Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne kike gadon asibiti yanzu haka
Kuma a bisa wannan ne nake baki hakuri da kiyafe ni ba da gangan nayi ba,sannan likitoci yan tabbatar min da cewa cikin dake jikin ki ya zube
Ya ƙara sa maganar yana sunkuyar da kai



Sosai naji wani abu ya soke ni a zuciya da ya cemin cikin ya zube kobaa komai naso ace na haife abinda ke tare da ni domin kuwa ban sani ba ko iya shi kaɗai ne rabona a duniya
Kafin na ankara naji hawaye ya wanke min fuska


"Baiwar Allah dan Allah kiyi hakuri wallahi ba da nufi nayi ba ,ki kira mijin ki nayi masa bayani insha Allahu nasan zai fahimta kaddara ce bata wuce ranar ta


Kallon shi nayi ina share hawaye na sannan nace
"karka damu bakomai dama haka Allah ya ƙaddara bazai zo duniya ba bare ya tarar da ɓacin ran dake cikin ta kuma yaji mummunan tarihin yadda akai aka same shi


Kallo na yayi alamar bai fahimta ba sannan yace
"Bangane ba mai kike nufi ?



"Karka damu Baba wannan ba abinda ya shafi rayuwar ka bane yanzu tai mako daya nake neman dan Allah makaranta nake so zan shiga sai dai bansan ya zanyi ba idan da hali dan Allah ka taima kamin




Kallo na yayi naya faɗin
"Karki damu na fahimta acikin rayuwar ki da akwai wani tabo insha Allahu zan taimaka miki akwai aboki na yana da makarkata zanmai magana




"To da wannan taimako da mutumin yamin ne na samu shiga makaranta har muka hadu da ke kuma abinda baki sani ba har muka gama ban taɓa biyan kudin Makaranta ba kyauta nayi Alhaji badamasi ya taimaki rayuwa ta fiye da tunanin ku da farko yaso na zauna agidan sa amma baki yadda
Na nemi gidan aikatau inda anan nake kwana duk wata kuma zasu bani albashi da shine nake duk suwa buƙatuna kuma har izuwa lokacin mahaifina bai neme ni ba shida ƙanwata



Lokacin da na gane ke ƴar waye sosai naso na juya miki baya amma da nayi shawara da yarinyar gidan da nake aiki ita ta hanani na cigaba da kulaki amma zuciya ta cike take da tsananin tsanar ki


Idan baki manta ba akwai lokacin da kika gyai ya ceni gidan ku bayan munje sai na ce miki nidai zan tafi kikayi kikayi na faɗa miki ya akai nace ba komai
To lokacin naga hoton Alhaji Mamman ne tare da ku gaba ɗaya wanda hakan yake nufin ke ƴar shi ce,bayan nabar gidan ku Company mahaifin ki nawuce inda na faɗamin ke ƙwata ce kuma yadda yalalata min rayuwa to tabbas kema sai na lalata taki



Yamin kashe di akan na fita harkar ki ko yasa a ɓatar dani ton daga Lokacin na sake sabon shiri akan ki
Uncle bash saurayi nane kuma abokin dadiro na lokacin da na faɗamai kudiri na akan kine yace zaija hankalin ki wajan cika burina


Rufy Allah shine shaida ta ban shiga rayuwar ki da niyyar na cutar da ke ba amma abinda mahaifin ki kayimin ne ya ja miki


Lokacin da naji zaakiyi aure sai da nayi kamar nai hauka sabida kwata kwata banso hakan ba naso ace kinyi cikin shege a gaban iyayan ki kamar yadda nima nayi domin Mahaifin ki yaji yadda nawa iyayan suka ji


Nayi ta kokarin ganin na lalata maganar auren inda anan ne na gano wanda zaki aure ba kowa bane face dan gidan Alhaji Musa a bokin ai kata masha'ar mahaifinki sosai abin yamin ciwo sun lalata rayuwar ƴar wasu amma suna so su gyara ta ƴaƴan su



Gaba ɗaya jikin Rufy har rawa yake sabida tsabar kuka tabbas iyayan su sun cuci rayuwar su sun bar musu tabon da bazai taɓa gogewa ba


Ibrahim kuwa gaba ɗaya jijiyoyin kansa sun tashi fuskar nan tayi jawurr idon sa abin tsoro sabida tsabar yadda yayi jaaa



Jamsy ce ta rarrafa inda yake tana faɗin
"Ibrahim kayiwa Allah da Annabin sa ka aure ni wallahi ina sonka da zuciya ɗaya kuma na maka alkawarin baza'a samu matsala daga gare ni ba insha Allahu
Ta faɗa tana kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro



"Noo jamsy bazan iya ba,jamsy bazan iya auren kiba domin ko na aure ki bazan taɓa samun kwanciyar hankali ba amma tabbas kin cancanci zama matata sai dai bazan iya shiga gurin da mahaifina ya shiga ba abin da kunya
Ki samo duk wanda kike so namiki alkawarin aura miki shi kuma zan bashi aiki idan bashi da shi


Daga haka ya tashi yayi hanyar waje ganin Rufy bata biyo shiba ne yasa ya dawo da baya da kanshi ya daga ta sabida gaba ɗaya jikin ta ya saki idan banda ajiyar zuciya ba abinda take yi



Tunda suka koma gida ba wanda ya iya cewa da kowa komai duk suka zube a falon Ibrahim kuka yake son yi ko zai samu sassauci a zuciyar sa sai dai ya rasa jikin wa zai jingina ya samu yayi kukan yadda ya ke so


Da rarrafe ya matsa inda Rufy take takure kanshi ya dora a kafadar ta kawai ya saki kuka mai taɓa zuciya jin kukan shine yasa Rufy ta yi shiru da wanda take
Ba shakka iyayan su sun cuci rayuwar su



A haka suka kwana a wajan maƙale da juna baccin ma ɓarawo ne ya ɗauke su su duk sai asuba Ibrahim ya farka yaga yadda suke sannan ya tashe ta



Haka suka wuni ranar kamar gidan mutuwa ba abinda kake ji sai ƙarar fanka kamar ba mutane agidan
Da daddare ne yace ta haɗa kayan ta zasu tafi Kano





************Alhamdulillah jikin jidda aiki yana ta samu domin yanzu ta rage wannan neme neman da takewa momcyn ta ba kamar da ba


Duk bayan kwana ɗaya zeey zata zo gida domin taga jikin nata ganin haka sai umman ta tace ta daina zuwa shida kansa mijin yazo yace ba komai yasan yadda zeey suke ita da jidda idan bata zoba bazata taba kwantar da hankalin ta ba domin ranar da tazo ta koma ma kwana tayi tana kuka ga ƙaramin ciki da take dauke da shi


To da wannan damar ne zeey ta samu take yawan zuwa wajan ƴar uwar ta duk da ba hira suke ba idan tazo sai dai kallan kallo




Aunty ce zaune cikin wasu manyan kujeru masu azabar kyau ita da wani babban mutum magana suke sai dai banajin abinda suke faɗa


Bayan sun gama maganar ne naga ya tashi yabar wajan ,wayar ta ta dakko daga cikin jaka hoton jidda ne a saman wayar tabbas tanason jidda sosai sai dai ba yadda zatai wa'adin zama da ita ya ƙare tayi ma'amala da yara kala kala amma ba wadda ta shiga zuciyar ta irin jidda hoton take ta kalla cike da kewar babyn ta


Kiran waya tayi minti kadan aka daga
"Hello besty yarinya nake so ƴar shekara goma sha uku na baki kwana biyu ki nemomin wadda kikasan ba zamu samu matsala da ita ba


Daga haka ta kashe wayar ,tana cigaba da kallon hoton jidda tana tuno nonon ta masu laushi da dadin taɓawa tare da durin ta da kullum cikin fitar da ruwan dadi yake baya taɓa ƙafewa




Bayan zuwan su Ibrahim Kano sun tara iyayan su waje ɗaya kuma sun faɗa musu cewa sun hadu da jamsy sai dai daga haka basu kuma cewa komai ba domin ai iyayan suna da hankali kuma daga jin haka sunsan to sunji duk abinda suka aikata


Daren da mahaifin Rufy yaji wannan labari kwana yayi bai bacci bayana ta tunani komin jamsy ta lalata musu mutun ci a idon ƴaƴan su
A cikin wannan daren ne ciwon sa yayi tsanani dama kuma ga ɓarin jiki yana fama da shi tsawan shekara biyu


Da safe suna zuwa asibiti likitoci suka ce jinin shi yahau sosai ana buƙatar abinda zai kwantar mai da hankali ba'a son ya dinga yawan tunani ko tuna wasu abubuwa da suka faru abaya domin ta hakane kadai za'a samu jinin ya sauka





