Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ranta komai zai zo ya wuce amma zuciyarta bai shirya ma yarda da zancensu ba balle har ya amince da shi. Ubaydullah shine masoyinta na farko kuma na ƙarshe, ita tunda ta taso ma bata taɓa son wani ba, ko crush na primary ko secondary school bata taɓa ba. Ubayd ta fara so tun lokacin da ya ɗauka mata tsumman abunta, tun lokacin bata san so ba.

Saboda Ubayd bata taɓa bawa wani damar shiga rayuwarta ba. Ko lokacin da take Jami'a da tayi tashe, samari ke mata chaa babu wanda ta taɓa buɗewa ƙofa. It has always being Ubayd and will always be.



Yayinda Asiya ke fama da damuwa, a chan gida kuwa Ale Faruƙ ya kasa ya tsare wajen ganin wannan biki ya tafi yadda ya kamata. Sati ukun nan gani yake kaman ba za su iso ba. Tun yanzu ya fara kiran kansa sirikin Gwamna har tambayar siriki yai da turanci aka ce masa Inlaw amma idan shi ya faɗa sai kaji kamar 'yanlo yace.

Yi masa kirari da sirikin Gwamna kaga ya ɗau kyautan dubu ya baka mutumin da ɗarinsa idan ba a mace ba baya iya bayarwa.



Tuni yasa aka yiwa gidansa sabon fenti. Matansa da sauran yaransa duk ya musu ɗinkin biki kala biyar biyar hatta yayyen Asiya da ke gidajen mazajensu ya aika musu da nasu kayan. Wannan kashe kuɗi ko a sallah albarka. Shi dai yanada abu ɗaya gidansa ana cima mai kyau amma wani siyan kayan sawa ko na ado to ko a sallah sai anyi da gaske, yawanci ma iyayen 'ya'yan ke musu. Haka batun makarantar boko idan ka wuce sakandare sai fa ka tallafawa kanka. Mace ɗaya ce tayi karatu a 'ya'yansa mata bayan Asiya, itama kuma a gidan mijinta tayi. Adda Hadiza kenan da ta karanci ɓangaren midwifery.





***



"It was for political reasons Bilkisu"



"Shine sai dai naji a bakin Babana"



"Sanda kika dawo bana gari kuma wannan magana bata waya bace"



"Saifuddeen ka rasa wacce zaka aura sai 'yar Kurma jikar maiƙusumbi" ta tintsire da dariya. "I'm sure ba wai zaka nemi haihuwa da ita bane ko? dan ba zan juri ganin 'ya'yan guragu, kutare da makafi a gidan nan ba"



Gwamna yai seƙeƙe yana kallonta. Ita ce dai da take zuwa gidan marayu tana ɗaukan hotuna da naƙasassun yara.



"Na ɗauka baka ƙyamar nakasassu Bilkisu"



"Oh please Saifuddeen. Ka sani sarai campaign nake yi"



Ido ya zuba mata ya rasa ma mi zai ce. She never seizes to amaze him.



"And Darling, ka sani zan haƙura ne kawai saboda lokacin campaign ya kusa, bana son abinda zai ɓata maka ƙuri'u. Abu na ƙarshe kuma shine ka nema mata wani gidan dan a nan" ta juya yatsarta manuniya "ni kaɗaice Matar Gwamna"...


2g Novels




Home / THE GOVERNOR'S WIFE / THE GOVERNOR'S WIFE 13
THE GOVERNOR'S WIFE 13
2g novels THE GOVERNOR'S WIFE






*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....







*©Azizat Hamza*



wattpad Azi_zat





Bismillahir Rahmanir Rahim









Book one









*Assalamu Alaikum*



*Barkanmu da warhaka. Babu kalmar da zan iya baku haƙuri da shi daya wuce na haɗa ku da Allah. Dan Allah kuyi haƙuri.*

*Ban so na kai waɗannan ranaku babu update babu bayani ba. Amma akwai dalilin daya sa na yi haka.*



*Kwanan baya nayi rubutu ina son na yi copy and paste sai nayi deleting nashi. I was blocked, for days na kasa sake typing. Daga baya nace ni da update sai na kammala typing part 1. Na dena hawa online ne saboda bana son distraction.*

*Wanda suka min magana ta whatsapp ko wattpad ban amsa ba, ina baku haƙuri. Wanda suka kirani numba na a kashe suma ina basu haƙuri. Ya kamata ace nayi muku bayani amma banyi ba. Ina neman afuwa akan haka.*

*Insha Allah part 2 zai fara zuwa daga ranan Asabat idan Allah ya kaimu.*



*Nagode da haƙuri da ni...*













13







Matar Gwamna. Ayyiriri Amarya"




"Queen Bee bana so, ki bari. Tukunna ma ya akayi kika sani? "



Queen Bee ta ɗaga mata waya tana faɗin Umma.



