Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Zahraddeen ta goyata zuwa wajen mota ana ta yi mata guda, suka dauki hanyar Zaria.



Basu isa Zaria ba sai karfe goma na dare, ‘yan’uwan Zahraddeen da mahaifiyarshi suka yi musu tarba ta mutunci da karramawa.



Kai tsaye dakin Innar Zahraddeen aka nufa da amarya. Ta rungume Marwah tana ta yi mata addu’a, aka bata amanar amarya ta ce ta karba, Allah Ya taya ta riko.



Daga nan ta yi musu jagora zuwa sassan Zahraddeen dake cikin gidan. Su Shahida, Badar, Rahima da sauransu duk a nan za su kwana. Tsarin flat din ya yi musu, ya basu sha’awa sosai; bai cika girma ba, ‘self-content’ ne.




Karfe sha biyu na dare kowa ya

kwanta, sai Marwah dake ta kuka cikin mayafinta, don a ganinta Daddy ya gama kashe mata rayuwa, har kukan ta ya tashi Shahida.



Ta mike ta zaunaa a gefen gadon ta ce, “Kukan nan ya isa haka Marwah, ina so in san damuwarki? Tunda abin nan dai anyi ya riga ya tabbata, ya kamata ki hakura haka nan ki karbi mijin da Allah Ya baki. Shin ma mene ne aibun Zahraddeen don Allah?”



Ta ce, “Ni ina ruwana da wani rashin aibunsa, ni dai kawai ba zan iya zama da yaron Babana bane, dama wani ne daban sai in hakura.



Dubi dan akurkin dakin da aka ajiye ni, sannan an kawo ni gida cike da mutane duk ‘yan kauye dasu, ana nufin a cikin su zan yi rayuwa?



Ke yanzu idan aka ce ki auri yaron Daddy za ki yarda ne? Sai ni da aka raina ma wayo? Ko nima bagidajiya ce irin Safah?”



Shahida ta yi murmushi ta ce, “Ki iya bakin ki Marwah, arziki na Allah ne,

kuma dare daya Allah kan yi Bature. Kuma ni miji in dai kamar Zahraddeen ne Daddy ya zabo min babu abinda zai hana ni in yi mishi biyayya, ba ma’aikacin Daddy ba ko masinjansa ne, in dai zai iya ci dani ya sha dani ya biya min bukatar aure, shi kenan.



Ki rage daukan duniya da fadi, kuma ki daina daukar rayuwa da zafi. Ki daina alfahari domin halin la’anannu ne.



Daddy gata ya yi miki domin ya kawo ki inda za a rike mishi ke cikin mutunci da amana, inda ba zai kasance cikin zullumin a hannun da kike ba, inda ya tabbatar ko bayan ransa, ba za a tozarta ki ba”.



Da maganganun Aunty Shahida ta kwana suna juyi a kwakwalwarta. Mai jama’a ke gani a tareda Zahraddeen ne? Wanda ita bata gani? Me yasa Zahradden keda kima da farin jini haka duk da ba dan kowa bane? Haka

su. Rahima ma_ suke ta _ fade. Zahraddeen bai iso Zaria ba sai washegari da safe.



Yana isowa motocin abokanshi suka juya da su Badar, Shahida da sauran jama’a Kaduna. Ya rage daga ita sai halinta.



Ta zuba ido don ganin ta inda Zahraddeen zai bullo ta zazzage masa rashin mutuncin da ko shi kare ne dole ya maida ita inda ya dauko ta. Tuni nasihar Shahidah ta bi ta _ bayan kunnen ta.



Motsin bude kofa ta ji tare da sallama, Inna Binta ta shigo Rabi’a kanwar Zahraddeen biye da ita, suna dauke da ma’adanan abinci da jug mai rike zafi. Suka ajiye daga gefen ta, ta dube ta tana murmushi ta ce,



“Tashi ki ci abinci, tun jiya an gaya min baki ci komai ba”.



Ta bisu da kallo cike da haushi, ta ce, “Na koshi ne”.



