Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke, wallahi kika kuskura kika bi ta ƙofar ciki daidai da rana ɗaya kika haɗa ni da Dadyn yara sai ranki ya yi mummunan ɓaci." Cikin damuwa Uwani ta amsa mata, Mami har za ta fita ta juyo ta ce. "Idan kuma kin gama ki same ni a falo."

Mami na fita Uwani ta jingina kai da bango, lokaci ɗaya hawaye ya fara ziraro mata.
"Yarinya a wannan lokacin kuka ba na ki ba ne, shi wannan aikin da kika ga Hajiya ta kawo ki mu dinga yi gata ne take yi miki. Saboda duk macen da ba ta iya girki ba wallahi ta faɗo a wurin miji, ki ci gaba da haƙuri watarana sai labari." Inna ta yi maganar ƙasa-ƙasa. Kukan da Uwani take yi ya yawaita jin kalaman Inna ya sa ta furta. "Wallahi ni kam na gaji Inna, gara na koma wurin Dada ni ban saba da wannan wahalar ba." Sai da Inna ta ɗan leƙa bakin ƙofa sannan ta sake ƙasa da murya ta ce. "Ita dama rayuwar aure ai takan zo wa bawa da al'amura mabanbanta. Ni na ɗauke ki tamkar jikata duk abin da yake damunki ki dinga samuna a fakaice kina gaya mini, amma kada ki bari kowa ya fahimci haka don gudun mu samu matsala ni da ke." Uwani ta ji daɗin yadda Inna ta amshe ta hannu bibbiyu, don haka ta share hawayenta ta fara taya ta duk abin da ya dace. A cikin aikin da suke yi ne Inna ta fahimci sam Uwani ba ta iya wani girki ba, hatta aikin ma wani abin sai ta koya mata.

Sai kusan tara saura sannan suka kammala komai, don har wanke-wanke babu abin da ba su gama ba. Uwani ce ta bi Inna dianing tana ganin yadda take yin komai, lokaci ɗaya Uwani ta nemi duk ƙuncin da take ciki ta rasa. Suna gab da barin kitchen ɗin ne Mami ta dawo tana bin Uwani da harara, ta dubi Inna ta ce. "Idan kun ƙarasa aikin ki ɗebo mata gero kwano ɗaya ta surfa, ta niƙe mini shi yau furar daka nake sha'awa." A sanyaye Inna ta amsa, Mami ta wuce ta buɗe tukwanen wurin, ganin abincin da Inna ta rage kusan na mutum bibbiyu ne ya sa Mami ta furta.

"An kai wa Lado abincinsa ne?" Da sauri Inna ta amsa. Mami ta sake haɗe fuska ta ce.
"Wannan abincin ai ya yi miki yawa Inna zuba mini a wancan plate ɗin."

"Dama ni da Uwani na rage mana..." Mami ta yi saurin katse Inna.
"Uwani idan ta gama za mu rage mata abincinta a wurinmu." Inna babu yadda ta iya haka ta ɗauki plate ta zuzzuba kamar yadda Mami ta buƙata, kusan shekararsu Takwas tana yi wa Mami aiki ba ta taɓa ganin ta yi mata iyaka da abinci ba sai yau, a ranta ta jinjina ƙarfin ƙiyayyar da take yi wa Uwani.

Uwani tana kuka haka ta karɓi geron ta nufi harabar gidan tana dakawa, tun ba a je ko ina ba hannunta ya fara kanta ga turmin dakan ba shi da girman kirki don a surfe ma sai da ta raba shi gida huɗu sannan ta gama dake shi.

Tun Uwani na cikin inuwa har rana ta same ta don sha biyun rana a lokacin ta kusa, tana nan tana daka su Shukra suka fito cikin shirinsu gwanin birgewa. Auta ce ta ƙarasa wurinta da sauri ta ce.
"Uwani me kike yi haka ne?" Uwani ta share hawayenta. Tausayin Uwani ya kama Auta, a sanyaye ta ce. "Ki yi haƙuri Uwani In shaa Allah Mami za ta gane abin da take ba ta kyautawa, unguwa za mu yanzu wallahi da na taya ki." Uwani ta gyaɗa mata kai sannan ta wuce wurin su Shukra da har sun fita bakin gate.

Fitar su Shukra ba jimawa ita ma Inna ta zo ta yi wa Uwani sallamar za ta je kasuwar Garu, Mami ta aike ta yin cefane. Ita kanta Inna ta so taya Uwani sai dai tana tsoron kar ta je ta yi abin da za ta bar aikinta, don da kuɗin albashinta take samun na rufin asiri.

Lokacin da Uwani ta gama ta gama galabaita, ga yunwa ga kuma gajiya. Can kitchen ta je ta ajiye wa Mami garin geron saboda ba ta san yadda za ta sarrafa shi ba, ta fito za ta shiga ta ƙofar falo ta hangi wani tafkeken jangwalagwada. Har a fili sai da Uwani ta saki murmushi, ta ɗauko tsumma a kitchen da sauri ta ƙarasa wurinsa ta yi A'uzubillahi sannan ta damƙe shi da hannunta, a wannan karon ta ci alwashin yadda Mami ta azabtar da ita to ita ma sai ta rama. Har ta gama tsara komai koda ta kwaɓe mata tana gamawa Kura za ta yi wurin Dada, kuma ko kashe ta za a yi ba za ta dawo gidan ba. Cikin sanɗa take tafiya har ta shiga falon babu motsin kowa daga can ɗakin Mami ta fara jiyo muryarta sama-sama da alama waya take yi. Ta matsa a hankali da niyyar ta buɗe ƙofar ta zura mata ƙadangaren ta ji Mami na faɗin.

"Haba Hajiya Karima kin gan ni fa na tuɓe kaya yanzu haka wanka zan shiga, don Allah ku jira ni. Kin san yadda nake bala'in son haɗuwa da matar DC kuwa? Kin san fa duk in da harkar manya take ba ma sanya da ita." Uwani ta saki murmushi da ta tuna tsiyar da za ta ƙulla wa Mami. A kan kunnen ta Mami ta gama wayar ta faɗa banɗaki, sai da ta tabbatar da wankan Mami ya fara nisa sannan ta buɗe ƙofar ɗakin a hankali ta shiga. Ƙofar banɗakin ta nufa sai ta fara murɗa ƙofar da sauri-sauri, daga ciki Mami na saɓa sabulu a fuska ta ji ana murɗa ƙofar. Mamaki ne ya kamata don ta san su Shukra ba sa nan, kuma ko suna nan ba za su buɗe mata banɗaki tana ciki ba.

"Waye a nan?"Mami ta tambaya a hassale.
Uwani ta kausashe murya ta ce, "Sarki ne ya zo da kansa ba aike ba." Da mamaki Mami ta furta. "Sarki wane iri? Kai waye da har za ka tsallake ko ina ka shigo ɗakin matar aure, kuma har ka nemi buɗe ni a banɗaki."

"Sarautar ce haka! Kuma na aure ki daga yau, tun da na samu sukunin mai gidanki ba ya nan. Dama tun ranar da aka yi maganar auren ɗanki Jafar ni ma na kai kuɗin aurenki, yanzu haka kuma na biyo ki ne domin na ɓarje amarci." Uwani ta ƙarasa maganar dariya na son ƙwace mata. A hargitse Mami ta ce.

"Kai malam wai waye kai ne ma? Ba ka da hankali za ka ce ka na son matar aure?" Uwani ta sake kausashe murya ta ce.

"Ni dai babban burina ki ba ni haɗin kai domin ni matashin saurayi ne dal, soyayya ce kawai ta sa na tsaya a kanki. Amma kada ki yi mamakin kasancewa ta wata halitar da ba irin taki ba." Uwani na gama faɗar haka ta buɗe ƙofar a hankali ta wurgar wa Mami Jangwalagwadan sannan ta janyo ƙofar da ƙarfi ta rufe, da yake da key a jikin ƙofar nan take Uwani ta murza key ɗin ta cire shi ta ajiye a gefen gadon Mami.

Lokacin da Mami ta ji abu ya sauka a kafaɗarta da sauri ta hau kiciniyar wanke kumfar fuskarta. Hannunta ta kai ta shafo kafaɗarta bayan ta wanke fuskarta, wani irin ƙadabarbar ta ji take jikinta ya hau karkarwa. Ta yi ta maza ta yi wurgi da shi, sai a lokacin idonta ya sauka akan tafkeken ƙadangaren. Da yake shi ma ya galabaita nan take suka fara 'yar tsere da Mami a banɗaki, duk yadda Mami ta so buɗe ƙofar sai ta gagara. Cikin Kuka Mami ta ce.
"Wayyo Allah Lado, Jafar kana ina ka kawo mini ɗauki." Uwani ta gimtse dariyarta, ta sake matsa wa jikin ƙofar ta ce. "A yanzu babu mai iya taimakonki domin amarci na zo ci. Kuma daga yanzu ni fa zan dinga rikiɗa har zuwa surar mutane ina kawo miki ziyara." Uwani na gama faɗar haka ta sulale ta fice daga ɗakin, cikin sauri ta zagaya ta wuce sashenta.

Jafar ta gani ya yi ɗaiɗai a falo yana bacci, da alama kallo yake yi bacci ya yi awon gaba da shi don ga remote nan a gefensa. A hankali ta wuce cikin ɗakinta ta faɗa kan gado tana sauke ajiyar zuciya, ƙugin da cikinta ke yi ne ya sake ankarar da ita yunwar da ke cin ta. Kitchen ta faɗa ta fara duba tukwane, ta ci karo da guntuwar Indomie da Jafar ya ci ya rage. Tukunyar ta ɗauko ya zuba shayi ta koma falo ta zauna ta ci, sannan ta buɗe bokitin dubulan ɗin ta ta ɗebo alkaki da dubulan na gararta ta baje a ƙasa ta ci gaba da loda wa cikinta. Tana cikin ci suka ji bugun ƙofa kamar za a ɓalle ta.

"Ranka ya daɗe! Ranka ya daɗe akwai abin da yake faruwa a sashen Hajiya." Jafar shi da Uwani kusan lokaci ɗaya suka miƙe a zabure, da sauri Jafar ya buɗe ƙofar ya ga Lado da Baba tsoho, a ɗimauce ya ce. "Lafiya Lado?"

"Ranka ya daɗe bugun ƙofa nake ji a sashen hajiya kuma idan aka buga bayan wani lokaci sai na ji shiru, kuma sama-sama nake jiyo muryar Hajiya kamar tana kuka." Jafar tun bai gama jin kalaman Lado ba shi da Uwani suka zuba a guje suka yi sashe ta, ganin haka ya sa Lado da Baba tsoho suka rufa musu baya.

Jafar na zuwa ɗakin Mami ya nufa, abin mamakin komai tsaf yake babu wata hayaniyar tashin hankali. Wani rin numfarfashi suka ji a cikin banɗaki, da sauri Jafar ya dinga buga ƙofar yana kiran sunanta. Bugun da Jafar yake yi ne ya sake farfaɗo da Mami daga suman da ta yi, wanda ta yi suma a cikin banɗakin babu adadi.

"Jafar! Wayyo Jafar ka shigo ka taimaka mini, wallahi ƙadangare ne zai haike mini." Mami ta yi maganar a galabaice don saboda wahalar da ta sha ko motsin kirki ba ta yi.
Da ƙarfi Jafar ya dinga buga ƙofar amma a ƙame take ƙyam ta ƙi buɗuwa, "Ranka shi daɗe wannan ba shi ne mabuɗin na?" Lado ya ɗago key ɗin da ke kan gadon Mami. Da sauri Jafar ya karɓa ya buɗe yana buɗewa ƙadangaren ya yo bakin ƙofar a guje, ganin haka ya sa daga Lado har Jafar suka ɗiba a guje. Sai da suka ga ya shige ƙarƙashin gado sannan suka fara leƙowa, Mami da rarrafe da jan ciki ta fara tahowa Baba tsoho ya tunkari ƙofar banɗakin da niyyar taimaka mata, yana leƙawa ya hangi Mami tumɓur da sauri ya juya da baya yana faɗin.

"Kai a'uzubillahi wannan lamari da muni yake."
Baba tsoho ya nufi bakin ƙofa su Jafar na ganin yadda ya dawo jiki a sanyaye Lado ya je zai shiga da sauri Baba tsoho ya girgiza kai ya furta. "Ummm-ummm ku dawo Lado abin babu kyawun gani."

Lado na zuwa ya ci karo da Mami na jan ciki, Mami da take a yunwace da neman taimako ta fara jan ƙafar wandon Lado tana faɗin. "Ku fitar da ni daga gidan, idan ba haka ba za su kashe ni." Ganin yanayin da Mami take ciki ya sa Lado ya fisge a guje yana faɗin. "Subhanallahi wannan lamarin ya munana Baba tsoho me ya sa ba ka buɗan aiki ba? Haka kawai zan ƙone idanuna." Jafar ya nufi wurin banɗakin, kamar haɗin baki Lado da Baba tsoho suka yi wata uwar sufa suka dafe kafaɗun Jafar suna faɗin. "Wallahi al'amarin akwai muni Jafar kada ka shiga." A ƙufule Jafar ya fisge ya ce. "Ni da uwata ne za ku yi mini iyaka? Duk halin da take ciki ni ba zan guje ta." Jafar ya fisge da ƙarfi ya tunkari wurin da Mami take.

Cikin hukunci Ubangiji gobe ne za mu kammala Free pages ɗinmu, idan kina buƙatar ci gaba za ki biya 500 ta wannan Acc Aisha Adam 3090957579 First bank sai shaidar ta wannan lambar 07062062624

#Ummou Aslam Bint Adam🌚
[30/06, 19:35] Ameerah Adam🌚: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.


SHAFI NA SHA UKU

Jin yadda jikin Uwani yake karkarwa ya sa Jafar ya kwantar da ita a jikinsa ya sa hannu ya fara bubbuga bayanta, nan take idanunsa suka yi jawur saboda ɓacin rai. Ya dubi mutumin murya a dashe ya furta.
"Ka san wa ka taɓa kuwa? Ka san wanne irin kuskure kake yunƙurin aikatawa. Wallahi sai na nuna maka bakin rijiya ba wurin wasan makaho ba ne." Jafar ya ƙarasa maganar yana yunƙurin cire Uwani daga jikinsa, cikin kuka Uwani ta furta. "Tsoro nake ji Ya Jafar don Allah kada ka sake tafiya."

Ajiyar zuciya Jafar ya sauke ya riƙe hannunta suka fara tafiya rai a ɓace, ganin haka ya sa Alhajin ya zuba a guje ya faɗa ɗakinsa ya datse ƙofa. Ɗakinsu suka wuce sai da Jafar ya sa key ya buɗe suka shiga, ya kai ta kan kujera ya zaunar da ita sannan ya ce. "Ki jira ji yanzu zan dawo." Fuska da hawaye Uwani ta furta.

"Ya Jafar kada ka tafi ya shigo mini."
Sunkuyawa ya yi daidai fuskarta ya ɗan hura mata iska ya furta.
"Ba abin da zai faru da ke yanzu zan dawo kin ji." A hankali Uwani ta gyaɗa masa kai sannan ya fice.

Ɗakin Alhajin ya koma ya yi bugun duniya ya ƙi buɗewa, shi kuwa Alhaji tumbin kuɗi jin ana buga ƙofar ɗakin abokinsa da ƙarfi, ya sa ya ƙara wa tashi ƙofar key sannan ya wuce banɗaki a guje jiki na rawa ya ɓuya.

Ganin ba shi da niyyar buɗewa ya sa Jafar ya zaro waya ya danna lambar DPO ɗin unguwar Zoo road, da yake abokinsa ne. Nan take ya sanar da shi abin da ya faru tsakanin Uwani da Alhajin. Sannan Jafar ya sauka ƙasa ya sanar da ma'aikatan reception abin da yake faruwa da kuma ɗakin da Alhajin yake ciki. Wata mata da ke gefe nan take ta furta.

"Kai malam Allah Ya yi maka albarka. Wallahi ni ma jiya da dare na ɗan fita unguwa na dawo haka wani ya dinga mini ɗan kira, da na shiga ɗaki har buga mini ƙofa ya yi ƙila ma shi ne." Jafar ya furzar da iska mai zafi ya ce. "Daga yau ai ba zai ƙara ba."

"A toh ai wasu mutanen gani suke idan suka ga mutum ya kama hotel kowa ma ɗan iska ne, Allah Ya kyauta."

Ba a ɗauki lokaci ba sai ga motar 'yan sanda ta ƙaraso, lokacin da suka je bakin ƙofar Alhaji sai da ƙyar ya buɗe musu ƙofa. Har ƙasa ya tsugunna yana ba wa Jafar haƙuri amma fir ya ƙi sauraronsa, yaran D.P.O bayan sun saka masa ankwa Jafar ya ce su wuce da shi zai zo daga baya.

A wurin da ya bar Uwani a nan ya koma ya same ta, fuskarta ta kumbura saboda kuka. Tana ganinsa ta yi zumbur! Ta miƙe tsaye. Bai kula ta ba ya koma can gefen gado ya zauna ya dafe kansa, wani irin ɗaci yake ji a maƙoshinsa ya ɗago murya can ƙasa ya ce.

"Ya aka yi mutumin nan ya biyo ki ke da na bar ki a ɗaki?" Zuciyar Uwani ɗaya ta fara masa jawabi.
"Ni fa kasan ƙafata ba ta saba zaman wuri ɗaya ba, gajiya na yi da zama shi ne na fita can ƙasa na sha iska. Da na dawo sai na rasa ɗakin nan, bisa tsautsayi na faɗa ɗakin wani ɗan iska..." Uwani ta kwashe komai ta gaya masa amma ba ta gaya masa irin azabar da ta yi wa Alhaji tumbin kuɗi ba, ta dai ce masa Allah ne ya ƙwato ta bayan ta fito wannan Alhajin ya biyo ta.

Tass! tass! Jafar ya sauke wa Uwani wasu tagwayen mari biyu a fuska, cikin ɓacin rai ya furta. "Uban waye ya ce ki fita? Ba ki da hankali za ki fita da waɗannan kayan?" Ganin yadda Jafar ya hargitse mata lokaci ya sa nan take jikinta ya fara karkarwa, ya rufe ta da faɗa tamkar zai rife ta da duka daga ƙarshe ya faɗa toilet ya bar ta a zaune. Bai jima ba ya fito har lokacin ransa a ɓace yake ya furta.

"Ki shiga ki yi wanka za mu wuce gida yanzu." Zani uwani ta ɗauka ta faɗa ban ɗaki kafin ta fito har Jafar ya gama shiryawa, gefe da gefen fuskar Uwani har ya ɗan kumbura don har lokacin ba ta daina hawaye ba.

Jafar na zaune a gefen gado ya hango Uwani ta fito don ita ta manta ko hula ma ba ta saka ba, a razane yake bin ta da kallo baki sake. Ganin irin kallon da Jafar yake bin ta da shi ya sa Uwata ta sha jinin jikinta, tana sake tunkaro shi Jafar ya zabura a guje ya nufi ƙofa yana faɗin.
"Wayyo Allah! Jama'a ku taimaka mini sun biyo ni nan ma!" Da yake ya manta ya datse ƙofar haka ya yi ta murɗawa ta ƙi buɗuwa. Cikin rashin fahimta Uwani ta ɗan waiga ta ce.
"Wai ya Jafar me yake faruwa ne?" Laƙwas Jafar ya yi ya zauna a ƙasa kamar mutum-mutumi yana kare mata kallon, tamkar ya ga sabuwar hallita. Uwani ta shiga goge kanta da towel ko a jikinta ta ce. "Malam ka fita zan shirya."

Har lokacin Jafar mamakin Uwani yake, ya shiga tariyo abin da ya dinga faruwa a cikin dare. Uwani ta fahimci sarai in da Jafar ya dosa, ta fito da kayan da za ta saka ta sake furta. "Don Allah ka fita zan shirya."

"Uwani ina gashinki?" Cikin halin ko in kula ta ce. "Dada ta aske mini tun rannan."

Miƙewa ya yi ya tako gabanta sannan ya furta. "Wato iskanci ne ya sa kika dinga tsora ta ni ko? Wallahi za ki shiga hannuna da ni kike zancen." Take dariyar da Uwani ke gimtsewa ta suɓuce mata. Jafar ya saki wani malalacin murmushin mugunta yana ayyana irin azabar da zai yi mata cikin ruwan sanyi ba tare da Daddy ya gane ba. Daga haka Jafar ya fice daga ɗakin, Uwani ta saka kayanta sannan ta haɗa ragowar kayanta da ke warwatse ta saka a jaka.

Ba su ɗauki lokaci ba suka shirya suka fito Jafar ya ƙarasa gaban ma'aikatan da ke reception ya biya duk abin da ya suka kashe, sannan ya yi musu sallama suka fita da yake akwai Manajan wurin da shi a ka kai Alhaji can police station. Domin a cewar Manajan Alhajin na ƙarƙashin kulawarsu dole ne su san halin da yake ciki.

Lokacin da su Uwani suka ƙarasa gida mommy ta rako ƙawarta Hajiya Binta bakin gate, ganin su Uwani ya sa Mami ta yi turus tana faɗin.

"Ya aka yi Jafar?" Jafar ya ɗan sosai, sannan ya gaida Hajiya Binta da ke bin sa da kallon tuhuma.

"Ƙawata wai kar dai raɗe-raɗin da nake ji a kan auren Jafar haka ne?" Hajiya Binta ta tambaya tana satar kallon Uwani. Ras! Gaban Mami ya faɗi, ta ɗan basar tana ƙirƙiro murmushin yaƙe ta ce. "Haba Hajiya Binta kina ganin akwai yarinyar da Jafar zai aura a duniyar nan bayan Safna? Ai me aiki ce ya taho mini da ita daga Lagos, a bakin gada take kwana shi ne ta roƙe shi Allah-Annabi wai ta dinga yi masa aiki. Da ya sanar da ni na ce idan zai taho ya kawo mini ita, kin san ɗa na kowa ne ƙawata." Cikin gamsuwa Hajiya Binta ta bi Uwani da wulaƙantaccen kallo ta furta.

"Ban da taɓarɓarewar zamani yanzu wannan yarinyar har ta isa kwanan gada, mtsww Allah Ya sawaƙe." Mami ta furta. "Amin dai, yo yaran da maza ke ba su ɗari biyar suna sa su a ɗaki ina za ki yi mamaki?" Kalaman Mami da ƙarshe da ta jefi Uwani da su ba ƙaramin zafi suka yi masa ba, don haka ko sallama bai yi wa Hajiya Binta ba ya wuce. Ita kanta Uwani kusan daskarewa ta yi a wurin jin irin munanan kalaman da Mami ta jefe ta da shi, tunanin da ta zurfafa ciki ne ya sa Jafar ya wuce ba tare da ta sani ba. A ɗan tsawace Mami ta ce.
"Tsawar me kike yi a gabanmu ne?" Babu yadda ta iya haka Uwani ta ja jaka jiki a sanyaye ta wuce ciki, kai tsaye sashensu ta shiga idanunta cike da ƙwallah.

Sanin Daddy ba ya gidan ya sa Mami kai tsaye ta wuce sashen su Jafar, a falo ta same su duka ta dubi Jafar ta ce.
"Wai fasa tafiyar ka yi ne Jafar?" Bai ɗago ya kalle ya ba ya furta, "Eh Mami." Jim ta yi tana nazartarsa ta furta.

"To haka za ka zauna ana tsorata ka har a sabauta mini kai?" Jafar ya furta. "Ai na biya ta Islama Islamic Center na karɓo magani, kuma ya ce mini za a dace In shaa Allah." Jafar shi kansa ya yi mamaki yadda ya tsara wa Mami wannan jawabin, Mami ta wurga wa Uwani mugun kallo ta ce.
"Wuce mu je akwai aikin da za ki yi mini." Babu musu Uwani ta bi bayan Mami, Jafar ya kwanta a kan doguwar kujewa. Haka kawai ya ji yana kewar Safna, don haka ya zaro waya ya kira ta suka fara hira.

Mami na shiga sashensu ta haɗo wa Uwani wanki duk da a lokacin magriba ta fara kawo kai, bayan gida ta zuba mata wankin ta yadda koda an yi a arashi Daddy ya dawo ba zai ganta ba ballanta ya yi mata faɗa. Kuma dama ta san ba ya gari, don haka za ta ci karenta babu babbaka akan Uwanin.
Cikin wankin da Mami ta haɗo wa Uwani har da labulaye da zannuwan gado, tun Uwani na wankin cikin daɗin rai har ta fara galabaita tun da ko a wurin Dada ba ita take yin wankin kayanta ba. Lokacin da aka kira sallar magriba Uwani wucewa ta yi sashenta don ya gabatar da sallah, tafiyarta babu jimawa Mami ta zagaya ta ga wurin wayam. Sai tsirarin kayan da ta shanya ga waɗansu nan a cikin ruwa.

Uwani na zaune tana zaman tahiya Jafar ya shiga ya zaune yana kallonta, a yadda ya lura da Uwani duk hatsabibanci da ƙiriniyarta ba ta wasa da sallah ko kaɗan. Hakan ba ƙaramin birge shi yake ba, yana nan zaune Mami ta shigo ko shi ba ta yi wa magana ba ta rufe Uwani da duka. Ganin dukan da take wa Uwani ba zai ƙare ba ya sa Jafar ya yi saurin shan gaban ta.

"Lafiya kuwa Mami? Me ta yi miki haka?" Jafar ya furta hankali a tashe.

"Lallai Jafar wannan abar har kake tarewa?" Mami ta faɗa tana sauke numfashi.

Ban da kuka babu abin da Uwani take yi, ga gefen bakinta ya fashe jini na ɗiga. Saboda yadda ta galabaita kukan da take yi ko fita ba ya yi, Mami ta sake zuba mata ranƙwashi a ka tana shirin yin magana Jafar ya ce. "Mami wai me ta yi miki?"

"Wanki na saka ta don iskanci za ta zube mini ta zo ta saka miji a gaba, idan uwarki ce ta saka

Please Login or Register in order to submit comment