Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da jamsy da kuma Farida suka cigaba da rayuwar su cikin farin ciki da kwanciyar hankali tare da mazajan su



Mota ce take ta faman sharara gudu kamar zata tashi sama sosai take gudu wanda duk mai hankali yagani yasaan gudun bana lafiya bane daga gani,tun suna tafiya ta cikin gari har suka dawo daji suke shiga wanda ba gida gaba ba gida baya ,motar dake gaban ce taje ta daki wani dutse nan da nan tahau gangarawa acikin dajin tana karo da bishiyu tana kaiwa ga wata bishiya ne ta tsaya take agun ta fara ci da wuta


Tun farkon sanda motar tayi karo da dutsen mutanan daya motar suka tsaya da gudun fitowa sukai dan ganin ina wannan motar take gangarawa akan idon su ta kama da wuta sannan naga sun juya suna kallon juna mazane guda uku dan haka suka jinjina hannu alamar yayi kyau sannan suka juya da baya domin fita daga cikin dajin



Kasan cewar dajin akwai mutane a cikin sa daga wani ɓangare hakan yasa tun sanda motocin suka shigo suka ɓuya domin an saba kawo musu hari ko kuma azo ayi kisan kai awajan jin ƙarar da sukayi ne na budurwar motar da kuma kanawar ta da wuta ne yasa suka fito da sauri dan ganin abinda ke faruwa har tafiyar waɗan can mazan sun gani dan haka suka gane na cikin motar da take ci da wuta biyo su akai


Wajan motar suka matsa dan ganin ko za'a iya samon wanda yayi rai aciki mutum daya ne wanda har wani wajan daga jikin sa ya fara ci da wuta gani alamar yana da rai dan sai ɗaga hannu yake alamar taimako yasa sukayi ƙoƙarin ɓalle kofar su fito da shi


Wasu daga cikin sune suka fara zagaye dajin ko Allah zaisa su samu wani abun ,daga can bayan dutse duk hango ƙafar mutum da sauri suka duba,macece kwance cikin jini itama tana numfashi dan haka aka dauke su zuwa cikin gari


Sosai suka tausaya musu domin ita wadda ta kone macece amma gaba daya fuskar ta ya lalace da hannun ta guda ɗaya bayan kuma ƙanana ƙananan gurare
Ita kuma ɗayar karaya ce har uku wanda daya daga ciki sai dai acire hannun dan bazai koma ba ga kuma a ƙafar ta har waje biyu sai kukkurejewa da tayi ,gaba ɗaya dai sun fita hayyacin su dan ba mai gane su ,sosai wadan nan bayin Allah suka taimake su



Bayan kwana uku zuwa lokacin jikin nasu yayi sauki sai mai kuna da take ta fama abun a fuskar ta ,wadan nan mutane da suka taimake su sun nemi suji wanne da liline yasa aka biyu su gashi su mata ba maza ba bare ace fadan daba
Sun faɗa musu sudai basu san ko suwaye suka biyo su ba kawai dai sunsan cewa ana binsu ne



Daga haka mutanen basu kuma tanbayar su komai ba duk da bai zama lallai abin da suka faɗa musu gaskiya ne ba






************Yau tunda ta tashi gaba ɗaya bata jin dadin jikin ta sai a hankali gashi suna ta shirye shiryen tafiya Kano za'ai bikin ƙanwar ta kasan cewar bata da ishashshiyar lafiya hakan yasa komai sai a hankali take yi



Tunda ta fara haɗa kayan yake kallon ta kwata kwata ya kasa gane mata kwana biyun nan duk ta canza ga wani hali da takeyi wanda ba nata ba abu kadan zai faɗa mata tahau fushi ko yanzun nan ta fara masifa,kallon ta yayi yana faɗin



"Wai kuwa anya baby lafiyar ki kalau kuwa gaba ɗaya kinyi wani iri idan Kanon ne baƙeson zuwa kiyi zaman ki ni sai muje da su hafiz kawai?


"Ba haka bane hubby wallahi kawai jina nake duk wani iri ga raina a ɓace kamar na sa kuka ...
"Kuka kuma baby muna zaune ƙalau ko na miki wani laifin ne ban sani ba ?
"Eh wallahi hubby k......


Wayar Ibrahim ce tayi ƙara dan haka tayi shiru daga maganar da take ,dagawa yayi ganin wanda yake kiran "munriga da mun shirya ƙarfe biyar jirgin mu zai tashi insha Allahu,daga haka ya kashe wayar yana kallon Rufy dake tsaye


"Baby kiyi sauri kinga hafiz yace yanzu zasu fito suje su tawo da Jamila sai su wuce airport muje mu same su acan gashi naga saura awa ɗaya jirgin mu ya tashi



Bayan saukar su Rufy a garin Kano direct gidan su aka wuce da su kasan cewar gobe za'a fara biki dama kuma Farida ba ƴar Kano bace a Kaduna hafiz ya auro ta


Sosai Ammy ta nuna farin cikin ganin yaran cikin kwanciyar hankali da alama ba wata matsala tsakanin su da mazajan su ,dakin Rufy na da suka shiga wanka sukai sannan sukayi sallah abinci aka kawo musu amma sai dai Rufy tace bataci fura da nono take so ,jamsy ce ta tsaya tana kallon ta ganin abinda take sone fa wato funkaso da miyar taushe amma tace bata ci kasa shiru tayi dan haka tace



"Wai kuwa besty lafiyar ki kalau yau kece kike cewa baƙyason funkaso to ko dai yayan nawa yayi ajiya ne bamu sani ba
Wata uwar harara Rufy ta yi mata tana faɗin
"Kin manta abinda yafi ajiya yayi ba ajiya ba


Farida da jamsy ne suka sa dariya bayan sun fara cin funkason suna faɗin
"To meye kuma na faɗa daga magana nifa dadi na da masu ƙaramin ciki masifa wallahi ,cewar Farida ,nan ma dariya jamsy tayi tana faɗin,wai wayaga idon besty a lebouroom chabbbb

Ai gaba ɗaya wannan hirar da su Farida suke nan da nan Rufy ta ciki tayi fammm kamar zata fashe saboda masifa su kuwa sun samu abinyi sai tsokanar ta suke



Washe gari aka tashi ana ta shirye shiryen biki domin yaune zasuyi coktel party kowa yana ta kazar kazar da walwala amma badda Rufy


Anty lami ce ƙanwar Ammy tace "wai kuwa Yaya fati kin lura da yanayin Rufaida gaba ɗaya kamar mai ƙaramin ciki duk ta ɗan yace tayi wani iri


Ammy dake zaune tana haɗa kaya tayi dariya tana
"Fati ai Rufaida kadai kika lura da ita sabida nata yafi fitowa fili amma duk su ukun da alamar tambaya akansu ,sai dai kuma ina tunanin basusan da cikin ba suma da alama


"Gaskiyar ki Yaya sai yanzu da kika faɗa na lura ita Rufaida da gani gado zatai laulayi mai sa fushi irin nawa
Ta ƙara sa maganar tana kallon su daga inda suke zaune su ukun suna hira








🍃🍃 SECONDARY SCHOOL🍃🍃



(Love& romantic story)



JAMA'A MUN KAWO

*Cornflakes
*Cocopops
*Madara
*Macaroni
*Taliya
*Kwaki
*Busashshen kifi
*Kayan kitchen
*Kayan bacci

Muna bada kwata ,rabin kwano,kwano,rabin buhu,buhu




Shalele ce💃





Paid page 83&84






_________Masha Allah anata biki cikin kwanciyar hankali an sha shagali yadda ya kamata yau ne kuma za'a daura aure inda daga nan kuma biki ya ƙare da yamma za'a wuce da amarya dakin mijin ta



Rufy tun da ta tashi take ta fama da zazzabi sama sama ga ciwan kai sai take alaƙanta hakan da hayaniyar gidan biki ,lokacin da yan ɗaurin aure suka dawo kowa ya fito anata hotuna su Farida ansha kyau Abdullahi ma yazo mijin jamsy jiya da daddre


Tun fitowar su Farida da jamsy Ibrahim yake zuba idon ganin tauraruwar shi ta bayya na amma shiru har aka fara daukar hoto hakuri ya kasa dan haka ya matsa inda jamsy suke tsaya ita da Abdullahi suna magana yana tanbayar ina Rufy bai ganta ba
Kallon shi tayi tana fadin "ayya wallahi besty tun safe batajin dadi tana ɗaki a kwace bacci take


Da sauri Ibrahim yasa kai zuwa cikin falon dan ganin halin da babyn sa take ciki dan gaba ɗaya ma ya manta gidan sirikan sa ne

Dai dai lokacin da ya isa kofar ɗakin zai shiga ne ƙanwar Ammy ta fito daga ciki ,take yaji wata irin kunya ya rufe shi domin baiyi zaton da mutum a ciki ba

"Anty ina wuni..,ya faɗa yana sosai kai alamar yaji kunya
Dariya tayi tana faɗin malam Ibrahim watakon tun da ka ɗauke min yarinya ta shike nan kayi wuyar gani ai shike nan ka shigo garin amma ko nema babu ka shiga tana ciki bacci take


Dariya yayi yana tura kofar tare da faɗin insha Allahu anty kafin mu koma zamu zo mu wunar miki

Bakin gadon da take kwance ya zauna yana ƙare mata kallo wani irin kyau yaga ta ƙara gashi tayi haske sosai har ɗaukar ido take
Tafin hannun ta ya kama sosai ya tsora ta ganin yadda yayi fari kamar ba jini jikin ta gashi yayi zafi


Kama mata hannun da yayi yasa ta farka ganin shine yasa ta sakar mishi murmushi tana faɗin
"Habby ya akai ka shigo nan ?


"Ba wannan ba baby kinsan baki da lafiya amma baki faɗamin ba kawai sai ki kwanta Aɗaki
"Hubby bafa wani abu bane zazzaɓi ne kawai muma ai anty ta bani pracetamol nasha kuma nasan zai sauka

"Gaskiya baby ban yadda ba kawai ki tashi mu tafi asibiti yafi


Ganin da gaske yake hakan yasa ta hakura ta tashi suka tafi su tafi asibitin ,a hanya suka hadu da maman shi tana shirin shigowa falon dan haka tace


"A'a sai ina kuma haka naga ka rakito ta ita da batajin dadi ina zaka kaita?
"Mama asibiti zankai ta sabida naga kamar da ba jini jikin ta duk tayi wani irin haske ta kode

"To gwani na gwanaye ita ta faɗa maka bata da jinin ko kai ne kuma ai tasha magani zazzabin zai.sauka
"Amma kuma mama... ,"Kaga daka ta yanzu jeka samo mata maltina da madara tasha dan ba abinda taci tun safe idan yaso kwatafi wajan bokan Turai din


Sosai maganar da maman Ibrahim tayi yasa Rufy dariya



Bayan sunje asibin duk wani gwaje gwaje da Yakamata ambata anyi kuma abinda suka tunani ya tabbata ciki ne da ita har na wata uku lokacin da wannan albishir ya isa kenan Ibrahim suma ne kawai baiba sabida tsabar farin ciki



Rufy kuwa banda shafa cikin ba abinda take wai itama yau tana ɗauke da ɗan ta na kanta mallakin ta alhamdulilah ya Allah Allah Nagode maka da kabani wannan kyauta
Abinda take iya cewa kenan


Ibrahim kuwa yana fitowa wayar hafiz ya kira ya fadamai sosai shima ya nuna jin dadin sa tare da fatan Allah ya bawa faridan shi shima
Daga nan wayar umman shi ya kira tana daga wa abinda ya fara cewa


"Mama munje an duba ta kumaa sun tabbatar min d tana da ciki har wata uku nima kwanan nan zan zam Baba..
"To rasa kunya naji sai ka kashe wayar
Cewar maman Ibrahim tana kashe ta cike da farin cikin wannan lamari


Sai yanzu ya tuna maman shi ce da kunya ya tsaya wannan zancen da ita



Kafin su dawo daga asibiti gaba ɗaya kowa yasan halin da ake cikin suna zuwa aka fara kaffa kaffa da ita kowa sai tan bayarta yake akwai abinda take so tun tanajin kunya har ta ware


Nan fa su Farida suka sata agaba sai tsokanar ta suke suna faɗin
"Ai dama tunda ta fara wannan fushin da wani banason ƙanshin abu nasan anyi kamu ƙallo ta faɗa raga







🍃🍃 SECONDARY SCHOOL🍃🍃




(Love & romantic story)





Shalele ce💃





Paid page 85&86





__________Alhamdulillah an gama biki lafiya amarya gidan ta su Rufy ansha ziyara sosai gidan yan uwa da dangin miji duk su ukun suke zuwa inda suka je har gidan su hafiz da Abdullahi mijin jamsy


Shirye shiryen koma wa Lagos suke amma ta Kaduna zasu biya gidan su Farida ,sosai jikin jamsy yayi mugun sanyi ganin yadda duk inda suka je daga cikin dangin kowa ake karɓar su hannu biyu sai taji inama itama aje nata dangin


A yaune motar su ta tashi zuwa Kaduna duk su shidan kasan cewar motar gidan su Ibrahim ce jif babba mai gida uku hakan yasa matan suka zauna gidan baya mazan kuma. Suna tsakiya sai driva a gaba


Hira suke sosai cike da nishadi Rufy ce ta kalli jamsy tana faɗin

"Besty kamar a hanyar Kaduna kika ce garin ku yake ko?

"Eh meyasa kika tanbaya

"Dama naga munzo ta wajan ne shine nayi tunanin mai zai hana muje kema kiga gida ko hubby
Ta ƙarasa maganar tana zura hannu inda Ibrahim ya ke


"Haka ne baby kinyi magana mai kyau gaskiya ya kamat ace Jamila kinje gida bai kamata ki riƙe mahaifin ki arai haka ba


Tunda suka fara maganar bata ce komai ba sai hawaye da ya fara biyo fuskar ta tana tuno da rayuwar ta ta baya


Kukan da ta fara ne Abdullahi yasa baki nan suka shiga bata hakuri da tausar ta akan ta yafewa mahaifin ta domin duk tsiya shiga haife ta


Da haka ne suka samu ta sakko inda ta shiga yiwa drive kwatancan hanyar zuwa gidan nasu
Cikin lokaci ƙalilan sai gasu sun bayya na agidan su jamsy sosai gaban ta yake faduwa domin bata san me zata tarar ba


Gidan ta gani gaba ɗaya ya canza kamar ba shiba da yake shekarun da yawa kusan shekara bakwai rabon ta da garin
Yara suka gani sunzo sun zagaye motar dan haka Abdullahi yace
"Ko zamu aika yaran nan su yimana sallama da shi

"A'a su sauka su shiga gidan idan yaso in yana nan zai fito ai
"Cewar hafiz

Hakan akai su ukun suka nufi cikin gidan ,gaban jamsy banda faduwa ba abinda yake cike da tsoro ,sallama sukayi sai dai shiru ba wanda ya amsa ganin haka yasa suka kalli juna kafin su sake hada baki wajan yin sallamar


Wata yar matashi ya ce ta fito daga ɗaki hannun ta rige da yaro tana jijjiga shi ,mutuwar tsaye jamsy tayi ganin Yar uwar ta ce da suke uwa daya uba daya Ummi


"Bayin Allah ku kuma daga ina dan gaskiya ban waye ku ba , Ummi ta faɗa tana karaso wa tsakar gidan


Duk gaba ɗaya shiru sukayi ganin haka yasa Farida cewa "dan Allah nan ne gidan malam Sani?
"Eh nan ne sai dai kuma shi baban baya nan sai zuwa dare zai dawo amma sai lafiya ko dan gaskiya ban taɓa ganin ku ba ?


Farida ce tace ,"jamsy yi magana mana kika yi shiru
Ganin kamar bata jiba yasa Rufy ta taɓa ta tana faɗin "besty kiyi magana mana kin tsaya kamar status


"Cikin rawar murya mai alamar karyewar zuciya da nuna raunin ta a fili tace,"Ummi baki gane niba?

Ummi da ta maida hankali wajan yaron dake hannun da sauri ta ɗago kanta jin Muryar da ko a mafarki bata taɓa zato ba ,domin ta dade da cire rai akan Yar uwar Tata bazata taɓa dawowa gare su ba


"Yaya Jamila kece ko mafarki nake dan Allah idan mafarki ne karku tashe ni,yaya Jamila nayi neman ki amma ban ganki ba kullum zuciya ta gayamin take zaki dawo sai dai tsawan shekaru shiru ba ko labarin ki ,dan Allah karki kuma tafiya ki barni


Tunda Ummi ta fara magana jamsy take kuka su Rufy na taya ta ,da sauri taje ta rungume Ummi tana daɗin

"Ummi nice ba mafarki kike ba ,yaya jamilar kice nadawo ummi bana fatan na kuma tafiya na barki yar uwa ta tayi kewar ki sosai

Wata irin rungume juna da sukayi ne yasa yaron hannun Ummi ya fara kuka ganin kamar basusan yanayi bane yasa Farida karɓar shi ta fara jijjiga shi



"Wai kuwa lafiyar ki kalau Ummi kika bar yaron nan yana kuka haka har waje nifa dadi na da ke wawta wallahi
Wata babbar macece wadda ashekara zatayi Kusan hamsin ta shigo tana wannan maganar ,kota kan abinda matar take faɗa Ummi bata biba ta nufe ta da gudu tana faɗin


"Umma Hassana kinga abinda nake gani yau gaskiya ne ba mafarki ba yaya Jamila ce ta dawo gida
Wadda aka kira da umma Hassana da sauri ta ƙara so wajan da jamsy take


"Da gaske Jamila tace wannan,Jamila meyasa kika gujemu dan mahaifin ki yace ki tafi hakan bayana nufin cewa muma muntsane kiba ,jamila munyi neman ki sau ba adadi sai dai bamu same kiba...


Garan muryar da akayi ne daga waje yasa tayi shiru da maganar da take
Baba ne ya shigo cikin gidan hannun sa dauke da ledoji


Wani irin mummunar faɗuwar gaba ce ta kama jamsy domin bata san yadda zasu kaya da mahaifin nata ba ,domin zai iya yiwuwa har yanzu bai huce ba ,cike da tsoro ta fara ja da baya inda shi kuma yake ƙara shigowa cikin gidan ba tare da ya lura da ita ba ya dai ga mutane a waje sun gaisa sukace wajan shi suka zo yace musu yana zuwa


Da gudu jamsy ta ƙara sa inda yake ta riƙe ƙafafun sa tana sakin kuka mai taɓa zuciya sosai take kukan tana faɗin
"Baba Dan girman Allah kayi hakuri ka yafemin wallahi ba laifina bane na tuba bazan sake ba Dan Allah karka sake korata a karo na biyu


Tunda ta fara magana yaji wani irin abu azuciyar shi domin Muryar ya kaɗai ta tabbatar mai da cewa wannan jamilar shice
Kafafunsa ya janye daga cikin hannun ta yana ja da baya .....








🍃🍃 SECONDARY SCHOOL🍃🍃




(Love& romantic story)




Shalele ce💃




Paid page 87&88





________Zaune suke a kofar dakin sunyi jugum jugum gaba ɗaya abin duniya ya ishe su gani yadda cikin lokaci ƙalilan yanayin halittar su ya sauya


"Fatima(Aunty) ya jamata zuwa yanzu mu fara shirin koma wa gida tunda dai kina ganin yadda bayin Allahn nan suke ɗawai niya damu abin ya isa kuma kinga ba ƙarfi ne da suba

Aunty ce ta juyo tana kallon kawar tata da fuskar ta da gaba ɗaya ta canza mama sabida wutar da ta kona ta ce
"Yanzu a haka kike so kice na shirya mu koma cikin gari da wannan fuskar ,tukunna kina tunanin madugu ya daina neman mune?


"Haba dai neman me zai mana bayan a gabansu yaran nasa mutarmu ta kama da wuta dan haka duk zatan su mun mutu yanzu ,dan haka zamu koma cikin yan uwan mu domin zama anan bazai mana ba


Da wannan tunanin su anty da fuska ta kone suka fara shirin barin garin cike da kewar yan garin domin sunyi musu halacci kuma sun tafi da alkawarin zasu dinga zuwa suna gaisawa






*********Tashi tsaye jamsy tayi tana girgiza kai hade da faɗin
"Baba kayiwa girman Allah kaya femin wallahi idan baka yafemin ba bazan taɓa samun rahma ba idan na mutu


Baki du su Rufy suka shiga bashi harda Ummi da umma Hassana ganin haka yasa baban ya daga musu hannu dan haka suka yi shiru kamar ruwa ya cinye su sai ajiyar zuciya kawai da akeji


"Tare kuke da waɗan can mazan na waje ?
Baba ya jufo tan bayar yana kallon jamsy ,kai ta daga mai dan haka yace
"Mamana jiki ce su shigo ,da sauri Ummi tayi hanyar waje domin kiran su Ibrahim



Tabarma umma Hassana ta shinfiɗa babba yadda kowa zai zauna Baba ne ya fara zama a tsakiya Sannan kowa ya zauna matan nadaga ɓan garan hagun sa sai maza a dama ,gyaran murya yayi kafin ya fara magana


"Bayin Allah ban waye kuba kuma kunce waje na kuma zo daga ina kenan ?


Kai duk suka sunkuyar su duka ganin yadda fuskar sa take ba wasa kafin Ibrahim cikin sanyin murya yafara magana
"Baba ni sunana Ibrahim Wannan matata ce sunan ta Rufaida ,ya faɗa yana nuna ta muna zaune ne a garin Kano

Hafiz ne ya karɓa inda shima ya gabatar da kansa tare da matar sa kafin Ibrahim ya fara magana cike da tunanin abinda sirikin nasa zaice dan da gani ba shida wasa
"Baba ni kuma sunana Ibrahim nine Wanda na aure Jamila,daga haka yaja baki yayi shiru


Kallon ta umma Hassana tayi ita da Ummi jin cewa tayi aure kafin Baba yace
"To naji kowa ya faɗi sunan sa amma baki faɗa min abin da ya kawo ku ba har yanzu


Ibrahim ne yayi ƙarfin halin cewa "dama Baba munzo ne domin mu baka hakuri akan Jamila dan Allah Baba a tausaya ayafe mata hannun ka baya rubewa ka yanke kayar duk lalacewa yar kace ko ina taje kuma duk abinda zata aika ta aduniya dole iyayan ta suna da kamashu aciki...



Hannu Baba ya ɗaga mai dan haka yayi shiru
"Bismillah Alhamdulillah dukkan yabo ya tabba ga Ubangiji Mai kowa mai komai ,naji duk bayanan da kuka yi abinda nake so ku fahimta Jamila ƴata ce ta ciki na kuma duk duniya ba wanda ya kaini sonta abinda ya faru wanccen lokacin muƙaddari ne fushi da ɓacin rai tare da baƙin cikin rasuwar mahaifiyar ta sune saka sa harna kore ta amma tun bayan tafiyar ta ba wanda ya kaini shiga tashin hankali domin lokacin da ƙananan shekaru abin ya faru
Na kore ne bayan laifin da ta aika ta daga baya zuciya ta ta cika da zullumin cewa yanzu na bata lasisin yin yadda ta ga dama ,ako da yaushe addu'a nake Allah ya dawo min da ita lafiya sauda yawan lokaci nakan kulle kaina a ɗaki nayi kuka sabida bansan halin da take ciki ba ,tun daga ranar da tabar gidan nan ban kuma sake samun farin ciki ba irin na yau nayi matuƙar farin cikin ganin ta cikin koshin lafiya Sannan abinda ya kuma kwantar min da hankali na cewa bata faɗa mummunar hanya ba shine da naji har aure tayi nayi farin ciki mara misaltuwa ,ke kuma Rufaida Nagode Miki Allah ya saka da mafificin alkairi domin wajan shekara uku kenan da nasan cewa kuna tare da Jamila kuma na samu labari akan ki yarinyar kirki ce Allah ya biyaki abinda kika mata
Ke kuma Jamila nayafe miki duniya da lahira ba tun yauba na daina fushi da ke


Wani irin kukan farin ciki ne ya kwace wa jamsy sosai ta rungume Ummi tanayi


Kasan cewar yamma tayi Baba yace bazasu tafi ba sai sun kwana anan nan fa sabuwar hira ta ɓarke tsakanin su matan inda Baba kuma suna waje shida su Ibrahim


Anan ne jamsy take jin mijin umma Hassana mutuwa yayi shine Baba ya aure ta ,itama Ummi tayi aure yanzu tazo gida ne a cikin garin Kaduna gidan ta yake



Washe gari da safe haka suka tashi cike da farin ciki hatta mutanan gari sunji jamsy ta dawo sai zuwa ake kallon ta Bama kamar yadda ta zama ƙatuwa fatar ta tayi kyau alamar jin dadi kowa ya ganta yasan tana cikin kwanciyar hankali


Son je gidajan yan uwa an gaisa a tsaitsaye inda tun da suka dawo kuma zazzaɓi ya rufe su su duka ukun pharmacyn da ke cikin garin suka je inda aka tabbar duk su ukun suna da ciki da wannan farin cikin suka dawo gida ai kuwa zo kaga mura wajan Baba da umma Hassana sosai umma Hassana ta kula da su sai da suka kuma kwana saboda jikin nasu kamin suka kama hanyar tafiya Kaduna tare da Ummi suka tafi dan itama zata koma gidan ta
An rabu zuciya cike da farin ciki da kewa ta karbi numbar Baba da zasu dinga waya da kuma ta umma Hassana ta Ummi kuwa duk su ukun suka karba









🍃🍃 SECONDARY SCHOOL🍃🍃




(Love & romantic story)




Shalele ce💃




Paid page 89&90






____________Kamar koyau she yauma sanye take da hijja bi har ƙasa tana tafiya cikin nutsuwa gaban ta kawai take kallo duk inda ta wuce kunji yara na faɗin Malama sai gobe a haka har ta karaso gidan su da sallama

Please Login or Register in order to submit comment