Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gyara komai da saka komai na gidan, tun da akwai wadataccen wuri za ku zauna a ƙaramin part ɗin da ke gefen na Maminku." Wani irin tuƙuƙin zafi ne a zuciyar Mami har za ta ƙi amimcewa da hakan sai kuma ta tuna da huɗubar ƙawarta Hajiya Falmata.

"Saboda haka muka yanke shawarar idan Allah Ya kai mu juma'a mai zuwa ne tariyarku, kuma bayan nan za a nema wa Uwani wata makarantar za ta ci gaba da karatunta. Idan ya so bayan sun yi hutu sai ka ɗauki matarka ku wuce wurin aiki." Jafar ya yi shiru ba tare da ya amsa ba. Wannan maganar ta ƙarshe ba ƙaramin daɗi ta yi wa Mami ba, don a wannan lokacin ne za ta ci karenta babu babbaka a kan Uwani.

"Ni iya abin da zan iya ce wa kenan, Dada kafin mu zo kan ki ko akwai mai magana a cikin?" Gabaɗaya suka girgiza kai ban da Baba Mustafa da ya ce yana da abin cewa.

"Sannu da ƙoƙari Yaya Allah Ya ƙara girma, duk bayananka a kan tsari suke. Amma abin da nake gani me zai hana a ɗaga tariyar ta su zuwa nan da kamar sati biyu zuwa uku, duba da yanayin ragowar shirye-shiryen da ya kamata a yi musu. Daga haɗa lefe har zuwa wani shirye-shirye na su na mata, sannan a wannan lokacin mahaifiyar yarinyar na cikin halin rashin 'yarta. Amma bayan wannan lokacin ita kanta za ta samu nutsuwar gudanar da bikin yadda ya kamata." Dada ta jinjina kai sannan ta furta.

"Wallahi Mustafa ka yi kyan kai, saboda Allah kamar gajiya na yi da Uwanin da za a ce nan da kwana huɗu a kai ta ɗakin miji." Baba Yunusa ya yi murmushi ya furta. "Wannan haka ne, Dada me za kike ganin ya dace bayan haka." Dada ta yi jim sannan ta furta.

"Ni dai kam nasiha ce zan yi wa Jafaru da ita Uwani, amma kam ba yanzu zan yi musu ba sai ranar da za su tare. Don ina gudun na tofar da yawun bakina a banza, su barbaɗar da nasihar da na yi musu tun kafin tariyarsu." Tambayar Mami aka yi ko tana da abin faɗa ta ce babu, don haka suka ƙarƙaren zaman tun ba a gama addu'a ba Mami ta sa ƙafarta ta fice rai a ɓace.


07062062624
#Ummou Aslam Bint Adam🌚
[30/06, 19:35] Ameerah Adam🌚: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.


SHAFI NA GOMA

Tun daga wannan ranar su baba Yunusa suka shiga hada-hadar shirye-shiryen tariyar auren Uwani da Jafar, a ɓangaren baba Mamman sai abin ya haɗe masa biyu ga tariyar su Mami ga kuma ta shirin su Jafar. Babba Mamman da kansa ya kira Jafar ya nemi da ya bada wani abin domin ba don da auren ya zo a haka ba, ba shi da tsarin haɗa wa ɗa namiji lefe sai dai ya yi komai da kansa ko ya fi ganin darajar auren da aka ba shi. Amma fir Jafar ya ce ba shi da wasu wadatattun kuɗi, sai da ya ga ran mahaifinsa ya ɓaci sosai sannan ya iya bayar da dubu ɗari uku. Su ma sai da Baba Mamman ya yi masa barazanar zai ɗaga wani filinsa ya sayar a haɗa wa Uwani lefen da shi sannan ya bayar.

Mami ban da 'yan uwanta babu wanda ta iya gaya wa sai kuma ƙawarta Hajiya Falmata da ta san da maganar, babban tashin hankalinta kada Hajiya Salima ta ji labari ta ce Safna ba za ta auri Jafar ba. Don haka ta kira Jafar a ɗaki ta gargaɗe shi a kan ko da wasa kada ya sake ya faɗa wa Safna maganar aurensa, don a yadda ta tsara auren ko wata biyu ba zai rufa ba Uwani za ta bar gidan da ƙafarta.

Dada da ƙafarta ta je har garinsu mahaifiyar Maryama ta sanar da su duk halin da ake ciki, ba ƙaramin murna suka yi ba suka yi fatan alheri. Haka Dada ta sa aka dinga sanarwa da jama'a wunin bikin Uwani, shi kuwa Jafar har kawo lokacin kallon abin yake kamar a mafarki.

Yana shiga ɗakin abokinsa Amir zama ya yi a gefen gado ya zuba uban tagumi, labule Amir ya ɗaga ya shiga hannunsa ɗauke da karan sigari yana zuƙa. Da mamaki ya dubi Jafar ya furta.

"Abokina yaushe ka shigo? Kai fa daɗina da kai ka yi wa mutum zuwan bazata, yanzu kuma da ka zuƙi warin 'yar so sai ka hau ni da sababi." Jafar bai ɗago ba ya furta.
"Miƙo mini kara ɗaya ka ba ni lighter zan zuƙa." Baki sake Amir ya ƙarasa bakin gadon ya ce. "Ko dai mafarki kake abokina?"

"Na ce ka ba ni." Jafar ya faɗa a ɗan zafafe. Ba musu ya miƙa masa, Jafar ya hau kiciniyar kunnawa. Ganin ya kasa saboda rashin sabo ya sa Amir ya karɓa ya kunna masa, Jafar ya kai baki ya zuƙa da ƙarfi lokaci ɗaya ya ƙware ya hau tari.

"Malam za ka kashe kanka a banza da wofi, wai me yake faruwa ne?"

"Da zan mutu ɗin ma ai da ya fi mini komai sauƙi." Cikin zaro ido Amir ya ce. "Wa ya ɓata maka rai ne?" Jafar ya kauda kai gefe murya a dashe ya ce.
"Aure aka yi mini."

Amir ya shafa gemu yana sakin wani murmushi sannan ya furta. "Ɗan iskan ƙarya. Kai yanzu don an maka auren ne har kake wannan..."

"Ka san wa aka aura mini? Uwani fa, wannan ƙanwar ta wa da ta taɓa sace maka tayar mashin." Jim Amir ya yi da sauri ya ce. "Wai wannan black beautyn? Amma fa kai shege ne, ka tsinci dami a kala ka zauna ka na sa kanka a damuwa?" Kalaman Amir suka ɓa ta ran Jafar bai tanka masa ba ya saka kai ya fice. Kafin ya ƙarasa fita Amir ya ce. "Billahillazi ni zan ɗauki nauyin kazar amarci idan muna raye." Jafar ya dawo da kansa a ƙufule ya ce.
"Sai dai ka cinye abarka don ubanka."

Amir ya bushe da dariya sannan ya bi bayan Jafar, sai da ya shawo kansa da ƙyar sannan ya labarta masa yadda auren na sa ya kasance. Sam Amir bai ga abin damuwa ba, don ce masa ya yi bayan auren Uwani babu jimawa kawai ya auri Safna tun da ita ce zaɓinsa.

Kamar yadda baba Mamman ya tsara juma'ar da ta zo a ita ce su Mami suka tare a sabon gidansu, babban gida ne sosai don haka Mami ta ƙara jin kanta ya daɗa girma. Ta dinga kallon Facalolinta tana basarwa don ita a yadda ta so sam ba ta so sun kwaso jiki da gayyar 'ya'yansu sun zo mata ba. Yamma liƙis suka fara haramar tafiya a nan ne kuma baba Mamman ya ce Dada ba za ta tafi ba sai ta yi kwana biyu. Da yake a part ɗin su Mami har da ɗakin Dada da banɗakinta a ciki, fasalin gidan ba ƙaramin birge Uwani ya yi ba. Don haka da ta ji Dada ta ce ba a ranar za su tafi ba ko a jikinta. Mami ba ƙaramin haushi ta ji ba, don dai tana shakkar Daddy shi ya sa ba ta yi wa Dada kora da hali ba har suka gama kwanakinsu suka koma.

Sannu a hankali kwanaki suka fara gangarowa har bikin su Uwani ya ƙaraso, shirye-shirye daga kowanne ɓangare ya yi nisa. Dangin mahaifiyar Uwani da mahaifiyarta ba ƙaramin ƙoƙari suka yi ba, haka su baba Yunusu su suka yi wa Uwanu komai har da su gara. Ƙawayen Uwani su Zulai, Hansatu, Furaira da Kubra sai rawar kai suke su a dole ga manyan ƙawayen amarya. Jafar kuwa ya yi wata irin rama ya ɗan yi duhu kamar shi ne macen, ita kuwa Uwani ko ajikinta sai ma warkajaminta take yi.

Ranar juma'a ita ce ranar da aka yi kamun Uwani kuma a ranar ne za a kai ta, tun ranar alhamis aka rangaɗa wa Uwani lallen dungulmi hannu da ƙafa. Ranar Juma'a da sassafe Dada ta ja Uwani uwar ɗaki ta ce.

"Uwani ni kam ina kunyar a kai ki ɗaki da wannan uwar kwarkwatar, kin san dai Jafaru da tsirfa tsiya. An ya ba aske miki kan nan zan yi baki alaikum, ba tare da wani ya sani ba." Ita kanta Uwani kan ya ishe ta ga yawa ba gyara ga kuma kwarkwata, don haka ba ta musa wa Dada ba. Da kanta ta karɓi kuɗi ta sayo reza, kamar masu yin wani ɓoyayyan sirri haka Dada da Uwani suka shige uwar ɗaki. Da farko almakashi Dada ta sa ta fara sauke mata kan tass sannan ta bi shi da reza ta yi mata ƙwal kwabo. Nan take Uwani ta ji wata ni'imtacciyar iska na shiga kanta, Dada ta bi ta banɗaki ta wanke mata kan tass sai ga kan Uwani ya fita ƙwal kamar bayan silba yana sheƙi. Bayan Uwani ta gama shiri ta kawo ɗankwali ta ɗaure kanta da shi, tun da ta ji iska na shigarta ta ci alwashin daga ranar idan kanta ya taru aski za ta dinga yi.

A daren ranar ne kuma aka shirya Uwani domin kai ta ɗakin mijinta, saboda haka Baba Yunusu ya tara 'yan uwansa aka yi wa Jafar da Uwani nasiha. Uwani na daga cikin mayafinta sai satar kallon iyayen nata take, Jafar kuwa ya haɗe fuska ya sunkuyar da kai ƙasa abin duniya ya haɗe masa. Har an zo fita da Uwani sai Dada ta ja ta gefe ta fara yi mata raɗa a kunne, lokaci ɗaya sai ji aka yi Uwani da Dada sun bushe da dariya. Bayan Dada ta gama mata nasiha sai kuma ta rushe da kuka, sai da aka lallashi Uwani sannan suka wuce Dada ta riƙe hannun Jafar da Uwani suka shiga mota. Ragowar 'yan kai amarya kuma suka bi sauran motoci aka wuce da su gidan Mami.

Sai da Dada ta kai Jafar da Uwani har sashen Mami domin ta yi musu nasiha, a yatsine ita da 'yan uwata suka tarbe su don yadda ta hangi Uwani tare da Jafar har ji ta yi kamar ta shaƙe ta. Su Dada na fitowa suka ci karo da su Amir shi da wasu abokan Jafar guda biyu.
Dada ta wuce da Uwani sashenta shi kuma ya wuce wurin su Amir.

"Ango ango!"
Amir ya furta yana dariyar ƙeta.
"Kai ba na son iskanci." Jafar ya faɗa a daƙile.

"Wato wata miyar fa sai dai a maƙota, abokina ga fa alƙawarina na cika." Amir ya yi maganar cike da shaƙiyanci yana ɗago masa ledar kaji. Jafar duk tsiyar da suke yi masa shiru ya yi ya ƙyale su, ganin dare ya fara yi ne ya sa suka tilasta masa shiga cikin gidan.

Har kan gado Dada ta kai Uwani, suna shiga ɗakin Uwani ta fisge mayafin tana kalle-kalle. Dada kuwa sai murmushi take tana sa wa su Baba Yunusa albarka. Sai da Dada ta zo tafiya a nan ne fa Uwani ta maƙele ta tana wani irin kuka mai ban tausayi, ita a dole sai Dada ta zauna. Sai da Inna Atika ta zare wa Uwani ido sannan ta koma laƙwas kan kado ta zauna. Gabaɗaya manya suka tafi daga Uwani sai ƙawayenta su Furaira.

"Ke kam Uwani a duniya me za ki nema? Ga miji kin samu ga gidan miji kamar na kwamihina. To ke kuwa kukan me za ki yi?" Furaira ta faɗa, da yake duk cikinsu ta girme musu nesa ba kusa ba. Uwani ta goge ƙwalla nan take su Furaira suka dinga yi wa Uwani huɗuba kala-kala, wani su ƙyalƙyale da dariya wani kuma su tashi su gwada abin da suka ce Uwani ta yi.

Suna cikin haka sai ga sallamar su Amir, Uwani da sauri ta ta ja mayafi ta rufe fuska tana murmushi, ita a dole irin kunyar nan ta amare. Tun da su Amir suka shigo Furaira take wata irin kwarkwasa, bayan sun gaisa a gefe ta hangi Jafar ya sunkuyar da kai ƙasa. Furaira ta ƙarasa gabansa fuskarta cike da ɗige-ɗige ta saka mayafin a kafaɗa, ga wasu hannuwan jajayen rigar mama da suka leƙo ta kafaɗarta. Furaira yi farrr da ido ta ce.

"Angonmu na ga kana cikin damuwa, idan ka yi haƙuri za mu ba ku wuri kai da amaryarka ku gwangwaje amarcinku, wannan tagumin ai ba naka ba..." Tun da Furaira ta fara magana Jafar ya kafe ta da ido yana kallon tsana, wani irin takaici ya mamaye shi. Jin abin da ta faɗa ya sa ya ɗago ya ɗauke fuskarta da mari. Sai ga Furaira daɓar a ƙasa, waɗansu manyan tagwayen taurari na yi mata yawo a fuska. Ganin abin da ya faru da Furaira ya sa su Zulai suka fita a guje har mayafai da ɗankwalayansu na faɗuwa ƙasa.

Amir na shirin magana Uwani ta buɗe kai daga cikin mayafi ta furta. "Haba Ya Jafar yanzu a gaban abokanka za ka zubar mini da mutumci? Furaira fa ka mara gaskiya ba ka..."
"Rufe mini ba ki."
Jafar ya buga mata tsawa, sai da ta muguɗa masa baki sannan ta shiga wurga masa harara don a wannan karon Jafar ya ba ta haushi sosai.

"To ango mu dai maƙasudin zuwanmu shi ne..." Da sauri Jafar ya katse Salis.
"Ba na son hayaniya Salis sai da safe." Amir ya gimtse dariya yana miƙa masa ledar kajin hannunsa ya ce.
"Au har korar mu kake, shegen gora mum muna kan hanya..." Gabaɗaya sauran abokan Jafar suka saka dariya, sai da suka yi wa Uwani sallama sannan suka fita. Uwani saboda ɓacin ran abin da ya yi wa su Furaira ko tanka musu ba ta yi ba.

Jafar na raka su ya koma falo ya zaune, a gajiye ya tuɓe babbar rigar jikinsa ya faɗa kan kujera yana lumshe idanu. Wayarsa ce ta fara neman agaji, da sauri ya ɗago ya duba. Safna ce ke kiransa don haka ya yi rejecting sannan ya kira ta.

"Baby wuni guda ka manta da ni." Daga can ɓangaren ta furta a shagwaɓe.
"Ta ya ya zan manta da ke cutie?" Ya amsa mata.

"Akwai wanda ya taɓa mini gwarzona ga dukkan alamu, baby me yake damunka? Kwana biyu na gagara gane kanka." Murmushi Jafar ya yi sannan ya furta.

"Daddy ne ya saka ni wani aikin so na gaji sosai."
"Ok, ka yi wanka ka huta da safe ma yi magana becouse akwai maganar da nake son yi da kai." Dam! Ƙirjin Jafar ya buga ba tare da ya san dalili ba, ya yi ƙarfin halin amsa mata sannan suka yi sallama.

Tun bayan fitar su Jafar Uwani ta fisge mayafin kanta, ta shiga ɓuruntun duba ɗakin ta buɗe wannan ta leƙa wannan. Bayan ta gama dube-dubenta ta koma bakin gado ta zauna, tuno huɗubar su Furaira ta yi da wacce Dada ta yi mata sai kawai ta saki murmushi. Banɗaki ta faɗa ta yi wanka, sannan ta buɗe akwatin lefenta ta zaro wata doguwar riga. Sai da ta ɗaga wata riga ta ƙare mata kallo sannan ta furta.

"Ashe shi ma ya Jafar ƙwallon ɗan iska ne a fakaice ban sani ba, dubi irin rigar fitsararrun indiya da ya sa aka sayo mini. Allah Ya sawaƙe ina zan yi wannan lalacewar Dada ta ga ya wa baba Mamman, haka kawai ya yi mini faɗa." Uwani ta cusa rigar cikin akwatin sannan ta zaro wasu riga da wando ta saka. Sabuwar hula ta farke ta saka a kan ƙwaryar molon kanta, sai kuma ta ciro wasu sababbin panties da rigar mama guda bibbiyu ta farke tana dariya. Can drower kayan Jafar ta buɗe ta jefa guda biyu sai kuma ta taka gado ta saƙale biyu a saman drower, ta koma tana bin ledar kajin da kallo ƙamshi na dukan hancinta. Ganin Jafar ba shi da niyyar dawowa ya sa ta ɗauko ledar kajin da sauran kayan shaye-shaye ta baje ta hau lodawa cikinta.

Uwani na nan zaune Jafar ya shiga ko kallon ƙurarta bai yi ba ya nufi drower kayansa domin ya ɗauki towel zai shiga wanka, yana buɗe drower sai jin abu ya yi a kansa rigar mama ta faɗo. Dama Uwani su Furaira sun ce ta yi haka ne, wai yin hakan na jan hankali ango da ƙara danƙon ƙauna. Shi kuwa Jafar yana buɗewa da ya ji abu ya faɗo kansa yaraf da sauri ya buga uban tsalle yana faɗin.

"Wayyo ɓera, wayyo Allah ɓera a kaina." Uwani na daga wurin da take zaune sai dariya take, a gefen kafaɗarsa ya hangi rigar a fusace ya fisge a yatsine ya furta.
"Mene ne wannan."
Uwani ta kanne dariyarta ta ɗan basar ta ce.

"Me ka gani to? Ba kai ka saƙalo a jikinka ba? Wai dama duk wannan muzuran da kake yi tsoron ɓera kake?" Jafar ya fisge rigar ya wurga mata, ya ƙarasa ya bige bakinta haɗe da matse shi da hannunsa. "Idan ba ki daina mini rashin kunya ba sai na fasa bakinki." Towel ya ɗauka har zai shiga toilet ɗin da ke cikin ɗakin ko me ya tuna sai ya fice ta nufi public toilet, bayan ya yi wanka ya ɗauko filo ya dawo falo ya kwanta. A kan kujera ya kwanta ya ji kwanciyar babu daɗi ya miƙe kenan ya ji bugun ƙofa, kafin ya tambaya ya ji muryar Mami da sauri ya buɗe Mami ta shiga tana bin ɗakin da wulaƙantaccan kallo.

"Ina kucakar nan take?" A sanyaye Jafar ya nuna ɗaki, kamar Uwani ta san da ita take sai ga ta ta leƙo falon hannunta ɗauke da cinyar kaza tana ci.

"Ke don Ubanki ba a koya miki ladabin gaida manya ba ne?" Mami ta furta cike da tsana.
"Mami na ce miki ki daina zagin iyayena musamman mahaifina da yake lahira..." Jafar ya katse Uwani cikin tsawa. "Ke ba ki da hankali ne? Idan Mami na magana na sake jin bakinki sai na yi ƙasa-ƙasa da ke."

"Ka bar ta ba sai ta rama zagin da na mata ba, 'yar iskar yarinya marar mutumci. Ban da ƙaddara ko a mai aikin gidan Jafar za ki zo ne." Uwani ta kafe Mami da kallo, Mami ta mayar da kallonta wurin Jafar. "Kai kuma ka lura da kanka, atoh ka dai gane abin da nake nufi. Wallahi ko da wasa kada na ji ka tsaya sauraron yarinyar nan ballantana wani abu ya ratsa tsakaninku, don wannan tsinannan auren wallahi ko wata biyu ba na saka ran ya kai ba." Jafar ya ɗan tsuke fuska.

"Me kike faɗa ne Mami don Allah? Yarinyar da ko kallonta ba na son yi." Zuciyar Mami fes ta ce. "Shi kenan Son Allah Ya yi maka albarka. Ke kuma da ma gobe kina yin sallar asuba ki zo sashena ina son ganinki, shegiyar yarinya da ido kamar na mujiya." Uwani na tsaye ta ji zuciyarta babu daɗi. Wannan shi ne karo na farko da wani ya taɓa yi mata abin da ya bugi zuciyarta, tana nan tsaye ta sake jin muryar Mami a kanta.

"Don uwarki ba magana nake yi miki, 'yar iska yarinya tsohuwar kakarki ta sangarta ki kina iskanci kala-kala. Da ƙafarki sai kin bar gidan nan da ni kuke zancen." Uwani ta sauke ajiyar zuciya rai a ɓace ta furta.

