Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kodai Barasar daya kwankwaɗa jiya da dare ne? Duk da likitan sa na chan Germany ya hana shi shan barasa. Duk da kuwa ya san ba zai iya dena sha ba, sai dai ya rage sha ba kamar da ba.



Allura da Likitan ya ma sa ya taimaka ma sa sosai dan har ya samu yayi bacci. Lokacin da ya farka kusan ƙarfe goma shaɗaya na safe.

Sha'awanatu ta taimaka ma sa yai wanka ta kawo ma sa abinci har kan gado amma bai iya ci ba sai shayi kawai ya sha.



Ƙishirwar giya ce ta dameshi dan duk da yana jin jiki yayi amanna idan ya ɗan kurɓi kaɗan zai samu sauƙi. Fita yai daga ɗakin Sha'awanatu ya wuce na sa ɗakin a nan ya fito da kwalbar giya ya kwankwaɗa ya girgiza kai ya sake kurɓan kaɗan sannan ya mayar da sauran ma'ajiyar sa.

Shiryawa yai ya fita saboda akwai meeting da zai yi da wasu contractors ƙarfe biyu na rana.





"Yanzu yadda baka da lafiya haka za ka fita?"



"To ya za ayi dole ne mu yiwa talakawa aiki"





"To. Amma ka dai yi tunani akan abinda na ce"



Dariya Gwamna ya fara yi sai kuma ya dafe ƙirjinsa saboda yadda ya ji ƙirjinsa na suya kaman an saka masa wuta.



"Your excellency jikin ne?"



Kafin ta ƙarisa maganar Excellency ya kai ƙasa.



"Your excellency, miya faru? Ƙirjin ka ne?"

"Waye a nan? a kira likita. Excellency... Saminu...Saminu ka tashi"



Lokacin da aka garzaya da Gwamna Asibiti ya riga ya cika likita ya ce zuciyar sa ce ta buga (cardiac arrest)...





***





Mataimakin Gwamna na zaune a office Chief security officer ya kira shi, kiran da ya ɗaga ma sa hankali sosai dan kuwa a kiɗime ya fice daga office ɗinsa ya wuce Asibiti.



Mummunan labarin da aka gaya ma sa a waya shi ya tarar a wajen domin kuwa Allah yayiwa Gwamna Saminu Bacchi rasuwa.





A chan Kachallah House kuwa Alhaji Sani Kachallah ne ke waya da mijin 'yar sa wato Saifuddeen wanda ya jaddada ma sa mutuwar Saminu Bacchi.



"Mi aka ce ya kashe shi?"



"Baba ba zan iya cewa komai ba yanzu"



Alhaji Sani Kachallah ya ce "ba komai zan kiraka anjima". Yana kashe wayar ya shiga kiran numbar Yallaɓai.



A chan gidan mataimakin Gwamna kuwa Bilkisu Kachallah ce zaune a falo tana cin gasashshiyar kifi da soyayyen dankalin turawa haɗe da lemo mai sanyi.



"Hansa'u, Hansa'u " Hansa'u ta fito da gudu.



Miƙo min remote ina son kallon news.



Hansa'u ta miƙa ma ta remote ɗin Bilkisu ta chanja channel daga Zee world zuwa Congo news...





***





Asiya Shahidah na zaune a sabon office ɗinta tana aiki akan computer abokin aikinta Ɗahiru ya shigo office ɗin da sauri.



"Shahidah kin san labarin dana ji kuwa daga fitata a office ɗin nan?"



"Miya faru?"



"Yanzu Abigail ta ke kawo rahoto cewa Gwamna ya rasu"



"Wani Gwamnan?"



"Gwamnan Congo mana"



"Innalillahi! Dan Allah?"



"Allah kuwa"



Asiya Shahidah ta miƙe ta bar office ɗin da sauri...







Kusan awa ɗaya da rasuwan sannan Mataimakin Gwamna kuma acting Gwamna ya bada sanarwan mutuwar Gwamna Saminu Bacchi.





*"Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun. Haƙiƙa dukkan mai rai mamaci ne. Muna yiwa Jahar Congo ta'aziya bisa rasuwan Mai girma Gwamna Alhaji Saminu Bacchi wanda Allah yai wa rasuwa yau shabakwai ga watan Nowamba. Haƙiƙa wannan jaha ta yi babban Rashi"* hawayen da ya zubo ma sa yai saurin sa hankerchief ya goge sannan ya cigaba da bayani

*" Insha Allahu za ayi jana'izar sa a gidan gwamnati da ƙarfe biyar na yamma"*





Asiya Shahidah da ke kallon news ɗin a talabijin da ke office ɗin su CY ta ce "Ikon Allah har da kukan munafurci kaman bai ji daɗin abinda ya faru ba, Shege. Ai yanzu kam jahar nan ta shiga uku a hannun wannan Wawan"



A ɓangaren Yallaɓai kuwa yana gama kallon bayanan da SSK yai ya danna remote ya kashe T V sannan ya kai duban sa ga Kachallah ya ce



"To kyan alƙawari dai cikawa. Ina fata Saifuddeen zai bamu haɗin kai"



"An gama Yallaɓai"





Yayinda wasu ke cikin baƙin ciki da rasuwan Saminu Bacchi wasu kuma na nan suna planning yadda za a juya Gwamnati.

Duniyar kenan. Tunma kafin a sa shi cikin ƙasa har an riga an cire shi daga lissafi.



Da 'yan siyasa za su dinga tunawa da cewa akwai ranar da dukiya ko matsayi ba zai amfanesu ba ƙila da za su tausayawa talakawan su.


*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....







*©Azizat Hamza*



wattpad Azi_zat





Bismillahir Rahmanir Rahim









Book one











04









"Rayuwa kenan. Yau kam Saminu Bacchi sai kwanciyar kabari"

Abba da ya kashe rediyon sa ya faɗa.



Ubayd ya ƙara da cewa "Ya tafi ba abunda ya ɗauka kuwa"





"Muna addu'ar Allah ya taya Saifuddeen riƙo Amin"



Ubayd ya ce Amin. Shiru ne ya biyo bayan haka na ɗan mintuna kafin Abba ya ɗaga kai ya ce " 'yata ta dawo kuwa?"





"Ƙila aiki ne ya tsaida ita"



"Ka je ka dubo min ita"



Bai musa ba ya miƙe yana karkaɗa key ɗin mota.





Lokacin da motar sa ta sako kai farfajiyar ma'aikatar su Asiya ya hangota tana shirin hawa babur ɗin CY. Yana ɗaya daga cikin abinda yasa ya ke ƙin aikinta irin yadda ba ta damuwa da irin mutanen da ta ke mu'amala da su. Ya sha hanata mu'amala da wannan camera man ɗin amma kaman ma duk cikin Kamfanin su tafi jituwa da shi.



Sarai ta hango shi amma ta kauda kai kamar ba ta ganshi ba. Sai da CY ya tada machine su ka fara tafiya ya kula da motar Ubayd.



"Aseey ba motar fiancee ɗin ki ba ne wannan"



"To sai me"



CY yai saurin taka birki har sai da Asiya ta bugu da bayanshi.





"Ya ka tsaya?"



"Bebz i no wan trouble, plz ki sauka"





"CY ka wuce mu tafi"



Lokacin da ya tada machine ɗin a hankali ya ja su har wajen da Ubayd yai parking motar sa Asiya na ta ma sa faɗa akan ya wuce su tafi amma bai saurareta ba.



"CY za ka haɗu da ni gobe ai. I will deal with you"



Bai kulata ba sai ɗagawa Ubayd hannu da yai yana faɗin "weldone Sir"



Ubayd ya sauke glass ƙasa ya ce "Sannu da ƙoƙari fa"



"Sannu Sir, a yiwa Amarya haƙuri yau ta gaji dayawa ne"





"Nagode"



Asiya ta watsawa CY harara kafin ta zaga ta je ta shiga motar Ubayd.





Sai da ya ga ta shige motar kafin ya ja machine ɗin sa yai gaba.



Ubayd bai ce mata komai ba ya tada motar su ka fara tafiya. Itama ba ta kula shi ba sai ma kwantar da kujera da ta yi ta rufe idonta kamar mai bacci.



Traffic ne ya riƙesu saboda ma su dawowa daga maƙabarta.



Ƙaran siren ne ya tada Asiya daga baccin daya sace ta. Ta rintse ido ta buɗe da kyau ganin har yanzu suna round about na GRA kenan ko kusa da gida ba su yi ba.

Sai da motocin Gwamna su ka wuce kafin aka basu hanya suma suka fara wucewa hakan ya sa Asiya ta ja tsaki.



