Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da abokin aikinta suna komawa gida wata babbar mota ta afka musu..."



"Is she alive?" Ya faɗa da tsananin damuwa a tattare da shi



"Na ji labarin dukansu suna raye. Ita Asiya ance nata da sauƙi amma shi ɗayan kam rai a hannun Allah"




"Hasbunallah! Keep me posted akan labarinta" ya faɗi labarinta kamar ita ɗaya akace tayi hatsarin.

Bayan fitan Sakatare daga office ɗinsa ya ɗaura haɓarsa akan hannunsa yana tuna siririn ushiryar dake tsakanin haƙoranta wanda yake ƙara mata kyau idan tana murmushi.






***





Umma ne a gefen gadon da aka kwantar da Asiya lokacin da Ubayd da Abba suka shigo. Abba ya tambayeta ko Asiyan ta tashi tace masa bata tashi ba. Lokacin daya zauna ta tambayeshi jikin abokin aikin Asiya Abba yace ance musu har yanzu bai farfaɗo ba. Ubayd ya ƙurawa Asiya da ke kwance ido bai san lokacin da hawaye ya fara zubo masa ba. Ba dan kariyar Allah ba da ita ne ke halin da CY yake ciki ko kuma ace da yanzu an jima da bisineta. Yai saurin goge hawayensa dan kar Umma ta gani. Alhamdulillah ya furta a ransa kafin ya yiwa su Umma sallama ya fita.




Ba a jima ba Asiya ta farka a karo na biyu tun safiyar yau. Da farko data farka kuka ta dinga yi tana faɗin a kaita wajen CY. Yadda ta birkice musu sai da aka mata alluran bacci.

Wannan karan ma data farka sunan CY ta kira. "Abba CY ya mutu ko?, sun kashe shi ko?"



"Kwantar da hankalinki Shahidah. Yana nan da ransa"

Da bata faɗa gefen titi ba, da ba wannan zancen akeyi akanta ba. Gefen goshinta, kunnenta da kafaɗarta sai kuma gwiwarta da ya kurje su kaɗai ne ciwon jikinta, sai dai saboda irin faɗuwar data yi duk jikinta ciwo yake mata.




Asiya ta sauke ajiyar zuciya hawaye na zubo mata.




"Abba idan CY ya mutu bazan taɓa yafe musu ba. Kuma sai na..."



"Asiya!" Ya kira sunanta da ƙarfi har sai da ta tsorata.



"Ba abinda zakiyi, kina jina? Nace ba abinda zakiyi. Zan mummunan saɓa miki idan kika sake maganan mutanen nan"



"Abba..."



"Zamuyi magana idan munje gida"



Ta kalli Abba da mamaki, ba yadda za ayi yai wannan maganar sai dai idan har yasan wani abu. Kenan Lamara Damana ya tuntuɓeshi.



Da yamma da Ubayd ya dawo ta tambayeshi ina CY yace mata CY na CUTH (Congo University Teaching Hospital ) an ɗaura shi a na'ura saboda ya shiga coma.

"Mutuwa zai yi ko?" Ta tambaya murya na rawa

"Mine mutuwa a hannun Allah take. Ki masa addu'a amma he's in a very bad shape infact an yanke masa hannu ɗaya"



"Ya Allah!" Ta riƙe baƙi.





'Yan wajen aikinsu sun zo sun gaisheta. MD shi kaɗai yazo da yamma lis kuma bai jima ba saboda lokacin ɗakin nata akwai mutane. Lokacin daya fita Abba ya bi bayansa da sauri. Bayan sun samu waje sun keɓe sannan MD ya bashi takardar dakatar da aiki na Asiya. Abban ne ya nemi hakan shiyasa yana karɓa ya masa godiya ya koma cikin Asibitin.

MD ya girgiza kai yana fata wannan ya zamowa Asiya mafita saboda ta tsokano tsuliyar dodo.



Kwanan Asiya biyar a Asibiti aka sallameta har lokacin kuwa ba suyi maganar abinda ya faru da kowa ba saboda Abba ya hanata. Kamar yadda kowa ya ɗauka cewa tsautsayi ne ya kawo hatsarin da suka yi Asiya ta san ba haka bane kuma ta san Abba da Ubayd ma sun san ba hakan bane.

