Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaƙinin haka Yallaɓai. Shi mutum ne mai biyayya"





Wani mai baƙin suit ya tari bakin Kachallah da cewa "inada shakka akan wannan"





"Mr Paul mi kake so ka ce, ba dai kana nufin za a rusa tsarin wannan gwamnatin ba..."



"Mr Paul, Alhaji Kachallah wannan ba abun ɗaga hankali ba ne. Har yanzu akwai sauran lokaci dan haka zamu cigaba da saka mishi ido kafin lokacin ya cika. Ko mi ka ce Yallaɓai?"







Yallaɓai ya kalli Mutumin da yai magana sannan ya maida dubansa ga Alhaji Kachallah da Mr Paul. A hankali ya fara shafa gemun sa yana yi yana murmushi. Murmushin Yallaɓai na da ma'anoni daban-daban amma a wannan lokaci dukkan su sun yarda cewa yana nufin su kwantar da hankalin su ne, wato akwai nasara a dukkan tsare-tsaren su.









***





LADIES HALAAL SALON & SPA waje ne da ya amsa sunan sa, domin kuwa dukkan abubuwan da ake gudanarwa a wajen suna ƙoƙarin tafiya da tsarin da bai kaucewa tsarin musulunci ba. Waje ne da Asiya-Shahida, Queen Bee da Alhaja Oyiza su ka buɗe saboda samawa mata wajen kula da jikin su. Ma'aikatan wajen dukkan su mata ne. Cikin ayyukan da su ke gudanarwa a wajen akwai wanke gashi, drying da kuma stretching, suna gyaran farce (menicure and pedicure). Ana kitso da kuma ƙunshi sannan watanni biyar da su ka wuce da su ka dawo sabon shagon su da ke anguwar GRA suka fara gyaran jiki da spa treatment a wajen (wanda ya haɗa da body, hair and foot massage, facial treatment da sauran su)





Shigowar Shahidah sashen da ake yin gyaran gashi da kitso ya sa wajen yai wani irin tsit. Precious da ke yiwa wata mata kitson wig ta tsaya da kitson tana kallon Shahida jikinta na ɓari.



Matar ta ɗan ɗago ta ce "ya ki ka tsaya?"





Tunda ba sa saida gashin wig kenan matar ce ta zo da abinta. Shahida ta faɗa a ranta.

Precious ba ta san ma Shahida na cikin shagon na su ba da ba za ta yi gigin fara yiwa matar nan kitson wig ba. Ta san dokar shagon su amma wannan matar Comissioner ce, duk da ta hannun Queen Bee ta zo ta tabbata za ta raɓi maiƙo a jikin matar, shiyasa da matar ta nuna kitson wig za a mata ba ta iya yi mata musu ba.



Shahida ta ƙaraso gaban matar sannan ta kalli Precious ta ce " ina bawa mutane dama ɗaya tak a rayuwa, na ƙarshe kenan da za ki sake taka mana dokan wannan shago. Ki maida mata kuɗinta ta bar mana waje"





"Malama ban gane mi ki ke cewa ba. Da alama ba ki san ko ni wacece ba ce"



"Duk wanda ya shigo wannan waje domin a masa wani abu a nan to sunan sa customer. A dalilin an ɓata miki lokaci za a maida miki kuɗin ki dan haka ki wuce wajen da su ke yin irin wannan kitso a ƙarasa miki a chan"



"What nonsense" matar ta faɗa a fusace tana miƙewa tsaye.





"Idan kin fita ki ɗan ɗaga idon ki sama za ki ga sunan wannan waje. Saka gashin wig baya cikin services na mu"



Daga haka Asiya-Shahida ta bar wajen. Tana jin matar tana ta zage-zage amma ko ajikinta. Ta yiwa matar farin sani. Habiba sunanta a ƙasan layinsu ta taso. ta tsula bariki sosai kafin ta auri kwamishinan ilimi shekaru uku da suka wuce.





Dole ta yi magana da Queen Bee ta jawa Precious kunne tunda ita ta bata aiki. Idan irin haka ya cigaba da faruwa Salon ɗin su zai zama babu wani banbanci tsakaninsa da sauran gama gari...






**






Shahidah na zaune tana zanawa Amarya Layla lalle a hannu ta ji matan da ke wajen sun saka ihu.



Basma ta ce "Jennifer ƙara mana volume mu ji mi ya ke cewa"

Kafin ta gama maganar ma ta riga ta ƙara volume ɗin.


Muryan daya doki kunnen Asiya ne ya sa ta jan dogon tsaki ba shiri.



"Yanzu dan Allah saboda wannan wawan ku ke ta ihu"



Banza su ka yi da ita suka cigaba da yaba mutumin da ke magana a cikin TV.



"Ki ga idon sa dan Allah, ko idon kaɗai Allah ya bashi wallahi an zuba ma sa baiwa" wata daga cikin ƙawayen Amarya da ake wa Lalle ta faɗa.



"Allah ya shiryeku gaskiya. Mutum tsohai-tsohai da shi ku dinga wani drooling akan sa kaman wasu ƙwailaye"



"Ke dai 'yar baƙin ciki ce Asiya. Allah ya isan ma SSK ɗin mu za ki kirashi tsoho"

Kafin ta yi magana kuwa Asabe ta ce "ni kin san Allah yanzu haka idan da za ace na zaɓi tsakanin SSK da kuma Ubayd ɗinki Asiya Wallahi Tallahi SSK zan zaɓa"



Asiya ta fusata ta kaiwa Asabe duka Asabe ta kauce tana yi ma ta dariya. Ranan har Asiya ta gama yiwa Amarya Lalle ba ta dena diri ba. Hayaƙi ne kawai bai fito daga bakin Asiya ba saboda yadda ta dinga faɗa akan an haɗa masoyinta Ubayd da SSK...







**







"Gashi nan ai ya ƙi biyan albashi ya bar mutane da yunwa. Idan ka yi magana kuma a fara ganin baƙin ka mtsww"



"Mine kina da abun dariya Allah. Tunda mu ka zauna a nan ba hiran da mu ka yi sai ta SSK. Ki rage ƙiyayyar ki gareshi please. Abun ya fara yawa"



"Amma Ya Ubayd..."



"Yanzu dai a ajiye maganar sa a gefe tukunna. Albishirin ki"



Asiya ta haɗe rai ta juyar da fiska gefe.



"My Aseeya haka zan tafi gida ba tareda kin min murmushinkin nan mai sanyaya min zuciya ba"



"Ka je SSK ya maka murmushin tunda ka damu da shi"



"Mi zan yi da murmushin ƙato bayan inada kyakykyawar budurwa a kusa da ni"



"Dama ina so na miki maganar gida ne amma tunda kinyi fushi shikenan"



"Dan Allah an gama gyara kitchen ɗin?" Ta faɗa cike da excitement.



"Wagga Bafulatana ba ta da kunya samsam"



"Eh ɗin" ta faɗa tana murguɗa ma sa baki.



"Kinga ɗan bakin nan da Allah zai kaimu wata biyar da kwana shauku da na jima da maganin sa"



Asiya ta yi saurin sunkuyar da kai tana rufe bakinta da tafin hannu tana murmushi cike da jin kunyarsa.



"Na rufe bakin ko?, gara ma ki sani a matse na ke wallahi. Abba dai ya cuceni daya saka bikin nan da nisa haka. Tunda Mustafan Faty bai gama shiryawa ba da anyi namu bikin idan ya so sai ayi na su daga baya"



"Ya Ubaydu wai ka je inji Abba" muryan ƙaninsa Musa ya doki kunnen sa.



"Musa kana so in zaneka ko? Za ka faɗo kanmu ba sallama sai kace wani dabba"



Musa ya fece daga wajen da sauri tun kafin Ubayd ya damƙeshi dan ya san halin yayan na sa sarai.



"Barin je wajen Abba"



"Idan ka je ka kai ma sa ƙorafin ka ƙila ya chanja ra'ayi"



"Ahaf ashe ba ni ɗaya na matsu ba kenan"



Ba ta amsa ma sa ba ta wuce ɗaki da sauri.



Murmushi yai mai daɗi yana addu'ar Allah ya kai shi lokacin da Asiya Shahidah za ta zama mata a gareshi.





Asiya na shiga ɗaki ta faɗa kan gado. Murmushi ta ke yi tana jin tsananin shauƙin son Ubayd. Ba za ta ce a matse ta ke ba amma harga Allah ba ta so aka saka bikin su wata shida ba, ta ɗauka wata uku ko huɗu Abba zai sa. Koda yake duk dalilin Mustafah wanda zai auri Faty aka kai bikin da nisa saboda ya ce bai gama shiri ba. Suma ɗin cikin wata shida kam sun gama shirya komai.



Ƙaran shigowar notification ta ji a wayarta da ke gefen gado, da sauri ta jawo wayar dan ta san ba zai wuce saƙon favourite poet ɗin ta ba ne wato KaSaSa. Ai kuwa tana buɗewa taga saƙon email ɗin daga KaSaSa ce. Tunda ta subscribing a website ɗin ta koyaushe ta ɗaura sabon poem za ta gani a email ɗinta.



Ta karanta poem ɗin ya fi sau biyar kafin ta miƙe ta je ta ɗauko littafinta da ta ke rubuta duk poetry na KaSaSa a ciki, ta rubuta sabon poem ɗin da aka turo. Idan Ubayd ya zo sallama dole ne ta karanta mishi poem ɗin dan ya taɓa zuciyarta sosai. A zuciyarta ta ce Allah ya zubawa KaSaSa baiwar kalamai.







***





Motoci guda biyar ne su ka shigo wani katafaren gida, irin gidajen nan ne da ƙusosin gwamnati da manyan 'yan kasuwa kaɗai ke iya mallakan su a wannan ƙasa, shi ɗan talaka sai dai ya gani kawai ya buɗe baki ya cika zuciyar sa da buri sannan ya kaɗa kai yai gaba, amma gidan yafi ƙarfinsa.



Motocin sun tsaya ne a farfajiyan gidan. Motar da ke tsakiya wacce ta fi kowanne kyau wani bodyguard ya buɗe ya fito daga gaban motar da sauri sannan ya buɗe ƙofar baya.

Ƙafafuwansa da ke sanye da designer sneakers ruwan toka ƙirar Dior ne suka fara sauka ƙasa kafin sauran jikin ya biyo baya. Dogo ne da tsayinsa zai kai kamu ɗaya da ɗigo takwas a ma'unin meter (1.8m) kusan a ido za ka ƙiyasta tsayinsa da ta shahararren ɗan film ɗin ƙasar India (Bollywood) wato Amitabh Bachchan.

Baƙi ne sosai irin baƙin da ya fi kama da na larabawan ƙasar Sudan. Sai dai na shi baƙin ya haɗu da hutu da jin daɗi sai ya zama har wani sheƙi ya ke yi yana ɗaukar ido. Idanunsa sun fi ko ina ɗaukar hankali a jikin sa. Fari fat da ɗigon baƙi wanda yai kamar an ɗiga baƙin tawada a cikin ruwan madara. Zara-zaran gashin ido da kuma gira da ke cike da baƙin gashi su suka haɗu suka ƙara ƙawata manyan idanunsa. Baƙin saje da ya haɗe da fiskarsa zuwa gemu da gashin baki suka bawa fiskar kyau da kamala.



A zahiri kallon yaro ake ma sa saboda kyaun jikinsa da ke ɓoye shekaru ,da kuma yadda akoda yaushe ya ke shiga irin ta Matasa. A ranakun Jummu'a da lokutan zuwa wajen taro na musamman kawai ya ke shiga irin ta Malam Bahaushe, amma fiye da rabin shigar sa shiga ce ta mutanen ƙasar waje. Ba abun mamaki ba ne ka ga SSK sanye da Tshirt da jeans a office tun ma kafin ya shiga siyasa har zuwa yanzu kuwa da su ke kan Gwamnati.

Kasancewar ya samu sa'ar karatu da wuri ya amshi Phd ɗin sa yana shekaru ashirin da bakwai ne yayinda ya kai matsayin Professor a shekarun sa talatin da biyar, kusan shekarun da ake ɗiba ma sa kenan idan an kalleshi wanda a zahiri an zaftare ma sa kusan shekaru goma kenan cikin shekarun sa.

Yanzu ma SSK na sanye ne da riga mai dogon hannu kalar sararin samaniya, irin yadda sama ke kasancewa a ƙarshen yammaci kafin dare kamar wajajen ƙarfe biyar da rabi zuwa shida ɗin nan, musamman a lokacin sanyi. Wandon jikin sa ta jeans ce kalar light blue, yana sanye da agogo da kuma zoben azurfa a yatsarsa ta tsakiya da ke hannunsa na dama.



Tuni bodyguard ya amshi jakar hannunsa bayan ya sara ma sa yana ƙame jiki tareda faɗin "Excellency"



Mataimakin Gwamna kenan *Professor Saifuddeen Sa'ad Kachallah* ingarman namiji mai cikar zati da haiba wanda a yanzu ya ke riƙe da jahar saboda Gwamna baya gari.



Kai tsaye cikin gidan sa ya wuce wanda ya gina da halaliyarsa tun ma kafin ya shiga siyasa dan ya ƙi komawa gidan gwamnati. Daga falon farko ba kowa sai dai yana iya jiyo hiran matarsa a ɗaya falon da wasu matan. Ya haura matattakala da zai kai shi sama inda ɗakunan gidan su ke. Ɗakin ƙaramin ɗan sa ya fara leƙawa. Yaron ɗan kimanin shekaru shida na zaune akan gado yana buga game a laptop ɗin sa. Sa'ad Saifuddeen Sa'ad Kachallah kenan wanda kowa ke kiransa da Junior. Ya kissing goshin yaron yana tambayarsa ko yayi homework ɗin sa yaron ya amsa da eh. Ya shafa kan yaron sannan ya miƙe ya fice daga ɗakin. Bai leƙa sauran ɗakunan yaran na shi ba saboda kwana uku da su ka wuce su ka tafi hutu. Babbar 'yar sa Nana Khadija ta tafi gidan ƙanwar matarsa yayinda Aisha da su ke kira da Mahira ta tafi wajen Dadda wato kakar sa.



Wanka SSK yai sannan ya sanya farar jallabiya ya fito saboda kiran sallah da ya ke jiyowa daga masallacin kusa da gidan sa.



Hajiya Bilkisu na zaune a falonta tareda wasu mata guda uku. Ɗaya matar Comissioner ce, ɗaya kuma matar wani Senator ce, sai ɗayar kuma tsohuwar comissioner of Health ce wato Dr Madam Helen Audu.



"Yanzu dai ina so komai ya tafi dai-dai gobe, kar ya zama saboda first lady ba ta nan sai mu kasa gudanar da taron yadda ya kamata"



"Hajiya Bilkisu kar ki ji komai, ai abinda ki ke yi a wannan jaha ko firstlady albarka" inji matar senator



Bilkisu ta yi ƙasaitacciyar murmushi ta ce "indai akan cigabar jahar nan ne dole na yi ƙoƙari wajen ganin komai ya tafi dai-dai"



Madam Helen ta ce "Hajiya Bilki ni zan wuce"



"Nagode Mommy, sai mun haɗu goben" Hajiya Bilki ta faɗa da sigar girmamawa saboda Madam Helen ta girme ta sosai, idan ba ta yi sittin ba to za ta kusa kaiwa hakan.

Bayan tafiyar Madam Helen da kusan minti shabiyar sannan sauran matan su ka tafi sai a lokacin Hajiya Bilkisu ta samu damar sauke nannauyan ajiyar zuciya tana tararradin yadda gobe zai kasance. Wannan ne karo na farko da za ta gudanar da babban taro ita kaɗai. Taro ne na matan Gwamnonin Arewa wanda tun kafin tafiyar Firstlady aka tsara shi, ita ne ta kawo shawaran kuma Firstlady ta amince da shi sai dai rashin Firstlady a gari ya sa aka yi tunanin ɗaga taron har sai ta dawo amma Hajiya Bilkisu ta nuna ba sai an ɗaga ba za ta wakilci Firstlady a wajen taron.



Bayan tafiyar matan nan ta lalubo wayar ta ta cigaba da bibiyar yadda za a sauki baƙin gobe ba tareda an samu matsala ba.



Lokacin da ta samu nitsuwa ta haura sama ɗakinta ta wuce ta yi wanka ta saka kaya sannan ta fara sallah, ta haɗa sallar La'asar, Maghriba da Isha wanda zirga-zirga bai sa ta samu yinsu akan lokaci ba.



Ƙarfe goma da kwata ta shiga ɗakin mijinta wanda ke kishingide akan gado yana danna waya yana murmushi.

Zuciyar Bilkisu sai da ya kusa bulloƙowa waje saboda tsallen da yai, kamar walƙiya ta zo ta ɗauke wayar hannunsa tana huci tana duba abinda ya sa shi irin wannan murmushi haka. Shafinsa ne da ya ke rubuta poems ya ke dubawa, ba mamaki yana dariya ne saboda yadda mabiya shafin ke alaƙanta shi da mace.

Saƙon wani fan ɗin sa ta gani da ya ke cewa shi a duniya ba macen da ya ke so kamar KaSaSa.



"Darling har yanzu ba za ka ce mu su kai namiji ba ne ba mace ba" sai kuma ta yi saurin gyara maganarta da cewa "gara su cigaba da yi maka ganin macen, kafin yanzu mata su dinga damunka da waya"



Mayar ma sa da wayar ta yi tana murmushi " My Darling ka san ina kishin ka dayawa"



Bai ce ma ta komai ba ya cigaba da duba saƙonnin masoyan na sa.



"Ka ci abinci?" ta tambaya lokacin da ta kwanta gefen sa.



"Na leƙa ɗakin Junior ya riga yayi bacci, i guess tare ku ka ci dinner kenan"

Still bai amsa ma ta ba.



Ta sani idan SSK yana harkan rubuce-rubucen sa baya taɓa ba da hankali a wani abun daban, shiyasa ta haƙura da maganan ta manna ma sa kiss a kumatu tareda faɗin goodnight ta ja bargo ta kwanta. Gobe babban rana ce a gareta shiyasa dole daren yau ta samu isasshen bacci.



A wajen SSK ba komai ya hanashi kula matar ta sa ba sai ganin cewa ɓata lokaci ne a gareshi ya faɗa ma ta kuskurenta. Shi ba ma'abocin yawar magana ba ne hakan ya sa tun farkon auren su ya ke ɗagawa Bilkisu ƙafa, sai dai maimakon abubuwan su ragu sai ya zama ƙaruwa kawai su ke yi.

Irin rayuwar da yai buri idan yai aure ba ita ce rayuwar da ya ke yi yanzu ba.



A wassu lokutan yakan yi tunanin idan da Misturah ya aurah abubuwa ba za su zo ma sa haka ba. Kafin ya faɗa soyayyar Misturah ta kasance abokiya a gareshi wacce ya ke iya gayawa damuwar sa, wacce ya ke iya neman shawara a gurinta kuma ya samu shawara mai kyau.

Duk da sun taso gida ɗaya babu wannan kusancin tsakanin sa da Bilkisu. Har yau da su ka kusan cika shekaru shabakwai da aure ba zai ce ya gama sanin halin Bilkisu ba haka nan itama yanada yaƙinin ba ta san wanene Saifuddeen ba. Suna rayuwa ne tareda shamaki kamar labule a tsakanin su. Tun kafin ya zama Mataimakin Gwamna baya samun kulawar daya dace a wajen Bilkisu sannan daga shiga gwamnati abubuwa suka sake taɓarɓarewa.

A lokutan dayake cikin ƙunci ya ke buƙatar nitsuwa daga matar sa. A lokutan da kansa ya ɗau zafi daga harkokin gwamnati ya ke buƙatar samun mafaka a wajen matar sa. A lokutan ne za ka ga Bilkisu ta shagalta da harkokin siyasa ko kasuwanci.



Tunda ta sako maganar taron matan Gwamnoni da za ayi baya tunanin ta sake saka shi a lissafinta. Idan har ta tuntuɓeshi to tana neman shawara ne bisa jadawalin da ta tsara na abubuwan da za a gabatar ranan.

SSK ya juya ya kalli Bilkisu da ta ke gwarti alamun baccinta yayi nisa kenan.



Kafin ka yi aure duk irin waɗannan ƙananan abubuwa ba ka saninsu sai kun zauna tare na wani lokaci.

Akwai lokutan da idan zai kwanta sai ya saka auduga ko earbud a kunnensa saboda yadda Gwartin Bilkisu ke hana shi bacci, a hankali har jikinsa ya saba da hakan.



Aure sai da haƙuri, abunda ake gayawa sabbin ma'aurata kenan. Alokacin ba sa gane me ake nufi da haƙuri har sai sun kwana biyu da aure.



A farkon auren su yayi haƙuri da lokutan da zai shiga banɗaki yaga Bilkisu ta jefa pant mai haɗe da pad cike da jini a loundary basket ɗin su. Ko kuma a lokutan da ta ke fama da mura ka ga tissue papers da ta face majina da shi a kan gadon su. Ba zai taɓa mantawa da ranan da ya shiga banɗaki tsantsin majina da aka fyace a ƙasan tile ya ɗebeshi ya faɗi ƙasa ba. Yayi haƙuri da kasancewarta ba ta girki saboda a gidan su bata yi, duk da kuwa girki na cikin abubuwan da ke taɓa ma sa zuciya. Girkin Misturah na ɗaya daga cikin abubuwan da suka saka shi faɗawa soyayyarta tun bai shirya hakan ba.



"Saif wannan pepper soup ɗin yana narka zuciyar namiji yana saka mishi nitsuwa. Inada yaƙinin koma mi yake damunka idan ka ci wannan peppersoup ɗin za ka samu sanyi" abinda ta faɗa kenan lokacin da ta miƙa ma sa ɗan ƙaramin food basket da ta riƙo ma sa.

Misturah ta yi gaskiya domin ranan da ya sha wannan peppersoup ɗin ya samu nitsuwa.



SSk ya kai hannunsa ya shafa gashin wig da ya ɗan bulloƙo ta gefen hular baccin Bilkisu.

Yayi haƙuri da kasancewarta mai saka gashin wig duk da kuwa warin gashin na tada ma sa hankali.

Namiji na son mace da za ta fahimceshi, ta saurari maganar sa. Sai dai Bilkisu ba ta ɗaya daga cikin irin matan nan.

Sau dubu Bilkisu za ta yi iƙirarin tana tsananin son shi tana kuma kishin sa, hakanan kuma sau dubu ba za tayi abubuwan da zai cire shamakin da ke tsakanin su ba, har ta samu damar mallake zuciyarsa.



A lokutan kaɗaici he find solitude in poetry, shiyasa ya ke ɓoye kansa da sunan KaSaSa wanda acronym ne na sunansa.



SSK yai murmushi ganin Bilkisu ta maki kanta tareda sosa tsakiyar kan.



Duk wani mulki daya ke da shi ya tsaya a bakin ƙofar gidan sa ne, a cikin gida shi mijin Bilkisu ne, Abban Nana, Mahira da kuma Junior.

SSK ya muskuta ya jawo Bilkisu jikinsa yana sauke ajiyar zuciya, rabon daya samu nitsuwar miji da mata daga gareta kusan sati biyu kenan.



"Darling na gaji" ta faɗa cikin magagin bacci



"Kar ki damu ba abinda zan yi" ya furta a hankali wani abu na sukan ƙirjinsa...







***





"Kina jina? zan turo miki kuɗin idan na dawo daga office. Ya jikin Muttaƙa?



Tana saƙale da waya a kunnenta yayinda ta ke ƙokarin ɗaura agogo a hannunta.



"Sumayya ki tabbatar Ale bai san da kuɗin nan ba. Kuɗin maganin Muttaƙa kuma ki tabbatar an siyi duka magungunan shi"



Ajiye wayar ta yi ta fice daga ɗakin. Kai tsaye kitchen ta wuce inda Umma ke ƙoƙarin raba abun kari. Kunun gyaɗa ta yi da ƙosai da kuma soyayyen dankalin Hausa.



"Umma zan wuce" ta faɗa da yaren kurame



Umman ta amsa ma ta da cewa ta tsaya ta ci abinci.



"Zan makara Umma, amma ki haɗa min kunun da dankalin in tafi da shi office"



Murmushi Umman ta yi sannan ta fara neman inda za ta zubawa Asiya kunun.



Minti shida kacal ta ƙara aciki ta fito ɗauke da jakarta da kuma ledan da Umma ta ba ta. Motar Ubayd na jiranta a ƙofar gida dan haka tana shiga ya ja motar da gudu. Gaisawa su ka yi a tsanake ta cigaba da duba wayarta tana bitar report ɗin da ta haɗa jiya.



Tafiyar minti shabiyu ya kaisu ma'aikatar su ta yiwa Ubayd sallama ta shige ciki yayinda shima Ubayd ya wuce Asibiti.



Tana shiga office ɗin su ta printing report ta wuce da shi office ɗin Editor I.



"Weldone Shahida" ya faɗa lokacin da su ka gama duba report ɗin tare wanda kusan gyaran da ke ciki kaɗan ne.

Tana komawa office ta samu sauran colleages ɗinta suna hiran taron da za ayi yau a jihar ta su. Da SSK da matar sa Bilkisu duk babu wanda ke burge Asiya a cikinsu.



"Shahida kin san wa za'a tura yau?"



Shahida ta girgiza kai tana cigaba da latsa laptop ɗinta.



Mike ya sake cewa " ina tunanin Abigail za a tura, gashi har yanzu ba ta iso ba"



"Mike kar ka dameni dan Allah. Idan ba ta zo ba MD zai iya bawa wani ai, ko kai ko Usman"





Ta sani magana ya ke son gaya mata akan kada ma tasa ran MD zai bari ta je ta covering report ɗin wajen taron da za ayi na matan Gwamnoni. Ba ta san mi ta tsarewa Mike ba a wannan office ɗin. Tun tana bautar ƙasa kafin a ɗauketa aiki yake sa mata ido cikin lamurranta.



Ta cigaba da aiki tana yi tana shan kununta.





CY ya shigo office ɗinsu da sauri. "Aseey ki je office ɗin MD yanzu-yanzu"



"Miya faru?" Ya ɗaga mata kafaɗa ya fita da sauri.



Ta yi saurin kurɓan sauran kunun daya rage sannan ta goge bakinta da tissue ta fice daga office ɗin da sauri tana lura da yadda Mike ke binta da mugun kallo.





Ba ta da ikon yiwa MD musu lokacin daya sanar da ita cewa itace za ta kawo rahoton wajen taron da za ayi yau.

Lokacin da za ta tafi ya ce "Asiya bana son shirme"



"Ok Sir"



Ta sani Abigail yai niyyar tura wa saboda Abigail ta fita gogewa a wajen aiki. Tunda aka buɗe gidan talabijin ɗin ta ke aiki da su kusan shekaru shahuɗu da suka wuce kenan. Rashin Abigail Manji ne ya sa MD ya waiwayeta. A wajen CY ta ke jin labarin wai Abigail tayi tafiya, jiya da daddare mahaifinta ya mutu a chan ƙauyen su.



Ba su kaɗai ba ne 'yan jarida da su ka zo ɗaukan rahoto kusan kowanne gidan jarida sun aiko da wakilan su. CY ya fito da kayan aiki ya shiga saita camera ɗin.





***





Chief of staff (COS) ne ya shigo ofishin mataimakin Gwamna da sauri hannunsa riƙe da ipad.



"Your Excellency za ka so ganin wannan"



SSK ya karɓi pad ɗin daga hannun COS ya danna kan video dake screen ɗin.



Yar jarida ce a gaban hall ɗin da ake taron matan gwamnoni tana bada rahoto.



"Kaman yadda al'umma su ka shaida irin almabazzarancin da akayi a wajen wannan taro wanda ake iƙirarin anyi shine saboda talakawa. Ko ta ina talaka zai anfana da mawaƙan nan Wizkid da Patoranking da aka ɗauko daga Lagos domin matan Gwamnoni su shaƙata da waƙoƙin su?. Yayinda matar mataimakin Gwamna wato Hajiya Bilkisu S Kachallah take magana akan yadda za a gina

Please Login or Register in order to submit comment