Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abinda ake tana fita doctor adegas ta karaso wajen Fandau tace ina hada ido dake naji tausayin ki meya kai ki beyewa mazan turawa daga kawo ki aiki suka baki ciki gashi yanzu kinsa uwar dakin ki tarasa yanda zatayi saide aminki allura."

Fandau tace" haka tace miki ni yar aiki ce?
Doctor tace "eh mana."
Fandau tace "bata gaya miki gaskiya ba."
Matar tace "daga yanayin kalaman ta tunfar ko nagane ba gaskiya bane dan Hadim kawata ce nasan halinta sarai gayamin gaskiya zan temaka miki."
Aguguje Fandau tabawa matar labarin ta.

Doctor tace "na gaskata ki kuma ciki tunna fari nagane cikin kawata ba na gaskiya bane amma kisani mijin ta yanada mugun kudi har ita kanta baza ki iya ja dasu ba temakon da zan miki dayane alluran batar da memory kine bazan miki ba amma na zubar da ciki yazama dole tunda zata gani idan bai zube ba dan tafiyanki sai gobe, inason kinuna na miki alluran kinuna kin manta komai idan kika je gida kikaga za'a iya dau miki mataki shikenan kinji kuma abin d...
Hadim ce tashigo "tana cewa tayar ko sai taji ciwo kafinnan
Doctor tace "ai har angama dayan saura na aborton din ai."
Hadim murmushi tayi tace"yanzu shikenan ta manta komai ko?
Doc tace" sosai."
Fandau tana gani matar ta dan na mata allura da zai zubar mata ciki takama ta ta zaunar ta ita abakin gagon tace "nan da anjima zakiga tafara zubarwa."
Hadim tace "nagode Hadim tana ganin wayan Fandau ta dauki wayan suka fita.

Suna fita Fandau ta fashe da wani irin kuka yanzu burina da kudiri na bazai cika ba kenan yanzu naje gida nace me, anya bazan kira matar nan nace tamin alluran nan ba kuwa? tana ciki haka taji cikin ta yayi wani irin murdawa juyi ta dingayi akan gadon tana ihu dan yafi nakuda ciwo tana jin abu yafara bin jikin ta har yasauko cinyar ta tasa hannun ta shafo tana ganin jinine tasake sakin wani kukan saide bawani jimawa taga jinin ya tsaya haka cikin ma ya dena ciwo.

sai yamma Hadim ta shigo, tasamu Fandau akwance jinin har yafara bushiwa anan Hadim ta sake tabbatar wa da lalle bata cikin hayyacen ta dan da tana cikin hayyacen ta zata tashi.


Tace" kinga anyi maganin ki yara sun zama nawa na har abada kije can uwar ki taci gaba da renon ki".

Dole ita ta gyara ta, Ita kuma Fandau sai juya ido take alamun bata san ma me akeba, da Hadim ta doka mata tsawa tace "kina jina kitashi." Bata ko motsaba tana kallon Hadim a shagwabe kamar yarinya janta Hadim tayi tafiyan ma dakyar takeyi haka ta kaita bathroom ta kitsata suka fito tana rike da hannun ta ta zaunar da ita akan kujera ta janza zanin gadon
Har zata fita ta tuno da ai yaka mata ace ta bata abinci waya tayi wa ma aikatan gidan suka kawo abinci ba ajimaba taje ta karbo tazo ta ajiye abincin ko kallon abincin batayi ba, irin bata sani ba saida Hadim ta zauna ta samata abaki nan ma kin taunawa tayi saida Hadim tasa abakin ta tafara taunawa sannan itama ta fara ahaka ta gama bata.
ALLAH sarki Hadim duk abin da takeyi cikin karfin hali takeyi dan tana jin jikinta sosai.

