Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

can kuma ya ce, “Mai yiwuwa ne ba ta yi na’am da al’amarin mu ba”.



Ta ce, “Babu komi, za ta huce a

hankalv’.



Daddy na saukowa daga matattakalar bene Mamin biye da shi rike da brief case dinsa ya yi tozali dasu a falon.



Ya yi murmushi yayin da Mami ta kara hade rai. Ya ce, “Dama ina son ganin ka”.



Ya mike cikin girmamawa ya bi bayansa suka nufi falon ganawa da bakinsa dake daga harabar gidan.



Daddy na bisa kujera, Zahraddeen na gefensa bisa kilishi. Daddy ya ce, “Ya sakon da na baka na



Wilcod din Abidjan?” Ya ce, “Ya zo ya amsa tun shekaran jiya”’.



Ya ce, “To madallah’’.



Sai kuma ya yi shiru, shi ma Zahraddeen kanshi na kasa. Ko motsin kirki ya kasa.



Can Daddy ya ce,



*““Zahraddeen”’.

Ya dago da fararen idanunshi ya dube shi amma bai amsa ba.



Ya ce, “Meke tsakaninka da Safah ne?”



Zahraddeen ya rude, ya soma indainda, saboda kwarjinin da Daddy ya kara yi masa, har ya soma ganin wautar kansa, da wuce gona da irin sa. Daddy ya yi murmushi ya ce,



“ Zahradden feel free with me. Ka amsa min mana, ni Babanka ne ba bakon ka bane’’.



Ya yi ta maza ya ce, “Am Daddy, dama.....dama ina son mu samu lokaci ne, sannan in gabatar maka da kaina a matsayin mai neman auren Safah, mun daidaita kanmu”’.



Daddy ya yi murmushi ya lumshe ido na “yan mintunsa sannan ya budesu a hankali akan Zahraddeen din ya ce, “Zahraddeen zaka iya hakura da son da kake wa Safah, ka juyar dashi ga ‘yar uwar ta? Ina nufin, ka _ auri abokiyar tagwaitakarta MARWAH?” A firgice ya dago ya dubi Daddy,

kamin ya yi magana Daddy ya ce, “Safah da mijinta, tun ranar da aka haife ta, amma idan kana ganin za ka lya auren ‘yar’uwarta sati mai zuwa ka kawo min sadakin naira dubu goma in daura muku aure rana ita yau. Lahadi kenan, zan daura auren Safah da Almustapha tare da naku. Tashi je ka ka yi shawara, ina sauraron ka”.



Ya bude baki zai yi magana Daddy ya ce, “Ka je ka yi shawara tukunna, ba zan yi hakan ba sai da amincewar ka. Ina sonka ne Zahraddeen, ina son hada jini da kai, saboda kai mutum ne na gar.



Banda shi wancan alkawari, ba abin da zai hanani baka wacce kake so cikin ‘ya’yana. Amma Safah da Marwah duk daya ne, abin da ya yi Safah shi ya yi Marwah, sai dai bambanci na akida da halayya wanda za ka iya lankwasawa cikin dan lokaci kalilan. Tunda har yanzu yara ne. Tashi jeka ka yi tunani sosai, ka kuma shawarci Innar ka, na baka kwanaki

uku ka zo min da abin da ka yanke”.



Zahraddeen ya mike ya fita, kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, ya nufi motarsa ya bude ya shiga ya zauna ya kwantar da kai a jikin sitiyari. Bai yi aune ba sai jin danshi ya yi a kan fuskarsa, ya mika hannu ya shafo su, hawaye ne, shi kansa bai san dalilin zubarsu ba.



Ya fi minti talatin a hakan, kamin ya ja motar masu gadi suka bude mishi get ya fita. Ya yarda ba zai samu Safah ba, amma ba ya jin da ranta zai iya auren ‘yar’ uwarta-shakikiyarta. Karewama wadda suka fito duniya tare a lokaci daya.