Inna ta ce, “Ko kadan ne ki daure ki taba, zama da yunwa ba shi da dadi. In

kuma baki son wannan ki gaya min wanda kike so ayi miki’.



Ta juyar da kai ta tabe baki a ranta tana cewa, “Dube ku don Allah, local daku, kune za ku yi min wani girki in ci?”



Da ta ga Inna ba za ta tafi ba dole sai ta ci abincin, sai ta ce, “Zan ci anjima kadan idan na yi brush”.



Inna ta ce, “To ko ke fa? Ko akwai wani aiki da Rabi’a za ta yi miki?’



Ta ce a takaice, “Babu”.



Inna ta juya ta fita, ta ce, “Rabi’a zauna mana ki taya ta hira kamin Dini ya shigo”.



Wai an ce shimfidar fuska........ ta fi ta tabarma, don haka Rabi’a ta lura da fizge-fizgen amaryar tasu, wanda ita Inna ba ta kula ba, kasancewarta ba mai sa ido ba, don haka ta ce,



“Zan yi walha ne Inna, anjima in ya fita sai in dawo”. Suka juya suka fita. Ta jawo kulolin guda biyu ta bude, funkason fulawa ne, sinasir, masa, kisra da miyar ganye, ya ji nama zuku-zuku, daya filas din kuma soyayyen dankali ne da kwai.



Ta mayar ta rufe don duka babu irin cimar ta. Ta jawo jug din ta bude, kunun farar shinkafa ne mai kyan gani, fari sol dashi yaji madarar NIDO yayl shar, da gani wadda ta dama ta kware da damun. Da zafinsa abin sha’ awa.



Ta ja wani matsiyacin tsaki tsuuuu! Kamar zata tsinke halshen ta. Ta koma ta kwanta yunwa na cin ta, tana tuna barities na dining din gidan ubanta, tana cewa cikin ranta, kowa yana aure don ya ci gaba, amma ita anyi mata auren da za ta koma baya.



Ba ta san da tsayuwar mutum a kanta ba, haka nan ba ta ji takun shigowar sa ba, kasancewarsa mutum mai nutsatstsen taku. Wani sassanyan kamshi ne mai ratsa zuciya da bargo, na turaren ‘Dior Addict’ wanda ba yau ta fara jin shi ba, saidai idan Zahraddeen din bai shigo wuri ba, shi

ya bakunci hancinta.



Idonta a lumshe yake, sai ta sake lumshe shi sabida dadin kamshin, ba sabida farin cikin zuwan mai kamshin ba, sannan ta bude su a kan angon nata, wanda ke cikin ruwan madarar yadin filted dinkin Mohammed. Idanunshi rufe cikin dark spaces, don haka ba za ka iya karantar halin da kwayar idanunshi ke ciki ba. Fuskarshi kadaran-kadahan, babu tsana babu tsangwama, amma babu fara’a, don ya gama karantar yarinyar ‘yar rainin arziki ce da rainin wayau. A ranshi fadi yake, “zan daidaita miki sahu”.



Ya ce a hankali, “Kin tashi lafiya?”



Ta balla mai harara tana daga kwance, a fusace ta ce, “Da ban tashi ba za ka ganni?”



Ya yi murmushi ya ce, “Zamu wuce Kaduna ta-sani (gaida surukai da yi musu ban gajiya da abokai da angwaye ke yi a washegarin ranar da aka kai musu amare a al’adar hausa) ,

any problem?”



Ta hura hanci ta sake galla mai harara da dara-daran idanunta tamkar kwayar idanun sa fado, ta ce, “Na yi maka kama da ‘ya’ yan dake cikin matsala?” Ya juya yana cewa, “Wannan kuma rayuwarki ce”.



Har ya kai bakin kofa zai fita ta ce, “Ka ga malam, dakata, ka yo min cefane in girka abin da zan ci, ba zan ci wannan jagwalgwalon ba.......... ”



Ya wani irin juyo gabadaya ya dube ta, sannan ya kada kai ya fice ba tare da ya ce da ita komi ba.



