Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dama
ku gani zan rike Nusaiba iya rayuwata.

Ta dube shi a dage ta ce,"Bakin alkami ya riga ya
bushe maka Naseer, domin jiya da daddare su
M.Umar da M.Lawar sun zo. Amma Abbanka ka
ya rantse, ya masu, babu ruwan sa a cikin
maganar ka.

Haka ni ma bai lamunce min ba.

Saboda haka ka makara, dabara kuma ta rage wa
mai shiga rijiya. Ina fatan ka gamsu. Yayi zuru
kafin, ya numfasa ya dube ta ido sun kawo
kwalla.

"Shi kenan Umma, na gode. Abinda na ke son ki
rokin min Abba, shine, don Allah yayi hkr, idan
na gaishe shi ya rinka amsawa. Ni zan fita, ga
wannan koda Ameer yana bukatar wani abu." Ya
ciro dubu 2, ya aje bisa hannun kujera ya tashi
ya fice.

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~­
~~~~~~~~~~------------------------------------------------------------------------------------------------


Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi



------------------------------------------------------------------------------------------------


Karfe 9 ta gota kadan Jeep din su Hajiya Zulai ta
yi fakin kofar gidan su Naseer. Suka fito Ummi na
rike da hannun Nusaiba. Ummi ta yi sallama
tsakar gida. Umma ta amsa daga falo, a lkcn
kuwa ta kammala shirya Ameer tsaf!Yana ta
tashin kamshin hoda. Bata dauki murya sosai ba,
don haka ta ce,"Maraba, ku shigo mana." Ummi
ta yaye labule. Umma ta mike baki har
kunne,"Hajiya!

Ah!

Nusaiba!

Sannun ku da zuwa."

Suka zauna a kujera Umma ta mikawa Ummi
Ameer, ta karbe shi. Sai ta wuce firj za ta dauko
kayan sha.

"Dama kin bar shi, kin san safiya ce." Duk da
haka ta kawo da Jus din kananan kwali da kufuna
2.

Bayan sun gaisa, Umma ta tambayi Alhj? Sai
Ummi ta ci gaba da cewa,"Ba wani abu ya kawo
mu ba.

Ameer mu ka zo tafiya da shi, ya zauna wajen
uwar sa ta shayar da shi. Ko dama 6acin rai ne
yasa aka aje shi."

Kwalla suka cika idanuwan Umma ta ce,"Gaskiya
ne kuwa, na ji dadi, domin a gaba daya wannan
al'amari Ameer shine abin tausayi.

Shi kuma wancan sakaran, ai kyale shi ya gasu,
duk da cewar ya ce yayi nadama." Ummi ta yi
dan murmushi ta ce,"Ai ba'a soyayya dole, mu
ma mun san haka shi yasa Alhj ya ce a gaya
masa, tana jiran takardarta, ko zuwa jibi. Insha-
Allah za mu turo mota akwashe kayan ta a dauki
motar ta."

Umma ta goge kwalla ta ce,"Ba laifi, ki yi hkr
Nusaiba kin ji? Allah ya amfana miki dan ki. Ta
dan sadda kai ta ce,"Ba komai Umma.

Idan kuma na yi miki wani laifi, ki yafe min." Ta
girgiza kai,"Baba abinda ki ka yi min Nusaiba,
Allah yayi miki albarka."

Ta ce,"Amin." Ummi ta ce,"To bari mu je, za ta
debi wasu kayan kafin a zo kwashewa." Umma ta
ce,"To bari in kawo maku wani makullin, ya fita
da na hannun sa."Nusaiba ta ce,"Ina Antina
Umma?

Ta ce,"Ita ma ta tafi."

Suka dubi juna, kafin Ummi ta tambaya,"Saboda
me?------------------------------------------------------------------------------------------------


Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi



------------------------------------------------------------------------------------------------


Zaharaddeen Shomar

Whatsapp 08168575100


Ajininsa yake 3-03
Posted by ANaM Dorayi on 11:46 PM, 21-Nov-15
_______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______

Fa ce,"Ita ma ba za ta zauna ba.

Sai Nusaiba ta dawo.

Kin ga ya 6ata 2 kenan, sai wani gyaran
Allah.

Nusaiba ta dafa kirji ido waje, sun kawo kwalla,
ta dubi Ummi ta ce,"Me yasa Antina za ta yi
haka? Ai ni ba zan ta6a dawowa ba, yakamata
yayi ta gane wamman.

Ummi mu je in debi kayan, mu wuce wajen
ta."

Suka mike, Umma ta kawo makulli. Nusaiba ta
debi kayayyakin da take son diba. Abubuwan
dake firj din ta duk ta kwaso ta kaiwa Umma.
Bayan Direba ya zuba kaya a mota, suka sallami
Umma suka rabu suna daga wa juna hannu.
>
Babu Abinda zata yi, Nusaiba ta hana ta tafiya,
babi abinda za ta iya yi.

Duk iya kaunar da take wa Nusaiba data zauna
dakinta, dole ta
kyale.------------------------------------------------------------------------------------------------


Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi



------------------------------------------------------------------------------------------------


Babban abin godiya ma shine, da suka tausayawa
baWan Allah suka zo da kan su suka dauke
shi.

Shi yasa take ta yi wa Allah godiya, ba 6ata lkc ta
kira wayar Abba a kasuwa, ta shaida masa. Ba
karamin farin ciki yayi ba, domin rabon sa da
fara'a tin asubahin jiya. Sai kuwa yau da aka ce
su Hjy sun zo da kan su sun dauki Ameer.

Cikin gidan su Zarah su kai sallama yanzu. Inna
ta amsa. Ta leko daga dakin Malam Umar. Ah!
Nusaiba! Maraba. Fit Zarah ta fito daga dakin
Inna, baki har kunne,"Amarya! Antina." Zarah ta
matso suka rungume juna." Kin dawo ko amarya?


Ta daga ta dube ta,"Haba Antina, zo mu je daga
cikin in gan ki."Ta kama hannunta suka shige
daki. Inna ta ce,"Ke Hajiya shigo nan, kafin su
gama ganawar. Ina fatan dai na dawo mata da
amaryarta ne, mu huta." Bata ce komai ba, suka
shige, tana 'yar dariya.

Nusaiba ta dubi Zarah,"Me yasa haka Antina? Bai
kamata ki yi wa yayanki haka ba." Ta ce,"Ni kuwa
a waje na hakan ya kamata, domin ciwon 'Ya
mace, duk na 'Ya mace ne. Na kuma shaku dake
amarya tafiyar ki za ki ta jefa ni cikin wani yanayi
na dacin rai."

Ta dafa kafadar ta, ta ce,"Kin fadi
gaskiya,"Antina, kuma na san ki ni nuna min
iyakar kaunar da ba duka mace za ta nuna wa
abokiyat zamanta wannan kaunar ba.

Allah ne ya kaddaro zan sami Ameer, amma ke
ce sila Antina.

Ban mancewa har ta kai ki ga rasa na ki cikin.
Ina so ki sani Naseer, yana da halayya masu
kyau, yana da kula tare da tsare hakki, ni ce
kawai da bai so yake nuna min banbanci.Bai
damu da ni ba, balle ya kula da hakkoki na. Kar
ki damu Antina, ba laifin yayanki ba ne. Allah ne
bai sa masa soyayyata ba, saboda haka na ke
rokon ki idan ya zo daukan ki, ki yarda ki bi shi,
domin ke ce rayuwar sa.

Ke yake so, da ya ke yake ra'ayin zaman aure.
Abin alfaharin ki ne a wannan zamanin da ki ka
sami miji kamar Naseer, mai tsayuwa akan
alkawarin soyayya. A karshe ina son ki sani, har
karshen rayuwata ba zan ta6a mancewa da ke ba
Antina. Hasalima dole wata rana Ameer wajen ki
zai dawo, kin ga har yanzu mu na tare ke nan.
Kin hakura ko?

Abinda ya fi ba Zarah mmk, shine ashe Nusaiba
na sane da abinda ya faru kafin Naseer ya shiga
dakin ta. Gaskiya Nusaiba mai hakuri ce, irin
wanda sai an sha bincike kafin a sami irin sa. Ta
zura mata ido cike da kwallan tausayi. Allah na
ganin bata son rabuwa da amaryar ta.

Nusaiba ta kamo hannun ta, ta dora bisa kan
ta,"Ki yi min Alkawarin Antina, a yau za ki koma
dakin ki, ba gobe ba, kin ji? Ta goce da kuka,
suka rungume juna, haka wahayen ya kubce wa
Nusaiba,"Za ki koma ko? Ta dago ta goge kwalla
ta ce,"Zan koma Amarya, amma kema ina rokon
ki idan a an dai-daita da su Abba, don Allah kar
ki kafe ki ce ba za ki dawo ba.Ta yi dan
murmushi, ta ce,"Shi ke nan, bari mu zo mu tafi,
sai mun yi waya, shi kenan na ji, alkawarin za ki
min kamar yadda na yi miki." Ta yi dan jim, kafin
ta ce,"Ai ba laifi na bane Antina, ke ma ba za ki
yarda in zauna inda ba'a so na ba."

Ta kada
kai.------------------------------------------------------------------------------------------------


Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi



------------------------------------------------------------------------------------------------


Da ke nan amarya, amma yanzu ina mai tabbatar
miki yayanmu yayi nadama, ko bai gaya min da
bakin sa ba, ni na yi imanin yana son ki, ba ki ga
yadda ya fita hayayyacin sa ba, lkcn da lalura ta
kama ki kuma ya kula da ke yadda
yakamata.

Ta ce,"Anitina ki na so ki gyara yayanki ne kawai,
amma ni na san tausayine irin na musulunci. Kin
san musulmi mai imani ya kan tausayawa dan-
uwansa a lkcn daya shiga wani hali.

A bar maganar nan Antina, ki yi min addu'ar
Allah ya zaba min abinda ya fi zama
alkhairi."

Ta numfasa, hannun ta bisa kafadar ta,"Zan miki
amarya. Allah yasa alkhairin a gidan yayanmu
yake."

Ta mike tana dan murmushi, ta fito ba tare da ta
ce komai ba, sbd bata son maimaita zancan.
Dakin da su Ummi suke, suka yi sallama. Inna na
rike da Ameer.

Zarah ta nufi gun sa, ta dauka, Ummi ta ce,"Zo
nan. Ta wuce wajen ta da Bebi a hannun ta, ta
tsugunna gefenta, ta dafa kafadar ta, ta ce,"
Zarah ba'a wasa da aure, hkr za ki yi ki koma
dakin ki kinji?Kan ta sunkuye tana dan ta6a
kuncin Ameer, ta amsa da kai, sannan ta
ce,"Wallahi Ummi Naseer ya gane kuskuren sa,
tun jiya yake kuka, yana bin mutane ya samu aje
masa biko. Abban sa ne ke fushi da shi, ya ki
bada hadin kai.

Don Allah Ummi, ku yafe masa ku bar amarya ta
dawo."

Ta ce,"Babu abinda Innar ki bata fada ba yanzu,
amma Naseer ya riga ya rushe katangarsa.

Alhj na da saukin kai, sai dai idan ka ta6i shi,
nan ne za ka gane ma yana da zafi.

Saboda haka ku taya mu addu'a. Allah yayi masa
zabi." Zarah ta yi shiru idunwanta suka kawo
kwalla. Ummi ta mike, ta ce,"Allah yasa mu
gana." Duk suka tashi suna fadin Amin.

Har mota suka rako su, sannan Zarah ta mikawa
Ummi yaron. Ta dubi Nusaiba, kowacce hawaye
ya zo mata, suka rungume juna. Da sauri Nusaiba
ta shige mota, haka ita ma Zarah ta ruga cikin
gida, bata son ganin tafiyar Nusaiba.

Hawayen ta suka yawaita, tana sharewa, wasu na
sauka. Direba ya damki hanya. Nusaiba ta yi
shiru cikin mota, ta sak'a wannan, ta kwance
wancan a game da maganganun Zarah. Tabbas
su Abba sun gaya mata Naseer yayi dawainiya da
ita sosai a cikin kwanakin nan 50 da ta samu
kanta a wani yanayi.Sai dai babu wanda zai
tantace me Naseer ke nufi cikin ransa? Ko ita ma
Zarah hasashe ta yi, domin da bakinta ta ce bai
fito fili ya gaya mata ba.

A cikin tunanin ne ta ji Ummi na fadin,"Ke ba shi
nono ya sha, ya
farka."------------------------------------------------------------------------------------------------


Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi



------------------------------------------------------------------------------------------------


Ta dube su firgigi. Ummi na masa mika tana
cewa ka sha barci ko? Nusaiba ta mika ruwa aka
ba shi, sannan ta karbe shi, ta mika masa nono
ya kama yana sha.

Nan da nan so da kaunar sa suka kara shiga
zuciyar ta har bata san lkcn da fa kura masa ido
ba.

Karo na farko da ta tantance kamanin
danta.

Tamkar Ameer na farko. Haka kuma hoton
Naseer take gani zahiri bisa cinyoyinta. Tsigar
jikinta ta tashi yar!

Saboda kyan surar yaron nan, musamman daya
buda ido tar!

Yana dube-duben sa.

Ya sha sosai. Ta juya shi daya gefen, nan ma ya
sha mai isar sa. Bai koma barci ba. Ummi ta
karbe shi, ta ci gaba da renon mai gida.

Jimawa kadan Kausar ta kira wayar Ummi, ta
mika wa Nusaiba ta ce,"Ungo Kausar ce." Ta
kar6a da saurinta, ta danna O.K."

"Hello."

Ta ce,"Hello Nusaiba ya karfin jiki?
Alhamdulillahi."

Ta ce,"Ya maganar Bebi ne? kin san Allah jiya ban
yi barci ba." Ta ce,"Bisa hanyar komawa gida
muke yanzu, mun je an dauko shi.Ta nisa ta
ce,"Better. Ai ni ba zan iya ba, ka aje a jariri, ai
ka cuce shi.

Shi me ya sani? Ta yi dan murmushi,"Kausar
kenan."

Ta ce,"Tare ku ke da Ummi ko? Bari in yi shiru,
idan kin kebe, kya kira ni. Ku sauka lafiya." Ta ce
amin. Ta kashe waya.

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~­
~~~~~~~~~~------------------------------------------------------------------------------------------------


Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi



------------------------------------------------------------------------------------------------


Sun iso gida 2 rana. Alhj na falon kasa. Suna
isowa Ameer yasa a kafada ya haye sama, yana
fadin "Ku hayo sama in gan ku."

Suka haye suka bar Direba na shigo da kaya.
Mariya na taya shi. Bayan sun natsa a
zaune.

Alhj ya dube su ya ce,"Bayan tafiyar ku. Yakubu
ya zo min da maganar Naseeer, haka shima
M.Balarabe ya kira ni a waya, kodayake yana min
godiya ne akan dauko Ameer da aka yi, har ya ce
zai zo musamman yayi min godiya.

Nace ya bar shi kawai, ta wayar ma ya wadatar,
na kuma ji dadi. To koma dai menene, ban son
mutane su dame ni akan maganar nan.

Lokacin da zan ba Naseer 'ya ta ban yi shawara
da kowa ba.

Shi yasa ban son kowa ya sanya min baki, duk
hukuncin da na yanke. Na riga na yanke shi.
Saboda haka na kira wayar Fatima, na gaya mata
za kikoma Jordan, ni zan kar6ar miki takardarki ki
a wajen Naseer.

Ina fatan hakan yayi dai-dai.

Idan kuma akwai gyara ina jin ku?

Ummi ta ce,"Zabin Nusaiba ne, me ki ka gani? Ta
ce,"Hakan ya ma fi Abba na.

Hankalina zai fi kwanciya."

Ya ce,"To shi kenan.

Insha Allahu nan da kwana 3 za ki bar kasar
nan.

Allah ya kawo miki mai son ki, ki aura."

Ummi ta ce,"Amin."Sun jima suna hira nan, kafin
Nusaiba ta dawo dakinta, duk bata da kuzari a
jikinta, ita kanta bata san dalilin ba. Ta dan
kwanta don ta huta. Sai ga Ummi da Ameer ya
sake tashi barci.

Ta kar6e shi. Ummi ta fice.

Bayan ya gama sha tashinfidar da shi, ita ma ta
kwanta tana fuskartar shi. Rike yatsun sa ta yi
tana dan kada su, tana murmushin jin dadi. Sai
da ta ci abincin rana, sannan ta kira Kausar suka
kebe. Ita ma Kausar din ta goyi bayan Alhj akan
komawar Nusaiba Jordan, domin a ganin ta zatafi
samun
nutsuwa.------------------------------------------------------------------------------------------------


Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi



------------------------------------------------------------------------------------------------


~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

Al'amarin Naseer kuwa, bayan ya baro wajen
Yakubu, don jin yadda suka yi da Alhj, ransa 6ace
ya isa gidan su Zarah.

An riga anyi sallar la'asar. Yana shiga Inna ta yi
masa albishir da cewa su Nusaiba sun zo, sun
dauki Ameer. Take nan yayi wa Ubangiji sujada,
yayi godiya gare shi, sbd tsabar tausayin da
Ameer ke ba shi.

Nan da nan wani yanki na 6acin ran sa ya goge.
Sai da ya natsa. Inna ta sake fadin,"Sannan su zo
nan sun rarrashi Zarah, ta ce za ta koma, nan
ma kai take jira, dama kuma ko ba ka zo ba, ni
zan maida ta anjima." Ya numfasa, kaunar
Nusaiba ta k'ara shigarsa.

Yarinya mai hankali, haka kawai ya tsaneta. Ko
me yasa? Ya karkada kai ya ce,"Inna na gode.
Ina Zaran take? Ta zo mu tafi." Ta ce,"Tana nan a
ciki tana jin ka." Ya mike daga inda yake zaune,
ya shiga dakin. Tana zaune bisa kujera, jakarta
na aje gefe.

Ya tsaya kan ta ya ce,"Sai na miki dukan
musulunci tukuna, bari ki gani." Ya nad'e gefen
rigar sa, ya tsula mata." Ni ki ke ba wuya ko? Ta
6alla masa harara. Ya mammare kuncinta.
Idanuwanta suka kawo kwalla, sbd Nusaiba da ta
fado mata rai.

Ya tsugunna ya kama kunnuwan sa 2, ,"Na tuba."
Ya zura mata ido, tana share kwalla," In dai
amarya ce, ki kwantar da hankalin ki. Insha Allah
za ta dawo. Taso mu tafi." Bata tanka masa ba,
ta mike tana ci gaba da share fuska, ya dauki
jakar tayo waje, ya biyo ta.

Inna tana zaune, suka sallame ta, ta k'ara jajja
masu kunni, suka tafi.

Ko cikn mota ta k'i magana, ya dubeta, yayi d'an
murmushi,"Zarah manya,

yanzu ke ma ko tausayina ba kya ji, ina ku ke so
in sa raina?

Ta yamutsa fuska, a karo na farko, ta ce da
shi.

Oho?

Ai dama wanda bai ji bari bari ba, zai ji hoho!


In banda son kai ma, wa ka ke zaton zai tausaya
maka?Ya ce,"Ke mana sanyin raina. Ina ganin ai
saboda ke hakan ta kasance, sbd sonki kadai na
aje wa zuciya ta. Bai kamata ki juya min baya ba,
idan duka duniya sun dora min laifi.

Kalaman sa suka sa jikinta yayi sanyi, ta yi dan
shiru kafin ta ce,"Na san haka yayana, amma
lokacin da kowa ke gaya maka gaskiya, bai dace
ka ki daukar maganar na gaba da kai ba.

Yanzu ina amfanin abinda ya faru? Ya kamo
hannunta ya ce,"Wallahi babu, ban ta6a gane ni
ba ni da wayau ba, sai wannan karon Zarah. Abin
kamar almara na ke ganin sa."

Ta ce,"To yanzu menene abin yi? Ya ce,"Gaskiya
ban sani ba, domin Yakubu ya je, amma Alhj ya
ce mai kama da ni ma bai son gani, balle ya ji
wata magana akan bikon Nusaiba.

A karshe ya ce masa ya riga ya soke ni a rayuwar
sa.

Kin ji bayanin Alhj, sbd haka ni ban da wata
dabara."

Ta yi tagumi, kafin ta ce,"Tabd'i!

Kai yanzu in tambaye ka tsakanin da Allah, ka na
son amarya ta dawo? Ya dube ta ya ce,"D'ari
bisa d'ari na zuciyata ke kaunar Nusaiba ta
dawo, sbd ta yi min abinda ba zan ta6a mancewa
da ita ba a rayuwa."

Ta ce,"To ka gwada wannan dabarar ka gani. Ka
ajiye wani tura mutante wajen sa, ka tafi da kan
ka, ka ce masa, sai ka ga abinda ya ture wa buzu
nadi.!Duk wata bak'ar magana da wulak'anci, ka
jure shi, da kansa zai hakura, yana ji, yana gani
zai sakar maka 'yar."

Yayi d'an murmushi,"Zarah ke nan, bai saurari
manya ba ma, sai ni uban laifi? To zan gwada.
Amma ni kunya ma na ke ji mu hada ido da shi."
Lallai ba sokake ta dawo ba, kunya ai murje ta
ake yi." An gama Zarah,"Allah yasa amarya ta
dawo, ko don in huta da ciwon kai."

Ta 6allo masa harara, ya dube ta yayi
murmushi,"Ai kin ga na dan sami sauki, ko
hararar na rinka sha ta isheni jin dadi." Ta d'an
buge shi a kafada,"Allah za ka sani yayana."
>
Ya take birki a kofar gida, ta dauko jaka a kujerar
baya, ta fito ta riga shiga gida. A falon Umma ya
isketa.

Umma na mata fada. Ya zauna gefe ya
ce,"Umma sun zo sun kar6i Ameer ko?

Cikin rashin kulawa ta ce,"Sun zo."

Ya ce,"An gode ma su."

Ta yi biris da shi ta ci gaba da mgnr ta da Zarah.
Jimawa kadan ta koma sasan su, ta yi share-
share da goge-goge.

Har dakin Nusaiba ta gyara shi, ta goge zuciyarta
na saka mata lallai amarya za ta dawo da zarar
Naseer ya je da kan shi.

Kwana 3 kenan Naseer ya kasa zuwa Kaduna, sbd
kunya da jin nauyin Alhj. Yau kan Zarah har kuka
tayi masa, tana hada shi da Allah da Manzon
sa.------------------------------------------------------------------------------------------------


Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi



------------------------------------------------------------------------------------------------


Yayi shiri tsaf!

Ya biya ya dauki Sageer suka danki hanya. Gida
suka fara zuwa. Mai gadi ya ce ma su babu kowa
cikin gidan, duk sun yi tafiya.Daga can ofis suka
nufa, sakataransa ya gaya masa Alhj ya tafi
Abuja.

Kai abinda babu sa'a. Haka suka dawo jiki babu
kwari tare da mamakin ina za su je kuma gaba
dayan su har da Nusaiba?

Koda suka dawo irin tambayar da Zarah ta rink'a
yi kenan.

Har ta k"arawa Naseer haushi ya ce,"Wai ina zan
sani ne Zarah da ki ka dame ni da tambayar
nan?

Haba!

Yayi tsaki, ya tashi ya bar mata gidan, don sai su
yi
fada.------------------------------------------------------------------------------------------------


Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi



------------------------------------------------------------------------------------------------


Karfe 10 na safiya su Alh. Basheer na filin jirgin.
An gama bincike, an tantance Nusaiba da Ameer
tare da kayayyakin ta. Suka yi sallma da su
Ummi, ta wuce tana hawaye sabeda Ameer bisa
kafadarta, hannunta daya yana kan Beby. Sai dai
jirgin da za su shiga, sai sun dan jira shi, ya
gama hutawa.

Kamar yadda aka bada sanarwa.

Duk fasinjojin da ake tantance su, na zaune falon,
kafin a ba su umurnin shiga jirgi. Nusaiba ta zo
ta zauna kusa da wata mata.

Ita ma rungume take da Bebi cikin shawul, ga
wata yarinya a tsaye gaban ta, za ta kai shekaru
4.

Tana zama, ba ta yi aune ba, ta ga yarinyar nan
a gabanta, tana ta6a Ameer,"Bebi! Mamanta ta
juyo tana murmushi ta ce,"Husna ba kya ji ko?
Ba na ce ki tsaya waje daya ba? Ta ce," Umma
kin ga Bebi mai kyau? Zo ki gan shi."

Suka fara dariya.

Nusaiba ta ce,"In ba ki shi ne ku hada da na ku?
Ta ce,"Eh.

------------------------------------------------------------------------------------------------


Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi



------------------------------------------------------------------------------------------------


Ya sunan shi? Ta ce,"Ameer, ke ya sunan ku? Ta
ce,"Adnan.

Mamanta ta ce,"Oh ni, kin ji dadin halinki
Husna."

Ko a jikin ta, sai k'ara kwanciya take jikin
Nusaiba, tana wasa da kuncin
Ameer.------------------------------------------------------------------------------------------------


Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473

Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi



------------------------------------------------------------------------------------------------


Tun daga nan hira ta goce tsakanin Maman
Husna da Nusaiba.

Kamar minti 15, aka sanarwa fasinjoji. Su wuce
su shiga jirgi.

Tare suka sa6a yara suka wuce, ita fa Husna bata
yarda ba, son Ameer take yi, don haka Nusaiba
ta kamawa jaka tana bin ta da gudu.(First class)
dukkan su za su zauna, sbd haka ga kujerar
Nusaiba, ga ta su. Adnan da Manan sa. Su dai ba
su yi sukuni ba. Sai da barci ya kwashe Husna.
Sun sauka lafiya, ga 'yan tarbar 'yan uwan su
nan fululu kowa na jira. Nusaiba ta dudduba,
bata hango Antinan ba, haka Maman Husna ke
fadin,"Husna kin ga Abbanki bai zo ba ko?

Tana rufe baki ta yana kira,"Husna! Ta kwace
hannun ta, ta bi 6angaran da ta hango shi."
Abba!

Karo na farko da Nusaiba ta dubi Abban Husna,
sam bata gaskanta idanuwan ta ba. Ta kara
duban sa da kyau, babu ko shakkar Ibrahim
ne.

Jikin ta duk yayi la'asar saboda al'ajabin sake
haduwar ta da Ibrahim, wanda tuni ta mance da
shi a duniya. Suna tafe Maman Husna na
fadin,"Sai yaushe ke nan?

Ta ce,"Ai ina hada layi na, za ki ji kira na. Ai ba
zan yi wasa da lambar da ki ka ba ni ba, dole ne
in kira Husna."

Suka yi dariya. Nusaiba yanke tabi wani
6angare,"Bari in jira su Antina a nan. Ta ce,"Ah!
Ba za ki sallama da Husnar ta ki ba." Ta ce kyale
ta, ta ga Abban ta, ta mance da ni." To shi
kenan, sai na ji ki." Ta wuce inda su Husna ke
tsaye da Abban ta, duk da cukuikuye shi, ta hana
shi sukuni.

Babban yaron dake tare da shi, ya rugo ya
rungume Maman su, shi ma zai kai shekara 6 ko
5 da rabi. Nusaiba na tsaye duk ta kosa Antinta
su zo.......Ta bar wajen. Don bata son Ibrahim ya
gan ta, kawai ji tayi Husna na rikota tana
fadin,"Zo ka gan shi Abba, Bebi mai kyau."

Gabanta ya fadi, ta waigo cikin tsarguwa, suna
hada ido da Abban Husna ya ji kamar zai fadi,
sbd faduwar gaba. Bai san lkcn da yayi zuru, ya
zuba mata ido ba.

Ta shiga dan yake, tana wa Husna magana,"Ke
wai ba mun yi sallama tun a jirgi ba?

Tsayuwayar Maman Husna wajen yasa Ibrahim ya
dawo duniyar daya tafi, yayin da Husna ke
fadin,"Abba na zai ga Bebi mai kyau.

Ka gan shi? Suka fara dariya, ya kar6e shi ya dan
daga sama ya ce,"Good day handsome Bebi!
>
Yayin da Nusaiba ta juya tana tambyara sunan
yayan Husna, ya ce,"Imran." Ta
ce,"Uhnmm..............Sunanka da dadi." Husna ta
ce,"Ni ma sunana da dadi. Ta kama habarta ta
ce,"Sosai ma, ke mai babban suna ma ba'a fadi,
shi yaya ake kiran ki Husna."

Dadi ya kamata har da yi wa Imran gwalo.

Ibrahin ya numfasa, ya dubi matar sa ya
ce,"Gaskiya wannan haduwa tana da ban mmk.
Ai dole ayi dalla-dalla. Wannan ita ce,"Nusaiban
da na ta6a ba ki labari. Nusaiba ga Madan din
na Sakina." Mamaki ya kama Maman Husna, take
nan kishi ya kulle ta. Ta dan daure fuskata ta
ce,"Ka ce min wacce ta kusan zarar min da
kai.

Nusaiba ma ta gyara fuska, ta ce,"Ki bar
maganar nan Maman Husna ta riga ta wuce." Ya
ce,"Sai zumunci ko? Yana da kyau, ina fatan kin
bata adires, kafin ta koma, za ta kawo mana
Ziyara."Sakina ta gyada kai tana yamutse
fuska,."Na dai bata lambar waya."

"Mts, ina ganin ya kamata mu wuce Abban
Husna, na fara gajiya wallahi."

Ya ce ,"Tunda ba'a zo daukan ki ba, why not ba
za ki bi mu, mu sauke ki gida ba? Sakina ta
kauda kai yayin da Nusaiba ke 'yar dariya, tana
fadin,"Ku bar shi Allah na gode. Ai na san za su
zo."

Ta mika hannu ta kar6i Ameer a hannun sa.
>
Ya maida hannaye aljihu, ya numfasa, amma bai
iya cewa komai ba.

Ta shashshafa kan su Husna ta ce,"Sai anjima ko
Husna!? "Bye-bye Bebi, sai ka zo gidan mu." Suka
yi sallama da Sakina, ba wata walwala a fuskarta,
ganin haka Ibrahim yayi gaba rike da hannayen
yaran sa.

Sakinta ta bi bayan su cike da kishin babu gaira
babu dalili.

Nusaiba na nan tsaye, duk takaicin al'amarin ya
dameta ta, kamar minti 5 da wucewar su.

Antinta ta iso,"Allah sarki Nusaiba, sorry,"Wallahi
sharrin mota ne, cak ta tsaya mana

Please Login or Register in order to submit comment