Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na gama kafin ki tafi fatan kin fahimta
Wannan maganar gaba ɗaya yana yinta ne ba tare da ya ɗago kansa ba


Baki Rufy ta tura tana magana ceke da shagwabar da batasan ta iya ba kuma batasan dalilin ta nayi ba kawai ta tsinci kanta da yi ne tace
"Amma fa kai da kanka kace na dinga tafi kada nasa ka kware kuma ni yanzu kace na zauna gashi bacci nake ji
Ta ƙarasa maganar tana tura baki hadi da murza ido yadda yara suke idan suna jin bacci


Tunda ta fara magana ya shagala da kallon ta bai taɓa ganin wacce shagwaɓa tayi wa kyau kamar yadda tayi wa Rufy ba tunda yake,shiru yayi mata ba tare da ya bata amsa ba tare da addu'ar Allah yasa ta kuma yin magana yaji domin maganar tayimai daɗi sosai

"Uhmm natafi Pleaseee
Ta faɗa tana jan karshen maganar wadda har sai da tsigar jikin sa ta tashi sabida yadda ta faɗi Please din

Kai kawai ya iya daga mata domin gaba ɗaya sai yaji ta saukar mai da wata irin kasala ,ahaka dai a daddafe ya karasa karyawa yabar gidan cike da tunanin ta


Yana fita Rufy ta fito falon hadda tsella sabida gano alamar nasara wayar da ya sai mata ta dakko Farida ta kira don ta bata labarin abinda ya faru,yadda faridan ta jita cikin farin ciki ne yasa tace mata zata zo gidan idan ta gama abinda takeyi






***********Alhamdulilah yau kwanan indo arba'in da komawa ga mahaliccin ta mutuwar ta daki inna sosai dan tun lokacin ba wanda zai ce ya kuma ganin walwalar ta kamar da ga kuma rainon indo ƙarama da takeyi
Yau juma'a dan haka tun safe ta gama abinda takeyi sabida tanaso taje masallaci kuma da wuri take tafiya sabida ta zauna a gaba gashi bayan an gama ana musu tafsir


Bayan an idar da sallah ne kamar yadda aka saba duk sati malam mai musu wa'azi ya fara bai dade da fara wa ba yace Akwai" bawan Allah yazo jiya yace yana son magana da mu akan wani abu da ya aikata kuma yake so ya faɗa sabida ya zama izna ga iyaye domin a kula ,to amma mun bukaci mutumin da ya fadi abinda ya faru kuma ya faɗa mana inda insha Allahu zakuji daga bakin sa kamar yadda muka masa alkawari


Magana mutumin ya fara cikin rawar murya
"Assalamu alaikum jama'a fatan anyi sallar juma'a lafiya nine nine wannan bakon mai niƙan da nazo na zauna a yayi na gudu nabar garin nan ba tare da kowa yasan meye dalili ba sai dai kuma ance alhaki kukuyo ne maishi yake bi dama kuma shi sharri dan aike ne duk inda ka tura shi zai je ya dawo,dan Allah idan iyayan indo suna nan ina neman afwar su domin kuwa nine nayi mata cikin da ke jikin ta amma wallahi hakan ba halina bane sharrin shaidan ne kuma a kanta na fara kuma daga ita na daina dan Allah dan Annabi kuyafe min itama ta yafemin nadawo kuma a shirye nake dana aure ta


Tunda ya fara wannan maganar gaba ɗaya wajan ya dau haya niya sai surutu mutane suke yi banda inna da tunsan da ya ra maganar take kuka tabbas tayi ganganci yaka mata ace tun da indo ta fara zumudin zuwa wajan mai niƙa ace ta gano abinda ke faruwa amma ina hakan bata faruwa ba sai da mai afkuwa ta afku


Jin yadda suke hayaniya ne yasa malamin da ke wajan ya daka musu tsawa wadda ita tasa suka yi shiru kamar ba mutum wajan
Kallon mai niƙa yayi sannan yace "cigaba da maganar ka



"Amma sai dai ba nine silar shigar indo cikin wannan halin ba face iyayan ta domin ko sanda na fara neman ta ta riga da ta buɗe kanta da kanta da hannu ita da bakin ta tace min tana ganin yadda Baba da innar ta sukeyi suma shine take so..
Daga haka malam ya daga mai hannu jin maganar zatai yawa tabbas maganar ta daki malamin kuma ta girgiza shi wanda har sai da takai da hawaye ya fito daga idon sa jin yadda iyaye suka yi sana diyyar jefa rayuwar yar su cikin masifa da bala'i


Magana ya fara yi a hankula dan gaba ɗaya jikin sa ya mutu"(innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un wannan wacce irin masifa ce muka shige ta ace iyaye sune zasu zama sanadin faɗa War yaran su a hallaka,dan Allah dan Annabi muji tsoron Allah musani watarana da Allah zai tanbaye mu akan kiwon da ya bamu kuma wannan kiwon ba komai bane face ƴaƴan mu ya muka tafiyar da rayuwar su ya muka basu tarbiyya ,taya kina uwa ta gari amma ace kece silar lalacewar ƴaƴan ki yaran yanzu ba kamar yaran da bane yanzu da wayon su ake haifar su zakuga yaro dan shekara biyu amma yasan anyi mai mai kyau ko mara kyau ba kamar yaran da ba
Ya kamat ace komai namu da zamuyi muna yinsa da lissafi bawai muyi ta yin abu kamar daddobi ba domin sune suke rayuwa haka kawai kara zube ba wani lissafi da zaran kin tara ƴaƴa to ya kamata ace kin tsara wani plan na yadda zasu tafi da rayuwar su kema kuma daga lokacin dole zaki canza wani abun na daga ɗabi'ar ki domin duk abinda kikayi yana kallo kuma da wannan abin zai tashi a ransa bar ganin shi yaro, ƙwaƙwalwar su tafi ta manya domin kuwa su fresh take ba wani tunani ko wata damuwa acikin ta,ya kamata ace daga lokacin da yaro yayi wayo iyaye su raba shinfiɗa da shi,misali yaro yayi shekara daya haka kunga ai lokacin zai iya zamana ya fara tafiya iya magana da dai sauran su to sai iyaye su koma kwantar da shi a ƙasa a samai katifar sa da ban idan ma yaron ki kinsan ba mai farkawa bane idan yayi bacci zaki iya kaishi dakin ƴan uwan sa in kuma shi kadai ne to yan daga kasan nan duk wani motsinsa kinaji,kuma dole sai kun rage sautin ku kuna saduwa da mai gida ya kamata a daina ashhhhh da washh don yanzu ba ku kadai bane idan bazai yiwu ba sai a toshe bakin
Yaron ki daga zarar ya shekara biyu sai ki samar mai wajan kwanciya ko daki idan ma ciki da runfane sai ki dawo da shi falo amma dan abin kunya kuga yaro godai godai dashi a kan gadon iyayan sa wai sabida shi kadai ne
Haka dai malamin yayi ta hakan hankali akan iyaye )




Sosai inna tashe kuka kamar ranta zai fita tabbas tayi kuskure ba ƙarami ba domin kuwa indo har tayi wajan shekara biyar suna kwana daki daka saboda kar wani abu ya same ta
Lokacin da suka tashi daga wajan ne mai niƙa yabi bayan ta ba tare da yasan ita ce mahaifiyar indo ba har gidan suka je kasan cewar indo ta taɓa mai kwatan ce ta haka ne ya gane gidan, sai da suka je kofar gidan yaga inna zata shiga sannan yayi mata magana


"Sannu Baba dama inaso ne zanyi magana da indo dan Allah
Kallon shi inna tayi sannan ta ciro indo ƙarama da ke cikin hijjabin ta ta miƙamai ,tsayawa yayi kamar bazai karɓa ba sai kuma ya amshe ta,kallo ta yake ganin yadda tayi kama da indo to kenan indo ta haihuwa cikin bai zube baa
kenan


Muryar inna ya tsinta saman kanshi tana faɗin
"Ga abinda indo ta tafi ya bari nan domin kuwa ita ta koma ga mahaliccin ta tun ranar da ta haihu
Tana gama faɗa ta shige gida sabida kukan da ya kwace mata ayau tabbas mutuwar indo ta dawo mata sabuwa ,Baba yana zaune tsakar gida yana jiran dawo War da kallon ta yayi ganin ta shigo hannun ta ba indo ƙarama kuma tana kuka



"Aaaa mairo ina kuma kika baro Indon nagan ki ke kadai ?
"Malam Mahaifin indo ne yazo tana wajan sa wanda indo take kai niƙa wajan sa shine ya mata ciki,malam ina dana sanin kasan cewa ta uwa domin ban zama uwar ta gari da kowanna ɗa zaiyi alfahari da ita ba,ina jin ciwo a zuciya ta da yafi wanda nake ji da ina jin zafi da yazama mune sanadin zaman indo haka yarinya daya Allah ya bamu kuma munyi wasarairai da rayuwar ta mune silar lalacewar rayuwar ta bana tunanin Allah zai yafe mana wannan abun....kuka sosai inna take abin tausayi dak mai imani sai ya tausaya mata yadda gaba ɗaya fuskar ta ta kumbura saboda tsananin kuka,ko lokacin mutuwar indo batai haka ba


"Kinga mairo dan Allah ya isa haka tashi maza ki shiga ciki bare naje wajan



Lokacin da inna ta fadawa mai niƙa maganar mutuwar indo kadan ne ya rage bai kida ta kaba sabida yadda maganar ta da ke shi ,maganar tayi matukar girgiza shi indo ta mutu innalillahi wa'inna ilaihirraji'un tabbas mutum baya mutuwa sai lokacin sa yayi amma ni nine sanadin mutuwar indo yanzu ina zan ganki indo na nemi yafiyar ki
Zubewa yayi kan guiwar sa yana riƙe da indo ƙarama ahannun sa kuka yake sosai domin ya dawo ne ya nemi yafiyar indo sannan kuma ya aure ta idan ta amince mai gashi yanzu bata nan indo ta mutu baza ta taɓa dawo wa ba



Baba ne ya fito ya same shi a wannan hali ya fito ne da niyyar ya mai cin mutuncin ci amma yadda ya ganshi da kuma yadda yaji yana surutu sai gaba ɗaya jikin sa yayi sanyi tabbas yasa ni kowanne bawa yana da tashi jarabawar to ita ta indo haka Tata take kuma dai a halin da ake ciki yanzu Tata rayuwar ta kare dan haka hakuri shine magani da fatan Allah ya jikan ta da dukkan Musulmi baki daya






*********Yauma sai da jamsy ta bi Ibrahim zuwa wajan aikin shi sosai ya nuna mata ɓacin ransa da kuma bibiyar Rayuwar shi da take kallon ta yayi cike da ɓacin rai sannan tace



"Wai dan Allah Jamila ana dole ne soyayya a da naso ki amma yanzu banayi to kuma sai ki damu rayuwa ta ki hanani sakat dan masifa duk kinbi kin isheni duk inda naje sai kinje ,a hakan kike tunanin zan so ki baki da aji kwata kwata idan kina son yin mutunci da daraja a wajan saurayi ki bari shi ya biki bawai ke kiyi ta bin shi ba har wani gari



Sosai maganar Ibrahim tayiwa jamsy zafi sai dai kuma bata tunanin wannan ihun nasa sai sa ta daina binshi domin kuwa sosai take kuma tayiwa kanta alkawarin sai ta aure shi ko ta halin ƙaƙa ne ko da kuwa zatai yawo tsirara


Tana gama wannan tunanin ta juya ta fice mai a office ba tare da tace mai komai ba da karfi ta buga mai kofar
Da kallo ya bita yana tsana tsaki hadi da fadin"ace mutum sam bashi da zuciya a rayuwar sa




Haka Ibrahim ya wuni da abubuwa kala biyu a zuciyar sa tunanin jamsy da Rufy sai dai kuma na Rufy yafi karfi domin idan ya tuna ta a yadda sukayi yau da safe sai ya tsinci kanshi cikin wani irin yanayi mai wahalar misal mutuwa idan ya tuna yadda tace mai Please sai kawai yaji jikin sa yahau wani irin yamami
Tsintar kanshi yayi kawai da son siya mata Chocolate din da take so dan haka ya tashi daga daga cikin masu aikin wajan ya aika ya siyomai kwalin da ɗaya sai bayan ya aika ne kuma yake ganin to wai meyasa ma yake son siya matan gashi tunanin ta duk ya dame shi ganin abin yana neman kamar yin karfi ne yasa ya tashi office din Hafiz ya tafi ko zai samu ya man ta






************Tsaf Rufy ta zaiya newa Farida yadda sukayi da Ibrahim yau da safe ai kuwa sun sha dariya kamar me nan Farida take ƙara bata wasu shawarwarin, sannan kuma ta kawo mata wasu daga cikin irin turaren da itake amfani da shi



Har sauri yake ya shigo gida sanda ya dawo cike da tunanin ko tayi bacci sabida goma saura bai taɓa kai wannan lokacin awaje ba,zaune ya same ta tana danna wayar hannun ta duk da cewa ba babba bace amma gema take aciki
Jiyayi kawai ya sauke ajiyar zuciya wadda har sai da ta fito fili, Rufy dake zaune ne ta tashi tsaye tana faɗin


"Ina ka tsaya kai dare haka gaba ɗaya kasa hankali na ya tashi duk wannan maganar tanayi ne bayan ta karɓi jakar hannun sa, Sannan ta mika hannu zata cire mai ri......





🍃🍃 SECONDARY SCHOOL🍃🍃




(Love & romantic story)




Shalele ce💃




Paid page 65&66




_________Kamar yadda suka tsara da Farida yaune take so ta fara shiga ɗakin Ibrahim sai dai ta rasa ta ina zata fara domin wani irin tsoro ne yake kamata duk da Farida tana karfa fa mata guiwa dan haka ta shirya tunkarar Ibrahim don karɓar mukullin dakin sai dai wata zuciyar tana faɗa mata ai karta bari yasan ne zatayi wannan tunanin shiya dauke mata hankali har lokacin ya kure bata gama abin karya wa ba
Shi kuma gogan yana can zaman jiran dan zuwa yanzu ya riga da ya saba da cikin girkin ta har takai idan ba abincin ta yaci ba sai yaji kamar baya koshi dan yasha zuwa aiki ya dawo haka ba tare da yaci komai ba bayan lemo



Cikin sauri sauri ganin ya wuce lokacin da yake fita har an fara kiran shi a waya ta shirya mai abincin mainar masa tayi da miya sai kuwa ruwan tea da yasha kayan ƙamshi sai tashi suke,ganin lokacin ya kure ne yasa ta shirya mai acikin foodflas ta ce ya tafi da shi kada makarar tayi yawa, to wannan dalili yaja har ya manta bai rufe dakin nashi ba
Yana fita ta lura mai rufe ba har sai da tayi tsallan murna kamar yasan abinda take da buƙata kenan,zama tayi ta karya Sannan ta gyara gidan ko ina yayi fess kafin ta fara kokarin shiga dakin nashi a karo na farko sabida ta gyara mai



Kamshin turaran shine ya fara mata sallama wadda harsai da ta rufe idon ta sabida turaran badai kamshi ba irin kamshin nan mai sanyaya zuciyar masoya kai harma makiyan ko da cikin fushi kajishi sai ya shiga ranka
Fesss ta samu dakin ba wani datti sabida Ibrahim badai tsafta ba amma duk da haka ta shiga gyara sosai ko ina ya kuma yin haske ta dakko sabon zanin gado cikin wadan da tasiya ta shinfi ɗa mai ta wanko toilet din fess sannan ta kunna turaran wuta dakin ya dau kanshi mai kwantar da hankali



Lokacin da taga ma duka abinda take azahar tayi dan haka sallah kawai tayi ta zauna karatu har akai la'asar sannan ta tashi a wajan kitchen ta shiga domin tunanin abinda zata dafa ta bure Ibrahim zuwa yanzu itama ta fara jin kanata a matsayin matar aure kamar kowacce mace ba kamar da ba da take wa kanta kallon yar aikinsa



Moi moi tayi musu yaji hanta sannan tayi miyar albasa sai tashin kanshi take sannan tayi zobo mai sanyi abindai gwanin sha'awa (mata mu dinga yi muna canza girki kar ace kullum muke nan cin shinkafa Yasin zaki gundiri oga🤣)
Lokacin da ta gama anyi magariba dan haka tayi wanka kafin tayi Sallah zama tayi ta shafe jikin ta da mayuka masu kamshi da sa laushin fata powder tashafa kadan sannan ta feshe jikin ta da turaruka masu tsada da dadin kamshi



Doguwar riga ta dakko mai karamin hannu bata kai mata har kasa ba amma dai ta sauka sosai rigar mai laushi ce hakan yasa ta biji kinta ta kwanta
Tsayawa tayi tana kare wa kanta kallo sai taga kamar ba ita ba yadda lokaci ɗaya ta canza fatarta har wani laushi take gashi ta kwanta luf luf kamar ba ita ba hakan Yasa sai take ganin abun wani iri



Falo ta dawo ta zauna zaman jiran dawowar sa bata dade sosai ba ya shigo gidan bakinsa dauke da sallama,tunda ya shigo yake kallon ta ganin tayi wani irin kyau fiye da ko yaushe
Tashi tayi hadda dan saurin ta wajan karasa wa inda yake tana faɗin Yaya sannun da zuwa ,ji yayi wani abu ya tsargamai tun daga kafar shi har cikin ƙwaƙwalwa sabida yadda tayi maganar kamar da gayya ta faɗa cikin wani irin salo mai daukar hankali



Jakar hannun sa ta karɓa sannan ta wuce ta barshi tsaye a wajan da kallo ya bita ganin yadda take juya mazaune take yaji wani arin abu ya taso mai





********Kaya suke haɗawa cikin trolly da alama tafiya zasuyi zuwa wani wajan,jidda ce zaune gaba ɗaya abin duniya ya isheta domin kwana biyu gaba ɗaya bata gane kan Antyn tata sabida gaba ɗaya ta canza kamar ba ita ba yanzu ta daina mata walwala kamar da sannan a gaban ta shekaran jiya tashi wata ƙawar ta wadda a da kwata kwata bata taɓa yadda ga ci wata idan ba jidda ba kallon Antyn tayi tana faɗin



"Momsy wai ina zamu jene naga sai zuba kayana kike cikin trolly ?

"Jidda ba inda zani kece dai lokaci yayi da zaki koma gidan ku da zaman


"A'a momsy bangane ba ina kuma zan koma dama ina da inda yafi nan ne Please kimin bayani!


"Ya isa jidda ya kama ta ki gane ni ba momsyn ki bace ni Auntyn kice munyi rayuwa ne na wani lokaci tare to yanzu komai yazo karshe dan haka zaki koma ga iyayan ki na ainihi


"Amma mommy Naga...
"Please jidda ki daka tamin banason yawan magana dan Allah na faɗa miki zaki tafi gidan ku cikin yan uwan ki wannan shine kawai magana


Zaman darshan jidda tayi hawaye na biyo fuskar ta domin gaba ɗaya kanta ya kulle idan momsy ba ita ce maman ta ba to wace kenan, tana ina kuma yanzu me takeyi,me hakan yake nufi


Abinka da Wadda kanta ba dai dai ba nan da nan kuwa taji kanta ya fara ciwo sabida tunanin da ta damu ƙwaƙwalwar ta da shi



Kamar yadda Aunty ta faɗa da kanta tasa jidda a moto bayan sallar magariba suka tafi unguwar su lokacin ba nuta ne sosai sabida duhu da gari ya fara
Kwata kwata jidda kin yadda tayi ta fito daga motar har saida Aunty ta Mata tsawa sannun ta fita,kayan sawar ta ta fito mata da su sannan ta nuna mata gidan bayan ta shiga Mota tana faɗin



"Nan shine gidan ku ki shiga ciki zakiga yan uwan ki
Daga haka ta ja motar ta tabar wajan ba tare da ta jira abinda jidda zata ce mata ba



Tun lokacin da motar ta tsaya a kofar gidan Baba zeey na kallon abinda ke faruwa tare da baban jidda kasan cewar suna daga wajan bishiya a zaune kallon ikon Allah suka tsaya yi ganin macece ta kako jidda kuma har ana kokawar fito da ita daga mota


Ganin tatafi tabar jiddan a tsaye a wajan ne kuma ita ko motsawa bata yiba ne yasa baban zeey cewa
"Ya kamata mu tashi muje don ganin meke faruwa


Sosai sukayi mamakin ganin jidda ce dan duk zaman da suke Basu san wa aka sauke ba
Baban zeey ne yakai hannu ya taɓota domin tabbatar da cewa ita din yake gani
Da sauri ta kwace hannun ta tana faɗin karka kuma taɓani,sosai yadda tayi maganar abin ya basu mamaki hadi da tsoro anya wannan jiddan su ce idan kuwa ita ce to lallai akwai ayar tanbaya akan ta domin kuwa kanta ba kalau yake ba




Daƙar aka samu ta shiga gidan shima da kokawa dan har baban ta yayi fushi yace a barta taje duk inda zata tunda bata da mutunci


Sai da baban zeey ya bashi hakuri tare da maman zeey da umman jidda da ta fara kuka tun sanda ta ganta sannan ya hakura


Tunda aka shigo da ita gidan take kuka kamar ranta zai fita sabida tsabar kuka a haka aka kwana batayi bacci ba suma kuma bata bassu sunyi baccin ba






🍃🍃 SECONDARY SCHOOL🍃🍃




(Love & romantic story)





Shalele ce💃




Paid page 67&68




____________Kwanan jidda uku da dawo wa amma haryau ba abinda ya canza kullum cikin kuka take idan anga tayi shiru to bacci tayi ba inda taje sai dai maganar ta guda ɗaya kullum shine a mai da ita wajan momsyn ta abinda take iya cewa kenan



Baban zeey ne yaga abin ya wuce lissafi tun suna ganin lamarin wasa da rainin hankali har abin ya fara fin karfin su baban jidda ya samu domin suyi magana akan lamarin


"A gaskiya ina ganin lamarin yarinyar nan kamar akwai sihiri a cikin sa sabida abin nata ya fara wuce tunanin mai hankali
Baban zeey ya faɗa yana kallan abokin nashi kuma ɗan uwan shi


Shiru baban jidda yayi yana tunani akan abinda aminin nasa ya faɗa tabbas gaskiya ne akai a lamar tanbaya a lamarin dan haka ya nisa sannan yace

"To yanzu me kake ganin za'ai kenan?


"Eh to ni dai na gama lissafin mu kira wani daga malaman mu da musulunci su duba ta sabida abin ya fara bani tsoro kwata kwata magana ɗaya takeyi kullum ko abinci da bata ci sai dai ayi mata dura


"Gaskiya ne shike nan insha Allahu idan anyi sallar magariba sai muyi magana da liman

Daga haka suka yanke shawarar abinda ya kamata ace sunyi





*********Yauma dai yana zaune cikin office ɗinsa aiki yake sosai sabida ya tara aiki kwana biyu bai samu zuwa ba sabida yayi zazzaɓi a tsaitsaye
Jin ƙarar an shigomai office ba tare da neman izini bane yasa ya girgiza kai domin yasan mutum daya ne yake mai haka shine hafiz dan haba bai ɗago kansa ba ya cigaba da abinda yake jin shirun yayi yawa ba'a shigo ba kuma ba'ayi magana bane yasa ya ɗago kansa Rufy ya gani a tsaye jikin kofar cikin doguwar riga baka da mayafin ta fuskar ta tayi fayau ba komai sai kwalli da tasawa idon ta sai tashin kamshi takeyi



Tashi yayi tsaye yana kallon ta, ita ma shi take kallo
"Ko dai bakayi farin ciki da gani na bane ,ta faɗa cikin shagwaɓa tana tsare shi da ido


Baisan ya akai murmushi ya kufce mai ba yana fadin "nayi mana amma waya kawo ki nan ɗin?
Ya faɗa dai dai lokacin da ya ƙara sa inda take tsaye


"Kai yaya dan Allah haka zaka sauƙi bakin ka yanzu ko zama bayi ba bare ka bani wani abu nasha harka fara tanbaya ta yadda akai to zan koma inda na fito kawai
Ta faɗa tana juyawa da niyyar zata fita daga office din


Da sauri yasa hannu ya riko ta yana faɗin haba sorry karki koma kinji wallahi yanzu haka ke nake tunani a raina muje ciki ki zauna


Da kallo ta bishi duk da ta fahimci baisan yayi wannan maganar ba amma har zuciyar ta taji daɗin jin hakan ko ba komai yanzu tasan yana sonta ko kuma tace ya fara sonta kamar yadda itama ta fara


Lemo da ruwa ya kawo mata mai sanyi sannan ya zauna a kusa da ita kasan cewar a kwai kujera two sita a office din
Sai yanzu ya lura ashe da basket ta shigo a hannun ta

Please Login or Register in order to submit comment