Washe garin Hadim da dama tagama duk wani ciku cikun tafiyan Fandau haka ta dauke ta da kanta dan bata son driver yasani wani tasamu a maikatan airport tace ya hadata dawani fasinja zata bashi amana haka akayin kuwa aka hadata dawani yaro bawani babba bane tace "bawan ALLAH yasunan ka yace" musa." tace" idan badamuwa zan baka amana." yace"Allah yabani ikon karba da kuma rikewa" tanuna Fandau tace "kaga wancen yarinya bata da lfy kuma ni nasame ta tunda guntun lafiyan ta tace min ita yar maiduguri ce amma yanzu idan an tambaye ta ma bata bada amsa, nayi mana shirin tafiya tare maigida na yakamu darashin lfy shine nawa tafiyan bai yuwuba, nace sune mamin wanda zaije Nigeria musulmi shene
Aka hadani dakai, kai dan inane?

yace " ni dan kano ne karatune yakawo ni yanzu ma hutu zan tafi."

"Yawwa kanina inaso ka kai min ita maiduguri nauyin da zan daura maka kenan zan baka kudin jirgin da zai kai ka can dakuma wanda zaka dawo harma da kari."
Yaron yace"amma wllh badan kin riga kin hadani da ALLAH ba da bazan karbi wannan aikin ba tunda kema kince baki san gidan su ba to yanzu ina zan kaita?
Hadim tace " wanan badamuwa bane ka kaita B R TV ko N T A maiduguri kace katsince tane amma kace a garin ka tsinceta." Dayake yarone bai wani san haka zai zame masa illah ba yayi saurin karba , Hadim ta bashi kudi meyawa tayi saurin barin airport din.

Yaron bai wani kai saurayi bama shiya kama hannun Fandau har cikin jirgin
Itako Fandau tana shiga tana zama tafara kuka, ba wajen zaman su daya bane da wanda aka hadasu tunda ta zauna kuka take yanzu haka zan koma gida nazo a siya zan koma awulakan ce to ina shi Nabil din kikasani ko bakin su daya da matarsa yasan metayi koma dama bawani tafiya dayayi tunda ta zauna wata mata yar gayu take binta da kallo itako Fandau ba alamun zatayin shiru, matar tasowa tayi tazo wajen ta, kanwata meyake damun ki haka tunda aka fara tafiyan nan sai kuka kike ko da akazo tambayan mezaki ce bakice komai ba kuma naga da yayanki ma kuka shigo ko kanin kine ."
Fandau batasan dalili ba kawai sai jitayi tace"ba yaya na bane banma sanshi ba kawai gani nayi yakama hannun mun shigo ."

"to meya saki kukan nan meke damunki ki gayamin?
Tace" gaya miki ba wani amfani dan idan kikaji tarihin rayuwa ta bazaki yarda ba, a bune da banta bajin sa aduniya ba."


"Kigaya min ko dawani taimakon da zanmiki", saida Fandau taci kukanta ta more tukun ta kwashi komai na rayuwan ta tagayawa matar, a firjice matar take jinta itako Fandau tunda tafara bata tsaya ba sai da taje karshin labarin ta.
Itama matar kuka take sosai, ko magana kasayi tayi tashi tayi tajen wajen ta, ganin kukan Habiba yayi yawa doctor Muktar yace" waike meya faru meke damun yariyar naga kin dade awajen ta Habiba ta kwasa shi komai ta fadawa doctor shikan sa abin ya firgita shi haka Habiba ta koma wajen Fandau ta yita lallashin ta har tadan saki jikin ta.

Hadim fal murna takoma gida. Dan ita abinda yake bata mamaki ba Nabil ba hatta yan gidan su da kawayen ta ba suwani nuna mata dokin cikin nan ba, ummin Nabil har yanzu bata kirata ba haka Inna ma mamar ta cema takira ta hatta kanwar ta Ashuwa bata kirata ba.

Ga babbar aminiyar ta ma Habiba data kirata cewa tayi baza ta samu daman zuwaba dan tana cikin shirin tafiya gida.

Kowa bayawani dokin cikin nan.

Jirgi su yana sauka atare suka fito da Fandau sun riga saurayin fitowa koya tsaya neman Fandau ne wayasan masa itade dama tun kafin susauka Habiba tace mata gidan mu zaki bimu dan mutantan ce gaskiya acikin maganan ki, sude har driver dinsu yaja basu ga idon Musa ba.

Sun sauka ne a ABUJA dan haka gidan doc na nan ABUJA suka yada zango suna shiga babban parlour gidan idon Fandau yasoma cin karo da tabkeken photon Nabil da yake jikin bango yana sanye da kayan ball yarike ball din ahannu sa turus ta tsaya tana nunu photon bakin ta yana rawa tafara magana "wllh gashinan shine shine shine".

"shine wa suka hada baki Muktar da Habiba."

"Shine wanda nake gaya muku sunan sa Muhammad ana kiransa Nabil ko Shiddams wllh shine."
Sai tasake yi musu bayani sosai suka yarda, abin yayi mugun bawa Habiba mamaki dan bata zaci kawar ta da wanan halin ba
"Abban Nofal me mafita."
"Mafita daya kawai mukaita gaban iyayen ta dan nasan bazasu iya jada suba, amma nima sheda ne alokacin cikin farko a toilet din office dina nace ta shiga tayi fitsari, saide mamaki na dana shiga sai naci karo da wani kwalba shima dana sa aka auna sai yanuna iran fisarin Hadim ne kinga yanuna da abinta tazo ko kuma ba abinda banyi dasu ba suzo awu suka ki, ga haifuwan gida suke dama abin yana bani mamaki amma awanan cikin sai suka yarda aka auna kuma bugu da kari ma ita Hadim awajen haka tace ashe itama darabon zata ga......
bai bari ta karasa ba."

Amma wanan bai isa sheda ba dan haka hakuri shiya dace dake mude zamu danka ki ga iyayen ki danni maiduguri ba bakona bane kusan ma garin mune anan aka haife ni kuma garin mama ta.
Inane anguwan ku?
Fandau tace " gargar doctor yace"ok anguwan Zannah Modu kenan Babana."
Da sauri Fandau ta kalle shi tace " nima shine Babana ai."
Da suari doc da Habiba suka kalle ta "Baban ki?
Habiba tace "haba sai yanzu na tuno inda nasan ta wllh itace wanan yariyar da nake gaya maka agidan Malam me girman kai kazama dinnan wllh tun agirgi nake mata kallo kamar na taba ganin me kaman ta Wllh itace."
Fandau daga idon tayi sosai ta zuba musu ido tabbas shine dan gidan Malam Dauda abokin Baban ta wanda idan yaje yan gidan su aketa turoruwan shiga bangaren bak'i gaishe shi shine take kiran matar sa me girman kai ashe ita ma kallon me girman kan suke mata.

Muktar yace "ke yar gidan Wacece acikin matan gidan." "Aisa
Rai abace doc yasake kallon ta yace "amma ba kanki kadai ba hatta Malam baki masa adalci ba shi me fada aji agari kuma duk abinda yasameki kije alhakin Baba Aisa ne dan ubanki kinsan Malam Dauda?
Tsawan yadaka mata yasa ta ja da baya tana gyada kai alaman eh
"kinsan ke me sunan wacece acikin matan sa?
tace " Inna Falta?
Yace"to ni Inna Falta ita ta haife ni, yanzu in ban da lalacewa irin na duniyar yanzu kamar ke da darajan ki da kimanki kibi na miji, gwara da suka miki haka kuma bawani gida da zan maidaki na kaiwa ubana wanan kayan bakin cikin, duk da Shiddams nada daman sani bazan kai ki ba sai kin koyi hankali da zaman duniya, wawuya sakarya ni ahannun na zaki dandani azaban da yawuce na gidan Shid ai."
"Haba dear kamata ahankali man da wanne zataji."

