Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

uwarta Hussaina. Shekaru uku da rasuwan matarsa kafin Mahaifinsa ya haɗa shi aure da Yahanasu wacce take marainiya a lokacin.

Lokacin daya auri Zainabu yaran Yaha uku ne duka mata. Aisha da suke kira da Ummi sai Fatima sai kuma Hindatu daga baya ne ta haifi Musa bayan ita Zainabun ta haifi ɗanta na fari wato Muhammad Habibu sai Lukman da suke kira da Gwani sai autanta Aliyu.



Sanda Zainabu ta tare ko wata huɗu batayi ba Malam Nuhu ya sata a makarantar kurame inda ake koya musu rubutu da karatu da kuma sana'o'i. A nan ne ta koyi ɗinki da saƙa.



Asiya Shahidah ta taso ne tsakanin gidan Gwani da Inna Talatu bata zuwa gidan Mahaifinta sai dai idan shine yazo ya ɗauketa dan Allah ya saka masa ƙaunar Asiya. Saboda ita ne ma ya dage da zuwa gidan Gwani duk bayan kwana biyu maimakon da da sai yai sati biyu uku bai leƙa mahaifin nasa ba. A duk lokacin da ya zo idan yaji Gwani yana yabon kwanyar Asiya akan tana ɗaukan karatu sai ya dinga jin wani nishaɗi a tattare da shi. Duk yaransa a wajen Gwani suke zuwa ɗaukan karatu tun suna shekara biyu da rabi yake sawa a tisa ƙeyarsu wajen Mahaifinsa. Kuma duk cikinsu idan ka cire babban ɗansa Nafi'u daya rasu babu wanda ya taɓa ji Gwani ya yabi kaifin ƙwaƙwalwarsa kaman yadda yake yabon Asiya. Wani lokaci idan yazo sai ya ce Asiya ta ɗauko Allonta ta biya masa karatu ya ji. Duk da idan ka cire karatun sallah shi kam Jahilin Ƙur'ani ne hakan bai hana shi jin daɗin karatun Asiya ba.

Allah ya buɗa masa arziƙi amma hakan bai hana wani lokacin ya ji kishin ƙannensa Malam da Zakari ba, wanda suma Malamai ne yanzu domin sunyi karatu mai zurfi.

Dake idan Asiya tazo gidan Ale Faruƙ damunsu take da rigima shiyasa basa ma son zuwanta gidan musamman Fulani da Tabawa. Bata taɓa yin shiru idan aka gaya mata magana.



Bayan Gambo tayi yayinta ta ƙare, lokacin maganinta ya dena ci, a lokacin ne kuma Ale Faruƙ ya lalubo musu wata mata mai suna Yawo. Daga chan wani ƙauye ta fito wanda ake yawan cewa ƙauyen akwai mayu a wajen. Ba budurwa bace dan aurenta bakwai amma tacewa Ale Faruƙ aurenta biyu. A rumfarsa suka haɗu ta zo siyayya, farar fatarta ya ja hankalinsa.





Sati biyu da tarewarta Ale Faruƙ ya fara ciwo. Idan ya tashi da safe sai yaji duk jikinsa na masa ciwo musamman hannu da ƙafafuwansa. Tun yana iya fita kasuwa har ya koma zaman gida saboda ko bai fita ba haka kawai jikinsa sai ya dinga ciwo. Ya je Asibiti an bashi maganin ciwon jiki amma duk da haka abun ba sauƙi.

Ana hakane kuwa biyu daga cikin 'ya'yansa suka rasu mace da namiji dukkansu 'yan ƙasa da shekaru goma. Abin duniya yabi ya isheshi, rashin fita kasuwa kamar yadda ya saba duk ya saka shi damuwa dan gani yake baza a kula masa da dukiyarsa kamar yadda ya kamata ba...



A gindin wata bishiyar giginya wasu mata guda uku suka haɗu a talatainin dare. Cikon ta huɗunsu ta taho tana basu haƙuri akan dalilin rashin zuwanta taron nasu da wuri.



"Ni kam Yawo keda kike da nisa ya akayi kika rigani zuwa?" Wacce ta zo yanzu tayi tambayar tana kallon farar cikinsu wacce duk da kasancewar dare ne sosai farin fiskarta na haskawa.



Yawo tayi dariya tace "ai dokina shegen gudu gareshi. Gashi chan na ɗaure shi a wancan bishiyar"



Matar ta juya ta kalli inda Yawo ta nuna mata sannan ta ƙyaƙyale da dariya tace "ashe zaki bani aronsa idan zan je taron mutanenmu da za ayi na ƙasa"



"A ina za ayi taron?" Wata tsohuwa tukuf a cikinsu ta tambaya.



"Wancan shekaran anyi a Kaduna ne amma wannnan shekaran a Ogbomosho za ayi"



"Kai yayi nisa ba zan je ba" tsohuwar ta faɗa tana lashe baki ganin naman da aka kawo musu wacce jaririyar Gambo ce da ko wata bata cika ba.



"Kai! Yawo gaskiya aurenki da Ale Faruƙ akwai daɗi. Kullum cikin ƙoshi muke"



Yawo ta baza haƙora tana dariya tace " nan gaba naman wancan 'yarsa daya fi so zan kawo, nasan ba ƙaramin daɗi za ta yi ba"

Dukkansu huɗun suka bushe da dariya marar daɗin ji.



Washegari Asma'u 'yar Gambo ta rasu. 'Yarta ta biyu kenan a gidan Ale.



Da yamma Mama da Asiya da matar Baffa Malam suka zo ta'aziyya gidan.



Suna falon Gambo Yawo ta shigo gaishe da Mama. Suna haɗa ido da Asiya ta fara mata murmushi. Asiya ta ce " Maman Rabi'u ga wadda ta cinye miki Asma'u" gaba ɗaya sai suka maida dubansu ga Yawo da Asiyar ke nunawa.

Yawo ta kama salati tana salallami harda fashewa da kuka.



Mama ta kwaɓi bakin Asiya tace "bana son shegen surutu Asiya. A ina kika ji wannan banzar maganar?"



Asiya ta tura baki tace "in ta cinye duka 'ya'yan Baba ai shikenan, nikam bazata iya cinyeni ba"



Mama ta ranƙwasheta tace ta rufe musu baki. Sannan ta shiga bawa Yawo haƙuri.



Maganar ta tsaya a ran Mama shiyasa da suka koma gida tace zata faɗawa Gwani idan ya dawo daga tafiya.



Ranan da dokin Yawo ya je Ogbomosho washegari Ale Faruƙ ya tashi ko yatsarsa baya iya ɗagawa. Yadda ka san wanda jikinsa ya shanye haka yake kwance a sanƙare ko'ina yana masa ciwo kamar anyita dukansa da taɓarya.



Bayan kwana huɗu da rasuwan Asma'u Gwani ya dawo. Da ya huta Mama ta gaya masa abinda Asiya ta faɗa, tareda faɗa masa cewa ranan da suka dawo, da dare Asiya ta dinga sunbatu cikin baccinta tana cewa babu wanda zai iya cin namanta.



Gwani ya ɗau Allo ya rubuta ayoyin shifa ya wanke da ruwan zamzam ya zuba a gora ya miƙe da kansa ya wuce gidan ɗansa.



Lokacin daya isa gidan kai tsaye sashin Ale ya shiga inda Ale Faruƙ ke shimfiɗe a kan tabarma a tsakiyar falonsa. Fulani da ɗansa Bello wanda shine babban ɗansa namiji ya gani a kusa dashi suna ƙoƙarin bashi kunu.



"Ya jikin nasa?"



"Yau kam Malam ko hannunsa ya kasa ɗagawa" Fulani ta amsa cike da tausayawa mijinta wanda duk yadda yake tana sonsa a haka.



Bello ya taimakawa Gwani wajen bawa Ale ruwan rubutu. Bayan ya sha, Gwani ya karanto addu'o'i ya tofa a hannunsa ya shafa masa a goshi, hannu da ƙafafuwansa. Da yamma ma yazo yai masa haka, washegari ma ya sake zuwa yai masa haka safe da yamma.



A rana ta uku kuwa da Yawo ta tashi hawa doki zata je majalisansu doki ya ƙi tashi, tayi tayi amma inaa ya ƙi ko matsawa gefe hakan ya sa ta haƙura da ɗaukansa. Da ta isa majalisa ta kai ƙorafin abinda ya faru wajen shugabarsu tsohuwa Ayya. Ayya tace ai mahaifin Ale Faruƙ ne ke shirin ɓata musu aiki kada ta bari ya sake zuwa wajensa. Naman Asiya ma da suke son ɗauka shima abin ya gagara shiyasa suka koma kan ƙanwarta Farida 'yar Halime wacce nan da kwana uku zasuyi abincin dare da ita.



Washegari ya kama kwanan Yawo dan haka ita ce ta kasa ta tsare a gefen Ale Faruƙ. Ƙarfe tara na safe sai ga Gwani ya zo yiwa Ale addu'a. Yawo ta garƙame falon da kwaɗo ta zauna a dakalin ƙofar shiga falon, yana zuwa tace masa Ale na barci yace kar a tashe shi.



Gwani yace ta buɗe masa ƙofa ya shiga ya dubashi ba zai tashe shi ba. Yawo ta tura baki tace sai dai ya dawo wani lokacin. Yadda ta dage ba zai shiga ba ya sa ya juya ya tafi, cikin ransa yana tunanin tabbas maganar Asiya gaskiya ce. Da yamma tareda ɗansa Malam suka zo, nan ma a ƙofar falon suka tarar da Yawo tana zaune daram kamar da safe. Wannan karan sai da Iyani da Fulani suka leƙo suna cewa Yawo ta buɗewa Gwani ƙofa domin tunda ya fara yiwa Ale addu'a suka fara ganin sauƙi.



Tana cikin magana Malam ya fito da wata dorina ya tsura mata a jiki yana faɗin "ƙarya kike la'ananniya, ƙarya kike Mayya"

Yawo ta saka ihu tana kuka.

"Kin cinye masa 'ya'ya za ki cinyeshi ko? Asirinki ya tonu" ya cigaba da zaneta. Ƙoƙarin gudu take amma Gwani da sauran Matan da yaran Ale kusan biyar sun tare wajen sun hanata gudu. Bello ma daya shigo bada jimawa ba itace ya sunkuco ya shiga taya Baffan nasa dukan Yawo.



Sai da Gwani ya tsaida su kafin suka dena dukanta. Ya tambayeta ta faɗa musu gaskiya. Yawo baki da hanci duk jini ta fara cewa ta tuba a yafeta.



Baffa Malam ya daka mata tsawa hakan yasa ta fara faɗan abinda tayi tace da gaske ne ita ta cinye yara uku a gidan amma Ale Faruƙ doki take da shi bawai cinyeshi zata yi ba.

Tabawa da ke gefe tayo kan Yawo da gudu ta fara dukanta tana yaguni. "Shegiya ɗan nawa shine doki, ɗan nawa kika mayar doki"

Da ƙyar Baffa Malam da Bello suka janyeta akan Yawo.



Gwani yace su ɗaureta kar wanda ya sake taɓata amma ina, samarin anguwa sukace basu yarda ba aka fita da Yawo ana bugu. Lokacin data suma aka fara ƙoƙarin ƙonata saiga wata tsohuwa ta ratsa cikin mutane ta zo ta taɓa Yawo shikenan ita da Yawo suka ɓace. Mutane kowa yai ta kansa sai 'yan tsiraru da suke da ƙarfin zuciya suka tsaya suna ihu suna faɗin duk ranan da suka kama Yawo ko wani maye ko mayya a garin ƙonashi za suyi.



Kwana uku da aka cigaba da yiwa Ale Faruƙ addu'a ya warke sarai kamar ba shi ba. Lokacin da yaji labarin cewa Asiya ce ta fara gane cewa Yawo Mayya ce hakan ya sa shi dagewa Gwani akan sai dai Asiya ta dawo gidansa da zama. Gwani bai musa ba tunda dai 'yarsa ce ya dai jaddada masa akan koyaushe Asiya ta dinga zuwa karatu.



Bayan Yawo sai da Ale Faruƙ yai shekaru huɗu kafin ya ƙara wani auren.


*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....







*©Azizat Hamza*



wattpad Azi_zat





Bismillahir Rahmanir Rahim









Book one



11







Dr Saifuddeen Sa'ad Kachallah saurayi ne mai kimanin shekaru ashirin da bakwai a duniya. A rana ta farko daya shigo jami'ar Congo a matsayin malami a ranan ƙaddararsa ta haɗu da ta Misturah Sulayman Adeyemi.



Da ya gama duk abinda zaiyi a ranan sai ya tattara kayansa ya wuce wajen motarsa. Ishirwa yake ji hakan ya sa shi wucewa wani kiosk da ake saida kayan masarufi da ke kusa da shi.



Yace da yarinyar da ke tsaye a shagon ta bashi ruwa mai sanyi na gora, yarinyar tace babu sai dai na leda. Saifddeen ya ɗan gyatsine fiska sannan ya ce "ok kawo"

Yarinyar ta miƙa masa ruwa guda biyu a leda, lokacin ne kuma wata budurwa baƙa ta iso kiosk ɗin ta ajiye litattafanta akan kantan wajen tana huci tace "Abeg Bisi give me cold water"

Ya kalli budurwar da tayi maganar. Baƙa ce amma ba sosai ba tana da ɗan jiki amma ba zaka kirata ƙatuwa ba. Ɗan ƙaramin mayafin data yafa ta cire ta fara fiffita dashi saboda yadda take haɗa uban zufa, da gani ta sha tafiya cikin rana.



"Sista Mistura e take ye easy"





"Omo iya ko easy oo, Professor Badmus fe pawa, wahala re ti po"





Saifuddeen ya kauda kansa daga kallon budurwar ya miƙawa mai shagon naira ɗari biyu.





"Ha! Oga i no get change oo"



Ta kalli budurwar tace " abi Sista Misturah e ni change ke bami se?"





"E lo?"



"200"



"Haa! Kilo ra?"



"Omi meji"



Saifuddeen ya katse hiransu da cewa " i'll come back for it tomorrow"





"Ok Sir"



Har ya juya ya fara tafiya sai ya dawo. Ba lallai ya tuna da chanjin ba gara kawai ya sayi wani abin ya bar mata sauran.

Bayan ta miƙa masa coke mai sanyi daya buƙata yace ya yafe mata sauran chanjin.





"Ode ni Bobo yi"

Budurwar ta furta a fili. Suna haɗa ido da Saifuddeen tayi saurin kauda kai dan gani tayi kaman ya ji abinda tace.



Bayan tafiyar Saifuddeen ita da mai shagon suka yi gulmar shi inda Baƙar budurwar ke cewa Saifuddeen irin sabbin ɗaliban nan ne masu rawan kai da burga.




Kwanansa biyu da fara aiki inda ya ke ɗaukan ɗalibai 'yan aji uku da 'yan aji huɗu sai kuma masu yin masters.

Bai saba cin abinci a waje ba amma takanas Dr Hassan da office ɗinsu ke kusa yazo ya ja shi akan suje cin abinci.

Canteen ɗin da suka je na wasu yarabawa ne, daga bakin wajen an rubuta *Iya Bola's Food*



Ba laifi wajen ya haɗu akwai tsafta amma duk da haka dan ta Saifuddeen ne ba zai ci abinci a wajen ba.




Bayan an serving ɗinsu abinci suna ci ya hango baƙar yarinyar ranan tana serving wasu abinci. Dr Hassan ne ya fara cinyewa inda ya ce da Saifuddeen zai wuce aji yanada ajin ƙarfe biyu. A lokacin bai san halin Dr Hassan bane ya jawoka cin abinci yatashi ya bar ka ka biya masa. Saifuddeen ya cigaba da cin abinci ahankali, lokacin daya gama ya zauna saboda wajen da ake biyan kuɗin a cike yake da ɗalibai, gaskiya wajen ana ciniki.

Yana zaune baƙar yarinyar tazo kwashe masa kwanuka.

"How much?" Ya faɗa a hankali




"400"



Arhan abincin da ya ji ya sashi ce mata na duka biyu yake nufi. Ta kalli ƙwayar idonsa sannan ta kauda kai tace " still 400"

Chanjin naira ɗari zata bashi amma yace ya yafe mata ya miƙe ya bar wajen ya bar Mistura da buɗe baki.




A ranan daya sake zuwa wajen shi ɗaya ya zo Mistura na ganinsa ta zo wajen da sauri

"Mr keep the change what can i serve you?"



" jolof rice and fish"




"With Dodo abi with chips?"



"What's Dodo?" Ya faɗa bil haƙƙi saboda bai sani ba.



Baƙar yarinyar ta ƙyalƙyale da dariya harda kama baki.



"Oga Ajebo, dodo is fried plaintain"



" Ok with Doodoo" ya ja sunan kamar dodon tatsuniya.



Lokacin da ta kawo abincin ta tambayeshi ko a aji ɗaya yake sannan a wani faculty.

Jin yace shi ba ɗan aji ɗaya bane ya sa ta tambayi ajinshi. Yai shiru yana kallonta saboda kamar kowa itama tunanin ɗalibi take masa. Ko ranan daya fara shiga aji ma ɗalibansa kallon raini suka masa sai da suka ji yace shi zai ɗaukesu darasi sannan jikinsu yai sanyi.




Lokacin da ta kawo masa abinci ta tambayeshi sunansa. Ya amsa da cewa

"Saifuddeen"

"Misturah, 400 lvl Economics. Tunda ka ƙi faɗamin wani aji kake, i can bet cewa ba zaka wuce 100lvl zuwa 200lvl ba"



"Miyasa kika ce haka?"



"Kana yi kaman wani JJC"



Saifuddeen yai murmushi ga mamakinsa sai ya ji tace " kana da kyau and i love your smile"



"Misturah...Misturah..."



"Maaa" ta amsa tana barin wajensa da sauri.



Cikin sati biyu da yai yana zuwa wajen sai gashi ya san komai nata. Shi kansa ya rasa dalilin daya sa ya zama regular a wajen kuma in har bata wajen ba zai ci abinci ba sai ya tabbatar tana nan kuma ita tayi serving ɗinsa.



Iya Bola mai saida abincin Ƙanwar Mahaifin Misturah ce kuma a wajenta ta taso tun tana shekara takwas. Ita ce ta ɗauki ɗauyin karatunta har yanzu da take final year.

Bai sanar da ita ko shi waye ba saboda ya sani yadda ta sake jiki da shi idan har ta san lecturer ne ba zata kula shi ba. Da bakinta tace masa bata mu'amala da malamai.

A sati na biyar da fara koyarwarsa aka bashi ajinsu Misturah. Farfesan daya ke ɗaukansu ya tafi wani conference na sati uku a ƙasar America.



Dr Kachallah ɗalibai da Malamai ke kiransa kuma sunan ba baƙo bane a wajen Misturah dan taji labarin tsaurinsa a wajen ɗalibai 'yan Pol science.

Lokacin da course rep ɗinsu ya gaya musu cewa Dr Kachallah ne zai ɗauki darasin Prof Badmus ta ji daɗi saboda ta tsani Prof Badmus, kowa ma a ajin ya tsaneshi domin yadda fiskarsa ke da muni haka zuciyarsa take. Yanada tsauri, baya sassautawa ɗalibai ko kaɗan gashi ba wai ya iya koyarwa bane dan ba a gane darasinsa.



Abinda Misturah ta sani gameda Dr Kachallah shine shi ɗin sabon Lecturer ne kuma yaro, dan sun ji ƙishin-ƙishin ɗin ko shekaru talatin bai kai ba sai dai akwai kwanya.



Lokacin daya shigo tana ƙoƙarin karanta wani journal ne da ya ke da nasaba da project topic ɗinta. Nitsuwar da ajin yai ya sa ta ɗago idonta car acikin na Saifuddeen da ke tsaye a wajen podium na ajin.



Da muryarsa mai sanyi yai bayani akan shi zai cigaba da ɗaukansu darasin Prof Badmus kafin ya dawo.



Sunan daya rubuta akan allo ta ƙurawa ido, da manyan baƙi ya rubuta *SAIFUDDEEN SA'AD KACHALLAH*



Sun gane darasin da yai musu sosai, sai dai matsalarsa ɗaya wato yawan jefo tambaya idan yana bayani. Haka kawai sai ya nunaka ya tambayeka wani abu sannan baka isa kace baka sani ba dan shi a ajinsa babu kalmar i don't know. Ya fi so ko baka sani ba ka yi abinda bature ke cewa attempt, dole sai ka faɗi amsar a naka fahimtar.

Misturah kam kasa nitsuwa tayi dan gani take idonsa na kanta ko kuma idan yai tambaya ya nuna mutum yace YOU gaba ɗaya sai ta ji ƙirjinta ya buga dan gani take kamar ita zaice.

Basu taɓa fahimtar darasin Prof Badmus irin na yau ba. Daga su 'yan Economics har 'yan Political science da suke yin darasin tare kowa ya yarda akwai banbanci a koyarwar Dr Kachallah data Prof Badmus nesa ba kusa ba.

Daya gama darasi ya bada damar ayi tambaya yawanci matan ajin suka dinga ɗaga hannu suna masa tambayar shirme dan dai kawai ya kulasu.



Kamar kullum bayan yayi sallar Azahar Iya Bola's food ya wuce ya samu waje ya zauna yana jiran Misturah sai dai ko mai kama da ita bai gani ba. Kwana uku ya jera yana zuwa wajen baya ganinta. A rana ta huɗu sai ya zo da wuri ya kuwa ci sa'a tana nan.



"Sir mi za a kawo maka?" Tayi tambayar kamar a yau ɗin ne ta fara ganinsa.



"Misturah ya kamata muyi magana..."



"Munada Semo, sakwara, Amala, Eba, white rice, jollof rice..."



Miƙewa yai ya bar mata wajen, ta bi bayansa da kallo cike da mamaki.

Daga ranan bata sake ganinsa ba dama gudunsa ta fara yanzu kuma sai ta fara dakon zuwansa amma shiru. Idan yazo ajinsu kuwa ko gefen da take baya kallo hakan yai matuƙar damunta. Wasa wasa gaba ɗaya ta rasa nitsuwarta.

Bayan sati ɗaya da yin hakan ta kasa ɗaukan shirunsa, ta kasa ɗaukan sharewar da ya ke mata.

Ta nemi inda office ɗinsa yake ta je ta sameshi dai dai zai fita ya tafi gida.



"Sir kayi haƙuri ranan..."



"No no no, ba laifin ki bane. I should have told you the truth tun ranan da kika tambayeni a wani aji nake"



"Kenan baka fushi dani?"



Sai da ya ɗau jakarsa sannan ya ce " na baki space ne saboda kince bakya son kowacce mu'amala da malaminki. A da ni ba malaminki bane amma yanzu..."



Sai bayan sati huɗu daf za a fara exams da Prof Badmus ya dawo ya karɓi ajinsa tukunna Misturah ta sake jiki da Dr S S Kachallah. A lokacin da su kayi hutu lokaci zuwa lokaci ya kan je gidansu. Tun Iya Bola na mata faɗa akan mu'amalarta da Saifuddeen har tazo ta haƙura tunda ta nuna mata cewa ba soyayya suke ba sannan kamalar Saifuddeen ya sa Iya Bola ta fara yarda da shi. Gaba ɗaya kasancewarsa ɗan babban gida bai sa mishi girman kai ba.



A wajen Misturah ne Saifuddeen ke iya sakewa ya faɗi son ransa yai abinda ya ga dama. A wajenta ya koyi cin abincin da yake da nasaba da ƙabilun kudancin ƙasar. A wajenta yake iya sakewa ya fayyace mata damuwar ransa, a wajenta ya samu ƙwarin gwiwar fitar da rubutunsa na waƙoƙi wanda ada sai dai ya rubuta ya zuba su a wardrobe. Dalilinta ya wallafa littafin rubutattun waƙoƙi da pen name Jabir Al Jabir yayi amfani da sunan na shekaru biyu kafin daga baya da suka rabu da Mistura ya koma amfani da suna KaSaSa.



Sai da Misturah ta gama aji huɗu tana jiran sakamako kafin Saifuddeen ya bayyana mata cewa yana sonta. Faɗuwa ne tazo dai dai da zama dan a wajen Misturah kam tun kafin ta san shi malami ne soyayyar Saifuddeen ya shiga zuciyarta.



Duk da ya san ba lallai bane a amince masa ya aureta kasancewa shi ba Bayarabe bane amma kuma ya ɗaura aniyar sai inda ƙarfinsa ya ƙare akan neman auren Misturah. Lokacin daya faɗawa Sikiru mijin Iya Bola cewa yana son ya turo magabatansa bai yi mamaki ba da yace masa sai ya nemi izinin 'yanuwansa a chan gida.



Letter Sikiru ya fara turawa chan garinsu ya musu bayanin waye Saifuddeen amma da aka dawo da amsa sai ya ga cewa wai basu amince Misturah ta auri bahaushe ba.

Mamaki ya kamashi dan da alama basu fahimci wani Kachallan yake nufi ba. Haka ya shirya ya wuce garin Akure. Lokacin daya fayyace musu asalin wanene Saifuddeen Kachallah mantawa sukayi da batun kudu da arewa suka ringa kiran ai Nigeria ɗaya ce kuma ya kamata a daina nuna banbance-banbancen ƙabila ko yanki. Cikin kashi ɗari na danginsu kashi tamanin da biyar sun amince da auren bayan sun ji kuɗi da mulkin gidan da Saifuddeen Kachallah ya fito.



Bayan Saifuddeen ya samu amsar daya ke so daga wajen Sikiru sai ya gabatar da buƙatarsa na son auren Misturah wajen Alhaji Sani. Ga mamakinsa sai yace masa ko zai auri wata mace to bayan ya auri Bilkisu ne, dama jira yake ta ƙarisa jarrabawarta na ƙarshe ta dawo ya haɗasu aure.

Ba zai taɓa iya yiwa Baba musu ba shiyasa ya amince da hakan. Sun taso da Bilkisu kuma tsakaninsu akwai jituwa sai dai bai taɓa sawa ransa zai iya auren mai irin halayen Bilkisu ba. Girman kai, Shagwaɓa, kasala, zafin rai da ma ra'ayin ƙin talaka sune halayenta da suka sha banban da tashi. A matsayin 'yar uwa yana sonta amma a matsayin matar aure gaskiya...



Lokacin daya faɗawa Misturah hukuncin da aka yanke masa ranta ya ɓaci sosai har take ce masa dama halinsu kenan 'yan arewa, gashi tun bai aureta ba yana mata maganar kishiya. Sai dai soyayyar Saifuddeen ta rufe mata ido shiyasa ta amince zata zo gidansa a matarsa ta biyu.



Wata ɗaya da rabi Bilkisu ta shigo Nigeria, tazo ta tarar da tsarin da aka shirya mata. Za ayi bikinta da Saifuddeen nan da watanni biyu sannan za ayi na Misturah da Saifuddeen wata bakwai bayan aurensu lokacin Misturah ta gama bautan ƙasa.



Da soyayyar Saifuddeen ta taso kuma tun kafin ta tafi jami'a ta riga ta sanar da mahaifinta cewa idan ya haɗa aurenta da wani ba Saifuddeen ba bazata aure shi ba.

Lokacin data tsara rayuwar aurenta bata tsara cewa za tayi tareda wata bare ba. Ita da Saifuddeen za su gina rayuwarsu kuma babu wacce ta isa ta shiga tsakaninsu.



Sati biyu bayan ta iso Nigeria tasa aka fara yiwa Misturah transfer daga inda take bautar ƙasa kusa da Jahar Congo zuwa chan kudu.

Bata taɓa ganin Misturah ba sai ranan data je gidansu ta kai mata letan relocation ɗinta tareda kashedin duk ranan data sake shigowa Congo saita sa an yankata sannan idan har bata sa an kashe maganar aurensu da Saifuddeen ba zata sa a kashe Iya Bola da iyalenta, ba nan ta tsaya ba har Akure tace za ta je tasa a ƙona family house ɗinsu da duk wanda ke ciki.

Dama anacewa Yarabawa da tsoro. Tuni Iya Bola da Sikiru suka shiga bata haƙuri yayinda Misturah ta riƙe takardan da aka miƙa mata tana furzar da numfashi mai zafi...



Ƙila Saifuddeen ba zai taɓa sanin dalilin tafiyar Misturah ba domin ranan daya je hira gidansu wasiƙarta Iya Bola ta bashi inda a wasiƙar Misturah ta bayyana masa cewa ba zata iya zuwa gidansa a ta biyu ba. Daren ranan duk yadda ya daure sai da yai hawaye saboda Misturah itace macen daya fara so a rayuwarsa. Bai nemeta ba kuma har bayan ya auri Bilkisu bai nemi inda Misturah take ba saboda shi mutum ne da baya son takurawa ɗanuwansa. Duk da yana sonta sosai amma hakan ba zai sa shi tursasa mata ba. Sai da shekaru suka ja kafin watarana daya haɗu da wata ƙawar Misturah ta gaya masa cewa Misturah tayi aure

Please Login or Register in order to submit comment