Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ilahirin jikin Jafar ban da karkarwa babu abin da yake yi, iya ƙarfinsa ya taƙarƙare yana gudu tun don tun da ya zo duniya bai taɓa cin karo da hallitar da ta ba shi tsoro lokaci ɗaya kamarta ba. Tashin hankalinsa ya ninku sakamakon jin ƙofar da za ta sada shi da gareji ta datse ƙam ta ƙi buɗuwa, ganin haka ya sa Jafar ya maƙale wani dogon ƙarfen da ke jikin rumfar harabar wurin. Cangala ƙafa Uwani ta fara yi ta fara wata shaƙuwa da ƙarfi tana zaro ido waje ta tunkare shi. Hannu ta sa ta fisgo ƙafarsa ɗaya sannan ta ce.

"Sai mun fige wannan ƙafar taka kamar yadda ake figar kaji, sannan mu ɗauke ka mu tafi da kai dajin tsumbur. Tun da har muka buɗe maka idanu kana iya ganin mu sai mun tafi da kai." Jafar a ruɗe ya furta.

"Wayyo Mami, wai Daddy ba kwa ji na ne? Ku taimaka mini kada su fige ni." Uwani ta fara wani juya idanu tana buɗe baki kamar mai shirin kai cizo, sai da ta sake zaro ido waje sannan ta kai baki ta gasa wa Jafar cizo a ƙafa. Ta sa hannunta na hagu ta yaƙuso ƙwaurinsa, ta ci gaba ta fisgar ƙafar tana faɗin.

"Ɗan tsita yau balangu za ka ci, sai mun babbake maka wannan cinyar guda ɗaya mai kama da ta sauro ka cinye."

Cikin azaba ya fisge a nan Allah Ya ba shi nasara ya buɗe ƙofar, ganin ɗakin Lado mai gadi ya fi kusa da shi ya sa ya nufi wurin a guje yana tafe yana waige. Abin da ya ƙara ɗaga masa hankali, bai wuce yadda idan ya waiga yake ganin Uwani na sake tunkaro shi tana zaro harshe waje.

A wannan karon Uwani ta sauya salon tafiya a hankali take tafiya tana zaro harshe, ta sake karkatar da kai ƙasa kamar yadda zombie suke yi. Lado mai gadi da ke zaune a kan kujera cikin gyagyaɗi ya ji gudun Jafar, a zabure ya miƙe yana faɗin.
"Ranka shi daɗe lafiya kuwa?"

Jafar ko ta kan Lado bai bi ba ya banke shi ya faɗa ɗakinsa ji kake garam! Ya doko ƙofar ya rufe, dabass! Lado ya faɗi saboda bangazar da Jafar ya yi masa ya yunƙura yana kaɗe jikinsa ya furta.

"Allah na tuba wane dare ne jemage bai gani ba? Ai sai daren mutuwarsa. Ni akwai wani aljani ko ɗan fashi da zai razana ni, ni da tun ban fi shekara biyar a duniya ba Baffa ya fara kwana da ni a wurin gadi..." Maganar Lado ta maƙale sakamakon hango Uwani da ya yi tana tafe tana ƙaƙƙanbare hannu, 'yar ƙaramar sandarsa ya ɗauka zai tunkari Uwani tsoro ya fara kama shi. Lado ya fara waige hankali a tashe ya cewa Jafar.

"Yallaɓai! Wai mene ne ma ya karo ka daga cikin gidan ne." Muryar Jafar a can ƙuryar ɗaki ya ce. "Lado gamo na yi don Allah ka yi wani abu a kai."

Lado ya fara tunkarar Uwani gabansa na faɗuwa, sai da ya tafi gadan-gadan kamar zai iya taɓuka wani abu sai kawai ya zuba a guje ya fara doka ƙofar ɗakinsa. Jafar na jin an fara doka ƙofar ɗakin Lado wani abu ya sake tsarga masa, jiki na karkarwa ya ce.
"Lado ya ake ciki ne kar dai sun fi ƙarfinka kai ma?"

