Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yafe maka ba." A hargitse Jafar ya ɗago, Mami na jin haka sai kawai ta rushe da kuka ta fice daga falon.

"Dama Daddy cewa na yi zan koma Lagos, saboda gidan nan ba ni da nutsuwa da shi." Jafar ya yi magana yana satar kallon mahaifinsa. Daddy ya jinjina kai ya ce.

"Hakan ma ya yi idan kana ganin ya fi a wurinka, amma ka sani a waɗannan kwanakin naka duk inda za ka saka ƙafa sai dai ka tafi da Uwani. Ba zai yiwu kwana biyu da yin aure ka tsallake yarinya ka bar ta a nan ba, sannan kuma wannan matsalar da ke faruwa zan nemar muku magani idan daga kai ne ko kuma daga ita ne." Wani malolon ɓacin rai ya tokare Jafar, ya haɗiyi yawu mai ɗaci ya furta.
"Shi kenan Daddy." Daga haka Daddy ya sake yi musu nasiha sannan ya sallame su.

Jafar na fita ya kira Amir a waya bayan sun gaisa yake ce masa ga shi nan zuwa, a lokacin da ya je Amir na zaune da Laptop a gabansa yana aikin tracking. Kamar mai ciwon haƙori haka Jafar ya yi sallama ciki-ciki ya zauna a bakin katifa.

"Ango ka sha mai, kai ka ga yadda saman hancinka yake ƙyalli. Shegen kaya kana so kana kai wa kasuwa." Amir ya yi maganar yana dariyar shaƙiyanci.
"Ba na son iskanci ni ba wannan ne ya kawo ni ba." Jafar ya furta rai a ɓace. Da ido Amir ya bi shi da kallo Jafar ya ci gaba da cewa.
"Zuwa na yi ka ba ni aron ɗaki na kamar sati biyu."

"Ni kuma na je ina? Ka san dai ai hutu muka dawo ko?" Jafar ya dage kai da hannuwa biyu cikin damuwa, Amir ya sanarwa yadda suka yi da Daddy sannan ya ɗora da cewa.

"Allah Ya sani ba zan iya tafiya Lagos da Uwani ba, haba kawai sai na fara nuna ta na ce ga matata. Kuma ka san duk yadda zan ɓoye wa Safna na yi aure matuƙar na je da Uwani sai asirina ya tonu." Jafar ya sauke ajiyar zuciya ransa na ɗaci ya ci gaba da magana.

"Ga Safna na shirin ɓallo mini ruwa ita ma." Nan ya kwashe hirar da suka yi da Safna, ya ɗora da cewa.
"Abokina don Allah ka ba ni mafita komai ya cushe mini, al'amura duka sun kwaɓe mini."

Shiru Amir ya yi yana nazari, da sauri ya ɗago ya ce. "Na samu mafita. Yanzu dai da farko ka ɗauki Uwani ka kama muku hotel, ba ka ce makaranta za a saka ta ba. Idan kuka cinye wannan hutun ka ga ai sai dai ka dinga zuwa ka na dawowa, ita kuma Safna idan har ba jagwal kake son haɗa wa kanka ba to ka yi mata dabara har zuwa nan da bayan kwana biyu, idan ya so kafin nan matsalar Uwani ta ragu sai ka ji da waccan matsalar." Jim Jafar ya yi jiki a sanyaye ya ce. "Sai kuma kawai na koma rayuwar hotel kamar wani ɗan iska."

"Wa ya ce maka 'yan iska ne kaɗai ke rayuwar hotel? Masaukin baƙi ne fa. Kuma idan ma iskancin za ka yi ai matarka ka ɗauka ko?" Amir ya yi maganar cikin zolaya. Sun ɗan taɓa hira sannan Jafar ya yi masa sallama ya wuce gida.

Daren wannan ranar a ɓangaren Mami suka kwana, Daddy ya sa aka buɗe musu ɗakin Dada suka shiga ciki. Fes yake babu ƙura a ciki, wannan karon Jafar bai kori Uwani daga kan gadon ba saboda a matuƙar tsorace yake. Kowannensu ya juya bayansa ya kwanta, bini-bini Uwani idan za ta gyara kwanciya sai ta ƙara tamke kai da ɗan kwali.

Kimanin ƙarfe tara na safe Uwani da Jafar suka shirya kowannensa ɗauke da jaka, Uwani kayanta ta ɗiba ta saka a akwati kamar yadda ya gaya mata. Mami da ta je yi wa Jafar sallama sai jaddada masa take ya kula da kansa tamkar wani mace, shi maganar tata har kunya ma take ba shi. Daddy ne ya ɗauke su a mota ya nufi tashar sabon gari da su, Jafar yana gani bai faɗa masa cewar ya fasa zuwa Lagos ba don nauyi yake ji ya ce masa hotel zai kama musu. Sai da ya tabbatar da motar Daddy ta yi nisa da tasha ya dubi Uwani ya ce.

"Sai ki ɗauko jakarki."
Ba musu Uwani ta fara jan jaka har suka samu mai adaidaita sahu, Jafar ya ce masa ya kai su Light Hotel da ke Zoo road.

"Ina kuma za mu?" Uwani ta watsa masa tambaya.

"Sayar da ke zan yi. Wallahi idan muka je kika yi mini ƙauyanci sai jikinki ya faɗa miki." Uwani ta ja bakinta ta yi gum tana kalle-kallen titi. Har cikin harabar hotel ɗin ya shigar da su, nan Uwani ta saki baki tana kalle-kalle don wani lokacin sai Jafar ya yi gaba zai waiga ya ƙwalla mata kira, reception ya tsaya ya cike duk abin da ya dace. Aka ba shi key ya tasa Uwani a gaba da ta saki ba ki tana kallon wurin.

"Don Allah ina ne nan ka kawo ni kamar Dubai da nake gani a TV?" Jin tambayar da Uwani ta yi masa ga kuma mutane na kallonsu ya sa ya ce. "Eh Dubai ce." Cikin lifter suka shiga Uwani ta ji wani irin zuuuuummmm A firgice ta ƙanƙame Jafar ta saki ihu, ƙirjinta sai bugawa yake. Sai da suka tsaya sannan Uwani ta ɗan ɗago da kanta amma har lokacin jikinta bai daina karkarwa ba.

"Malama sake ni."
Jafar ya faɗa yana yakice Uwani. Kamar sabuwar munafuka haka Uwani ta dinga raba idanu kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci a tsorace take. Buɗe ɗakin ya yi suka shiga, a gajiye ya zube a kujera Uwani ta tashi ta fara leƙa ɗakin.

"Don Allah ina muka zo Ya Jafar?"
"Light Hotel." Jafar ya amsa mata a taƙaice.
A zabure Uwani ta miƙe tsaye jiki na rawa ta ce, "Wallahi ba zan kwana Otal ba salon haka kawai a dinga ce mini 'yar iska." Uwani ta dubi Jafar a yamutse ta ce.
"Ya Jafar ina maka kallon mutumci ashe kai ma kana cikin sahun sababbin 'yan iska ashe ban sani ba..." Jafar ya bige wa Uwani baki, cikin jin zafi ta sa hannu ta dafe bakin ta furta.

"Wallahi ban yafe ba..." Ba ta ƙarasa magana ya sake bige bakinta. Uwani ta zauna a gefen gado tana watsa masa harara. Wayarsa ya zaro ya fara dannawa, Uwani ta ci gaba da zama cikin gundura don ita tsarin wurin sam bai yi mata ba.

"Ni fa yunwa nake ji." Uwani ta yi maganar, Jafar ya yi kamar bai ji ba. Sai da ta maimaita sau uku amma ko ƙurar ta bai kalla ba, ta tashi ta leƙa ta window a nan ta hango mutane na zirga-zirga a farfajiyar wurin.

