Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana faɗin ba zai yiwu ba, babu wanda ya isa ya tsige Saifuddeen matuƙar yana raye.

Yana gama waya ya kira Mr Paul yana masa kashedi akan indai shine ya haɗa hannu da Umaru Kwom dan a tsige Saifuddeen to ya sani ba su isa ba. Ba a taɓa tsige Gwamna a jahar Congo ba kuma baza a fara akan ɗansa ba.



Mr Paul ya saka dariya yana faɗin miye abin tsoro idan har ya san Saifuddeen bashida abin aibu. Ai trial za a fara idan ya kare kansa bisa duk zargin da za ai masa ai shikenan.

Alhaji Sani ya kashe wayar ya kira Yallaɓai, nan ma nunawa yai duk wanda yasa aka tsige Saifuddeen sai ya ga bayansa a jihar. Yallaɓai ya kwantar masa da hankali akan indai ya yarda da Saifuddeen to ai babu mai tsige shi a kujerarsa.



Da wuri Gwamna ya isa gida yau, ƙarfe huɗu da rabi yana falonsa. Bilkisu ya kira yace ta sameshi a falonsa. Yana zaune ya miƙe ƙafafuwansa akan table wayarsa ta fara ƙara, yana ganin sunan Attaruhu yai murmushi sannan ya ɗauka.



"Your Excellency Ummata ba ta da lafiya, na taho gida tun ɗazu. Idan ba matsala ina so na kwana a gidanmu"



"Ba matsala"



Ƙiit ta kashe wayar.



Ba dan Abba da yace bai yadda ta kwana ba ai ba abinda zai sa ta kira Gwamna ta nemi izininsa. Ta kusa ta daina amsa sunan matarsa balle ace komai za tayi sai ta tambayeshi.



Minti ishirin yai yana jiran Bilkisu saboda bata gida lokacin da ya kirata.



Tana shigowa gidan, Hansa'u da ke kallo a falo ta karɓi jaka da gyalenta ta wuce mata da shi ɗaki. Bilkisu ta ƙarisa sashen Gwamna.



Ta riga ta samu tabbaci akan babu wanda ya isa ya tsige mijinta shiyasa ta shigo gidan hankali kwance.



"Na san kin ji labarin Impeachment notice da aka kawo"



"Wahala kawai za su bawa kansu, ba wanda ya isa ya tsige ka"



"Ki fara tattara kayanmu, zamu koma asalin gidanmu"



"Wasa kake ko?"



"Zan yi resigning Bilkisu. Kin sani tun farko ba wai ina son harkan nan bane, ina yin komai ne saboda Baba. Munada komai Bilkisu kafin wannan matsayin babu abinda muka rasa na rayuwa. Bayan komai ya lafa dukkanmu zamu bar ƙasar nan. Nana, Mahirah, Junior duk zasu samu kulawar mu"





Bilkisu ta fara kallon gefe da gefenta sannan tace "akwai abinda ka sha ne kafin na shigo?"



"Bilkisu siyasa ba a jinina yake ba, i'm failing the people, i'm failing my family. Ki duba yadda Nana ta lalace a ƙarƙashinmu because we are busy doing other things"



"Ba ka hau kujerar nan dan na zamo matar Gwamnan wata shida ba. Shekara takwas zan yi a matsayin nan kuma babu wanda ya isa ya ja da hakan"



"Bilkisu"



"Idan ka yi resigning gawata za ka zo ka tarar a gidan nan, ba inda zan je, siyasa kuwa yanzu ka fara dan wanda kayi a baya sharar fage ne"



Gwamna ya zubawa matarsa ido yana kallon yadda ta ke magana da izza kaman ta san gaibu.



"Suma masu son tsigekan muna nan jira muga da wani ƙaryar za su tuhumeka"





***



Umma tayi-tayi Asiya ta tafi gidanta ta ƙi. Kunyar 'yarta take ji wai sun je Asibiti tare ance musu ciki gareta. Bata san ciki gareta ba da ba za ta bari su je Asibiti tare ba. Yawan amai da zazzaɓi da take ji ta ɗauka malaria ce, ta ma siyi maganin malaria ta sha na kwana uku amma sauƙin sai a hankali. Ali daya shigo da rana ya samu tana sheƙa amai sai ya ji tsoro ya kira Asiya ya sanar da ita saboda Abba baya nan Inna Yaha ma ta fita.



Asiya kam ko ajikinta sai murna take yi za a haifa musu ƙani ko ƙanwa. Ta shiga kitchen ta haɗawa mahaifiyarta dambun couscous da ya ji kayan lambu da hanta.

Lokacin da ta kawo tare suka zauna, suna ci tana bata labarin wasu 'yan ƙauye da suka zo kwanakin baya wai su dangin Matar Gwamna ne. Suka zo su kusan takwas da tsummokaransu har da zabi da suka riƙo wai za su bawa Gwamna, da aka hanasu shiga suka ƙi tafiya suka tsaya a bakin gate, ƙarshe aka nemo Yaya Bello ya zo ya gansu yace bai taɓa ganinsu ba. Asiya tace abinda ya fi bata dariya wai su da Yafendon Tabawa uwa ɗaya uba ɗaya suke.

Umma ma sai da tayi murmushi. Asiya ta cigaba da gaya mata cewa kusan kullum sai an kirata ana ƙaryar dangi da ita. Akwai wadda tace ƙanwar Ale Faruƙ ce Asiya tace mata Ale ba shi da ƙanwa mace.



Bayan Isha Ya Ubayd ya zo gaida Umma. Sama-sama suka gaisa da Asiya kowa da abinda yake ji a zuciyarsa.



"Asiya we have to talk" ya faɗa yana nufin ta yiwa Umma bayani.

Umma dai ta yiwa Asiya kashedi akan ta sani ita ɗin matar wani ne dan haka ta kama kanta.

A ɗakin suka yi maganan nasu wanda ko Umma da bata jin abinda suke faɗa zai da ta zargi akwai matsala. Da ta tambayi Asiya mi suke faɗa Asiya ta mata ƙaryar magana suke akan bikin Faty da za ayi, tace sai anyi Kamu shi kuma yace ba za ayi ba. Umma tace mata ta bari yai abinda ya dace domin ya fita kusa da Faty.



Ubayd dai fita yai a ɗakin ransa ba daɗi.



*THE GOVERNOR'S WIFE*

...... MATAR GWAMNA....







*©Azizat Hamza*

wattpad Azi_zat







Bismillahir Rahmanir Rahim









Book one





19





Da dare kusan ƙarfe goma COS ya je wajen Yallaɓai, batun tsige Gwamna da ake shirin yi ya kawoshi. Ya sani Umaru Kwom ne da wannan shiri amma kuma yana da yaƙini akwai sa hannun Mr Paul a ciki.



"Yallaɓai baka ce komai ba. Kana so a tsige Saifuddeen ne?"





Yallaɓai yai dariya yace "Lamara kenan, kana ganin za su iya tsige shi ne?"



"Amma tunda suka fara maganar ai sun shirya wa abun ne"



" idan sun shiryawa abun ai Alhaji Sani Kachallah ma a shirye yake"





"Hakane kam, amma nayi mamaki da kace kada na faɗawa kowa cewa Asiya ta haɗa hannu da Umaru Kwom"



"Wannan rikicin cikin gida ne, mu zuba musu ido kawai"




"Yarinyar fa abin tsoro ce, kada gaba ta zo tana bamu matsala"



"Ina ganin akwai rawar da Asiya zata taka a gwamnati Saifuddeen Kachallah, The girl has Charisma"

Yallaɓai yai maganar yana shafa gemunsa.






***



Maganar tsige Gwamna da ake yi ya ja hankalin ƙasar kan siyasar jahar Congo. Ko'ina ka shiga maganar ake yi. Mutane da dama sun yarda Saifuddeen Kachallah mutum ne adali, yayinda wasu maganar albashin 'yan fensho da ba a biyaba ya sa suke ganin ya gaza.



A ɓangaren Asiya ko ɗar ba ta ji ba da Ubayd ya mata magana akan kada ta aikata abinda tayi niyya. So take ayita ta ƙare, ana tsige shi za ta nemi takardar saki idan ya ƙi bata kuma kotu zata kai shi a musu Khul'i.

Ba abinda zai sata farinciki sama da ta ji yau ance mata an tsige Saifuddeen daga muƙaminsa na Gwamna. Ranan ƙila sai ta zuba ruwa a ƙasa ta sha.



A ɓangaren Bilkisu kuwa ta rantse babu wanda ya isa ya tsige mijinta. Idan aka tsige Saifuddeen tamkar an mata tsirara ne a kasuwa.

Shima Alhaji Sani Kachallah ya shiga ya fita akan maganar dan har wajen party chairman na ƙasa yaje sun bashi tabbacin indai Saifuddeen bashida laifi ba wanda zai tsigeshi.


Wannan magana yasa Alhaji Sani ya gane akwai mutane masu fiska biyu, kai har uku ma a tafiyarsu, kuma da sannu idan ƙura ta lafa zai yi maganin 'yan banza.



Sun zaɓi ranan da Gwamna zai je buɗe stadium da aka gyara a matsayin ranan da za a wallafa dalilin daya sa za a tsige Gwamna. Lokacin da Umaru Kwom yace zai sa a jefi Gwamna Asiya tayi na'am da hakan. Duk abinda zai ƙasƙantar da Saifuddeen Kachallah to tana so.



Abinda Asiya bata sani ba shine, shirin da take da Umaru Kwom daban, shima shirin da yake da nasa mashawartan daban. Ita burinta ta ɗau fansa akan Gwamna Saifuddeen ne shi kuma burinsa ya hamɓarar da Saifuddeen saboda ya samu ƙarfin gwiwa a zaɓen da za ayi. Idan ya tsaya takara da Saifuddeen to ba makawa zai rasa kujerar amma idan da wani daban ne yana da yaƙinin zai ci zaɓe.






***

Ranan Asabat ƙarfe tara da rabi Gwamna ya fita daga gida zai fara zuwa Kachallah house kafin ya wuce Stadium.




Asiya ta zauna a ɗaki tana jiran komai ya tafi yadda aka tsara.

Ƙarfe goma saura kwata wayarta ya fara ringing, ta ɗauka da sauri ganin Fou'ad Salisu ke kiranta. Bayanin da ya fara mata ne ya sata miƙewa tsaye da sauri dan ta tabbatar dai kunnenta ya ji dai dai.

"Hello kina jina? Na ce ba Gwamna ke da wannan account ɗin ba. Alhaji Sani Kachallah ne. Account ɗin Sa'ad Kachallah an buɗeshi lokacin Gwamna yana shekara goma a duniya, bashi da masaniya akan account ɗin. Na gayawa Umaru Kwom amma ina ganin kema ya kamata ki sani"



Tabbas ta ji shi a karo na farkon da yai maganar. Ɗimuwa, kiɗima da gigicewa shine ya sa ta daskarewa a wajen.




Asiya ta tunɓuke ɗankwalin kanta ta yi cilli da shi lokacin da wayar da ke ɗare a kunnenta ya faɗo ƙasa.

"Na shiga uku ni Asiya" ta faɗa tana dafa ƙirjinta



*idan labarin nan ya fita, sunana zai kafa tarihi a duniya. Zai kafa tarihin cewa ni ce Matar Gwamna ta farko a tarihin ƙasar nan da na yaƙi mugun Gwamna na kawo ƙarshen sa*


Abinda ta faɗawa Ubayd kenan ranan da ya mata magana a kan abinda take shirin yi.



Kalamansa suka fara dawo mata filla filla a kwanyarta.



"Asiya ki dena abinda kike yi. Babu kyau. Gwamna adalin mutum ne, shi ɗan Adam ne, zai iya yin kuskure kamar kowa, ki masa uzuri. Kar ki manta fa MIJIN KI ne. Ko ban aureki ba Asiya har gobe ke ƙanwata ce, dan haka ba zan taɓa bari kiyi abinda zai jawo miki dana sani ba. Ki riƙe mijin ki da kyau ki dena ƙoƙarin hamɓarar dashi. Ki rungumi mijinki Asiya, we are not meant to be"




Ta durƙusa ƙasa ta ɗauki wayarta da sauri. Hannunta ɓari ya ke lokacin da take ƙoƙarin kunna wayar saboda ta mutu lokacin da ta faɗi ƙasa.