Lado da ke cikin tashin hankali ganin Uwani ta zo daf da shi ya fara fitsare wandonsa ba tare da ya sani ba. Uwani ta fisgi sandar hannunsa tana wage baki, ta zuba masa tana caccaka masa tsinin sandar a baya. Cikin tashin hankali Lado ya fashe da kuka ya furta.
"Yallaɓai don Allah ka taimaka mini, ni ma fa na shiga hannu." Jafar da ke cikin ɗakin jin Lado na kuka shi ma sai ya fashe da kuka don ya san tun da aka fi ƙarfin Lado shi ma yana nan ɗakin za su zo su cim masa.

Daga can saman window Uwani ta hango Mami na ziro kai tana leƙen abin da yake faruwa, Uwani ta ɗaga kai tana wani gwale fuska ta nuno Mami da sandar hannunta ta ce. "Keeee me leƙen nan! Wallahi za mu mayar da fuskarki ƙeya, mu ɗebo ƙafafunki mu dawo da su ƙirjinki. Shi kuma ƙirjinki mu mayar da shi gadon bayanki." Tun Mami ba ta gama jin abin da Uwani ke faɗa ba ta yi saurin banke gilas ɗin window. Lado na ganin ya ɗan samu sarari ya zuba uban ihu ya nufi sashen su Mami a guje. Uwani ta rufa masa baya tana tafe tana ranƙwala masa sanda a baya, Lado ban da ihu babu abin da yake saki.
Jafar da ke cikin ɗakin Lado ya yi sharkaɓa da gumi jikinsa ban da karkarwa babu abin da yake yi. Lokaci ɗaya ya ji zazzaɓi ya rufe masa jiki, a lokacin da ya ji Uwani ta bi Lado a guje da sauri Jafar ya ja zani ya tura kansa a ciki yana kalmar shahada.

Lado na tura ƙofar sashen Mami ya tura ƙofar da datse da sakata jiki na rawa, da ƙarfi Uwani ta fara kartar ƙofar tana faɗin.
"Za mu jijjige ƙauren gidan mu shigo, mu banka wa mutanen cikin gidan wuta. Ko kuma mu burtso ta ƙarƙashin ƙasa mu kwashe ku tass."

A guje Lado ya shiga cikin gidan, da ɗakin Mami ya fara cin karo don haka ya banka da ƙarfin gaske ya faɗa ciki. Mami na kwance a kan gado cikin bargo ban da karkarwa babu abin da jikinta take yi, jin an yi sufa a kan gadon da take ciki an shige bargo ya sa ta yi tsammanin ko Daddy ne shi ma aka tsora ta yake neman ɗauki.

Sai da Uwani ta tabbatar da Lado ya gama tsurewa sannan ta yarda sandar ta nufi sashenta, kayan jikinta cire ta saka wata doguwar riga har ƙasa sannan ta shiga banɗaki ya wanke fuskarta ta haye gado ta kwanta abin ta.

Duk budurin da ake yi Daddy da su Shukra sam ba su sani ba, da yake Daddy ya tsaya nafilfulu bai kwanta da wuri ba. Kwanciyarsa babu jimawa bacci mai nauyi ya yi awon gaba da shi, da ma Mami ba ɗaki ɗaya suke kwana ba tun ranar da ya je mata da maganar auren Jafar ta yi masa yaji take kwana a ɗakinta. Don haka ko da suka tare a sabon gidan ma, ba ta sauya zani ba.

Daga Mami har Lado babu wanda ya gane wanda yake kusa da shi, don haka sai da asuba ta yi Lado ya zuro kai a hankali. A daidai lokacin Mami ta ɗago kai karaf suka haɗa ido da shi, a zabure Mami ta ja da baya fuska a murtuke ta ce.
"Lado! Uban me ya kawo ka ɗakina?"

Sai a lokacin Lado yake bin ɗakin da kallo, don shi dai bai san lokacin da ya shiga ba. Hankali a tashe ya furta.
"Hajiya wallahi sai dai idan kawo ni aka yi! Wallahi ba ni na kawo kaina ba. Aljanun da suka biyo Jafar ne suka kawo ni..." A zafafe Mami ta katse shi.

"Fita don Ubanka Lado." Kamar sabon munafiki haka Lado ya fita yana waige-waige, kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci yana cikin tashin hankali. Banɗaki Mami ta faɗa ta ɗauro alwala ta yi sallar asuba, da yake gari ya yi haske sosai fita ta yi ta nufi sashen Uwani. A lokacin da ta fara buga ƙofa Uwani tana kwance, ta fara magana.
"Waye?"

"Uwarki ce." Mami ta amsa a taƙaice.
Babu musu Uwani ta buɗe ƙofar ta furta. "Ina kwana..."

"Riƙe gaisuwarki, ina Jafar yake?" Uwani ta wara hannuwa ta ce. "Ni ma ban wayi gari na gan shi ba, yanzu nake shirin zuwa na tambaye ki." Rass gaban Mami ya faɗi, da sauri ta fice daga sashen Uwani ta nufi wurin Lado da ke zaune a kujera yana jin rediyo.

"Lado ba ka ga fitar Jafar ba?" Mami ta tambaya.

"Hajiya ai Jafar na cikin ɗakina tun daren jiya, yanzu haka na yi-na yi ya buɗe wallahi ya ƙi, ni tsorona ma kada mutanen ɓoyen nan su dawo su tarfa ni a wurin nan." Lado ya ƙarasa maganar wasu tagwayen ƙwalla na zuba. Mami ba ta ƙarasa jin maganar Lado ba ta nufi ɗakin tana bugawa.

"Son buɗe mini ƙofa Maminka ce." Daga cikin ɗakin muryar Jafar can ƙasa ya furta. "Mami ku miƙo mini ruwan alwala, ba zan iya fitowa ba wallahi gwagwiye mini ƙafa za su yi." Duk yadda Mami ta so Jafar ya buɗe ƙofar fir ya ƙi buɗewa, Lado ya miƙa masa ruwa ta window da sauri Mami ta nufi sashensu kai tsaye ta wuce ɗakin Daddy.

Da sallama Mami ta shiga, turus ta yi ganin Daddy na zaune a kan dadduma yana karatun Alƙur'ani. Ganin Daddy ba shi da niyyar sallame karatun ya sa Mami ta furta. "Daddy gidan nan fa babu lafiya. Domin ganin idona na ga aljanu a daren jiya, yanzu haka Jafar yana ɗakin Lado tun daren jiya ya ƙi fitowa. Ka ga dai yau kwananmu ashirin da biyu a gidan nan ko kunama ba ta taɓa tsoratar da mu ba, amma zuwan yarinyar nan ga shi aljanunta suna neman sabauta mini yaro." Daddy ya kafe Mami da kallo, a daƙile ya furta. "Allah Ya sawaƙe." Ran Mami a ɓace ta ce.

"Iya abin da za ka iya faɗa kenan Daddyn yara? An ya kana ƙaunata ni da 'ya'yana yanzu kuwa?" Sai Mami ta fara zubar da ƙwalla. Daddy bai tanka mata ba ya rufe Kur'anin sannan ya naɗe dadduma ya fice daga ɗakin.

Duk abin da yake faruwa Lado ya zayyana wa Daddy, Daddy ya isa bakin window ɗakin Lado ya leƙa. Ban da gumi babu abin da Jafar yake yi, da ƙyar Daddy ya shawo kan Jafar ya buɗe ƙofar. Lokaci ɗaya Jafar duk ya yi zuru-zuru, Mami ta ƙarasa ta ruƙo hannunsa tana faɗin. "Son amma babu abin da yake damunka ko?" Uwani da ta ƙarasa ta nuna kamar ba ta san abin da yake faruwa ba ta ce.