"Asiya" ya dakatar da ita lokacin da ta ke shirin fita daga mota.





Ta juyo ta kalleshi ba tareda ta ce komai ba.





"Zan kiraki bayan sallar Isha"



"Ok" ta faɗa sannan ta fita.



Data shiga gida tana jin shewar Abida ƙawar Hindatu mai murya kaman na maza. Ta dawo kenan ta faɗa a ranta sannan ta wuce ɗakin Umma.



Bayan ta yi sallar isha tana kwance akan sallaya tana danna waya kiran Ubayd ya shigo. Ta san dalilin kiran shiyasa ba ta ma ɗauka ba ta miƙe ta fice daga ɗakin.



"Yau kuma shigar ta malamai ne"

Ubayd ya faɗa lokacin da ta ke ƙoƙarin zama akan kujerar roba da ke gefen sa.



"Idan ma gatse ne ka san dai daga gidan Malaman na fito"



"Shiyasa na ke alfahari da cewa jikar Gwani Baba zan aura. Allah ya jiƙan rai"





"Ka huce kenan?"



"My Aseeya kenan. Kin riga kin sani bana iya fushi da ke ai. Ki yi haƙuri"



Asiya ta ɗan haɗe rai tana tura baki.



"Kwantar da hankalinki ba haka nan na zo biko ba, na zo da kayan sulhu"



Yana maganar ya jawo ledar da ke gefensa ya ɗaura akan cinyarta.



"Whoa! Pringles, chocolates. Ba dan halin ka ba dai kaima ka yi haƙuri" tana maganar tana buɗe robar pringles ɗin.



"Ya Ubayd gaskiya yau ka yi abin kirki" tana maganar bakinta yana ƙurmus-ƙurmus.



"Ba za a sammini ba?"



"In your dreams. Ka san yanzu a zaune sai na cinye wannan bai isheni ba"



Ganin ya sakata farin ciki ya sa shi yi mata hiran shirye-shiryen bikin su da tsarin yadda komai zai kasance. Yau baya so ayi maganar kowa sai ta su. Ana taɗi ya tuno mata da ranan da ya fara ganinta a gidan su hakan ya sa Asiya mingirewa da dariya tanayi tana "kai Ya Ubayd"

Farkon haɗuwar su tana shekara shaɗaya a duniya ta zo yiwa ummanta hutu. Lokacin 'yar mitsila da ita amma wai tana JSS 2.



Ya shigo gidan ya ga tsumma a kan igiyar shanya, bai kawo komai a ransa ba ya cire ya tsoma cikin ruwan Omo ya fara wanke machine ɗin Abba da shi.

Kamar daga sama ya ji wata siririwar murya tana salati a bayansa ya juyo a ɗan firgice dan ya ɗauka ba kowa a gidan na su, biki ake a gidan su Addaye ƙanwar Abba, duk 'yan gidan suna chan.



"Lahaula... Sallalahu Alaihi wa Sallam. Tsumman abuna!" sai kuma ta riƙe baki tana zaro ido.



Ubaydullah yana riƙe da tsumman ya kalleta da mamaki ya ce "tsumman miye? Tukunna ke daga ina?" Bai yi aune ba Siririyar yarinya mai wushirya ta yi wuf ta karɓe tsumman daga hannunsa ta shige ɗakin Umma da gudu, bai ƙare mamaki ba sai daya ji ta bugo ƙofar ɗakin da ƙarfi.



Shi kam bai gane mi ya ke faruwa ba. Ya dai ƙarasa wanke machine ɗin hakanan.



Har ya gama abunda zai yi ya fita yarinyar ba ta fito ba. Sai bayan magariba daya dawo gidan ya tambayi ƙanwar sa Ummi wace baƙuwa su ka yi a gidan. Ummi ta sanar da shi 'yar Umma Kurma ce itace Asiya Shahidan ta da Abba ya basu labari.



Tun daga lokacin kuwa Asiya ke gudunsa har ranan da ya titsiye ta yana tambayarta miye dalilin ta na ƙwace tsumman ranan. Yadda ta dinga inda-inda ne ya sa ya fahimci tsumman miye.

Ƙannensa sun wuce nan ai dan tun lokacin da ya taɓa kama ƙanwarsa Ummi tana ɓoye tsumma cikin zani ya ɗaurawa kansa siyawa ƙannensa audugar mata tun ma yana shekaru shabakwai kenan balle yanzu daya ke shatara shigar sa Jami'a ya sake wayewa.



A ranan ya je ya siyowa Asiya auduga ya bawa Ummi ya ce ta nunawa Asiya yadda za ta yi amfani da shi.

A hankali-A hankali kafin ta ƙare hutun ta dena jin kunyar sa tana ɗan sakewa da shi. Tun tana zuwa hutu gidan har ya zamo lokacin da za ta shiga Jami'a ta dawo gidan su da zama gaba ɗaya.

Har yau idan yana son ya tsokali Asiya to kalmomi biyu kacal zai faɗa ya tunzurata *"tsumman abuna"*



Bai bar gidan ba sai ƙarfe goma saura minti biyar nan ma dan baya son tsallake dokar Abba ne wato baya son hiran ƙarfe goma.



Asiya na komawa ɗaki da ta duba wayarta ta ga saƙon KaSaSa a email ɗinta wanda waƙar da ta rubuta yau akan mutuwa ne, wanda tai wa Marigayi Gwamna Saminu Bacchi.

Bayan ta karanta kuwa sai da ta tuno mutuwa biyu da su ka fi girgizata a rayuwarta. Mutuwar Kakanta Gwani da kuma mutuwar ƙaninta ɗan shekaru biyu wanda ya rasu a bayanta.

Auri sakin mahaifinsu ne ya je ya auro wata mai juju. Dan idan abu ya haɗata da sauran matansa duka ta ke musu, shima kuwa da ƙyar ya sha a wajenta ranan da ya mareta ta kamashi da kokawa sai da ƙyar aka raba su. Ba dan an raba da wuri bama alamu sun nuna Ale Faruƙ ne zai sha kashi a wajen Indo, dan Indo irin matan nan ne ma su ƙarfi, ga jiki ga tsawo. Ale Faruƙ na sane da dukan miji da akace tanayi wanda ya rabata da sauran mazaje uku da ta aura a baya amma ya rufe ido ya ce Indo-ƙarfi zai aura.



Bayan faɗan ne kuwa Ale Faruƙ ya saketa ashe tanada ciki. Da ke ba ta da hankali yaron ko suna ba ayi ba ta zo ta ajiye shi gaban Tabawa mahaifiyar Ale Faruƙ wai ga tsiyar su nan.

Haka yaro ya taso ba gata. Tabawa ma da ƙyar ta ke kula da shi dan Ale Faruƙ baya kawo kuɗin madara sai ta tsiya-tsiya.

Da yaron ya fara wayo ba shi da wata gata a gidan sai ta Asiya. A haka ya taso a yarjale har Allah ya ɗau ransa lokacin yayi wani zazzaɓi mai zafi Asiya ta goya shi tana jijjigashi a bayanta saboda kuka dayake ta tsalawa har Allah ya karɓi ran sa. Shekarunta tara a lokacin amma har yau ba ta taɓa manta yadda abun ya faru ba. Ya jima da rasuwa a bayanta ba ta sani ba har sai da ta zo kwantar da shi lokacin za ta yi wanki dan ta ɗauka bacci yai sai ta ga idonsa a kafe ta fara jijjigashi amma inaa babu alamun motsi nan ta saka ihu ta fita tana ƙwalawa Tabawa kira...



***







"Seriously Justice ina tsoro. Kwana biyun nan bana iya bacci fa. This is so sudden for me"

Bayan Justice Yunus ya gama yi ma sa nasiha ta jan hankali ne ya ce "Shikenan na gode. Ka gaida Maman 'yan biyu"...



"Kai da waye a waya?"



Ta faɗa lokacin da ta ƙaraso wajensa tana zuba ƙanshi.



"Justice"



"Oh Galadima. Hope zai zo rantsarwar ka"



" i dont think so dan ya ce suna Las Vegas"





"Ayya! Allah ya dawo da su lafiya. Muma gashi babu halin tafiya tunda ga yadda lamarin Ubangiji ya kasance. Just like a dream"



"Just like a dream kam. Har yanzu ina jimamin mutuwar Gwamna"



"Haka Allah ya ke lamarinsa. Idan lokaci yayi babu makawa sai an tafi"



"Hakane. Muma duk lokaci mu ke jira"



Kallonta yai da kyau sannan ya ɗaga gira sama ya ce " sai ina?"



"Zamu je shopping ni da yara. Duk cikin kayan su babu na zuwa swearing in naka a ciki. I think dole a chanja mu su wardrobe kwanan nan"



"Hmmm. I trust you Bilkisu" ya faɗa yana ɗan jijjiga kai



"Miye?"



"Allah ya kiyaye hanya"



Kiss ta manna ma sa a baki kafin ta fice daga ɗakin ya bi bayanta da kallo. "Mata kenan, wai duk cikin kayan da ta ke dasu babu na zuwa wajen rantsarwar sa da za ayi ranan Monday".





"Seriously Mommy i cant believe yanzu mune first family of the state" Nana ta faɗa tana dariya



"Well get used to it, dan yanzu aka fara governor's daughter"

Bilkisu ta faɗa tana murmushi.

Nana ta saka ihu.

Har su ka isa Kachallah House hiran yadda rayuwar su za ta kasance yanzu su ke yi.





Sai da su ka fara isa ɓangaren Hajiya Aisha wato mahaifiyar Bilkisu kafin su ka wuce gaida Dadda mahaifiyar Alhaji Sani Kachallah.



Ko da su ka gaisa Bilkisu ta tambayi ina Mahira ta ke, Dadda ta ce ta wuce Islamiyya.



"Yanzu yarinyar nan abinda za ta min kenan bayan na ce ma ta zamu zo"



"Inaga ta manta ne" Dadda ta faɗa tana tauna goro.



Ba su jima a gidan ba su ka wuce bayan sun barwa Dadda saƙo akan idan Mahira ta dawo ta je gida Bilkisun na nemanta.



***







Farar Shadda ya saka ɗinkin babbar riga haɗe da baƙin hula zanna, ya saka baƙin shoe ƙirar Loius Vitton. Ya duba kan sa a madubi ba ƙarya ya fito sosai. Sai dai a ƙarƙashin wannan kayan zuciyar sa ce ke bugawa da ƙarfi kaman za ta ɓula ƙirjinsa ta fito.

Lokacin da aka rantsar da shi a matsayin mataimakin Gwamna bai tsinci kan sa cikin fargaba da tsoro kaman na yau ba kodan yanzu matsayinsa ya chanja ne?



Ya fesa turarukan sa ma su ƙanshi guda uku sannan ya fito daga ɗakinsa ya wuce ɗakin Bilkisu. A tunanin sa ta gama shiryawa amma har lokacin ana kan yi mata kwalliya. Tamkar biki za a yi haka Hajiya Bilkisu ta nemo professional make up artist da za ta gyara ma ta fiska yau.



"Your excellency" mai kwalliyar ta faɗa tana wani ƙamewa.



Bilkisu ta ɗago ido ta ce " Darling ka gama shiryawa, yi haƙuri yanzu zan gama nima"



Tun kafin ta ƙarisa maganar ya riga ya fice inda ya wuce ɗakin yaran sa. An gamawa Nana da Airah kwalliya Mahira ake yiwa lokacin daya shigo. Fiskarta tamau alamun ba ta so a dole ake mata. Ya sani ta ɓangaren son ƙyale-ƙyale kam Nana ce ta ɗauko komai na Bilkisu amma Mahira bai dameta ba.



"Daddy Governor" Nana ta faɗa tana ƙarasowa wajen sa.



"Yi a hankali N Luv kar ki ɓata ma sa farin kaya" Airah ta faɗa daga inda ta ke zaune tana danna waya.



" Daddy selfie ɗaya kafin ka tafi please"



Bai so ba amma dole haka ya tsaya Nana ta mu su selfie kafin ya wuce ɗakin Junior inda tuni Hansa'u ta shirya shi dan lokacin da ya shiga ɗakin ma yana buga game ne. Ya kama hannunsa su ka fice daga ɗakin...







Kotu ya cika maƙil da mutane da kuma 'yan jarida. Bayan Alƙali ya shigo ya tsaya sannan Gwamna Saifuddeen Sa'ad Kachallah ya shigo biye da bodyguard ɗin sa. Bilkisu kaman ta narke saboda farinciki ganin Mijinta a gaban Alkali wai za a rantsar da shi a matsayin Gwamna.



Lokacin da SSK ya dafa alƙur'ani ya maimaita kalmar da Alƙali ya faɗa wato*I...Saifuddeen Sa'ad Kachallah. Do solemly swear...* lumshe ido Bilkisu ta yi sannan ta kai dubanta ga ɓangarenta na dama inda Alhaji Sani Kachallah ke zaune ɗauke da Junior a cinyarsa. Irin yadda fiskarsa ke washe da farin ciki da annashuwa ko ita da ta ke Matar Saifuddeen albarka. Mahaifinta shine musabbabin saka Saifuddeen a harkar siyasa and yanzu ne zai ga alfanun sadaukarwar da yai a rayuwar Saifuddeen domin yanzu shi ɗin Gwamnan Jahar Congo ne....







***











Asiya ba ta yi tsammanin kira daga MD ɗin su ba dan rabonta da shi tun ranan da aka bata suspension letter.

Sai da ta ƙarisa aikin da ta ke yi kafin ta wuce office ɗinsa.



"Sannu da aiki Sir"



"Yawwa Asiya. Ya aikin?"



"Alhamdulillah"



"Inada assignment da za ki yi. Idan kin carrying out na shi da kyau za ki dawo aikin ki na da"



Washe fiska Asiya ta yi ta ce "Sir wani assignment ne?"



Wata takarda ya tura gabanta ya ce "muna so ki yiwa Gwamna Interview"



Murmushin fiskar Asiya ya ɓace ɓat. Wata na biyu kenan da SSK ya zama Gwamna kuma har yanzu ya ƙi yin interview da kowani gidan jarida. Sau ɗaya yai press conference sati ɗaya bayan an rantsar da shi a matsayin Gwamna.



"Sir i think Hill TV ta nemi hira da shi kwanakin baya kuma ya ƙi"



"Shiyasa na ce assignment ne. Ko dai yanzu akwai aikin daya gagari Asiya-Shahidah ne?"



Asiya ta ƙunshe baki tareda sauke ajiyar zuciya.



"Ba komai Sir zan nemi permission daga gidan Gwamnati kafin satin nan ya ƙare Insha Allah"



Ko da ta bar ofishin sa office ɗin su CY ta wuce ta sameshi yana editing wani video da za a ɗaura anjima.



"Babez ya na ga kin haɗe rai?"



"za ka rakani Government office gobe"



"Government office? Why?"



"Kai dai ka shirya kawai".



"Okey dokey"





***





Ƙarfe takwas saura suna bakin Gidan Gwamnati. Ba su samu matsalar shiga ba suna nuna ID card ɗin su aka ce su wuce.

Wani security ne ya mu su rakiya har ofishin Sakataren Gwamna.



Asiya ta yiwa Mr Baffayo Sakataren Gwamna bayanin abinda ke tafe da su. Bayan ta gama ya ce " Malama Asiya na ji daɗin zuwan ku gaskiya sai dai Mai Girma Gwamna ya ce ba zai yi zama da kowani ɗan jarida ba yanzu, sai dai ko gaba"



"Ranka shi daɗe, Hill TV zata yi hira da shi ne gameda tarihin rayuwar sa babu maganar siyasa a ciki"



"Malama Asiya kenan. Zai fi dai ku haƙura zuwa lokacin da Gwamna zai so yin hiran da kan shi"



"Sir da dai ka miƙawa Gwamna letter ɗin mu ƙila a dace" ta faɗa a marairaice



Sakatare ya karɓi wasiƙar ya ce zai miƙawa Gwamna.

Su ka ma sa godiya su ka tafi.



Koda Gwamna ya dawo Sakatare bai ba shi wasiƙar ba, bai ma gaya masa su Asiya sun zo ba.



Asiya na nan tana jiran kiran Sakatare amma shiru. Washegari ƙarfe goma ta sake komawa ofishin Gwamna.



"Kin ga abinda na faɗa miki ɗin ne dai, Gwamna ya ce ba zai karɓi gayyatar ku ba"



"Dan Allah Malam ka sa baki. I really need to take his interview"



"Ki yi haƙuri. Zan dai sake yi ma sa magana ince kin sake zuwa. Kin san matsalar ne. Akwai wanda su ka fi ki naci sunyita zuwa Kwanakin baya, ƙarshe Gwamna ya ce kar a sake bari ɗan jarida ya zo ofishin sa amma..."



"Oh haka ko?" Asiya ta faɗa a hasale



Sakatare ya zuba ido yana kallonta da mamaki.



Asiya ta ciro wasiƙar da su ka ajiye ma sa jiya a ƙasan laptop da ya ke aiki da shi.



"Zan iya rantsewa wannan bai je hannun Gwamna ba"



Sakatare ya fara kame-kame. Allah na gani girman shekarunsa da Asiya ta gani ya sa ta iya controlling kanta ba ta ma sa rashin mutunci ba.



"Zan dawo gobe, zan jira ko ƙarfe nawane sai na ga Gwamna da kaina na bashi wasiƙar. Zan haƙura ne kawai idan shi da bakinsa ya ce ba zai yi hira da ni ba"



Daga haka ta fice daga office ɗin ta bar Sakatare baki buɗe.



Bayan tafiyar Asiya da Sakatare ya shiga wajen Gwamna kai ma sa wasu takardu sai ya haɗa da wasiƙar Asiya.



"Wannan fa?" Gwamna ya tambaya yana ɗaga envelope ɗin da wasiƙar ke ciki.



"Your excellency gidan talibijin na Hill TV ke son hira da kai"



"Malam Baffayo hira da 'yan jarida sai gaba, we have better things to do with our time now"



"Yes excellency"



Daga haka ya fita bai sake ɗago maganar ba.



Washegari kuwa kamar yadda Asiya tayi alƙawari sai gata a ofishin Gwamnati sai dai wannan karan ko ƙarasawa ofishin Sakataren Gwamna ba ta yi ba aka dakatar da ita.



"Ban gane in tafi ba. Ina son ganin Gwamna ko akwai dokar da ta hana hakan?" Asiya ta faɗa wa security guard ɗin daya tsareta cikin tsawa.



"Gwamna baya office ki je ki dawo wani lokaci"



"Ba inda zan je. Gwamna yana nan. I need to have audience with him"



" idan ba ki fita ta lallami ba, za a fita da ke ta ƙarfi. So please leave"



"Ba inda zan je fa" Asiya ta faɗa tana gyara tsayuwarta.





A ofishin Sakatare kuwa Gwamna ne ya zo wucewa zuwa wani exco meeting ya jiyo hayaniyar da ake yi hakan ya sa shi ya ɗan tsaya.



COS da ke bayan sa ya kalli Sakatare cikin tsawa yace "wai wacece a wajen nan ne?"



"Wata 'yar jarida ce ta dage sai ta ga Gwamna".



"Kul ka taɓa ni, wallahi yatsata ka taɓa sai ka san wacece Asiya-Shahida a garin nan. Na san 'yanci na dan haka kar ka kuskura ka min barazana"



Wannan karan tana maganar ta zauna a kan kujera da ke Lobby ɗin tareda ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana huci.



"Malam Baffayo ka ce ta dawo ranan Monday"

Ba da ƙarfi yai maganar ba amma duk sun ji shi. Bai jira mai Sakataren zai ce ba ya wuce abinsa.





Asiya ta zauna na kusan minti shabiyar kafin Sakatare ya fito.



"Malama Asiya ya da haɗe rai haka"



"Ba fa inda zan je" ta faɗa tana girgiza kai



Sakatare ya miƙa ma ta wani envelop. Tana gama karanta takardar da ke cikin envelope ɗin ta saka ihu. Sai kuma ta yi saurin rufe bakinta da hannunta.



Sakatare yai dariya ya ce " gaskiya kin taki sa'a. Gwamna ya amince ya ganki ranan Monday, best of luck"



Fiska a washe Asiya ta ma sa godiya ta tafi. Shi kan sa Sakatare yayi mamaki da amincewar Gwamna cikin sauƙi haka.





***



A chan ɗakin da ake taro kuwa dukkan wanda ya ke da alaƙa da wannan taro ya riga ya hallara dama Gwamnan kawai ake jira.



COS ne ya ja masa kujera ya zauna yana kallon mutanen da ke wajen ɗaya bayan ɗaya. Kusan minti guda ya ɗauka sannan ya ja dogon numfashi sannan ya ce "gentlemen ina buƙatar report na wannan wata"





"Kwamishina Isiaka" Gwamna ya kira yana duban wani ƙaton baƙin mutum sanye da babbar riga kalar light blue. Kwamishinan ilimi yai gyaran murya sannan ya fara bada bayani wanda ya ɗaukeshi tsawon minti huɗu da rabi.



"Not impressive Kwamishina Isiaka. Ban

Please Login or Register in order to submit comment