Kafin su wuce gida ta roƙi Ubayd da ke tuƙi akan ya kaita taga CY. Da farko ya ƙi amma data takura sai Umma tace ya kaita itama tana son zuwa dubashi.



Lokacin da taga CY kwance an jona masa wasu na'ura a jiki sai kawai ta fashe da kuka. Da Allah yayiwo CY mace da zata iya cewa har abada ba za ta iya samun ƙawa kamarta ba saboda yadda jininsu ya haɗu kuma suka fahimci juna, sai dai CY namiji ne shiyasa abotar tasu take da iyaka.

Sun gaisa da mahaifiyarshi inda take jadaddawa Asiya cewa Gwamna ya biya kuɗin aikin da za a masa a ƙasar waje takardunta da ake processing yasa basu tafi ba sai wani sati. Jin Josephine mahaifiyar CY ta ambaci sunan Gwamna yasa zuciyar Asiya ta cunkushe, tsanar mutumin ya sake sauka mata. Munafuki ta faɗa a ranta, shine ya jawo wannan matsalar sannan yake ƙoƙarin rufe bakin mutane da maganar biyan kuɗin aiki. Ita Asiya ba zata yi shiru ba, tayi alkawari.



Sanda suka isa gida Abba ya zaunar da ita ya mata bayani.



"Abinda ya faru Asiya ki ɗauke shi a matsayin ƙaddara. Ki riƙe bakin ki da zargi domin ba abinda hakan zai jawo sai fitina. Na saka an dakatar dake daga aikin ki, daga yanzu babu ke babu aikin jarida. Ban sani ba idan kin koma ƙarƙashin ikon Ubaydullah ko zai barki kiyi amma iya watannin daya rage miki ƙarƙashin kulawata, na dakatar da aikin ki"



Asiya tayi saƙeƙe tana kallonsa



"Waɗanda kika samu saɓani da su sun zo sun karɓi laptop ɗinki na gida da wajen aiki dama wayarki amma sun dawo da wayar taki jiya. Sun bayarda saƙo a baki *ki cigaba da rayuwarki kamar komai bai faru ba, hakan zai sa su manta da komai*"



"Abba ya zaka min haka?" Ta ma rasa haushin wanne ɗaya za ta ji. Na halin da CY ya shiga saboda ita ne ko kuwa dai na aikin da ya hanata ne ko kuma na ɗauke laptop ɗinta da COS ya sa akayi. Abin takaicin ma a laptop ɗin kawai ta tura recording ɗin ba ta riga ta tura a wani wajen ba.



"Asiya ki yiwa Allah ki manta da komai. Bana so ko da Umman ki kiyi wannan maganar saboda kar hankalinta ya tashi"



"Abba dafa na mutu yanzu, dafa..."



"Ki godewa Allah kawai ki riƙe bakin ki Asiya"



Abba bai bata daman magana ba sai kawai ta fashe masa da kuka, da tayi mai isarta ta miƙe ta bar falon.



Tuwon shinkafa miyar taushe Umma ta zubo mata bayan tayi sallar Isha, ta haɗa mata da zoɓo mai sanyi. Duk yadda take marmarin ci kafin a girka yanzu ya fita mata aka saboda rasa recorder ɗinta da tayi, koya akayi suka samu recorder ɗin ma oho, dan a ƙasan katifar Umma ta saka bayan ta gama kwafan abinda ke ciki zuwa laptop ɗinta. It means bata da wani evidence kenan.

Umma ta katse mata tunani da cewa ta ci abinci

"Umma ki bani a baki" ta faɗa da yaren kurame. Umma tayi murmushi ta wanke hannu ta fara bata a baki.



Ƙarfe shabiyu na dare tanata juyi a kam gado ta kasa yin bacci. Wayarta da Abba ya bata an share komai na kai kamar sabon waya. Tunanin rashin imani irin na Gwamna ya tsaya mata a rai, ita yanzu ta daina ganin laifin COS ma dan gani take da umurnin Gwamna ya aiwatar da komai.

Ƙarshe ta jawo wayarta ta sake downloading twitter da facebook da aka goge. Tana saka gmail da password ɗinta na da ta samu access zuwa ga tsohon account ɗinta nan da nan ta shiga rubuta dogon article a blog website nata, data gama ta kwafa ta kai shi twitter ta jerasu a dogon thread of tweets . Ta kai facebook ma ta posting a wall nata. Tana ganin duka rubutun ya hau tace "Excellency yanzu aka fara wasan"

Yadda ake fama da talauci da wasu matsaloli wannan rubutu nata tabbas zai jawo hankalin mutane kan Gwamna and this is good.

Kalaman ɗan jarida suna da kaifi, kalaman da ke iya kunna jita-jita tsakanin al'umma ya maida gaskiya ƙarya sannan ƙarya ta koma gaskiya.

Kusan minti goma shabiyar kafin ta fara ganin comment na 'yan tsirarun mutanen da suka gani. Tana bin comments ɗin tana murmushi idan taga wanda ya yabi Gwamna kuma sai ta yi tsaki.

Asiya bata kwanta ba sai ƙarfe uku da rabi, dake Umma a ɗakin Abba ta kwana yasa bata samu mai tashinta da Asuba ba sai ƙarfe shida saura minti biyar da Umma ta shigo ɗakin ta tasheta sallah...





***



Chief of Staff Lamara Damana yana kwance kusa da matarsa ƙarfe huɗu da rabi wayarsa ta shiga ƙara. Bayan ya ɗau wayar miƙewa yai ya bar kan gadon dan wanda ya kira ɗin special agent ɗinsa ne mai kula masa da hidimominsa a yanar gizo.

"Ina jinka Felix" ya faɗa lokacin daya zauna a kujeran dake falonsa.



"Asiya again?" Ya faɗa yana cizen leɓe. Lokacin da aka tabbatar masa Asiya bata mutu ba sannan bata ji ciwo sosai ba yaso ya sa a ƙarisata a Asibiti amma daga baya ya chanja ra'ayinsa. Beside ita macece dole taji kashedin iyayenta.



Yanzu da Felix ke karanto masa abinda ta ɗaura yayi mamakin ƙarfin halinta.

"This girl! Yanzu dai kasa a blocking accounts nata, sannan ka controlling duk wata jarida da zata yi sharyi akan abinda ta rubuta"



Lokacin da Asiya ta idar da sallan Asuba ko Azkar bata yi ba ta jawo waya ta fara duba twitter account ɗinta sai dai kash! An riga an banning account ɗin tun misalin ƙarfe biyar na Asuba, ta zaro ido waje tareda duba website nata cikin sauri sai dai shima an blocking na shi, facebook ma haka.

Tayi ƙoƙarin searching article ɗin a google amma an sauke shi gaba ɗaya babu ko mai kama da shi.



"Nooo" ta faɗa tana kaiwa sallayar da ta ke kai duka...





Gwamna na zaune a office wayarsa ta shiga ƙara yana dubawa yaga sunan Baba.

"Saifu mi yake faruwane? Yanzu nake jin wai Umaru Kwom yayi wata magana a twitter akan abinda wata 'yar jarida ta ɗaura"



"Bani da labari Baba amma yanzu zan tabbatar"



"Nayi magana da COS amma ka tabbatar da adviser ɗinka ya kashe duk wani hayaniya da za ayi a yanar gizo akan maganar"



Gwamna na ajiye waya ya kira mai magana da yawunsa a yanar gizo.



Umaru Kwom abokin adawar Saifuddeen Kachallah ne saboda lokacin yana tareda Alhaji Sani Kachallah ya so ya zamo mataimakin tsohon Gwamna Saminu Bacchi amma Alhaji Sani ya ƙi ya tsaida Saifuddeen, tunda aka tsaida shi kuwa ya fice daga jam'iyyarsu ta CDA ya koma Q party.



Lokacin da Special adviser Ahmad Tanko ya shigo ko kaɗan Gwamna bai ji daɗin yadda aka ƙi sanar dashi abinda ya faru ba.



"Mi Umaru Kwom ya ce?"



"Excellency an riga an cire duk wani tweet ko post na 'yar jaridar amma awa biyu da suka wuce Umaru Kwom ya tweeting wasu maganganu daga ƙarshe ya haɗa da screenshot na tweet ɗin 'yar jaridar"



"What did he say?" Gwamna ya faɗa da ƙarfi.



Ahmad ya fito da wayarsa ya fara karanta tweet ɗin "inada tabbacin 'yar jaridan nan tayi gaskiya duba da yadda Gwamna ya biya kuɗin aikin da za ayi wa Clement Yohanna a ƙasar waje. Idan ba a manta ba Clement da Asiya sune suka je interview ranan, idan har babu lauje a cikin naɗi ba abinda zai sa ayi yunƙurin hallaka 'yar jaridar a ranan da tayi maganar mutuwar Gwamna Saminu Bacchi. Bisa wannan, muna so mu gayawa Gwamnatin SSK cewa duk abinda ya sami Asiya 'yar jarida nan gaba zamu yi ƙaran Gwamnati. #a binciki mutuwar tsohon Gwamna"



SSK ya sauke ajiyar zuciya kafin yace Ahmad ya miƙa masa wayar yaga rubutun da Asiya tayi.

Bayan ya gama karantawa ya miƙa masa wayar yace ya fita masa daga office ɗinsa.



Ba yadda za ayi Asiya tayi wannan iƙirarin idan har ba wai ta ga ko ta ji wani abu ranan da suka zo bane. Dole ne ya gana da 'yar jarida Asiya Shahidah...









***





"Shikenan ai tunda kinyi gaban kanki, kin nuna cewa ba nina haifeki ba"



"Abba ba haka bane, Wallahi ba haka bane"



"Kinyi gaskiya Asiya, ba nina haifeki ba ban kuma manta da hakan ba.Tunda ban isa na baki shawara ki bi ba shikenan Allah ya baki sa'a. Kije kiyi magana da Umaru Kwom daganan ku wuce kotu ku bi wa Marigayi Saminu Bacchi hakkinsa"



Asiya ta kalli Abba tana zaro ido. Kenan Ubayd ya gaya masa komai.



"Tashi ki tafi"



"Abba..."



"Tashi ki tafi kawai"



Jiki a sanyaye ta fice daga falon.



Ɗazu Umaru Kwom da kansa ya kirata yace yana son haɗuwa da ita saboda su tattauna iƙirarin da tayi a yanar gizo. Ya tabbatar mata yana tareda ita ɗari bisa ɗari. Bata ɗauka Abba zai fassara maganar haka ba. Abba bai taɓa faɗin magana makamancin wannan ba hakan na nuna ba ƙaramin fushi yai da ita ba. Ubayd ma tun safe daya kira ya gama balbaleta da masifa bai sake waiwayanta ba, koda ta kirashi dan ta sanar dashi kiran Umaru Kwom ƙin ɗaukar wayarta yai.



Lokacin da zata shiga ɗakinsu ta ji Hindatu na mata habaici wai 'karyar 'yan siyasa' bata tanka mata ba ta shige ɗaki. Rasa ma mi zatayi tayi dan yadda ran Abba ya ɓaci bata jin zata iya zuwa wajen Umaru Kwom.



Da yamma lis tana kitchen tana haɗawa Umma zoɓonta na siyarwa Ubayd ya shigo da sallama. Kasa amsa sallamar tayi saboda wani tsoro da taji ya taso mata lokaci guda. Umma ba ji take ba bata ma san anyi sallamar ba tana faman tuƙa tuwon Masara.



"Inna Yaha ina Asiya?" Ubayd ya faɗa bayan ya leƙa ɗakin Umma bai ga kowa ba.

Inna Yaha dake ƙullin gyaɗa ta kauda kai gefe tace "kaban ajiyarta ne?"



Bai ma gama jin mi take faɗa ba ya wuce kitchen.

Suna haɗa ido da Asiya ta ji gabanta ya faɗi. Idon Ubayd ya kaɗa yayi ja.



Sama-sama ya gaishe da Umma yace da Asiya ta biyo shi.



"Yaya Ubayd miya faru?"

Bai kulata ba ya fice daga kitchen ɗin cikin sauri.



"A dai bi a hankali har yanzu ba a shafa Fatihan ba" Inna Yaha ta faɗa tana tauna gyaɗa.



Da Asiya da Ubayd ɗin duk babu wanda ya kulata suka shige falon Abba.



"I'm disappointed in you Asiya. Ban ma san mizan faɗa ba. Tunda attension kike nema kin samu yanzu. Congratulations! Gwamna zai zo wajenki yau da dare"



"Gwamna kuma?"



"Abinda kike nema kenan ina, kin samu sai mi ya rage kuma"



Zuciyarta ne ya tafaso. Taya zai zargeta da neman suna.



"Kar ka gaya min magana, idan baza ka tayani neman hakkina ba baka da ikon zargina"



"Asiya kar ki kawo mana rikicin siyasa gidan nan. We are happy the way we are"



"Ni ban san mi kake nufi ba. Ni ba harka nake son yi da 'yan siyasa ba i just wanted to..."



"A gaban Gwani aka mari Abba" maganarsa ya katseta.



"Mari?"



"Yes Asiya. Abba bai gaya miki yadda komai ya faru bane saboda baya so ya ɗaga miki hankali, amma ke ba abinda kika sani sai kanki. Ranan da suka zo karɓan Laptop ɗinki Gwani na wajen shi ya faɗa min komai. Asiya yaron da bai kai sa'an Habibu ba ya ɗaga hannu ya mari Abba saboda ke..."



"Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun"



"Ko kin san Lamara Damana yayiwa Abba kashedi da kashe ni da ke da su Habibu? Ko kin san saboda hakane ya je ya samu MD ɗinku akan ya sallameki?. Ofcourse ke ba ruwanki tunda kinada irinsu Umaru Kwom da zasu goya miki baya idan wani abu ya same ki.



"Asiya end this thing once and for all Dan Allah. In har da gaske kina sona ki ajiye maganar nan, idan ta kama ma ki rubuta cewa abinda kika faɗa ƙarya kikeyi indai hakan zai kawo maslaha to kiyi. I'm having bad feeling about this Asiya"



Bai jira amsarta ba ya fice daga falon ya barta tsaye tana hawaye.



Da Abba ya dawo daga sallar Isha ya kirata ya sanar mata Gwamna zai zo wajenta anjima. Bata nuna masa cewa Ubayd ya gaya mata ba saima haƙuri data shiga bashi kan abinda ta jawo masa...



***



Daga office bai wuce gidan Gwamnati ba asalin gidansa ya wuce ya chanja kaya daga office suit zuwa riga da wando da face cap duka baƙaƙe ya haɗa da baƙin glass saboda yaiwa fiskarsa kariya dan kar a ganeshi. Daga nan ya ɗauki tsohon drebansa yace ya kaishi layin 'yan dabino. Sakatare ya riga ya kira dreban ya masa bayanin gidansu Asiya dan haka bai tsaya ko'ina ba sai ƙofar gidan.



Lokacin da aka tsaya yayi kusan minti biyu kafin Gwamna ya kira numbar Abba ya sanar dashi gashi a ƙofar gida. Ko minti ɗaya bai cika ba Abba ya buɗe ƙofar falonsa dake fiskantar ƙofar gida ya fito jiki na rawa. An riga an kashe wutan ƙofar gidan shiyasa da akwai ɗan duhu. Yana ƙarasowa Gwamna ya buɗe ƙofa ya fito kafin kace me sun shige falon Abba.

Sai da Gwamna ya zauna kafin Abba ya zauna yana risinawa duk da zai bawa Gwamnan shekaru kusan goma shatakwas amma girma girma ne.



A tsanake suka gaisa kafin Abba yace masa bari ya kira Asiya.



Asiya na ɗakin Umma ta takure waje guda Abba ya shigo da sallama.



"Yana jiranki"



"Abba" ta faɗa a hankali kamar mai ciwon baki

Abba ya samu gefen gado ya zauna ko kallon Asiya bai yi ba har ta fice daga ɗakin sanye da dogon hijabin sallarta.



Ƙanshin turarensa ya game falon dan tana buɗe ƙofa ƙanshinsa ne ya mata marhaban. Kallon tsana ta bishi da shi har ta zo ta zauna daura da shi. Har lokacin data zauna bai ɗago ya kalleta ba, idonsa na kan wayarsa. Ganin bashida niyyar magana yasa Asiya tace " akwai abinda nake yi kafin na fito, zan koma"

Har ta fidda ran zai amsa tana shirin miƙewa ta bar masa falon taji yace "miyasa kike zargina? Mi kika sani?"'



Da ita mai ashariya ce da ta ɗura masa ƙazamar ashar a wajen.

"Ji wani tambayar rainin hankali a nan. Your excellency na san komai, na san abinda ka aikata amma kuma zan yi shiru ne kawai saboda Abbana. Sannan ka sani akwai Allah "



Lokacin daya ɗago ido bataga ƙwayar idonsaba saboda face cap ɗinsa ya tare.

Sai dai duk da haka sai da taji bugun ƙirjinta ya chanja.



" na yaba da jajircewarki sai dai zargi babu shaida matsalace Asya. Umaru Kwom zai yi amfani dake ne ya yar, you are too young for that



"Idan kinada shaida akan abinda kike iƙirari kuma, kina iya gabatar min yanzu"



Wani abune yazo ya tokare mata maƙoƙaro dai-dai lokacin da take ƙoƙarin kurma ihu. Ita Gwamna zai rainawa hankali bayan shi ya aiko akazo aka ɗauke recorder da laptop ɗinta.

Bata san ya akayi ta samu ƙwarin gwiwa ba, ƙila tsanarsa da tayi ne ya bata wannan ƙwarin gwiwa, ƙila kuma saboda marin da Ubayd yace anyiwa Abba ne.



Jug ɗin ruwa da aka ajiye a tsakiyar centre table ta ɗauka ta buɗe ta watsawa Gwamna a fiska.

"Wannan shine shaidar ka, Azzalumi"



Tana tsaye riƙe da jug ƙirjinta na bugawa da ƙarfi kamar zai ɓallo, ta kasa ko motsawa a wajen.

Ya kai sakan arba'in kafin Gwamna ya iya cire hular kansa ya buɗe manyan idanunsa. Loƙacin da ƙwayar idonsa ya shiga cikin na Asiya tsabar tsoro saida fitsari ya tsirto wa Asiya.

Yai shirin buɗe baki yai magana amma ya fasa kawai sai ya miƙe tsaye, bai gama miƙewa ba Asiya ta fece da gudu ta bar falon...


*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....







*©Azizat Hamza*



wattpad Azi_zat





Bismillahir Rahmanir Rahim









Book one







08





"Jiya na yi bacci da wuri ban san yaushe ka shigo ba"





Gwamna bai kulata ba ya cigaba da kurɓan shayin dake hannunsa a hankali

"gobe zan wuce China, idan na gama siyayya a chan zan wuce Dubai"



"Na ɗauka wata uku uku kike zuwa sari" ya faɗa yana kallonta





"Manager yace ana buƙatan sabbin kaya, ka san latest goodies nake shigowa da shi"



"Ok"



Bai sake cewa komai ba ya cigaba da cin abinci a hankali.


Jiya bai shiga gidan da wuri ba sai kusan ƙarfe biyu saura na dare. Baccin awa biyu yai ya sake miƙewa dolene ya je office da wuri saboda wani exco meeting da zasu yi ƙarfe takwas na safe. Har yanzu bai bar mamakin abinda Asiya ta masa ba. Gaskiya yarinyar tanada ƙarfin hali.



Jiyan Asiya na fecewa yai murmushi dan abin dariya ya bashi. Yana fita cikin sauri ya je ya shige mota Dreba ya wuce da shi gidansa. A nan ya chanja kaya ya ɗan huta kafin ya shiga rubuta waƙa, kafin ya ankara ƙarfe ɗaya tayi dan haka ya tattara komai ya koma gidan Gwamnati. Sai daya leƙa ɗakunan yaran kafin ya je ya kwanta. Ya lura da cewa Nana da Zunairah sun rugume juna cikin bargo amma bai ɗauke shi komai ba. Mahirah kuma da alama karatu take bacci ya ɗauketa dan ga littafin nan gefen gado yana shirin faɗowa. Ya ɗauki littafin mai suna Americanah ya ajiye a gefen side drawer yai murmushi domin Mahirah ce ta ɗauko son karatunsa, bayan ya kashe wuta sannan ya wuce ɗakinsa inda Bilkisu ke kwance ta jima da barin nahiyar Africa...






Ta sani abinda tayi bai dace ba, shiyasa lokacin data fito banɗaki ta shige da gudu. Bata fito ba kuwa sai da Inna Yaha ta fara ƙwanƙwasa ƙofar. Lokacin data isa ɗakin Umma, Abba baya nan dan haka ta fara ƙoƙarin chanja kaya ƙirjinta na wani irin dokawa kamar wanda tayi tsere.



Washegari kasa zuwa gaida Abba tayi tana zaune a ɗaki ta kasa leƙa ko ƙofar ɗaki tunda tayi Alwalar Asuba.

Ɗumamen da ke gabanta ma turashi gefe tayi dan ba iya ci zatayi ba.

Shigowar Abba ɗakin da sallama yasa ta miƙewa a firgice, tun jiya take jimamin shirun Abba.

Shiga ta musamman yai, yasa babbar riga kamar mai zuwa ɗaurin aure.



"Ina kwana Abba" ta faɗi tana rusunawa



"Lafiya Asiya Shahidah"




"Abba kayi haƙuri, wallahi ban san ya akayi na watsa masa ruwan ba"



"Ba tarbiyyan gidan nan bane. Ba kuma tarbiyyan Gwani bane Allah ya jiƙan rai. Girmama na gaba koda ba Shugaba bane tarbiyyan musulunci kenan, tarbiyyan da nake da yaƙinin mun miki kenan Asiya. To amma..."




"Abba ka yafe min"



Shi kansa Abba tun jiya ya kasa yarda Asiya ce tayi haka sai yanzu da ta jaddada masa. Jiya ya ji gudun Asiya zuwa banɗaki bai kai minti ɗaya ba kuma ya ji ƙaran tashin mota hakan ya sashi zuwa falon nasa da sauri.



Jug ya fara gani a ƙasa, wajen da Gwamna ya zauna kuma akwai alaman ruwa a wajen. Ya duba ƙasan wajen nan ma akwai ruwa a malale. Wajen baiyi kamada kwaɓewar ruwa bisa tsautsayi ba yafi kama da cewa watsashi akayi.


Kasa gaskata cewa Asiya ce ta aikata hakan yayi. Ya so kiran Gwamna amma rasa abinda zai faɗa masa ya sa ya fasa kiran. Ya kwana da tunanin mi zai yi, daga baya ya yanke shawaran zuwa wajen Gwamna ya bashi haƙuri. Lokacin daya tura saƙo wa Gwamna da bai ga reply ba tsoro ya shige shi. Bayan kamar minti arba'in Gwamna ya masa reply akan ya zo ƙarfe goma da minti shabiyar.



"Zan je na bawa Gwamna haƙuri dan gidana ba gidan da ake walaƙanta baƙo bane balle baƙo kuma shugaba. Kamar yadda na faɗa kiyi duk abinda kika ga dama"



Yana juyawa yai kiciɓis da Umma. Allah Sarki ta jima a wajen amma dake bata ji bata san mi suke tattaunawa ba. Ta shiga tambayar Abba miya ke faruwa amma yace mata kar ta damu idan ya dawo zai mata bayani.


Bayan fitar sa Umma ta tsare Asiya da tambayoyi. Daga ƙarshe dai sai da Asiyar ta faɗa mata abinda tayi. Umma ta kama baki tana zaro ido...



Abba na fita waje Ubayd na ƙoƙarin tsaida motarsa. Bai gaya masa abinda Asiya tayiwa Gwamna ba ya dai ce ya zo ya raka shi wajen Gwamna.

Haka suka wuce gidan Gwamnati kowa da abinda ke ransa.




Daga waje Ubayd ya nuna ID card ɗinsa amma duk da haka sai da masu gadi suka kira suka tabbatar da ana tsammanin zuwan su kafin aka barsu suka shiga ciki.

Wani security ya musu jagora har ofishin Sakataren Gwamna bayan ya sanar da Gwamna zuwansu sannan yace su shiga ciki.



Kwarjini Gwamna ya ƙara yiwa Abba. Kunyarsa ta gama cika shi lokacin da Gwamna da kansa ya miƙa masa hannu sukayi musabaha sannan ya jagorance su zuwa wajen kujeru inda yake zama ya tattauna da baƙinsa.




"Ranka shi daɗe, ba zan iya bayyana maka yadda raina ya ɓaci jiya ba. Ina roƙon ka dan Allah kayi haƙuri ka yafe mata. Asiya..."



"Ba komai Malam Nuhu, ya wuce a wajena. Infact na yaba da ƙarfin gwiwarta. Sai dai ina tausayin mijin da zata aura kar watarana yai laifi ya

Please Login or Register in order to submit comment