Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki za ki ajiye mata." Mami ta yi maganar tana dungurin Uwani, cikin kuka Uwani ta ce. "Sallah aka kira shi ne na zo na yi..." Da sauri Mami ta sake doke Uwani nan take bakinta ya sake fashewa.

"Haba Mami, ina ce Haladu ne yake yin wanki. Kuma sallah fa ta ce ta zo..." Tas! Mami ta ɗauke Jafar da mari, ba ta tanka masa ba ta figi hijabin Uwani ta fara janta a ƙasa, ba shiri Uwani ta miƙe ta bi Mami. Saboda ɓacin rai tun ba su gama fita ba Jafar ya gegare su ya fice daga gidan zuciyarsa na suya.

"Iyeee Allah Jafar watsa mini ƙasa za ka yi a ido yaushe har ka san zafin mace. Wallahi dole kai ma na ɗauki mataki a kanka." Mami ta yi maganar a ɗan tsorace don ta yi tsammanin ko wuta za ta jefa Uwani sai dai Jafar ya taya ta ba dai ya hana ba.

A cikin duhu ga sauro haka Uwani ta wanke ragowar kayan da ba ta ƙarasa ba, kanta ban da ciwo babu abin da yake yi. Bayan ta gama ne ta nufi sashen Mami har ƙasa ta zube ta furta. "Na gama wankin." A yamutse Mami ta dube ta tana shirin sallamarta Shukra ta shiga ɗakin tana taunar cingam ta ce. "Ke zan saka ki aiki yanzu saura ki yi mini hauka." Uwani ta ɗaga kai a galabaice ta amsa wa Shukra. Auta da ke zaune a gefe duk sai ta ji babu daɗi, tana son ta yi magana amma tana tsoron faɗan Mami.

"Kina ji Shukra na yi miki magana ba za ki iya amsawa ba?" Mami ta yi maganar tana haurin Uwani. Sai da ta goge ƙwallar idonta sannan ta rarrafa gaban Shukra ta tsugunna.

"Ga Salim nan ya faka motarsa a cikin gate, za ki je ki wanke masa kuma wallahi idan ba ta wanku ba sai kin sake." Da sauri Auta ta furta. "Aunty Shukra wankin mota fa?"

Shukra ta sake shan kunu ta ce, "Waya na yi da shi zai kai wankin mota ya ce ba zai samu zuwa yau ba, so don haka na ce ya zo gida za a wanke masa saboda ina son magana da shi." Cikin tausaya Auta ta ce, "To shi kenan zan ta ya ki Uwani..."

"Waye ya gayyace ki? Uwar iyayi da kankanba?" Mami ta katse Auta.

Shukra ce ta yi gaba Uwani ta bi bayanta a lokacin zazzaɓi har ya fara rufe ta, lokacin da suka ƙarasa Salim na cikin mota. Da ya hango su ne ya fito yana sakarwa Shukra murmushi.

"You are welcome dear." Shukra ta furta tana fari da ido.

"Beb an ya zan iya jiran sati ukun nan masu zuwa kuwa? Kin ga yadda kika yi kyau." Salim ya furta cikin shauƙin soyayya, Shukra ba ƙaramin daɗi ta ji ba kin kissa ta ce.

"Well mu je mu zauna, ga 'yar aikin Mami za ta wanke maka mota."
"Za ta iya kuwa Baby? Na ga mata ba sa wankin mota." Salim ya faɗa yana bin Uwani da ke rakaɓe a gefe. Shukra ta dubi Uwani a tsawace ta ce. "Ke ba ki iya gaisuwa ba ne?" Jikin Uwani na rawa ta tsugunna ta gaishe da Salim, sannan Shukra ta ɗan yi murmushi ta furta.

"Ai in gaya maka daga motar Daddy har ta ya Jafar ita take wankewa za ka sha mamaki." Shukra da Salim suka wuce wurin wasu fararen kujeru, daga wurin da suke zauna suna iya hango Uwani da duk abin da take yi.

Sai da ta goge ƙwallar idonta sannan ta ɗauki bokiti ta fara ɗebo ruwa, da yake wurin ɗiban ruwan yana da ɗan nisa da wurin wankin motar a galabaice ta fara wankin motar har ta gama.

Gaban Shukra Uwani ta je ta tsaya ta ce, "Na gama wankewa." Shukra ta bi ta da harara sannan ta ce.
"Matso nan."
Ba musu Uwani ta matsa gaban Shukra, da ƙarfin tsiya ta fisgo Uwani har sai da ta bugu da ɗan ƙaramin table ɗin da ke gabansu ta ce.
"Don ubanki ke ba ki da ladabi ba za ki iya tsugunnawa ba?" Shukra ta ƙarasa maganar tana zuba wa Uwani ranƙwashi.

"Haba Beb da kin ƙyale ta kin san irin yaran nan ba wani tarbiyya suke samu ba, so don sun yi haka ni ba zan yi mamaki ba." Salim ya faɗa a ɗan ƙyamace yana duban Uwani da ta gama jiƙe wa da ruwa sharkaf.

"Dallah tashi ki ba ni wuri kina tafe da baƙi kamar na zunubi." Dariya sosai Salim ya yi jin abin da Shukra ta faɗa ya furta. "Wai yaushe kika koyi masifa ne love?"

"Haba ka rabu da ni na tsani yarinyar nan wallahi." Uwani na laɓe a ta bayan fulawiyin da ke zagaye da harabar gidan, takaici ya mamaye zuciyarta. Wani tunani ne ya faɗo mata don haka da sauri ta zagaya can bayan gidan, ta ɗebo irin manyan bokitan fentin nan guda biyu waɗanda ta gama wanki da su. Sai da ta yagi wata igiya ta haɗa hannuwansu ta ɗaure, sannan ta saki murmushin mugunta. Cikin sanɗa ta fara tafiya ta cikin fulawoyi, a daidai bayan su Shukra ta tsaya ta ji Salim yana faɗin.

"Haba ke dai Baby ba kya mantuwa, wannan fa mahaukacin ma shammatata kawai ya yi amma yadda nake ƙaunarki akwai abin da zan ga zai cutar da ke na gudu ban taimaki rayuwata ba, ke ce fa rayuwata ke ni fa idan za ki rayu da farinciki zan iya sadaukar da komai ciki kuwa har da numfashin da nake zuƙa." Shukra ta rangwaɗa kai cikin farinciki, tana shirin ba shi amsa Uwani ta saki murmushi duk da zazzaɓin da ke jikinta. Sai da ta daidaita saitin kansu sannan ta ɗaga bokitan fentin hannunta, ta kifa musu a kansu ta saka iya ƙarfinta ta danne saman ta yadda ba za su iya fisgewa ba. Salim da abin ya haɗe masa biyu ga zafin hula ga na bokiti ya ware murya cikin ihu ya ce. "Wayyo Allah wuyana!"

"Wayyo kaina, Baby kana ina!" Shukra ta faɗa a ɗimauce. Daga Salim har ita sai ɗaga hannuwa suke cikin neman taimako. Sai da Uwani ta ga sun fara galabaita sannan ta fisgo hannun bokitin ta baya, da yake ƙafafuwansu na ƙasan table ɗin da ke gabansu faɗuwar da za su yi ta baya sai suka taho da table ɗin da ƙafafuwansu. Uwani na ganin za su kai ƙasa ta yi saurin matsawa a guje, sai ji kake rugugum! kacacar kofuna da ruwan jarkar duka sun watso kansu. Ga bokiti ya sarƙafe su ga kuma ƙafafuwasu sarƙafe a cikin table, Uwani ta laɓe a cikin shukoki tana dariya ƙasa-ƙasa don duk ƙwaƙwar mutum ba zai gano da mutum ɓoye a wurin ba.

Da ƙyar Salim ya samu ya zaro ƙafarsa daga cikin Table, ya tashi zai zuba a guje Uwani da ke laɓe ta sake fisgo shi da yake igiyar tana hannunta. Daɓar Salim ya koma ya faɗi hankali a tashe ya ce. "Jama'a a taimaka mana wallahi jana ake yi."

Shukra ce ta yunƙura ta tashi a guje saboda tashin hankali ko yunƙurin cire bokitin ba ta yi ba, ita da Salim suka zuba a guje a daidai lokacin Jafar ya shigo harabar gidan. Turus ya yi ya ɗan fara ja da baya ganin ƙafafuwan mace da namiji suna tafe da bokiti a kai, da yake ba sa ganin gabansu yana ganin sun tunkaro shi ya zube takalmansa shi ma ya shige a guje yana ihun. "Wayyo Allah! Lado kana ina?" Jin ihun Jafar ya sake ruɗa su Salim, a wannan lokacin Lado ya zagayo da buta a hannu shi ma turus ya yi yana kallon ikon Allah. Da ƙyar Salim ya samu ya cire bokitin kansa, hular ta faɗi can gefe. Dama takalminsa na cikin ƙasan table ya jima da fita, iya ƙarfinsa ya tattara ya fita a guje yana faɗin, "Jama'a ku duba mini kaina idan yana gangar jikina." Sai a lokacin Lado ya gane shi, ya bi bayansa yana faɗin.

"Alhaji ka bar motarka." Lado na ƙarasawa bakin gate ko ƙurar Salim bai gani ba sai agogonsa da links ɗin hannun rigarsa da suka zube a wurin.

Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki turo ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 idan littafi ya kammala za ki turo 800
Free pgs ɗinmu ya kusa ƙarewa🫠

#Ummou Aslam Bint Adam🌚
[30/06, 19:35] Ameerah Adam🌚: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.

SHAFI NA SHA BIYAR

*BOJUWA HERBAL'S & SCENTS*
*Suna kawo Saiwowin da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.*
*Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah*
*Saiwowin tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru*
*Saiwowin matsi gangariya*
*Original gadalin mata*
*Ƴaƴan gadali na asali*
*Original gumba*
*Tsumin Saiwowi*
*Tsumin kwakwa da Dabino*
*Igiyar alkairi*
*Zumar goran tula*
*Hakkin daka na musamman na asali*
*Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*.
*Akwai bridal package*
*Mai jego package*
*Ƴar gata package*.
*Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.*
*A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne*
*Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi*
*08032773332*
*Iyah Basiru na gaisuwa*😅

Jafar na shiga da ya ga a halin da Mami take ciki turus ya yi, da sauri ya juya cikin damuwa ya dubi Uwani ya ce. "Maza ki shirya ta za mu wuce asibiti."

Uwani da ke gimtse dariyarta ta wuce sumi-sumi kamar sabuwar munafuka ta ƙarasa wurin Mami da ke sharɓe a ƙasa.
Baba tsoho shi da Lado dama tuni suka fito harabar gidan, suna nan tsaye Jafar ya fito abin duniya ya dame shi.
"Kai Jafaru, wai ya aka yi ƙadangare ya shiga har banɗakin mahaifiyarka? Ko dai ture aka yi mata?" Jiki a sanyaye Jafar ya ce, "Wallahi Baba tsoho ban da masaniya, ka na gani dai kune kuka kira ni ina ɗaki." Daga haka gabaɗaya suka yi jigum-jigum.

Abin ka da mai ƙiba Uwani da ta ɗago Mami sai dai ka ji ta sake komawa sharaf, kuma har lokacin idanun Mami a rufe suke. Da ƙyar Uwani ta samu ta ja Mami a ƙasa kamar rago, ta ƙarasa da ita bakin gado tana zaunar da ita a kai ta sake tafiya sharaf, kayan da ta gani a gefe wanda Mami ta ɗauko za ta sa su ta fara dubawa. Rigar maman Mami ta ɗauko ai kuwa Uwani tana ɗaga wa ta faɗi a wurin tana ƙyaƙyata dariya saboda girmanta, sai da ta yi mai isarta sannan ta miƙe ta fara kiciniyar saka wa Mami.
Da ƙyar Uwani ta samu ta shirya Mami sannan ta leƙa waje ta kira Jafar, yana zuwa nan take ya kama Mami ita ma Uwani ta kama ta suka fita ita. A kujerar baya suka saka Mami, Jafar ya kunna motarsa suka wuce asibiti. Suna zuwa asibiti da sauri aka karɓi Mami aka shiga da ita, aka fara ba ta agajin gaggawa. Sai da Jafar ya ga Mami ta samu bacci sannan ya samu sukunin kiran Daddy ya sanar da shi halin da ake ciki, a nan take yake sanar da shi yana hanyarsa ta dawowa.

Lokacin da Mami ta farka gabaɗaya iyalanta na wurin, Daddy ne ya matsa gaban gadon ya fara yi mata sannu. Da wani irin kallo take bin sa ta yunƙura ta cukumo wuyan rigarsa a zabure tana faɗin.
"Wallahi ba zan aure ka ba, ni ina da aure har da 'ya'yana!" Da sauri Daddy ya riƙo ta, Mami ta ɗago kai tana ƙare masa kallo sai gani suka yi Mami ta sake tafiya luuuu a sume. Har rige-rigen fita kiran Likita suke yi, babu jimawa Dr Nura ya shiga cikin shigarsa ta likitoci. Sai da ya gama jin bayaninsu sannan ya ce gabaɗaya su fita, don yana son ba ta kulawa babu buƙatar hayaniya. Daddy ya so zama don ciwon na Mami ba ƙaramin tsoro ya ba shi ba amma Dr ya ce ya fita.

Wata allura ya yi wa Mami ba ta fi minti ɗaya ba ta sake farfaɗowa, tana daga kwance ta ga Dr Nura tsaye a kanta cikin fararen kaya ga farin gilas maƙale a idonsa.

"Wato wannan karon rikiɗe mini ka yi zuwa wannan surar kenan? Wannan fa idan ba da gaske na yi na ƙwaci kaina ba sai ya illata ni ya cuci iyalina." Duk waɗannan maganganun Mami na yin su a cikin zuciyarta ne, ta dai kafe Dr Nura da kallo ko ƙiftawa ba ta yi. Ta fara motsa baki a hankali tana biya Ayatulkursiyyu.

"Sannu Hajiya! Yanzu yaya kike jin jikin na ki?" Dr Nura ya tambaye ta yana gyara tsayuwarsa. A hankali ta yunƙura ta tashi zaune tana ɗan dafe kanta, cikin shammata Mami ta suri dogon ƙarfen nan da ake maƙala ledar ƙarin ruwa a jiki ta shiga zungura masa tana kwaɗa masa. Idan Mami ta karanta Ayatulkursiyyu ta tofa masa sai ta ɗaga ƙarfen ta ba shi ƙwal.

Hankali a tashe Dr Nura ya shige can kusurwar ɗakin yana faɗin.
"Help! Help! Help!" Mami ta sake zungura masa ƙarfen tana faɗin.

"Wato don ubanka har surar Nasara kake rikiɗewa ai wallahi yau ko ni ko kai." Dr Nura ganin neman agajin da yake yi da harshen turanci ba zai kai shi ba, ya sa ya taƙarƙare cikin ihun tashin hankali ya ce. "Wayyo Allah! Jama'a Patient ɗin nan za ta halaka ni."

Su Daddy na daga waje suka jiyo ihun Dr Nura, da gudu suka taho za su buɗe ƙofar, sai dai da yake Mami na jingine da ƙofar tana jin alamun za a buɗe ta sake danna ƙofar da ƙarfi tana zungurin Dr. Ganin Mami na niyyar illata shi ya sa ya faɗa ƙarƙashin gadon asibitin, da ƙyar su Daddy suka turo ƙofar suna ganin ta da ƙarfen suka shiga kallon-kallo suma suna ja da baya. Daddy ne ya murɗe hannun Mami ya karɓe ƙarfen ya ajiye, sororo ta yi ta fara kallonsu ɗaya bayan ɗaya sannan ta ce.

"Daddyn yara da gaske kune? Ina ne nan?"

Kafin Daddy ya ba ta amsa tuni Dr Nura ya yi wata irin sufa irin ta jaruman indiya ya fice daga ɗakin, glass da takalmansa kusan lokaci ɗaya suka yi tsalle sama suka zube a tsakar ɗakin sai dai hakan bai sa ya tsaya ko waige ba ballana ya ɗebi abin sa.

Kan gado Daddy ya zaunar da ita yana yi mata sannu, sai ji suka yi ta fashe da kuka tana faɗin. "Daddyn yara ni dai daga nan ka wuce Kura da ni, har abada ba zan sake kwana a gidan can ba." Kamar ƙaramar yarinya Daddy ya shiga lallashinta sai da ta yi shiru sannan ya tambaye ta ainihin abin da ya faru.

Tiryan-tiryan Mami ta sanar da shi abin da ta ji da kuma shigowar ƙadangaren, don ita ko shigar su Jafar ba ta sani ba saboda ta yi suma ya fi bakwai a cikin banɗakin. A yanzu shi kansa Daddy ya fara yarda da cewar gidan ba su kaɗai ba ne, saboda ya sake kwantar mata da hankali ya ce ya amince za su koma can da zama. Uwani na rakuɓe a gefe ta yi zuru tana ƙarewa fuskar Mami kallo, tana mamakin yadda Mami ta zabge ta zuƙe a wuni guda, suna haɗa ido ta doko mata harara ba shiri Uwani ta janye idonta gefe.

Daddy da kansa ya koma kiran likitan da zai sake duba Mami duk da ya lura ciwon ba na asibiti ba ne, da ƙyar ya samu Dr Samira ta je ta duba Mami ta saka mata ƙarin ruwa da allurai bayan wani lokaci aka sallame ta. Su Shukra ko kaɗan ba su so komawa Kura ba don dai babu yadda suka iya ne, ita kuwa Uwani murna fal ciki. Daddy ne ya kwashe su suka ɗebo kayan sakawarsu. Mami kuwa fir ta ƙi yarda ta shiga gidan sai a mota suka bar ta.

Su Shukra sun ɗauki hanyar Kura babu jimawa Salim ya kira ta a kan zai je ya ɗauki motarsa, bai dai gaya mata ba amma a cikin ransa ya ƙissima ba zai sake zuwa gidansu ba har zuwa lokacin da za a ɗaura musu aure.
Adaidaita sahu ne ya sauke shi a ƙofar gidan Daddy, gaban Salim ne ya fara faɗuwa a hankali ya yi ta maza ya ƙarasa jikin gate ɗin ya fara ƙwanƙwasawa. Daga cikin gidan Lado ya furta.

"Waye nan?"

"Lado ni ne." Zuro kai Lado ya yi yana ganin Salim ya washe baki ya ce, "Allah Ya taimake ka, yau kaine da rana tsaka." Salim ya miƙa masa mukullin motarsa ya ce.

"Shiga ka tuƙo motata ka fito mini da ita." Sororo Lado ya yi ya furta. "Ranka ya daɗe ni da ko mashin ban iya tuƙawa ba, ina ni ina tuƙa mota?"

"Lado amma gidan nan ba ku kaɗai ba ne a ciki, ka na gani dai rannan aka so tafiya da mu a bokiti ban da ƙarfin addu'armu da ta iyaye da tuni wani zancen ake ba wannan ba." Lado ya yi jim sannan ya ce.
"Ranka shi daɗe naka ai mai sauƙi ne." To yau dai in faɗa maka tik da ka sani haka ƙadangare ya tarfa Hajiya tumɓur tana wanka. Kai yanzu haka ma suna can hanyar Kura don gabaɗaya Hajiya ta rikice, ban da sha'anin iska ina ka taɓa jin ƙadangare ya auri mutum? Wai ƙadangare ne fa yake ce mata amarci zai sha da ita, ina ka taɓa ganin ƙadangare na magana?To Kai kuwa ma a shekarun Hajiya ban da neman cika wa da imani me take nema a wurin namiji ballantana ƙadangare? To ɗazun nan sun zo ɗiban kaya za su wuce Kura Uwani ta kwashe komai ta faɗa mini." Take cikin Salim ya sake kaɗawa, ganin ya ɗan fara ja da baya Lado ya ce.

"Ni ma fa Baffa nake jira ya zo a yi wacce za a yi, idan har ƙadangare zai auri Hajiya ni waye da ƙangaruwa ba za ta aure ni ba. Haka kawai ina zaune ta murƙushe ni cikin dare babu mai ceton rai." Salim ya zaro ido ciki a tsure ya ci gaba da ja baya. Lado ganin haka ya sa ya ce.

"Ranka shi daɗe ina za ka je ne? Ka shigo ka ɗauki motarka mana." Salim ya zabura a razane ya furta.
"Allah Ya tsare ni wallahi, zan aiko a ɗaukar mini ita daga baya don ita kanta motar kafin na fara hawa sai an yi mata sauka biyar." Daga haka Salim ya juya ko sallama bai yi wa Lado ba yana zuba sauri.

Da zuwan su Mami Kura ba a ɗauki lokaci ba, labarin abin da ya faru da ita ya watsu cikin gidan gabaɗaya. Facalolinta sai zuwa suke duba ta, wanda yawanci zuwan da suke yi da biyu suke yi. Domin masu yi mata dariya a bayan fage sun fi yawa saboda irin habaicin da ta dinga yi musu a lokacin da za su tare. Sai daga baya Dada ta shiga a lokacin yawancin mutane sun watse daga Daddy sai su Jafar, Uwani kuwa dama tun da ta shiga gidan ta yi sashen Dada daga nan ta wuce wurin turken awakinta.

Sannu a hankali jikin Mami yake ƙara samun sauƙi, ganin yadda Mami ta yi laushi ya sa Uwani ta yi tsammanin ko Mami sauya halinta ne. A haka sai da suka shafe kusan kwana goma a cikin gidan, kuma a wannan kwanakin kullin sai Daddy ya sa an yi saukar karatun Alƙur'ani. Wannan saken da Uwani ta samu ya sa hankalinta ya kwanta, ta manta da matsalar Mami gabaɗaya. Don tun da suka koma Kura sau biyu ta shiga duba Mami, kuma ba wata kyakkyawar fuska take samu ba.

Su Mami ba su suka koma gidansu ba sai bai fi saura sati guda bikin Shukra ba, da ƙyar Mami ta yarda ta koma kuma kafin ta koma sai da suka yi musayar ɗaki da Daddy, ita ta koma ɗakin Daddy shi ya koma ɗakinta. A kwalemar fitar da kayan ne aka fitar da Jangwalagwadan da ya shiga ɗakinta, don shi kansa ya galabaita. A lokacin da za su tafi ne Uwani ta saka kuka don cewa ta yi fir ba za ta koma ba, sai da Dada ta lallaɓa ita da Daddy ta amince amma sai cewa ta yi sai dai idan da awakinta za ta koma. Ba musu Daddy ya amince ya ce zai yanki wani wuri a cikin farfajiyar gidan a yi wa awakinta wuri, amma sai bayan bikin su Shukra. Cikin farinciki Uwani ta bi Jafar suka wuce duk da shi ma ba wata fuska take samu a wurinsa ba, amma ba ya zagin ta ko cin zarafin ta.

Shirye-shirye sun fara kankama a wurin su Mami da wurin iyayen Salim, da yake Mami na zirga-zirga sai tsangwama da takurar da take yi wa Uwani ta yi sauƙi. Haka kuma Uwani ta fara gogewa da aikin da suke yi da Inna, don wani lokacin ma idan Inna ta gaya mata yadda za ta sarrafa abu ita take yi.

Tun ana gobe kamun bikin Shukra hankalin Mami yake a tashe sakamakon wayar da suka yi da mahaifiyar Safna, a kan cewar za su zo ranar Juma'a da safe su tafi ranar Lahadi bayan ɗaurin aure. Sakamakon biyo jirgin da za su yi daga Lagos zuwa Kano.
Tun da suka gama wayar gumi yake keto wa Mami. Ganin ta rasa mafita ya sa ta kira Shukra ɗaki.

"Shukra ina tsoron asirinmu ya tonu, ina gudun duk plan ɗin da na shirya ya wargatse. Kin san dai matuƙar Safna da mahaifiyarta suka zo gidan ko yaya ne za su iya fuskantar Jafar na da aure, alhalin ni kuma ban sanar da kowa ba bayan Hajiya Falmata." Shiru Shukra ta yi sannan ta ce.

"Hanya ɗaya ce, mu nemo abin da zai sa Yaya ya sake ta kawai."
"Ta wace hanya kenan?" Shukra ta zuba tagumi tana nazari, da sauri ta dafa Mami ta ce.

"Na samo mafita, kin san me za a yi Mami?" Mami ta girgiza kai da sauri.
"Sata kawai za mu laƙa mata, ba kin ce Daddy ya ba ki ajiyar wasu kuɗi masu yawa ba? To da su za mu yi amfani." Shukra ta yi ƙasa da murya tana tsara wa Mami yadda za su yi, lokaci ɗaya suka saki dariyar samun mafita.

Suna gama tattaunawa Mami ta ɗebo damin kuɗin ta damƙa wa Shukra, Shukra ta ɓoye su a cikin jakarta kai tsaye ta nufi sashen Uwani ita da ƙawarta Fatima. Kuma ko Fatima ba ta san da plan ɗin su Mami ba. Tun da Uwani ta tare sau ɗaya Shukra ta taɓa shiga sai a wannan ranar ta yi na biyu.
Shiru ta ji falon babu kowa, sallama ta rangaɗa daga cikin ɗaki ta ji Uwani ta amsa. Ita ma Uwani dawowarta kenan daga sashen Mami don tun da Dada ta zo kusan wuni guda a cen take yi, idan ta dawo ɓangarenta sai dai ko wani uzurin ne ya dawo da ita. Uwani na fitowa Shukra ta ɗan saki fuska tana murmushi ta ce, "Ki je Mami tana kiranki. Sannan kuma ƙawata Fatima za ta yi Sallar Walha, sashenmu hayaniya ta yi yawa shi ya sa na ce ta zo nan." Uwani sakato ta yi tana mamakin yau rana ɗaya da har Shukra ta sakar mata fuska,

Please Login or Register in order to submit comment