Doctor yace"Wanan yar iskan za'abi a sannu, ko ke bance kibita a sannu ba", yana gama fadan haka ya haura sama
Habiba tace "ishiru Mamana, dama Abban Nofol haka yake yanada zafi akan kannen sa, kiyi hakuri nasan kema kina da lefin yarda da namiji, shiddams abokin sane sosai nasan za'a shawo kan abin kafin akai ga manya, saide ina tsoron kishin Hadim nayi mamakin jin da kanta take kai miki Shddams na yarda lalle akan buri ba abinda bawa bazai yiba,
ga daki nan kushiga keda su Ummulkkairi ina zuwa."
itama ta haye saman


Nabil yayi yayi yarasa Fandau a waya yagaji ranan da gobe zasu dawo yakasa hakuri ya tambayi Hadim saicewa tayi tana nan nima ta kaina nake.

A ranan da Nabil ya sauka ita kuma Hadim har ranan akwance take jiki sai abinda ya karuma ciwo, sai dare Nabil ya lalla ba yayi bangaren Fandau ba inda bai duba ba bai ganta ba cikin faduwan gaba yafita
"Halima ina wannan yarinyar?

Cikin rashin damuwa Hadim tace "wace yarinya kuma?

"Fandau mana."
"au dana sunan ta kenan kai da karike sunan ma bakada aikin shine, to ma meya kaika part din nata ma, ya mukayi dakai."
"Halima amsa zaki ban tana ina?

Tana maiduguri, na kasa hakuri na turata dan idan na biyewa tausayi irin naka wankin hula zai iya kaimu dare na tura ta anan ta masa bayanin komai.
"Dan me zaki yanke hukunci bada sani naba."
Tace "dan baka da iko akai ne, ni na aurota kuma dan na sallame ta ban......
Ai Nabil yama manta dawani ciki ajikin ta wani irin shaka yamata wanda saida yaga alamun zata rasa numfashin ta yanda idannu ta suka fito.
Sakinta yayi ahankali yace" Halima dan ALLAH karki dauki al'amura na da wasa, wllh zuciya ta zata fashe da gaske kin zubar da cikin Fatima da gaske kinsa amma ta alluran idan ta ganni baza ta gane nima gayamin gsky kin illata min Fati na."

Hadim hannun ta awuyan ta tace "eh eh na aika ta."

"Hadim meyasa kika min haka inda kinsan halin da gangan jikina da zuciya ta suka shiga akan yarinyan nan da koda kudi aka hadaki bazaki min hakaba meyasa meyasa?

"Shid saboda nina samu na aura maka ita saboda wani bukata tamu kuma mun samu biyan mukatan zaman me zatayi mana a gida, yanzu wannan har yakai kayi yun kurin kasheni."

Nabil cikin wani irin karajin da ya firgita ba Hadim ba har su Fujjirat
Yace "ai yun kurin kashe ki kadan ne har uwar ki da kuman ki sai sunyi nadaman haifuwan ki idan baki ne momin mata ta cikin kwanaki ukku ba kuma da lafiya ta dan duk inda lfy yake sai kin nemo, zakuyi nadama."

"Nabil ne kake gayawa haka, uwata bata ci darajan ita Yaya ce awajen ta ka uwar taci darajan daukana da tayi tabaka aure bana."

"Aure fa kikace a tsakani na dake yanzu bawani aure naba ki kwanan 3 kine momin mata ta bawani aure a tsakanin mu balle naga darajan sa".
Hadim dafe kirjin ta tayin tana jawo numfashita amma ita yaga gare ta kasa fusgo numfashi tayi jikake yif ta zube kasa ba wani alamum numfashi.

