Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sha ruwan zafi" yai maganar yana dariya

Abba ya dara yayinda Ubayd ya sunkuyar da kai yana kallon fiskar wayarsa wanda hoton Asiya ne a wayar, bai ɗago ba sai da yaji Abba yace " ka ji abinda Gwamna yace ko Ubaydullahi, sai ka zage damtse"




Gwamna ya kalli Ubayd sannan ya kalli Abba hakan yasa Abba yai saurin cewa "ɗana kenan Ubaydullahi wanda zai aureta nan da watanni kaɗan masu zuwa"



"Allah ya musu jagora"



Abba ya amsa da Amin. Ko sakan talatin ba ayi ba Sakatare ya shigo ya ce da Gwamna lokacin tafiya yayi. Gwamna ya miƙe yai wa su Abba sallama dan fita zasuyi da tawagarsa zuwa wani ƙauye da akace za a buɗe firamare school na farko a wajen...



Gwamna yana ƙauye Alhaji Sani Kachallah ya kira shi akan yana son ganinsa idan ya dawo.

A ofishin Gwamna suka tattauna sabon batun daya ɓullo wai Matar tsohon Gwamna tana son shigar da Gwamna Saifuddeen ƙara.



"Umaru Kwom ne da wannan aiki. Shegiya ko idda bata gamaba tana maganar shiga kotu" Alhaji Sani ya faɗa da ƙarfi.




"Ko sun shiga kotu Baba ba abinda zasu samu sai baƙin ciki. Saminu Bacchi died a natural dead. Ni da likitan mun tattauna kuma ya gaya min jininsa ne ya hau sosai, stress ya sa shi faɗuwa har..."



"Na san wannan Saifu. Abinda nake gujewa shine wannnan maganar zata ɓata maka lokaci. Zaka ɓata ƙarfinka wajen biyewa shirmensu sannan alokacin Kamfen zasu dinga ɓata maka suna da zancen. Mutumin da ke karkara idan aka ce masa Saifuddeen Kachallah ne ya kashe tsohon Gwamna ba zai nemi gaskiyar magana ba. Abinda zai yi shine shi da iyalensa ba zasu zaɓi Saifuddeen Kachallah ba. And kasan ƙarfin ƙuri'un 'yan ƙauye kuwa ?"



"Baba inaga gara su shiga kotun a gama maganar kawai sab..." sai yai shiru tunowa da yai yadda Abba ke ƙoƙarin risinawa lokacin da yake bashi haƙuri. Idan aka shigar da maganar nan kotu Asiya za ta shigo ciki kuma za ta iya zuwa kurkuku ko ta biya tara mai yawa idan bata iya kare iƙirarinta da shaidu ba.



"Kar ka damu zan yi maganin matsalar. komai zai warware"



***







Musababbin zuwanta China ba dan saro kaya bane sai dan ta ga Malamin taurari wato Tsu Zhang. Shekaru ishirin da suka wuce a garin New Haven, Connecticut ta ƙasar America lokacin tana karatu a Jami'ar Yale wata Ƙawarta mai suna Paula ta gayyaceta wani taro da za ayi na mabiya addinin Buddha, inda aka gayyaci Malamin addini wato Monk Tsu Zhang ya zo ya yi mu su Lakca. Bayan an gama lakcan Paula da saurayinta Simon wanda basu jima da shiga addinin Buddhancin ba suka nemi ganawa da Malami Tsu Zhang, ya ba su lokaci da adreshin wajen da zasu sameshi.

Bilkisu ba ta bisu ba lokacin da suka je ganinsa amma ga mamakinta da suka dawo Paula tace mata Tsu Zhang ya faɗi saƙo a bata.

"Yace kinada ƙaddarar matar babban mutum yace tauraronki zai haska tareda ta mijinki"



"Haka yace? Taya ya sani?"



Tambayoyinta kenan lokacin da Paula ta sanar da ita saƙon Tsu Zhang. Bata tuna da wannan batu ba sai ranar da aka rantsar da Mijinta a matsayin Gwamna. Godiya take son yiwa Tsu Zhang shiyasa ta nemi ƙawarta Paula wacce take aure a ƙasar Brazil. Paula ita ta bata addreshing Tsu Zhang a China.



Bata sha wahalar samun inda Tsu Zhang yake ba sai dai kuma sai da ta booking lokaci saboda yanzu Tsu Zhang ya tsufa baya karɓan baƙi sosai.

A wani tafkeken temple (wurin bautan gumaka) Bilkisu ta samu Tsu Zhang. Lokacin da aka kaita wajensa ta jima zaune tana jiransa saboda meditation da yake yi. Lokacin daya buɗe ido bai juyo gareta ba, daga inda yake zaune yana fuskantar ƙaton gunkin Buddha dake ɗakin yace " akwai wani tauraro daya fito a gefen tauraron mijinki. Yadda tauraronki ke haskawa tareda ta mijinki haka wannan tauraro zai dinga haskawa tareda shi har sai tauraron mijinki ya haskaka fiye da tunaninki. Idan kikayi ƙoƙarin disashe wannan tauraro babu makawa da taki tauraron data mijinki haskensu zai dinga disashewa. Ki sani taurari uku a waje ɗaya suna bada haske na ban mamaki "



"Ban gane ba..."



Hannu ya ɗaga mata hakan ya sa tayi shiru. An riga an gaya mata cewa Tsu Zhang idan yai magana baya ƙarawa sannan baya maimitawa.





Har ta bar temple ɗin hankalinta bai kwanta ba. Wani irin tauraro ne ya shiga tsakaninta da ta Saifuddeen?...





***





Abba daya dawo bai gayawa Asiya komai ba, ya dai yiwa Umma bayanin komai, tareda faɗa mata yadda Gwamna ya tarbesu da mutunci suka rabu ana raha. Ubayd kam ko gidan bai shigo ba dan har yanzu fishi yake da ita.



Umma ta bata shawaran ta je ta bawa Gwamna haƙuri amma har yanzu bata yanke shawaran zuwa ba. Gani take idan ta je kamar ta ƙasƙanta kanta a wajen Gwamna ne.



Haka dai ta dinga saƙa da warwara har dare. Ƙarfe takwas da minti Arba'in Ubayd ya kirata yace ta sameshi a waje. Da murna ta fita dan a ganinta ya sauƙo kenan.



"Kin ji cewa Sha'awanatu Bacchi zata shigar da ƙara akan kashe mijinta da aka yi?" Ya faɗa yana tsareta da ido.



"Na gani a newsline"



"Kin shirya shiga kotu dan kare kanki kenan?"



"Ya Ubayd..."



"Tambaya na miki"



" ban so haka ta faru ba"



"Abinda kike so kenan Asiya. Ina so ki sani cewa shari'arku ta tsaya a wajen gidan nan. Nothing should happen to my family Asiya, kada abinda ya samu Abba ko wani acikin gidan nan. Rigimarku ta siyasa ta tsaya chan nesa da mu"...





Washegari ƙarfe shaɗaya ta shirya ta wuce gidan Gwamnati. Indai baiwa Gwamna haƙuri shi zai sa Umma da Abba da Ubayd suyi farin ciki da ita to za tayi. Wunin jiya ko kallon kirki Abba bai mata ba. A duniyar nan babu Uban da take da shi daya wuce Abba. Ale Faruƙ haihuwarta kawai yai amma Abba shine Ubanta.



Tunda ta fito daga keke Napep zuwa shiganta Gate sai ɗaukan hotonta ake ta yi. Ta turawa Sakatare text jiya da dare bayan ta bar wajen Ubayd akan tana son ganin Gwamna kuma shi yace ta zo ƙarfe shaɗaya na safe.



Tana isa wajensa yace ta shige ofishin, Gwamna yana jiranta. Gwamna ne zaune tareda Alhaji Sani Kachallah lokacin data shiga ofishin.



" 'yar jarida mai ƙwazo" Alhaji Sani ya faɗa yana murmushi.



Asiya tayi saƙeƙe tana kallonsa.



"Bismillah, zo ki zauna ai wannan zama naki ne"



Ɗan ɗosanuwa tayi a bakin kujera ta dinga kallonsu ɗaya bayan ɗaya yayinda ta sha jinin jikinta saboda kwarjini da suka mata.



Alhaji Sani ya ɗauki kofin shayin da ke gabansa ya kurɓi kaɗan kafin ya kalli Asiya yace " akwai saƙon da za ki gani gobe. Tukwici ne daga gareni. Ina fata idan kin ga saƙon zai faranta miki rai sosai"



Haƙuri ta zo bawa Gwamna amma kuma ta kasa furta komai. Bata gane inda maganar Alhaji Sani ya dosa ba.



Da ƙyar ta iya haɗa kalmomi biyu tace "ban gane..."



"Idan kinje gida ki gaishe da mahaifinki"



Ba sai ya ƙara magana ba ta sani managarsa na nufin ta tashi ta tafi.



Gwamna baishe da ita uffan ba sai ma kauda kansa da yai gefe...



Daga gidan Gwamnati shagonsu ta wuce wanda tunda sukayi hatsari rabonta da wajen. Tana wajen Umaru Kwom ya turo mata saƙo akan ya kamata su haɗu

su tattauna. Ta tura masa saƙo akan yai haƙuri ba zata iya taimaka masa ba.



Saƙon Alhaji Sani Kachallah ya isowa Asiya ƙarfe takwas na safe lokacin tana shirin fita shago tunda yanzu ta bar aiki a Hill TV. Aliyu ne ya shigo ɗakinsu da gudu sanye da uniform ɗin makaranta.



"Miya sa baka tafi makaranta ba Ali?"



"Anty Shahidah wai kije yanzu-yanzu inji Abba" ya faɗa sannan ya ruga da gudu.



Hijab ɗin Umma dake kan gado ta saka sannan ta wuce falon Abba da sauri.



Tana zuwa ta ganshi ya ƙurawa TV idanu.



Baice komai ba dan haka itama ta maida hankalinta kan talabijin ɗin. Bayan minti uku sannan aka fara karanta labarin daya sakata riƙe kai. Hotonta aka nuna tana magana da wani security a bakin gate ɗin gidan Gwamnati sannan ga tanan tana ƙoƙarin shiga office ɗin Gwamna daga nan kuma sai aka nuna hoton wasiƙa zuwa ga Gwamna wanda sunanta da sa hannunta ke ƙasa. Mai karanta labaran yana karanta wasiƙar hawaye na zubowa a idon Asiya yayinda ilahirin jikinta ya ɗau rawa.

Cin mutuncin da za a mata kenan a ɓata mata suna.



Abba ya rage volume ɗin TVn sannan ya juyo ya kalli Asiya.



"Abba wallahi ban rubuta wata wasiƙa ba"



"Wanda bai ji bari ba ai zai ji hoho ko Asiya. Kin dai ji yadda 'yan siyasa suka juya labarinki"



"Na shiga uku"



"Kiyi addu'a Allah ya sa ya tsaya a iya haka. Idan kuma taurin kai da kika saba za ki yi to Bismillah"





Kafin ƙarfe goma na safe ko ina ya ɗauka 'yar jarida Asiya Shahidah Faruƙ Baba ta yiwa Gwamna tayin soyayyarta ne shiyasa ta yaɓa masa baƙin fenti da bai amince da ita ba. Hatta cikin rahoton data kawo tana aibanta SSK lokacin daya ke mataimakin Gwamna sai da aka nemo aka dinga yaɗawa.

Kowa a jahar sai tofa albarkacin bakinsa yake yi akan zancen. Wasu suce Asiya irin matan nan ne masu bibiyar 'yan siyasa amma shi Gwamna SSK babu ruwansa da harkan mata. Wasu kuma suce neman suna take yi saboda ta fitar da labarin da zai yi fice da ita a duniya amma dake Allah ba azzalumin bawa bane shiyasa asirinta ya tonu. Wasu kuma cewa suke akwai lauje a cikin naɗi ƙila an yiwa Asiya barazana ne shiyasa ta rubuta wasiƙar nan. Wasu kuma suna ganin 'yan adawa ne suka biyata dan ta ɓatawa Gwamna suna. Maganganu dai kala-kala.



Maganar shigar da ƙara da ake ta raɗe-raɗin Matar tsohon Gwamna za ta yi kuwa sai ya zo ya bi ruwa.

Lokacin da Likitan tsohon Gwamna yai bayani a gidan talabijin tareda fitar da report na gwaje-gwajen da akayiwa Gwamna Saminu Bacchi bayan rasuwarsa hatta Umaru Kwom sai da ya ji jikinsa yayi sanyi domin babu yadda za ayi ya samu nasara kan tuggun daya shiryawa SSK duk da kuwa ya yarda koda SSK bai sa an kashe Saminu Bacchi ba to Alhaji Sani Kachallah zai iya aiwatar da hakan.



A ranan wani Malamin addini ya fito yai bayani akan yarda da ƙaddara mai kyau ko marar kyau. Yai maganar cewa yana cikin rashin yarda da ƙaddara mutum ya fara bibiyar dalilin mutuwar wani. Gwamna Saminu Bacchi lokacinsa ne yayi shiyasa Allah ya ɗauki ransa abinda al'umma za su yi shine a cigaba da yi masa addu'a da shi da duk wanda suka riga mutuwa. Ita kuma Asiya Allah ya shiryeta.

A rana ɗaya tal sunan Asiya ya chanja zuwa maƙaryaciya. Washe gari da safe wani mawaƙi ya shiga studio ya sake waƙa yana yabon Gwamna yana aibata sunan Asiya.



Sai da Asiya ta gama shirya kayanta tsaf kafin ta wuce falon Abba, baya nan dan haka ta tura masa saƙo akan cewa zata koma gidan Baffa Malam.



Idonta yayi jaa duk sun kumbura saboda kuka. Umma ta goyi bayan shawaran data yanke data ce zata je ta zauna a gidan Baffanta har sai saura sati biyu bikinta kafin ta dawo...





***





"Your excellency inada magana"



"Bismillah Malam Baffayo"



"Yarinyar nan Asiya rayuwarta na cikin haɗari"



Gwamna ya zaro ido cike da mamaki.



" na samu labari daga majiya mai ƙarfi cewa mutanen Umaru Kwom suna son kasheta saboda a tada sabuwar fitina tunda wancan ta mutu"



"How could they, ina kaji wannan magana?"



Sakatare yace " Excellency a bar kaza a cikin gashin ta"



Lokacin daya bar office kai tsaye Kachallah house ya wuce wajen Alhaji Sani.



Bayan ya yiwa Alhaji Sani bayanin da Sakatarensa ya masa sai kawai ya ga ya ɓigire da dariya har da kakkautawa.



Ya sake baki yana kallon Baffan nasa.



"Wani lokaci Saifu kaman baka san mi ake nufi da siyasa ba. Ba abin mamaki bane idan sun yi niyyar kasheta saboda wata manufarsu, sai dai duk ta inda suka ɓullo ina nan ina jiransu. Har yaushe ma Umaru ya girma da zai ce zai ja dani"



Wani abu ya daki zuciyar Saifuddeen. Ana maganar kashe ran yarinyar da bata ji ba bata gani ba amma yana dariya. Ba zai taɓa bari a hallaka rai a rikicin Gwamnatinsa ba.



"Baba ba zan bari su taɓa lafiyarta ba balle ma har su kasheta matuƙar ina raye"



Alhaji Sani ya kalli SSK da alamar tambaya a bakinsa amma bai furta ba sai yace " kenan zaka aureta?"



"Baba ban gane ba" Gwamna ya faɗa cikin rashin fahimtar manufar Alhaji Sani Kachallah.



"Hanya ɗaya da zaka iya kareta kenan Saifu" Alhaji Sani faɗa yana cigaba da dariya.







WAIWAYE...




*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....







*©Azizat Hamza*



wattpad Azi_zat

Bismillahir Rahmanir Rahim









Book one





09









*WAIWAYE*



















Abu ne da muka sani cewa Allah zai iya jarrabtar mu ta kowani fanni na rayuwarmu. Zai iya jarrabtarmu ta wajen dukiya, lafiya, 'ya'ya, mata, 'yanuwa, iyaye da sauransu.



Asalin iyayen Lukman Fulanin Baroroji ne wanda basa zama waje guda su jima.

Lukman yaro ne da aka haifeshi da ƙusumbi (hunchback). Yana shekara uku mahaifiyar sa ta rasu wajen haihuwa. Matar uban sa da ake kira da Gaji ta ce ba za ta iya riƙe shi ba, shiyasa Uban sa ya damƙa shi wajen Yayar mahaifiyarsa mai suna Habbi. Yana cika shekara biyar a wajenta ta ɗauke shi ta kaishi wajen Malam AbdulWahab Falke Almajiranci wanda ya kasance Kawu a wajen mijin ta.





Tunda aka damƙa Lukman wajen Malam kuwa Mahaifin sa bai taɓa waiwayan sa ba har Allah ya ɗau ran sa, shekaru biyar bayan rasuwan Asiya mahaifiyar Lukman ɗin. Itama Inna Habbin sau ɗaya ta je ta duba Lukman daga nan ba ta sake zuwa ba har rai yai halin sa.







Malam Falke ya zamewa Lukman Uwa da Uba sannan Malami. Duk cikin Almajiran Malam, Lukman ya fi ƙoƙari da hazaƙa. Ya maida hankali sosai wajen karatu. Ɗan sarari da su ke samu da sauran ke watayawa cikin gari shi yana amfani da wannan lokaci ne yai ta ƙoƙarin rubutu a Allon sa.







Malam Falke Allah bai bashi 'ya'ya dayawa ba. Yaran sa biyar ne kacal sai kuma 'ya'yan da ya ke riƙewa. Huɗu daga ciki mata ɗaya kuma namiji. Kafin a kawo masa Lukman ɗansa namiji ya jima da rasuwa, dan shekaransa shida ya rasu bayan wata ƙaramar jinya.



Dayawa mutane sukan ɗauki Lukman a matsayin ɗan Malam ne saboda irin kulawar da Malam ke bashi.



A hankali da ya dinga lura da baiwar karatu da Allah ya bawa Lukman sai ya zamana ya fara ba shi karatu na musamman. Duk wani ilimi da ya ke da shi to yana ƙoƙarin ya ga cewa Lukman ya samu, yana ma sa tanadin zama magajin sa. Koyaushe baya rabuwa da yiwa Lukman Du'a'ul Fahmi.



Lukman yana shekara tara yai saukan ƙur'ani (tartil) yana shekaru shahuɗu yai haddar ƙur'ani kuma cikin watanni bakwai ya rubuta ƙur'ani da ka.

A hankali ya dinga haddace manya-manyan litattafai na addini. Yana shekara shabakwai Malam ya tura shi Borno wajen wani Babban Malami. Bai dawo ba sai da yai shekaru huɗu a chan. A sanda ya dawo ne kuwa ya tarar da Malam ya aura masa wata 'yarsa.






Rumaysa'u wacce aka fi kira da Tabawa ita ce auta cikin 'ya'yan Malam. Ita ce kuma Allah ya jarrabce shi da ita.

Saɓanin sauran yayyanta da su ka yi karatu sosai har su ka yi sauka tun ma kafin ya aurar da su ita fir ta ƙi karatun.

Bayan nan, ƙiriniya da yawace-yawace da ta tsirfata da tara samari ya sa ya ce zai haɗata aure da wani Almajirin sa. Tabawa ta ƙeƙasa ƙasa ta ce ba za ta auri Almajiri ba. Yayi yayi da ita ta ce ba za ta aure shi ba. Ƙarshe ma ta kai ƙarar sa wajen Maigari.




Malam ya haƙura ya aura ma ta wanda ta kawo ta ce tana so. Da ke babu albarkan iyaye auren dudu wata biyar su ka yi ya rabu ta dawo gida ta fara zawarci. Kafin kace me sunan Tabawan Malam ya sake zama tamkar waƙa a wajen samari da bazawarai.

Lokacin da Malam ya ce ta fito da miji sai ta nuna Chukudi a matsayin wanda ta ke so. Kasuwanci ya kawo Chukudi garin, ɗan kuɗin da ya ke kashewa Tabawa shine ya tsole ma ta ido har ta zaɓeshi a matsayin wanda za ta aura, duk da addinin su ba ɗaya ba, al'adar su ba ɗaya ba, uwa uba ba asan minene asalin sa ba.



Wannan karan da Malam ya hanata auren sai wayan gari aka yi aka ga ta gudu daga gidan. Ita da Chukudi aka neme su a gari aka rasa. Wannan cin mutuncin har kwantar da Malam yai, kamar ma ba zai tashi ba sai kuma bayan ya sha jinyar watanni sai gashi ya samu sauƙi amma baƙin cikin da Tabawa ta ƙunsa ma sa yana nan yana cinsa, kullum addu'ar sa gareta Allah ya shiryar da ita. Ya sha tsayuwar dare akan lamarinta sai dai ita ɗin wata jarrabawa ce da Allah ya ma sa.




Shekara ɗaya da rabi kafin Tabawa ta dawo gida. Ranan da ta dawo mutanen gidan da ƙyar su ka ganeta saboda lalacewa da ta yi. Bayan ta bi Chukudi zuwa ƙauyen su ashe niyyansa shine ya tsafeta yai kuɗi da ita. Da ƙyar Allah ya kuɓutar da ita daga kaidinsa, sai dai tunda ta bar ƙauyen ta rasa gane kanta. Ta jima tana garari kafin ta samu ta warke ta dawo wajen Babanta dan ta san nan ne kawai gatan ta.

Malam ya karɓeta ne da sharaɗi guda, za ta zauna tsakani da Allah da duk wanda ya aura ma ta. Kaman da gaske ta ce ta amince.

A take ya ɗaura ma ta aure da Lukman ya kuma tura wasiƙa akan Lukman ya dawo gida idan Malaminsa ya sallameshi. Bai samu dawowa ba sai bayan wata uku.




Kafin ya dawo Malam ya gyara ma sa ɗakuna biyu cikin gidansa inda anan za su zauna da Tabawa.



Lokacin da Malam ya sanar da Lukman maganar auren da yai masa ya sha mamaki sosai. Ya san halin Tabawa sarai kuma duk abinda ke faruwa babu wanda ba shi da masaniya akai. Ba wai ba zai karɓi zaɓin Malam ba ne amma yana tunanin anya kuwa Tabawa za ta zauna da shi?



Tsoronsa kuwa ya tabbata domin lokacin da Malam ya haɗa su zai mu su nasiha Tabawa ta ƙeƙasa ƙasa akan ba za ta auri Mai ƙusumbi ba. Ita duk zaman nan ta ɗauka ɗaya daga cikin manyan Almajiran Malam aka aura mata, bata san Lukman Maiƙusumbi ba ne.




"Baba ba zan zauna da Maiƙusumbi, Miskini, marar asali ba. Duk cikin Almajiranka ba wanda ba sa zuwa wajen 'yan uwan su lokaci zuwa lokaci amma wannan bai taɓa zuwa wajen na shi ba. Ƙila ma ɗan shege ne"



"Rumaysa'u!"




"Baba zan auri kowa amma banda shi Wallahi"



"Na fi ƙarfin Miskini" ta ƙara jadda masa kafin ta fice daga ɗakin Malam ɗin.




Duk ƙoƙarin da Lukman ya ke akan kada yai hawaye agaban Malam sai da hawaye su ka zubo ma sa.


Dai-dai yana gogewa da gefen hannun rigansa Malam ya ce "Lukman ka tashi ka je za a kawo maka ita yanzu"







"Malam ka yi haƙuri Dan Allah, tunda ba ta so a bari na sawwwaƙa ma ta"



Ran Malam cike da ƙuna ya ce " ka san Allah idan har Rumaysa'u ba ta karɓi auren ka ba sai na tsine mata"



Lukman ya zaro ido waje.



"Kai ne aka cuta da na haɗaka aure da mace kamar Rumaysa'u, na yi haka ne dan ko Allah zai shiryar min da ita ta hanyar ka"





A chan cikin gida kuwa Tabawa ta dinga faɗa wai a rasa wanda za a aura ma ta sai Maiƙusumbi. Wata Gwoggon ta da ke gidan ta fito ta dinga surfa mata masifa.

Yadda ta dinga kiranta da butulu shiyasa jikinta yai sanyi.

Duk da tarin laifuffukanta itakam ta ƙwammace ta zauna ba aure da ta auri Lukman Maiƙusumbi. Kusan shekaru biyu kawai Lukman ya ba ta. Tun suna yara ta tsaneshi. Yadda Malam ya ja shi a jiki ya maida shi ɗansa na dole ba ƙaramin ɓata ma ta rai ya ke yi ba.





Bayan Gwoggo ta ƙare mata faɗan ita da Kulu yayar Tabawan suka tarkaɗata zuwa sashen da aka gyarawa Lukman. Tabawa ta sa a ranta zata zauna ne zuwa abubuwa su lafa, nan da lokaci kaɗan za ta rabu da shi ko da ta ƙarfi ne.



Har ta fara bacci Lukman ya shigo ɗakin jikin sa a sanyaye. Umurnin Malam na ƙarshe kafin ya taho ne ya dagula ma sa lissafi.



"Wallahi idan har ba ka tare da matarka daren yau ba. Ban yafe karatun da na koya maka ba"



A gigice ya bar wajen saboda bai ga alaman wasa a wajen Malam ɗin ba.



Da lallami ya nemi Tabawa amma ta ƙi bashi haɗin kai wannan ya sa shi binta da ƙarfi ya karɓi haƙƙin sa. Ya sha tsinuwa a wajen Tabawa kam kafin ya gama saboda da farko ta rena ma sa kan cewa za ta iya ƙwatan kanta a wajen sa. Ƙaramin ruwa gareshi shiyasa ta ke ma sa kallon ƙashi da rai ba ta san yadda ya ke a bushe haka ya ke da ƙarfi ba.



Tun daga ranan kuwa ba abinda ya sake shiga tsakanin su. Iya kyautatawa yana yi ma ta amma itakam kullum cikin zagi da tsinuwar sa ta ke, tareda cewa ya saketa indai shi ɗan halak ne.



Awata na biyu da auren ta gane ciki gareta. Ta yi kukan baƙin ciki sosai dan haɗa iri da Lukman mugun abu ne a wajenta.



Wasu ƙulle-ƙullen magani ta nema ta sha wai dan cikin ya fita. Ba ta jima da shan maganin ba ta cika gidan da ihu. Iyaji Mahaifiyarta ta zo ta sameta cikin jini.

Kwanan ta uku a Asibiti kafin aka sallameta. Sai da su ka dawo gidan ne ma Iyaji ta tabbatar ma ta da cewa cikin jikinta na nan.



Ta sake shiga damuwa dan da ƙarfi ba ta son abin cikin ta.

Ƙarshe Sheɗan ya kaɗa mata kai ta aiwatar da abinda ya zo ya rabata da Mahaifinta har abada.



Guba ta zubawa Lukman a abinci akan idan ya ci ya mutu sai ta yi takabar sa ta huta da auren baƙin ciki.



Lukman ya zo ya fara cin abincin kenan ko loma biyar bai yi ba wani jikan gidan ya leƙo akan ya je Malam na kiran sa. Ya wanke hannu ya fita.



Yana wajen Malam suna magana cikin sa ya fara murɗawa tun yana daurewa har ya riƙe cikin yana murƙususu a ƙasa. Malam ya ɗauke shi aka yi Asibiti da shi bayan ya bashi zumar daya tofa ayoyin shifa a ciki. A chan ne aka ce mu su maganin ɓera ya ci.



Ko tantama Malam bai yi ba ya sawa ransa Tabawa ce da wannan aikin. Sawa yai a kira ma sa ita. Lokacin da ta zo yana tare da Lukman da ke zaune gefen sa yayi wani fayau da shi saboda a yau ɗin ne aka sallameshi daga Asibiti.



Ko gaisuwarta Malam bai amsa ba ya umurci Lukman ya saketa. Takardar da Malam ya miƙo ma sa ya karɓa hannunsa na rawa.



"Ka rubuta ma ta saki na ce" ya sake maimaita ma sa da ɗan karfi.



Alƙalamin da ke gefen Malam ya ɗauka ya rubuta wa Rumaysa'u saki ɗaya da rubutun Ajami.



Yana rubutun Tabawa na murmushi.

Malam ya dubeta ya ce "Bayan Lukman bana tunanin za ki samu wani namijin ƙware da zai sake neman auren ki Rumaysa'u".



Magana ce ya mata amma kasancewarsa Uba gareta sai abin ya zame mata baki.



Abin mamaki ko Wata ba'ayi ba da rabuwar su Malam ya aurawa Lukman 'yar uwarta wadda su ke 'ya'yan Baffanu (cousins).



Indo budurwace mai ƙarancin shekaru amma ta yi biyayya ga zaɓin Malam ta zauna da Lukman tsakani da Allah.



Cikin Tabawa na wata takwas Malam ya rasu mutuwar da ya girgiza su sosai.

Sati uku da rasuwan ta haifi ɗa namiji. Sunan Baba ta so sakawa amma saboda jinin Lukman ne sai ta ƙyamaci hakan. Da kanta ta samu Lukman akan sunan ɗanta Faruƙu. Ranan suna kuwa bai chanja ɗin ba aka sawa yaro Faruƙ.





Tunaninta ta rabu da auren Lukman za ta buɗe da wani auren mai kyau sai kuma duniya ta

Please Login or Register in order to submit comment