Ba aure ya damu ya yi da wuri ba. Kasancewarsa saurayi da bai taba aure ba, ba kuma shashanci yake yi ba, balle ya tantance yanada bukatar mace soon ko a’ah. Safahn kawai yake so, soyayyarta ce ta sanya mishi son yin auren. To amma ya zai yi ya budi baki ya ce da Daddy baya son ‘yar cikinshi,

wanda shi a ganinsa karamci ne ya yi mishi?



Me yasa Safah ta boye mishi cewa akwai alkawarin dan’uwanta a kanta? Tayi masa wasa da hankali da zuciya.....Har ya iso gida bai san inda hankalinsa yake ba. Kuma tambayar da yake so yayi mata kenan, hakika tayi mai wasa da zuciya, don bazai iya cewa ta yaudare shi ba, don ya yarda son da take masa na gaske ne, na tsakani da Allah ne.




Alh. Aliko na zaune a falon shi, ya kira Mami ya ce ta turo mishi Safah. Tana zaune a bakin gadonta ta yl tagumi, Marwah na jera kayansu da aka kawo daga wanki cikin wardrobe. Mami ta yi sallama ta shigo dakin. A hanzarce Safah ta dago kyawawan idanunta ta dube ta. Kallo daya za ka yl mata ka san cewa cikin damuwa take, damuwa mai tsanani.



Mami ta balla mata harara ta ce, ““Taso muje”’.

Ta mike babu kuzari ta bi bayan Mamin har falon Daddy. Jikinta a matukar sanyaye, don ta tabbata Mami ta fasa kwan.



Daddy yana ta aiki cikin takardu da farin gilashi a idanun shi lokacin da suka shigo.



Ya janye takardun gefe ya kuma cire gilashin ya bi Safah da kallo a lokacin da take zama a carpet. Kallo daya ya yi mata ya karanto matsananciyar damuwar da take ciki. Don duk ta zabge cikin kwana daya kacal.



In banda alkawarin da ya yi, da matsayin Imam a wurinsa, da ba abinda zai hana shi baiwa wannan soyayyar goyon baya, ba ya son Zahraddeen ya kubucewa gidansa, don haka ne ya yanke shawarar wanke Marwah ya ba shi in har ya amince. Ya tabbata ahankali zai sota, sabida tanada nata kualities din itama. Duk da ya san ita din mai dagawa ce (ba kamar Safah ba), amma abu kKadan yana tankwara ta.

Sannan ba zai taba dauke alkawarin Imam ba, sai in har shi da kansa ne ya ce baya yi, wanda ya san har abada hakan ba za ta faru ba.

*************************⬇**********************
************* Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > [email protected]

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels



Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************


Ya kai duban shi ga Hajiya Zainab ya ga yadda ta hade fuska ta yi murtuk, Sai ya yi murmushi ya ce.



‘A lokuta da dama ku mata kuna bani mamaki, kina kin Zahraddeen ne saboda kawai yana karkashi na. Ba kya duba asali, halayya, addini da dabi’a.



Manzo (S.A.W) yaron Nana Khadija ne, kuma ya aure ta, ta kuma so shi saboda nagartattun halayensa da amanarsa.



Ba za ki yi la’akari da wannan ba ki kuma duba cewa soyayya hadin Allah ce, ba yin mutum ba?”



Ya maida duban shi ga Safah, wadda kalaman mahaifinta ke sanyaya mata zuciya, har ta soma hango alamun nasara cikin al’amarin ta.



Idanunta suka cicciko ta ce,



“Don Allah Daddy ka bawa Mami

hakuri, ina son Zahraddeen shima yana so na. Mami Zahraddeen ma mutumin kirki ne wallahi.



Ni ban ce bana son Ya Imam ba, amma bana yi mishi soyayya ta aure, Zahraddeen nake so Mami ba zan iya auren Ya Imam ba.....”



