Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta shigo gidan cike da gajiyar koyar War da ta dawo


"Mama², fitowa maman zeey tayi daga kitchen tana faɗin wallahi kekam jidda zanga ranar da zaki girma kullum shekaru ƙaruwa suke amma lamarin ki ƙara lalace wa yake to yanzu kuma kiran me kike min daga shigowar ki ?


"Wallahi mama wanka nake so nayi na gaji ruwan dumi nake so ne nasan babu wajan umma
Kai mama ta girgiza tana faɗin
"Idan kikai wani abun kamar ba Malama ba yanzu fa kika dawo daga koyar da yara amma kinzo gida kina shagwaɓa abinda kike ko ɗan ki Arif bayayin sa


Dariya jidda tayi tana "to ai mama idan banyi muku shagwaɓar ba wazanwa ku kadai ne da ni ,ni kin tunamin bari na kira sister dazon ta kirani ina aji ban daga ba
Wayar ta ta ciru daga jaka ta fara kokarin danna kiran zeey ,sallamar da akai agidan ne yasa ta daka ta tana amsa sallamar mata ne su biyu suka shigo gidan da kallo jidda ta bisu ganin kwata kwata bata san fuskar ba Musamman wadda taga fuskar ta ta kone ,gwarama ɗayar tana mata kallon sani sai dai ta manta a ina tasan ta



"Jidda baki gane mu ba ko ?
Da sauri ta ɗago jin kamar tasan mai wannan Muryar to amma idan ta santa a ina kenan ....


Umma ce ta fito daga ɓangaren ta sabida kiran da take tayiwa jiddan taji ta shiru ,tsayawa tayi ganin wasu sababbin fuskoki agidan


"Bayin Allah ku kuma daga ina haka ?umma ta tanbaya dai dai lokacin da ta ƙara so inda suke tsaya


Aunty wacce tuni idon ta ya ciko da hawaye ce ta fara magana
"Nice Auntyn su jidda da Zainab a SECONDARY SCHOOL


Amatukar razane jidda taja baya ganin abin kamar a mafarki Aunty ya akai ta koma haka ,umma ce ta shiga kiran mama nan da nan ta fito


"Dan Allah ku bamu waje mu zauna muyi muku bayanin abinda yake tafe da mu ...


"Malama daka ta waje awanne gidan kenan duk abinda kuka shuka abaya bai isa ba shine watakon zaku debo jiki ku tawo har kuma maganar a baku waje to wallahi tunkafin na ƙirga uku maza maza ku ficemin agidan idan kuma kunki to lallai zakuga abinda zai biyo baya domin kwata kwata bazai muku dadi ba



"Dan Allah mama kiyi hakuri wallahi wannan karan bada mugun nufi muka zo gidan nan ba hasalima munzo ne domin mu bawa su jidda hakuri akan abinda muka musu arayuwa duk da nasan kwata kwata ban can can ci su yafe min ba amma su dubu girman Allah suyi hakuri,ko iya haka Allah ya nuna ishara domin tun a duniya na fara girbar abinda na shuka dan Allah dan Annabi jidda kuyi hakuri kuya femin nasani na cuce ku arayuwa



"Jidda ki dubi girman Allah kiyi hakuri hakkin ku nasan bazai barmu ba arayuwa amma idan kuka furta kunya fe mana to zamuji sauki ta wani wajan duk da nafi cutar ki wallahi sharrin shaidan ne da kuma san abin duniya da burin ta rawa sai gashi tunkafin aje ko ina rayuwar ta juyamin baya,kuma ni nasani hakkin kine wallahi yake bibiya ta
Dubi yadda nazama ba wanda yake iya gane ni koke sanda muka shigo nasan baki gane ni ba ,bayan cutar da na kamu da ita


Tunda Aunty ta fara magana gaba ɗaya jikin su mama yayi mugun sanyi ganin yadda gaba ɗaya Aunty ta koma kamar ba ita ba duk kamanni ta sun canza sai ma da ta buɗe musu wani sashi daga jikin ta da ya kone sai da tsigar jikin su ta tashi


Tabbas Allah ba azzalumin bawan sa bane kuma duk daran dadewa sai Allah yabi wa wanda aka zalunta hakkin ta,ga dai shi tun kafin aje ko ina Anty ta fara ganin ishara ko da iya wannan kunar aka barta to taga rayuwa


Shiru jidda tayi tana tuna abubuwan da Aunty tayi mata arayuwa tabbas duk da Aunty ta lalata mata rayuwa ne amma tasan Aunty tana son ta tsakani da Allah ,a baya tayi alkawarin bazata taba yafe mata ba komai zai faru sai dai kuma ayanzu da ta ganta gaba ɗaya sai taji jikin ta ya mutu wani mugun tausayin ta ya kamata


Baban ta da abban zeey ne suka shigo gidan nan suka tarar da abinda ke faruwa sun tausaya wa rayuwar su Aunty kuma Baba ka musu nasiha sosai da sosai ka ƙara tsora tar da su domin duniyar nan ba abakin komai take ba
Sannan a matsayin su na iyayan su jidda sun yafe musu abinda sukayi musu kuma sunsa baki akan jidda tace ta yafe musu
Shiru jidda tayi kamar bazatai magana ba domin gaba ɗaya komai dawo mata yake cikin ƙwaƙwalwar ta sabo fill


Umma ce ta shiga bata baki akan ta furta taya fe musu domin itama mai laifi ce awajan Ubangijin ta kuna ta nemi yafi ya ya yafe mata dan haka itama ta yafe musu sai ta ƙara ganin haske a rayuwar ta domin Ubangiji yanason mutum mai yafiya ako da yaushe duk abinda akai ma kaya fe sai Allah ya saka ma cikin ruwan sanyi


Kanta ta matsar gefe domin kwata kwata bata son gani ko inuwar Aunty kamin tace
"Na yafe Allah ya yafe mana baki daya


Sosai Aunty suka shiga godiya kamar wadan da akayi wa bushara da gidan aljanna kamin suka tashi suka bar gidan ,inda suka bar su mama da mataccen jiki domin duk sunyi sanyi da lamarin duniya



Daki jidda ta shiga ta dokko wayar ta wani irin hawaye ne ya shiga bin kuncin ta wanda bata san nameye ba kawai kukan taji yazo mana ba yanda ta iya haka ta saki kukan
Sai da tayi iya isar ta kafin ta kira zeey inda ta shiga bata labarin abinda ya faru sosai itama taji wani iri kuma tace itama ta yafe duk abinda suka musu






BAYAN SHEKARA BIYR



************* Gida ne babba sosai iya ganin ku cikin gidan na shiga amma sai kai ne aya kulle ganin gidan part uku ne to kenan gidan hayane ko me ,ko kuma dai mata uku ne da mai gidan ganin ba Ni da mai bani amsa hakan yasa na nufi part din tsakiya inda daga nan nake jiyo hayaniyar yara falon ta bude ba shiga Masha Allah na furta sabida ya tsaru sosai ba wani kayan ƙyale ƙyale aka saba kawai komai mai tsada ne kuma color da ta dace da falon


Yara ne su guda hudu suke wasa a falon uku daga ciki kamar yan uku domin girman su ɗaya hatta da kayan jikin su kawai dai biyu a ciki mata ne ɗaya kuma namiji gaba dayan su baza su wuce shekara biyar ba sai kuma yarinya karama a zaune a kujera batafi shekara biyu ba


Mace daya daga cikin yan ukun ce ta dau remote ta chanza Chennal da sauri na mijin ya sauka a kujerar yana karbar remote din bayan ya kai mata duka

Kuka tasa awajan ,daga ciki naji ana magana wata mata ce ta fito tana faɗin "gaskiya Khalifa bakajin magana sau nawa ina fadama banason saurin duka kuma ba na fadama Zuhra yayar ka ceba dan gidan ku ko dan kaga tsayin ku daya to ta baka wata uku

Sai da ta gama faɗan ta juyo sunnan na gane wace jamsy ce ta zama babbar mace da alama hutu da kwanciyar hankali sun zauna


Da gudu Khalifa yayi waje yana sa kuka akan faɗan da tayi masa kai ta girgiza tana faɗin zaka dawo ne kasame ni


Part din farko ya shiga yana kiran " mamy² wacce ya kira da mamy ce ta fito tana faɗin dan gidan mamy mai kuma ya faru ne irin wannan kiran haka Rufy ce ta zama wata hamshakiya kamar ba ita ba tayi ƙiba abinta


"Ummi ce ta ce wai Zuhra ta girme ni kuma dai dady yace nine babban Yaya
Dariya Rufy tayi domin kuwa tasan tatsuniyar gizo bata wuce ta koki dama kullum sai anyi wannan maganar
"Eh kai ne babban yaya amma dai ka daina dukan su babban yaya baya duka kaji ,yanzu jeka wajan Didi kace Ina gaishe ta kaji twins sun fara kuka


Fita yayi daga part din ya nufi ɗayan ita kuma ta shiga ɗaki wajan twins da suka fara kuka nono ta shiga basu




Da daddare kamar yadda aka saba waje ɗaya ake cin abinci duk gidan har mazajan su yaran a haɗa musu sai kowa kuma ya zuba abinda yayi mai anayi ana hira da yake akwai wajan shan iska babba agidan dan haka da daddare duk nan suke zama cin abinci


Su Ibrahim yanzu an zama manyan magidan ta ga kuma uwa uba kudi an samu alhamdulilah rayuwa lafiya kalau ake yin ta kowa yana farin ciki tare da matar sa da kuma ƴaƴan Sa


Bayan an gama akai sallama kowa ya nufi part ɗinsa Zuhra ce ƴar Rufy tace "mamy wajan finah ƴar gidan Farida take nufi Ni dai zan kwana
Khalifa ne ya kallo ta to nima anan zan kwana


Ibrahim ne ya kalle shi yana girgiza kai kafin yace
"Ai babban yaya baya kwana cikin mata yanzu abinda za'ai kai da husna (yar gidan jamsy ta biyu) zaku kwana tare shike nan kaga an raba ko
Kai ya daga mai alamar ya yadda


Daga nan kowa ya wuce part din sa bayan anyi sallama da juna



Rufy ce zaune bakin gado tana shirya twins cikin kayan baccin su Ibrahim ya shigo


"Baby ayi maza maza a gama shirya su azo a shirya baban su shima
Dariya Rufy tayi tana faɗin "kai hubby yanzu da yaran ka uku ka girma ai


"Chabb lallai yariyar nan to aini ko Zuhra na aurar karshe kenan to wallahi bazan girma ba wajan matata
Dariya tayi tana kantar da twins sannan ta matsa kusa da shi tana faɗin


Nima mijina bana son ka girma awaje na nafison kayi ta zama a yaron ka kaji Ni kuma zan kula da kai yadda ya kamata





Bangaran Farida sai da ta yiwa finah da Zuhra addu'ar bacci sannan ta baro dakin su ta shiga nata lokacin hafiz yana zaune
"Au abban finah ai na zata kayi bacci yadda na dade dinnan


"Bacci fa kika ce ai jira nake kizo ki bani abin daɗin nan naki ya ƙara sa maganar yana tsare ta da ido

"Kai wasa kake dai ko yanda na zama jagwal dinnan salon kawai ka tsokano min nakuda ban shirya ba

"Haba dai karki karaya kadan zanyi insha Allahu ba abinda zai faru kuma ma ai dama idan ana harka nakudar tazo haihuwar tafi sauki
Daga haka ya samu yayi nasarar hade bakin su waje ɗaya



Jamsy ce zaune bakin mudubi sai shafa hura take masu kamshin gaske gaba ɗaya dakin ya dau kanshin Abdullahi dake danna waya ganin jan ran da take mai yayi yawa ya sa ya aje wayar cikin sanda yazo inda take sai ji kawai tayi yayi sama da ita yana
"Haba dan Allah sweetie sai jamin rai kike gaba ɗaya kamshin humrar ki ta gama cika ni






ALHAMDULILAH

Anan na kawo karshen wannan littafin nawa ina fatan kun fahimci abinda nake so a fahimta aciki
Dan Allah wanda nayiwa ba dai dai ba ya yafe min dan Adam ajizi ne Ako da yaushe mu masu laifi ne


Inawa kowa fatan alkairi ,wadan da suka juri bibiya ta Ina GODIYA SOSAI ALLAH ya bar zumunci ya haɗa kowannnen mu da alkairin watan da yake tunkaro mu ameen

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment