Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register



Malam ya nunfasa yace " Alhamdulilah anan ya kwashe abinda yafaru duk yaga yawa sarki abinda yafaru
da Fandau har auren Bagana da Shateema atake Malam yasa aje adauko Shateema da iyalin sa

Ai Malam da kansa yayiwa Maimartaba iso har d'akin mama Aisa tana ganin dan uwan ta duk da yawan shekarun saida ta gane shi dan ba rawani ahaka yaje aiko Mekewa tayi tace "Ya Barumi Dasauri ya karasa inda take yakama hannun ta ya zaunar da ita yace Aisa yar uwata cikin Ummana nine Barumin ki ban guje miki da gandan ba sai dan ina son na tsira da lafiyana kema shiyasa nasa Baba ya aura miki wada bazai taba sha awan zaman Niger ba balle yane mi sarauta su gama da dake amma duk da haka bamu tsira ba saida sukayi abin da nazo na karbi sarauta suka huta."

da ganan ita ma ya kwashe komai ya gaya mata agaban ki shiyoyin ta da kuma su Ummi da Maman Hadim da ita kanta Hadim din azuciyar tace ba banza ba Fandau ta keda kalan yan sarauta ashe ita gada tayi uwa da uba Nabil yajijina kai yaji dadin samun asalin Mama dama abin yake shirin yi kenan idan komai ya daidai ta zai dauki su Mama ajen neman dangin ta sai gasu dakan su
Malam yaga batar masa Nabil da sauran mutane Fandau jin abin take kamar amafarki wai dangin Mama kawai sai ta tashi taje ta fad'awa Barumi ta sa kuka ana cikin haka Bagana da Shateema suka shigo cak Maimartaba ya meke ganin Shattema ma yazama cikeken namiji daga gani naira yazauna masa wanda ko yan uwan sa na can ba abinda zasu nuna basa hatta Afwan wanda yabiyo bayan Shateema ka rasawa yayi wajen sa ya rungumo shi yana "cewa aboki nagode haka kaza marmin da d'ana ina ma da Hjy Kare mukazo taga Shattemanta da kullum take min maganan sa.
Shateema "cikin firgici yace "Sayinna waye wannan shiwaye tunda nake ba wanda ya taba rungumana sai Mama Aisa.
Malam yace wannan dan uwan mamar ka Aisa ne ciki daya kuma shine mahaifin ka ai Shateema bai san san da yasake raruman mutumin da akace baban sane kuka yasa har Mama da Bagana da Fandau kowa kuka Shateema yace "kaine dan uwan mama dan ga kaman ku daya da ita amma idan kaine babana meyasa kaman ta dani kabawa wani buzu yakawoni.

,"ban manta kaba d'ana buzun da yakawo ka gashi can a waje tare muke dashi yayan maman kane kamar ku daya kuma su buzaye ne akwai kannen ka maza Afwan yana aikin a India Dr ne sai Zannah shikuma shi yagajeni asiyasa shi nabar wa kujera na na minister mata na 3 mahaifiyar ku itace uwar gida inada yara dayawa yanzu haka Afwan yataso gobe zai sauka ananan sai mu iba mutafi kuga dangi.

Inna ZAINABU tace "yo ashe ba abanza ba Aisa take da dattako ahen jinin sarauta ce.

Mazan suka tashi suka fita sai Nabil ne kawai azaune Har su Ummi sukayi sallama suka tafi
Hadim tace my star ka tashi mutafi Nabil ya Kalli Fandau yace "gawan zata b'ata mana lokaci nan malama tashi zamu tafi.
Tadaga ta kalle shi tace "Allah yakiyaye"

Nabil ya zoro ido yace "ban gane ba kina nufin ba tare zamu tafi ba.?

"tace ai yanzu nacewa Abban Nol yagaya wa Aunty anan zan kwana.

Nabil yace "ke kuma me gamin ki da gidan wata Aunty bayan da naki gidan.
Hadim tabe baki tayi zuciyar ta yana bugawa wani kallo da taga Nabil ya nayiwa Fandau kamar bakowa awajen sai su
Hadim Tace "Bagana nemo min Maaf acikin gidan yayi wani wajen zanu tafi.

Bagana tace "ai Aunty yaron nan bayaji ko kadan yana ta faman dukan yaran mutane har Tajjudee ma bai ba riba kije kine mi kayan ki dan idan nasa mu yana dukar mana yara bazan bari ba.

Itade Hadim fita tayi Nabil ko yakafe sai Fandau ta tashi sun tafi.
Bagana tace "Mama kishiga cikin maganan nan mana.

Mama tace "Bagana rabu dasu sunfi kusa yanzu tare suka zo ko sallama bata muku ba a gidan Mutarin.

Nabil yace "Mama nifa ba gidan Mutari zan gaita ba gidan ta.

Dariya Mama tayi tace wane gidan kuma ban da abin ka haka akeyi.
Yace "Mama me? ake to.
"kabari akai ta idan ansa ranan tareya haka akeyi.
,"hama Mama wane irin tariya bayan ba musulumci bani kar kibata kofa mana.

Mama tace "Malam karami kaje matar ka tana jiranka Fandau sai anshiya.

Komawa yayi yazauna yace" tagama shirin ita Hadim bari nasa akai ta,
ita kuma ta gama mutafi ko nan da dare ne .
Mama tace " ajaf shirin lokaci guda zatayi ne sai nanda kaman sati idan anyi dawuri ma kenan."
atsorace Nabil yace "Mama kina tufin ma yanzu zan tafi da *mata* ba wannan din wane irin shiri ne ni gidana da komai idan wani abu zata dauka anan ta fada inshiyar mata da kaina yanzu amma banda horon kwana ni daya mama kinsan yanda nayi missing dinta kisa ta tashi ko na hada d'a Sayinna.

Itako Mama shiru tayi shida magana ita da jin kunya me ake da girma cikin turawa kwata kwata a d'abiyun Nabil ba na tsaren kanuri ko Shateema da ya girma aga banta ba zayi wanan rashin kunyan agaban ta ba.

"Mama kinyin shiru my one tana wajen tana jiran mu.

Dabara mama ta masa dan tasan zai iya zuwa ya hada da Malam kuma ba ruwan Malam zai ce ta bishi
tace "kaga yanzu dan uwana yazo inaso idan dare yayi mugana ajunan mu suma Bagana da Shateema anan zamu kwana dan haka gobe sai kazo kutafi.

"To Mama bari nasa agai my one sai mu kwana ayi firan dani.

Mama tace "a a baza ayi haka dani ba shima Shateeman inda yana da wata matar ai bazan rike shima dan bai dace ba matar ka baza taji dadi ba,
ai adalcin da akecewa kayi fa dama irin wannan ne kar kanuna fifiko tsakanin matanka zai iya kawo fituna da gaba dole asamu wacce tafi kwanta mata arai amma ka danne kar nuna afile ko ita wanda ka fison kar ka bari ta gane ita kafi so dan kar tayi anfani da damarta ta dagawa yar uwar ta kai.

Nabil yace "tabbas Mama da wacce ta fiso amma mama kimin adua kar ta gane dan kar ta mana girman kai.

Bagana dariya tayi sosai

Itako Fandau gaban tane ya fadi towayafi so kenan cikin su

Mama tace "wannan damar kace kai zaka zama namiji duk da nasan dama kai namijine yanzu
kaide kaje goben kadawo akwai karin nasiha da zan maka.

"Yanzu Mama haka zan bar matata na tafi anya ba ashigar min hakki ba wllh badan keba bazan barta ba.

"yawwa to nagode d'an albarka kaje.

Cikin takunsa na isa ya taka har inda Fandau take ya sugunnan ahankali yace "kinga kinjawo mana ko da ina cewa ki tashin nan kika tashi da ba tace kizaun ba dan ma bani kadai nayi asara ba har dake,

Asali ma ni inada wanda zata mayemin gurbin ki,
kece da asara dan wata k'ila nabaki y'ar da aka kwace ayau dako biyu zan baki har da bonus,
amma yanzu me zan samu narage zafi nafa sa araina yau...
Dassuri Fandau ta meke dan gani take su Mama sunajin meyake cewa amma ko taku daya batayi ba caraf ya cakke kugunta a tsorace ta juyo ta Kalli inda mama da Bagana suke basu suke kallo ba amma da ganin yanda sukayin shiru sun san me akeciki
Fisgewa tayi zata kwace jikin ta ya juyo ta ita yana mata tani irin kallo hannun yasa yarike hannayen ta bakin sa yakai setting nata yace "nace mezan samu my baby.
Idon tane yaciko da kwallah dan wanan tozar cin nasa da meyayi kama agaban uwata.

Girgiza mata kai yayi yace "to me ba anmiki yanda kike soba bazaki bini ba me na kukan kuma.
Ahankali tace dan Allah ka cikani.
Lumshe ido yayi yace '' Wow ko kinsan har da irin wannan muryar naki nayi missing.
Bakin sa yake kaiwa kusa tasan zai iya yin abinda yafi haka dan haka cikin karfi ta fisge tage kusa da mama da ta sunkuyar da kai Bagana ko danne danne dake awaya tana mamakin Nabil da rashin kunya

Yace "Mama kingan ta ko wai bazata rakani ba.

Mama har zata ce rakashi sai tatuna da rashin kunyan sa idan yafita wajen ma ba fasawa zai yiba ga kofar gidan su da jama a daranan Allah kar yaje yayi wani abun,
tace "a a bar rakiyan nan kasan Fandau tana da kunya me damuwan ka darakiya kaida gobe zan baka ita gaba daya.

"kallon Fandau yayi yace "Mata wai kunya kikeji?
Fandau ko kallon inda yake batayi ba
Ya juyo kan Mama yace kigaya mata ba kunya tsakanin miji da mata hakafa tayi tamin abaya ma sai fa kin koya mata wasu abubuwa abaya na mata uzuri da auren na rashin shirine baki bata nasiyan aure ba amma yanzu nasan zaki gaya mata komai bana son wani kunya.

Mama da abin yade na bata mamaki tace "ai shine nake son ka barta amata komai akoya bata komai.
Yace "shike nan Mama ki mata kafin goben.
Amma nima anjima da daddare zan kawo Akkam ya dauki Akkaam da yake zaune cikin keken sa zai fita
Fandau tace "Mama kice ya barmin Akkaram.
Mama da sota ke kawai taga ya tafi tace "ba anjima zai kawo shiba.
Juyowa yayi tare da kanne mata ido yayi mata murmushi ya fice.

Bagana tace "Mama wannan rawan kan YaShid dinnan anya zai iya zama da mata 2 awajen daya.
Mama tace" akwai de matsala saide muca ALLAH ya kawo musu zaman lafiya.

"Amma Mama da alamun kamar yafison ya Fandau fako.
Mama tace gaya miki yayi.?
"A a kawai alamu nagani.
Mama ta daure fuska tace "to karna karajin haka abakin ki
Nabil yasa mu Hadim da yara amota tacika fam yana shiga
yace "
Sorry my one.

"Yanzu abu Fuj ina ka tsaya.

wllh Mata ce wai tamin rakiya taki
Hadim ajiyan zuciya ta sauke cikin muryar tausayi tace" yanzu my tsar shikenan munza ma mu 3 kishiya ta tabbata akaina kenan ko?

Jawota yayi yace " *hukuncin Allah* wannan mukaddari shiku ma hakkunne akan kowane me imani Halima bamu tsara rayuwar muda haka ba muntsara ne iya mu amma kaddara ta daura mu akan wanda Allah ya tsara mana yazamuyi kuma ke kika fara kawo wannan shawaran da naje na gana da ita nagano yar gidan Zannah ce saida na koma nace miki abin nen bazai yuwu ba amma kikace Zaiyuwu kika nace akayi abinnan kinga yanzu yazaga yo ta inda yafi karfinmu dole muzauna da ita murungumi kaddara shiko kaddara mekyu da marar kyu duk kar bansa imani ne kidena sa komai aranki ba abin da zai faru da zaman mu zanci gaba da sonki zannu na miki tattali fiye da da idan gidana ya gyaru kece idan ya b'aci kece wannan yarinyar yanda kika horata haka zatayi idan kika so kuzauna lafiya nasan zaku zauna idan kika so fitina zakuyi wanda nasan kece da asara dan idan Kuna zaman lafiya yaran baza su kane wacece uwar ba koda zasu gane sai sunyi wayon da baza su iya nuna miki ban banci ba amma idan ba azaman lafiya nasan tunsuna yara zasu gane kuka bayan mahaifiyar su zasu koma inde kuna zaman lafiya ba abin da zaku nema kurasa.

Goge hawaye ta tayi tace, "to yanzu kana nufin kana sonta fiye dani koyan da kake nunawa kafi sonta kaduba yanda karukice da batanan kadinga gayamin magan ganu shine nake ga zaman bazai min dadi ba.

Goge mata hawayen yayi yace "waya kaya miki na fison ta da na rasa ta nariki ce ai inda ke narasa da saide arasani haba Hadim dimata dama nasoki balle yanzu da kika rikemin yara kike nuna musu so ai yanzu inde naga kun zaun nafiya zan soki fiye da da.

"towa kafi so acikin mu.

Shiru yayi can yace "Gaskiya yanzu bazan iya cewa ga wacce nafi soba abin da nasani ku dukka matana ne saide ance zuciya ta fison mekyutata mata to idan na zauna daku duk wacce tafison kwanciyar hankali na inaga ita ce.
Hadim ta sauke Ajiyan zuciya ta dauki Akkam da yake kuka tace "ALLAH Abu FUJJI wannan ma yashi ga raina ina son sa.

Dariya Nabil yayi yace "to komu koma wajen Baban ki zannah ya hada miki dashi dan naga yafi sonki fiye da Fandau din ma.
Ita ba dariya tayi tace "wllh kuwa ni ma haka kurum naji ina mutu kar sonsa dan yanzu bazan ce maka gawan da nafi so tsakanin shida Babana ba Gaskiya da can jin labarin Zannah nake yanzu naga halin nasa da akecewa Zannan barno katan barno afili,

Yanzu fa da zance inason har Akkaam din saiya hadamin dako naji dadi toma meyasa bance har shiba.
Nabil dariya yayi yace "zaki iya mana ai kin kware da mugunta kina gani tace abata FUJJI kika kijin tausayinta har kuka ta miki tana cewa Aunty kiji tausayina amma ki kak'i.

Tace"haba taya zanji tausayin ta bayan nice abin tausayin ai da gaiya nakafe nima FUJJI nake so tunda nasan kafi sonta ko ta dalilin ta nima sona zai karu.
Yace 'Gaskiya kam bana jin zan sake son wani fiyeda Ummuna.
drive yaja suka tafi

Da yamma Fandau sugama waya da Habiba ta kaya bata har sunwuce kaduna.
Fandau tace "haba Aunty kuma sai kibar ni.

Ni na isa na fito da matar Shiddams nasan de naga ma miki abinda zan miki sai fatan Allah yakawo zaman lafiya akwai sauran abubuwan ki kije gidan Aunty Maimuna nan ne zakifi sakewa kiyi gidan ku gidan jama a ne shiya sa yar sundan ma acan ta sauka kiyi kitafi tana jiranki.

Fandau tace "yanzu Aunty sai yaushe.?

Habiba tace "Sai kunzo London zance.

"umm Aunty agaida min Haris da Kairat Nol muyin fad'a.

YaMainuna ce takira ta tace tazo tawuri mai mata aikin tazo dan Wata aka dauko a sudan wada zatayi wa Fandau aiki Habiba ce ta biya kudin komai
Fandau ta gayawa Mama zata tafi gidan YaMainuna mama tace ga wanan ki tafi dashi gaba daya zaki shanyen ai gwara kawai kije da ga can rashin kunyan mijin ki yayi yawa ita de Fandau ta dauki jarkan ta shige d'aki dan ta shirya ta rasa meyasa ta ko ina ana ta dura mata abubuwa gashi maran ta sai ciwo yake mata

Yar sudan ta murjen jikin Fandau sosai rami aka tona mu sammanin aka sata ciki aka fura wuta t
Da wasu ingan tattun itacuwa ake gasa Fandau dashi aka rufeta da barko sai kamshi yake ta shi sai ta kakayi kwanaki ukku ana mata gada ma Fandau da laushin fata abin yasake karuwa sai wanda yagani ita kanta me kyaran da akace matar Shiddams ce sai tasake azama wani irin shek'i da sansi take kowa ya kalleta sai yasake kallon ta arana na 4 Mama ta kirata tace duk abinda za ayi yau tazo ta koma gidan da
"Mama aikin fa ba Agamaba.

"ko ba agama ba kisan yanda zakiyi rasshin kuyar Nabil ya ishini bazan iya daukan magan ganun da yake fada ba yau har da Malam ya hadani jiya ma Ummin sa yaturo min wai tazo taji na boye masa mata ko ina shirin hana shine na gaya masa harda kuka yayi wa Malam abin ya isheni yanzu nazo akiran Malam yace zaikira Maimunan ma.

Fandau tana kashi waya ta gayawa Maimuna suka gayawa yar sudan tace "ai wannan aikin da na mata ya isheta ai namata aikin mekyu saide abin da nake so dake wanan aikin da namiki kisamu duk bayan wata 6 ana miki dan maku meduguri kuna da abubuwa muma anan ake kai mana wasu Gaskiya an miki aiki duk da dama fatan ki mekyu ne.

Wow wani Lalle da aka zubawa Fandau da kitso abin sai wanda yagani bayan tayi sallahn isshai ne wata me makeup ta zezara mata kwalleyan da ko mama baza ta gaji da kallon ta ba
Ta ko ina sai
ta kifta sai kamshi take bazawa ta tsaya agaban mirror ta na kallon kanta tace yanzu dama haka nake da kyu lalle a aurena na farko nacuki kaina da ta tuna yanda aka kaita daren farkon kamar wata sobon kamu ita kanta sai da taji kamar kar ta yafewa kanta

YaMainuna ta shiro tace "Fandau kizo mutafi Baa har yayi waya wai ga Nabil agida ai nikam yau sai na ga Nabil dinnan ido da ido

Agidan ta samu yan uwanta mata dayawa sunzo rakata ALLAH sarki Bagana sun tafi Niger da Shateema dan da harda Mama aka shiya tafiya sai Malam yace abari Fandau ta koma gidanta sai shi yakai maman da kansa inyaso sai suzo dasu Shateema dan bayan da ba ayi da shateema maba yatare can yaki shi yafi son Nigeria ba arage shi da komai ba

Mama tayiwa Fandau nasiya haka YaMainuna tayi ta zagawa da ita d'akin matan gidan wada yanzu sun sauko gaba daya suma sunmata nasiya BaGaji ko harda neman yafiya
Sai d'akin Malam shima nasiya yamata sosai san nan yadauko Qur ani da sallaya ya bata kamar yanda yake yiwa dukan yaran idan idan za akaita d'akin miji
Yace" kibi mijin ki rike Qur ani ki kula da ibada daga kar she yadauko alkebba kamar yanda yake yiwa sauran yaran ya rufa mata dan sai anbiya dasu fada kowace amaryar agidan zannah sai ankaita gidan SHEHU SHEHU yasa akai ta shiya sa Nabil da yazo shi zai kai matar sa abashi aka ce A a yayi zuciya ya tafi abin sa
YaMainuna tace "Baa gobe munshirya walima zamuyi wa yar uwar mu.