Ai kuwa ta kara harzika Mamin, daga dan sanyin data yi da nasihar Daddy, ta buge bakinta ta ce,



“Ashe baki da kunya Safah? Ni kike gayawa kina son wani bayan Da na da na raina na yi mishi tarbiyyar da nake so? A gabana kike cewa ba za ki iya auren Almustapha........ ”



Sai ta soma kuka,



“....Tunda ka daure mata gindi ku tozarta alkawari, shi kenan zan bar muku gidanku, don bani da idanun da zan dubi Imam, alhalin tana auren wani can. Ka aura mata duk wanda kuke so...”



Daddy shiru ya yi yana kallon su, ya dubi Mami da har ta kai bakin kofa ya ce, “Zainabu”’.

Sai ta dakata, amma ba ta juyo ba.



Ya ce, “Kin ji hukuncina ne kamin ki yanke naki hukuncin? Dawo_ ki zauna’’.



Ta koma ta zauna.



Ya ce, “Ba tsoron ki nake ji ba, ba kuma so nake in yi miki abin da kike so ba, illa nima na san muhimmancin alkawari, kuma ni da bakina na yi wannan alkawarin ba ke ba.



Don haka na yanke cewa zan baiwa



Zahraddeen Marwah....”



A razane Safah ta dago ta dubi Daddy. Ya girgiza mata kai ya ce, “Ki yi hakuri Safah, gara ka auri wanda ke sonka, a kan ka auri wanda kake so!. Bana kin al’amarin ki da Zahraddeen, ko kadan bana ki, sai dai ba zan iya daga alkawarin Imam a kanki ba. Na yi kokarin neman mafita mafi maslaha na kasa sai wannan din. Wato bana so Zahraddeen ya kubuce mana.



Ki sowa ‘yar’uwarki abin da kike sowa kanki. Ki yi min alfarma Safah

in cika wannan alkawarin nawa, ni kuma in yi miki duk abinda kike so a duniya. Alfarmarki nake nema, Safah, zan samu?”



Kuka ya _ci_ karfinta, tausayin mahaifinta ya lullubeta, ganin yadda ya karyar da murya ya kwantar da kai yana rokonta kamar ba shi ya haifeta yayi ta wahala da ita har ta girma, ya kawo Zahraddeen din cikin rayuwarsu har ta ganshi ta ji tana so. Ta ce cikin rishin kuka,



“Ka yi duk yadda kake so da mu Daddy....har abada mu masu biyayya a gareka ne. Na yarda da hujjar ka. Na yi maka wannan alfarmar Daddy....” Ta ci gaba da kuka a hankali.



Zuciyar Daddy ta karye, ya ce,



“To amma Safah, kukan na mene ne haka? Kukan ki, na nuna min cewa..... na zalunce ky’.



Ta yi saurin toshe bakinta da mayafinta, ta hadiye kukan da karfi ta ce,



“Babu zalunci tsakaninmu dakuDaddy, sai kauna marar misali, kai Allah Ya baiwa ragamar zaba mana mijin aure.



Matsalata yadda zan lallashi zuciyar tawa, ta hakura, ta daina_ son Zahraddeen, ta amince da hukuncin ka Daddy....”



Ya yi murmushi ya ce,



“Da dai ba Almustapha da Zahraddeen zan aura muku ba, shine zan tsaya ina lallashin ku.



Amma na san hannun da zan bada ku, hannu ne da ba zan taba yin dana sani



ba”



of Ok Kk

Y



adda Zahradeen ya kwana bai runtsa ba, haka Safah ta kwana tana juyi a gadon ta. Inda duk ta _ juya maganganun Daddy ke yi mata kuwwa a kwanya.



Ta yarda ta saduda ta amince Zahraddeen, ya haramta gare ta, soyayyarsu ta zama mafarki mai dadi, irin wanda dan adam kan yi, ya farka yana mai cizon yatsar kasancewarsa reality, tunda har Daddy ya yi wannnan hukuncin. Dreams _§$are conceibed, but not all dreams are born alibe. Some are aborted. Others are stillborn!