🍃🍃 SECONDARY SCHOOL🍃🍃




(Love & romantic story)




Shalele ce💃



ASSALAMU ALAIKUM BARKA DA WANNAN LOKACI FATAN KOWA YANA CIKIN KOSHIN LAFIYA DAN ALLAH KUYI HAKURI DA JINA DA KUKAYI SHIRU KWANA BIYU WALLAHI JIKIN NE SAI A HANKULA AMMA YANZU ALHAMDULILLAH





Paid page 73&74





___________Alhamdulillah yanzu jikin jidda ya warware sai kuma abin da ba za'a rasa ba amma yanzu tana magana kuma tana gane dawa take tare sai dai idan abin ya motsa ne kuma sai ayi ta fama dama kuma shi sauki sai a hankula




Sosai jikin mahaifin Rufy yayi tsanani domin kuwa jinin nasa yayi sama sosai likitoci sunyi iya kokarin su wajan ganin sun samo bakin abin sai dai kuma abin ya ci tura dan haka suka ce a tsaya kawai a zubawa sarautar Allah ido


Yau take Litinin 21/8/2023 kuma a yaune mahaifin Rufaida yace ga garin ku nan da asuba( kullu nafsin za'iƙatul maut) Tabbas duk kan wani mairai sai ya ɗan ɗana zafin fitar rai


Mutuwar Alhaji Mamman sosai ta girgiza ahalinsa harma da na waje duk da boyayyar ɗabi'ar sa da ba'a sani ba mutum ne na mutane Sannan yana da kirki fiye da tunani ga taimakon mabuƙata,to da yake ɗan adam tara yake bai cika goma ba dole sai an samu nakaso a wani wajan to wannan mummunar ɗabi'a ita ce kawai za'a iya cewa aibun sa kuma itama ba wanda ya sani , sosai ya samu shaida wajan mutane



Rufy tayi kuka kamar ba gobe domin mutuwar ta taɓa ta sosai bataso mahaifin ta ya rasu yanzu ba taso sun hadu da jamsy ya nemi yafiyar ta sai dai kuma hakan bai yiwu ba rai yayi halinsa


(Mudai sai dai muce Allah ya jikan magabatan mu ya kauta namu zuwan yasa muyi kyakkyawan ƙarshe AMEEN)



Bayan kwana hudu Sannan jamsy tazo Kano lokacin da taji mahaifin Rufy ya rasu sosai ta girgiza lallai rayuwar nan idan ka zauna kayi tunani ba komai bace ,dan haka ta shirya zata je gida domin yiwa ammyn Rufy da ita kanta Rufyn gaisuwa



Misalin ƙarfe uku na yamma ta ƙara so kofar gidan har zuwa lokacin akwai mutane a waje a zaune ƴan zaman makoki kasan cewar shi Babban mutum


Cikin gidan ta shiga shima da mutane amma ba sosai ba dan haka direct ɗakin Rufy ta wuce dan tasan anan ne zata same ta ,ai kuwa tana shiga dai dai lokacin ita kuma Rufy ta fito daga wanka

Tayi mamakin ganin jamsyn dan batayi zatan ta dawo daga Lagos ba cike da wata irin kunyar jamsyn da take ji yanzu ta nuna mata wajan zama, gaisawa sukayi kan Rufy a ƙasa domin tun da taji abinda ya shiga tsakanin ta da mahaifin ta da sirikin ta take jin wani irin kunyar kallon jamsyn
Cikin sanyin murya take faɗin


"Jamsy dan girman Allah ki yafewa mahaifi na, naso ace kun hadu ya nemi ya fiyar ki sai dai kuma mun makara ,amma idan kina ganin bazaki iya yafemai ba shike nan ba komai bazan ji haushin ki ba domin nasan an cuceki a rayuwa
Duk wannan maganar tanayin tane hawaye yana zubo mata



Hannu jamsy tasa ta janyo ta jikin ta tana faɗin
Rufy na yafewa Abba kuma ina fatan Allah ya yafe mana gaba ɗaya domin muma masu laifi ne , Allah ya jikan sa yasa ya huta


Sosai Rufy taji daɗin yadda jamsy ta yafewa mahaifin ta dan haka cike da farin ciki ta rungume ta sannan ta saki kuka wanda zabata iya cewa ga dalilin kukan nata ba
Shin na farin cikin ta yafewa mahaifin nata ne ,ko kuma na rasuwar sane




Tom haka dai rayuwa take idan yau kaine gobe ba kai bane ,idan kai ake yayi to wataran wani za'ai koda kuwa kana duniyar fatan mu Allah yasa muyi ƙarshe mai kyau

Bayan kwana goma da rasuwar Alhaji Mamman sannan jamsy da Ibrahim suka hadu har da Rufy a wajan ,magana suke akan matsalar jamsy Ibrahim ne ya kalle ta yana faɗin
"Kina son mahaifina kuma zaki iya auren shi?


A matuƙar razane suka ɗago kansu daga jamsy har Rufy domin basuyi zaton Ibrahim zaiyi wannan maganar ba kwata kwata


Ganin yadda suke kallon shine yasa yace ,"bacewa nayi ku tsaya kallo na ba kamar kunga bakuwar halitta tanbaya nayi dan haka amsa nake buƙata


Sunkuyar da kanta ƙasa jamsy tayi tana wasa ha zoben dake hannun ta tace
"A'a


"Kar kiji komai idan har kinason sa to tabbas xansa ya aure ki ko tayaya dan haka ki fadi gaskiya


"A gaskiya Ibrahim bazan iya auren mahaifin kana badan komai ba sai kawai ina matuƙar ƙaunar ka ,amma tunda kace bazan same kaba na baka wuƙa da nama duk wanda kaga ya dace ka auramin daga yanzu na ɗau ƙeka a matsayin dan uwa na da muka fito ciki ɗaya


Sosai jamsy ta bashi tausayi Tabbas tana da kirki sannan tana da zuciya mai kyau domin da wata ce hakan ya kasan ce a kanta Allah ne kawai yasan abinda zata aika ta, Allah yana son mutum mai tafiya koda kuwa shi aka cuta


"Shike nan naji zanyi tunani akai kuma na gobe da wannan matsayi da kika bani , sannan abu na gaba ki shirya zamuje da ke domin daddy ya nemi yafiyar ki akan abinda suka aika ta miki


"A'a Ibrahim baza'ai haka ba duk abinda kaga ya faru to muƙaddari ne daga Allah dama Allah ya rubuta hakan zata faru ,to ni dai na yafe mu su wallahi basai munje ko ina ba ina fatan kuma Allah ya yafe musu da mu baki ɗaya


Jikin Ibrahim ne yayi sanyi sosai ganin yadda jamsy take da saukin kai da ba haka ya ɗauke ta ba


Kallon ta ta mayar kan Rufy da tayi shiru kamar ba ta wajan ,hannu tasa ta riko nata sannan ta fara magana kamar haka


"Rufy ki yafemin na sani na cutar da ke akan abinda ba laifin ki ba , tabbas nayi wawta da nace zan dau fansa akan ki da kuma muguwar shawara da ake bani ita ce tayi tasiri a kaina har nayi tunanin cutar da rayuwar ki Kum......


Hannu Rufy tasa ta toshe mata baki hawaye yana biyo idon ta take faɗin
"Kwata kwata jamsy ban taɓa jin haushin ki ba ko kadan balle yanzu da nasan komai nice ma ya kamata na nemi yafiyar ki dan haka komai ya wuce insha Allahu mun dawo kamar da





Bayan sati biyu sannan Ibrahim da Rufy suka fara shirye shiryen koma wa Lagos Rufy taso jamsy ta bita amma sai ta ƙi yarda dan haka suka tafi su kadai
Lokacin da suka ƙara sa gida ne Farida mayar hafiz tazo domin taya Rufy gyara gidan sabida yayi kura sosai wata ɗaya da wani abu ba mutum a cikin sa



Anan ne take kuma yi mata gaisuwa dama kuma sunzo Kanon ita da hafiz ana i gobe uku ta kwana a gidan su Rufy
Hira suke yi shike da nishadi domin yanzu akwai sabo sosai tsakanin su,anan ne Farida take faɗa mata ya kamata yanzu tunda sun dawo to lallai ta koma ɗakin mijin ta da kwana


"Gaskiya bazan iya zuwa nace zan kwana dakin sa ba ai abun ba aji kamar ba mace ba nuɗin
Dariya Farida tayi jin abinda Rufy tace tana faɗin


"Banda abin ki ai dama ba kai tsaye zaki je kice zaki kwanta ba ke dabarar nan ta mata baki iya ba
Zaki iya cemai kinga wani abin tsoro haka dan haka bazaki iya kwana a ɗakin ba kinga ai zaice to ku kwana tare


Kallon ta Rufy tayi tana faɗin
"To abin tsoro kamar me kenan zance na gani ,kuma ma nifa wallahi kunyar kwanciya zanyi tare da shi


"Au kunya like cewa shike nan zauna wata ta kwace miki miji kinaji kina gani yadda take daukar wankan nan kina gani ba budurwar da yake burgewa ne


Jin Farida ta kira wata yasa nan take Rufy taji wani irin zafi a zuciyar ta (Akace kishi kumallon mata)to shine ya motsawa Rufy dan haka cikin sauri tace
"To nidai faɗamin abinda zance na gani mu bar maganar wata


Ganin yadda lokaci ɗaya tayi ne yasa Farida sakin dariya bata shirya ba tana fadi.
"Waiii irin wannan kishi haka Rufy anya kuwa zaki bar shi nan gaba ya ƙara aure daga misali kin bi kin rikice


"Ni ba wani rikice wa da nayi kece dai kike gani haka,kuma ai ko nayi kishin mijina ne

Jin haka yasa Farida ta kuma sakin dariya tana faɗin ,"aaa lamarin ki babba ne


To daga nan ne ta faɗa mata abinda zata ce idan Ibrahim ya dawo gidan sannan ta mata sallama ta tafi domin hafiz bazai zoba bare su tafi tare



Lokacin da Ibrahim ya dawo ta gama girki tayi wanka dama kuma trollyn kayan ta suna falo basu mayar ba dan haka ta dau kayan da take buƙata ta sa
Riga da wando ne wandon dogo ne kayan pink color ne masu laushi sosai suka karbi jikin ta, sannan tabi ko ina ba shafe da turare mai daɗin kamshi



Ruwan wanka ta fara faɗamai yayi sannan ta zuba abinci Kowa da nashi suka fara ci suna hira jefi jefi sai dai gaba ɗaya hankalin ta yana kan yadda zai dau maganar da zata faɗamai take
A wannan zaman da sukayi a Kano yasa sun saki jiki da junan su har hakan yasa suke hira



Bayan ya gama ne ya zauna yana kallo kasan cewar yanzu yasa musu tv wajan shadaya ya tashi ya nufi ɗaki zai kwanta dai dai lokacin ruwan sama ya sakko


Harya shiga ɗaki ya tuna wayar sa ya barta a falon dan haka ya dawo lokacin Rufy ta kasa faɗamai dan haka tayi tunanin kwanciya kan kujera koda zai fito ya ganta yayi magana

Ai kuwa yana ganin ta yace
"A'a bazaki tafi ɗaki bane kika zauna anan ga ruwa kinaji an fara !


Cike da fargabar abin da zaice mata tace
"Dama ɗazu da muna gyarawa ne muka ga kunama kuma kafin mu kashe ta ta gudu to shine nake tsoron kwana cikin dakin karta harbe ni


"Kuna ma kuma acikin gidan nan? To ai kwana anan bazai miki ba tashi muje ɗakin na gani ko zan ganta


Jin abinda tace ne yasa da sauri tace
"a'a kawai kaje ka kwanta a ɗakin ka ni zan kwana anan idan yaso da safe ka duba

Jin haka da yayi yasa ya gyada kai yana juya wa ya nufi ɗakin sa ba tare da ya kuma cewa komai ba
Ganin ya juya yasa ta bishi da kallo hawaye yana cika idon ta kenan har yanzu Ibrahim bai fara son ta ba tunda bazai iya cewa ta tawo ɗakin sa ta kwana ba ya barta a kan kujera


Harya kai bakin kofa zai shiga yaga kamar bai dace ba idan ya barta anan dan haka ya juyo yana faɗin
" To kizo mu kwanta tare mana idan ba damuwa
Daga haka ya shige cikin dakin ba tare da ya jira abinda zata ce ba



Jin haka yasa ta kama kallon shin harya shige ciki
Kenan bazai iya jerawa da ita bane yasa ya wuce ya bata guri ko me hakan yake nu fi


Tana cikin wannan tunanin ne yaji wata irin tsawa gashi an dauke wuta kuma ba fitila a hannun ta dan haka da sauri ta nufi ɗakin sa ta shiga
Lokacin tuni ya kwanta jin abin gadon da tayi yasa ta gane tazo bakin gadon dan haka ta hau ba tare da tunanin komai ba


