita ta biyu Ina da sake wlh da sake Dad bafa zai yuwu ba nifa idan babu dama yaronnan Na'im ya dawo satin daya wucce ma har tsaraba ya kawomin da kuma atamfofi har uku kawai ka bashi dama ya turo ayi mgnr amma wlh yata bazata taba auren irin Gdan sarautar Katsina ba na tsani ahlin Sa'eed kuma azan taba hada jinina dasu ba..."




Dafe kuncinta tayi da sauri saboda baqon abinda bata taba sani ba a gurin mijin nata ya nunata da yatsa yace “kina haukanki Lubabatu nine da dangina muke da iko da Aishatu bakeba kuma daga rana irin ta yau zan fara gwada ikona akanta bandama rashin kara irin taki harni zaki kalli tsabar idona kice bakyason dan dan'wana wanda mukazo duniya tare to bari kiji da Sa'eed da Sa'ad abu dayane kuma dole ki hqr da tsarin masarautarmu don bans tare da masarauta ba yana nufin nabarta kenan ba so Samha ta Mainah Abdu ce kuma tunda abin naki yazo da rashin mutunci wlh babu abinda zaa canza yanda akasa da Mus'ab haka zaayi da Abdu ko kinaso ko bakyaso ni dake maga wanda zaibi wani" juyawa yayi ya fice daga gdan zuciyarsa na tafasa yana fita ya kira Mai martaba ya sanar dashi abinda ke faruwa ya tura masa number waliyin Mus'ab a take Mai martaba ya kirashi ya sanar dashi shine waliyin Aishatu yanason ganinsa washegari kuwa sukaxo garin Katsina sosai sukayi mgn ta manya dole Mai martaba yace to babu komai amma fah yarinya tana neman canza raayi saboda haka suzo sati me zuwa zai daura auren Samha da Mus'ab wannan abu ba qaramin citta yabawa Mus'ab ba nandanan ya fara shirye²nsa.




Shikuwa Abdul tunda ya rasa Samha ya shiga wani hali lamarin har tsoro ya fara bawa Mai martaba duk ya susuce bashi da aiki sai kuka yaje garin Abuja yafi sau goma haka zai gama yawonsa ya dawo duk ya rame yayi baqi bashi da aiki sai tunani yakan kulle kansa a daki ya bai leqo ko farfajiyar gdan sarautar ba Fulani Amina ta shiga damuwa da lamarin dan nata da soyayya take azabtar dashi gashi baimasan inda zai samu yarinyar da yakeso ba yauma suna zaune ta kawo masa ziyara dakinsa kansa yana saman cinyarta tana shafa sumarsa tana share masa hawayen fuskarsa yace “Fulani Samha tasoni fiye da duk yanda kike tunani ta dauki amanar kanta ta bani ta yarda dani kuma ta nunamin qauna amma naqi yarda da soyayyarta gareni naqi gasqata gskyrta yanzu gashi ta tafi ta barni wlh fulani da nasan inda Samha take zanje tayimin duk hukuncin da take ganin ya dace dani indai zata aminta ta aureni wlh bazani iya rayuwa da kowacce mace ba idan ba Samha ba ita nakeso itace burina fulani naqita saboda ina tunanin bazan taba samun budurcinta ba sai gashi da kaina na rabata da budurcinta a lkcn dabai dace ba na cutar da ita yanzu kallon danakeyi mata a baya shi mijinta zaiyi mata idan ya gane itadin ba varging bace meyasa taqi ta bani damar gyara barnar da nayi da kaina?" Numfashi Fulani ta sauke tace “na fada maka kaci gaba da addu'a idan Samha rabonka ce zatazo gareka ko kai kaje amma kayi qoqarin fitar da mata kasan halin mahaifinku tunda yariga ya sakoka a gaba to saiyayi maka garama ka kawo da kanka kafin ya waiwayeka nasan yanzu hidimar bikin Gimbiya Aysha ne ya dauke masa hankali amma tabbas zai waiwayeka" ajiyar zuciya yayi ya share hawayensa yace “gobe zan sake komawa Abuja idan na dace na sameta zan dawo idan ban sameta ba zan wucce England zanyi wani aiki na wata

Please Login or Register in order to submit comment