Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

COS daya kawo masa jaridar.



"Umaru Kwom"



"Umaru Kwom? Hmmm wannan mutumi dai ya ɗau aniyar ɓata mini suna kafin zaɓe"




COS yai shiru yana nazari, ya faɗawa Gwamna waye mai rubuta labaran nan ne ko kuma ya gayawa Kachallah. Idan ya faɗawa Gwamna zai shiga tashin hankali, amma ba abinda zai iya yi akai. Lokacin da ya gayawa Kachallah cewa Asiya ce 'yar jaridar da ta saurari maganansa kwanaki ba abinda aka mata dan haka zai yi shiru ya zubawa dukkansu biyu ido zuwa lokacin da zasu gano da kansu wanda ke ɓata musu suna a jaridar Climax.



"Ina son sanin waye ɗan jaridar da ke rubutun nan"




"Angama Excellency, za a nemo koma wanene" COS ya faɗa yana murmushin mugunta.





***




Asiya tana zaune ta shirya kayanta tsaf tana jira Sumayya ta gama haɗa nata kayan su tafi.



"Ni kam Anty Allah bana so mu bar nan, a chan fa takura za mu yi"



"Idan ba za ki bini ba, kya iya wucewa hostel daga nan" Asiya ta faɗa tana hararanta.



Babban labari take bibiya kuma dole sai tana gidan Gwamnati za ta samu. Irin kira da saƙonnin da Nana ke tura mata ya sa tayi zargin ko yarinyar 'yar maɗigo ce. Har a whatsapp idan tayi hoto sai ta turawa Asiya wai ta gani ko tayi kyau.



Yaya Bello ne ya kaisu gidan. Asiya ta shiga gidan tana addu'ar Allah ya sa ta samu ta gama komai cikin ƙanƙanin lokaci.




Masu aikin gidan sun ganeta sai dai ganinta da kaya yasa suka tsaya cirko cirko. Babu wanda ya faɗa musu Amaryar Gwamna za ta zo. Gashi Gwamna da Bilkisu ba sa nan balle aje a tambayesu.



Hansa'u da ta fito ta kalli Asiya zaune a falo ta ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya, gabanta kuma akwatuna ne guda uku. Hansa'u ta yi murmushin gefen baki dan ta hango drama idan Bilkisu ta dawo.



"Hajiya Barka da zuwa, a shiga miki da kayan ciki ne?"




"Kira min Nana" Asiya ta faɗa tana danna wayarta



Hansa'u ta wuce ɗakin Nana da gudu.

Lokacin da ta shiga cacar baki ta samu Nana da Zunnairah na yi.




"A wani dalilin za ki ce ta dawo gidan nan idan ba soyayya ku ke ba"



" Tana da ikon zama a gidan nan saboda itama matar Daddy ce. Sannan idan ma soyayyar muke ina ruwanki. Ke mata nawa kike da shi. Yes ina sonta"




Hansa'u tayi gyaran murya, dukkansu suka juyo suna dubanta. Ta taɓa kamasu suna aikata maɗigo tun farko-farkon fara aikinta a gidan. Sun mata kashedi akan kada ta kuskura ta faɗawa kowa, sai dai ba kashedinsu ne ya sata yin shiru ba. Aikinta bai bata daman tona musu asiri ba sannan ta lura Bilkisu gafalalliyar Uwa ce. Wani lokaci tana gani suna abinda bai dace ba amma sai tayi shiru.



"Hajiya Asiya tana neman ki "



"Ina zuwa"


Nana za ta fita Zunnairah ta riƙe hannunta tace " wallahi duk ranan dana kamaki da ita sai na gayawa Daddy komai"



" ni kuma sai na faɗawa kowa cewa ke ɗin 'yar shegiya ce, da cikin ki Mommynki ta yi aure"



Zunnairah ta kaiwa Nana duka Nana ta goce ta fice daga ɗakin da gudu.




Zunnairah ta dunƙule hannu tana huci.

Tun ranan da ta saurari faɗan iyayenta abin ya taɓa mata ƙwaƙwalwa. Tana shekara shaɗaya a lokacin ta buƙaci mahaifinta ya kaita karatu ƙasar waje, lokacin yawanci 'yan ajinsu 'ya'yan manya da suka gama firamare tare iyayensu sun kaisu ƙasar waje.

"Ni zan kashewa shegiya kuɗi" amsar daya bata kenan data faɗa mata buƙatarta. Ta wuce ɗakin mahaifiyarta tana kuka. Daren ranan bayan ta kwanta ta jiyo Iyayenta na faɗa inda mahaifinta ke cewa ba lallai bane ace cikinsa ne tunda ba budurwa ya sameta ba, sannan koda suke tare ai tanada wasu samarin. Yayinda mahaifiyarta take cewa idan bai yadda Zunnairah 'yarsa bace ya je ayi gwajin DNA.




"Koma minene dai ba zan kashe mata kuɗi ba. Idan ba zata boarding school da aka sama mata ba ta haƙura da karatun"



Da wannan aka tura Zunnairah boarding school a nan kuma aka koya mata maɗigo...




Nana na zuwa falo ta rungume Asiya tana dariya. Ita ta mata jagora har ɗakin da ke kallon nata tace ta zauna a ɗakin idan Daddy ya dawo sai ta zaɓi ɗakin daya mata.



Bilkisu bata shigo gidan ba sai chan yammaci. Tana zuwa kuwa aka ce mata Asiya ta zo, ta haura sama kaman za ta tashi sama.



Ɗakin Nana za ta shiga ta ga Zunnairah ta fito daga ciki.

"Ina take?"



"Wa?"



"Shegiyar da ta shigo min gidana"



Zunnairah ta nuna mata ɗakin da Asiya take.



Bilkisu ta banko ƙofa ta shigo ɗakin tana huci.

Nana da Asiya da Sumayya ne ke zaune akan gado suna hira.



"Ku bamu waje"



"Mommy daga zuwanki" Nana ta faɗa tana tura baki.



"Ki fata ko na ci miki mutuncin, wawuya kawai"

Kafin ta gama magana ma Sumayya ta fice daga ɗakin, yayinda Nana ta fice tana buga ƙafa.



"Ehen, mi ya kawo ki?" Bilkisu ta faɗa bayan su Nana sun fita.



"Mi ya kawoni kuma?"



"Uban wa ya baki damar zuwa gidan nan?"



"Inaga dai kin manta cewa ni da ke matsayinmu ɗaya. Yadda kike da iko da gidan nan haka nake da shi"



"Never. I am the first lady of the state, ba ki da matsayi a nan. Ki koma inda kika fito kafin na sa a maida ki ta ƙarfi"



Asiya ta miƙa mata wayarta tace "gashi, kira shi ki ce masa ba zaki bi umurninsa ba"



"Shi...shi Saifuddeen yace ki tattaro ki dawo nan?" Bilkisu tayi tambayar ta kasa gaskata hakan. Gwamna ba zai taɓa kawo Asiya ba bayan ya san ba ta so.



"Ki tattara kayanki ki koma inda kika fito"



"Idan kinga na tafi, to Excellency ne da kansa yace na bar gidan nan"





"Asiya kike ko wa. Ki fita a gidan nan kafin rayuka su ɓaci"





"Bismillah, Bilkisu Kachallah" Asiya ta faɗa tana dariya.





Bilkisu na fita daga ɗakin ta shiga kiran Gwamna, bai ɗauka ba hakan ya sake tunzurata. Lokacin daya kira bayan minti talatin ihu ta fara masa a wayar kan a wani dalilin zai cewa Asiya ta dawo gidan Gwamnati. Gwamna yace koma minene ta bari ya dawo.

Bilkisu har ƙarfe shaɗayan dare haka ta zauna zaman jiran dawowar Gwamna. Lokacin da ya shigo gida shabiyu saura a falonsa ya samu Bilkisu tana zaman jiransa.



"Ina ji, miya kawota gidana?"



Da rana bayan sun yi waya da Bilkisu, kiran Asiya yai dan ya ji dalilin dawowarta Gidan Gwamnati amma sai tace tana son zama a gidan ne, tana son sanin ya ake ji idan ana zaune a gidan gwamnati a matsayin Matar Gwamna.



"Saifuddeen ina jin ka"



"Bilkisu ke ba yarinya bace, ku ba yara bane. Ka da ku ɗaga min hankali dan Allah, akwai abubuwa dayawa a kaina"



"Haka ma zaka ce...haka ma zaka ce ko"



Gwamna ya wuce ɗaki ya barta a wajen.

Da sun san abinda ke damunsa yanzu da ba za su fara faɗa akan gida ba.

Ya kasa biyan albashin 'yan fensho da suke bin gwamnati har na wata huɗu, ga kumadu 'yan secretariat da malaman Sakandare duka sai dai ya biya su kaso hamsin na albashinsu wannan watan.



Lokacin da yayi wanka ya kwanta, bacci ƙaurace masa yai. Yana so koda kaɗan ne ya samu ya rintsa amma zuciyarsa tana cikin ƙunci nan da kwanaki kaɗan idan bai biya albashi ba mutane zasu fara magana. Ƙarshe dai sai daya sha maganin bacci kafin bacci ya ɗauke shi.







***



Da sassafiya kira ya shigo wayar Asiya tana dubawa taga numbar ƙasar waje . Tana ɗauka aka kira sunanta "Aseey"



"Ya Allah! C Y?, kana nan, ya kake ya jiki"



" lafiya Excellency, jiki da sauƙi"



"Gaskiya na ji daɗi C Y, ya hannunka"



"An samin na roba"



"Sorry ka ji"



"Ki tayani yiwa Gwamna godiya, he's a good man Wallahi, na ji daɗi da aka ce kin aure shi"



"Tsaya, tsaya, CY kana asibitin ma gulma kake. Waya gaya ma na auri Gwamna?"



CY ya ƙyalƙyale da dariya yace " har video ɗin dinner ɗinku na gani"



"Magulmaci, yaushe za ka dawo?"



" sunce za su sallameni nan da sati biyu haka"



"Na missing ɗinka sosai"



"Rufa min asiri kar Gwamna ya sa a harbeni"



Asiya ta sa dariya.



Kaman haɗin baki suna gama waya da CY sai ga kiran Fou'ad Salisu. Kafin ta amsa kiran sai da ta shige banɗaki ta kulle ƙofa.



"Ina jinka Fou'ad"



Daga ɓangaren Fou'ad ya fara yi mata bayani "akwai wani account mai suna Sa'ad Kachallah, inaga na Gwamna ne. Lokacin da Gwamna ya bayar da takardar shaidar kuɗi da dukiyar daya mallaka kafin a rantsar da shi bai haɗa da wannan account ɗin ba, sannan account ɗin duk wata akwai miliyoyin kuɗi da ake turawa ciki. Zan ƙarisa bincike na tabbatar da gaskiyar komai"



Asiya cike da farin ciki tace " idan aka tabbatar account ɗin nashi ne za a iya tsige shi kenan?"



"Za'a iya"



Asiya ta yi murmushin jin daɗi...



***





Sumayya tana gama lectures na ƙarfe shabiyu ta hau keke ta wuce Asibitin da Ubayd ke aiki. Ta samu yana tareda marar lafiya dan haka sai da ta jira kusan minti talatin kafin yace ta shigo.



Da suka gaisa Sumayya ta masa bayanin abinda ya kawota. Murya na rawa tace

"Yaya Ubaydullah, Ina tsoron abinda zai faru idan Gwamna ya gane Anty Asiya tana cin amanarsa"



Ubayd ya jawo kujerarsa gaba ya gyara zama da kyau yace "mi take yi?"



"Dan Allah kar ka faɗa mata cewa ni na gaya maka. Anty Asiya tana son ɓatawa Gwamna suna, da bakinta tace min sai ta sa an tsige Gwamna hankalinta zai kwanta"



Ubayd ya ɗan jijjiga kai alamar ta cigaba.



"Anty Asiya ta san Nana 'yar Gwamna tana shaye-shaye sannan...sannan"



Abin yai wa Sumayya nauyin faɗa.



"Kar ki ji tsoro ba abinda zai faru"



"Nana 'yar lesbian ce, Anty Asiya tace zata wallafa hotonta da ta 'yaruwarta suna kiss tsirara"



"Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun"



"Dan Allah ka hanata, Wallahi Gwamna yanada kirki ba zai taɓa jin daɗi ba idan aka buga hoton 'yarsa tsirara a jarida"

Ta ƙarisa maganar kamar za ta yi kuka.



Ubayd ya ja dogon numfashi yace " kar ki damu zan kirata"



Sai da yai sallar Azahar kafin ya kira numbar Asiya har yanzu sunan da yai saving da shi ne bai chanja ba wato *Mine* yanzu kam dole ya chanja numbar ko dan gudun zargi.



Asiya za ta shiga wanka ta ji wayarta na ringing. Tunaninta Mr Bassey ne shiyasa ta koma ta ɗau wayar dan ta gaya masa nan da anjima kaɗan za ta tura masa labarin da ta rubuta. Ta gama rubutun editting ɗinsa kawai za ta yi.



Tana duba wayar ta ga sunan Ubayd.

"Ya Ubayd kuma?" Ta furta a fili, sai da wayar ya kusa yankewa ta ɗauka tareda sauke ajiyar zuciya.



"Asiya ke ce kike rubutu a jaridar Climax ko?" Ya katse shirun na su

"Ya Ubayd dan Allah kada kace na dena"



"Ai ban isa na hanaki abinda kika yi niyya ba. Ina ce taurin kanki ne ya zamo mafarin komai"



"Ya Ubayd..."



"Yanzu ba za ki karɓi hukuncin Allah a rayuwarki ba. Yanzu Asiya har zuciyarki ya bushe za ki iya nuna hoton tsiraicin yara ƙanana a jarida"



"Za a rufe inda bai kamata ya fito ba, ina dai so a gansu suna aikata maɗigo ne"



"Idan har haka kika zamo Asiya, Alhamdulillah da ban aure ki ba. Asiya kin san ya yaran nan za su ƙare rayuwarsu idan kika tona musu asiri haka. Kina kiran Gwamna Azzalumi amma inaga sunan daya kamata ki fara kiran kan ki kenan"



"Kar ka zageni Ubayd. Ni miye Gwamna da matarsa ba su min ba, har yau akwai mutane dayawa da suke min kallon karuwa"



"Asiya kina da ilimi, da da yanzu ba ɗaya bane. Yanzu Gwamna mijin kine"



"Mijin da bana so ba, bana son shi Ya Ubayd, ba zan taɓa son shi ba"



"Idan kika wallafa hotunan tsiraicin yaran nan bana tunanin Allah zai yafe miki Asiya"



Daga haka ya kashe wayar.



Asiya ta fashe da kuka. Da ta yi mai isarta ta shiga banɗaki ta fara wanka. Komai ya zo mata da sauƙi sai gashi Ubayd yana so ya dagula mata lissafi.



Kwananta huɗu a gidan ta kama Nana da Zunnairah akan gado, ba tareda sun ankara da ita a ɗakin ba ta ɗauke su hoto ta fita.

Ta zo tana editing hoton a laptop Sumayya ta gani hankalinta ya tashi. Asiya tace mata maganin 'yan iska za ta yi.

Da farko labari za ta rubuta akan hoton da Mr Bassey ya turo mata, wani hoton Nana ce a wajen party tana shan shisha. Hoton bai jima sosai ba dan ba zai fi wata ɗaya da aka ɗauka ba. Ko a ina ya samo hoton oho ita dai damuwarta ta yi rubutu ta aibata Gwamna sai kuma kwatsam ta samu hoton da ya fi wancan armashi.



Tana fitowa daga banɗaki ɗaure da towel ta dafe ƙirji saboda ganin Gwamna da tayi riƙe da wayarta.

Idonsa ya kaɗa yayi ja sai ta fara tunanin kodai ya ga hoton Nana ne, to amma kuma wayarta akwai password.

Ringing wayar ta fara yi hakan ya sa ya miƙa mata wayar. Jiki a sanyaye ta ƙariso ta karɓi wayan a hannunsa. *Ubayd Luv* ta gani ƙarara a fiskar wayar, ta ɗaga ido ta kalli Gwamna wanda shima kallonta yake yi.



"Akwai taron da zamuje gobe da ƙarfe goma na safe" daga haka ya fice daga ɗakin.



"Ashe dai bai gani ba" ta faɗa a hankali.

Ba ta ɗau wayar ba sai da ta je ta kulle ƙofa kar wani ya sake shigo mata ɗaki bagtatan.



Kiran numbar Ubayd tayi bayan ta zauna a gefen gado.



Lokacin da ta ɗauka roƙonta ya fara yi akan dan Allah kada ta wallafa hotunan nan. Yadda ya dinga yi mata nasiha yasa dole ta haƙura da abinda tayi niyya, tace masa ba zata wallafa hoton ba.



Da suka gama wayar ta saka kaya ta jawo laptop ɗinta ta goge rubutun da tayi da farko ta fara rubuta wani sabo akan hoton da Mr Bassey ya turo mata.



***



Washegari aka fitar da labari mai taken *'yar Gwamna tana shaye-shaye* rubutun ya soki Gwamnatin Saifuddeen Kachallah inda aka bayyana cewa yadda Gwamna bai iya kula da tarbiyar 'yarsa ba haka zalika ba zai iya kula da haƙƙin talakawa ba. Duk da jaridar bata fito ta bayyana cewa Nana Kachallah 'yar maɗigo bace amma ta yi ishara da hakan ta hanyar cewa akwai alamun Nana Kachallah za ta iya zama 'yar maɗigo saboda illar shaye-shaye.



Gwamna bai samu ganin jaridar da aka wallafa ba sai da ya dawo daga taron buɗe wani Asibiti da suka je a wata ƙaramar hukuma shi da matansa biyu.



Lokacin da ya ga hoton 'yarsa tana zuƙan shisha sai dayai ƙwalla Allah ya taimaka ma babu kowa a office ɗin nasa. Gaba ɗaya komai ya fice masa a kai, tunda aka fitar da hoton birthday ɗinta ya ja mata kunne akan irin shigar da take yi sannan ya hanata fita idan ba makaranta ko gidan kakanninta ba.

Amma a haka bai tsira ba, mulkin gaba ɗaya ya ishe shi. Lokacin da yake koyarwa yanada lokacin iyalinsa sosai amma tunda ya shiga siyasa yanayin zama da iyalinsa ya ja baya, musamman yanzu da yake kan kujerar Gwamna.



Kiran Direban yaransa yai yace ya je ya ɗauko Nana a makaranta ya kaita Kachallah house.



Shima ɗin bayan ya samu zuciyarsa ta ɗanyi sanyi Kachallah House ɗin ya wuce.



Yana zuwa ya samu Dadda na yi mata faɗa, suma sun ga jaridar.

Dadda shigewa ɗakinta tayi ta basu waje. Nana da idonta ya ciko da hawaye ta shiga rantse-rantsen sau ɗaya ne kuma a wajen party aka tirsasata saboda ƙaryar da Bilkisu tace tayi kenan.



"Hoton bai yi kama da yarinyar da aka tursasa ba, ya fi kama da yarinyar da ta ƙware wajen shan shisha dama wasu abubuwan"



"Daddy I swear..."



"Ki gaya min gaskiya yanzu, ko kuma na sa a binciki jininki a duba min traces na kayan maye. Idan aka samu Nana ba za ki so ki sake kirana mahaifinki ba"



Nana ta tsorata da yanayinsa, yadda ya ɗau fushi ba abinda ba zai iya yi ba.



Ƙarshe da taga gaskiyar ce kawai zata fishsheta sai ta sanar da shi komai. Zunnairah ce ta koya mata shan syrup da shisha.

"Wani mummunan abun ta kuma koya miki?"



"Babu. Allah babu" Nana ta yi saurin faɗa tana fashewa da kuka.



" Khadijah ba zan bar nan ba sai kin gaya min duk abinda Zunnairah ta koya miki. Idan kika min ƙarya zan gane dan nasa a bincika mini CCTV camera da ke cikin gida" duk da sai yanzu yake danasanin ƙin yarda a saka masa CCTV a gida da yai.



Tsoro ya ɗarsu a zuciyar Nana, kenan duk abinda suke da Zunnairah Daddy zai gani. Idan haka ne ta kaɗe.



"Ina jin ki Khadijah"



"Daddy ka yafe min, wallahi ba laifina bane. Airah ce, Airah ce ta kemin wasu abubuwa tun bana so har na zo na fara so. I swear Daddy na dena, cewa tayi zata faɗa maka shiyasa na sake yi"



Gwamna ya jingina kansa da kujera yana faɗin "Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun"



*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....







*©Azizat Hamza*



wattpad Azi_zat





Bismillahir Rahmanir Rahim









Book one







18





Asiya ce ta fara shiga falon. Ta samu Gwamna yana zaune yayi tagumi. Ya mata tsufa, idonsa ya faɗa, ƙasan idonsa ya yi baƙi, ga furfura kaɗan-kaɗan a jikin gemunsa. Asiya ta zuba masa ido ba tareda tace komai ba.

Minti uku sai ga Bilkisu ta shigo ɗankwali a hannu.





"Saifuddeen koma wanene ya rubuta labarin nan sai na sa an nemoshi an hukunta shi. In fact sai nayi kaca-kaca da jaridar Climax"



"Nana tana zama a gidan nan tareda ke amma baki san tana shaye-shaye ba"




"Kar ka kawo min wannan Saifuddeen, ka san ina ƙoƙari akan yarana, especially Nana. Zunnairah ce ta koya mata. Na riga na turata wajen uwarta kafin ta ɓata min 'ya"

Ta zauna gefensa kafin ta cigaba da magana

"Saifuddeen kai ne Gwamna, ya kamata ka ƙwace lasisin gidan jaridar Climax. Ta ya za su ce Nana zata zama 'yar lesbian"



"Saboda da gaske ne" Gwamna ya furta a hankali




Bilkisu ta zaro ido.



"Da gaske kuma? Mi kake nufi?"




"Nana ta faɗa min komai. Ita da Zunnairah suna aikata maɗigo a gidan nan kuma babu wanda ya sani cikinmu, saboda mun gaza, mun gaza Bilkisu. Ba jaridar Climax zamu bincika ba, kanmu za mu bincika a matsayinmu na iyaye"





Jikin Bilkisu yai sanyi, ta fara yin fifita da ɗankwalin hannunta duk da kuwa sanyin AC ya ratsa falon.



Kaman wanda aka tsikari Bilkisu haka ta tashi ta fice daga falon.



"Tsanar da kika min har ta kai haka"



Asiya ta zaro ido dan a tunaninta ya gano cewa ita ta rubuta labarin ne, sai kuma ta ji ya ƙara da cewa.




"Na karɓi wayan Nana, na ga irin saƙonni data dinga tura miki. Lokacin da tace tana sonki miyasa baki faɗa min ba? A matsayina na Uba ba kya ganin ya dace na san 'yata tana yiwa wata mace 'yaruwarta kallon da bai dace ba"



In dai ya ga chats ɗinsu to babu halin ta masa ƙarya dan a ƙasan wajen da Nana ta ce mata "I love you" tambayarta tayi wani irin so, Nana ta amsa da cewa " ina son lips ɗinki, ƙirjinki, bayanki, kai komai na halittar ki"




"Ko a tunaninki yarinyar shekara shabiyar ya kamata ta dinga faɗin irin wannan maganganu?"



Idan ya cigaba da bin diddigi zai iya alaƙantata da jaridar Climax kuma ba yanzu take so ya sani ba. Ta yi saurin cewa " ni ban ɗauki wannan komai ba tunda na ga kamar tarbiyyan gidan kenan. Kana gani 'ya'yanka na yin shiga da bai dace ba a cikin gidan nan bayan akwai ma'aikata maza, baka taɓa musu magana ba, ban taɓa gani suna karatun addini ba, bana ma tunanin suna zuwa Islamiyya. Rayuwar da kuka ɗaurasu irin ta turawa ce, sannan a wajen mahaifiyarsu ni jikar maiƙusumbi ce, a wajenka kuma ni hajar Kamfen ce. Taya zan ƙalubalanci abinda 'yarka ke faɗa mini, ƙila ba matsala bane a wajenku"



Tun kafin ta gama bayanin Gwamna ke kokawa da numfashinsa, yana ƙoƙarin ciro inhaler a aljihunsa inhaler ta faɗi ƙasa.


Asiya ta yi saurin ɗauko inhaler ta matsa kusa da shi ta jijjiga sannan ta miƙa masa, ya haɗa da hannunta ya matsa inhaler ɗin a bakinsa.



Kallonsa ta ke yi yadda lokaci guda ya rikiɗe har jijiyoyinsa sun taso saboda wahala. Matsayinsa ba komai bane a hannun wannan lalura.



"Nagode" ya faɗa bayan numfashinsa ya daidaita.




Asiya ta girgiza kai sannan ta fita daga falon zuciyarta fal. Ta ji daɗin ganinsa cikin halin tashin hankali, itama haka mahaifiyarta ta shiga damuwa lokacin da aka ɓata mata suna a media.

"Yadda Umma ta zubda hawaye saboda abinda kuka min haka kaima sai ka zubda hawaye saboda 'yarka. Ita kuma waccar kucakar matar taka rananda aka koreku a gidan nan zata san cewa ba a dawwama a matsayin Matar Gwamna"



Da wannan tunanin Asiya ta shige ɗakinta tana jiran yadda za su ji wata sati idan aka kai masa impeachment notice.




Daren ranan Gwamna ya je ya samu Alhaji Sani akan yana son ajiye aikinsa.



"Kanada hankali kuwa, Saifu mi kake nufi za ka yi resigning. Saboda abinda wata jaridar ƙarya ta rubuta akan 'yarka. Miye ne a ciki idan duniya ta san Nana na shaye-shaye, kai ne kaɗai Gwamnan da yake da yara masu shaye-shaye. Ban yarda da wannan maganar ba, ta mutu a nan"




"Baba ko da ban yi resigning ba, ba zan nemi takarar zaɓen bana ba"



"Ba za ka ɓata min shiri ba Saifu, shekara takwas ɗin nan sai kayi Gwamna a jahar nan. Ban yafe ba idan ka yi resigning"



"Baba..."




"Idan kuma zaka nuna min cewa ba nina haifeka ba to, Bismillah"



Gwamna yai shiru bai iya cewa komai ba.

Kafin ya bar gidan sai daya leƙa sashen Dadda. Ya samu Mahira tana karatun ƙur'ani a falon Dadda. Zuciyarsa yai sanyi, da zai maida hannun agogo baya da duka yaransa biyun zai ajiyewa Dadda, ƙila da Nana itama halin Mahirah za ta tashi da shi



"Ina 'yaruwar ki?"

Ya tambaya bayan ta gaisheshi.




"Tana bacci"



"Dadda fa?"



"Tana sashen GrandMa"



"Mahirah"



"Yes Daddy" ta amsa tana rufe ƙur'anin da ke hannunta



"Akwai abinda kike buƙata, ina nufin baki da matsala, ba abinda ke damunki?"



Mahirah ta girgiza kai tausayin mahaifinta ya kamata. Yana ƙoƙari sosai a kansu, shi dai kawai sanyinsa ne da yai yawa yasa a mafiya lokuta yake biyewa mahaifiyarsu.



"Ehm Daddy, Dan Allah kar a kai Nana ƙasar waje, idan aka barta a nan ma zata warke, zata dena duk abinda take yi"



"Allah ya miki Albarka" Mahirah ta amsa da Amin.

Shima tunanin da ya zo masa kenan da Alhaji Sani ya ce bai amince ya ajiye muƙaminsa ba. Dama da ya amince ɗin yai niyyar zai tattare iyalinsa ne su koma ƙasar waje, a nan kuma zai kai Nana rehabilitation centre har sinadarin ƙwayoyin da tai ta sha ya bar jininta. Sannan a cire mata sha'awar mata.



***



Labarin 'yar Gwamna ya zamo abin hira a kowanne lungu da saƙo na Jahar. Kowa sai tofa albarkacin bakinsa yake. Wasu na zagin Gwamna wajen rashin bawa 'yarsa tarbiyya wasu kuma na ganin cewa laifin first lady ce saboda ai mace aka sani da tarbiyya domin itace ke tare da 'ya'ya koda yaushe.



Mai bawa firstlady shawara ya fito ya ƙaryata maganar maɗigo da jaridar Climax ta soki 'yar Gwamna da shi sannan sun rantse cewa Nana Kachallah bata shaye-shaye, a wajen party ƙawayenta suka tursasata ta sha shisha. Kuma za su shigar da jaridar Climax ƙara.



Ko kaɗan Asiya ba ta ji ɗar ba da wannan magana koba komai ta samu abinda take so, yadda aka yi ta yawo da ita a yanar gizo ana gulmanta haka nan itama Nana za ayi ta gulmanta har zuwa wani lokaci, kuma hakan zai ƙona ran Gwamna ita kuma duk abinda zai ɓata masa rai sai ta yi.

Yanzu jira kawai take ta rubuta labarin da zai wargaza Gwamnatin Saifuddeen Kachallah.







***





Ranan Litinin ƙarfe tara na safe aka kawowa Gwamna notice na impeachment trial. Bai yi mamaki ba saboda tun lokacin daya rage kuɗin allowance da ake bawa members na state house of assembly suka fara nuna ɓacin ransu gareshi. Ba abinda zasu iya tuhumarsa da shi. Record ɗinsa is clean. Sai dai dama tunda yana son ajiye aiki ƙila yanzu Alhaji Sani zai bari yai resigning kafin a fara trial ɗin.



Ya kira Alhaji Sani ya sanar da shi gameda takardar da aka kawo, tun a wayan ya bircike

Please Login or Register in order to submit comment