"Ya Jafar ina ka shiga da asuba na ga ba ka nan." Jafar ya bi Uwani da shanyayyun idanunsa da kallo, Mami ta wurga mata harara sannan ta ja hannunsa suka wuce sashenta. Uwani ta gimtse dariyarta ganin yadda Jafar yake tafe yana ɗimgisa ƙafa, sai ƙara wani shagwaɓe wa Mami yake.

Daddy ne ya koma wurin Lado ya sake tambayarsa tsakaninsa da Allah a kan abin da ya faɗa masa, don shi bai yarda da abin da Mami ta faɗa ba. Gani yake kamar wani sabon shirin suka ɓullo da shi, sai da ya ji ta bakin Lado ya kuma nuna masa shatin bayansa wurin da Uwani ta caccaka masa sandar wurinsa sannan Daddy ya yarda.
Shiru Daddy ya yi yana nazari, a iya zamansu dai a gidan ba su ga wani baƙon abu ba. Sai tunaninsa ya tsaya a kan ko Uwani tana da iska, ya fi aminta da wannan tunanin na shi a kan mutanen jikin Uwani ne suke yunƙurin tashi tun da dama wasu sai an yi aure suke nuna kansu.

Jafar wanka ya yi Mami ta dafa masa tea ya sha sannan ya samu ya kwanta bacci ya yi awon gaba da shi, ita kuwa Uwani tana can zaune Daddy ya leƙa ya kira ta ya ce ta nufi sashen su Mami ta zaune akwai baƙin da zai kira za su yi saukar Alƙur'ani a cikin gidan. A rakaɓe Uwani ta zauna a falon, sai uwar harara da Mami take auna mata don ma Daddy yana gidan amma ta ci burin tun a ranar ta fara hora ta da aikin wahala.

Sai kusan sha biyun rana ragowar 'yan uwan mahaifiyar Uwani da wasu tsirarun 'yan uwan Dada suka sake dawowa ganin gidan Uwani, sai a lokacin ne Uwani ta ɗan saki jiki suka dinga hira. Mami ba don ta so ba ta sa Inna mai aiki ta girka musu abinci, bayan sallar la'asar kuma kowa ya kama gabansa.

Daren ranar da ƙyar Daddy ya shawo kan Jafar suka koma sashensu, don ita Uwani fir nunaawa ta yi ba ta gane abin da Jafar da su Mami suke faɗa ba. Dalilin haka ya sa Daddy ya sake tabbatar da ƙila mutanen jikin Uwani ne suka tsora ta su. Sai da suka ci abinci a ɓangaren su Mami sannan suka nufi na su, suna zaune a falo zaman kurame wayar Jafar ta fara ringing. Number Safna ya gani bai san dalili ba haka kawai ya ji gabansa ya faɗi, a hankali ya ɗauki wayar daga can ɓangaren aka furta.

"Haba Baby wai ina ka shiga ɗazu na kira no respond." Jafar ya saki murmushi. "Cutie na gaya miki kwana biyu ba na zama but am very sorry, In shaa Allah haka ba za ta ƙara faruwa ba."

"Beb dama fa Daddy ne na ji yana yunƙurin haɗa ni da wani cousin ɗina, ni kuma na ce masa ina da wanda nake so. So yanzu dai ya ce kawai ka fito..." Tun Safna ba ta gama magana ba Jafar ya miƙe a zabure, "Da gaske kike Cutie?" Jin yadda ya karɓi maganar ne ya sa Safna ta ce. "Da wani abu ne Baby?" Jafar ya ɗan wayance yana sosa ƙeya ya furta. "Am ba komai Dear kawai na yi mamaki ne, na ɗauka Dad ba zai bari a yi maganar aurenmu yanzu ba." Cikin jin daɗi Safna ta ce.

"No ka san Daddy bai da matsala."
Jafar ya ma manta Uwani na wurin shi da Safna suka ci gaba da hirar soyayya, ya tabbatar mata da zai sanar da mahaifinsa duk abin da ake ciki.

Baki sake Uwani ke bin sa da kallo tana mamakin yadda yake sakin murmushi. "Ya Jafar dama kana dariya haka?" Uwani ta tambaya.

"Sai ki hana ni, da waya ce ki zauna ki saka mini ido?" Uwani ta tura baki gaba. Suna nan zaune sai ga kiran Dada ya shigo wayarsa. Sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗauka yana faɗin.

"Tsohuwa mai ran ƙarfe." Dada ta saki murmushi ta furta. "Lallai Jafaru dare guda wai amarci ya ɓoye ka, ja'irin yaro da ana baka ka na ƙin karɓa..."
"Kin san Allah Dada zan kashe wayata." Jafar ya furta a taƙaice.

"Yoo kashe mana Jafaru, ai ubanka Mamman na nan. Ni ba zan aiki uwarka Saro ba saboda ba ganin mutumcina take ba. Amma wallahi ka kashe mini waya ban gaisa da Uwani ba sai na kira ubanka Mamman ya kawo mata waya." Jafar bai tanka ba ya miƙa wa Uwani waya.

"Dada ni dai gaskiya wurinki zan dawo, gidan nan babu daɗi ko kaɗan." Dada ta washe baki ta furta. "Haba Uwanita ai dama gidan aure kowa a sannu yake sabawa, lokacin da aka kawo Saratu uwar Jafaru ta haura wata biyu tana guduwa gida. Amma ba ga shi yanzu Saro ta murje tana zuba mulki ba, ke dai duk shawarwarin da na baki na riƙe miji ki riƙe su gam, kin san dai halin Jafaru da baƙin halin tsiya. Kar dai ki ɓata masa ya sa bakin bindiga ya harbe mini ke." Gaban Uwani ya faɗi, da sauri ta ce.

"Kuma sai ya harbe ni fa ko Dada?" Jafar da ke jin duk abin da suke faɗa ya kalli Uwani ganin lokaci ɗaya ta firgice.

"Wallahi indai halin Jafaru da na sani ne tsaf zai harbe ki, yo ba Mamman ne ya haifo shi ba. Ai Allah kaɗai ya san haƙurin da Saro take yi da shi, ni ina zargin duk rashin mutumcin da take yi ma Mamman ne ya koya mata. Atoh kowa dai ya san mata na da alkunya, kuma idan kika ga mace ta canza daga mijinta ne. Ni dai yanzu duk wannan hirar da muke yi kada ki bari Jafaru ya ji, don sai ya sanar da Mamman. Ina zaman-zamana tun daga ƙuruciya ban taɓa sanin wurin Hukuma ba Mamman ya yi ƙarata. " Uwani ta ce.

"Dada wai ina na Madina ko cigiyata ba ya yi ne? Ina su Lawan kina dai kula da su ko?" Lokaci ɗaya Dada ta bushe da dariya sannan ta ce. "Na Madina fa ya tafi wurin wata Goggon su Sabi'u, ni ban san na Madina neman aure yake ba sai jiya, ashe shi ya sa kullin a cikin sayen turaren binta sudan yake. Ni dama na jima ina yi wa na Madina addu'ar Allah Ya damƙa shi hannu mata ta gari..."

"Dada zan yi amfani da wata na gaji da wannan hirar ta ku." Jafar Ya faɗa yana ƙoƙarin karɓar wayarsa. Daga can ɓangaren Dada ta ce. "Jafaruruna gaskiya na ji daɗin yadda na ji zamanku kai da Uwani, amma don Allah ka sayo mata waya ma dinga gaisawa idan kana gida." Jafar zai yi magana Dada ta katse shi.

"Kai gaskiya kar ma ka saya wa Uwani waya ka yi asarar kuɗinka, haka kawai kuna zaune lafiya ta haɗa lamba ta kira maka mutanen duniya. Kwanki da ta ɗauki wayata sai ji na yi ta kira wani ɗan yuniyon..."
"Shi kenan sai da safe Dada." Jafar ya katse ta yana karɓar wayar daga hannun Uwani. Dada ta saki murmushi ta ce. "Allah mai iko wai Jafaru ne yau yake zumuɗin kashe waya saboda ga mace a gefensa." Ɓacin ran kalaman Dada ya sa ya katse wayar ba tare da ya tanka mata ba.

Dare ne ya fara yi don haka Uwani ta gaji da kallon da take yi, ɗaki ta shiga ta fara duba akwati domin ta ɗauko rigar bacci ta saka. Tsulum ta ga Jafar ya shigo da sauri sai wani wuri-wuri yake yi.
"Malam ka fita zan sauya kaya." Uwani ta furta.

Banza ya yi mata don a yadda ta lura da Jafar kamar a tsorace yake, don haka ta ɗauki wata doguwar riga ta shige banɗaki. Sai da ta sauya kayan sannan ta koma ɗakin, tana shirin hawa kan gado ta ga ya jefa mata filo ƙasa.

"Ina zaki je?"
"Kwanciya zan yi." Ta amsa masa a taƙaice.

"Daga yau a nan ƙasa za ki dinga kwana idan ba haka ba ranki zai yi mummunan ɓaci." Jafar ya yi maganar yana ɗaukan jallabiyarsa ya shiga banɗaki, sai da ya sauya kaya ya fito sannan ya haye gado ya kwanta. Uwani ta ɗauki filon ta koma can gefen gado tana shirin ajiye filo Jafar ya riƙo kunnenta da ƙarfi ya murɗe.

"Kin raina abin da na faɗa miki ne? To ki kwanta Allah Ya ba ki sa'a." Ya ƙarasa maganar yana murɗe mata kunne har sai da Uwani ta ɗan ƙwalla ƙara.

Babu yadda ta iya haka ta koma ƙasa ta yarda fulo ta kwanta, bayan wani lokaci gabaɗaya bacci ya yi awon gaba da su.

Cikin dare Uwani ta ji sanyi ya dame ta ga bargon na su Jafar ya ɗauka ya rufa da shi, cikin sanɗa ta ɗauki filo ta koma can gefen gado ta janyo bargon ta rufa. A wannan karon ma Jafar yana juyowa cikin bacci ya ji ya sake shafo ƙwaryar molo, Uwani da ke bacci jin ana shafa ƙwaryar molon kanta ya sa ta buɗe ido. Da yake ƙeyarta ce ke kallon fuskar Jafar sai ta maƙe murya ta ce.

"Kada ka motsa, idan ka yi yunƙurin guduwa sai na tsinke ƙafafuwanka." Jafar na jin haka sai kawai ya taƙarƙare ya rushe da kuka, ya fara biya duk wata addu'a da ke bakinsa. Sun ɗan jima a haka suka ji an fara kiran assalatu, Uwani ta fara wani gurnani tana wani bubbuga hannuwa sannan ta ce. "A yanzu za ka iya fita ka je ka yi sallah." Tun ba ta rufe baki ba Jafar ya buga tsalle ya fice a guje, yana fita ya ci karo da Daddy jikinsa na rawa ya furta. "Daddy wallahi gidan nan da aljanu Allah ba zan ƙara kwana a ciki ba." Ganin yadda jikin Jafar ke rawa ya sa Daddy ya riƙe shi gam a jikinsa, riƙe hannunsa ya yi suka fara tunkarar sashensu. Da sauri Jafar ya fara kiciniyar fisge hannunsa ya ce. "Daddy ina za mu shiga?" Daddy ya saki murmushi irin na manya ya ce. "Trust me son, ka san dai ba zan cutar da kai ba." Shiru Jafar ya yi suna tafe gabansa na faɗuwa har suka shiga, cikin shammata Uwani ba ta yi tsammani ba suka yi ido huɗu da Daddy. Cikin tashin hankali Uwani ta zaro ido, ta kai hannu ta dafe kanta.

Na ce kin turo kuɗin littafinki kuwa? Yau promo ɗin zai ƙare💃🏻 faka-faka ki turo 400 Aisha Adam First bank shedar biya ta wannan lambar 07062062624 idan yau ta wuce za ki turo 500 maza hanzarta kada a yi babu ke🫠

07062062624
#Ummou Aslam Bint Adam🌚
[30/06, 19:35] Ameerah Adam🌚: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.


SHAFI NA SHA BIYU

Ganin yadda Uwani ta tsorata ya sa Daddy ɗan kawar da kansa, duk da a falo suka ci karo da ita za ta fito. A fili Uwani ta sauke ajiyar zuciya, ta sauke hannunta daga kanta don kaɗan ya rage asirinta bai tonu ba. Saboda ta ɗaura ɗan kwalinta a kanta kenan su Daddy suka shiga.

"Barka da asuba Daddy." Uwani ta furta.
"Barka dai Uwani me yake faruwa ne?" Daddy ya tambaye ta yana kallon yanayinta. Sai da ta saci kallon Jafar sannan ta ce.
"Wallahi Daddy ban sani ba, ina cikin banɗaki na ji ihun Ya Jafar, fitowar da na yi kenan zan bi shi na ga abin da yake faruwa." Ganin yadda Uwani ta rattabo bayani kamar ba ta san abin da yake faruwa ba ya sa Daddy ya aminta da ita, don haka ya furta.

"Ki ɗauko hijabinki ki taho sashen Maminku." Daga haka Daddy ya juya, Jafar ya yi saurin bin bayansa.

"Ka sako kayanka mana Jafar." Daddy ya katse shi. Sai a lokacin Jafar ya lura daga shi sai singlet da gajeren wando.
"Uwani miƙo mini kayana." Uwani ta wuce ɗakin tana ƙumshe dariyarta ganin yadda Jafar ya tsure lokaci ɗaya. Tana miƙa masa kayan ya yi sauri ya sa, yana cikin saka riga Uwani ta janyo hijabinta za ta fita da sauri Jafar ya fisgo hannunta ya ce.

"Ina za ki tafi ki bar ni, ki jira ni mana na gama shiryawa. "A wannan karon sai da dariya ta ƙwacewa Uwani ta ce.
"Wai don Allah a wurin training ba a fitar da masu tsoro da marasa tsoro ne a cikin aikinku ne?" Jafar ya wurga mata harara.

Sai bayan da suka yi breakfast sannan Daddy ya kira Jafar, Uwani da Mami sannan ya fara magana.
"Dalilin da ya sa na tara ku bisa wata matsala da ke faruwa daga jiya zuwa yau, a baya ban yi niyyar sanar da 'yan uwana ba amma yanzu..."

"Daddyn yara babu fa buƙatar a tsaya ɓata lokaci, raba wannan auren shi ne mafi amfani a gare mu. Ina ji ina gani sheɗanu ba za su kashe mini ɗa ba, wannan yarinyar ba alkairi ba ce a wurinmu face annoba." Shiru Dadday ya yi yana sauraron Mami har ta gama. Sannan ya ɗora da cewa.

"Ka buɗe kunenka da kyau ka saurari abin da zan sanar da kai Jafar." Daddy ya furta rai a ɓace. Jafar ya gyaɗa masa kai, Daddy ya ci gaba.
"Ga Uwani nan ni da 'yan uwana da kuma mahaifiyarmu mun damƙa maka ita amana, wallahi ko bayan raina idan ka rabu da ita ban

Please Login or Register in order to submit comment