"Mami wannan ce magana ta ƙarshe da zan gaya miki a kan zagin iyayena, zan jure komai amma ban da zaginsu. Dada ta daban ce a wurina amma matuƙar kika ci gaba da zaginsu ni ma..." Maganar Uwani ta katse sakamakon marin da Jafar ya sauke mata. Take idonta ya ciko da ƙwalla ta dube shi za ta yi magana ya katse ta.
"Uwata ba sa'arki ba ce..."

"Kenan ni iyayena ne sa'anninta? Wallahi ba zan jura ba..." Tas tass Mami ta sake ɗauke fuskar Uwani da mari. "Na zagi Uwarki sai ki rama don ubanki."

Ban da ruwan hawaye babu abin da Uwani take yi, Mami ta gama ci mata mutumci sannan ta fice daga ɗakin. Tsaki Jafar ya saki ya wuce ya ɗauko bargo ya koma falo ya shimfiɗa ya kwanta zuciyarsa na suya, ta koma ta ɗauko mayafinta ta yafa ta zo za ta fice. Da sauri Jafar ya fisgo ta fuska a haɗe ya ce.

"Gidan uban wa za ki a tsohon daren nan?"

"Gidan da na fito tun da nan ba gidan zinare ba ne." Uwani ta ba shi amsa a zafafe. Tana gama magana ta sake miƙewa za ta fita ya sha gabanta. "Wallahi ba don Daddy na gidan nan ba, da babu abin da zai sa na hana ki fita. Shashasha ƙazamar banza da wofi." Daga haka Jafar ya sa key ya rufe ƙofar. Uwani ta koma ciki rai a ɓace. A ƙasa ta zauna tana nazarin hanyar da za ta samarwa kanta mafita, don ta tabbata idan ta ce a haka za ta ci gaba da zama a gidan nan ba za ta sha ruwa ba. Kuma ita dai wannan ƙerarran gidan ba za ta so ta fita daga shi ba ko don ta dinga cin daɗi kuma ta gyara wa Mami zama.

Ƙurajen da suka fara tsattsafo mata a kai ne suka fara yi mata raɗaɗi, don haka ta ɗauko jakarta ta ciro farar hoda ta bursune kanta, fuskarta har zuwa wuyanta. Hamma ta fara saki tana gyangyaɗi ba shiri ta ɗauki fulo ita ma ta nufi falo. A lokacin da ta shiga falon Jafar har ya kashe fitilar falon ya yi bacci, a gefe ta yarda filonta ta kwanta ita ma nan take bacci ya yi awon gaba da ita.

Lokacin da dare ya tsala Jafar na cikin bacci juyin da zai yi sai jin mutum ya yi a kusa da shi, a tunaninsa Uwani ce don haka ya miƙa hannu sai ji ya yi ya shafo kan mutum da rantal da aski. A zabure ya tashi yana faɗin.
"Kwarto ne zai shigo mana gida." Ya ɗaga hannu da ƙarfin gaske ya ɗaka wa Uwani duka a baya a tunaninsa kwarto ne. Tun da ya san ban da haka babu abin da zai kawo namiji ya kwanta a kusa da shi. A zabure Uwani ta tashi tana susar baya, sai a lokacin Jafar ya kunna fitilar ɗakin. Cikin tashin hankali ya fara ja da baya ganin baƙuwar fuskar da ya gani fururu da hoda, a hankali Uwani ta fara tunkaro shi. Jafar ya fara ja baya yana faɗin.

"Don Allah waye kai?" Uwani ta ci gaba da matsowa ganin ta tunkaro shi gadan-gadan ya sa Jafar ya zuba a guje ya fice daga ɗakin yana faɗin.
"Wayyo Allahna." Ita ma Uwani ta rufa wa Jafar baya a guje tana gudu tana wani irin gurnani.

Daga yau zan tafi hutun sallah sai ranar Laraba (19/06/2024) zan ci gaba da posting In Shaa Allah.
Littafin Uwani 500 ne amma daga yau zuwa ranar Laraba 19/06/2024 duk wacce ta za biya za ta turo 400 ta wannan Acc ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank Evidance ta wannan number
07062062624 na rage muku 100 for Happy Sallah. Mutanen Nijar su tuntuɓe ni.
Ina fatan 'yan uwa za a bi nama saffa-saffa don gujewa rikicewar ciki.😂

07062062624
#Ummou Aslam Bint Adam🌚
[30/06, 19:35] Ameerah Adam🌚: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.


SHAFI NA SHA ƊAYA



Please Login or Register in order to submit comment