Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

komai, ina mai neman gafarar
tarin laifin da na yi miki. Da ace ki na cikin
hankalin ki a lokacin da na ke tare da ke a
asibiti. Da kin tabbatar da cewa na tuba, na
kuma fad'a cikin kaunar ki, son ki ya kama ni, a
lokacin da zaman mu tare ya zo k'arshe. SAKI
DAYA na yi miki ya ke ma'abociyar hakuri.
Amma ki sani, a duk bagun numfashin da zuciya
ta za ta yi a duniya, tare da bikon soyayyarki.
Da ace zan sake samun wata dama ta auran ki,
na yi rantsuwa da wanda ya halicce ni, zan
nuna miki za6i na gari Abba yayi miki. A karshe
ina addu'ar Allah ya raya mana Ameer, rayuwa
mai kyau cikin addinin musulunci. Mai son
kiNaseer Iliyas Balarabe!
Bata gaskanta idon ta ba, balle ta yarda da
abinda ta gani a rubuce. Ta sake maimaitawa.
Ta tsaya kasake tana sauke Numfashi. Me ke
cikin ranta wanda bata tantance shi ba? Kamar
farin ciki ne ya kamata, to me yasa hawaye ke
neman kubcewa?
-----------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Gaba daya ta kidime. Ta sake duba takardar
bisa sunan mai ita Naseer Iliyas Balarabe! Ta
cicci6o Ameer ta rungume shi tana fadin,"Tare
za mu koma gidan Babanka! Allah na yafe
masa! Da kyar ta sami barcin kirki. Da safe ta
tafi gaida Alhjn, tun daga fuskarta ya shaida
tana cikin walwala, ba kamar dawowar ta jiya
ba. Bayan sun gaisa, ya ce,"Kin ga sak'on? Ta
amsa da kai, tana d'an murmushi. Ya dan dago
habarta, ya ce,"To yaya? Ya fito bazawarin? Ta
fado jikin sa ta kudundune fuska,"Kai Abba! Ya
fasje da dariya,"Shi ke nan, na bari, to tashi ki
ji." Ta mike ya ce,"Na san anjima zai zo, sai da
ba shi da labarin komai, illa Ameer da zai
dauka. Za'a ci kwalliya ko? Ta tashi da gudu, ta
bar dakin. Ya kama dariya yana kwanciya bisa
kujera,"Bebin Abba kenan 'yar albarka.," Karfe 9
da rabi Naseer ya iso gidan su, don gaida iyayen
sa kamar yadda ya saba duk ranar asabar da
lahadi. Yana shigowa. Malam Balarabe ya hau
fada,"Kai menene dalilin kulle wayoyin ka.
Alh.Basheer na ta neman ka tun jiya, bai same
ka ba? Ya ce,"Uhm.............Ba su da caji ne. Ya
ce,"Amma kai k'aryar ka ko hanyar masallaci
bata sani ba Idan babu Nepa, ba akwai jenareto
ba? Yayi shiru." Watau abin zai dawo ko? Da
sauri ya ce,"A'a Abba! Ya ce,"To mike maza!
Yana neman ka." Ya mike yana fadin,"Sai na
dawo. "Umma ce kadai ta amsa mashi. Ya wuce
babu kuzari.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sha daya yana ofis din Alhj ko zama bai yi ba,
yace ya ke can gida ya dauke shi, an riga an
gama kimtsa kayansa. Tafe yake kawai, amma
ko alama baya son ganin Nusaiba, kar kwadayin
dawo da ita ya taso masa. A haka ya iso. Yayi ta
maza yayi sallama falon. Ummi ke zaune a falon
ta yi masa sannu da zuwa, ya tsugunna ya
gaishe ta. Ta kira Mariya, ta ce ta kira Nusaiba,
ita kuma ta haye sama abin ta. Yayi zuru a
zaune kirjinsa na duka. Mariya ta kawo masa
tiran kayan motsa baki. Bai ta6a komai ba, wani
lafiyayyen kamshi ya doki hancinsa. Ya ware ido
saitin kofa. Zuwa can Nusaiba ta ratso rike da
hannun. Ameer. Ya zura masa ido, ashe ma
kadan ya gani, kyan Ameer a hoto. Jikin sa ya
dauki rawa. Nusaiba ta daki zuciyar sa sosai. Bai
daina kallon su ba har suka iso tsakar falon, tayi
masa sannu da zuwa. Baki sake ya amsa. Ta
zauna ta dubi Ameer ta ce,"Ga Abba." Ya kura
mata ido ya ce,"Abba? Ta yi dan
murmushi,"Babanka ne, je ka." Ta tura shi ya
nufo Naseer. Mikewa yayi ya tarbe shi, ya
rungume, "Oyoyo Abba na! Ya jima da shi a
kirjin sa, kafin suka zauna, ya dora shi bisa
cinyoyinsa, suka bi juna da kallo.
Ya ce,"Ka sanni? Ya girgiza kai. Ya ce,"Baba ne.
Ka ce Baba inji? Ya ce,"Baba." Ya sumbace shi a
dukkan kuncin sa. Sannan ya dubi Nusaiba,
suka hada ido, yayi dan murmushi, ya ce,"Kun
dawo lafiya? Ta ce,"Lafiya lau, ya su Antina da
su Umma? Ya ce,"Lafiyar su lau, sun ce a gaishe
ki." Ta ce,"Ina amsawa." Suka yi shiru na dan
lokaci, kafin suka sake kallon juna. Kowa yayi
murmushi, ya dauke ido. Naseer ya kama
yatsun Ameer ya hau kadawa, ya rasa abinda
zai ce. Ameer ne ya katse shirun,"Baba, wai tare
za mu tafi? Ya tallafo kuncin sa ya ce,"A'a za ka
zauna tare da Mama tukuna ko? Ka na so? Ya
kada kai,"Ni zan bi ka." Ya kwanto jikin sa ya
lafe. Ya k'ara rungume shi, ya dubi Nuasaiba,
murmushi kawai take yi kafin ta ce,"Yaro ya san
gaskiya." Ya ce,"Wace gaskiya? Ai kyan sa ya
zauna tare da ke in rink'a zuwa ina ganin sa."
Ta ce,"A gidan wani? Ya 6ata fuska ya ce,"Anan
gidan na ke nufi, idan son samu ne, mu kasance
yana ganin mu tare kowane lokaci, shi zai
taimaka ya san mu ne iyayen sa. Ta dan kada
kai,"To ai kuma ba zama na zo yi ba gidan.
Matsalar kenan." Ya sauke numfashi yayi shiru,
ba don shi da abin fadi ba. Ta ci gaba da
cewa,"Yanzu za ku tafi a fito da kayayyakin??
Ya dan kalle ta, kin kosa ne mu tafi? Ban ce ba,
ayi hakuri." Haka hirar ta ci gaba su kamo nan,
su kamo can, alamun babu natsuwa a tattare
da Naseer. Sun sami awa 2 tare. Ya kwaso
kayan Ameer ya taho da shi, hankalin sa tashe.
A Zariya kowa na murnar ganin Ameer, shi ta
shi ragaggiya ce, sbd zullumin sun kusa rabuwa
da Nusaiba kwata-kwata sai wata k'addara za ta
hado su Shi yasa kodayaushe yana Kaduna tare
da Ameer wai yana kawo mata shi ne ta gan
shi. Dariya take yi, ta ce ta gode."
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sati 2 suka wuce Naseer na lilo tsakanin Kaduna
da Zariya. A yau da la'asar ya isa bayan barin sa
makaranta ya sa Ameer a mota suka zo. Suna
tare da Nusaiba a waje suna shan iska.
Alh.Basheer ya dawo, Naseer ya nufe shi suka
gaisa daga nan Alhjn ya ce,"Yauwa tunda ga ka,
shi kenan sai ka kai wa Malam Balarabe katin
daurin auran Kanwar ta ka, wani satin." Naseer
ya dask'are nan, har Alhj ya dauko jakar sa a
mota ya buda, ya debo katuna." Ungo guda 10
ka ba shi. Haka kuma ga na ka nan, in za ka ba
Friend din ka ne, in ba ka Twenty? Kamar ya
ce,"A'a." Sai wata zuciya ta hana shi, ya ce,"Toh
Alhj." Ya mika masa guda 30. Yasa hannu ya
kar6a.
Bayan sun yi sallama da Alhj, ya wuce ciki gida,
ran sa 6ace, ya koma gun Nusaiba,"Me za ki
6oye min? Ashe Next week ne auran ki shine ko
ki gaya min? Ni na isa in hana ne? Baki sake ta
ce,"Shirin gaya maka na ke yi, sai Abba ya dawo
ka tashi. Ayi hakuri. Ya suri Ameer,"Mu mun
tafi. Allah ya bada zaman lafiya." Ya wuce ya
bar ta zaune tana masa dariya. Yana zuwa, ya
watsa katuna bayan mota, suka tafi. Iya wuya
yake yau. Duk wanda ya ta6a shi, zai ji masifa,
gida ya wuce da katunan bai kai wa Abba na shi
ba. Yana zaune. Zarah da Ameer kadai ke
hidimarsu cikin gidan Baya ko fahimce shi ba,
suna kici ita da dan lelwn ta, suna girki. Yayi
nisa a tunanin sa, kamar ya hadiye zuciya, don
haushi. Me zai ci da katuna, banda ya banka wa
'yan iska wuta? Ya zabura a fusace ya fado
kicin, babu magana ya hau bincike, ya 6aro
mata da kayan cikin dirowar sama. Tayi tsaue
tana fadi,"Yayana me ka ke nema? Ashana." Ta
ga ya dauka, yai waje. Ta jefar da ludayi, ta
biyo shi,"Yayana me za ka yi da ashana? Ya
buda mota ya kwaso katuna, ya aje k'asa. Kafin
ya kyasta ashanar ta kwashe su. Ya kama da
karfin yana fadi,"Ki saki na ce ko? Ta dade bata
yi auran ba, idan har sai mun je masu daurin
aure! Ya fizzge iya rabon sa, ya watsar kasa, ya
kyasta ashana. Ya cinna, yayin da Zarah ta buda
ambulan, don ganin takardun da yake rawar
jikin konawa? Kati ta gani ta zaro shi ta karanta.
Dada masa duka ta yi a tsakar baya, yana duke
yana cinna wuta, ta fadi da karfi,"Kai yaya na
da kai ne! Duba ka gani,"Naseer Iliyas Balarabe
aka sa! Ya mike ya fige katin a hannun ta, ya
karanta. Gaba daya jikinsa yayi la'asar, ya zura
mata ido, sannan ya dafe goshi, duk kunya ta
kama shi. Ta ce,"Komai ba ka bincike, sai ka
yanke hukunci." Ya rungumo ta, hayaki yayi
sama, ta ce,"Ga dai sauran nan na cin wuta." Ya
sake ta ya hau tsalle yana kashewa, tana masa
dariya, duk da haka wasu sun k'one, wasu
kuma sun yi dameji. Ya kwaso yana nuna
mata,"Ni yanzu yaya zan yi? Katunan nan har
da Abba? Ta yamutsa fuska, ta dubi Ameer dake
tsaye gefenta, ta ce,"Mu ina ruwanmu ko
sweetyna? Ya amsa da kai, yana dariya. Ta
mik'a masa hannu,"Come on give me five! Ya
bata hannu, suka kashe. Ta sure shi, ta ce,"Zo
mu tafi abin mu, kar abincin mu ya kone. Baban
ka ya zare! Ya kawo mata wawura, ta kwasa da
gudu. T-shirt da wandon dake jikin ta ya bata
damar gudu sosai. Ameer dariya yake yana
murna. Kicin ya iske su suna ta yi masa
dariya."Don Allah ki aje girkin nan, ki zo ki raka
ni." Ta kama k'ugu, ta tambayi Ameer,,"Mu
muka ce ya konawa Abba kati?
Ya girgiza kai,"A'a, ta dube shi ta nuna shi da
ludayi,"Ka ji ko? Saboda haka ba ruwan mu." Ya
matso ya manne da jikinta,"Don Allah ki daina
wasa, ki zo mu tafi."Ta k'are masa kallo kafin ta
ce,"Jira ni ina zuwa." Ya sumbace ta, saboda
Ameer yayi waje. Ta sauke numfashi, ta
ce,"Allah na gode maka amarya za ta dawo." Ta
sauke girki ta kashe (Cooker), ko dama sitiyu ce,
ta rage mata. Daki ta je ta dora (After dress)
akan kayan jikin ta, ta yafo mayanin ta fito, ta
kulle gida. Ta same su a mota. Suka tafi Ameer
na bisa cinyoyin ta. Shi kuwa waya ya dauko ya
kira Sageer a Bauchi."Banza, ka na can za'a sha
shagali! Shagalin me? Amaryar Zarah za ta
dawo." Ah haba don Allah? Komai yayi dai-dai
kenan." Ya ce,"Walllahi ni ban ma san Abban na
ta ya hakura ba, kati kawai ya ba ni dazu." Cikin
murna ya ce,"Congrats. Insha Allahu zan zo a
daura da ni, wannan dole ne. Yaushe ne? Next
week,"Ai kuwa zan zo da yardar Allah." Suka yi
sallama ya aje waya. Ya dubi Zarah,"Ya ce, yana
gaishe ki." Ina ansawa. Amma ba ka gaya masa
ka zare ba, har ka kona katunan." Ya dunkule
hannu ya dora bisa kuncinta. Allah zan kwashe
miki hakora, ki kiyaye ni!
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Ya kuwa kama, ya danna masa cizo, ya janye da
sauri yana dariya. Su ma suna yi masa. Ya shafa
kan Ameer ya ce,"Ta koya ma mugunta ko? Ya
lafe a kirjin ta, suka kwakume juna. Naseer ya
sha mamaki da suka kai wa su Abba ragowar
katin da suka rage masu kyau guda 15. Malam
Balarabe ya ce idan ya na son k'ari ya zo ya ba
shi. Kunshi 1 ya fito da su, wani samfu daban
kuma bugun Malam Balarabe. Abin ya daure wa
Nasrr kai, ya ce,"Ni fa ban gane ba? Umma ta
ce,"Ai ba za ka gane ba, domin Abbanka da Alhj
sun barka cikin duhu. Amma tun ranar da ka zo
da Ameer gidan nan. Alhjn ya gaya wa Malam
cewaR Nusaiba za ta dawo." Ya shagwa6e
fuska,"Saboda Allah ya za'a min haka? Da na
mutu fa kafin lokacin saboda damuwa? Zarah ta
ce,"Sai a rufe ka mu ci sadaka. Ya harare ta.
Umma na fadin, gaya masa dai Zarah. Take nan
ta ba su labarin abinda yayi dazu. Me za su yi
ba dariya ba. Koda ya je Kaduna dariya suka
rinka yi masa, musamman Nusaiba. Shirye-
shirye ya kankama. Da yawa mutane ba sun san
Nusaiba bata gidan Naseer ba, sai da suka sake
ganin kati, musamman jama'ar Alhj. Ranar
juma'a da daddare Sageer ya iso, don haka da
shi aka daura aure. Washe gari karfe 1 da rabi
na rana.
Antin Jordan ta dubi Naseer ta ce,"Lalai kai mai
sa'a ne, ka yi wa Allah godiya, domin yayi maka
baiwa." Ya sunkuyar da kai,"Na gode Anti." Ya
wuce ta bi shi da kallo. Ibrahim ya fado mata,
tausayin sa ya kamata. Ranar daya zo Injinya na
masa bayanin hukuncin da Alhj ya yanke har ya
bar wajen, fadi yake,"Ai dama na san Abba baya
so na. Wannan karon ma har da Nusaiba, tunda
ta iya barin k'asar nan, ba tare da sani na ba."
Ta girgiza kai, ta ce a ranta,"Matar mutum
kabarin sa." A ranar Nusaiba ta tare su Kausar
suka rako ta. Suna shigowa Zarah ta kar6e ta,
suka rungume juna, ta kamo ta zuwa sashinta.
Kausar na ta fama da tsohin cikin ta, ta ya6e
bakin gado. Naseer ya shigo, bayan sun gama
cin abincin, suna shirin komawa. Ya ce,"To ga
motar can sun shawo man sun dawo." Kausar ta
ce,"Na ga ka na rawar jiki ne Jah-Jah, sai wani
korarmu ka ke, ni fa ina nan an sai jibi zan
koma." Ya ce,"Ga Jah-Jah nan a gaban ki, kin yi
wani turus, in za ki kai jibin? Aka kwashe da
dariya. Ta ce,"Anan gidan kuwa." Ya ce,"Ina,
taso maza in lalla6a ki in sa a mota, kar ki caza
min aiki. Ina angwancina, ace in taso asibiti zan
kai ki." Ta ce,"Gaskiya ne, ba laifin ka ba ne,
tana ji ta yi shiru, shi yasa ka ke kara fadi. Ta
na shiru. Antin Jordan ta shigo.
"Kausar cicci6o mana, sai da nace ki yi zaman ki
gida, ki ka ki." Simi-simi Naseer ya fice. Kausar
ta ce,"Ya ka tsere? Dawo mana mu ci gaba. Ka
na Angwanci ko? Ya waigo a bakin kofa, ya amsa
da kai, ya wuce yana dariya. Duk an watse.
Kowa ya koma muhalinsa. Ba ango kadai ba,
hatta Ameer yana murnar ganin Maman sa a
cikin gidan, yayi ta tsalle-tsallensa ya bi can, ya
bi nan. Amma yana cin abinci. Zarah ta yi masa
wanka, gadon ta ya haye yayi barcin, bai nemi
Maman sa ba. Tana zaune misalin 9, nazarin
litattafanta take yi. Naseer ya shigo. Ta dube shi
tana. Murmushi,"Ango kenan. Kamshin nan yayi
Wallahi." Ya tsugunna ya dada mata duka a
baya,"Ba kya ji ko? Ta ce,"Na kai ka rashin ji? Ya
ciji kunnanta, ta shafi wajen, ta ce,"Amarya na
jiran ka, tashi mu je in raka ka." Ta aje littafi ta
kamo hannun sa, ya mike ya rungumo kafadar
ta, suka fito zuwa sashin amrya. Ta turo kafar
tare da sallama ta shiga. Amarya ta sha ado, sai
wanda ya gani. Zarah ta ce,"Kai amarya, ai sai
yayan mu ya mance sunansa." Ta sunkuyar da
kai,"Antina kin dame ni tun dazu." Ta ce,"To
babu ruwana, ga shi nan na kawo shi amana,
gobe in an ga ya susuce, ke ce." Ta kama baki
tana 'yar dariya. Ya kamo kunnanta,"Shi yasa
nace ba kya jin, zo ki wuce." Yana rike da
kunnan ya kai ta kofa, suna dariya. Ta tsaya ta
ce,"Amarya ya kore ni, sai da safe kenan."Ita dai
ta kasa magana, sai dariya. Zarah ta ja kofa."
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Ya tsaya ya k'are mata kallo, sannan ya sauke
numfashi. Ya tako a hankali ya tsugunna
gabanta, suka dubi juna, ta dan kauda kai, tana
murmushi. A natse ya kwantar da kan sa bisa
kafafuwanta, ya nisa yayi dan shiru. Haka ita
ma take kallon sa idanuwanta suka kawo kwalla.
Bata san lkcn da ta dora kan ta bisa bayan sa
ba. Sun jima shiru haka kafin ya ce,"Na gode
Allah, na sake gode masa daya nuna min
wannan rana. Haka kuma na gode wa Abba
daya sake mallaka min ke. Na yi kuskure gare ki
Nusaiba wanda baya misaltuwa, ba na kuma
son tuna su. Ki yafe min Nusaiba. Ta
ce,"Tuntuni na yafe maka yayanmu. Ya wuce."
Ya dago ya ce,"Na gode." Kin san wani abu? Ta
kada kai. Ya lalibo aljihunsa ya dauko kudi, ya
kamo hannun ta ya dora mata, ta ce "Na
menene? Kudin ki ne, canjin ki dubu 15 da ki ka
ba ni a asibiti. Ta saki baki tana kallon sa,"Kai
yayanmu, shekara 2 da rabi? Ya sake kwantar
da kan sa, ya ce,"Ba zan ta6a mancewa da su
ba Nusaiba, domin daga ranar da ki ka miko
min su. Allah ya manna min son ki a raina. A
lkcn ba wai ba ni da su ba ne, amma ba su da
amfani, tunda ban san yadda zan yi in ciro su
ba. Alhalin ina matukar bukatar su. Da gaggawa.
Kin min abinda ba zan ta6a mancewa da ke ba
rayuwa, kin taimake ni a lkcn da na wulak'anta
ki na.......... Ta rufe bakin sa."Na ce ya wuce
yayan mu, ka daina tunawa."
Ya dube ta ido cike da kwalla,"Kar ki yi
kokwanto Nusaba, Ina son ki! Ina son ki!! Ina
son ki Nusaiba!!!
Ta ce ,"Na sani." To kice kina so na in ji, ko sau
1 ne."
Ta yi dan murmushi ta ce, "Ina son ka yayan
mu.
Ga kuma kudin ka har canji na bar ma ka."
Yahayo shimfidar sosai, ya ce,"Kin saye baki na
ke nan? Ta yi 'yar dariya,"Na siya."
To me ki ke sha'awar sha? Ta
ce,"Uhm.......Cock, irin mai dan inabin nan. Ka
gane ai? Ya tsura mata ido, tana masa dariya.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaman lafiya mai ban sha'awa ga kowa ya dore
a gidan Naseer. Hankalinsa kwance, ba shi da
matsala. Ya k'are Digirinsa. Shine gwarzon
shekara, wanda ya fito da ajin farko a fanni da
yake karanta, sannan ajin farko cikin jerin
wadanda suka zo na farko a sauran kwasa-
kwasai a wannan shekara.
Don haka yana daya daga cikin masu rubuta
jarabawar tantance masu tafiya Turai don karo
ilimi tare da tallafin gwamnati. Kowa yayi masa
murna. Shi kan sa ganin abin yake kamar a
mafarki. Allah yayi gaskiya ya ce tashi in
taimake ka.
Tabbas hake ne, Naseer ya ga Zahiri.
A Kaduna suka rubuta jarabawa 'yan makwanni
tsakani sakamo ya fito.
Naseer ya haye ya ci Nasarar tafita Ingila.
Shirye-shirye ya kankama a lokacin cikin Nusaiba
ya fara tsufa, domin kuwa ya shiga wata na 7.
Ranar da zai tafi daren kasa barci yayi, saboda
tunanin shekara 1 ba zai ga iyalansa ba,
wad'anda ya riga ya aje su cikin ransa, baya son
kasancewa da kowa sai su.
A duk inda yake. Allah.Allah yake ya yi yadawo
gida, saboda tsabar son da yake musu.
Amma babu yadda zai yi, yana son ci gaba kuma
a yanzu ya tauna dadin karatu ya dandana ya
gane fa'idar sa. Kan dole ya dake zuciyar sa.
Washe gari karfe 8 na dare jirgi ya cilla da su
birnin Sarauniya. Sun kama karatu gadan-gadan,
amma kodayaushe cikin waya suke da iyalansa.
A haka watan haihuwar Nusaiba ya tsaya.
Umma ta sa ido sosai a kan ta, babu ranar da
bata zuwa Hanwa. Allah da ikonsa da safe ta
fara nakuda, ga shi Zarah na da jarabawa kuma
ta karshe ce, don kammala NCE din ta. Duk da
haka ta hada kayan haihuwa ta wuce da
Nusaiba asibiti.
Sai da ta tabbtar an shiga da ita dakin haihuwa
kafin ta kira Umma ta gaya mata asibitin da
suke.
Nan take Umma ta watsar da abinda take, ta
biyo hanya.
Tana isowa 8 dai-dai, sannan Zarah ta bar mata
Ameer, ta wuce jarabawa, ta iske an shiga, sai
da ta sha surutu, ta samu aka ba ta fefar.
Da namiji Nusaiba ta sake Haifa, lafiya lau daga
ita har Bebin.
Umma da Ameer na murna. Nan da nan ta kira
wayar Ummi, ta shaida mata ta sake sabon
ango....
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------





Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100





Ajinisa Yake3-06
Posted by ANaM Dorayi on 12:04 PM, 25-Nov-15
Under: Ajininsa yake
_______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______
Suka yi farin ciki. Ta lallatsa ta nemo lambar
Naseer.
Suna gaisuwa, kudinta suka kare.
Tir!
Haushi ya kama ta, sai ga shi ya kira,"Menene
Umma?
Ta ce,"Ka yi Da. Nusaiba ta haihu yanzu." Farin
ciki kamar yayi tsuntsu ya baro Ingila." Ina take
Umma? Ta ce,"Ai tana ciki ba su riga sun fito da
su ba, amma sun ce lafiya kalau suke ita da
Bebin."
Alhamdu-lillah! Allah ya amfana mana." Ta
ce,"Amin. Haka ya kasance cikin doki, kamar
yadda Zarah ke makaranta cikin zakuwa da son
ta koma wajen Nusaiba.
Kafin yamma gidan su ya cika da baki 'yan barka,
angon karni kuwa ya ki barin mai jego sakat da
waya, shi so yake ji kukan Bebi, "Bebi kuma ya ki
yin kukan.
Barcin sa kawai yake kwasa.
Ranar suna, yaro ya ci sunan Alhj. Haka kuwa
suke kiran sa(Alhaji) Ya ci gaba da girma tamkar
Ameer, shi yasa idan Naseer ya rufe ido, baya
ganin kowa illah 'ya'yan sa, tamakar 'yan 2.
Watanni 3 bayan haihuwar ta. Alh.Basheer zai tafi
harkokinsa Turai, ya wuce wa Naseer da hotunan
dan sa, ya gan shi. Hankalinsa ya kwanta. Ya cire
na Ameer daga firem ya zira wanda suke su 2.
An ci gaba, renan Naseer Jah-Jah. Shi kansa yana
mamakin kansa.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Kwanci tashi, shekara ta zagayo. Naseer ya dawo
cikin iyalansa, kamar yadda yake so. Bayan ya
huta sati 1. Alhj ya kira shi suka tafi bargar
dawakansa. Abin ya ba shi mamaki, irin
dawakan da ya gani suna harbin iska.
Sake da baki ya dubi Alhj yace "Abba za'a fara
wasa ne? Ya dafa shi ya ce,"Haka na ke zato,
idan na sami amincewar Jah-Jah."
Bakin sa har kunne ya ce,"Abba in dora sirdi in
hau? Yayi murmushi ,"Why not."
Ya kira mai kula da wajen, ya ce,"Je kawo sirdi."
Nan da nan ya dora Naseer ya haye jikin sa na
rawa ya zagaye bargar dawakan.
Kamar kar ya sauka, dokin yayi masa dadi."
Abba yaushe za'a fara? Ya ce,"Yau da yamma
za'a fara a tisaye, sannan akwai club guda 3 da
na ba takardar gayyata wasan sada zumunci.
DABAI ta dawo sabuwa."
Ya ce,"Insha- Allah kuma gagara gasar masu
gasa." Ya kamo shi suka nufo mota yana
fadin,"Akwai wani kokari da na ke maka, amma
ba zan gaya maka ko menene ba, sai Allah ya
tabbatar da abin, za ka ji.
Ka ci gaba da addu'a.
Allah za6a mafi alkhairi." Ya dan rankwafa ya
ce,"To Abba, na gode.
Allah ya saka da alkhairi."
Wasa ya kankama. (DABAI RIDERS) ta dawo
duniyar tseran Polo. Tutar Naseer Jah-Jah ta yi
sama ta neman ta wuce yadda take da can
baya.
Watannin 9 yana ketawa cikin kungiyoyin Polo,
yana ba su mamaki.
Kwatsam!
Abinda Alhj ke masa kokari ya samu. Ba wani
abuba ne, illa samun shiga shaharrariyar
kungiyar wasan Polo ta kasar Potugal.
Naseer fa kamar yayi hauka, don murna.
Haka Malam Balarabe, bai san abinda zai ce da
Alh.Basheer ba.
Kamar yadda aka bukace shi, daya iso 15 ga
wata, haka yayi sallama da kowa suka tafi tare
da Alhjn.
Sun gwada shi, sun ga iya kwarewar sa a zahiri
ko dama Alhj ya sha kai masu SD filet din
wasaninsa na gida da waje.
Kwarai sun gamsu da wasan Naseer, kuma da
alamun za'a samu da shi. Can Alhj ya baro shi
yana fafatawa cikin turawa.
A lokacin ne ya k'ara tabbatar cewa komai in ka
na da ilimi ya fi tafiya dai-dai, musamman a
wannan zamani.
An bashi gida da motar hawa. Naseer ya
kasance ba shi da wata matsala sai ta kewar
iyalan sa.
Ita ma sun kusa magance ta.
Cikin watanni 2 takardun zamansa dindin a
Potugal suka kamala, ya sami izinin shigowa da
iyalansa. Babu son kai. Zarah ce ta fara zuwa a
matsayin ta, ta babba. Ameer yayi kukan son
biyo ta, amma ina makaranta, ta hana.
Wai! Wa ya gane min Zarah a Potugal?
Ta shakata kwarai tsawon wata 1, ta koma
Nusaiba ta damk'o hanya. Haka suka kasance
suna yi wata guda-guda babu matsala balle
tashin hankali. Kowacce ta zo Naseer yana jin
dadin kasancewar tare da ita, bisa adalci da
tsoron Allah.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Shekara 5 Naseer yayi karfi sosai a k'asar
Potugal a fagen tseren Polo. Yayi farin jini kwarai
da gaske, kowa na son shi. Sau da yawa wasu
kungiyoyin na kawo masa cafka ta hanyar ninka
masa abinda yake samu, amma ya kauda kai,
saboda Alh.Basheer. Domin a halin yanzu arziki
sai dai ya ba wani, bai ma san iya wadanda
suke cin gajiyar sa ba a gida Najeriya.
Duk shekara idan ya je hutu. Bayan dawowa ba
tare daya buda wata cibiyar siye da siyarwa ya
zuba matasa sun samun abinci ba. Hatta Naseer
B dan hassada, ya saduda ya nemi gafara, ya
dawo yana cin arzikin da Allah yayi wa Naseer.
Yayi farin jini ba na wasa ba a Potugal, domin
har tallace-tallace yake wa manyan kamafoni ta
hanyar sana'arsa.
Ba kananan dololi yake kamawa ba, kowacce
talla yayi. A 'yan shekarun nan biyar. Nusaiba ta
hada 'ya'yanta 4 a gidan Naseer, 2 maza, 2
mata.
Hakika hankalin Naseer a kwance yake, kuma
Alhj ya lura karfi sosai a club din sa, tseren
dawaki sai dai ya ba 'yan baya tirenin. Saboda
haka yayi iya yin sa wajen Injiniya Ahmad Kaita
ta hannun sa ya samar masa a aikin yi ta
6angaran karatun da yayi, don kar ya tafi a
banza.
Allah mai ko! Takarda kawai aka ba Naseer ya je
inta-biyu ofishin(Internet Globl Services) reshen
Potugal, take nan suka yarda da takardunsa. Ya
sami shiga aiki. Duk da haka bai bar Polo ba,
amma ya zama na manya, wanda ake son tafiya
da shi, musamman a gagarumin wasan duniya.
A farkon wannan watan Zarah ce ke da zuwa
Potugal, a filin jirgi ya je ya dauko ta. Suka shiga
harkokin su kamar yadda

Please Login or Register in order to submit comment