Duk motsin da take yana jinta sai dai yayi kamar baya kan gadon ,ya fahimci tsawar da taji ne ya shigo da ita dan har ɗan bigewa tayi kuma da ta hau gadon hadda sauke ajiyar zuciya


Lamo tayi a gadon tana shaƙar ƙamshin turaren da aka sawa bedshet din take tana cikin wannan abinne aka kuma wata irin tsawa da harshi Ibrahim din sai da ya tsora ta


Batare da ta sani ba jin wannan tsawar yasa ta murgina inda yake,tsawa aka kuma yi dan haka ta juya da sauri batayi aune ba a wannan juyin sai jin bakin ta tayi ya sauka cikin na Ibrahim


Kenan inda ta juya shima nan yake kallo da sauri tayi ƙoƙarin matsawa sai dai kuma tuni yasa hannu ya riko nata idon shi tar akan fuskar ta yana ganin yadda ta zafi ido ta ikon Dan hasken da ke shigowa ta window







🍃🍃 SECONDARY SCHOOL🍃🍃




(Love& romantic story)




Shalele ce💃




Paid page 75&76






____________Washe gari da safe gaba ɗaya Rufy kasa hada ido tayi da Ibrahim sabida wata irin kunyar shi da take ji,shi kuwa gogan ko ajikin sa harkar gaban sa kawai yake sai dai jefi jefi yana kallon ta yana tunawa da wani abu, lallai jiya yasha romance sai dai bai zurfafa ba ganin yadda bata saki jikin ta sosai ba
Tunawa yayi cewa tayi ma'amala da wasu mazan awaje take yaji irin azababban kishi ya taso mai wani irin haushin ta ya kamashi ganin yadda jiya jikin ta yake rawa kamar sabuwar budurwa kuma yasan ba haka take wa waɗan can ba


Jin kamar idan ya cigaba da tunanin za'a samu matsala ne yasa shi katsewa da ya tuna cewa waɗan can ma da abin ya faru ba laifin ta bane
To amma ai yasan gaba ɗaya sun gama kwashe kayan gonar yanzu ba abinda zai samu sai ciyayi


Sallamar hafiz da Farida ce ta katsemai tunanin da yake nan suna zauna suna taɓa hira har ya gama karyawa sannan suka tafi aiki suka bar matan agidan
Bayan tafiyar sune Farida ta taimaka mata suka gyara gidan sunayi suna hira


Anan ne Rufy tayi tunanin ko ta faɗa mata yadda sukayi da Ibrahim ko kuma dai tayi shiru tunda sirrin tane ita da mijin ta
Ganin bata da wata hanya da ya wuce ta faɗa mata ne yasa ta bata labarin yadda sukai ,sosai Farida ta nuna jin dadin ta ganin komai ya kusa zuwa ƙarshe sannan ta kuma bata wasu shawarwarin da suka dace



Tunda suka fita yake bawa hafiz labarin yadda sukayi da jamsy sai dai bai faɗamai suwaye suka lalata mata rayuwa ba sabida gudun zubewar mutuncin iyayan su anan ne hafiz yake cewa mai zai hana Ibrahim ya haɗa auren su fai manajan su na wajan aiki dama matar shi ta mutu ga yara biyu ta barmai idan har jamsy zata riƙe yaran sai suyi auren su
Da wanann shawarar suka ƙara sa wajan aiki sun nemi Abdullahi domin su tattauna kuma sun faɗamai budurwa ce sai dai tsautsayi da ya faɗa mata akai mata fyade iyanan kawai suka tsaya
Batare da tunanin komai ba yace ya amince domin yasa iyayan gidan nashi bazasu mai mugun zaɓe ba



Lokacin da Ibrahim ya dawo gida da yamma yake bawa Rufy labarin yadda sukayi da Abdullahi sosai ta nuna farin cikin ta anan take ta kira jamsy tana mata albishir da ta samu mihi,ta nuna jin dadin ta duk da zuciyar ta ba dadi tana son Ibrahim matuƙa sai dai tasan yayi mata nisa sai hakuri



Tun daga wannan ranar Rufy ta dawo kwana dakin Ibrahim har yanzu kuma ba abinda ya kuma shiga tsakanin su bayan wannan romance da sukayi zadai suyi baccin su wani

Please Login or Register in order to submit comment