Malam yace "a ina zakuyi waliman ?

"a gidan ta zamuyi.
Malam yace "a a Maimutatu sau nawa take kaya muku bana so inde gidan da abokiyar zama to kugama duk abinda zakuyi agida inde ba taron suna ba ban hana ba.?

"Eh Baa wannan dinne yazo akureren lokaci bamu zaci za ayi tariyar yanzu ba ne.

"to ku hakura tunda ba sabon aure bane kuma ta adua ainda kuke ya isar.

YaMainuna tace "to Baa Allah yakara maka yawan rai.
Ta gyarawa Fandau alkebba akan lifayan ta ta kama hannun ta suka fita
Zasu shiga mota Fandau yace
tace"Yamuna ba zan shiga wajen Mama ba?
"a a Fandau kuka zaki mana ai kungama.

Gunsu matar SHEHU tayiwa Fandau nasiya tare da bata turaruka da wasu abubuwa ta hada mata bayi 2 tace zasu koya mata wasu abubuwa da zai mata amfani sannan aka rakata bangaren SHEHU yamata nashi nasiyan tare da yimata kyuta
Aka kwashesu sai gidan Nabil da yake shagari quarters gida ne nagani na fad'a dan an shafti jeji inya ganin ka fadin yanda gidan yake b'ata lokacine
Part din Hadim aka fara yi da ita
Hadim uwar yan mata ta tarasu suna zaune su yasmin Hadim ta karbe su bayabo ba fallasa da sukace amana dariya tayi tace "amana na karba Aunty muna tun agaban Baa.
Addua sukayi suka ce to inane part din nata dakan ta tashi ta kama hannun Fandau ta raka ta har bedroom tace "bari akawo muku abinci.

Suka ce laki barshi wllh munci a gida kuma da muka je sheuri sai da kuka kara.
Tace "aiko dan ku akayi dan haka sai kun tafi dashi.
Zahra tace "Wllh zaki hadamu da aiki dan wllh kowacce gidan ta zata wuce dare yayi.
AISHA tace "akawo kawai sai akai gidan ai zaiyin amfani suda suke da almarai.
Bayan tafiyan su Fandau zama tayi agan gado meyafi wandan dadi na bari ana farko *DAMA TA* ya kufcemin gani cikin yan uwana ankawoni cikin mutumci
Tana wannan taci anbude kofa dama fuskan ta arufe yake amma daya ke liffayan shara sharane tana ganin su gaban tane taji yabadi tunowa da ranan da ta fara ganin su ahaka ta gan su randa Sani ya kaita London ahaka suka shigo shigan su iri daya hannun su sakale da na juna suna tabu ahankali suyi matukar kyu koda yake dama sarakan kyune dan Fandau kyun Hadim har tsoro yake bata
Ahaka suka karasa suna jifanta da murmushi tana kallon su tacikin mayafin sai da suka zo kusa ta sunkuyar da kai zama sukayi abakin gagon Hadim ce ta fara magana tace amarriya ko me dan kiraki mani kinga tarishi ya maimaita kansa ko nice de Halima Jaji nashiko miki da mikina Muhammad akaro na biyu kamar yanda muka maki mamaki awancen karan yau ma zamu sake jefaki..............


*kashhh* 🤦‍♀
*Sister kuyi hakuri bana jin dadi ne wllh*
*B JATTKO*
[3/9, 3:08 PM] BATUL ADAM JATTKO: *DAMA TA*




*NA*

*BATUL ADAM JATTKO*

Wanan shafin nakune group na masoyan Fandau da Nabil khulud na baku wannan duk ka 🤣🤣🤣

🌈Kainuwa writers Asso🤝🏻

*48*

Cikin wani salon mamakin domin mun jijina miki kedin me sa a ce ba k'aramin sa a kikaci ba kin samu mijina kuma nima na yarda na karbe ki abokiyar zama dalilin karamcin da Baban ki yamin shiya nunamin Duniya ba komai bane shi tunda har ya danne barin cikin yar da ya haifa yabawa yar wani hakan yanunamin wannan hadisin da ake cewa kasowa dan uwan ka abin da kasowa kanka,
ina fatan zamuyi zama na fashimtar juna my star ba kace komai ba.

Murmushi yayi yace my one inada abinta cance amma naga bakuwar tamu kamar ta nacikin bak'unta ne saida safe zamuyi zama na musamman.
Hadim tace" ummm to yanzu saide nace muku saida safen ku ko,
auna manta ban fa siyi baki.

Nabil yace "Gaskiya ne dan yanda aka ja faska aka rufen nan inaga saikin siya.

Hadim haurawa tayi kan gadon ta dan d'aga mayafin ido ta zaro tayi saurin sakin mayafin tana karanta Innalillashi azuciyar ta ita da kamshin da take ji ajikin Fandau tun sanda zata rakota d'aki ma yake sawa gabanta yake faduwa balle
Yanda taga fuskan ta tasan ta sha gyara duk da bawani tarkacen makeup ne afuskan ba dan ko janbaki ba asamata ba dan meyin makeup din haka tace lips dinta kalan yayi daidai da makeup dinta dan shima ja ne gashi sai sheki suke
yanzu wannan zan bari da mijina nashiga ukku amma sai ta dinka karanto adua sai ta sauke ajiyan zuciya
Nabil yace "yade my one?
Murmushi tayi tace "wllh my star amarriyar tayi nayi kuskuren bude fuskan ta batare da biyaba yanzu de kai zaka biya.
Dariya yayi yace "ai nasan my one tana jidani baza ta yanka min abin da bazan iya ba me ki keso na bada.?

Hadim tarasa mezata ce kawai sai ta Kalli hannun sa tace "zobin ka zaka bamu.

Yakalli tsadeden zoben yatsan sa wanda yake iri daya dana yatsan Hadim ma ya ciro ya meka mata ta karba ta janjo hannun Fandau zata sa mata a ya tsanta wani irin laushi taji wanda Hadim bata ta b'a sanmanin akwai shi fatan mutum ba ga Lallen nan yagama hawa kan hannun Nabil zubawa hannun ido yayi Allah Allah yake Hadim ta fita dan idan ta matsa zai iya kof sawa agaban natama zoben taga ya karawan hannun nata kyu dayake na farin daham ne
Da ganan ta sauko a gadon tameke hannun ta yaruko yace "ya haka yana kallon fuskanta tace" da akayi me?
"naga kin meke baki budemin fuskan da nabiya ba.

Azuciyarta tace bazan iya budewa naga ka kalli wanan fuskan nata ba
Afili kuma
Tace" ai dan ansai da maka abu balalle abude kagani ba zaka iya budewa da kanka musamman amarriya ai angonta yaka mata ya bude ta dan abata matsyin ta na amarriya ko.
"to yanzu ina zaki da kika meke.?
Hadim tace "kasan nabar yara banason wani yafar ka bai ganni ba.
yace "ok muje na rakaki.
Suka fice
A parlour ta tsaya tace "ka koma rakiyan ya isa Allah ya tashemu lafiya.
Yace "nide sai na kaiki har wajen yaran ki naga kwanciyar ku.
Haka suka tafi har bedroom din Hadim sai da ta kwanta yayi adua yasha feta sannan ya da go fuskan ta cikin damuwa yace "my one ke ta musamman ce wllh ina tunanin yanda zan iya kwana ba tare da inajin nun fashin ki ajikina ba bawai bana son kasan cewa da Fandau bane a

Please Login or Register in order to submit comment