Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

furta mata kalmar nan sai jikinta yayi sanyi tausayinsa da tausayin kanta abinda wanda takeso ya kasa yi mata a kenan sadaukarwar da Abdul ya kasa yimata a rayuwa kenan gata Dr Mus'ab yayi mata yana sonta a duk yanda take kalmarsa kenan kullum.




Wasu hawaye ne suka zubo mata tace “yaushe zaka taho?" Ya fahimci damuwa a muryarta don haka ya saisaita murya yace “yanzu wanka kawai zanyi na taho amma naji damuwa a muryarki meye ya kawota cikin rayuwar matata?" Ajiyar zuciya tayi tace “soyayyarka gareni itace take sanyayamin jiki da kuma bani mamaki ka tayani da addu'a Allah yasa nasoka kamar yanda kake sona Sir" numfashi ya sauke yace “ta daina baki mamaki kinji my wife ganinan zuwa yanzu ki tanadarmin breakfast dakanki nakeso kiyimin saboda ki fara samun ladan aure tun yanzu" murmushi tayi tace “angama ranka ya dade" sukayi dariya tare da ajiye wayoyin a tare.......







. *UMMUH HAIRAN CE...* ✍🏻
[2/11, 2:59 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_AD_*



*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*




*15*




9:00am Mus'ab ya sauka a garin Abuja lkcn ta gama shirya masa breakfast din a dinning din falon baqi ta koma dakinta tayi wanka ta sheqa kwalliyar ta cikin wani Lagos less purple mai masifar kyau da tsada wanda akayiwa dinkin riga da siket tayi kyau matuqa Mamy ce ta daura mara dankwali ta yafa mayafi purple komai nata purple ne Idan kuka dauke sarqa da dan kunnen azurfar datasa ta dauki zobbanta tasa ta dubi yatsunta wanda Abdul yasa mata ranar da zasu rabu shita zubawa ido tana kallonsa tana tuno kalamansa na rana Samha ki qaddara a ranki yayanki Abdul yana sonki komai nufine na Allah amma inaji a jikina zamu rayu cikin inuwa daya koban aureki yanzu ba wataran zamu kasance tare tabbas alaqata dake bazata tashi a banza ba akwai wani boyayyan abu tsakaninmu damu bamu sani ba"




Shigowar Mamy ne yasata janye idonta daga kan zoben ta janyota jikinta tace “dana yana jiranki a parlourn baqi yanzu idan kin tafi shikenan sai munzo Imo State gurinki zanyi missing dinki Pretty amma babu komai watarana ma sainayi watanni banganki ba kinacan gurin mijinki ko?" Ta fada tana dago mata da fuskarta sukayi murmushi lkc daya tare dayiwa juna kiss ta kama hanunta suka fita ita ta yafa mata mayafin sannan tayi murmushi tace “masha Allah kyakkyawata Allah yaci gaba da tsaremin ke kinji ki kula don Allah banason qawance da yayan talakawa da zasu dora miki ciwon kai"




Itadai daga kai kawai tayi tarasa meyasa Mamynta bata qaunar talaka bayan tasani har baban Mamy ya rasu wato kakanta a gdan darni suke a Maiduguri sai bayan rasuwarsa Dad ya gyara musu gdansu.
Shiga parlourn tayi da sallamarta ya dago fuskarsa ya zuba mata ido yana murmushi yace “masha Allah tsarki ya tabbata ga ubangijin daya halicci wannan mata tawa kyakkyawa" murmushi tayi tayi qasa ta rusuna tace “ina kwana" dariya abin ya bashi sosai wai yau shi Mus'ab shine Samha take yima ladabi haka kamar wani ubanta harda rusunawa ta gaisheshi.




Dagota yayi yana murmushi ta zuba masa ido yana da kyau daidai nashi shima yanada haske da manyan idanu saidai bashi da dogon hancin sosai lebensa yanada dan fadi kadan baqi sosai kamar wanda yakeshan sigari amma halitta ce hakan don ko ashana bai taba qartawa ya zuqa ba lumshe idonta tayi tare da janyewa ta koma ta zauna tana hango fuskar Abdul dinta fari tas kyakkyawa me yalwar dogon hanci da qananun lumsassun idanu lebensa jane sosai sai gashin girarsa me gazarzar yanada zara-zaran gashin ido irin nata saidai ita idanunta manya ne.




Iskar da taji ya hura mata a idanunta ne yasata dawowa hayyacinta tayi ajiyar zuciya tare da jan flat ta fara zuba masa cheeps din ta hada masa ta zuba masa kunun mardan da Mamy tayi masa ta tura masa ya dauka yakai mata bakinta noqe kafada tayi yayi murmushi ya fara cin abincin yana yabawa da dadinsa shigowar Dad ne yasata miqewa ta nufeshi ya buda mata hanunsa ta shiga yayi kissing tsakiyar kanta yace “zamu tafi saikun taho mu mota zamu hau" ajiyar zuciya tayi tace “shikenan Dad zamu rigaku zuwa yau zakaga My Abdul dina" murmushi yayi ya kalli Mus'ab daya lura mgnr tata batayi masa dadi ba yace “ai yace bazai samu damar zuwa ba munyi waya dashi jiya yayan naki akwai shiririta" yana fadin haka ya fice.




Suna gama cin abincin suka miqe driver yakaisu airport suka hau jirgi sai Kanon dabo suna zuwa driven gdansu Dr Mus'ab yazo ya daukesu suka nufi cikin makarantar kamar hadin baki shima Abdul sun shigo shida Manson shine yake driving din zuciyarsa tana cike da farin cikin ganin Samhar saboda mugun kewarta yakeyi da tarin maganganu a bakinsa da shikadai yasan irinsu lkc daya motocin sukayi parking hakanan yaji gabansa yana faduwa ya zuba idanunsa kan motar da tayi parking kusa da tasu Dr Mus'ab ya bude ya fito yana dariya ya zagaya ta saitin inda Samha take ya bude mata gaban Abdul ya qara bada wani rass yana kallon qafarta data fara zurowa kafin daga bisani ta fito gaba dayanta wata uwar zabura yayi yace “Sam...Samha itace wlh Samha ce Mansoor da gaske auren mutumin nan zatayi?" Wani uban tsaki Manson yaja yace.




“To Ina ruwanka da wanda zata aura tunda dai bakai bane Mainah Abdu kace bakaso ta hqr ta cireka daga zuciyarta har ta bawa wanda yake sonta dama ya fito zasuyi auransu na qauna don Allah dubesu fah kai salon bai burgeka ba da gani kasan Allah yayi mawa yarinyar nan sauyi...." Wani uban mari ya zafga masa yace “zanci durun uwarka Mansoor ficemin daga mota ka fice nace...." Dariya sosai Manson yake ya bude motar ya rufe masa ya leqa ta window yace “kadai bi a sannu matar wani ce tariga tayi maka nisa" kifa kansa yayi a sitiyarin yana fadin “ Innanillahi wa innah ilaihirraji'un oh my God" yana mgnr zuciyarsa na wani irin tiriri gashin jikinsa ya wani miqe saboda bala'in kishi nandanan qananun idanunsa suka qara qanqancewa suka kada sukayi jawur jikinsa har wani rawa yakeyi.