*to dama de na gayamu ku Nabil bai iya bacin rai ba me nufin san nacewa ba maganan aure Hadim ta saku ne?*

*to masoya ina Hadim zata fara neman Fandau me zai faru*

*B JATTKO*
[2/4, 9:46 AM] ‪+234 810 507 7087‬: *DAMATA*




*NA*




*BATUL ADAM JATTKO*


Khadija salisu
Mmn Nabil
Muna tari



(Editing mzz daddy)







*38*



*Y*ana gani har takai kasa baiyi yunkurin tareta ba dan shima ta kansa yake, ji yake kamar yafadi yanda zuciyar sa take wani irin tafasa yanzu shikenan Fatima bazata gane niba acikin sabon kwakwalwar tata? ko zata soni kaman da? ranan da zan tafi ma fa sai da ta furtamin kalmar so.
Meyasa ni ban bata amsa mata ba?
Hadim kin cuceni, shi yanzu bama ta tonan asiri yake ba yagan ta kadai ne burin sa.

Hadim meyasa kikamin haka, mena miki?
Dakyar ya taka kafafun sa ya karasa inda fridge yaka ya dauko roban ruwa ya fincike murfin yana daga tsaye yasaki ruwan me uban sanyi akanta ai a firgice ta saki ajiyan zuciya
"ai baki isa ki mutu baki nemomin mata ta ba."

Hadim dafe kirjin ta tayi setting inda yake mata zafi.

"haba Shid kaji tausayi na mana kanason rasani ne idan wasa kakemin kadena, banason kana ambaton wanan yariyar da matar ka ko kanason kasheni ne? ni kake cewa karna mutu sai nemo maka matar kar cikin kwanaki ukku, idan ban sameta ba ba aure atsakanin mu, bani ba iyayena ma zasuyi danasanin haifuwata da'gaske ne? Wllh wannan sautin kunnena ya bani muryar tane ya fara tsarkewa .

Shikuma yanda yaran suke kukane yasa ya dauki su Ma'aruf ya kama hannun Fujjirat zai fita.

Hadim tace" Shid kar kafita kabar ni cikin wanan halin kaji tausayina".

Ko juyowa bai yiba
"Habibi kar kafita Habibi inacikin wani hali".
Saida taji k'aran buga kofa sanan ta,
kwantar da kanta da take jin yana mata wanin irin ciwo, ko makiyin ta yaga halin da take ciki zai ji tausayin ta.

Da kansa yakai yaran bangaren ma aikata yazo ya fada mota baima jira security dinshi ba yaja mota direct airport ya wuce office Oeid yana shiga Oeid ya mike yana cewa "welcome Shid" mika masa hannu Nabil yayi sannan suka zauna, ba yani ya masa nayana son a tabbatar masa da tafiyan Fandau, ya fadi sunan ta na jikin passport aiko atake aka bincika aka tabbatar masa da tafiyan ta yace aduba masa mu amullan ta acikin jirgin tunda gashi Security's ya mai daukan wajen, ya nuna inda Musa yakama hanun ta suka shiga cikin jirgin amma saime da aka kira security na cikin jirgin ya turo da audio recording na ranan sai cewa yayi yayi delete din su, hannu Nabil ya dunkule jikinsa sai rawa yake Oeid yace "aiko da Dr MD akayi tafiyan aranan amma bazai wani santa ba saide dauki numbern shi Musan da sauri suka yarda da wanan, bugu daya Musa ya dauka suna masa bayani yace"wllh da yazo sauka ba neman da baiyiwa yarinyar nan ba amma bai ganta ba saide tun acikin jirgi yaga wata taje wajen ta yaga suna fira alhalin shi Hadim tace masa bata magana kuma har matar yanema bai ganta ba".
Nabil dura masa ashar yayi yace "to ka nemota duk inda tayi inba hakaba zaka gane kuren ka".
Yaro ko dama dan maikudi ne, suko yaran masu kudi ko na kwarai suka kashe sunsan bawani abunda zai samesu dan haka cikin isa yace "nide amana akace an bani kuma saboda ALLAH aka hadani na karba dan bangan ta ba za ace wani idan ban nemota ba zan gane kurena, kai waye da zaka gayamin wanan kasanne waye kuwa?

Nabil da kalaman yaron ya sake bugansa ko magana bai tsaya ya masa ba ya kashe wayan atake ya kira office yan sanda na kano yadauki address din yaron ya tura musu yace sukamo shi harsai yazo.
A take suka amsa komawa yayi mota harzai tada yaga zuwan sa gida ba shida wani amfani dan idan yaci gaba da kallon Hadim zai iya hallaka ta kuma ma me zai zaunayi a garin bayan an tabbatar masa da FATIN sa tana can, amma yakira sani yace ya bincika yace ba wani labari gwara yaje daga gidan ayi komai agaban sa yafi, ya ciro wayan sa yacewa wani daga cikin yaran sa yace ya kawo masa su Fuj yana airport dan bayajin zai iya barwa Hadim yaran sa.
Shikuma ya fita yayi ciku cikun tafiya nan danan aka maida jirgin da zai je sudan akace sai yafar sauka a 9ja dole maiduguri yafara yada zango saboda ya ajiye yaran kafin yashiga neman Fandau.


Dr MD tunda ya shiga d'aki ya fara safa da marwa wanan wane irin zalunci ne abokin sa yayi? wato shine dalilin da yasa yayiwa Malam wanan hidima, shine yasa yafifi ta mama Aisa acikin matan Malam ko, har shigowan Habiba yana tunani tace "haba Abban Nofal wllh banji dadin yanda kayiwa yarinyar nan ba, yaci ace kamata yaki taji sauki tasha wahala."
"My Habtee naji tausayen ta kawai inason nuna mata kuren tane, tana mace tabi saurayi yanzu da wanda zai lalata rayuwanta ne fa?
"hakane tayi lefi amma me mafita?

Yace "A yanayin bayanan ta nagane Shid yakamu da sonta kuma nasan zai nemeta yanzu idan na dauke ta na kaita gidan Malam shid yana zuwa zai dauketa ya bada ita dan yanason Shid kuma bai kamata Shid yasake samun ta a araha ba inason sai yayi kuka yayi nadama sosai kafinnan zamu koma da ita London zansa ta makaran tawaye tasan al alamarin rayuwa,
Inason sai shida kansa yakai kansa gaban malam ya tunawakansa asiri ya wahala wajen nemanta kafin nan ta zama cikakkiyar mace wanda zata iya kwatarwa kanta yanci."

Tafa hannu Habiba tayi tace"yawwa my sweetheart wllh Hadim zata gane kuren ta dan sunban mamaki daga ita har shi."

Ummi da abokiyar zamanta Hjy bintu wanda suke kira da *Iya* sunyi mamakin ganin Nabil a rikice wanda ko gaisuwan wani irin yake amsawa.
Iya tace"Shid lafiya yau sai kukazo ina Haliman?" Grema yace "kaida yara ne kawai ina take?

Ajiyan zuciya yayi yace "yayesu tayi ni kuma kawai na daukosu su zauna ahannu ku ita Fujjirat zan kaita gargar gidan Malam."

Ummi tace "amma ko yayesu akayi bai kamata arabasu da mahaifiyar su ba kuma ni bakomai nake jiba irin yaya ZAINABU, yanzu koni bazan tsira ba zata ce dasanina akayi, dan haka nide bazan karbi yaran tazo ta gama tozartani gaban yara ba, yaya saide ke idan zaki karba."
*Iya* tace" a a wace ne."

Ummi tace " to dauki su duk ka kaimata su karma kanuna kafara zuwa ta nan kuma kar kace Hadim ce tasaka kawo su gwara kace ra'ayin kane."

Nabil yace "Girema dauki yaran nan kakaiwa Inna nema gani nan zuwa yaja hannun Fujjirat suka fita. Direct gidan *Zannah* yasa driver yakai shi yana zuwa ya tarar tarar da shi yayi manyan bak'i.

Almajiran da yaran gidan suka ta kwasan gaisuwa kota kansu baya bi shide baiki yana shiga yayi tozale da Fatin sa ba dan yanzu ba wani fargaba ko tsoro na ganin ya gurfanar da kansa agaban malam ba, inde zai sameta. A tsakar gida ya gaida matan gidan ya wuce part din mama bai ganta ba ta na area din kitchen dan duba yanda ma'aikatan suke sarrafa abincin dan malam yana da bak'i. Zama yayi akan kujera ya daura Fujjirat saman cinyar sa amma me yana dagowa yaci karo da wani tafkeken photo Fandau alike a bango tayi irin tsayowan rike kugunta nan tasha hoda da janbaki kan ta kile dinnan duk da bawani kyau tayi ba Bagana tasa anyi editing dinshi ba laifi, ya kasa dauke idon sa akan pics din.

"kai lale da bak'in ba zata, ko dama daga Rasha din nan kuka yo ne?

Ahankali ya janye idon sa akan pics din ya zamo kasa yana gaida mama, itako mama daukan Fuj tayi tana amsawa. Mama ta daga ta kalli Nabil da take ta masa magana baya bata amsa sai taga photon Fandau yake kallon."

"kaide baka gajiya da tafiye ta fiye gashi kana shirin koyawa Hajara ni da kun bani ita ai gara ma Shateema yaki barmin Tajjudin yana manta nono suka karbi kayansu."

"au shima anyaye shi kenan?
"Eh ai uwar da juna."
*Azuciyar sa yace"zuri ar ki akwai albarka gashi daike kin tsaya a 2*

A fili kuma yace" ai dama yanzu Fuj zata zauna awajen ki har sai na dawo."

Mama tace"aiko na nagode".

Sake kallon pic din yayi yace "mama wanan yariyar fa?

Mama takalli photo cikin sosuwan rai tace" kanwar kace."

"Mama ya banta bajin kin kira sunan taba tana ina yanzu haka?

Hawayen da mama take boyewa ya biyo kumatun ta. Ta tashi ta koma daf dashi yanda bawan da zaiji zancen.

Tace"Muhammad ban taba gayawa wane wanan maganan ba dagani sai malam sai Bagana muka san zancen nan amma bansan meyasa naji inason gaya maba sai dan nasan kai mai kaunata ne nasan kuma zaka rike sirrina daganan ta gaya masa yan da akayi suka rasa Fandau har yanda malam ya rufe bakin mutane da cewa ya mata aurene da bako, ta karashe zancen cikin kuka."

Nabil shima hannun mama yakamo ya hada dana Fujjirat ya dam ke yasa kuka, dakyar mama ta lalashe shi ganin Fujjirat ta fara kuka.

"ni yanzu cikin kwana kin nan ma mafarkin tane yake damu na kullum cikin kuka nake ganin ta."

Nabil tsoro ne ya sake kamashi karfa tana cikin mumunan hannun gashi atunanin sa zaizo ya sameta amma shiru.

"to mama tunda ta tafi bawani mataki da aka dauka na neman ta."

"malam cewa yake yana addua akanta kar naji komai."

*yanzu kenan idan nasa mu Fatima nakawota wajen Malam zaice dama ni ya aurawa awuce wajen yazanyi na samota?*

A fili kuma yace "mama zan samota zan kawo miki ita da hannuna." bai jira amsan taba yamike da sauri yace "mama sai na dawo zan sa Grema ya kawo mata kayanta."
"Ai idan kayane karma kadamu tana da kaya agidan nan sif dina cike da kayanta Hajara akwai sutura ai".



Har yanzu wajen Malam da bak'i dan haka kawai wucewa yayi.

Jidda ce take jan motan Yasmin tana gefe sai Gana da Zahra suna baya zasu wuce daidai Gargar anguwan Zannah Yasmin tace" yawwa Jidda dan ALLAH ranan da muka raka Aunty Hadim daukan Fuj gidan Malam a parlour matar ina pic dinda na nuna miki da muka fito nake cewa na taba sanin me kama da ita amma na manta to

Please Login or Register in order to submit comment