Wayar na kunnuwa ta shiga lalubo numbar Mr Bassey, tana danna numbar ta ƙara wayar a kunnenta, ga kowanne ringing da ke fita yana dai dai da dokawar da zuciyarta ke yiwa ƙirjinta yana ƙoƙarin barin mazauninsa.



"Hello. Mr Bassey. Kar a fitar da labarin nan. A dakatar da komai" ta faɗa da iya ƙarfin muryarta.




"Miya faru Hajiya?" Ya faɗa cike da mamaki bayan awa biyu da su ka wuce aka gaya mi shi cewa ya wallafa labarin.



"Dan Ubanka na ce a dakatar da komai, komai na ce"



Ɗif dodon kunnenta ya buga saboda dena jin komai da ta yi na wasu daƙiƙu. Lokaci guda ta yi fatan inama kaman Umma Allah yayi ta marar ji marar magana.



Durƙusawa ta yi ƙasa, ƙafafuwanta da gwiwowinta su ka nitse cikin lallausan Italian carpet da ke ɗakin. A yanzu maimakon laushin carpet ɗin kaushin sa take ji, ji ma take kamar a cikin harawan dabbobin Umma ƙafafuwanta suke.



*" Hajiya, ai kusan minti talatin kenan da wallafa labarin a website ɗin mu da shafukan sada zumunta. Yanzu haka an fitar da jaridan kasuwa"*




Bata iya cewa Mr Bassey komai ba saboda aikin gama ya gama.



Idan labarin nan ya isa ga Gwamna zai yi bincike, ba za a daɗe ba zai gano cewa itace da wannan aikin, ita ce take yiwa jaridar Climax rubutu. Idan aka jefi Gwamna ba lallai ya san akwai hannunta a ciki ba, tunda yana da maƙiya dayawa zai ma ɗauka mutanen Umaru Kwom ne da wannan aikin. Amma idan ya san ta haɗa hannu da Umaru Kwom wajen hamɓarar da shi...



Ta sa hannu ta dafe ƙirjinta da tuntuni ya ke ta bugu da ƙarfi. Ɗumi ta ji a kumatunta hakan ya sa ta shafa wajen da sauri.

Karo na farko kenan tun zamanta MATAR GWAMNA ta yi hawayen danasanin abubuwan data aikata.



Idan komai ya fito fili sunanta a tarihi zai koma Maƙaryaciya, Mayaudariya kuma Munafuka.

Kyakykyawan fiskar Gwamna ta hango yana faɗin "Asya WHY?"



T V dake ɗakinta ta yi saurin kunnawa ta nemi remote ta lalumo tashar Hill TV dan ta san za su bayyana koma minene dalla dalla.

Daga wajen da ake kawo rahoton kai tsaye na buɗe filin wasan ƙwallon ƙafa da aka gyara suka yanke zuwa labari da ɗumi-ɗuminsa. An bayyana dalilin daya sa ake son tsige Gwamna Saifuddeen. Shekaru shabiyar da suka wuce ya ci zarafin wata yarinya lokacin da ya ke koyarwa a Jami'ar Congo.

Asiya ta zaro ido ganin abinda aka rubuta da kuma abinda mai karanto labaren ke faɗi wanda bai kama hankali ba. Ba abinda ta rubutawa jaridar Climax kenan ba. Ta yi saurin jawo wayarta ta duba website ɗin jaridar Climax ta ga suma labarin cin zarafin da Prof. Saifuddeen yai wa wata ɗalibarsa Lami Ninja suka wallafa. Kanta ya kulle dan abu daban ta rubuta abu daban aka wallafa. Wacece ma Lami Ninja?.



Ta nemo numbar Umaru Kwom ta danna masa kira, ba a ɗauka ba sai a bugu na uku.



"Alhaji Umaru ban gane abinda ake faɗa ba. Na ɗauka maganar kuɗi ake"



"Kuɗin Alhaji Sani ne ba nashi ba, ba za a tuhumeshi da wannan ba shiyasa muka nemo abinda zai hamɓarar da shi cikin sauƙi"



"Miyasa ba a gaya min ba, miyasa ka barni cikin duhu?"



"Siyasar kenan Yarinya " daga haka Umaru Kwom ya sa dariya ya kashe wayar.



Asiya tayi taga taga kamar zata faɗi.

Kenan Ubayd yayi gaskiya da ya ce zai iya yiwuwa duk abinda ake Gwamna bai sani ba, ƙila kisan Saminu Bacchi ma bai san komai akai ba.

"Ki yiwa kanki adalci Asiya, a iya zaman da kika yi da Gwamna Saifuddeen kinga alamar zai iya kisa saboda mulki, kinga alamar kuɗi da dukiya za su ruɗe shi?"

Tambayar da Ubayd ya mata kenan amma ta bari ƙiyayya da son zuciya suka sa ta amsa da cewa "eh, Saifuddeen Kachallah zai iya duk abubuwan daka lissafo"



"Ko kin san saboda ya kuɓutar da ke daga hannun Umaru Kwom ya aure ki. Abba ya faɗa min komai, kuma na yarda cewa saboda ya tseratar da rayuwarki ya aureki. He's protecting you Asiya. Umaru Kwom amfani da ke zai yi ya yar. Idan kika gama masa aiki juya miki baya zai yi..."



"Tatsuniya kenan Ya Ubayd, ni yarinya ce da zai kareni, wani irin kariya ne da ba zai iya bani ba har sai ya aureni?"



Dana sani ƙeya. Da ta saurari Ubayd ranan da duk wannan bai faru ba.



A iya zaman wata biyu da sati ɗaya da ta yi a gidansa ta zalunce shi, ya mata laifi, amma ita laifin data masa ya ninka nasa sau dubu.



Ta kai dubanta ga talabejin inda aka nuna Gwamna na buɗe Stadium daya gyara, hannunsa riƙe da Almakashi zai yanka ribbon ɗin da aka sa. Ta ƙura masa ido kaman yau ta fara ganinsa, tabon sallah da ya fito dal a saman goshinsa, dimple ɗinsa da ya ke lotsawa idan yana magana, sajensa da gemu da suka ƙawata fiskarsa. Bata taɓa yarda ba idan mutane na faɗa amma yau zuciyarta da idanunta sun amince Saifuddeen Sa'ad Kachallah yana da kyau.



Ta rintse idanunta lokacin da ta tuno cewa Umaru Kwom ya tsara za a jefi Gwamna da zaran ya gama hidimar buɗe Stadium.

Ta jawo wayarta ta yi abu na ƙarshe da take ganin zai fishsheta.

"Allah Sa'id ni" ta furta a hankali, ta kwanta kan gado ta fashe da kuka mai ɗaci...









A nan na kawo ƙarshen littafi na ɗaya a labarin Matar Gwamna.





*Shin za a jefi Gwamna?*

*Wani hukunci zai biyo bayan abinda Asiya ta aikata?*

*Ya maganar tsige Gwamna?.*

*Shin Hansa'u zata samu abinda take nema a wajen Bilkisu Kachallah?, wacece ma Hansa'u*

*Shin Umaru Kwom zai yi nasara akan Gwamna Saifuddeen?*

*Wacece Lami Ninja da aka ce Gwamna Saifuddeen ya ciwa zarafi lokacin da yake koyarwa?*

*Shin Gwamna zai iya yin gaban kansa kuwa? Ko dai Alhaji Sani ne zai cigaba da juya shi*

*shin Bilkisu Kachallah zata bari tauraron Asiya ya haska kuwa?*

*Yaushe Asiya za ta gane cewa ita ce Attaruhu?*

*Akwai yiwuwar soyayya mai daɗi tsakanin Gwamna Saifuddeen da Asiya Shahidah. Kuwa?*



*kaɗan kenan daga cikin batutuwan da za ku gani a kashi na biyu*

From 2g Hausa Novel

Compiled by Hausa Novels Online (Telegram Channel)

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment