Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan marayu, talakawa na nan suna alhinin rashin albashi, rashin ruwa ga uwa uba malaman makarantar firamare da ke yajin aiki tun sati uku da suka wuce har yanzu Gwamnati ba ta waiwayesu ba.

Na zanta da wasu matasa inda su ka bayyana mini cewa taron da Hajiya Bilkisu ta yi wani farfaganda ce kawai da ke son ɗauke hankalin talakawa daga matsalolin da su ka sha mu su kai..."





Tsaida video ɗin yai ya miƙawa COS ipad ɗin



"Your excellency kana buƙatar mu tuntuɓi gidan talabijin na Hill TV ne?"



"A'a"



COS na fita daga office ɗin SSK ya ɗau waya ya kira commisioner of finance...


*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....







*©Azizat Hamza*



wattpad Azi_zat





Bismillahir Rahmanir Rahim









Book one













03







"Aseey we are dead" CY ya faɗa lokacin da suka shiga mota za su koma office.

"Ni fa ka ganni nan ba na tsoron ta ɓaci wallahi. Gaskiya ce zan faɗa ko da ba za ta yiwa wasu daɗi ba. Idan ban faɗi gaskiya ba miye amfanin aikin jaridan da na ke yi"



"Dama kin fi kusa da MD ai"





"Kai ka san wannan"



Lokacin da su ka isa office Asiya ta ɗauka MD zai ma ta faɗa amma bai ce komai ba. Ta yi mamaki kam dan indai MD da ta sani ne to da tuni ya fara diri akan ta sako maganar albashi a rahoton da ta kawo.






Awa ɗaya bayan SSK ya kalli rahoton Asiya, ya saka hannu aka sakewa ma'aikata albashin su, zuwa yammaci kusan fiye da rabin ma'aikata kowa ya ji alert ɗin albashinsa.

Mintuna kaɗan bayan SSK ya sake albashi kiran Gwamna Saminu Bacchi ya shigo wayarsa.

Duk da Gwamna Saminu ya girme shi da shekarun da ba za su wuce biyar zuwa shida ba, SSK bai chanchanci irin tsawan da Gwamnan ya masa ba akan ya sake albashi kafin ya dawo.




Bayan ya ajiye wayar ne ya fara tunanin anya kuwa zai iya cigaba da irin wannan tozarcin..





***



Daf an kusa tashi aka kawowa Asiya Shahida letter daga office ɗin MD. Tana gama karantawa ta wuce office ɗin sa da sauri.



"Sir yanzu aka kawo min wannan letter, ban gane ba. Two weeks suspension sannan ka maida ni copy editor"



"Kafin ki tafi ki je ki reporting a wajen News Director"




"Sir???"





"Ba za ki sake airing komai ba har sai kin iya banbanta professional da personal affairs"




Sai yanzu ta gane ashe shirunsa ɗazu ba yana nufin cewa ransa bai ɓaci da abinda ta yi ba ne.



"Idan kuma ba ki gyara ba, Hill TV za ta iya ɗaukan mataki mai tsauri akan ki"




Haƙuri ya ke so ta bashi ta sani kuma ba zata bayarba.



"Shikenan Sir, nagode" daga haka ta fice daga office ɗin tana dunƙunƙune takardar da ke hannunta.

Ko jira lokacin tashi ba ta yi ba ta ɗau jakarta ta bar station ɗin...










Asiya na zaune akan stool a ƙofar ɗakinsu tana yiwa Ummanta kitso Ubayd ya shigo gidan da sallama. Da sauri Umma ta jawo hijabinta da ke gefe ta saka ta bar Shahidah da buɗe baki. Umma ba dai kunya ba. Ta faɗa a zuciyarta. Wai dan ma ba ayi aurenta da Ubayd ba kenan.

Ubayd ya tsugunna ya gaishe da Umma. Ya iya gaisuwa kam amma har yanzu bai fahimtar yaren kurame sosai kodan bai taso a gidan ba ne?




Ya ajiyewa Umma wata ƙatuwar leda tareda kuɗi acikin envelop.

Umma ta shiga yi ma sa godiya, ta zunguri ƙafar Asiya alamar ta tayata yiwa Ubayd godiya.






"Ya Ubayd yaushe aka yi albashi?"




"Ai inaga ke ce dalilin wannan albashin, da safe da ki ka yi maganan albashin nan zuwa ƙarfe ɗayan rana mutane sun fara ganin alert. Ni nawa ya shigo ƙarfe uku da rabi ne lokacin ina Alwala a masallaci"



"Mugu ba. Yana tsoron kar ubangidan sa ya dawo ya samu bai biya albashi ba ya haushi da faɗa"




"Ikon Allah, yanzu ya biya albashin ma bai miki ba"



"Dama ya so yin kasuwanci da albashin mutane ne, Allah ya kamashi"



Ubayd ya girgiza kai kawai ya wuce ɗakin Inna Yaha dan ya kai mata nata kayan.





***



Yau Gwamna ya dawo daga tafiyar da yai, kusan ya ƙara kwanaki biyu bisa ranan daya ɗiba zai dawo. A ranan ne kuma abubuwa da dama suka faru.



A chan gidan Yallaɓai Alhaji Kachallah ne zaune a falon gidan yana jiran fitowar Yallaɓai. Kusan minti ishirin da biyar yai yana zaman jiran sa kafin ya fito yana dogara sandar ƙarfe wacce ta ke ta ado ba wai dan yanada matsalar ƙafa ba.



Minti biyar ya ɗauka yana yiwa Yallaɓai bayanin abinda ke tafe da shi.

Ya ƙara da cewa " ina fata idan lokaci yayi ba za a juya min baya ba"



Yallaɓai yai murmushi ya ce "Alhaji Kachallah ka sani sarai bana magana biyu. Abu ɗaya ne zai sa na chanja maganata, idan har shi ya karya dokar wannan tafiya"



"Ina tsoron kada Mr Paul ya idda mugun nufinsa. Idan har kujerar mataimakin Gwamna ta kuɓuce mani, Yallaɓai za a samu matsala a wannan tafiya"



"Ka kwantar da hankalinka ba abinda Mr Paul zai iya yi"



Alhaji Kachallah ya miƙe ya ce "ni zan wuce"





Bayan tafiyar Alhaji Kachallah Yallaɓai ya dubi kujerar da Alhaji Kachallan ya tashi akai, itace dai kujeran da Mr Paul ya zauna akai jiya yana kawo ƙorafinsa akan a dakatar da tafiyar Alhaji Kachallah saboda akwai giɓi sosai a tafiyar ta sa.



"Ba shi da experience ko kaɗan a wannan harka Yallaɓai. Yanada sanyin zuciya idan aka ɗaura shi akan kujera zamu samu matsala da shi. Ya kamata a datse..."



Yallaɓai ya ɗagawa Mr Paul hannu. Mr Paul yai tsit yana zazzare idanu.



Yallaɓai yai murmushin gefen baki, yana son irin wannan wasan...









***







Cikin shiga ta alfarma shiga ta ƙasaitattun mata Hajiya Bilkisu ta fito daga ɗakinta. Wani tsadadden leshi fari ta saka ɗinkin buba da zani, ta saka takalmi mai tsini kalar ja wanda yai dai-dai da kalar clutch bag ɗinta, ɗan kunne da awarwaro da kuma sarƙa,

Tana takunta ɗaiɗai har ta sauko ƙasa.



"Hajjaju Makkatun, Hajjan Gwamna, Hajjan mu" ta faɗa tana ƙyalƙyalewa da dariya tana ɗan tafa hannu.



"Hansa'u kenan"



"Hajja idan na girma ina son zama kaman ki"



Wani lokaci takan ɗan tausayawa Hansa'u. Wacce ta kawota ta gaya mata cewa auren wuri aka mata tana shekara goma shauku, ta wahala sosai a wajen Kishiyarta. Tana shekaru shabiyar mijin ya rasu. Ba a jima ba ta haihu ɗan bai zo da rai ba wannan psychological trauma ɗin shine ya taɓa ma ta ƙwaƙwalwa. Anyita magani ana tunanin Aljanu ne ko sammu amma shiru. Bayan shekaru ana jinya shine wata Gwoggonta ta kawota Birni dan ta koyi sana'a tunda ta ƙi auruwa. Hansa'u akwai aiki kam amma akwai shirme da shiririta dan har yanzu hankalin ta kaman na budurwar ƙauye ce 'yar shekaru shabiyar. Kusan ko da Hajiya Bilkisu ta girmeta to abinda za ta bata ba zai wuce shekaru biyu ba.



"Hansa'u Malamin Junior ya zo ko?"



"Eh Juno yana karatu da malamin sa a waje"



"Good, idan ya gama lesson ki tabbatar yayi wanka kafin ya ci abinci. Ni zan fita"





"Hajjan mu a kawo mana tsaraba"



Hajiya Bilkisu ta ɗan yi dariya sannan ta fita daga gidan ta nufi motarta inda driver ke jiranta.



Kai tsaye gidan Gwamnati aka wuce da ita. Ba wannan ne farkon zuwanta gidan ba amma abin mamaki ba a bari ta ƙarisa falon First lady ba kamar yadda ta saba yi idan ta zo. Mai aikin gidan ta ce ma ta First lady na da manyan baƙi dan haka ta jira a falon baƙi kafin su tafi.



Da farko abin ya yiwa Hajiya Bilkisu banbaraƙwai saboda irin haka bai taɓa faruwa ba amma daga baya sai ta yi tunanin ko dai first lady na tare da surkuwanta ce. Ba abu ne ɓoyayye ba a wajenta irin takun saƙa da ke tsakanin First lady da Maman Gwamna. Rabuwa su ka yi da matarsa ta farko wacce sun yi kusan shekaru ashirin da biyu tare kafin su ka rabun, hakan kuma ba ƙaramin ƙona ran mahaifiyar Saminu Bacchi yai ba, Murjanatu itace uwar 'ya'yan sa guda shida amma haka ya rufe ido ya shure ya saketa ya auro Hajiya Sha'awanatu. Kusan shekaran su bakwai da aure amma har yanzun tsakaninta da Mahaifiyar Saminu Bacchi ba sa ga maciji.





Zaman jiran da ta ke gani ba zai wuce minti ishirin zuwa talatin ba shine ya zamana har ya wuce awa biyu.



Sau biyu tana turawa a duba ma ta first lady amma sai a ce tana tareda baƙi.

Tun Bilkisu na ɗaukan abun ba komai ba har ya zo ya fara ba ta haushi.

Awa uku da zamanta a falon ta miƙe tsaye dan ta wuce gida zuciyarta cike da ƙuna. Barka da dawowa ta zo yiwa First lady ba wai zaman walaƙanci ba. Ko bakin ƙofa ba ta kai ba ta jiyo shewar first lady da wasu mata. Ta juya a fusace dan ganin su waye su ka fita mutunci a wajen first lady ɗin, lokacin da ta juya first lady ce ke saukowa ƙasa biye da ita kuma Hajiya Hadiza matar Senator da Hajiya Kaltume matar Commisioner.



Hajiya Bilkisu ta bi su da kallon mamaki. Saboda waɗannan matan First lady ta zaunar da ita na tsawon awa uku.





"Ba ki tafi ba?" First lady ta faɗa da mamaki



Hajiya Bilkisu ta buɗe baki cikin kaɗuwa.





"Bilkisu Kachallah. Ashe ke ce ake ta damun First lady wai tana da baƙuwa"



Hajiya Hadiza kenan da wannan magana.



"First lady saboda waɗannan kika shanyani kaman kayan wanki" ta yi maganar tana nuna su.



"Tabbas saboda su kuwa. Bilkisu na ji duk abinda kika yi tun kafin na dawo amma ki sani ba zan lamunci hakan ba. Taron matan Gwamnoni aka ce za ayi ba na matan mataimakan Gwamnoni ba. This is the last time da za ki sake haɗa taro idan bana gari"







"Sai da muka gaya ma ta ta bari ki dawo kafin ayi taron nan amma ta ƙi. Wallahi matar Gwamnan Ekiti sai da ta gasa mana magana a wajen taron nan, kin san yarabawa ai"



"Ni! Ni ki ke wa munafurci Hadiza?"



Hajiya Hadiza ta juya kai tana tura baki.



"Ki tsaya iya matsayinki Bilkisu sai a samu zaman lafiya" First lady ta faɗa a fusace



Hajiya Bilkisu ta haɗiyi wani abu daya tokare mata maƙoƙoro.



"Nagode First lady. Dama na zo yi miki barka da dawowa ne amma na ga alama ba ki cancanci gaisuwar ba. Mu kwana lafiya"



Hajiya Bilkisu ta juya da sauri ta fice daga gidan.

A cikin mota danne ƙirjinta ta yi saboda yadda ya ke bugawa yana sukanta. Ba ta iya ɓacin rai ba dan tana farawa zuciyarta ke fara ciwo. Shekarun baya ance tanada hawan jini shiyasa ta ke kaffa-kaffa da duk abinda zai ɓata ma ta rai.



Bayan ta koma gida ba wanda ta kula ta wuce ɗakinta ta sa key sannan ta kwanta akan gado har lokacin ba ta cire hannu a ƙirjin ba dan ji take idan ta cire zuciyarta zai iya bugawa. Ƙarshe ta tashi ta ɗauko maganinta ta watsa a baki ta haɗiye zuwa minti shabiyar maganin ya fara aiki dan bugun ƙirjinta ya fara raguwa.



Idan ba ƙaddara ba da First lady da Hajiya Hadiza da ita Hajiya Kaltumen dukkan su babu sa'anta cikin su. Idan ba muƙami da mazajen su ke riƙe da shi ba babu wadda a cikin su ta taka ƙafarta wajen gata da daraja. *Bilkisu Sani Kachallah* ce fa. Waye bai san tarihin ahalin gidan Kachallah ba. Familyn Kachallah su ne da Jahar Congo gaba ɗaya.



Bilkisu Kachallah ba za ta iya tuna lokacin da bacci ya ɗauketa ba. Ta dai farka tsakar dare ta ganta kwance da kayan jikinta sai alokacin ta tashi ta cire kayan ta saka na bacci sannan ta dawo kan gadon ta zauna dan bacci ya washe a idonta, tunani kala-kala ta zauna yi har Asuba.





***





Shahidah na bacci wayarta ya hau ƙara. Ta sa hannu ta jawo wayar da ke gefen gado saura kaɗan ya faɗo ƙasa.



"Hello" ta faɗa da muryan bacci



"Mine kin tashi kuwa? Na kusa isowa fa"



"Ka manta anyi suspending ɗina jiya"



"Subhanallahi! Ok ok barin zo in gaida Abba sai na wuce office..." ai bai ƙarisa bama Asiya ta kashe wayar saboda baccin da ke cinta.





Da sassafiya Bilkisu ta shirya ta sauko ƙasa. Daga wajen dining room wanda ke haɗe da babban falon ƙasa ɗan ta Junior ya ƙwala ma ta kira "Mommy" ta juya da sauri tana maƙalawa fiskarta murmushin bogi wanda ya ɓoye ɓacin rai da ta ke ciki.



"My boy"



"A'a Nana yaushe kika dawo. Zunairah ya Maman ki?" Ta jera maganar tun kafin ta iso wajen su



"Mommy ina za ki sani kuwa. Jiya ina miki magana haka kika shareni kika wuce sama. Daga baya na je na yita buga ƙofar ki amma shiru ba ki buɗe ba"



"Sorry Dear, jiya na gaji ne dayawa"



"Miyasa Junior ke cin abinci shi ɗaya ina Hansa'u?"



"Hansa'u" ta ƙwala ma ta kira da ƙarfi



"Mommy Airah ce ta aiketa ta kawo mata boiled egg"



"Ok girls barin fita, idan Daddyn ku ya tashi ku ce ma sa na tafi Kachallah House"





Bayan tafiyar Hajiya Bilkisu sai ga Hansa'u ta fito da wani bowl ɗauke da ƙwai guda uku ta ajiye a gaban Zunairah.



Zunairah ta zaro ido ganin ƙwai da ɓawonsa a jiki sai tiririn zafi ya ke



"And what is this? N Luv kinga shirmen wannan crazy old fool ɗin ko?"



Nana ta kalli Hansa'u ta ce " yanzu Hansa'u ita ki ke so ta cire ɓawon ƙwan kenan?"



"Ke ce ki ka ce na kawo shi kwili-kwili (quickly-quickly) kuma na ji Hajiya na kira shiyasa na kawo shi haka nan"



"Dalla je ki ɓare ƙwan ki kawo" Nana ta faɗa da tsawa.



Hansa'u ta ɗauke kwanon ta koma kitchen da sauri.







Hajiya Bilkisu da ta fito ba ta wuce ko'ina ba sai Kachallah House. Da ta shiga gidan ba ta wuce sashen kowa ba sai sashen mahaifinsu wanda ya ke gefe da asalin cikin gidan, a nan ya ke karɓan baƙin sa a nan kuma ya ke duk wasu harkokin sa. Sashen ya ƙunshi falo guda ɗaya da dining room sai manyan ɗakuna guda huɗu. Ba kowane ya sani ba amma ita Bilkisu ta san akwai falon sirri a gidan wanda Mahaifinsu ke karɓan baƙi na musamman inda ake yin meeting na tsakar dare a ciki.



Shekarunta shabiyar lokacin da ta gano ɗakin, ta je duba wani littafi a library ɗinsa ne hannunta ya danna wani switch a jikin bango sai gashi carpet ɗin wajen ya ɗage. Ba tareda tsoro ba ta leƙa wajen daya buɗe ɗin sai taga matakala ce a wajen. Ta sa ƙafa ta fara taka matakalar har ta nitse ciki dan falon underground ne. Ta san turawa na yin ɗaki ko basement a cikin ƙasa amma ba ta taɓa tunanin sashen mahaifin na su na da irin wannan ba. Falo ne Babba da ya sha kayan alatu fiye da ɗaya falon sai ɗakuna biyu wanda tayi-tayi ya buɗu ya ƙi buɗuwa shiyasa ma ta haƙura ta fito ba tareda ta ga abinda ke ciki ba.





Ta ci sa'a Baban na su na nan dan lokacin ne ma ya ke ƙoƙarin karyawa ga tulin abinci kala-kala da aka ajiye ma sa wanda aƙalla mutum shida za su iya cin abincin su ƙoshi sarai.



"Bilkisu" ya kira sunanta da mamaki.



Ya duba agogon hannunsa ya ga ƙarfe bakwai da minti arba'in da bakwai.



"Lafiya dai ko?"



"Lafiya Baba"



Bayan ya tambayi lafiyar mijinta da 'ya'yanta sannan ya tambayi mi ke tafe da ita da sassafen nan dan yasan haka kawai Bilkisu ba za ta nemeshi ba.



"Saifu ne zai miki kishiya?"



"Baba idan kishiya ce ai da sauƙi. Baba tambaya na zo yi"



Alhaji Sani Kachallah ya suɗe romon kan rago da ke shirin gangarowa zuwa gwiwar hannunsa. Wani lokaci idan Mahaifinsu yai wani abun kamar wani faƙiri wanda ba shi da gata ko kaɗan. Yanzu miye na suɗe hannu?. Ta yi saurin kauda wannan tunanin a ranta ta maida hankalinta zuwa abunda ya kawota.



"Baba yaushe Saifuddeen zai zama Gwamna?"



Alhaji Kachallah ya saka bredi ya dangwali romo zai kai baki ya ji maganar Bilkisu ta ma sa dirar bazata.



"Wace tambaya ce kuma wannan?"



"Baba dan Allah ka amsa min tambayata"



Alhaji Kachallah ya kalli idon 'yarsa da kyau ko zai gano wani abu amma bai karanci komai a fiskarta ba sai tsananin ɓacin rai, ya ce " idan Saminu Bacchi ya ƙarisa tenure ɗin sa guda biyu Jaha za ta koma ta Saifu dan shi za mu tsayar a zaɓe na gaba"



"A taƙaice kusan shekaru biyar kenan?"



Alhaji Kachallah ya ture kwanon gaban sa gefe ya ɗaura hannu akan table yana zubawa Bilkisu ido.



"Babu yadda za'ayi Saifuddeen ya zama Gwamna kafin lokacin?. Baba ku ne da gwamnati, ku kuke juya jahar nan, mi zai hana ka ɗaura Saifuddeen a kujerar Gwamna, shekaru biyar ma su zuwa sun yi nisa sosai"



"Bilkisu!"



"Baba break the rules, boycott the protocols make Saifuddeen the governor and..."





Idan da bai yi tunanin hakan ba to yanzu Bilkisu ta ankarar da shi. Mr Paul da ya ke son haɗa ma sa manaƙisa a wajen Yallaɓai dole ne ya nuna ma sa cewa kafin mutum ya ga biri to biri ya gan shi.



Bayan fitar Bilkisu daga falon, Alhaji Kachallah ya faɗa kogin tunani. Ta ina zai fara? Akwai gaskiya a hasashen Bilkisu dole ne ya san yadda zai yi ya shawo kan matsalar tun kafin lokaci ya ƙure a juye ma sa baya.





***





"Miyake faruwa naga kwana biyu ba kya fita"



SSK yai maganar yana zama gefen gadon Bilkisu tareda kissing goshinta.



"Ba na jin fitan ne kawai. Ina buƙatar hutu ne ma"



"Nima ina buƙatar hutun nan Allah. Inaga tunda Gwamna ya dawo why not mu je UK hutu ko da na sati biyu ne?"



"Its a good idea gaskiya. Muna buƙatan hutun nan sosai" ta yi maganar tana murmushi.



SSK bai jima da fita daga ɗakinta ba wayarta ya hau ruri. Madam Bintu ta gani a jikin screen ɗin hakan ya sa ta faɗaɗa murmushinta. Ta yi saurin ɗaukan kiran tana faɗin " mutanen Turkiyya kin shigo kenan"



Daga ɓangaren Madam Bintu ta ce "na shigo jiya da dare zan shigo wajen ki anjima"



"To sai kin zo"



Ƙarfe biyar da rabi sai ga Madam Bintu a gidan ta. Hansa'u ta kira ta kawo musu abin taɓawa.



"Har yanzu ba ki rabu da wannan matar ba bayan shirmen da ta yi kwanaki"



"Bintu tausayi ta ke bani Allah. Besides yanzu ta iya aiki sosai ba kaman farkon kawota ba sai dai ba a rasata da shirme kam. Most importantly tana sani dariya and that's help alot ga mu ma su hawan jini"





"Ok" ta faɗa tana ƙarewa Hansa'u kallo. Gani ta ke kaman idon matar na mata kama da wacce ta sani amma ta rasa gano ko wacece.



Bayan Hansa'u ta bar wajen Madam Bintu ta tambayi Bilkisu yadda taron matan Gwamnoni ya kasance dan lokacin da aka yi taron ba ta ƙasar.



"Ba abunda zan ce miki Bintu sai dai in ce kawai taro yayi kyau. Kuma za a sake wani taron nan ba da daɗewa ba"



Madam Bintu ta kalli Hajiya Bilkisu cikin rashin fahimta, maimakon ta mata ƙarin bayani sai kawai ta fashe da wata ƙasaitacciyar dariya.







**

A chan gidan Yallaɓai kuwa Chief of Staff (COS) ɗin Gwamna ne a gaban Yallaɓai yana ma sa bayani mai mahimmanci wanda ya sa Yallaɓai nitsuwa na ban mamaki. Har ya gama bayanin Yallaɓai bai ce komai ba sai ma murza gemunsa da ya fara yi a hankali.



Ba kasafai ya ke samun ma su taurin zuciya irin ta KACHALLAH ba. Shekaru da dama an taɓa yunƙurin aikata irin wannan abu sai dai kuma komai ya zo ya chanja a ƙurarren lokaci.



"Ka haɗa meeting da Kachallah cikin satin nan" Yallaɓai ya faɗa bayan yayi dogon nazari.



COS yai murmushin gefen baki dan ya san yanzu liyafa za ta cigaba. Ya ƙwallafa rai sosai akan Gwamna Saminu Bacchi sai dai cikin shekaru uku da yai a kan mulki sun samu saɓani sosai domin lokacin da idon Gwamna Saminu ya buɗe da kuɗi sai ya zamana yana ƙoƙarin take duk wata hanya da su suke yagan rabon su, yanata wawure komai shi kaɗai da iyalin sa ba dan Yallaɓai ya tsayar ma sa ba wasu abubuwan haka za su dinga wuce shi.



Saifuddeen Sa'ad Kachallah daban ya ke da Gwamna Saminu, kuɗi ba za su ruɗe shi ba. SSK ya gaji arziƙi irin arziƙin da ko da ba zai yi wani aiki ba zai isheshi ci da iyalen sa har iya karshen rayuwar su ba tareda sun yi talauci ba.

SSK shine mafita a gareshi da shi da KACHALLAH.





***



"Wallahi an cuceni Ya Ubayd. MD mugu ne wallahi"



Ubayd yai murmushi ya ce " ni kam ya min dai-dai, dama daurewa kawai na ke yi amma kullum aka nunaki a TV sai na ji kamar zuciyata za ta fashe"



"To ta Allah ba taka ba. Sai an maidani reporting unit"



"Ina kishin ki Asiya na haƙura ne kawai saboda babu yadda zan yi amma Allah idan ki ka shigo gidana ba za ki sake bayyana a TV ba, ko dai ki tsaya aiki a bayan fage ko kuma ki haƙura da aikin"



"Ya Ubayd you are joking right"



"I'm not Asiya. Gara ma ki saba da inda aka kai ki yanzu"



Sati ɗaya da suspension ɗin ta aka kirata akan ta dawo. Yau ta fara fita aiki amma duk ta ji ba daɗi ba ta son ɓangaren da aka kaita ko kaɗan.



"Ya Ubayd ba haka mu ka yi da kai ba baka ce za ka rabani da aikina ba"



"Ba rabaki zanyi da aikin ki ba na dai ce bayan munyi aure ba ƙaton da zai sake ganin ki a TV yana ƙare miki kallo especially with irin shigan da ki ke yi" yai maganar da ɗan ƙarfi



Asiya ta miƙe daga kujeran da ta ke zaune ta ce "ba ka isa ba kuwa"



Ta wuce ta barshi a wajen baki buɗe.



Washegari ko jiran sa ba ta tsaya yi ba ta hau keke ta wuce office...







***





" na gaya miki babu kuɗi a ƙasa, duk wani abu da zamuyi yanzu mutane za su yi magana. We need this year to work on something saboda campaign da za a fara nan da watanni huɗu ma su zuwa"



Gwamna Saminu Bacchi kenan yana ƙoƙarin lallashin matar sa.



"Kana so ka ce min ba ka da kuɗin da zamu celebrating 8years anniversary na mu?"



"Ba wai ba kuɗin bane amma kuɗin campaign ne"



"Kar ka gaya min magana dan Allah. Uban me Saifuddeen Kachallah ke da shi da zai iya celebrating 15yrs anniversary na su a tsakiyar teku shekaru biyu da suka wuce. Na je party ɗin fa. Sati biyu aka yi a cikin jirgin ruwa wanda komai da komai da mutanen ciki su ka yi yana wuyan sa"



"Sha'awanatu. Saifuddeen Kachallah millionaire ne tun kafin mu hau gwamnati ko mi zai yi ba wanda zai zargeshi amma ni..."



"Ba zan yadda ba fa. Dole ne ayi anniversary party namu a Italy. Wallahi kai ka ke sawa ma Bilkisu Kachallah tana raina ni. Ina matar Gwamna amma ko motan da ta ke hawa tafi tawa"



"Yanzu kinsan ya za ayi ne? Za mu yi party amma a nan Nigeria. Bamu jima da dawowa daga ƙasar waje ba idan muka sake fita mutane za su yi magana..."



"Wai ina ruwanka da mutane ne. Kai fa Gwamna ne. Gwamnar jahar CONGO wancan tafiyar Asibiti ka je wannan tafiyar kuma yana cikin yiwa iyalinka hidima ne"





" Amma Sha'awa..."



Daga haka Gwamna Saminu Bacchi ya haɗiye sauran maganar sa saboda haɗe bakin su da Sha'awanatu ta yi.





Washegari da safe Gwamna ya tashi da wani irin ciwon kai da ciwon ƙirji, ciwon ne ma ya tashe shi daga bacci tun ƙusan ƙarfe huɗun Asuba.



Wasa-wasa har ƙarfe shida jikin ba sauƙi duk da kuwa ya sha magungunan sa.



"Za mu wuce Asibiti ne ko a kira maka likita?" First lady ta tambaya cike da fargaba.



"Ki kira Likita" ya faɗa da ƙyar saboda yadda ƙirjinsa ke takure.



Bai kai awa ɗaya ba saiga likitan sa ya iso koda ya duba shi cewa yai jinin sa ne ya hau sosai idan akwai wata damuwa da ke ransa to yai ƙoƙarin kauda ita dan abunda ya sa a ransa ka iya jawo ma sa bugawar zuciya.



Shi dai ya sani bai sa komai a ransa ba. Ba a fara campaign ba balle ya ce shine ke ɗaga ma sa hankali. To

Please Login or Register in order to submit comment