Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idan ance ya kwace bazai iya ba
Gumi ne yake keto mata salati kawai take yi
wani irin ne shine taji yazo mata sake kenkeme Nabil tayi gem
Hadim sai yanzu ta tsorata dan bata taba ganin haifuwa ba azaton ta fitan raine ganin yanda Fandau take yun kuri cikin karfi
Abin ya bata tsoro tace "Nabil idan ta mutu yaza muyi
Tafa de haka tana cikin riki cewa

Shiko Nabil yanda Fandau da danke shi ko halin magana ba shida shi balle yayi yunkurin ta shi
Shikan sa gumi ne yake keto masa duk addua da yazo bakin shi yake tofa mata

Cikin sa a Wani yunkurin tayi da karfi sai gawata sun guceci y'a ta fado dama yau riga da zani tasa zanin dama ya dade da kuncewa sai ciket din ta na ciki
ajiyan zuciya ta sauke ta saki Nabil
Shima jahota yayi jikin sa ganin yanda take sauke ajiyan zuciya ya rungume ta gyam yana sakin ajiyan zuciya bai masan me aka haifa ba
Sai jiyayi Hadim tana tace"kutuma macce macen ma baka me kamar ki kika haifa mana
Nabil
Yace "alhamdulilah alhamdulilah
sai faman shafa kan Fandau yake

yace "yanzu ina ne yake miki ciwo sai a sannan Fandau ta bude ido tace ruwa zan sha da sauri Nabil ya saketa yayi hanyan kitchen yana zuwa ya bude fridge ya dauko roban ruwa ya daga kanta yaba ta kurba daya tayi ta tuno da mejego bata shan ruwan sanyi asanin ta ta zare bakin ta tace na zafi nake so
Ya juya zai hanyan kitchen Hadim da take ta faman fadan anhafi macce kuma baka amma kuma ta daga yar ta daura ta a cinyar ta na goge bata furka

Tace "Nabil kaga macce ta haifa fa
Yace "good mekyun kenan
Tasake cewa "amma fa tafita kyu zo kagan ta
Yace ina zuwa

Hadim
Zanin Fandau da yake cikin jine Hadim ta jawo ta kwan tar da yar ta nufi lokan gadon fandau inda dama ta tana di almaka shin ta zare duk takawo part din ta ajiye ta dauko ta seta yatsanta kamar yanda aka mata bayan yankan cibiya ta yanke ta daure ta dauko wani zanin a whardrob din Fandau ta nade yar dai dai lokacin Nabil yafito da cup ahannun ya tashi Fandau ya bata
Hadim ta kalle shi ta bata rai tace wai Nabil mehaka ruwan ma sai kai zaka bata
Cikin tsawa tace keee kalle ni idan zaki ware maki ware ki temaki kanki dan mu muna fita adakin nan ba kara shigo miki zamu yiba sai munje mun dawo kafin nan kin gama jegon dan muna zuwa zamu daura daga inda muka tsaya kin haihowa mijina abin da yake so macce ni namiji nake so dan haka baki kubuta ba da namijin kika haifane ma wata kila shi ya hakura mu sallame ki inkinga mun barki to kin haifi namjiji
Amma abin da zan gaya miki ki temaki kanki kicire ragonci ki kasa jikin ki da ruwan dimi dan inda wanan sun kucece yar ta fito ba karamin budewa yayi ba
Inba haka ba kirube Wllh
tana gama fadan haka ta dauki zanin Fandau da yake cikin jini ta daura ajikin ta cire siket din ta ta zauna dabar acikin jinen da kazan tar haifuwan ta na Goggo ga cinyar ta take tayi jagab kamar ita ta haihu ta meke

ta kalle Nabil tace "zomu tafi Mu nunawa yasmin ko
Nabil ya kalle Fandau da kanta yake sunkuye tana zaune cikin jinin har yanzu
yakalli Hadim data rungumi jaririiya tana jiran sufita

Yace"haba yaza mufita mutar ta cikin wannan hali mu temaka mata da koda gyaran wajen ne mana

yamutsa fuska Hadim tayi tace wllh bazan iya ba zuciya ta bakaga yanda yake tashi ba ko wannan tsayuwan karfin hali nake
Gazanin ta dana daura dan yazama sheda awajen yasmin da ma aikatan gidan nan ya dameni da wani irin garni sona ke muje na kunce zuciya ta sai haurowa yake

Nabil yace " toki tsaya ni zan gyara
daukan Fandau yayi yayi hanyan bathroom da ita wani kishine ya kama Hadim cikin tsawa tace "my star a gabana kake daukan wata

Yajuyo ya mata wani irin kallo
yace "meyasa wani lokaci imanin ki bashida yawane idan ban dauke taba kina ga zata iya tafiya ne aga ban idon ki taci wannan a zaban
Itama cikin bacin rai da kishin yanda Fandau tayi wani lif ajikin Mijin ta

Tace"to meye wani a zaba a haihuwar macce macce fa ta haifa
Nabil wani kallo ya mata yace "in fisari kayan ragone kaza ma tayi mana yana fadan haka ya shige da Fandau bathroom ya sauketa abakin bathtub ya hada mata ruwan wanka me dimin ya sata yace "zaki iya yin wankan ko gyada masa kai tayi
Yace yawwa kidin ga kula da kanki dan mu ayau zamu tafi dan su ummi dama basu so Hadim ta haihu a nan ba sai cewa mukayi doctor yace ba ason tayi zaman jirgi cikin zai iya samun matsala dan haka muka musu alkawarin aranan da ta haihu aranan zamu taho dan haka ki kula da kanki kinji abin da tace ai zaki iya rubewa dan ki kula nima ina kaisu zan dawo cikin kwana ukku nan zaki ganni
Bata ce komai ba shikuma har yaje bakin kofa ya sake dawowa yarugume Fandau yace "wllh ko ban zauna da keba kina da mushin manci arayuwa ta daga nan har karshen ta
Kin bani abu biyu arawuwa wanda bazan taba mantawa da shiba
*Budurcinki*
Dakuma
*Y'ata ta fari*
Kissing din lips dinta yayi yace "ke ta musamman ce

Ita ko Hadim Nabil yana gaya mata wannan maganan tayi tsororo a tsaya ta bisa da kallo tana mai maita
_idan fisari kayan ragone kaza ma tayi mana_
Idan ta fashince shi gatse ya mata ne ko gori yanzu ni Hadim har nayi saken da Nabil zai gaya min wannan maganan kuma yasa hannun sa agaba na yadauki macce wanda ni bai taba dauka naba koda bani da lafiya sai yace nayi girma
Me hakan ke nufi
Kwaban zuciyar ta tayin da cewa tausayin ta yaji ganin ta wahala ita ma kan ta lokacin da Fandau take cikin nakudan ta tausa ya mata balle Nabil sarkin tausayi
Kukan baby ne yadawo da ita haiyacin ta tayi saurin kijjigata
Alokacin Nabil yafito ko kallon inda jaririiya da Hadim bai yiba yafara gyara wajen
Hadim cikin mamaki take binsa da kallo yau *shidmas* guda da sa hannu cikin jine yana aiki tukuru tas ya goge wajen yashiga yafita yana cikin wanke kayan jinen ne yaju ya yakalli Fandau da take ta faman gasa jikin ta da towel sai da ya gama wanke komai na kayan da ta haifu mabiya kuwa dakyar yasa mu yayi fishing din sa

Ya karasa inda take
yace "wankan ya isa haka kodan kin wahalu fa ba keba ai koni sai nayi wankan sati ina ga wannan matsa da akamin Duk jikina ciwo yakeyi a tare suka fito

yasa mu Hadim tacika fam
Sai faman jijiga jaririiya take
abakin gado fandau da zauna shikuma yayi hanyan kitchen
Tace ina kuma zaka sake Komawa

Bai kalle taba yace" zan hada mata tea me kaurine
Aiko Hadim tasake cika cikin fusata tace wai me kake nufine

Ko juyowa bai yiba ya wuce kitchen
Bayan yaka wowa Fandau tea din yabata karba tayi ta fara sha

Yaka rasa wajen Hadim da bakomai cikin idon ta sai tsabar bala i
Yasan idan bai yin lallami ba sauki dafa ta yayi yace maman baby girl ya akayi ne muga yartaki kinwani kan kame ta dan rowa

Bata rai Hadim tayi
Tace"Nabil kasan me kayi kuwa
Cikin salon sa na yaudara yace "menayi?
Tace"baka ma san me kayi ba a gabana fa kake tattalin wata macce
Yace ba tattalin ta nayi ba kinsan ance dan tuwon gobe ake wanne tukunya

Duk magan ganun su cikin kunne Fandau dan bawani nesa suke ba

hima kansa yana fadan haka yaji wani iri azuciyar sa yace Allah yasa bata ji ba amma yana juyawa ya ga idon ta da hankalin ta duk akan su da gani yanayin kallon da
Take musu taji komai

Hadim tace "aisai kai karbi yar karike yasa hannun yakarbi yar ita kuma Hadim jagaf jagaf da jine ajiki ta fara ta fiya wanda baisa nima zaice haifuwan gaske yi
Dariya yakama Nabil daya tuno lokacin da hadim ta zage ta na ta shafa kazan tan haiwuwa ajikin ta
Ga zanin Fandau
Daga nan suka fito
Hadim tana takawa Ahankali sai wani cicci je baki take
Aiko kamar yanda suka zata a man falon ko suka samu
Yasmin tana kallo
Ai tana hango su dagudu tayi inda suke aunty karde haifuwa kikayi ne ina tan take tayi kan ai tama manta dawani tsoron Nabil da suke yi wanda ko waje yaje tofa basa zama awajen dan shi ko kamal wanda yabiyo bayan sa soron sa yake
Kai har yayinsa mata su zainab wada suke uba daya suna tsoron sa dan Iya uwar gida maman su zainab cewa take kar karaga musu ai kaine babba tunda kaine namiji amma sai ga yasmin taca muko ya baby ha hannun sa tana tace "memuka samu mugani meka mata yayi
Yajuyo yana yiwa hadim sannu harda riketa kamar wanda ita tayi nakudan

Yasmin tace lahhhhh anty kin haifi me kama da Kala wllh suna kama da kala
Hadim sake kallon jaririya ta tana murmushi dan mata so yariyar tayi baki ma amma taji dadi da aka dan ganta tada Kala Kala kanwar Nabil ce uba daya ita ma yar gakin iYa ce
Wow amma fa hancin ta irin na yashid dakum.. ...

Hararan ta Nabil yayi tayi gum da bakin ta

Tabi bayan su suka haye sama
Toilet hadim ta wuce ta tayi saurin yin jifa da zanin duk jikin ta karni yake wani irin amai ne taji yana taso mata wanka tayi yafi so 5 turare kam bawan da ba ta fesa ba tafito daure da towel bata ga Nabil ba dan tasan yaje daya dakin wanka ne yanda jikin sa ya baci
Yasmin ce da waya ahannu sai kolotun ihu ta ke takira wannan idan tafa da ko amsa bata sayawa ji zata kashe takira wani
Hadim ce tazo ta zauna abakin gadon yasimin tace"aunty kin ganki uwa ras kaman bake kika haifu ba
Amma ANTY tare kuka haifu da yashid ko yanda naga duk jikin sa jine har yafiki baci

Gaban hadim ne yafadi ras tace ban gane kamar bani na haifuba
Yasmin tace "wllh anty fuskan ki tayau kamar baki sha wahalan nakuda ba sai tafiyan ki da ya canza kawai anty

Hadim tace"yasmin kinada yawan shirme a maganan ki mekomin wayata naki ra Habiba da su faridan Amjad
Suzo suga baby dan yanzu zamu wuce
Kita shi ki hada mana kayan mu

Yasmin tace "yawwa anty ina siyayyan kayan baby da mukayi kinga kamar nida yashid munsan macce zaki haifa muka dinga iban kayan baby girl keko kikayi ta jidan na baby boy
Wai ina suke ma wllh akwai wani mekyu dama na nace idan macce ce shi za afara sa mata
Hadim tace "inaga fa anwuce da shi 9ja dan kayan da muka bari anan ba yawa duk mun aika anty yanzu wazai mata wanka Hadim tace "bana jin za ayima ta wanka anan sai munje gida dan awai wasu abubuwan da ake yiwa diya macce a wankan fari a al adan muna shuwa
Yasmin tace "shuwa iyayen....
Keee bani man zaitun da auduga na goge mata jiki dashi tana maganan tana kiran wayan Habiba babbar amini yar ta
Aiko habiba cikin ihu itama da murna ta kaye waya kawayenta zallah nanan London take kira dan su zo suka baby kafin suta fi tana ganin kitan yangida amma bata dau ka
Tafijin kawayen baye idan ta tuna kyutan da kungiya su tayi akan abin da a ka Haifa baki yaki rufuwa
Nabil kwance cikin
Bathtub yayi shiru nunani yakeyi wai dama haka nakuda da haihu yake da azaba Lalle annabi yayi gaskiya da yace abi uwa uwa uwa ummattii
Akwai wani hassari da akayin agaban sa ankayi ta mutuwa da raunuka manya harda wanda kafansa ya fille yabar gan gan jikin sa amma mai ga yashiga halin da Fandau tashiga ba
Anya yayiwa uwar Fandau a dalci da yara bata da yarta gashi ita ma Fandau din zai rabata da yar ta
Yar fa nima tawa yar ta girma a mata haka
Tsaki yayi afili yace aine y'ata tafi karfin haka yata
Wllh ina ma wani zai ganta tana yawo a kafa balle ya yaudareta kofilin wasa zan shiga aisai na hada ta da body gard sannan baza tayi Rayuwar Nigeria ba
Da wannan karfin guiwan yafara gasa jikin sa da yake masa ciwo baye kafadun sa inda nan Fandau tafi matsewa

Sun samu rakiyan dinben mutane wada yafi na da zuwa airport doctor Muktar ko kin zuwa yayi dan yaji mugun haushi da wai Hadim haifuwan gida tayi kuma bayan hakama yayi yayi subari aduba lafiyan ta amma sunki shiya fijiye mata ma karuwa dan yar da girman ta
Haka agidan ma Hadim kin yarda tayi kowa ya bata wanka sai fada suke da mamar ta sai tace ita zata iya ai ita ba yarinyar bace ummin Nabil ma tasa baki tace Hadim kibari a koya miki abubuwan kinga haifuwan farine
Ai ita kanta ummi ce mata tayi ita fa bame kanin siraicin ta dan bakyu wani yaga siraicin wani

_Niko nace keko kika gama ganin na Fandau_ _a he kinsan da haka_

Haka suka rabu da ita ga hade haden na shuwa ba kadan ba amma haka suka bata ta shiga dashi idan na tsugun none zata zuba tana gani zai gama hayakin sa yagama idan na wanka ne ko wanke wajen tayi floshing dinsu
da wayan ta ma take shiga tayi zaman ta tana chatting dinta da kawayen ta akan baby

Nabil ya sake sunkurar da kai a gaban Maman Fandau yace"yauwa mama idan macce ta haifu me dame ya ka mata abata
Mama tace kowani irin abinci ne inde megina jikine da kuma wanda zai sa ruwan nono ya gudano zata iya ci

Shiru Nabil yayi dan yagane mama bata gane meya ke nufiba yanda yaga anayiwa Hadim shidema ya tabbatar idan macce ta haifu ba abarinta haka dan yaji su ummi sunayiwa Hadim fada ta dage da abinda zai gyarata

Dan haka ya yir yawa kansa tafiya London a gobe in yaso ya dawo kafin suna
Sunkurar da kai yayi cikin kunya yace "ina nufun wada zai gyara mata jiki
Mama murmushi tayi tace "inban da abin ka Malam k'arami ai shuwa sun san irin wanan abubuwan ai
Sake sunkuyar da kai Nabil yayi
Yace"basu bata ba ita kuma tace naki take so
Murmushi mama tasake yi tace Allah sarki Halima y'ata wllh nima ina sonta tana da kirki da iya gimama mutum insha ALLAH gobe idan zanje duba yar jikalle zankai mata
Nabil yace "Mama ai kunyan ki take ji ni zaki bawa na kai mata ko kinje kar kimata zance ta ce kunya ta keji
Mama tace"shikenan idan naba da antsayo abubuwan sai nakira ka awayan ko
yace to" mungode mama tace rufe min baki har kai zaka bude baki kace zaka min godeya akan wani kan kanin abu
Nabil dubi yanda ka mayar ni kamar nina yi cikin ka da haifuwan ka bangare na ya ban ban da dana kishiyoyi na dubi yanda ka ajiyenin komai na rayuwa kullum sai kakira ne mun gaisa ga yaron dakin ka kullum sai kace yazo yaduba abinda nake bukata
amma abin da nake soda kai sauran matan ma kana musu baka gafa yanda ban isa fitowa tsakar gida ba za afara min gorin na shanye zubiyar ka har taka nas suka je gidan ku suka gayawa Hjjy hajara dan ma ita bane daukan irinwanan bane sai tace musu haka halin danta yake da kyuta suyi hakuri ran da yajiyo kuma zai muku kaga duk suma kana musun amma Gaskiya bai kai nawa ba,
ni kaina ina mamakin yanda kake nuna ban ban ci a tsaka nen mu kaga dole su zargi wani abu,

Shidi man nawan ne yafina su dan haka nake neman alfar ma wajen ka kana mana komai dai dai


Nabil ransa ne yabaci yadade dagano matan nan basa son mama shiya sa ma yake jin haushin su yake kuma nuna ban dancin amma idan ba haka ba shi kishiyar uwar sa ma amatsayin Uwa yadauke ta bai taba ban ban ta iya da ummi ba
Yayi kwafa badan mama tace alfarma tane maba da abin da ya saba musun ma de nawa zai yi dan shi a rayuwan sa ya tsani mutum me hassada

Yameke yana cewa to shikenan mama
Hada komai kafin na dawo agidan ABBA musa sai nabiyo ba karba dan ni gobe fitan asuba zanyi
Har kofan babban falon ta tara kosa tayi saurin komawa kafin afara yada mata mgn dan tana jin muryoyin mutan gidan

Yanzu dan Allah baza suma ka alfarman wasan nan daya ba abari idan anyi suna katafi
zaka tafi ka barmu duk yanda kake son babyn ka

Nabil da yake wasa da baby yace"baby wai kinji Momin ki tana hanawa naje nema muku kudi bayan da mun nemi na banza ma balle yanzu gaku masu bukata kun fara zuwa
Dariya tayi tace" wai kai yanzu meyasa baka fiye son mgn dani ba komai sai kagayawa baby
shima dariya yayi yace ai ke komai na fada sai kinmin musu ita ko bata yimin komai nayi tana so
Dariya ta sake yi tace "amma Wllh ABBAn fujjirat zaka haukace
Yaci ro wayan sa yana daukan baby da su kansa ma
Hadim tace "yanzu idan katafi saifa ran gobe suna yace "eh Kamal da Girema zasu yikomai da kuke buka ta
Nima da baki zanzo Hadim cikin zunudi tace har da su Sir ko dan da alkawarin mu zai zo nabil yace "eh mana ni abubuwan su ma mamaki yake bani baki ga yanda suke zumudi babyn nan ba,
Yanzu haka Duk sunce sai sunjo da yawan suma basu taba sanin ida Nigeria yake ba

Fandau suna fita ta sauke cup din abakin ta kala man Nabil yana mata daci wai
_dan tuwon gobe ake wanke tukunya_

Kuka ne ya kwace mata wane irin Duniya take cikine meyake faruwa da ita kamar a farki amma yaki karewa
Afili tace sakai yar mama banga komai ba ma inde wanan azaban nakudan mama ta sha nazo Duniya na gujeta to banga komai ba
Gashi nan tun ba ayi nisa ba Allah ya fara saka mata naguje ta nema gashi nan an raba ni da abin da na haifa wanda ko ganinta banyi ba baza ta masan ne na haifeta ba
amma ALLAH kai kasan manufa ta akan haka banyi dan na kuntata mama ba nayine dan zuwa gaba musa mu yanci na mema mata jin dadi na har abada ahe ni kuskure nayi bansa niba,
dan yanzu nasan dacin rabuwa da d'a nima da ba shakuwa nayi da ita ba ba wahalan renon ta nayiba naji d'acin rabuwa da ita balle mama yata ji da ta rasani
ALLAH kayafeni

Haka Fandau tayi tashiga ruwan zafi tayi kokarin da cikin kwana ukku ba kace ita ta haifi wannan yar ba ga abinci wanda taga dama zata tafa taci tacika cikin ta daruwan tea mezafi sosai wani lokacin yana kona ta har kuka take amma sabar wayo irin na Fandau tasan shine kadai magani awajen ta dan haka bata wasa dan yaran kanuri bade sani ciwon kai
Yarinya karama amma za kaga tasan komai

Yasmin kwance acinya uwar ta inna ZAINABU uwar danja kenan inji Hadim
Tace"inna nifa naga abubuwan mamaki a haifuwan nan na Aunty ciki kamar na aljanu wataran ya girma wataran yazama kara mi kai wata ran ma babu zan gani dan nasha kamata ba cikin abin da yafi ban mamaki saman sakiya tun rar da muka je suka hanani shiga wai da aljanu basa son bako amma su kullum sai sunyi ta shiga tunba ma yashid ko anty tayi Baccci haka sai yashiga ko idan anty ta tafi anguwa sai ya shika kuma ya dade idan su biyu ne kuma ba sosai suke jimawa ba

Amma abinda yafibani mamaki asaman anty ta haifu
Kuma ai idan macce ta haifu bata sallah meyasa ita anty naka tayi sallah ranan da ta haifu
Inna da abin dubawa fa awannan haifuwan nasu da kinga shikara da shekaru suna neman haifuwan ba ayita ba sai da kikace tunda baza ta haifu ba zaki sashi yayi aure sannan aka samu ciki nede jikina yana bani akwai wani abu tabbasas kuma hak....

... Wani irin tsawa inna ZAINABU ta.......


*Tofa nima nayar da*
*Da maganan Hadim *yasmin dinnan muguwar yar sa ido ce*


_B JATTKO_
[2/7, 9:24 PM] ‪+234 905 844 3838‬: DAMA TA


NA













BATUL ADAM JATTKO


GODIYA TA MUSAMMAN GA WADANDA SUKA KIRANI DA WANDA SUKAYIMIN TA'AZIYYA THOUGH ONLINE NAGODE NAGODE ALLAH YABARMU DA SOYYAYAR JUNA, ANA TARE🤝

30







Tace ashe yasmin bakida hankali, wanne irin maganane wannan din? Daza kice kinada shakku akan haihuwarta kodazu danaje gidan tana bawa 'yarta nono,

yasmin tace "Allah inna kiyarda maganata kinsan yanda akayi aka samu ruwan nonon ne shinema yakara sakamin shakku don likita dinda take cikin jirgin takira tace yau kwananta 3 da haihuwa amma haryanzu ruwan nono bai sauko mata ba matar sai tace mata meye dalili sai takalleni tacemin inkoma gurin zamana toh day anan bansan ya akayi ba sai naga tana bawa 'yar nono sai inna zainab tayi shuru cande sai tace wasu daman ruwan nono baya sauko musu dawuri balle ita da kikace randa tahaihu nema,

Tasake sai tace "toh inna meyasa tace kwananta 3 da haihuwa
Inna ZAINABU cikin fada takoreta agurin tacemata kedan Allah kitashi kibani guri banason surkullen zance ni bana daukan magananda bashida ma'ana kinsan halina sarai yasmin de tatashi tana zumbure zumburen baki




Nabil tsugunne gaban mama tana fada masa yanda za'ayi amfani da magungunan
shiko dayaga bazai iyaba kawai sai yaciro pen yake rubutawa tana masa bayani a tsinake idan yarubuta sai yajefa acikin ledan ahaka tagamama sa bayayin
yatashi ya bata salama

Hadim ko ajikin ta da Nabil zaitafi dan tasan Fandau tana jego
Kuma ma ita haryanzu bata wani dauki fandau din da mushin manci sosai ba

Fandau ta shafa nonowan ta da sukayin hulu hulu dan cikan ruwa acikin yau kwannan ta 4 da haifuwa amma ciwon ta keji

Please Login or Register in order to submit comment