"Haba Asiya! So kike a kaiki gidan Gwamna kamar wata ƙwarangal. Look at you"



"Idan wannan ya kawoki, tashi ki tafi"



"Baki isa ba, Wallahi baki isa ki ja mana kunya ba. Dole sai anyi miki gyaran nan"




"Zaki yi ki barni dan ba abinda zanyi"



Duk yadda Queen Bee ta so su fara gyara Asiya bata ba da haɗin kai ba. Duk da Umma ta sa baki hakan baisa ta chanja ra'ayinta ba.




Ana saura kwana bakwai a ɗaura aure, da safe irin ƙarfe goma shaɗaya aka kawo lefen Asiya. Lokacin bata gida, ta raka Sumayya makaranta, za ta fara registration dan ta samu admission a Jami'ar Congo.



Lokacin da Asiya da Sumayya suka shigo gidan, a cike suka samu da mutane, yawanci maƙota ne sai kuma 'yan tsirarun 'yanuwansu dake zaune a Congo.



Faty 'yar Inna Yaha ce ta jata suka shige falon Abba saboda ɗakin Umma a cike yake da baƙi.




"Ban gane mi yake faruwa ba, wani taro ake yi a gidan?"



" 'yaruwa kinga lefenki kuwa?"




Ƙoƙarin buɗe ɗakin Abba ta shiga yi Asiya ta katseta. Bata buƙatar ganin koma minene aka kawo. Ashe shiyasa jiya da yamma Umma da Fatyn suka wuni suyan kaji a kitchen.



"Ki barshi Faty, ba sai na gani ba" Faty bata bari ta ƙarisa ba ta jata suka shige ɗakin.

Akwatuna ne akan gado gefen gado da duk wajen da akwai sarari. Wasu baƙaƙe, wasu ja, wasu blue, wasu brown, wasu lemon green da kalan silver.




"Ashirin da huɗu cif" Faty ta faɗa tana wage haƙora.



"Yanzu Anty Faty an buɗe dukkansu?" Sumayya ta tambaya cike da farin ciki.



"Guda shabiyu aka buɗe, Hajiya Adda tace a barsu haka, wai da ana maida kayan an rasa zannuwa uku a ciki"




Asiya juyawa tayi ta bar musu ɗakin dan ba zata juri ganin kayan takaicin nan ba. Ubayd ya kammala haɗa kayanta kawowa ne kawai ba ayi ba. Akwatuna biyar ne kuma ta riga ta san minene a ciki saboda fiye da rabin kayan kuɗi ya bata ta siya, wasu kuma sukan je siya tare. Lefen da Ubayd ya haɗa shi take so, ba wannan kayan ƙaryar ba.



Fita tayi daga gidan gaba ɗay ta wuce shagonsu. Tana cikin keke text ɗin Umma ya shigo, ta maida mata amsa da cewa shago zata je.







Saura kwana huɗu ɗaurin aure sai ga text ɗin Ubayd a wayarta, yace ta zo ta sameshi a office ɗinsa da ƙarfe biyar na yamma. Ƙarfe uku text ɗin ya shigo, dan haka tana sallar La'asar ta ce da Umma zata fita, Umma tace ba inda za ta je. Hakan ya sa ta mata ƙarya akan gidansu Queen Bee za su je karɓan saƙo ita da Sumayya. Umma tace su je amma lallai su dawo kafin ƙarfe shida na yamma.





***



"Daddy da gaske aure zaka ƙara?" Nana tayi magana tana tsare mahaifinta da idanu.



Gwamna yai shiru bai ce komai ba.



"Ka bata amsa mana Mijin 'yar Kurma"



Gwamna ya maida dubansa ga Hansa'u da ke bawa Junior abinci a baki yace "Kada ki sake bashi abinci a baki. Kada wanda ya sake bashi abinci a baki"



"Tuba nake ranka ya daɗe" Hansa'u ta faɗa tana ajiye cokalin da ke hannunta



"Kar ka saukar da fushinka akan ɗana. Kai ka sawa kanka auren jikar maiƙusumbi" Nana da Zunnairah suka fara dariya ƙasa-ƙasa.



Ko kallon Bilkisu bai yi ba ya miƙe ya bar dining room ɗin. A irin wannan ranaku da yake samun daman zama da iyalinsa ba abinda yake so sama da soyayyarsu. Sai dai yanzu kam Bilkisu ta gaza bashi wannan soyayyar. Dolene ya takawa Bilkisu birki. Juniour ba yaro bane da sai an bashi abinci a baki. Nana ta yi girman da bai kamata ta masa magana karangatsau haka ba, sai dai koma minene shi ya jawo wa kansa.



A ƙaramin falo Bilkisu ta zauna ita da babbar ƙawarta Madam Bintu suna tattaunawa kan kasuwancinsu. Bayan Hansa'u ta kawo musu abin taɓawa sai kawai suka ga ta zauna a tsakiyar falon ta ƙurawa TV ido.



"Hansa'u lafiya? Baki da aikin yi ne?"



"Shirin su Aarti da Yash zan kalla"



"A duk faɗin gidan nan sai a nan zaki yi kallo. Tashi maza ki bani waje" Bilkisu ta daka mata tsawa.



"Kema dai Bilkisu miyasa zaki kawota nan. A chan gidanku ma tana shirme balle a nan"



"Akwai ƙauyanci a tattare da ita amma ta iya aiki ne Bintu. Kuma gaskiya ban sake da ma'aikatan gidan nan ba duba da cewa sun yiwa Sha'awanatu aiki a baya. In fact, chief cook ɗin ma sai dana sa aka chanja shi"



"Wai baza ki tashin bane?"

Hansa'u ta miƙe tana susa kai ta bar wajen.



***



Da sauri-sauri take tafiya zuciyarta na tsalle a cikin ƙirjinta. Ita kaɗai ta san ya take ji a ranta.

Tana son shi, tana fushi da shi, tana kuma tausayinshi.



Sai da ta ja dogon numfashi kafin ta buɗe ƙofar office ɗinsa a hankali.

Ubayd na zaune a madaidaicin office ɗinsa da ke ɗauke da wata na'ura da ake duba idon mutane. Akwai kujeru biyu na zaman masu jinya. Akwai manyan hotonan ido da akayi rubutu ajiki a bangon office ɗin.



Farar riga da likitoci ke sanyawa ya ɗaura akan jamfar da ya saka kalar toka. Fiskarsa ɗauke da baƙin gilashi daya ɓoye idanunsa.

Sautin karatun ƙur'ani ke fitowa daga laptop ɗinsa, shigowarsu ya sa shi katse karatun.



"Ina wuni Yaya" Sumayya ta gaisheshi idonta na kallon ƙasa, duk da yana sanye da gilashi ba zata iya kallon idonsa ba.

Duk cikin 'ya'yan Ale, Asiya ta fi jituwa da Sumayya shiyasa ya mata farin sani. Tun kafin ta ƙare Sakandare ta sha zuwa hutu wajen Asiya.



"Lafiya Sumayya, yaushe a gari?"



"Na ɗan kwana biyu"



"Bismillah, ga kujera"



"Barin baku guri" bata ji ma mi yake faɗa ba ta fice daga office ɗin da sauri har lokacin Asiya na tsaye ta zubawa Ubayd ido.





"Ki zauna Asiya"



Kafin ta zo ta tanadi maganganun da za ta faɗa masa amma ganin fiskarsa ya share komai na kwanyarta.



"Asiya ..."



"Kai na ke so Ya Ubayd, fight for me, fight for us" ta faɗa lokacin da ta zauna



"Asiya muyi haƙuri"



"Zamu iya guduwa Ya Ubayd, there's still time. Mu je Kano gidan..."



"Ba inda zamu je Asiya"



"Saboda ka dena sona? Saboda kana tsoro, Saboda..."



"Saboda na karɓi ƙaddarata da hannu bibbiyu. Saboda nayi alƙawarin yiwa mahaifina biyayya matuƙar ba abune daya saɓawa addini ba"





"Oh! Ni ce ban san mi nake ba ko. Ni ce bana girmama iyayena ko?"





"Ina sonki Asiya Shahidah. Bana tunanin zan so wata kamar yadda nake son ki. Amma in har aurenki da Gwamna zai kawo..."



"Ya isa!" Miƙewa Asiya tayi tsaye, ta sa hannu ta goge fiskarta fes babu ko ɗigon hawaye.



"Ya Ubayd ka ci amanata, ka ci amanar soyayyarmu. Zan auri Gwamna, but mark my words Ya Ubayd, Ni Asiya sai na ga ƙarshen Gwamnatinsa, Ka huta lafiya"



"Mine... Asiya... Asiya... Asiya"



Ciro hankerchief yai daga aljihun labcoat ɗinsa ya shiga goge gumin goshinsa, Shikenan daga yau bashida ikon kiranta Mine. Lokacin daya cire gilashin idonsa sakanni kaɗan bayan fitan Asiya, hawaye ne masu ɗumi suka fara gangaro masa. Chan cikin zuciyarsa kuma yana yiwa Asiya addu'ar Allah ya sassauta zuciyarta kar taje tayi abinda za tayi dana sani daga baya...





**



Kwana uku saura ɗaurin aure gari ya ɗauka cewa Gwamna zai ƙara aure. Ba kuma kowa zai aura ba sai 'yar jaridan nan da ta so ɓata masa suna kwanakin baya.

Mutane suka fara tofa albarkacin bakinsu akan batun, wasu na ganin kwata-kwata bai dace ba, wasu kuma suka fara cewa ai dama chan karuwarsa ce, maganganu dai kala-kala.



Bilkisu Kachallah ce ta juya akalar maganar inda ta fito ta bayyana cewa tausayin mahaifin Asiya yasa Gwamna ke son auren Asiya Faruƙ Baba. Ta bayyana cewa, sun samu labarin saurayin da zai aureta ya fasa saboda abinda ta aikata, kuma yadda duniya ta riga ta san abinda Asiya ta yi babu namijin da zai so aurenta. Yadda iyayenta sukayi ta roƙon Gwamna shiyasa ya ji tausayinsu, ya musu wannan alfarmar akan zai auri Asiya dan ya rufa mata asiri...



An gama zanawa Asiya lalle tana jira ya bushe a cire Queen Bee ta gaya mata abinda ta gani yana yawo a social media.



"Baby kar ki damu, idan kika shiga gidan ki yi maganin shegiya" Queen Bee ta faɗa dan ta kwantar ma Asiya hankali



"Yanzu Ya Ubayd ma sai da aka ɓata masa suna"



"Shahidah dan Allah kar ki saka wannan a ranki. Bari kiga a ɗaura auren nan, wallahi sai abinda kika ce a faɗa za'a faɗa"



Tunda ta bar office ɗin Ubayd ta sawa ranta indai ta shiga gidan Gwamna Saifuddeen Kachallah to sai inda ƙarfinta ya ƙare amma yadda ya rabata da masoyinta itama sai ta rabashi da kujerarsa.

Tun daga lokacin ta sake jikinta duk abinda akace tayi, tanayi.





***



Minti arba'in kenan da kiran Bilkisu da yai amma har yanzu bai ga idonta ba.



"Darling" ta faɗa lokacin da ta shigo ɗakinsa fiskarta ɗauke da murmushi.



"Sorry na jima, maganar aurenka ne ya riƙeni. Ka san cewa Hajiyan Saudiyya zata shigo gobe, yaushe rabonta da Nigeria. Ni inaga ma kamar jira dama take a min kishiya ta zo taron biki"



"Bilkisu please!"



"Idan akan abinda na faɗa ne to ka sani duk abinda zai ɗaga darajarka a idon mutane zan yi, saboda an kusa zaɓe"



"Ba sai kin ci zarafin iyayenta ba Bilkisu. Ya kamata ki san..."



"Idan akan wannan ka kirani, then excuse me, inada aikin yi"



"Ba wannan kaɗai bane" ya faɗa ƙasa-ƙasa yana ƙoƙarin danne ɓacin ransa.



"Asiya zata zauna a gidanmu na da..."



"Asiya zata zauna a Kachallah House" Bilkisu ta ƙatse shi tun kafin ya dasa aya.



"Na riga nayi magana da Hajiya Umma akan za'a..."



"Matarka zata zauna a Kachallah house. Idan kuma chan bai isheta ba ka iya siya mata wani gidan daban amma wancan gidan Bilkisu ne" tana gama maganar ta fice masa daga ɗaki.



Dunƙule hannunsa yai yana huci. A waje shi Gwamna ne, a cikin gida kuma shi mijin Bilkisu ne. Ba yau ta fara fita daga ɗaki idan suna tsaka da magana mai mahimmanci ba amma yau abin ya taɓa shi sosai.





***





*Takawarki lafiya Asiya Matar Gwamna.... Ayyiriri yiriri yiriri*



Guɗa da kirari ke tashi ta ko'ina, masu watsa filawowi nayi, masu yawo da turaren wuta nayi, haka aka shigo da Amarya Asiya ɓangaren Hajiya Dadda kakar Gwamna. Hajiya Dadda na zaune da wasu manyan mata aka zaunar da Asiya gabanta, Asiya na sanye da alkyabba ruwan Gwal ko fiskanta ba a gani saboda hular alkyabban ya rufe. Dadda ta riƙo hannun Asiya ta dinga zuba mata addu'a. Bayan an gama da wajen Hajiya Dadda aka kai Asiya wajen Hajiya Aisha mahaifiyar Bilkisu.



Hajiya Umma ce ke gaba akan komai, tunda Gwamna ya kirata ya gaya mata cewa a Kachallah House Asiya zata zauna ta shiga faɗa, wai sam ba zai yiwu ba. Bilkisu ba zata ja musu magana ba. Yadda aka riga aka tsara hakan za ayi. Za a fara kawo Asiya Kachallah House tayi kwana ɗaya, washegari a wuce da ita gidan Saifuddeen.

Duk cikin ƙannen Alhaji Sani, Hajiya Umma ce macen da ko shi Alhaji Sanin ba ƙaramin shakkanta yake ba. Tanada faɗa sosai kuma bata ragewa kowa.



Bai san ya suka ƙare da Bilkisu ba, da dare daya shigo gida Bilkisu ta sameshi akan cewa ya sani bata yadda a saka Asiya a sama ba. Indai wannan ne da sauƙi dan dama a ƙasan aka shiryawa Asiya kayanta.



Bayan sun bar sashen Hajiya Aisha sai aka wuce da Asiya ɓangaren Saifuddeen lokacin yana saurayi. Ƙaramin falo ne da ɗaki a ciki haɗe da banɗaki.



Anata shigowa gaishe da Amarya sai ƙarfe shaɗaya da rabi Hajiya Umma ta kori mutane aka bar Asiya da ƙanwarta Sumayya, Faty da kuma ƙawarta Queen Bee.



Gobe da safe za'ayi wuni da yamma kuma ayi dinner wanda Bilkisu Kachallah ta shirya.



Bayan an watse ne Asiya ta samu ta cire kaya ta shiga banɗaki dake cikin ɗakin ta fara wanka. Kuka ta saka lokacin da ruwan shower ya fara sauka mata. Kukan da bata yi ba lokacin da za'a kawota, kukan da bata yi ba lokacin da aka kaita gaban Abba yai mata nasiha.



" an ɗauraaaa, Anty Asiya kin zama matar Gwamna" maganan Sumayya kenan tana tsaye dai dai ƙofar ɗakin Umma.



Live aka nuna ɗaurin auren a gidajen talabijin. Hakan ya sa 'yan biki suka cika falon Abba da ɗakin Inna Yaha sai kuma masu kallo a waya. Umma kam dama babu TV a ɗakinta shiyasa Asiya ta samu salama, ta kwanta tana ayyana abubuwa da dama a ranta. Su uku ne a ɗakin sanda Sumayya ta leƙo tana faɗa mata munanan kalamai. Umma da ba jin mi ta faɗa tayi ba ta cigaba da ninke kaya. Wata Goggon Asiyan da ke kwance saboda ciwon kai ta miƙe zaune tana doka kabbara lokacin da taji abinda Sumayya ta faɗa.



"Anty kinga fiskar Ale kuwa ? da aka nunoshi kaman mai tallen Makilin..."



"bar nan Sumayya!"



Sumayya ta sake labule ta sa gudu.





Buga ƙofar da Queen Bee ke yi ya sa ta yi firgigit ta dawo hayyacinta.



"Governor's wife, fata zaki chanja a banɗakin ne wai? Muma zamu watsa ruwan fa"



Bata kulata ba sai kawai ta matsi shower gel ta fara shafawa a dogon gashinta wanda ruwa data bari ya zuba mata akai ya sa ruwan mai ya mamaye ilahirin jikinta. Ba ƙaramin gyara gashin ya sha ba a hannun Queen Bee saboda harkanta kenan.

Bayan ta gama wanke kan ya dena fitar da mai sannan ta yi wanka ta ɗaura towel ta fito.



"Queen Bee akwai hand dryer a kayanki?"



"Yanzu wanke kai kikayi tun Ango bai gani ba"

Queen Bee ta faɗa tana taɓe baki.



"Kin zo da shi, e ko a'a?" Tayi maganar da ɗan ƙarfi dan ruwan kanta ya fara sauka ƙasa saboda bata goge kan ba.



"Barin ɗauko miki"



Faty na zaune bakin gado tana kallon ikon Allah. Babu walwala ko kaɗan tattare da Asiya irin na Amaren nan. Lokacin da aka kira mai hoto cikin gida ana ɗaukan hotuna ko sau ɗaya bata murmusa ba, ƙarshe ma cewa tayi kanta na ciwo ba zata iya tsayuwa ba.

Anya Asiya ba zata yi wani mugun abu ba kuwa wajen dinner ɗin da za ayi? Ko kuma ma idan an kaita tayi ƙoƙarin illata Gwamna. Tayi saurin kauda tunanin a ranta da cewa Asiya na da ilimi ba zata yi wannan haukan ba.

Asiya ta kunna hand dryer ta fara busar da gashinta, Faty ta miƙe daga inda take kishingiɗe ta ce " kawo na miki"



Lokacin da Queen Bee ta fito daga banɗaki suka rutsa Asiya da ke shirin bacci da nasiha. Faty a matsayinta na ƙanwar Ubayd kuma ƙawa ga Asiya tunda duk cikin 'ya'yan Inna Yaha itace suka shaƙu ƙwarai, shiyasa ma aka saka aurensu lokaci guda ita da Asiya kafin lamari ya chanja. Faty ta bata shawaran ta manta da Ubayd ta rungumi mijin da Allah ya bata.



Queen Bee ma a matsayinta na babbar ƙawa wacce suka yi Jami'a tare, sannan suka haɗa business tare, ta bawa Asiya shawaran haƙuri da hukuncin Allah.



Asiya jinsu kawai take amma ba abinda ta ɗauka cikin maganganunsu. Tun kafin Queen Bee ta ida maganarta Asiya tace ta gaji, bacci za ta yi.

Asiya ta samu gefen Sumayya da ta jima da bacci ta kwanta zuciyarta na harbawa da sauri-sauri.







***



Zurmemiyar wuƙa Asiya ta ɗauko a kitchen ta wuce ɗakin Gwamna da shi. Yana tsaye sanye da farar jallabiya yana waya ya bata baya, a hankali ta ƙariso ta zurma masa wuƙa a gefen cikinsa.

Gwamna ya saki ƙara, ya juyo a hankali yai taga-taga kamar zai faɗi ƙasa Asiya ta riƙo shi "I hate you Saifuddeen Kachallah" ta faɗa tareda ƙara danna wuƙar ciki sosai.



Buɗe idon da Asiya tayi ta hango ceiling ɗin ɗakin. Dogon numfashi ta ja kafin ta ce a ranta " ba zan kashe ka ba sai dai..."



*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....







*©Azizat Hamza*



wattpad Azi_zat





Bismillahir Rahmanir Rahim









Book one







14





***





Tunda su Asiya suka ci abinci suka koma sashen Dadda. Daga safe zuwa yammaci baƙi ne ke ta shigowa ganin Amarya. Matan manya da kuma manyan manyan Mata da su kayi suna a ƙasar. Wasu kallon ƙwaƙwaf ne ya kawosu saboda a samu latest gist da za a tattauna idan an haɗe a wajen shaƙatawa, wasu kuwa sun zo ganin Asiya Shahidan da ake kururutawa ne saboda ba su santa a Talabijin ba. Wasu kuma sun zo ne domin samun gindi a wajen Asiya dan basa shiri da Bilkisu Kachallah.



Asiya bata bada fiskar da zai sa a gane tana cikin matsala ba. Ko Faty da Queen Bee sun yi mamakin yadda ta sake tana dariya cikin mutane kamar auren soyayya akayi.

Kusan ƙarfe biyar da rabi na yamma Anty Saudah ƙanwar Bilkisu ta kawo musu wata jaka tace kayan da Amarya zata saka ne a wajen dinner. Basu waiwayi kayan ba saboda suna cikin jama'a.

Ƙarfe bakwai da minti Arba'in bayan Asiya ta idar da sallar Isha ta shiga banɗaki ta watsa ruwa. Suna ɓangaren da suka kwana jiya, su huɗu ne a ɗakin a chan falo kuma ƙawayen Asiya na makaranta ne da abokanan aikinta da suka samu pass ake wa kwalliya. Queen Bee ce ta karɓo pass ɗin dan haka Asiya bata san iya mutanenta da zasu zo wajen dinner ba.




Tunda Queen Bee ta fito da kaya Asiya ke girgiza kai, amma bata ƙi ta su Faty ba da suka ce ta dai gwada ta gani. Abu ɗaya ta sa aranta shine ko ta sha giyan wake ba za ta sa wannan kayan ta fita waje ba. Gown ɗin yayi ba ƙarya, ya amshi jikinta, duk wani tudu na jikinta ya fito sosai, sai dai rigar offshoulder ce rabin ƙirjinta a waje yake sai net da aka rufe wajen da shi wanda ko makaho ya shafa ya san ba abinda net ɗin ya tare. Cikinta ma net ɗin aka saka saboda an fafe lace ɗin wajen ne aka saka net. Ɗinkin yayi kamar bra ta saka da skirt sai aka rufe sauran wajen da ke bayyane da net.



"Inaga za mu nemi shawl da zai je da kayan kawai sai..."




"Baki da hankali Bahijja" ta kira sunan Queen Bee na asali.



"Gaskiya dai wannan kayan sai a hankali" Faty ta faɗa tana girgiza kai, sai yanzu da Asiya ta sa kayan ta gano akwai matsala.






"Bilkisu Kachallah ta riga ta rubuta headline da zai fito gobe a labarai idan na sa kayan nan. Beside, ni ba mahaukaciya bace na san darajan gidan dana fito"



"Anty dan Allah barin ɗauke ki a hoto, wallahi kin yi kyau" Sumayya ce da wannan maganar.



"Ban yadda ba... ki bari" sai kawai ta haƙura ta tsaya saboda Sumayyan ta riga ta fara ɗaukanta hoto.



Ɗaya kayan dake cikin jakar ma babu kanta, atampa ce da aka yiwa fitanniyar ɗinki. Ko gwadawa batayi ba ta tura gefe.



Ba abinda ya rage sai dai su saka abinda suke da shi.




"Ko na yiwa Hajiya Umma magana ne? tunda dama tace za a kawo mana kaya na ce an riga an kawo" Queen Bee ta faɗa tana kallon Asiya da ke zaune a gefen gado daga ita sai zani.



"Akwai wani gown a jakar da nace ki tahomin da shi Sumy, ɗauko min"



Tayi maganar kaman mai shirin yin kuka. Malaysian gown ne data gani a Amazon watanni kaɗan da suka wuce. Simple gown ce ruwan madara da aka yiwa design da duwatsu ruwan gwal. Model ɗin data saka kayan ta yi rolling da gyalen kayan ta saka crown a kanta kamar sarauniya. Asiya alokacin data ga kayan hango kanta ta yi sanye da irin kayan tana zaune kusa da Ubayd a ranan da za ayi kamunsu.




Su Queen Bee sun yaba da gown ɗin, sai dai kamar yai kaɗan ace Matar Gwamna guda ta sanya gown irin wannan da kuɗinsa ba zai wuce dubu hamsin ba. Kuɗin shipping dana kayan duka-duka dubu arba'in da huɗu Asiya ta siya a kuɗin Nigeria.



Lokacin da Queen Bee ke mata rolling gyale wasu mata suka shigo wai suyi sauri motoci sun fara isowa, Gwamna ya kusa ƙarisowa.




Asiya tace ba make up, amma duk da haka sai da Queen Bee ta shafa mata powder, ta sa mata mascara ya ƙara fito da dogon gashin idonta, sai kwalli da man leɓe, shikenan.



Ɗankunne da sarƙan diamond da aka haɗo a

Please Login or Register in order to submit comment