Ta tuno da kalaman noble - laureate - Zaynab Alkali.



Ta juya kallon ta ga _ gadon ‘yar uwarta Marwah, barcin ta take cikin sukuni da alama ba ta da matsala a rayuwa. Kuma bata san menene SO ba.



A ganin ta yau ba mai sa’a a duniya kamar Marwah, tunda bata taba dandana zakin so ko dacin sa ba (a tsammaninta). Gashi dai ta fita rawar kai, amma bata taba yin kankanbar sanya kanta cikin soyayyah ba, balle ta zo ta zame mata ciwo mai kama da cancer; ; it starts from one cell, and spread to other cells, tunda ta faro ne daga zuciya kawai, amma ta kurda har cikin kashi da bargo, jijiya da jinin jiki, har ma da ‘nerbous system’ bata tsaya anan ba, saida ta cigaba tayi attacking sukuni da farin cikinta. Wayar ta dake karkashin filonta ta soma ruri cikin tune din da ta tabbatar Zahraddeen ne. Ta yi har ta tsinke ta

kasa dauka, don ba ta san me za ta ce da shi ba, zai kara luguiguita zuciyarta ne kawai.



Ta yarda ta amince tunda har Daddy ya yi furucin aure tsakaninsa da ‘yar’ uwarta da suka fito duniya a tare, suka sha nono daya, to ta yanke duk wata alaka ta soyayya dake tsakaninsu, da karfin tauhidi ba da nata karfin ba.



Ya kira ya fi sau goma amma ba ta dauka ba. A karshe ma kashe wayar ta yi gaba daya, ta kifa kanta cikin filonta, ta lumshe ido cikin halin tausayin kanta.



Don Zahraddeen ba abin tausayi bane a ganinta, tunda anyi masa toshiyar baki da cancadediyar budurwa da ta fi ta kyau mai daukar hankali.





“To kema ai anyi miki toshiyar bakin da zankadeden miji na nunawa sa’a, na fita tsara, na nunawa sarki........, wanda da ana likawa da zaki iya likawa a goshi, kiyi tinkaho da zamowarsa miji a gareki, wanda ba

don jinin ‘yan uwantaka ba, da ba abinda zai yi dake inda a hanya kuka hadu, a mataki da matsayin rayuwa irin nashi”



Wani bangare na zuciyarta yace.... “Kayya! Ba a nan take ba!!!”.



Itama ta yi gaggawar kalubalantar zuciyar tata da cewa,



“...soyayya yin Allah ce, ba _ yin mutum ba. Ba ruwanta da_sura, nasaba, asali, matsayi, ilimi ko mukami. Zahraddeen take so, kuma a halin yanzu ta hakura da shi tunda ya



zama rabon ‘yar’ uwarta. 2K OK 3K Kk



A ZARIA



Har karfe goma na safe, Zahraddeen bai fito ya gaishe da Inna Binta ba, kamar yadda ya saba in har yana gidan.



Inna ta ce da kanwarsa Rabi’a ‘yar kimanin shekaru goma sha uku,



“Anya lafiya har yanzu Yayan ku bai fito ba?”



Rabi’a dake tuyar masa ta tsame

hannun ta tana wankewa_ cikin tukunya ta ce,



“Bari in je in dubo shi’.



Nura ya ce, “Yau da asubahi ko masallaci bai je ba’.



Inna ta damu sosai, ta ce, “Bar min tuyar tashi jeki ki gano”’.



Ta mike bayan ta wanke hannun ta nufi sashen Yayan nasu.



Ta kwankwasa ta yi sallama bai amsa ba, ta sake daga murya ta yi sallama amma shiru. Don haka ta murda marikin kofar, anyi sa’a bai sanya mukulli ba.



Ta shiga dakin nan ta hango shi can tsakiyar gado kudundune cikin bargo yana ta rawar dari. Ta karasa ta ce, “Yayanmu lafiya har yanzu baka fito ba?”



Cikin dasasshiyar murya ya ce, “kara rufa min bargon can Rabi’a sanyi nake ji”.



Ta ce a raunane, “Sanyi Yaya? A wannan uban zafin da ake zabgawa? Ko dai baka da lafiya?”

Ya kasa ce mata komai, sai ya lumshe idonsa. Ta karaso ta daura hannun ta a goshinsa, zafi rau! Ta taba wuyanshi kamar an yarfa mishi wuta.



Da sauri ta fita tana gayawa Inna Binta. Tare suka dawo dakin har da Nura, Inna ta zauna a gefen shi duk ta rude.



Ta ce, “Ka san baka da lafiya shine ko waya ba za ka yi ka fadi ba? Sai ka zauna kai kadai cikin daki?”



Ya yi shiru bai yi magana ba. Ta ce, “Ina mukullin motar ku je asibiti?’



A nan ne ya yi magana da kyar, ya ce,



“Nura samo min paracetamol kawai, ba sai mun je asibiti ba, ‘its just a tension...”. Nura ya juya ya fita.



Inna ta ce da Rabi’a ta hada mishi ruwan wanka, ita kuma ta fita ta kawo mishi abin kari, kunun gyada da masa mai laushi da zafinta da miyar ganye, taji naman kaji zuku-zuku.



Bayan ya fito daga wankan Inna da Rabi’a suka sa shi a tsakiya da roko da lallashi, Inna ta samu ya ci kadan.

Nura ya dawo da maganin Rabi’a ta dauko gorar ruwan ‘faro’ mara sanyi a karamin firjinsa, ta tstyaya a tambulan ta mika mishi.



Ya karba ya sha, ya koma ya jingina da gadonshi ya runtse idonsa. Nura da Rabi’a suka fita, amma Inna ta kasa tafiya ta barshi.



Ta ce, “Ni kuwa tun jiya da ka shigo Sai nake ganin kamar akwai abin da ke damun ka, ka boye baka gaya min ba”. Ya bude idonshi a hankali yana kallon Inna, ya tabbatar da cewa Inna mutum ce mai kyakkyawan tunani da hangen nesa.



Ba shi da abokin shawara a duniya da ya wuce Innar_ shi, tana _bashi Sshawarwarin da idan ya bisu yana ganin yakini a ciki.



Amma ya rasa dalilin shi na kasa gaya mata damuwar shi wannan karon. A karshe ya yanke shawarar gaya mata komai, ko babu komi za ta ba shi shawara a kai, ya san abin da zai ce da Alh. Aliko idan ya tambaye shi

shawarar da ya yanke cikin kwanaki ukun da ya diba mishi. Don wallahi bai san me zai ce da shi ba.



Ya yi ajiyar zuciya ya dubi mahaifiyar shi Inna Binta, damuwa_ karara kwance a bamalliyar fuskarta, amma ba ta katse mishi hanzari ba har ya yi tunaninshi mai isar shi.



Ya maida idanun shi ya lumshe ya ce, “Inna kin san ‘yan biyun Alhajinmu ko?”



Ta ce, “Safah da Marwah da ka ce suna karatu a nan Zaria?”



Ya ce, “Eh, su. To ina son daya, mun dade muna soyayya, to amma jiya Alhaji ya yi kirana ya tambaye ni abinda ke tsakaninmu, na gaya masa ina son aurenta, shine yake gaya min cewa akwai alkawarin dan’uwanta a kanta, wanda ni bata taba gaya min ba, amma ya bani Marwah idan na amince sati mai zuwa in kawo sadaki ya daura mana aure.



To Inna kin ji damuwa ta, Safah nake so ba ‘yar’uwarta ba. Amma ba zan

lya badawa Alhaji kasa a ido ba, don na san karamci ya yi min na kuma san yadda yake kauna ta.



Ya kuma gaya min cewa yana son hada zuri’a dani ne kawai, gashi ni kuma bana son ta ‘yar’ uwarta nake so. Idan na aure ta na zalunce ta, na kuma zalunci kaina, tunda bana sonta, itama ba so na take yi ba’.



Inna ta yi shiru tana tuna alherin Alhaji Aliko gare su tun ranar da Allah ya hada shi da Zahradeen. Ta kuma tuno nata burin na son aurawa Zahraddeen jikar Yayarta Anisa wadda ke karatun karamar sakandire a halin yanzu a makarantar Sarauniya Amina.



Amma kamar yadda Zahraddeen ya ce ne ba za su iya watsawa Alh. Aliko kasa a ido ba, idan Anisa matarsa ce ko nan gaba sai ya aure ta, tunda sa’ar Rabi’a ce, shekarunta sha uku kenan. To amma su auro ‘yar Alhaji Aliko su ajiyeta a ina? A dan gidansu da bai fi dakin injin wutar lantarki ga ‘yar Dan

Kasa ba? Duk da cewa Zahraddeen yana gini a cikin Kaduna, amma tana tsoron anya? Ba za ta fi karfinsa ba? Sai kuma_ tayi wani tunani, Zahraddeen baya daga _cikin sakarkarun maza, namiji ne sak, da ke tsaye kan kafafun shi. A karshe ta yi tunanin komai na Allah ne, kuma matar mutum kabarinsa. Ta dubi Zahraddeen ta ce,



“Alh. Aliko ya fi karfin komi a gurinmu, in har muna da shi, kuma muna da iko.



Shi mai saka ka yi aure ne ko da ba diyar cikin shi zai baka ba. Sannan duk mai son ka, saboda halayenka, ba karamin masoyin ka bane. Balle wanda zai yi maka kyautar diya sukutum ba tare da la’akari da kai wane ne ba, wato mene ne matsayinka gare shi?



Saboda haka sanya hannu bibbiyu ka karbi kyautar uban gidanka, ka yi fatan Allah ya hadaka da alherin dake tare da ita, ya rabaka da sharrin dake

gare ta.



Sau da dama abin da muka kallafa rai ga son shi ba alheri bane a gare mu, wanda bama so din shine alherin. Amma ka yi istikhara har zuwa lokacin da ya diba maka, nima zan taya ka. Idan ka ji zuciyarka ta kwanta da al’amarin to akwai alheri a cik1’. Shine kuma za ka kwantar da kanka ka hau ciwo a kan ‘yar wannan magana da ba ta fi karfin ayi aiki da hankali da tunani wajen warware ta ba?




A’a, bana son hakan. Tashi ka shiga hidimominka kaji Deeni?”’. Zahraddeen ya yi murmushi, ya yunkura ya mike. Har wani sabon kuzari ya ji. Inna ta ce,



“To ko kai fa?”



Kwana uku Zahraddeen da Inna Binta suna ta istikhara tare da neman zabin Allah, idan auren diyar Alh. Aliko alheri ne a garesu, to Allah Ya tabbatar. Idan babu alheri Allah Ya wargaza ba tare da ran kowa ya baci ba.
Cikin jerin gwanon masu saukowa daga matattakalar jirgin Birgin Atlantic har da Engineer Imam Zubair Dan Kasa. Sanye yake da jibgegiyar bakar kwat mai kauri wadda_ tsayinta har gwiwoyinsa, ya saya kwayar idanunshi cikin bakin space saboda hazo.



Dogon wandon ‘Armani’ ne baki a jikinshi, a ciki kuma ‘American-Suit’ ne launin toka-toka wato = grey. Saukarsu kenan a filin jirgin Heathrow din London daga Glasgow, inda yawancin fasinjoji a nan za su sauka (transit). Inda jirgin zai sake lodin masu tashi zuwa Ikkon Najeriya a asubahin washegari.



Imam bai gayawa kowa cewa zai zo ba, haka nan zuciyarshi ta tunkudo shi ga son tahowa saboda yawan mafarkemafarken da yake yi a dan tsukin duk

a kan Safah.



Don haka Mami na kicin ta jiyo ihun Aunty Shahida wadda ita ma saukar ta kenan daga Benin inda ta kammala bautar kasar ta.



Da sauri Mami ta fito da ludayin miya a hannun ta, a daidai lokacin da Surajo mai yi musu wanki ke aje manyamanyan jakokin da Imam din ya zo dasu.



A lokacin yana bangaren Hajiya Maama bai idasa shigowa falon gidan ba. Murnar tsohuwar ta kasa boyuwa ta ce, “Oyoyo! Maigidana, yanzu kake tafe shine ko waya balle in yi girkin karbar ka?”



Ya zauna kusa da ita har kafadunsu na gugar na juna, kaunar da yake yiwa Kakarsa Hajiya Maama, Allah kadai Ya san iyakarta, ya ce,



“Kai, tsohuwar nan da ran karfe kike, kin ki margayawa mu samu mu Ci gumba, na ce bana yi da ke, baki yi min ba amma kin nace sai ni”.



Ta kai masa duka da maficinta ya

kauce yana yi mata murmushi, wanda da ka gani ka san na kauna da kewa ne ziryan.



Ta ce, “Yo borancin me zan yi? Tunda wadda ka kallafawa ran ba son ka take yi ba, ai ba zan ji tsoron yin kishi da ita ba.



Ina nan za ka zo ka same ni kana ‘yar murya idan ta wulakanto ka”.



Ya sunkuci kwanon furar ta ya yi waje dashi, shi da Shahida suna yi mata dariya. Saidai kuma wannan kalma da Hajiya ta ambata BA SON KA TAKE YI BA ta taba zuciyar Imam ba dan kadan ba.



Marwah ba ta gidan ta je shopping sai ‘yar mulkin ita kadai a falo tana kwance cikin kujera da littafinta a hannu, ko karatun take ko tunani take oho, ita ta barma kanta sani.



Wani irin lallausan kamshi da mutum daya rak ta sani da shi a duniya wato na turaren ‘burberry - brit’ cakude da ‘akba-amara’ ya bakunci hancinta. A lokacin da ya russuna daidai kanta ya

zare littafin daga hannunta.



Ta juyo tana kallon shi da idanuwanta narai-narai da hawayen dake son zubowa, don a ganinta (mai takurawa rayuwarta ya zo), ba ta ce komi ba.



Shi kuwa murmushi ya yi, yana mamakin yadda Safah ta kara girma, ta kara kyau, ta kara gogewa. A tsayin watanni tara da ya yi bai ganta ba, bai ji muryarta ba.



A haka Mami ta fito kicin tana kallonsu basu ankara da ita ba. Da sauri ta koma kicin din tana mai tasbihi ga Allah a zuciyarta.



Ba ta taba ganin perfect-match na miji da mata da suka dace da juna irin Safah da Almustapha ba, ga _ shi kamarsu daya, kamar an tsaga kara. Haske kawai ya fita. Hasken ma bana fata bane, na zaman kasar sanyi ne kawai.



Safah ce ta fara dauke idonta sannan ta hade fuska sosai ko kalmar sannu da zuwa da take mishi a da, yau bai samu ba. Karshe ma mikewa ta yi tabar mishi falon.Ya yi dariya ganin yadda ta cika, ta yi tam, kiris take jira ta fashe.



Shahidah kuwa dake gefe tana kallon su ciwo ta ji sosai na halin ko in kula da Safah ta nunawa _ dan’uwanta, wanda ya taho tun daga_ tsakiyar duniya don ya gansu, abin mamaki akan

Please Login or Register in order to submit comment