Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

za ta fige maman jikinta, suna nan tsaitsaye ruwan nono ya fara dawo wa Jawahir ta hanci da kunnuwanta. Wannan yanayin da  ta shiga ya sake faɗar da gaban mutanen wurin, cikin masifa Jakadiya ta fara magana. "Wannan wacce irin masifa aka kawo mana saboda Allah, yarinyar tun da aka kawo ku sai faɗar mana da gaba kike yi." Mai gado jiki a sabule ta karɓi Jawahir ta fita zuwa bakin wata bishiya ta zauna cikin sarewa ta fara zubar da ƙwallah. Jawahir ta jima a haka sannan nonon da ke fita daga jikinta ya dakata da zuba, ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ta sake goge mata haɗe da saka ta a baya ta goya ta. A ranar kusan kwanan zaune mai gado ta yi cike da rashin sabo da zaman baƙunta, uwa-uba rashin kyakkayawan makwancin saɓanin wanda suka saɓa kwana a ciki.

  Cikin Dare.

     Wata doguwar hanyar ya bi samɓal yana tafiya wacce babu komai sai dogayan bishiyu, tsawo da girmansu ya haddasa wa wurin duhu mai ban tsoro. Daga bayansa ya ji kamar ana bibiyarsa don haka ya yi saurin waigawa cikin tsoro da tashin hankali, wata baƙar mage mai ratsin fari ya gani tana tafe tana shinshina sawunsa. Tun bai yi wayo ba yake ƙaunar kyanwa don haka ya tsugunna da niyyar kai hannu kanta, da sauri ya ji an fisge shi gefe waɗansu surutai na tashi sama-sama a cikin kunnuwansa. Waigawa ya yi bai sake ganinta ba, ya ci gaba da tafiya. A jikin wata murgujejiyar bishiyar kuka ya hangi wata rantsatstsiyar karaga, "Je ka ƙarasa kan karagarka." Ya ji an furta masa. Wani irin sanyi ya ji yana ratsa shi, jiki a sanyaye ya fara takawa da niyyar hawa kan shimfiɗar da ke ɗauke da karagar, ga mamakinsa sai ji ya yi wannan baƙar magen ta hankaɗa shi gefe ɗaya. Ta ɗora wani mulmulallan abu mai kama da ƙawai a kan karagar, sannan ta fara zagaye karagar cikin ƙasaita. A can ƙasa ya faɗi kansa ya bugu da wani farin dutse take jini ya fara ɗiga, dafa wurin ya yi cikin azaba sai gani ya yi magen ta ƙaraso tana lasar jinin da ke zuba daga goshinsa. Ta fara ɗaga kanta tana da alamar tana son kai wa kansa farmaki wurin da ragowar jinin yake ɗiga. Ganin ta dumfaro shi ya sa ya ci gaba da ja baya zuciyarsa na dakan luguje, ganin haka ya sa magen ta fara wata irin dariya fiƙoƙinta na zubowa ƙasa ɗaya bayan ɗaya. Duk wurin da fiƙar ta faɗa sai ƙasar wurin ta rufta har ta yi tsalle za ta damƙi saman goshinsa. Firgigit Kamalu ya tashi cikin matsanancin tsoro, firgici da tashin hankali. A lokacin dare ya tsala sosai, ban da munsharin mutanen ɗakin da kukan tsuntsaye babu abin da yake tashi. Jin abu na gangaro masa a goshi ya sa ya kai hannunsa ga mamakinsa ya ji ya taɓa abu, da sauri ya yunƙura zuwa wurin aci-balbal ɗin da ke kunne a gefen ɗakin ya haske. Rass! Gabansa ya faɗi, jikinsa ya ɗauki karkarwa kamar mazari.

"Jini!" Ya furta a kiɗime.

Yana shirin komawa ya tashi Baffajo ya sanar da shi abin da faru ya ji an dafa kafaɗarsa.

"Wannan gidan ba irin kowanne gida ba ne, sai ka ɗaura ɗamarar juriya da jajircewa. Gadon gidanku ba a sansu da sarewa ba, ka zama jarumi mara tsoro a haka ne za ka ƙwaci kanka. Ka gode wa Allah da ba ta yi nasarar yagar naman jikinka ba, kuma kada ka ɗauka za ta haƙuri. Wannan daɗɗaɗiyar mummunar manufa ca tunkafin haihuwarka, zan yi takaici ƙwarai matuƙar ta yi nasara a kanka kamar yadda ta ci galaba a kan mahaifiyar..." Sam Kamalu baya fahimtar kalaman da farin dattijon ke gaya masa, cike da damuwa ya katse shi. "Don Allah wane ne kai? Ya aka yi ka san mafarkin da na yi?" Murmushi Dattijon ya yi, "Yaro man kaza! Da sannu za ka fahimci turbar da nake son ɗora ka, izza da ƙasaitar jinin Sarki Muhammad Safwan ba za ta tashi a banza ba. Ba ni zan bayyana wa duniya waye kai ba, izza da tasirin jinin sarautar da ke jikinka ne zai bayyana wane ne kai. Ni Aminin Kakankakanka ne, ina bibiyar al'amarinka saboda waɗansu muhimman abubuwa da tasirinsu. Ta so mu je ka wanke ciwonka a wancan rafin, idan gari ya waye kada ka sanar da kowa mummunan mafarkinka hatta Baffajo da Inna wuro, domin wannan gidan sarautar cike yake da idanu mabanbanta."

  Tamkar raƙumi da akaɗa haka Kamalu ya bi bayan tsohon yana gaba shi kuma yana biye da shi, lokacin da suka ƙarasa bakin rafin wani irin sanyi ne ya fara ratsa shi har sai da jikinsa ya ɗauki rawar ɗari. Kaf kaf kaf haƙoransa suka fara rawa, ga wata irin juwa da take ƙoƙarin fisgar shi ko ta halin ƙaƙa, ɗagowa ya yi a wahalce ya furta. "Ba zan iya ba, ba zan iya zuwa ba sanyi nake ji." Rufe bakin Kamalu sai dajjijon ya sa hannunsa a tsakiyar goshinsa, a hankali ya ji sanyin da yake ji yana raguwa, "Ba na jin daɗi a duk lokacin da ga karaya a ƙwayar idonka, daga yau kada na sake jin ka furta kalmar gazawa. Tabbas za ka iya domin duk tsawon lokacin da muka ɗauka lokacinka muke jira, mu je ka aiwatar da abin da yake gabanka." Dattijon ya faɗa yana kama hannun Kamalu ya sanya ƙafarsa ta dama a cikin rafin, wani irin zuuu! Ya ji har cikin kwanyarsa. Gabansa na faɗuwa ya tsugunna a ɗebi ruwan ya wanke ciwonsa kamar yadda tsohon yake ba shi umarni, yana gamawa ya sake ba shi umarnin wanke fuskarsa ya ɗura masa ruwan a cikin kunnuwansa. Ruwan ya gani ya fara kaɗawa a hankali, daga baya kuma ya ga igiyar ruwan tana katantanwa da su. Yana shirin guduwa tsohon ya riƙe shi tsam a jikinsa, ganin a kowanne lokaci yana iya halaka ya sa Kamalu runtse idonsa. Sannu a hankali ya ji komai yana lafawa, hakan ya sa shi buɗe idonsa suka fara takowa suka fito daga ciki. Wani irin sauti yake ji cikin sigar kururuwa da neman ɗauki, lokaci ɗaya ya ji zuciyarsa na fisgar gangar jikinsa. Tafiya yake yi ba tare da ya san wurin da yake jefa ƙafafuwansa ba har ya zagaya wurin da yake jin ƙarajin sautin na kusantarsa a bayan ɗakin Mai martaba. A saitin kusurwar yamma ya hangi wani mulmulallan abu baƙi saboda duhu bai tantance takamaiman mene ne ba. Cikin dakiya da ƙarfin zucuya ya sa ka hannu da niyyar tonowa take zoben hannunsa ya mamaye wurin da haske, a nan ya yi tozali da wani abu mai tsananin wari da siffar jarirai har sai da ya ji tamkar ya amayar da kayan cikinsa. Tsaki ya yi cike da jin haushin abin da ya aikata, shi kansa bai san dalilin da ya sa shi aikata haka ba, ya dai ji ba za iya haƙura ba har sai ya taimaki abin da yake cikin ƙarƙashin ƙasar. Koda ya koma sama da ƙasa ya nemi Dattijon ya rasa, a bakin ƙofar ɗakinsu ya hangi Baffajo yana kai wa da kawowa yana ganin Kamalu ya ƙarasa yana tambayarsa inda ya je.

"Baffajo fitsari ne ya tashe ni, na ga kana bacci shi ya sa ban tashe ka ba." Ya tsinci kansa da ƙin faɗa wa Baffajo gaskiyar abin da ya faru. Riƙo hannunsa Baffajo ya yi tsam kamar wani zai ƙwace shi suka ƙarasa cikin ɗakin, ƙwallah ce ta ciko idanun Baffajo ya furta. "A wannan farautar da aka yi mana mun rasa Salele Kamalu yanzu haka ban san duniyar da ya nufa ba, don Allah kada ka yi yunƙurin abin da zai raba ni da kai, ka ga wancan rafin dai an ce hallaka mutane yake don Allah koda wasa kada na ga gilmawarka a wurin." Kamalu ya jinjina kai sannan ya koma ya kwanta cike da tausayin mahaifinsa.

  Tun da asubar fari aka tashi duka Bayin da ke sashen kamar yadda aka sunnanta musu, bayan sun idar da sallar asuba Uwar Bayi ta shiga raba wa sababbin Bayi aikin da za su gudanar, waɗanda suka san aikinsu kuwa suka ci gaba ɗorawa daga inda suka tsaya. Sai da rana ta fara fitowa sannan suka samu zarafin kai abinci cikin bakunansu, Mai gado ita da Inna wuro kusan ɗura suka yi wa kansu da sauran baƙin Bayin da aka kawo su rana ɗaya. Baiwa Fatsim na ganin yadda suke cin abinci ta saki shewa tana yi musu kallon sheƙeƙe ta furta. "Ahayye! Allah na dawo inji kishiyar mai yaji, duk wannan feleƙen da kuke yi gumi ce ba ta yi gumi ba. Amma da sannu za ku gane karatuna." Gabaɗaya babu wanda ya tanka musu, wata Dattijuwa da suka ji ana jira da Uwar tuwo ta ƙarasa wurin ta ce, "Tun wuri ku cire kawaici da kara ku fara ƙwatar wa kanku 'yanci idan ba haka ba kowa takaku zai yi kamar takalmin sawarsa. Wannan gidan yana da matuƙar bambamci da wuraren da kuka fito..." Sallamar Jakadiya ta katse ta, fuska a haɗe ta dube su ɗaya bayan ɗaya. "Zan ɗebi sababbin Bayi gabaɗayanku zan kai ku sashen Fulani Umaima tana son zaɓar waɗanda suka yi mata domin tana buƙatar ƙarin masu yi mata hidima." Jin babu wanda ya tanka mata ya sa ta buga musu tsawa, jiki na rawa duka suka miƙe sai Inna wuro da ke faman jera loma da sauri don ita idan tana cin abinci tana tashi duk daɗin abinci ba ta iya cinsa, ballantana a nan da abincin dare da suka ci ko kaɗan bai ishe su. Jakadiya ta leƙa ganin Inna wuro na zaune. "Ke ce shafaffiya da mai ba ki ji abin da na ce ba?" Baki na rawa Inna wuro ta sanar da ita uzurinta, ai kuwa lokaci ɗaya ta ji an kwashe mata da dariya.

"Ke a tsammaninki tun da kika shigo masarautar nan kina da sauran ikon da kanki? Ko kin manta matsayinki na Baiwa ne? Idan ba ki sani ba ki sani a yadda kika a cikin gidan nan sai yadda aka yi da ke, idan aka so ki kwana a tsaye dole ki kwana, gara tun wuri ki yakicewa kanki ɗan guntun 'yancin da kike taƙama da shi." A sanyaye Inna wuro ta tashi, idanunta suka ciko da ƙwalla. A duniya babu abin da ta tsana sama da yarfi da tozartawa. Babu yadda suka iya haka suka bi bayan Jakadiya haka kawai Mai gado ta tsinci gabanta na matsanancin faɗuwa, tun da suka nufi sashen Fulani Umaima Jawahir ke wani irin mutsu-mutsu har zuwa lokacin da Jakadiya ta sa suka jeru ɗaya bayan ɗaya. A hankali ta fara bin Bayin tana duba su a wulaƙance cikin yarfi da ƙasƙantarwa. Tana zuwa daidai kan Mai gado gabanta ya yanke ya faɗi, ta dube ta a yamutse. "A sauko da wannan jaririyar." Ba musu Mai gado ta kunto Jawahir da jikinta ya yi wani irin sanyi kamar wacce aka ciro daga ƙanƙara. Sauke idanun Fulani Umaima a kan ƙwayar idon Jawahir ya haddasa mata matsananciyar faɗuwar gaba, kalaman Bamaguje suka faɗo mata. Ba ta sake tsinkewa da lamarin ba sai da ta yi tozali da goshinta.

😁😁 Yanzu ne za a fara buga wasan, Shin me yake shirin faruwa tsakanin Fulani Umaima da Jawahir. Wai ma wace ce Jawahir ɗin nan kuma mutum ce ko Aljan?

Ina Dattijon nan kuma me ye alaƙarsa da Shu'umar Masarauta, wai ma me ye silar wannan abubuwan da ke faruwa? Akwai ɓoyayyan sirri mai ƙarfi da Dattijon nan ya sani mai ya sa bai aiwatar da komai ba sai da Kamalu ya zo. Wai shin Bayin Masarautar da shi Kansa Sarki Abdul'aziz za su gane shi ɗin jinin masarauta ne? Idan Fulani Umaima ta fahimta me kuke tunanin za ta aiwatar? Ina labarin Abubakar zai warke a nan gaba ko a'a?😢 Fulani babba tana warkewa daga cutar fitsari ko bata warkewa?

Maza hanzarta kada ki bari a yi babu ke, salon labarin daban yake. Namu ba irin nasu ba ne💃🏼💃🏼💃🏼 na san ba ku manta da BAƘAR DAULA ko AN YA BAIWA CE da ZAUJATU JINNUL-ASHIQ ba. Kar ki bari a yi babu ke wannan kafcan.🥳🥳🥳💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼

*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624. Cmplt doc 800 ne*






An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment