Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka saba. Zarah na
nason ziyartar Singafo da Malesiya, don haka
washe gari suka wuce suka kwana 4. Kwana
bibbiyu a kowace k'asa. Sun ci gaba da hutawa
a Potugal.
Sati 2 dai-dai da zuwanta, ciwon ciki mai
tsananin gaske ya murda. Zarah kamar ba za ta
yi rai ba. Naseer ya gaggauta kai ta asibiti.
Babu 6ata lokaci ta ga Likita ya bata kwararrran
bincike. Allah da iko tare da yin yadda yaso.
Wai Zarah ciki gare ta na sati 2 a wajen mahifa.
Naseer yayi wa Likitan ta bayanin matsalarta.
Nan da nan aka buda bakin mahaifa aka maida
cikin mazaunin sa. Ta sami kulawa sosai a
asibitin har ta wartsake.
Yayin da Naseer tuni yayi waya gida, ya shaida
masu halin da ake ciki. Kowa ya sha mamaki.
Shi yasa tana murmurewa ta fara amsa
wayayinsa masu gaishe ta, musamman Nusaiba
da ta kan bugu sau 3 zuwa 4 a rana. Mafarin
zamanta a Potugal kenan tana samun taimakon
daya kamata.
Anyi wa yara hutu. Nusaiba ta aje su wajen
Umma, ta zo duba Antinta, sati 2 ta koma gida.
Sannu a hankali cikinta ya wuce wata 7, ya shiga
na 8 kuma Bebi lafiya lau, kowa na ta murna,
musamman Naseer da yake tausaya wa Zarah.
Rashin da, ga ta ita ma ita kadai wajen iyayen
ta. Satin da za ta shiga wata na 9, jini ya goce
kamar famfo.
Da kyar suka tsaida jinin suka shiga binciken
mai ya kawo hakan.
Ai da gudu Likita yasa aka gara ta tiyata, bai yi
bayanin komai ba, sai da ya ciro k'aton Bebin
namji, sannan yayi mata duk abinda ya ga ya
dace, don tsira da lafiyar ta.
Daga Bisani ya kira Naseer ofishinsa yake gaya
masa matsalar da Zarah ta samu. Mahaifarta ta
fashe gaba daya, wanda dole ya kasance ya
fitar da ita baki daya, hakan shine wajibi a gare
ta, don zaman lafiyar ta.
Kuka ne kadai Naseer bai yi ba, amma ilahirin
hankalinsa ya tashi. Gani yake yi kamar ma cire
mahaifar, zai iya jawo mata wata matsalar, sai
da likita yayi masa bayani sosai, sannan ya
gamsu. Yayi addu'ar Allah ya k'ara mata lafiya,
ya kuma bar mata abinda aka samu, ita ma ta
rink'a ganin abin ta.
Ko gida Najeriya hankalin su ba kwance yake ba,
duk Nusaiba ta k'osa a kammala mata biza ta
tafi.
Bayan kwana 3 kuwa ta isa Potugal.
Antin tana a kwamce, duk ta rame ta dushe,
bata san lkcn da ta fara zubda hawaye ba.
Ga Bebi kato, gwanin sha'awa kuma duk 'ya'yan
Naseer da shi suke kama, har matan.
Nan ta zauna tare da Bebi (Aliyu), zuwa lkcn da
Zarah ta yi sarai, tsawon kwana 12 a asibiti,
kafin Likita ya bata sallama suka dawo gida.
Sai da Zarah ta yi 40, ita da Aliyunta, sai k'ara
murjewa suke, ita dai Zarah ta ki sakin jinkinta
dashi, gani take kamar shi ma mutuwar zai yi.
Sun dawo gida Najeriya yana da kwana 45, gaba
dayan su da Naseer.
Gagarumar walima ya shirya, bata wasa ba,
'yan uwa da abokan arziki suka taru, aka taya
juna murnar samun Aliyu tare da fatan Allah ya
raya shi cikin danginsa, rayuwar Islama. Sati 1
Naseer yayi ya dawo Potugal.
Tun Zaran na fidda rai da Aliyu, tana ganin yau
zai mutu ko gobe har ta zo ta saki jikinta,
zuciyar ta ta zauna waje daya ta daina ba Aliyu
mutuwa. Watansa 9 kenan yayi girman mamaki,
da kan shi yake mikewa tsaye, yana nema cira
k'afa yayi tafiya.
Yana kuwa shan ja wajen 'yan uwan sa suna son
yayi tafiya dole.
Rayuwar su mai dadi suke sha, tare da abokan
huldar shi, domin a halin yanzu Sageer yana
lakcarin a nan (State Poly) da yaransa 3. Kausar
na da 2. Zumunxin su kodayaushe k'ara k'arfi
yake tare da k'aruwar arziki. Ko Zarah ta gyara
gidan su dai-dai gwargwado tare da taimakon
Naseer. A cikin su da iyayen su babu wanda bai
keta hazo ba, ya sauke faralinsa. Komai maka
Allah shekaruna mikawa hada da tarindaukaka.
Naseer ke zaune shi kadai bisa kujeran alfarma
a farfajiyar bayan gidansa. Yayi shiru ya
zunduma taunan baya, har ya zo kan rayuwar
da yake cikin ta a halin yanzu.
Ya dubi tafkeken gidan sa a birnin Potugal,
mallakar sa wanda ya zuba makudan daloli ya
siya. Babu abinda ke ransa, sai dumbin godiya
ga Ubangiji da yayi masa baiwar da ba kowa ke
samun irin ta ba.
Sannan ya mallaka masa ingantattun mata na
nunuwa a fadin duniya.Zarah idan ya tuna irin
baiwar da Allah yayi mata na kaifin hankali da
sanin yakamata, ya tuna ita ta fara gaya masa
rayuwa shirin Allah ce, bai kamata Dan-adam
yana alkawari a hurumin da ba nasa ba, sai ya
ji son ta ya shafe ko'ina a jikin sa, yana neman
zautar da shi.
Nusaiba matar da yake wa yak'inin sa'a ce a
gare shi, Allah ne yayi masa arziki daga gare ta,
'ya'ya da dukiya tare da fice a duniya. In dai
ana maganar wasan Polo, duk masoya wasan
sun san da Naseer Jah-Jah.
Shi yasa idan ya dube ta, haka kawai ya kan ji
hawaye sun cika idanuwansa, sbd tsabar
tausayin kan sa, da ace ya rasa ta akan wautar
banza. Son ta ruwa ne, ya aje wa ransa, don ko
ya fadi, shi kansa yana ganin karya yake yi.
Yayi mika, take nan kewar su ta kama shi,
domin babu ko dayan su a tare da shi. Zarah
na jarabawar karshe ta kamala B-ed din ta.
Nusaiba kuwa ta na watan haihuwa ta 6.
Ita kadayaushe ta fi son haihuwa a gida. Gaba
daya hankalin sa ya koma gun sun, daren nan
ya kasa barci. Kamar wasa zuciyar sa ta rasa
sukuni, ba shiri ya nemi hutun shekara.
Bai hada sati ba, ya baro Potugal, sai ganin sa
suka yi kwatsam!
-----------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
'Ya'yan sa suka baibaye shi, tun isowar sa har
la'asar yana tare da su. Direba yayi kiran su
lkcn Islamiyya, kowanne ya fito cikin shiri, ya
shiga mota. Direba ya wuce da su. Zarah ta idar
da Sallah, ta fito babban falo ta iske Nusaiba
zaune tana kallo.
Kusa da ita ta zauna tana fadin,"Ki na nan ki na
kallon fadace-fadacen nan da ya ki ci ya
kicinyewa." Ta ce,"Ke dai bari, ai ni wannan
fadan na k'asashen larabawan nan tsoro yake
ba ni." Zarah ta ce, ke me kika fahimta daga
gare shi?
Ta ce,"Karshen duniya mana. Dama ance idan
zamani ya zo karshe, alamun har da 6arkewar
rikicin k'asashen gabas ta tsakiya. Yanzu dubi
k'asashe nawa ke rigima, ana kashe su, kamar
ana kashe kiyashi, tsakanin mu a musulmi
kenan."
Zarah ta tallafe kunci ta ce,"Wannan rayuwa
tana firgita ni, me mu2m ya kamata yayi, banda
ya kadaita Allah, yayi masa ibada, sannan idan
ya ci, ya bada sadaka, don neman karshe mai
kyau? Ta ce,"Wallahi kuwa Antina, musamman
na mu mata da aka ce mun fi yawa a gidan
wuta.
Biyayyar aure ce matsalar mu komai muka yi
gidan miji lada ne. Amma sai ki ga abin ya
gagara.
Kar ma ace miki akwai abokiyar zama, abin ya fi
kazanta.
Sai ki ga mace ta mance cewar akwai hikimomi
da yawa cikin auren mace fiya da daya shi yasa
Ubangiji ya halasta shi.
Haka kawai ta dauki bakin kishi ta dorawa
kanta, daga nan ne za ta fadawa hallaka.
Allah ya kiyashe mu.
Zarah ta kamo hannun ta, suka runtse,"Kin yi
gaskiya amarya, shi yasa na ke wa Allah godiya
da yasa ke ce abokiyar zama na." Ta yi
murmushi,"Ni din Antina? Na fi kowa farin cikin
samunki. Allah ya k'ara hada kan mu, ta yadda
yayanmu zai ci gaba da samun kwanciyar
hankali.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Tafi suka ji ana yi ta bayan su.
Duk suka waigo,yayan na su ne a tsaye yana jin
su. Ya zagayo suna dariya ya tsaya gaban su, ya
ce,"To a matsa min in zauna." Suka ware ya
zauna tsakiyar su." Allah ya kamaku, ashe zama
ku ke kuna gumalta ko? Zarah ta kama baki,
"Lah!
Allah mai halitta, jaba ta dubi bakin mijinta.
Gulmar me kuma a mu ka yi ta ka?
Ya kamo kunneta. Nusaiba na kwasar dariya, ya
ce,"Ita jabar 6ata dubin ta ba ne? Ta ce,"Oho."
Ya k'ara murdawa, ta yi k'ara. Nusaiba ta kamo
na shi ta ce,"Allah sakar min Antina, ko ni ma in
cire na ka. "Ya saki ya dube ta,"I see, kun hada
kai ko?
O.k, yayi kyau, ke ba zan ta6a ba, kin zama
yangwam!
Amma ke, za mu hadu."
Duk suka yi dariya.
Ya rungumo kafadansu ya sake fadin,"Allah ya
yi maku albarka, kun zama abin alfahari na, kun
zama jigon rayuwa ta.
Na kuma gane rayuwa shirin Ubangiji ce,
mutane da yawa suna samun dama, amma sai
su ki amafi da da damar har ta wuce su, daga
baya su zo suna cizon yatsa.
Allah ya ba mu ikon amafin da damar mu."
Suka nisa suka amsa da Amin.
Kowacce ta dora kanta bisa kafadar gefen sa.
Suka yi shiru na 'yan dakikai.
Cikin shirun ne suka ji kamar suatin T.V, a wani
sashi na gidan. Naseer ya ce ,"Wai ba duka
yaran nan sun taifi makaranta ba?.
Eh mana."
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Ya mike yana fadin,"Ga sautin (Game) can ina j?
Duk suka mike suka bi shi sashin yara. Ameer
ne ya kuke yana buga Game na tseren Polo,
sautin T.V ya rage can k'asa, yi yake kamar zai
tashi sama, sbd kwaikwayon yadda dawakan ke
gudu. Naseer ya lalla6o ya cafke kunnansa, a
tsorace ya waigo manyan idanuwan nan na sa.
Suka kara yo waje tamkar Naseer a zamanin da
yake shagalinsa a filin sukuwa.
Bai tanka masa ba, yai ta jan kunnan sa har
falo, sai su Zarah ke ta faman salati suna
fadin,"Amma dai Ameer Allah ya shirye ka!
Ya tsaya ya k'are masa kallo, kafin ya ce,"Kai ne
babba, amma babban kwabo? Kullum da kai ake
complain! To zan kwashe Game din tunda shi ke
hana ka zuwa makaranta! Yayi sukuiti yana
kumbura.
Nusaiba ta zungure shi, "Maras kunya, sai anyi
magana, ya rink'a cika yana hura hanci, wa ka fi
zuciya? Come on wuce ka dau ko jaka Lado ya
kai ka! Zarah ta kamo shi,"Wuce mu je, ka
dauko jakar, kai ba ka ganin kannin ka sun tafi?
Ta raka shi ya dauko jaka. Nusaiba na ta fada,
ta fita ta kira Lado Direba, yasa shi a mota zai
wuce da shi."
Nusaiba ta zauna kusa da Naseer ta ce,"Ameer
sai addu, ace yaro baya maida hankali a karatu.
Sai game din tsiya? Shi yasa ban so ka kawo
masu wannan sabin Game din ba."
Ya ce,"Zai bari ne." Zarah ta dawo ta zauna inda
ta tashi,"Ameer kenan an dai tafi ana ta
kunci,"Nusaiba ta ce,"Ai kin ji Babansa ya ce zai
bari ne, amma complain din Ameer yayi yawa,
ko makarantar kuka suke da rashin maida
hankalinsa, ga masifa, ni na rasa irin sa."
Ya ce,"Ni kuwa in na kalle shi, dariya yake ba
ni." Kin ji ko Antina? Ta ce,"Ya dai kamata ka sa
baki, ka yi masa fada sosai, kafin ka bar garin
nan, kila ya fi jin na ka. Ameer yan aikin gidan
nan bai kyale ba, haka 'yan kanninsa. Aliyu
kadai bakin sa ke ceton sa da yake duk gautan
ja ne.
Baba na da Alhaji kuwa, sai dai su yi kuka su
share hawaye, balle kuma 'yan matan."
Ya kama kai, ya ce,"Wayyo Abba na, duk
wannan laifin shi kadai? Wai ba yarinta bace?
Nusaiba ta ce,Yarinta? Me yasa............
Ya katseta,"Ya isa! A yimin shut up nace! Rashin
jin nan fa kowa yayi shi, ke kin yi, ke ma kin yi.
Ni ma na yi."
Nusaiba ta ce,"Oho, ashe abin gado ne, ta
6angaranka, amma mu ba muyi rashin jin kin
zuwa makaranta ba."
Yayi 'yar dariya ya ce,"Yan rainin wayau, kun
cika ni da , kamar ban san sirrin kowacce ba."
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Zarah ta gyara zama ta ce,"Ai sai ka
fadi"Yalla6ai, mu na ji." Ya dube ta, ya ce,"Ke fa
kullum ki na like bayan taga, ki na zuba ihu,
hawaye sharaf-sharaf, majina har baki. Da an
tambaye ki menene? Sai ki ce kudin (Break) dina
ne suka 6ace."
Ya fadi yana kwaikwayon muryart har da
shashshekar kuka.
Ya juya kan Nusaiba,"Ke kuma ai Abba ya gaya
min da zarar Direba ya fito da mota, zai kai ki
makaranta, sai ki ce kashi ki ke ji."
Ni din?
Zarah ta ce,"Ke ma ki ka tsaya tambayar sa. Ta
figo filon kujera. Nusaiba ma ta dauko na ta,
suka rufe shi da duka.
Me zai yi ba dariya ba, yana fadin,"Mugaye,
k'arya na yi.........?
Na kwashe 'yan biro na da takarduna na bar
gidan, don ba zan iya ceton Naseer ba.
Tsokanar fada A JININ SA YAKE!!! ,
saboda haka ALHAMDU-LILLAH, na gaji da
shari"a.
Idan kuma akwai ma iyawa, to Bismillah!
Jah-Jah na can yana dakuwa a hannun zaratan
matan sa.."
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
afuwan bakujini da wuriba sakamakon wayata
tadan samu matsala, daga bayakuma nadanyi
rashim lafiya, your prayer is needed pls






Zaharaddeen Shomar
Whatspp 08168575100

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment