Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya farfado
Itako Fandau sai kuka take amma bana ciwon da take jiba
Ahaka
Ba Alta ta kawo wayan ta durkusa tameka masa
Kiran sojojin da suke tsaron kofan sa yayi dan lokacin doka yayi dole sai su zasu kai shi hospital
Su hudu ne suka shigo suka dauki Nabil zasu fita dashi itama Fandau ta meke zata bisu cikin tsawa Malam yace "ina zaki kuma tace" zan bisu yace"zauba." bude ido Nabil yayi cikin da shewar murya yace "kusaukeni a hankali suka sauke shi amma yana dubawa yaga duk matan Malam suna d'kin shiko arayuwan sa basu masa ba sam kuma bazai iyace komai agaban suba yadaga ya Kalli Malam yace "Malam inason ganinku kaida Mama
Malam ya Kalli matan da sojojin tunkafin yayi magana sojojin suka fice suma matan suna zunbure zun buren baki suka fita dan de basu isa su furta wani abu agaban Malam bane
Nabil ya Kalli Mama yace "Mama dan ALLAH kiyi Hakuri nasan ban kyuta ba na shigo har d'akin ki na dakar miki yarinya bayan banwake lefina nada ba na daura wani nikai na tsani hallina dan nasan zai iya sawa ha hanani
( *Hasken rayuwa ta Aisha sada* ,)
Amma Mama nasan Fandau bata san irin sonda nake mata bane bata san yanda na mutu akanta bane da ko na mutu ba zatayi sha awan cewa za ta auri wani ba yanzu lefin da nayi wa Fandau har yakai ta shukun tani da haka ina raye agabana take waya dawani kigaya mata inhar nine mijinta to ta kiyaye abin da zai tuzurani haka wllh wataran saide akwashi gawata
Tashi yayi ahankali yakara sa inda take ya zube guwoyinsa yakamo hannun ta yace "Fatina meyasa kika gujeni meyasa tun a chatting da mukeyi baki baiya namin ganki ba shiya sa kike cewa kina gujemin nadama duk sanda nagane kewacece baki san rashinki barazana ne na rasa rayuwa ta agareni ba
Kiyi magana mana ya matsa hannunta wada yake mata ciwonne kuwa wani kara ta kwallah cikin
Dama Malam da Mama sun fice tunda dama bakinta ne duk basu ga fitan suba

"me yasa kika boyemin kanki Fatina?
Zubura baki tayi ta janye hannun ta cikin tasa nata ta daura hannnun cikin tafin hannun ta dayan tafara juya kai
"Ayyya mata nine ko ya sake jawo hannun ta fizge har hannun ya kumbura yazubawa hannun ido yana gani yasan tar gadene kunsan dan ball baiwani dauki targade abakin komai ba dan she tunyana yaro ya iya gyaran targade idan yayi da kansa yake gyara kayansa ko idan acinkin abokan sa wani yayi yana gyarawa
Fakon idon ta yayi yaja hannun nata k'ara tasa jawota yayi jikinsa cikin dabara ya hadeta sosai da jikin sa yanda zata saki jikinta yana mata wani wasanni har ya fara gyara mata hannun ita ko Fandau jinta aduniyar da tajima tana nema yasa tayi lamo saida taji zafinyayi zafi ta fara jan hannunta tana kuka da yaga kukan nata zaiyi karfi kawai saiya hade bakinsu waje daya amma yana jan hannun wani kara tasa alokacin da yatsan ya fada ya gyaru kenan sake hade bakinsu yayi yanawani irin fitar da nunfashi itama haka sai da yayi facale da kayan jikinta da dafi zafi yake aika mata sakonne yazame mata tamkar wani mayunwacin zaki saida taga yakusa isa babban fada duk da itama ba abinda take so irin abin amma ta daure tameke da karfi ta fusge ta tunkuda shi tameke
Daga kansa yayi yana kallon ta idonsa yayi jajir cikin wani irin muryan da yake janyoshi cancikin makogoro yace "me haka Fatina?
itako sai kare jikinta take tana jada baya da rarafe ya karasa inda take zai kamota ta matsa
"yace mehaka?
"kai kai zan tambaya mehaka zakazo har cikin dakin uwata kanemi kayi lalata dani bayan kasakeni kaban dinbin jama a
"Mata na mayar da kefa wllh karkimin haka kar.

" karka renamin hankali mana kana nufin Fandau din dane daka yaudara ka aura
a gaban din bin mutane ubanda ya haifeka yace bani da iddan ka tun dana haifu bamu haduba dan haka bawani maidani da kayi.

"kiyarda indaura miki iddan yanzu wllh dole su hakura subarmu."

"Lalle Nabil duk dama nagane jikina kake so fiye da komai wllh banzaci abin har yakai haka ba karasa inda zaka nemi jikina sai dakin uwata."

"wllh bakiyi karya ba inason jikinki kuma ko aina zan iya neman sa tunda ina son komai naki inaso.
Cikin karaji tace "dama nasan jikina kakeso ai duk sanda jikina yadena baka sha awa zaka dena yayina ne kawai nikuma yanzu kadena moran jikina dan......
Cikin muryar tausayi yace" karki min haka wllh bazan iya daukan wannan horan ba idan baki amince dani ba wllh nakai gejin komai zai iya faruwa dani yana maganan yana dafa maransa
Tana ganin gasansa jitashi gaban ta yayi mugun faduwa da sauri ta dauki riganta ta sa shiko yanda ta sunkuya ta dauki rigan ne idon sa akan dukkan halitun jikinta da yafi so maranshi yasake dafewa maransa da yakeji kamar zai kashi shi ya kwata yana birgima dafe da maran "yanzu mata bazaki ji tausayi naba itako tama gasa juyowa dan ita tsoron sama takeji
Ayanda yake
Karasa wa tayi gaban gadon ta dauki Akkaram da yake bacci ta tayi hanyan waje saida take bakin k'ofan fita tajuyo ta kalle shi yana nan inda yake yana ta juyi

Tace "shikenan tunda bazaka fita mana ad'aki ba nina bar maka.
"dan Allah karki fita wllh zan iya shiga kowane irin hali idan na rasaki.
Kiduba halinda nake ciki."

"Wllh bazanji tausayinka ba nagaya maka kadena samuna da araha."

"wllh ke bame arahabace idan kinason duk abinda na balla ka aduniya zanbaki kibiyamin bukata yafi."

Abinda nake so dayane awajen kuma ka tabbarar minda bazan samu ba shine kace kana sona."

"idan ana magana kidena kawo banun so Fandau sonki yayiwa bakina girma da na furtashi idan kuma kinaso nafurta ne _INASONKI INA SONKI_ ."
"Taya zanyar da kai bayan kai din makarya cine mayaudari kayaudare ni kamin karya har gaban iyayena kace nabi wata saudia bana sonjin son naka dan bansa meshi asanda nake soba taya zanyar da da kai bayan nasan kai waye ne afannin yausara.

"Wallashi yanda nake sonki ban tabajin ina yiwa wani abuso kamarki ba kiyar da dani ki bani DAMA ki karbi sona zaki sameni mai amana akaru na 2."

"a a Rike abinka dan banyar da dashi ba."

dukan kirjinsa yayi da karfi Wayyo zuciya bazakayi magana ba kafito kanuna mata son nata da yake dankare atare dakai baka da amfani inde bazaka yi magana ba kafito zuciya Fatina shiyasa nace miki sonki abaki bazai faduba.
Zatafita mamakinta kawai sai taji fashiwan kukan Nabil tana juyowa taga kuka yake wuiwui yana dukan kansa da kirjin sa rasa ma yazata yi tayi dan bazata iya fita ta barshi acikin wannan haliba dan tayi mugun tausayin sa gashi idan ta tuna gargadin Dr da Baban Nabil sai taji idan ta amince dashi yanzu ba ta kyuta ba amma sai wani zukiya yace idan yamutu wa akayiwa asara dama ba anacewa tsakanin macce da miji sai ALLAH ba kawai saita fara takawa ahankali har kinda yake shiko kukan yake cigaba da rusawa
Karasawa tayi ta zauna ta daura Akkam aciyar ta sannan ta dago habar Nabil idon sa yayi ja da fuskan sa
tace "ka dena dukan kirjin ka haka mekake sone.
"kenake so much.
"To aigani gaban ga"
Kawai sai ya jawota zan hade bakinsu tayi saurin girgiza kanta
Tace "tokaga abinda yake tabarar min da jikina kawai kake sha awa kenan
yace "komai naki inaso nide nasan inason komai naki."
Ganin bazai yuwuba saida lallami yasa tayi da baran gwara ta lallaba shin
"to kaga yanzu bai kamata muyi wani abu adakin Mama ba kabari da safen asan yanda za ayi."

Dasauri yace "to mufita agidan.

"a a Abu Fuj baka tsoron yanda mutanen gidan zasu fassara ni yanzu ma tun dazu nakasa fita a part din Mama amma haka ma ban tsira ba har na ake biyoni da bakaken magan ganu sai ma gobe idan yaransu da suke aure sunzo zanji sauran."

"kigayanin suwaye suka gayamiki magana?
Wllh bazan bar duk me kunta ta mikiba. "
Tace"a a kar kaga lefisu ni cime babban lefi ai abinma yazomin cikin sauki banzata zaizo da haka ba."

"to yanzu yakike sonnayi."

"Kajen dasafen kadawo."

Kamar wani yaro haka ta dinga lallamin sa dakyar ta tasamu ya yarda zai tafi amma saida yadan rage zafi

Yana rugume da Akkam suka fito falo yace "wllh duk harda lefin Dr wanan yaron cemin yayi wai dansa ne shiyasa nake son ki gayamin gaskiya ya akayi kika gamu da su dashi shegen BG din."
" duk gobe zakaji.
A parlour ma daker suka rabu dazuman shikam anan sai kwana dan yajima da sallama escort dinsa ba inda zaijen sai anyita ta kare
Ita ko Fandau tana samu yana fita tarufo kofan tana cewa zaka gane kurinka tunda nasanu *DAMATA Bazan bari DAMAR* ta kufce min ba saina rama duk abin da kayimin amma har ta kwanta kalmo minsa na soyyyya daya furta mata ne yake mata yawo akunne gakuma kamshin turaren sa da tajima tana mafarkin sa ajikinta wani k'aran dadi tayi da tatuna wataran ko tace nanda dan kankani lokaci zata amarce juyi tadingayi tana murmushi

shima anasa

ban garin hakane kwana yayi yana juyin dan ALLAH ALLAH yake gari yawaye abashi matar sa banda suranta ba abinda yake bijiro masa
Sai asuba yasa mu bacci bayan yadado daga sallah falon da ya kwanan yakoma yakwata akan kujera saiko yasamu bacin ya kwashishi cikin mafarkin me dadi

Washe gari Fandau bayan anyi sallan asuba ta durkusa ta gaida Mama tace "Mama inason naje gidan Bagana Mama ta kalleta taganta da shijab har katsa kibari ita ma zata zo anjima kad'an zaki ganta idan kikaje sauran yan uwanki idan suka zo bazasu ji dadi ba.
"Mama idan na zauna ma awajen su ba fita zanyi ba ba komai zai kawosu basai sai yada magana.

Mama tace "to kema kinsani dole ki zauna ki karbi lefinki kafin komai ya wuce ai kinyi abinda ba atabayin ba azurir ku dole ayi maganan kuma dole ki karba kina ji jiya ma da nafita wajen girki su Ya Karu ba maganan da basu gayamin ba ashe su amin bai musu dadi ba wai nayi muku rokon Allah duk kunsamu masu kudi suke bakin ciki da Bagana ma balle ke wai zaki wari BilAL dan gidan Alhajji Maina Gange masu kudin garinan ga na hada jini da Nabil wanda zamu lashe dukan dukiyar sa nayiwa matar asirin ancire mata mahaifa Lalle nayi aiki,
kede kinsan ba rabuwa zakiyi da magana ba yanzu idan ki kaje gidan Bagana haka zaduce kinnuna ban banci kizauna sai andan kwan biyu.

Fandau tace " Mama idan nazauna agigannan to plan dinmu da baban YaShid bazai yuwuba ba YaShid yana da shigen naci akan abinda yake so kinga jiya ma wai saiya tafi dani dakyar nalallaba yafice yace agidan nan zai kwana idan ina gidan Bagana kinga bazai gane ina canba."

"shiru Mama tayi can tace"gaskiya bai kamata kije gidan BAgana ba idan dole sai kinfitan gwara kije gidan Dr Mutarin yafi sauki idan Tazo taje ta sameki ajan da sauran yan uwanki yafi kiware kidan Bagana kije ko.

"to.
Fandau tace dande baza ta iya musu da Mama bane amma ita gani take gidan Dr Nabil zai iya zuwa kuma ta b'aran da zaiyi agidan yafi nanan dan ba shayin kowa yake ba shi yasa ma Dr din yace ta zauna anan.

"to Mama ki kira drive kigaya masa zan fita ta kofan baya.

"a a wai yanzu da asuban nan zaki tafin.

"Mama idan gari yawaje ya tashi ya ganni ai zai san inda zanje."

Mama tace "to ta kira drive yace ta fito dan dama amakotan yake gidan Malam na saukan bak'i

"amma zaki bar Dauda ko? Dan ban gaji da ganin saba."
"Mama ni kingaji da gani na?
ta fadi haka cikin shagwaba

Mama "a a dan kin ce zaki tafine."

"wllh Mama nima ban gama abubuwan da zan gayamiki ba balle na gaji da ganinki dan de idan na zauna da matsala ne kawai.

"to ALLAH yatemaka Malam yace cikin satinnan za agama komai amma fa yace yaran zai raba muku keda Hadim kowa yadauki 2 - 2.
"What! Mama yaran za araba?
"Eh adalcin dazaiyi kenan a tsakanin ku nima nayarda da hakan dan Hadim abin tausayi ce bazata kara haifuwa ba kuma idan akadu ba itama tana da hakkin na shayarwa.
Fandau bataji dadin abin ba taso abata yaran ta tanunawa Hadim bata isa ba amma bata da iko akan abinda Malam ya yanke
Cikin muryar tausayi tace "to Mama amma Fujjirat za abani na hada da Akkam ita tarike su Maaf ko?

"Eh nima zanso haka itace macce ita yaka mata abaki dan nima haka kurun nake son yarinyar.
Fandau tace "yawwa Mama shikenan zan tafi."
"To kigaida Habiban au
Yawwa anjima zan bada wani abu akai miki zan rubuta miki yanda zakiyin amfani dashi.
Fandau tace "to ta meke
Mama tace "kishiga kigaida matan gidan ki musu sallama.

Ranta ab'ace tafita dan ita inba dan Mama ba da baza taje wani gaida su ba dama bata zuwa gaida su bare yanzu da tayi abin fad'a

part din Bagaji ta fara shiga amma sai da taci kunu takoma Fandau dinta nada da suke shayi tukun ta shiga sallaman ta maciki ciki tayi tasa meta akan salllaya tana jan carbi yaran kuma duk suna karatun Qur anin ta zauna a kujera Meram ce tafito a d'aki tace "Ya Fandau sannu da suwa.
Murmushi "Fandau tayi tace "iyeee Merama anzama yan mata."

"YaFandau kekuma kin zama yar gayu."

BaGaji ta sallame lazimin
Tace"Merama ta zama yan mata amma ina roka mata Allah kar tayi yanma tanci irin naki nashiga duniya a auri dan Duniya daga baya azo abayar ta bazawara naki ma kadai ya isa dama ance duk gidan babban malami ko babban dan siyasa sai ansamu abin fada yanzu gashi mukece ki ka janyo mana abin fad'an....

Fandau azuciyar tace wanan kam *HUKUNCIN ALLAH* ~ne inji Garkuwa muna jira~

afili kuma katse BaGaji tayi da cewa
"ina kwana dama Mama tace na shiko mu gaisa.

"yo ai dama ko baki fada ba nasan ke akaran kanki bazaki zo gaishimu ma da dakike cikin Summa da kwarkatar kima bakizo ba balle yanzu da kikaga ma kwancin manya ai ita ma uwar taki bakomai ne yasa ta turoki ba dan muga yanda kika komane,
koda tana turoki gaida mune to agaban mu akayi komai ke sakkeyace bazawara saide aci wanda aka tara ke har kin isa ki auri mijin Hadim baturiya maganan auren jikan Kange kuma fitar sunfi karfin ku saide kiyi zawarcin cikin almajiran kidan wada yaga zai iya ya dauka...
Itade Mekewa tayi tafice part din Bakaru shima hakan ne yafaru tanayin sallama
Bakaru tae"lalle yau wanake kani ya shigomin kamar Fandau lalle Duniya yafi gaba ba ruwa iya jima tunda yakoyawa Fandau shigowa inda mutane suke Duniya makaranta to zauna mana manyan zawarawa agidan Zannah.

Fandau tace "a a basai na zauna ba Mamata tace na zo na gaidaki ina kwana.
"ba shakka dole ki gaidani atsaye dan kinkai ai kin aurin Shiddams kina shirin auran jikan Kange kinga ai dole ki gaidani atsaye.
dasauri Fandau ta fita dan ita bata daukan raini tana iya biye mata
Sai part ita amarriya gidan wada yanzu idan mutum yagani zaice tariya mama shigowa gidan dan ita take bin bayan Mama kuma ita tanada yara manya mama bata samu haifuwa dawuriba
Ita ma sallama tayi mata tace BaAlta inakwana.
cikin fara ata amsa dan kita bata da halin wadancan kawai tana tsoron sune ita ma Fandau har tadauki jikanta wada aka kawo mata yaye dan gidan Amsatu wanda take sa ar Fandau ce kuma dama suna dan shiri kadan da Fandau tace "Bani yasunan sa Sultan sunan Baban kune tamasa wasa tace Bani zandan fita idan Amsatu tazo ta sameni gidan Dr na polo.
Ba Alta tace "to zangaya mata Munyi waya kuwa tace zata zo zan gaya mata gwara kije can nima banso zamanki agidan nan ba kwara candin yafiye miki kafi amaida auren ku dan wllh abun yana damuna saida nasamu Malam jiyana ce amma a addini yasan kinada idda yabari ake zancen auren wani shine yake cimin dama shirine da aurenku nayi murna ALLAH yatsareki da sharrin wannan matar tasa.
"Ameen Fandau tace tareda cewa "Baani ina Nana?
"ai am mata aure itada inana da Ramatu har sun kusa shikara.
Abin yabawa Fandau mamaki aurin gidan suna yara yanzu yaran da kannen Bagana ne har anmusu aure

Afili tace" shiyasa naga kowa su bangan su ba.

"eh ai duk zasuzo yau inaga dan Nana muyi waya tace zatazo itama suma sauran nasan iyayen su sungaya musu.
"to Bani natafi.
"ina Dauda?
"yana wajen Mama
Tana fitowan takofan baya tafita dan yansa idon Almajiran tasamu driver yana jiranta ta shiga baya yaja tace "dan gwaza ashe har yanzu kaine kake jan matan gida.
yace "Eh Wllh ansha canzani gidan wasu Hakiman amma sai nasa Malam yane mamin alfarma inajin dadin aiki da gidan Malam.

Bayan yasauketa da zauri shige gidan jin kukan Ummulkkairi tanayin sallama dukka suka juyo har Dr suna folon "Alhamdulilah amma ya haka da safen nan ko kema kasa baccin kikayi kamar na ummuna kingan ta tun dare muke fama wai sai an kaita wajen Aunty Kirki.
Fandau tana dariya tace
"Ayya kharina iyeee yar gidan wacece taware hannunta Khairi tazo ta gudu ta dakata sama
Tace"yar gidan Aunty kirki ce tama haka suke ko amakaranta tazo shiyasa takewa Fujj ma

"ina Nol Nol dinna.
Haris yace "na bacci
Fandau ta durkusa ta gaida Dr da Anuty Habiba
Habiba tace ina Akkam din kuma.
"Yana wajen Mama.

Habiba tace "to ya akayi kika fito da wanan kuban safen haka.
Fandau ta gaya mata abinda yafaru

Habiba tace "Ayya kinshiga hannun maza.

Dr dariya yayi yace "dama ai nace ta kiyaye Shiddams idan ransa ya baci hauka yakeyi shiya sa a makaran ta har malamai suna tsoron sa dan idan ransa ya baci baya musu ta dadi yanzu ya hannun?.

"Da sauki ai tace
Fandau tayiwa su Nol da kharat wanka Haris da kansa yakeyi bayan sunyi break fast Fandau ta kunna wayan ta hau YouTube tasauke film suna kallo taka message yayi yawa a whassapp dinta ta cewa su Kharat kuje kuduba kar su Momy subarku da gudu yaran suka fita ita kuma ta bude whassapp taga ashe cakwakiya ake sosai acikin group nasu Habiba ta gabatar da ita a matar shiddams ta biyu kowa yana fadan albar kacin bakin sa sosai suke fada aiko sai ga Hadim dinma ta fara ruwan asher tana cewa ita tafi kalfin ta zauna da kishiya dama ita tasa ya aureta dan ta haifa musu yara amma yanzu yasaketa da ganan tabada labarin Fandau ashe har da wanan video da Nabil yayiwa Fandau a haduwa suna farkon ta tura musu
Wasu dayawa gan gancin Hadim suka gani wasu tausayin Fandau dan dayawa sun bita private suna gaskanta abin wasu kuma suna bayan Hadim ana ta zagin Habiba Farida amarriyan Amjad wanda basa shiri da Hadim saboda kishiyar ta Zahra kawar tace itace tayi ta tura rawa tana cewa woohohho yau ranan farin ciki da murna
Itama Habiba tace "dakenan take Fandau yazu ko Fantastic take nan danan ta fara tura pic din Fandau nan danan aka fara wow beautiful lady Amina matar BilAL dayake tasan komai ita ma tace "woow kaji yar kanurin asali ai amma kawas kin iya zabe fa nima kine mowa my sweet dina iran wanan ta haifa mana yariya kamar Fujji Biebiee ai nan danan akafara turo pic din Fujjirat ana cewa Wllh suna kama sosai
Hadim tace "nace muku kudena zancen ta wlllh jiyannan yasaketa dan kunsan nafi karfin zama da kishiya ita ma muna fukar Habiban da taturo maganar nan kuma har agidan ta zauna ita ta mayar ta mutum ita taci amanata zan sameta har gidanta ashi ita tana bakin cikin duk mijina yafi nakowa kudi duk abin da nake mata bata gani tacimin amana ni Hadim sai gani da ido wllh.

Ita ma Habiba zata maida mata da ganan de matar Usman da taga abin zai b'aci ta *Removed* din kowa Tarufe *group* din
Daga nan Fandau tayi dariya afili daba a rufeba da sunji murtani dagan nan takoma bude yan private
_slm sunana Farida matar Amjad Abokin Shiddams na san kinga yanda muka yi a grp amma naso ace kin fito kin nuna musu ba kya tsoron su kishiyata kawar Hadim ce kinga muna zaman lafiya amma Hadim gaba take dani har tafi kishiyar tawa kishina kullum burina naga yanda zatayi idan akace an mata shishiya cikin ikon Allah wai yau sai ga Hadim da kishiya kishiyar mana BANGIRMA wacce ta game gida da yara ashi duk soyyyyar Hadim da Shiddams zai iyayi mata shishiya wai yayi aure dukda ita ta hada kuma tace ta raba wllh nayi murna ALLAH yasa maganan mmn Nol kaskiya ne da tace anmaida auren kuna da gaske ke kanwar Dr MD?_
Murmushi tayi ta maida mata Ripley
_Ameen Waalaikumus salam Ayya duk naji labarin ku abakin Aunty Habiba bacce bansani ba hatta pic dinku kai kunsha zuwa gidan ma kina ganin ku amma bana fitowa Eh Dr yayana ne kuma auren muda shiddams banajin akwai ranan rabuwa sunana Fatima Muhammad Zannah Gargar nima inason mukasan cetare FARIDA Amjad_

_Masha ALLAH dafatan zansamu karbuwa awajenki muyi zumunci maganan Grp kuma awai wani Grp shima yawanci mumatan abokanne aciki kinga yanzu haka zancen yayadu duk Grp na mu zancen ake kuma kinada masoya duk da itama Hadim tanada nata masoyan zan sa kiciki amma inason idan kinshiga karki kiyi sanya kinuna kema kinkaisu kibude idon ki sosai kishiga awayen idan kika nuna sanya suka renaki wllh abin bazai miki dadi ba ga amarriya usman ma tanason kuyin zumunci dan itama kishiyar ta kawar Hadim ce kewani bayanin masai kinzo London._
Fandau tama yar mata
_Eh sis dama Aunty Habiba ta gayanin halin kowa nagode_

Haka Tayita budewa sakonni wasu su zageta wasun su kuma irin FARIDA ne

Ummi dakira Nabil yace yana Gargar

tace ,"to kazo gidan gashinan antaru za ayi meeting kai kawai ake jira.yace "to
Amma saida yashiga bangaren Mama yagaisheta yanata raba ido yaga inda Fandau zata fito sai yaga shiru yadauki Akkam yana masa wasa yace "Mama amma Akkam yafi su Maaf kama dani ko?
Dariya Mama tayi tace "gasunan de duk kodaddun rana.
Dariya yayi yace
"Mama ina take ne?
Mama tace wah?
Yace "Mama mata mana.

"Wacece kuma mata?
"cikin shagwaba yace "matata mana uwar yarana.

Dariya mama tayi tace "yanzu agabana kake kiran matarka mata baka kunyata.
"Haba Mama wllh ni nafijin kunyar Ummi ma akanki dan me d'a zaiji kunyar uwar sa bayan itace maganin kukansa Mama kisa baki abani matata a yau wllh agidan nan na kwanan falon bak'i kiga jikina duk sauro sun cijeni ga rashin matata duk banyi bacci ma.

"Ayya Nabil dina zan maka iya kokari naka ka koma da matar ka amma kaima ya haka daka cewa kazo kanemin biko sai kazo ka hauta da duka.

"Mama rainane ya baci amma nabata hakuri tana ina?
Mama tace
"Ayya inaga tashiga gaida matan gidan.
Shiruru yana zaune har Ummi ta sake kira tukun yace Mama akirata mugaisa zanje nadado?

Mama tace "jeka kadawo din kaga inaga kiran Ummi kane ko?
kafin ya bata amsa akasake kira mekewa yayi yace
"Mama inazuwa amma da Akkam zanta fi FUJJI ta nason sa.
*Gidan su Nabil*
Iyayen Hadim har kishirar uwar ta da Abba Musa yayan su Ummi da Baba Inusa kanin Baban Nabil da Inna zainabu da sauran yan uwa najiki bayan Nabil yashigo aka gama tsara komai ayanzu kam mamar Hadim tayarda kuma ta bada hakuri zata janje karan da tayi dan ita ma tana ganin Fandau tayarda lallle ita ta haifi Fujjirat babanta ko rasa bakin magana yayi dan Malam yana da kiba sosai kuma dan shima yayi karatu awajen Malam saide yagayawa wani Malam ciki bacin rai

Please Login or Register in order to submit comment