Ita kuwa Samha tunda ta dira a farfajiyar B.U.K take rarraba ido taga ta inda Abdul zai bullo amma babushi babu alamarshi wata sabuwar qaddara lkcn dataje amsar posting letter dinta saitaga an turata Katsina daga ita har Rahmah sosai iyayenta da masoyinta Mus'ab da Rahmah sukayi murna da sauyin da aka samu saboda dama bason zuwa kudun sukeyi ba amma ita haka kawai tunda tagani gabanta yake faduwa ta rasa dalili daga qarshe dai ta alaqanta hakan da cewa saboda asalinta ne da bata sani ba sannan garin masoyinta ne “shi ko Ina aka kaishi?" Tambayar data yiwa kanta kenan amma batada amsa hakanan ta yini raba ido domin ganinsa amma yaqi bari tagansa ta wucce ta gaban motarsa yakai sau uku yana kallonta haushin ganinta da wani ya hanashi yimata mgn yasan da alqawarin da yayi mata na idan sunzo zaije su gaisa da Dad dinta saboda yanda ta nuna tanason hakan amma kishi ya hanashi cika Mata wannan alqawarin ta kirashi a waya yakai sau goma amma bai daga ba da haushi ya ishetama jifa tayi da wayar ta koma ta kwanta jikin Dad dinta tace “yaqi dagawa Dad yaqi zuwa ku gaisa Dad kace zaka Saudi don Allah kayimin dawafi Allah ya mantar dani Abdul a rayuwata kowacce alfarma na nema a gurinsa bayayimin saboda ya tsaneni" Mamy ce tace “inda kinsan yanda na tsani yaron nan Samha dakin daina mgnrsa a gabana bantabajin kince yasaki farin ciki ba kullum quntata miki yake amma dake bakida hankali kinqi mantawa dashi"





*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[2/11, 2:59 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_AD_*



*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*




*16*




Kallon Mamy tayi tace “wlh Mamy bayin kaina bane addu'a kawai nake buqata daga gareku” haka iyayenta suka hadu sukaita rarrashinta hardai suka samu ta hqr gdan da Dad ya siya a Kano anan cikin unguwar sallari nan suka sauka ita kuma Rahmah ta tafi gda kwanaki uku tsakani Dad ya gama mata shirinsu tsaf har gda sukaje suka dauki Rams suka wucce garin Katsinan dikko dakin kara kunya gareku ba tsoro ba saida Dad ya gama yi musu komai sannan sukayi sallama a kusa da camp din ya kama musu gda ya zuba musu komai na buqatar rayuwa gda sosai ya tsara musu kamar na matar aure.




Saida sukayi hutun kwana biyu sannan suka fara zuwa camp din itadai Samha tunda tazo garin Katsina take fama da faduwar gaba haka suka yini a camp din sannan sukaje makarantar da aka turasu.
Sun fara aiki gadan² a cikin sati biyu rayuwar Katsina ta fara yimata dadi Dad yazo ya kawo mata ziyara shida wani mutum da yace mata qaninsa ne nan mutumin yake fada mata akwai yaronsa daya da yaron babban yayansu suma zasuzo dan babban yayan nasune baiji dadiba shiyasa basu fara zuwa Camp din ba dake Samha ba sanin dadin zumuncin tayi ba bata wani nuna damuwarta da yayyannata da akace zasuzo campus din suyi aiki tare ba sukayi sallama suka tafi tafiyarsi da kamar minti talatin suna zaune akan wani dakali anata yiwa yan bautar qasa trainning suna hira da Rams akan bikin Samha suna tsara yanda abubuwan zasu kasance kamar daga sama taji sallamar Abdul da sauri kuma cikin mamaki ta dago kanta idonsu ya sarqe da juna yayi mata murmushinsa me tsada yace “My Samha kin bani ciwon kai sosai har saida nayi jinya” wani mugun kallo da take masa shine yasashi kallon jikinsa sosai Manson dake qarasowa yace “salon takun qaunarku dabanne inason ganinku tare matsayin ma'aurata wlh amma kayi sakaci wani ya rigaka" miqewa tayi zuciyarta na tafasa wani haushinsa takeji baa taba yimata rashin mutunci irin wanda Abdul yayi mata ba ta tsayar da mahaifinta ta takura masa sai yazo wajen Indection dinsu kawai saboda ta hadasu su gaisa amma ya watsa mata qasa a ido har yanzu idan ta tuna wannan abun bata sanin sanda hawaye yake wanke mata fuska.




Gurin motarta ta nufa ta bude zata shiga ya biyota da sauri ya riqo hanunta ya hadata da motar ya dago fuskarta da idanunta yake zubar da hawaye ya matso sosai har jikinsa yana gugar nata yanda ya kafeta da idone yasata lumshe nata bata ankara ba kawai taji harshensa saman kuncinta yana yawo dashi yana lashe hawayen nata ya hadeta sosai a jikinta tanajin yanda yake sauke ajiyar zuciya daqyar ta iya tureshi ta shige motar ta zauna shima shiga yayi da sauri ya zauna a mazaunin driver yace “nayi tunanin zakiyi mamaki da kikaga an dawo daku Katsina maimakon Imo da akayi niyyar turaku" dagowa tayi ta kalleshi cikin mamaki tace “kanada masaniya ne akan dalilin?" Murmushi yayi yace “nine na shirya komai saboda bazan iya barinki kije garin da bakida kowa ba bakisan kowa ba zuciyata bazata huta da tunaninki da halin da kike ciki ba amma yanzu kinga hankalina kwance"




Wata iska ta furzar me zafi tace “wannan ba huruminka bane kuma banji dadi ba ban gode ba" murmushin yaqe yayi yace “har yanzu kina sona meyasa kika zabi dauko wani kisashi a gurbin da nake tunanin wataqila zai zama nawa meyasa kika zabi rayuwa da wani namiji bani ba Samha kinsan yanda nake jinki kuwa a Raina...." Daga masa hanu tayi tace “don Allah banason mgnr banza Abdul dane kake da gurbi a zuciyata amma banda yanzu course na samu wanda yafika yake sona tsakani da Allah badon tunanin mezankai masa mezai samu a jikina ba"




Wani kallo yakeyi mata wanda ta rasa gane menene yake nufi kawai sai taji ya murda key din motar ya kunna ta ya fita daga Campus din batace masa qala ba har suka shiga wata unguwa G.R.A ce da babu yawan jama'ar a cikinta yayi horn jikin wani gda aka bude ya shiga yayi parking ya bude ya fita itama ya bude mata amma tayi zamanta ta shareshi zuciya gareshi kamar kuturu ya fincikota da qarfi ya figeta ya nufi qofar shiga gdan da ita ya bude suka shiga wani bangarene qarami dakine kawai da parlour sai dinning ya zaunar da ita a kujerar ya tsuguna a gabanta ya dago kanta yace “bakisanni bane Samha bakisan yanda na tsani wannan banza malamin da kike shirin aure ba wlh koda har yanzu zuciyata ta kasa gasqata gskyrki amma bazan taba so ace na rasaki ba kada kiyi aure Samha ki bari lkc yana zuwa da zamu kasance tare" wasu hawaye ne suka zubo mata tace “me kakeso nayi maka bayan wanda nayi maka a baya kanaso naci gaba da yaudarar kaina akanka Abdul kanaso naci gaba da wahalar da kaina a kanka bayan nasani bani kadai nakeda haqqi akan kaina ba iyayena ma sunada haqi a kaina saboda Ina roqonka ka fita cikin rayuwata ka qyaleni nayi rayuwa da wanda qaddara ta zabamin wlh inason Mus'ab saboda yana sona da qoqarin yaga ya farantamin sadaukarwar daka kasa yiwa soyayyata ita yayimin ya yarda zai rayu dani a duk inda nake kuma nima na amince zan rayu dashi a haka zan bashi farin ciki zan mallaka masa abinda na dade ina tanadinsa ruwa da iska zafi da sanyi da rudin samarin jami'a baisa na yarda na sallama shi ba zan aureshi Abdul kuma zanyi masa biyayya kamar yanda ka sanar dani kuma ka koyar dani a matsayinka na malamina"




Miqewa tayi ta dauki key dinta daya dora akan site table din dake kusa dashi ta juya zata fita yayi saurin riqota yace “ki saurareni don Allah wlh sonki na azabtar dani Samha na yarda zan aureki a haka...” saurin rufe masa baki tayi yabi zara²n yatsunta da kallo tayi wani murmushi me ciwo tace “ka daina Abdul sau daya tak nakeba da so kaina fara bawa kace bakaso Abdul duk wanda ya qika a fari ai yariga ya qika wlh koda ace duniya zata hadu kan na canza zabi to zan zabi wani amma bakai ba sanda nasoka da aure nasoka amma yanzu banasonka Abdul" baki ya saki yana kallonta lallai akwai rikici a gaba wai shi Samha take kallon tsabar idonsa take cewa batasonsa da aure Samhar da take kuka saboda soyayyar sa Samhar da har asibiti ta kwanta saboda shi amma yau itace take fada masa haka meyasa bata qisa tun farko ba sai yanzu daya fara qoqarin tursasa zuciyarsa ta yakice zargi ta sota sauran lbrn sai sun hadu a matakin qarshe meyasa take qoqarin nuna masa bashida muhimmanci a gurinta yanzu kamar da tana nufin ya gama yimata amfanin da takeso yayi Mata kenan ta watsashi a dozvin?




Bai ankara da fitarta ba saida yaji tashin motarta ya fito da sauri amma kafin ya ida fitowa harta fice daga gdan duk da batasan garin Katsina ba haka tayita kurdawa har takai kanta gdanta zuciyarta cunkushe da tunanin rashin kyautawarta gareshi amma data tuna a baya lkcn da take cikin giyar sonsa take neman daukinsa watsi yayi da ita ta rintse idonta tana tuna irin marin da yayi mata ranar data furta masa kalmar so kalamansa na ranar suna dawo mata “me zanyi dake karuwa ballagaza wadda batasan darajar kanta ba yama zaayi kice kinaso na nace ina soyayya dawa jahila irinki wannan ma ai wulaqantani kikayi Samha me zance da iyayena a ina na samoki ADANDI?" Wani uban birki taci wanda yakusa sata hatsari ta buga kanta a jikin sitiyari ta bashe da kuka tana qara tariyo kalamansa na qarshe da suka girgiza duniyarta “wasu sun qwaquleki sun tsotseki sun sanya dick dinsu cikin Varginia dinki Samha sannan ni kuma nazo na aureki a matsayin budurwa dama zaki sassauta ki karbi sadakin bazawara da nayi Manerge dake amma bazan taba auren budurwa irinki nace na auri budurwa ba ke bari kiji Samha a tsarina ko bazawarar da aka taru aka shafa fatiha namiji daya ya wudata ya shigeta yaji dadinta za dacinta bazan taba aure ba saboda inason gaban matata ya zama sirrina ni kadai Samha dama namiji daya ne yasanki da da sauqi amma a yanda yanayinki yake nunawa maza sunfi dari sun raba cinyoyinki sun shiga jikinki sunji dadin dake tattare dake ni'imarki duk sun kwashe to me zaki kawomin gdana a matsayina na mijinki?"




Wani sabon kuka ta saki tana jinjina girman qiyayyar da Abdul yake mata da har yake danganta ta da karuwanci qazafi Abdul yakeyi mata fa tunda baitaba kamata ba a fili tace “ Hasbunallahu wa ni'imalwakil" tafi awa daya a gurin kafin ta iya settling mind dinta taja motar ta koma gda tana zuwa ta fada bandaki tayi wanka tayi sallolinta ta koma ta kwanta tare dayiwa zuciyarta alqawarin duk wata qofa ta soyayya zata kulleta tsakaninta da Abdul zumuncin ma idan da hali a daina tunda dama ita ta qirqirar musu shi ba kamawa yayi suyishi dole ba.




*****



Haka kwanaki sukayita tafiya rayuwa camp akwai dadi a gurin Samha saboda ita dama Allah ya halicceta dason wasannin motsa jiki hakanan Idan sun fita sun dawo zasu samu guri na musamman suda wasu abokan karatunsu suyita wasanninsu suna daukewa juna kewa sometimes saidai ya samu guri ya zauna ya rinqa hangenta daga nesa saboda yawan furta mata kalmar so da yakeyi yana neman karya Mata zuciya yasa ta datse igiyar zumuncin dake tsakaninsu badon komai ba saidon gudun shiga haqqin Dr Mus'ab da yake iyakar qoqarinsa wajan ganin ya sanyata farin ciki ya mayar da hanyar Katsina kamar Fagge da Nassarawa L.G.A baya kwana uku cikkaku sai yazo ya yinar mata anan yake fada mata ya samu admission a Oxford University zaije yayi Masters dinsa amma yafiso su tafi tare tunda yanzu sunci watanni uku saura uku yana ganin tafiyar zatazo daidai da bikinsu.




Yauma ya kawo mata ziyarar bazata batare da tayi tsammani ba da yake wayarta a hostel din da suka kama saboda canza kaya ta barta wata copper ce tazo tace “kene Samha Sa'ad Dandoki" daga mata kai tayi tace “eh nice" nan ta sanar da ita anason ganinta ta nufi gurin da yayi parking daidai lkcn motar Abdul da abokansa ta shigo yaci burki ganin ta bude motar ta shiga ya zuba mawa motar ido zuciyarsa na tafasa yace “kun gani ko na fada muku Samha bazata canza ba yanzu waye wannan din yazo gunta mene alaqarta dashi me zasuyi a cikin motar kunga fah fitama zasuyi" yana fadin haka yaci wani uban ribbers yabi bayan motar Dr Mus'ab din Dr Mus'ab ya lura da motar kamar su takebi amma abinka da C.I.D duk yanda yasan zai bata hankalin Mus'ab saida yayi bai daina binsu ba saida yaga sun shiga wani shopping mall sunyi parking sannan shima yayi parking tare da ajiyar zuciya wani baqin ciki ys tokare maqogaron abokan nasa Ja'afar yace “gsky ya kamata ka daina zargin yarinyar nan to waima ina ruwanka da lamarinta ne tunda da bakai zaka aureta ba haba gsky iskancin ka yayi yawa Mainah Abdu”





Dago qananun lumsassun idanunsa yayi da suka kada sukayi jawur ya kwantar da kansa a kujera wasu hawaye suka zubo masa yace “bazaku gane bane Ja'afar ance sai kana zina kake zargin wani yanayi amma wlh ni ba haka bane inason gasqata Samha amma na kasa kuma nasan ba komai bane kishinta da soyayyarta shine yasa nakasa dauke idona akanta wlh Ja'afar yanda nakejin Samha da kishinta a raina banajin kishin Yasmin qanwata haka na rasa yanda zanyi na gasqata Samha ko nayi qoqarin hakan sai zuciyata take fadamin yaudarar kaina nakeyi wani ya santa kai shi kansa wannan mutumin da zata aura gani nake kamar morarta yakeyi bansan ya akayi shaidan yayi tasiri a kaina wajen cusamin zargi da kokwanto akan Samha haka ba"..........






*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[2/11, 2:59 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_AD_*



*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*





_Sister Aisha Gwazawa wannan pg nakine a madadina da sauran members na ADANDI VIP SECTION muna qara isar da saqon ta'aziyyarmu gareki Allah yajiqan wanda ya rasu muku yasa mu cika da imani munayi miki barka da dawowa zauren fafatawa saboda munyi kewarki irin sosai dinnan._




*17*



Sun jima a cikin shopping Mall din suna siyayya duk wani abu da yasan zasu buqata saida ya siya musu hatta da part sannan suka fito yana riqe da hanunta suna dariya takai hanunta taja gemunsa daidai lkcn da Abdul ya dago kansa dagakan sitiyarin don cewa yayi da abokan nasa su tafi kawai shi zai taho idan yaga fitowarsu aikuwa wata qusa yaji ta caki qirjinsa data sashi dafewa da sauri jikinsa yana wata irin rawa a fili yace “kai! Kai!! Ina wlh da sake bude motar yayi kamar zai fita sai kuma ya fasa saboda yana bala'in tsoron jizginta ba kunyar jizgashi zataji a gaban Mus'ab ba shikuma zai iya daukar komai banda wannan a shigo har masarautar sa a jizgashi.




Mota suka shiga suka dauki hanyar komawa campus din sunata hirarsu ta masoya suna zuwa suka dauki Rahmah suka wucce ya sauke musu kayan a gdan sannan ya sake daukar kudi ya bata har naira dubu hamsin taqi karba daqyar ya lallabata ta amsa ya tafi sukuma suka shige suka zauna suna bude kayan ba zato babu tsammani sukaji an banko qofar an shigo suka miqe da sauri ganin Abdul yasata sauke ajiyar zuciya idanunsa akan nononta data sakesu ko bra babu saboda ita ba gwanar sanya bra bace indai ba fita zatayi ba ganin inda hankalinsa yake yasata daukar hijjab tasa.




Ya hadiye wani yawu me daci ya fara matsowa kusa da ita tana janyewa har saida sukakai qarshen bangon dakin ya sanya hanunsa ya riqe kafadarta idanunsa sun qara ciki saboda bala'i sai hawaye yake fitarwa bakinsa na rawa yace “wato bazaki gane abinda nake fada miki ba ko meyasa kikeson dole saikin wahalar dani meyasa bazaki rabu da wannan dan iskan mutumin ba wlh kinji na rantse miki Samha basonki yakeyi ba qarya yake miki akwai qudurinsa akanki Samha nasan wayeshi nayi abubuwa da yawa akansa aikina baizo kansa bane amma saboda dalilin rabani dake da yake shirin yi shiyasa na dakatar da wanda nakeyi nakai hankalina gareshi Samha zaki yarda ki auri mutumin da uwarsa take kallonki a matsayin karuwa kilaki yar DANDI mutumin daya kasa bayar da hujjar kare matsayinki a gurin iyayensa mutumin da yake boye miki abubuwa da yawa akansa nasan ya fada miki zai tafi Oxford University qaro karatu a zahiri ba haka bane ya boyewa matarsa da iyayensa aurenki ne saboda a karon farko sun nuna qin amincewarsu ga aurenki saboda tabon da gibin da kikayiwa tarbiyyarki matsalata daya ce Samha inada kishi kuma a gdanmu akwai al'adar da dole budurcinki shine zai fansheki kekuma kin zubar da naki a titi Samha idan kin amince min zan aureki amma zan nemi budurwa wacce bata taba sanin namiji ba na aura kafin ke inyaso ke saina aureki matsayin bazawara kinga babu wanda zai buqaci qyallen budurcinki da saf....."




Bata bari ya rufe bakinsa ba ta daukeshi da wani gigitaccen mari jikake tasss tasss yayi saurin sakinta tare da ja da baya ya cije lebansa har saida ya fashe jikinsa da haqoransa na rawa baitaba sanin haka zafin mari yakeba sai yau da Samha ta mareshi dama haka takeji duk lkcn daya mareta amma bata taba nuna masa ba.




Bata bashi damar cewa komai ba tace “tur munafiki mayaudari meson bata sunnar ma'aiki na tsani maqaryacin mutum irinka a rayuwata Abdul meka mayar danine yar iska wadda batasan ciwon kanta ba Abdul kaima kasan ciwon kanka bareni to kayi gaggawar fita daga rayuwata na tsaneka Abdul na tsani mutum mara sanin darajar dan'adam irinka ka wahalar dani lkcn da banida yanda zanyi shine ya cetoni yasoni a lkcn daka qini akan wata hujjarka mara tushe ya kula dani yajani a jikinsa ya soni da raunina kuma kullum kalmarsa yana sona a yadda nake kaje ka auri yammata hudu ka baresu ka hudasu rana dayama domin cika

Please Login or Register in order to submit comment