"Bawan Allah ka taimaka mini yunwa nake ji." Uwani ta ƙwalla wa wani mutum kira da ta gan shi ya wuce da take away a hannu.

"Mai farar rigar nan don Allah ka taimaka mini..."
Cikin zafin nama Jafar ya ƙarasa ya fisgo Uwani. Da ƙarfi ya wurga ta kan gado yana huci ya ce. "Ke wacce irin mahaukaciya ce ne? Wallahi kika nemi ki tara mini jama'a sai na zane miki jikinki."

"Ba na gaya maka yunwa nake ji ba? Wallahi ka kiyayi hukuncin Ubangiji atoh, a kan mage ma wata ta shiga wutar jahannama, ka san ni ma ka kashe ni da yunwa duk gatanka babu mai hanaka shiga Hawiya." Jafar ya yi yunƙurin kai mata duka da sauri Uwani ta zille tana dariya, tana gani ya ɗauki waya ya kira ita dai ta ji yana turanci amma ba ta san abin da yake faɗa ba. Bayan awa ɗaya sai ji ta yi an ƙwanƙwaso musu ƙofa, Jafar ya karɓi abincin ya dire. Plate ɗinsa ya ɗauka bai tanka wa matai ba, ganin haka ya sa ita ma ta sauka ta ɗauka ta fara cin abinci. Bayan ta gama babu jimawa aka kira sallar Azahar, tana idarwa ta ɓingire a akan dadduma bacci ya yi gaba da ita.

Tun da Jafar ya fita sallar Azahar bai dawo da wuri ba, kusan sallar La'asar Uwani ta farka shi ma sanyin AC ne ya dame ta. Banɗaki ta shiga yin alwala tana ta jinjina lamarin ƙayatuwar banɗakin da kuma nasu ɗakinsu, bayan ta idar da sallah atamfar jikinta ta sauya ta ɗauko wasu riga da wando baƙaƙe ta saka. Sai wata farar hula da ta ɗora a kanta, ta saka hijabinta ƙarami. Jin zaman ta yi ya gundure ta don haka ta buɗe ƙofar a hankali tana leƙe-leƙe. Sai a lokacin da lura da fasalin ɗakunan duk suna kallon juna sai dai kowacce ƙofa a datse take. Tafiya ta fara yi tana kalle-kalle ba ta yi aune ba sai ji ta yi garam ƙofar ɗakin ta datse, Uwani ba ta wani damu ba ta ci gaba da tafiya har ta fita wurin wata baranda ta hangi step ɗin bene. Takawa ta fara yi a hankali har ta sauka sai ganinta ta yi ta sauka can farfajiyar wurin da ta hango mutane na kai-kawo. A kan ɗaya daga cikin kujerun harabar wurin ta zauna, a gefe ɗaya kuma swimming fool ne tsirarun mutane sun zauna suna saka ƙafarsu a cikin. Abin ba ƙaramin birge Uwani ya yi ba, abu ɗaya ne ya takurata ganin yadda wani Alhaji da ke gefenta ya zuba mata idanu da sun haɗa ido sai ya sakar mata murmushi, ko ya kashe mata ido ɗaya. Kiransa ta ji an yi a waya ya ɗauka yana barin harabar wurin. Babu jimawa ita ma ta tashi ta nufi hanyar ƙafar benen da ta sauko, wata hanya ta bi wacce take ganin kamar hanyar ɗakinsu ce. Amma sai ta ga ta gagara gane ainihin ɗakinsu, wata ƙofa ta gani a buɗe. Ta ga yanayin wurin ya yi mata kama da ɗakinsu da sauri ta tura ƙofar, turus ta yi tana kallon mutumin.
Mutumin ɗazu da ta ga an kira a waya ne, ya washe mata baki yana faɗin.

"Ranki shi daɗe ke kaɗai ce?" Uwani ta yi saurin kawar da kai gefe don jibgegen mutumin daga shi sai gajeren wando, ya ɗora towel a kafaɗarsa da alama wanka zai shiga.

"Eh ɗakina nake nema?" Kallon tsaf ya yi mata, nan take ya lura da Uwani farin shigar zuwa hotel ce. Ba ta yi aune ba ta ji ya janyo hannunta ciki ya datse ƙofar, ya fara shafa gemu ya ce. "Ranki shi daɗe ni fa dama tun ɗazu nake ɗago miki hannu ba ki fahimta ba ne." Uwani ta fisge hannunta da sauri ta ce.

"Malam ni ba 'yar iska ba ce ka buɗe mini ƙofa." Alhajin mai tumbin kuɗi ya ajiye towel ɗin a gefen gado, ya sake tunkarar Uwani ya furta. "Yarinya kada ki cuci kanki, yayyafin kuɗi zan yi miki ko awa guda ba za ki yi ba za ki kama gabanki." Ya ƙarasa maganar yana sake riƙo hannun Uwani.

Uwani ta fisge tana ja da baya, Alhaji mai tunbin kuɗi ya lashe baki yana faɗin. "Ni fa tun da na yi arba da ke yawuna ya tsinke, dama tunanina ɗaya na san yadda za a yi na yi arba da ke." Alhaji tumbin kuɗi na rufe baki Uwani ta sunkuyar da kai ƙasa tana ɗagowa sai ji ya yi ta fara ɓaɓɓaka dariya. Juya idanunta ta yi ta fara wani ƙobare hannuwa cikin wata irin murya ta fara magana.

"A yau za ka mutu tun da har ka taɓo mana goɗiya 'yar sarkin mayun aljanu." Uwani ta fara tunkarar Alhaji tumbin kuɗi tana wani murɗe kai gefe. A can gefen gado ta hango belt ɗinsa sai ta buga wani uban tsalle ta suri belt ɗin, daidai wurin ƙarfen ta shammaci Alhaji ta zuba masa a baya. A zabure Alhaji ya ƙandare yana faɗin. "Wash! Bayana."

Uwani ta dafa hannuwanta biyu a saman kanta, tana motsi da bakinta. Ganin haka ya sa Alhaji ya saki baki yana kallonta a tsorace.

"Uwar ƙwaƙwido ki ɗauke gashin kaina a yanzu, saboda mummunan hukunci za mu zartar a yanzu. Ki mayar mini da kaina babu gashi irin na wannan tsinannan da yake gabana." Uwani na gama faɗin haka ta fisge hular kanta, nan take Alhaji tumbin kuɗi ya zaro ido cikin tashin hankali ganin kan Uwani babu gashi. Uwani ta fara wani gurnani tana tunkararsa, ganin haka ya sa Alhaji ya taƙarƙare ya zuba uban ihu yana faɗin.
"Wayyo Allah maman Garzali ki taimaka mini za a hallaka ni."

Uwani ta maƙe wuya tana zaro harshe ta ce. "Za mu kwashe wannan tumbin naka mu zuba maka duwatsu a ciki, domin kana cin amanar Maman Garzali matarka. Zan kuma fafe ƙoƙon ƙeyarka na dura maka ruwan tekun maliya a ciki." Da sauri Alhaji tumbin kuɗi ya dafe ƙeyarsa ya zuba a guje, hawaye haɗe da majina suka wanke masa fuska.

"Matso ka hau saman silin ko ka hau kan fanka, idan ba haka ba zan sa a yi sama da kai ko a nutse ƙarƙashin ƙasa da kai." Jiki na karkarwa Alhaji ya hau saman gado ya fara tsalle zai hau saman silin, idan ya yi tsalle ɗaya sai ka ji ɗass! Uwani ta zuba masa duka da belt. A galabaice ya dubi Uwani ya ce, "Don Allah ku yi mini rai wallahi a yanzu jinina zai iya hawa, ko nawa kuke so zan ba ku amma ku ƙyale ni." Uwani ta yi wani farrr da idanu, sannan ta ce. "Mu ba matsiyata ba ne, ba ma buƙatar kuɗinka Dama mu yawo muke Otel-otel muna hukunta masu hali irin naku masu lalata 'ya'yan mutane."

"Wallahi har abada na daina ba zan sake ba don Allah ku yi mini rai."

Uwani ta wurƙila ƙafa tana kanne ido ɗaya ta ce, "Za mu ƙyale ka amma da sharaɗin sai ka cinye sabulun wankan da ke banɗakinka, ko kuma mu farke cikinka mu tura maka 'ya'yan aljanu bakwai..." Tun Uwani ba ta gama magana ba Alhaji ya faɗa banɗaki da gudu ya ɗauko ragowar sabulun wankansa ya tura baki, yana ci yana kuka haka ya cinye sabulun bakinsa sai kumfa yake.

Uwani ta suri hularta a fakaici ta riƙe sannan ta sake ɓaɓɓaka wata irin dariya ta ce. "A zo a buɗewa Goɗiyar mayun aljanu ƙofa." Ba musu Alhaji tumbin kuɗi ya buɗe mata ƙofar, jikinsa banda karkarwa da gumi babu abin da yake yi.

Sai da Uwani ta fita ta sauke ajiyar zuciya don ita kanta ilahirin jikinta karkarwa yake, duk abin da take yi ƙarfin hali ne don ta lura da ta nuna masa tsoronta a fili ba abin da zai hana bai ci galaba a kanta ba.
Daga ɗaki mai kallon na Alhaji tumbin kuɗi ta ji wani mutum yana yi mata ɗan kira, a shekaru shi ma bai fi sa'an Alhajin ba. Yi ta yi kamar ba ta gan shi ba gabanta sai faɗuwa yake. Ta bayanta ta ji ya fara biyo ta yana faɗin.

"Haba 'yan mata kada ki yi wasa da damarki, abin da abokina ya ba ki ni zan ninka miki shi." A tunanin mutumin tun da ya ga Uwani ta fito daga ɗakin abokinsa ita ma 'yar hannu ce. Ganin haka ya sa Uwani ta fara sauri mutumin na biye da ita har dai ta ga da gaske yake ta saka gudu, tana yunƙurin shan kwana sai ta ji ta yi karo mutum. Cikin tashin hankali ta furta.

"Don Allah ku taimaka mini wallahi ɗan iska ne ya biyo ni." Mutumin da kawo kansa kenan ya furta.
"Haba 'yan mata ni fa ko awa guda ba za ki yi mini ba, don Allah ki bari..." Maganarsa ta maƙale sakamakon arba da ya yi da Uwani riƙe da Jafar.

"Kai yaro wannan fa ba kalar yara ba ce. Don 'yan shiloli kamar su sun wuce ajinku." Cikin ɓacin rai Jafar ya furta.
"Amma dai Allah wadaran hali irin na lalatattun tsofaffi kamar ku."
Jin muryar Jafar ya sa Uwani ta ɗago da sauri don ko kaɗan ba ta taɓa tsammanin shi ba ne, suna haɗa ido ta riƙe shi ƙam jikinta na rawa cikin kuka ta furta. "Ya Jafar." Sai kawai kuka ya sake cin ƙarfinta.

Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki turo ta Acc Aisha Adam 3090957579 First bank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624
Free pages ɗinmu ya kusa ƙarewa🫠


#Ummou Aslam Bint Adam🌚
[30/06, 19:35] Ameerah Adam🌚: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.

SHAFI NA SHA HUƊU

*BOJUWA HERBAL'S & SCENTS*
*Suna kawo Saiwowin da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.*
*Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah*
*Saiwowin tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru*
*Saiwowin matsi gangariya*
*Original gadalin mata*
*Ƴaƴan gadali na asali*
*Original gumba*
*Tsumin Saiwowi*
*Tsumin kwakwa da Dabino*
*Igiyar alkairi*
*Zumar goran tula*
*Hakkin daka na musamman na asali*
*Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*.
*Akwai bridal package*
*Mai jego package*
*Ƴar gata package*.
*Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.*
*A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne*
*Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi*
*08032773332*
*Iyah Basiru na gaisuwa*😅

A sanyaye Lado ya ɗebo agogo da links ɗin Salim ya dawo cikin gidan, sai dai yana shiga ga wutar harabar wajen ta ɗauke. Ga kuma ƙarar duka da ake yi wa Shukra tana ihu, zuwa can kuma sai ya ji an yi wurgi da bokiti an zuba cikin gida a guje. Gudun kada abin da ya same su, shi ma ya zo kansa ya sa Lado ya shige ɗakinsa ya danno ƙofa ya rufe don shi kansa bai manta abin da aka yi masa a tsakar dare ba.

Da gudu Uwani ta bi bayan Shukra tana gurnani tana zabga mata igiyar a baya har Shukra ta fara kama ƙafar bene Uwani ba ta daina dukanta ba, tana hawa sai ga Shukra na rarrafe tana kuka saboda tashin hankali. Sai da ta ga Shukra ta shige sannan Uwani ta yi saurin ɗebe bokitan ta mayar da su wurin da suke, ta je ta ɗaga table ɗin ta mayar da ruwan jarkokin kai sannan ta koma ta kunna ƙwan fitilar harabar wurin ta wuce sashenta.

A lokacin da ta shiga sashenta shiru babu motsin Jafar, ta zube a kan kujera kanta na matsanancin ciwo kamar zai tsage gida biyu. Uwar ɗakinta ta wuce don ta sauya kayan jikinta saboda rawar ɗarin da take yi, ɗrower kayanta ta buɗe tana shirin miƙa hannu ta yi ido biyu da Jafar tsugunne a cikin.

Uwani ta basar kaman ba ta san abin da ya faru ba ta ce, "Kai kuma Ya Jafar mene ne haka?" Jafar ya fara wuri-wuri sannan ya ce.

"Wai Uwani ke ce kika zama biyu ko ya aka yi?" Jafar ya wurga mata tambaya.

"Wai me ka mayar da ni ne ya Jafar? Ni fa yanzu na gama yi wa saurayin Shukra wankin mota bayan na gama yi wa Mami wanki..." Cikin sauri ya katse ta.
"Wankin me? Ke kika wanke wa Salim mota? To su waye na gani da bokiti a kansu suna ihu?" Uwani ta wara hannu ta ce. "Ni kam ban sani ba, ƙila dai mutanen gidan ne suke son buɗe maka ido." Jafar ya yi fakare yana nazari, abu ɗaya ne ya fi tsaye masa a rai wai Uwani ce ta wanke wa Salim mota. A fili ta ji ya furta, "Dole sai na ɗauki mataki a kanta." Uwani ta yi saurin tambayarsa. "Wace ce?" Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya furta. "Babu komai."

Saboda tsabar gajiya Uwani na sauya kaya ta ɗauro alwalar Isha'i ta gabatar da sallah, a nan kan dadduma bacci ya yi awon gaba da ita.
A yadda ya ga tana sauke numfashi sama-sama ba ƙaramin tausayi ta ba shi ba, ya ƙarasa ya cire mata hijabin ya ji jikinta ya ɗauki zafi zau! Cikin jakarsa ya duba ya ɗauko Paracetamol, ya jima yana tashinta sannan ta tashi ya ba ta magani. Duk yadda ya yi da ta tashi ta ci abinci ƙi ya yi, ya rabu da ita ya haye gado ya kwanta.

Shukra da rarrafe ta ƙarasa falon Mami, babu ɗankwali ballantana mayafi ko takalmi, a razane Mami ta fara tambayar Shukra.

"Ke Shukra lafiyarki kuwa?"

"Mami ki ɓoye ni bokiti ne, wallahi bokiti ne ya danne mu ni da Salim." Da mamaki Mami ta ce, "Kamar ya bokiti ne Shukra? Shi bokiti mutum ne da zai iya motsi har ya danne ku. Wai ma ina ɗankwalinki?" Shukra fuska da ta gama jagulewa da makeup da hawaye ta zayyanewa Mami duk abin da ya faru, Cikin damuwa Mami ta ce.
"Ni fa wallahi ina zargin yarinyar nan tana da Aljanu, mu dai tun da muka tare babu wani abin tashin hankali da muka taɓa gani. Amma tun ranar da yarinyar nan ta zo gidan nan masifar yau daban ta gobe daban, yanzu bala'in har ya kai kina hira ke da Salim ana razana ku? Gaskiya dole a san abin yi." Daga haka Mami ta shiga lallashin Shukra, da ƙyar a daren ranar Shukra ta yarda ta kwana a ɗakinsu. Da yake Daddy ba ya gari ya sa asubar fari Shukra ta koma ɗakin Mami bayan ta yi sallar asuba ta koma ta kwanta.

Washgari

Tun bayan sallar asuba Uwani da Jafar har sun koma bacci, suka ji bugun ƙofa. Jafar ne ya je ya buɗe da mamakin mai buga musu ƙofa da farar safiya. Karo ya kusa yi da Mami a ɗan duburburce ya ce. "Mami ke ce tun yanzu?"

Mami ta ƙare masa kallo ta ce, "Eh ni ce, ina Uwani take?" Jafar ya ɗan sosa kai ya ce. "Tana ciki bacci take yi."

"Ciki ina? Uwar ɗaki?" Jafar ya gyaɗa kai. Cikin sauri Mami ta ce, "To kai kuma a ina ka kwanta?"

A ɗan kunyace Jafar ya ce, "Ni ma a ciki na kwanta..."

"Laha'ilaha'illallahu Jafar tun ba a je ko ina ba?" Salatin Mami ya katse shi. A ɗan duburburce ya ce. "Am ai ita a ƙasa take kwana ni nake kwana a kan gado." A fili Mami ta sauke ajiyar zuciya tana murmushi ta wuce cikin ɗakin. Yadda Jafar ya faɗa mata haka abin yake, bacci Uwani take sosai a ƙasa saboda gajiya. Mami ta ɗauki ruwan jarkar da ke kan mudubinta ta sheƙa mata, a zabure ta tashi tana waige Mami ta taɓe baki ta ce. "Ki zo ki wuce kitchen za ki taya Inna haɗa breakfast, kin saki baki kina bacci ai duk gidan nan babu bawanki da zai dafa miki ki dinga ci." Jafar kamar ya yi magana sai dai kuma ya yi shiru, tun da yake bai taɓa samun saɓanin da mahaifiyarsa da har za ta mare shi ba, don haka ya kawar da kai har Uwani da Mami suka fice daga ɗakin.

Suna tafe Mami ban da masifa babu abin da take mata, kai tsaye kitchen suka wuce. A lokacin Inna har ta fara haɗa kayan breakfast, suna shiga Mami ta dubi Inna ta furta. "Inna daga yau Uwani za ta dinga zuwa tana ta ya ki haɗa kayan breakfast." Inna ta washe baki cikin jin daɗi ta ce. "Allah Ya taimaki Hajiya, ina matuƙar godiya. " Uwani da har lokacin bacci bai gama sakinta ba, ta fara murza ido. Ba ta yi aune ba sai jin ranƙwashin Mami ta yi a kanta ta furta. "Kin ga dai ta hanyar da na biyo da

Please Login or Register in order to submit comment