Wannan ya fi komi bakanta mata rai, don so take ya kula ta su haura, ta samu hanyar yarfa mishi rashin mutuncin da za ya sake ta.



Amma kamar ya san takun nata ya ki kula ta. Ta lura shima miskilin kanshi ne, da bai dauki al’amarin mace a bakin komi ba.



Tunda suka hawo kan titi shi da Kutama zuciyar shi zugi take, zai

dauki komi amma ban da a raina mahafiyarshi.



Girkin Innar tashi ne jagwalgwalo? Ya yi kuta ya ce a fili, “Yarinya zan yi maganin ki, zan koya miki hankalin da baki da shi’.



Kutama ya ce, “Wace yarinya kake magana kai kadai kamar zararre?’’



Ya girgiza kai, “Barni kawai Kutama, ina jin lokacin daina aiki na da ‘Dan Kasa Holdings’ ya zo!”.



A gaggauce Kutama ya faka mota a gefen titi ya ce, “Me ya yi zafi Zahraddeen? Kowa na ganin ka lucky tunda ka zamo surukin Dan Kasa? Ka gama tsallake SIRADIN RAYUWA, ka gama samun duk wani ALHERI na rayuwa da dan adam ke burin samu. Ka bar TUNA BAYA...(lokacin kuncin talauci), haka kawai zaka jawo mana GIRMA YA FADI...... alhalin kai da arziki ana yi muku kallon ALKAWARI HAR BAYAN RAI, kada ka jawowa kanka ABARI YA HUCE... irinna’ Prof. Junaidu

Galadanchi, ka zamo mai YAKANAH akan diya mace, ZUCIYAR MUTUM....ita take jawo masa danaSani, me ya yi zafi har da hakan za ta faru?”



Idanunshi sun kada sunyi jajir ya ce, “Ina so in nunawa diyarsa da ke cewa BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE surukuta ta da shi, bata da alaka da arzikin sa. Na auri “yarsa ne don kaunar da yake mini, amma ba don kwadayin arzikinsa ba.



Daga yau ba zan kara aiki a karkashin wani ba, sai a karkashin gwamnati. Tunda hakan illa ne ga martaba da mutunci na a idon diyarsa. Idan zan yi yawo ‘naked’ (tsirara) ba zan kara aiki a karkashin Dan-Kasa ba.



Sannan ba zan taba sakinta ba saboda kaunar da nake yiwa mahaifinta. Idan za ta iya zama dani a matsayina na talaka ta zauna, idan ba za ta iya ba zabi ya rage nata......



Amma sai nayi mata saiti wallahitallahi. Yadda nan gaba bazata kuma

yiwa wani rainin arziki ba, wai don yana ci a karkashin mahaifinta....” Ahmad ya ce,



“Kada ka yi haka Zahraddeen, Alh. Alhaji Aliko bai cancanci wannan sakayyar daga gareka ba...... ” Lumsassun idanun shi ya_ sauke ahankali akan Kutama.... “Kutama sai in zauna in zama mijin hotiho da lafiyata, da kuruciya ta, da ilimina, da martaba ta da komai? Ko ko sai in zauna in zama mijin Hajiya don kawai a ce ina auren diyarsa?



Dama a ce yarinyar ta san mutuncin mutane ne kamar ‘yar uwarta da da sauki, to ba ta san wannan ba”’. Kutama ya ce, “Wai me ta yi maka ne?”



Ya ce, “Ban sani ba, tunda duk bayanin nan da na bata lokaci na nayi maka baka fahimci komai ba”.



Ya ce, “Na fahimce ka mana, sai dai bana bayan ra’ayinka.



KUDI! Sune mutuncin da martabar my friend. Ya fada yana bubbuga

kafadunsa.



Kada zuciya da shirmen mace yasa ka yi saki-na-dafe, ka san dai yadda yanayin kasar tamu yake a yanzu. Takamar ka shine kana da kwalayen ilimi, to akwai wadanda suka fi ka fal a kasar nan amma suna nan zube ‘unemployed (babu aikin yi). Zahraddeen wulakancin da rainin yana tsiro ne? Ko yana toho a jikin dan Adam?



Balle nawa yarinyar take? Da ka dora mata nauyin kirjinka ka kalallame ta da kalaman soyayya shi kenan za ka mantar da ita shirmen ta. Kai fa ‘giant’ ne Zahraddeen. Irin mazan da baku da yawa a duniya. Wallahi ba irin ku ne mace ke cewa bata so ba, duk abinda take takama dashi kuwa; kyau, ilmi ko arziki.



To kai matsalata da kai ‘fadin rai’ da ‘ji da kai’. Ko da yake YEEESSS.....! Kana da abubuwan da za ka yiwa diya mace yanga dasu ko ‘yar shugaban kasa ce ba ‘yar Aliko ba.

To ka yi amfani da wadannan makaman da Allah ya baka, ka yi yakin neman soyayyarta dasu ku zauna lafiya.



Amma fa ra’ayina ne wannan nake gaya maka, don gaba nake da kai na fi ka edperience a kan rayuwar yau. Ban ce lallai ka yarda dani ba, amma ka yi tunani”.



Ya tada injin motar suka hau kwalta suka ci gaba da tafiya.



Zahraddeen kallon sa kawai yake, yana mamakin matacciyar zuciya irin ta al’umma, sabida kudi sai su sarayar da martabarsu da mutuncin da Allah Yayi musu, Ubangiji (SWA) da kanSa Yace “Na girmama bani — Adam!” sai bai ga amfanin ci gaba da magana da mutum mai karamin tunani da kwadayi irin sa ba.



Don haka ya ja bakinshi ya yi shiru. Har suka shigo Kaduna bai bari sun kara yin maganar ba.

Nan suka hadu da sauran abokansu suka je wa Daddy Ta-sani. Daddy ya yi murna sosai har ‘yar kwaryakwaryar walima yasa aka hada musu. Zahraddeen ya tambayi Imam Daddy ya ce ya je Abuja kan shirye-shiryen komawar shi, don gobe zai tafi.



Suka shiga suka gaida Mami, fuskarta ba yabo ba fallasa ta amsa musu, Ssannan ta kawo atamfofin English masu dauke da hoton Safah da Marwah da angwayen nasu da aka bugo daga Ghana na taya murnar aure ta ce su kai wa matansu, da botikai cike da kayan gara su alkaki, nakiya, dubulan, cin-cin, bakilawa ta basu. Duk da ranta bai son Zahraddeen da auren diyarta, amma ya ya Za ta yi? Alhaji Aliko ya fi karfin gidansa. Zahraddeen ya riga ya zamo bangaren iyalin ta. Basu bar gidan ba sai bayan la’asar, motocin kayan gara suka mara musu baya.



Inna Binta na alwalar sallar magariba aka soma shigo mata da buhunhuna da

katon-katon da bokitai tare da jarkokin mai iyakar ganinta.



Duk fadin tsakar gidansu cika ya yi taf, tun tana salati har ta yo lullubi ta fito tana ce da masu saukewa “Ina zan kai wadannan kayan? Ku barsu haka nan’.



Basu bari ba sai da suka gama saukewa tsaf sannan suka kada kan motocinsu suka tafi, ko tukuicinta basu tsaya karba ba.



Zahraddeen na shigowa ta soma fada ta ce, “Lallai yasa a maidawa Alh. Aliko wadannan buhunhunan ita ba ta da yadda za ta yi dasu, sai ka ce siyar musu da ‘yar ya yi?”



Zahraddeen shiru ya yi kamar ruwa ya cinye shi, don ya san halin Alhajin nasu, yanzu idan ya ce a mayar zai yiwa al’amarin wata fassara ta daban ne.



A nan ne yake gayawa Inna kyautar gidan da ya yi masa, da ya ce ba zai karba ranshi ne ya baci, kuma bai fasa kyautar da ya yin ba.

Har karfe sha biyun dare yana tare da mahaifiyarshi suna ta hirarsu irin ta da da mahaifi. Sai da Rabi’a ta shigo za ta kwanta ne Inna ta ce ya tafi haka dare ya yi, ita ma barci take ji.



Sannan ne ya yi mata sallama ya tafi. Ya yi amfani da makullanshi ya bude kofar glass (slidingdoor) ta falon sassanshi ya shiga falon.



Babu kowa babu motsin komai sai hucin split wadda ta ni’imta falon sosai kamar babu wani mahaluki a cikin sassan saboda yadda falon ya yi shiru. Ya shiga wara idanu a hankali yana kallon yadda aka tsara falon kamar kana falon Alh. Aliko sabida tsari ba tarkace ba.



Dakinshi ya nufa kai tsaye ya sunce ya shiga toilet ya sakarwa kanshi shower na ruwa mai sanyi. Ya fito yana tsane kai da karamin tawul yayin da babban ke daure a kugun shi.



Ya dubi kanshi cikin madubi, ya yarda cewa shi namiji ne mai surar MAZA irin wadanda basu da yawa a cikin

al’umma. Kamar yadda Kutama ya fada.



Ga koshin lafiya da kuzari, sannan da dakakkiyar zuciya. Kwakwalwar da kullum a shirye take da daukar duk abinda aka koyar da ita. Idan har yana da wadannan ilhamomin, mai zai hana ya ci gaba da yunkurin neman ilimi da fafutukar rayuwa? He has to applaud the idea that, Indibidual is an actor seeking for goal......



(and these goals are endless/limitless) wato basu da karshe.



In haka ne mai zai sa ya zauna diya mace na yi mishi kallon raini saboda kawai yana ma’aikacin § Babanta? Namijin da ya san ciwon kansa, ba mace ce kawai a gabanshi ba, bai dauketa a matsayin jigon rayuwa ba, sai dai wani bangare na rayuwar namiji, wanda amfanin nata bangaren bai zuwa ma sai ana cikin kwanciyar hankali (when the goals are achiebed). Ba ta san cewa shima ba sonta yake yi ba, ya aure ta ne kawai don ya darajja

kaunar mahaifinta gareshi? Gaskiya ne da ‘yan magana ke cewa ‘Allah daya gari bam-bam’, kuma ‘kowa da halinsa’, sannan ‘kama da wane bata wane’ halinta ba daya bane da na ‘yar’uwarta ba! Ta kowanne bangare basu yi tarayyah ba, to ya zaiyi? Sai hakuri da kaddara. Domin cikar imani. Har ya yi shirin kwanciya ya yi light off ya tuna cewa duk = rashin mutuncinta hakkinsa ne ya dinga bincikar lafiyar ta.



Ya ja dogon tsaki ya safko daga lallausar gadonshi ya zura ‘bed shoe’ ya zura farar jallabiyyarsa, ya murda kofa ya fito ya nufi dakin nata. Sallama ya yi tare da murda kofar ya shiga. Dakin duhu didim, sai dai hasken fitilar barci koriya. Ya dauka zai samu ta yi barci a makeken gadon ta, sai ya samu akasin abin da ya yi zato.



Tana bisa darduma daga can kuryar dakin ta yi nisa cikin sujjadarta, cikin

yalwataccen hijabin sallah. Ya rufe kofar ya koma ya jingina da kofar a hankali, idanunshi a runtse.



Sai kuma ya bude ya dubi kulolin dake gefensa wadanda ya san na Inna ne. Na rana ya tadda na safe, na dare ya tadda na rana.



Ya sunkuya yana bubbudewa yana haskawa da wayarshi, ko cokali daya ba a diba ba, wanda ke nufin, har zuwa yanzun ba ta sa komai a cikinta ba, saboda tana kyankyamin mahaifiyarshi.



Da kanshi ya kwashe filas-filas din ya kai kicin. Ya samu leda ya juye duk abincin. Ba zai so Inna ta gani ba don ranta za ya sosu.



Ya yankewa ranshi gobe zai yo mata cefanen, kada ta kashe kanta da yunwa a daura mishi jakar tsaba, kaji su bishi. Dakinshi ya koma ya sauya riga. Ya dauki makullin mota ya fita.



“Yahuza Soya Spot’ ya nufa ya sayo gasassun kaji biyu da robobin ‘fresh milk’ din ‘Oldenburger’ masu sanyi,

ya zuba a gaban motar ya dawo gida. Yadda ya barta haka ya dawo ya same ta, wato deep in sujjadah. Ya tambayi kansa me take roka ne haka? Bai yi zaton ‘ya’yan gata irin ta masu ji da kansu da takama da iyayensu suna da bukata ba”.



A gefen ta ya ajiye ledojin ya juya ya fita. Sai da ya koma daki duk haushin kansa ya kama shi. Me yasa ya sayo mata? Me yasa zai biye mata ta raina abincin gidan su? Wanda kuma hakan raini ne ga mahaifiyar shi karara. Nan zuciyar shi ta tunatar da shi cewa “hakkin ka ne ka ciyar da ita, ba hakkin mahaifiyar ka bane ciyar da matar ka”.



Da wannan ya kwanta ya lumshe ido, yana kukkullawa yana kwakkwancewa, game da future din rayuwarshi ta gaba, da kuma matakan da zai dauka wajen daidaita sahun Marwah Aliko Dan Kasa, ta san wane ne talaka? Ba abin wulakantawa bane. Kowa da ka gani a duniya ba

wulakantacce bane duk yadda yake, saidai in shi ya wulakanta kansa. Cikin darajojin da Allah Ya yiwa dan adam, babu zancen kudi a cikinsu. Wulakantaccen dan adam shine wanda ya dogara da wani, ba da Allah ba. Wanda yake ganin in ba wannan dan adam din da ya dogara dashi ba, to bashi da madogara. (Allah Ka bamu wadatar zuci irinta Zahraddeen ameen, Takori)



AImustapha Zubair Dan Kasa (Imam), ke sharara gudu a kan titin da zai dawo da kai Kaduna daga garin Abuja, yana daidai ‘zuma rock’ cikin motarshi banguish tun farkon shigowarta, a wannan lokacin banguish bata zo Najeriya ba, zai iya kiran kansa mutum na farko, dake yawo a cikin ta a Abuja gabadaya. Yana gab da shiga garin Minna wayar Mami ta shigo, ya yi amfani da hannun daman shi wajen amsa wayar yayin da yake tuki da na hagun cikin kwarewa da gwaninta.



Mami ta ce, “Ka taso ne?”



“Har na kusa isowa Minna Mami, nan da ‘two hours’ insha Allah zan iso”. Ya kashe wayar tare da kara taka totur din motar sosai, gudu yake kamar zai tashi sama. (Tukin Mota), na daya daga cikin abubuwan da ke sanya shi nishadi. Har dai ace motar mai budadden sama ce.



Sanye yake da shadda coffee kala kanshi babu hula, wanda hakan ya bayyanar da tulin kwantacciyar sumar kanshi baka sidik mai santsi da sheki. Yana jin kansa cikin wasu mutane kalilan masu sa’ar samun duk abinda suke so a rayuwa, tunda Allah Ya mallaka mishi abin da rai da zuciyarshi ke so, tsayin shekaru goma sha tara. At last, ya samu. Don haka ba shi da abin da zai ce da mahaliccin shi sai godiya, da neman dadin

falalarsa da ni’imarsa.



Karfe shida da rabi ya shigo garin Gwamna, don haka kai tsaye alwala ya yi a harabar gidan ya wuce masallaci don samun = jam’in maghariba.



Mami ta kwankwasa kofar dakin da ta ji an kulle da makulli, Safah ta zo ta bude, sanye take da ‘shirt’ da wando samfurin polo kalar ruwan zuma, ta matse gashin kanta daga tsakiya. Mami sai ta ga ‘yarta ta kara kyau na ban mamaki. Ko da yake hasken amarci daban ne, ta yi murmushi ta ce, “Mene ne na sanya mukulli a kofar?” Ta ce, “Haka nan’’.



Mami ta sake yin murmushi, ta san don wanda ake kulle kofar. Tunda aka tafi kai Marwah Zaria tun shekaranjiya ko falo ba ta kara lekowa ba.



A dakinsu take hidimominta ta kulle kanta ba ta son yin mu’amala da kowa. Daga Mami har angon babu wanda ke shiga sabgarta, shi ba ya garin ma tun wayewar garin litinin ya

wuce Abuja, inda yake fafutukar bisar ta da passport dinta da ya amsa wurin Mami.



Ta ce, “Fito maza ki tayani aiki, ai tunda Marwah ta tafi na san na yi rashin mai taimaka min a kichin”’.



Ta yi rau-rau da ido kamar za ta yi kuka ta ce, “Kai Mami ni bana tayaki?”



Ta ce, “Da yaushe da yaushe kike taya nin? Kin ga bana son dogon turanci wuce muje”’.



Haka tasa ta a gaba har kicin tana cewa, “In ban da Imam din wa zai iya zama dake? Ga kiwa ga son jiki, ga yawan kwanciya kamar mage, bakya um bakya um-um kamar_ wata jikakkiyar tsumma.



Ayi mace sai ka ce namiji, daga takarda sai biro? Ko huda-huda yana samun lokaci ya_ shiga _cikin ‘yan’uwansa ya yi mu’amala mai dadi dasu.



In bakya hutar da idanuwanki in kin tsufa za ki samu matsala dasu kin ji na

gaya miki’.





Ta rausayar da kai ta ce, “Nice zan tsufa Mami?”



Ta ce, “A’a, ba za ki tsufa ba tunda hurul-eeni ce?”



Ta yi smiling har wushiryarta da jerarrun hakoran’ suka fito. Ta taimakawa Mami suka hada abincin dare mai rai da motsi suka jera a dining, sauri take a gama ta gudu kada Imam ya zo ya same ta wanda take Allah-Allah ranar tafiyar shi ta zo ya bar gidan ta huta, don bata da masaniyar yaushe zai tafin.



Dan halak din kuma dan gatan Mamin sai ga shi ya shigo cikin takunshi na sassarfa ya shigo kicin din.



Daga bakin kofa ya tsaya yana kare mata kallo kamar bai san ta ba. Daga Mami har ita babu wanda ya san da shigowar sa, hirar su suke suna dariya. Sai da ya kalle ta son ransa sannan ya yl gyaran murya ya ce, “Mami wane delicious ake shirya mana ne? Irin wannan ‘aroma’ haka tun daga bakin get?”



Tana murmushi ta ce, “Duk naka ne, na san ka tunda ka bar gida ba za ka tsaya ka ci wani kwakkwaran abinci ba sai shirme wanda baya rike hanji’’. Ya yi dariya kadan ya ce, “Mami kina sangarta ni, sai na tafi inda bani da gata in yi ta ragaita.....”



Ta ce, “Ga shi kuma Allah ya baka makiwaciyar mata, ya ya za a yi kenan?”



Ya kai duban shi ga sashen da take, idanunshi a sanyaye, ta hade fuska ta yi murtuk kamar hadari, kai ka ce tunda aka halicceta ba ta taba dariya ba sai hura hanci take.



Ya girgiza kai ya ce, “A haka zan yi maneji Mami, an ce “da babu.....”



Ta karasa mishi “.....Gara babu dadi!”. Ita dai ba ta tanka musu ba, karewa ma ko inda yake ba ta kalla ba ta tsallake su za ta wuce. Muryarshi ta yi kasa so cool ya ce, “Kin gani ko Mami za ta tafi ta kulle kofa saboda ga dodonta ya zo....”

Ita ma Mamin ranta babu dadi, tausayin Imam take ji sosai. Ciwon kana so ba a sonka matukar ciwo ne da shi.



Ta ce, “To ya

Please Login or Register in order to submit comment