Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idonta ko kunyar kwayar idanun ta yarinyar nan bata ji ba, a take ta ji ta fara tsanar Safah, duk da cewa ita dinma ‘yar uwarta ce, amma ai wata kusan..... hausawa suka ce “ta fi wata”, amma ta ga shi bai damu ba, dariya ma yakeyi sabida rashin zuciya. Mami ta fito fuskarta yalwace da murmushi, ya isa gareta ya amshi tray din da ke hannunta. Hannun shi ta kama suka isa dining tare, ita ta yi serbing din shi da kanta.



A lokacin da Daddy ke saukowa daga matattakalar bene, ya yi arba da Imam ba zato ba tsammani.



Ya ce, “What a surprize? Cikin satin nan nake shirin cewa ka zo, to kuma

sai ga ka. Amma me yasa baka sanar dani zuwan ka ba?”



Yana dariya ya ce, “Nima tafiyar ban shirya mata ba Daddy, kamar wanda aka tunkudo haka nan na ji duk hankalina yayo gida....(nostalgia)” Marwah ta shigo da ledoji biyu a hannunta ta yi arba da Yayannasu, ta watsar da ledojin ta rugo da gudu kamar za ta rungume shi, amma sai ta tsaya a gabansa ta maida hannuwanta baya ta sarke su tana dariya.



Ya mika mata hannu ya ce, “Come on.... my dear Sissy, na yi kewar ku da yawa”.



Ba ta mika mishi hannun ba ta yi dariya ta ce, “Har dani Ya Imam a wadanda ka yi missing? Ban yarda ba”.



Ya dan fiddo ido “Na yi karya kenan, gemai-gemai da ni ko?”



“A’a, ni ban ce ba’. Ta fada cikin dariya.



“To ki yarda dani, I missed all of you a lot”.

Marwah ta ji dadi, yau ne rana ta farko da ya taba yi mata kalami na kulawa tun tasowar su.



Mami ta ce, “Kyale Marwa ka ci abincin nan Imam’.



Ya ce, “Bari Mami in fara shan furar uwargida na”



Sai da ya shanye furar Haj. Maama, sannan ya aje jug din ya soma cin abincin Mamiunsa, cike da nishadi da kewa mai yawa. W ata tara ba kwana tara ba.





Ya ce, “Gaskiya ne da Bature ya ce, “No place like home”. Mami na yi missing girkin ki yadda bakya zato, kullum na zo cin abincin gongoni sai na tuna ki Mami, na tuna girkin ki mai sawa mutum ya manta sunan sa.



Ba don kowa da inda Allah Ya tsaga mishi hanyar abincinshi ba, da babu inda zan je in barku Mami’.



Ta yi murmushi ta ce, “Imam kenan, nima kullum sai na tunaka, sai in ce da Imam yana nan da kaza ta faru, da kaza bata faru ba’.

Marwah ta shiga dakinsu da ledojinta, sai ta tarar da Safah tana sanya kayan barci, ga dukkan alamu kwanciya za ta yl.



Ta girgiza kai ta shiga toilet ta yo alwala, a ranta tana cewa da wannan banzan yaron ne ya zo da yanzu tana nan tana shafe-shafe da murje-murje. Ta yi alwalarta ta yi sallar isha’i, ta fice falo inda ake ta hira ta barta a nan. Kwanan Safah uku a daki ba ta fitowa don kar su hadu da Yaya Imam din, ko yunwa take ji sai dai ta yi waya kichin a kai mata abinda take so. Shi ma Imam din ya share ta baya shiga sabgarta, ga shi ga dukkan alamu a yanzu kam ya fara amincewa da gaske Safah ta ke ba ta son shi.



Idan a da yana yi mata uzuri da kuruciya a yanzu fa? Shekarunta goma sha tara, ta isa ta bambance abinda take so da wanda ba ta so. Wato dai ta isa ta yiwa rayuwarta ZABI ba tare da an tursasa ta ba.



Shi kuma ya amince ba zai aure ta

bisa tursasawar iyaye ba. Zai yi mata yadda take so muddin ta furta da bakinta cewa ba ta son shi.



A dakin Hajiya Mama yake a safiyar yau suna hira, ta ce, “Ban da abin kuruciya irin na Safah ga dan’uwanki jinin jikinki, wanda ya san ciwo da darajarki, amma ki nace sai wani can da bai san zafin ki ba?”



Sai kuma ta tuna da wa take magana, ta yi hanzarin gyara subutar bakinta, ta ce, “Au, wanda yake son Safah shi Alhaji zai baiwa Marwah’’.



Imam ya yi tsai da ranshi yana duban ta a tsanake. Ji yayi tamkar aradu ta rikito kansas Amma _ ya _ nuna maganarta ba ta taba zuciyarshi ba.



Ta hanyar cewa



“Shi wanda take so din a ina yake?’ Hajiya Mama ta ga babu amfanin yiwa Jikan nata rufa-rufa, kallo daya ta yi mishi ta karanci matsanancin KISHI a kwayar idanunshi.



Duk sai ta ji babu dadi, ta kuma yi Allah wadai da surutun ta. Koda yake

dole kuma ta gaya mishi yadda abun yake, tunda kuma Daddy ya kashe maganar.



Ta ce, “Ma’aikacin Alhaji ne, wa yake da suna? Ni sunan wuyar fada yake mini’.



Ya ce a nitse, “Kutama ko Peter ko Maitama?”’



Ta ce, “Kai, ba haka na ji sunan ba”. Ya mike ya zura takalmin shi yana cewa, “Idan kin tuna ki kira ni, kin san baki san sunanshi ba kika fara gaya mini?”



Ta ce, “Dawo ka zauna zan tuna a hankalv’.



Ya ce, “Kada ma ki tuna, bana son j1’.



Karfe sha biyu na rana Zahraddeen ya shigo gidan, cikin shadda edcelcior maroon colour, kanshi babu hula wanda hakan ya _ bayyanar da kwantacciyar sumar_ kanshi ta Mallawan usli, sai sheki shaddarshi take tana maiko tana nuna tsadarta. Kiris ya rage suyi karo da Imam dake

fitowa daga kofar cikin — gida. Dukkansu basu san juna ba sai a suna. Imam ya kan ji sunan ZAHRADDEEN MAITAMA a bakin Daddy ba tun yanzu ba, ta yadda yawan ambaton Zahraddeen din da Daddy ke yi Imam ya fahimci shi din wani hadimi ne mai muhimmanci ga Daddyn, domin adadin kaunarka da mutum adadin yawan ambaton sa a bakin ka, Zahraddeen kan ji dana ALMUSTAPHA a_ bakin Daddy, amma basu taba ganin juna ba.



A take Zahraddeen ya yankewa zuciyarshi wannan ne Almustapha, tunda ga kamannin Safah nan a kyakkyawar fuskarsa, ta wani fannin kuma da Daddy yake kama.



A take ya ce, “Imam.....”



Shi kuma ya ce, “Maitama....”



Suka yi hannu suna murmushi. Amma fa zuciyar kowanne na zabalbala da kishin dan uwan ansa, amma fa tsabtataccen kishi na masu aiki da hankali da tunani, ba kallon juna suke

don son hango aibu ko nakasun junan su ba ko makamancin hakan a’ah, kallo ne na son hango how much lucky are you??? Kowannensu ganin dan uwansa yake a matsayin wanda yafi kowa sa’a a duniya. Imam ya fasa fita ya yiwa Zahraddeen jagora har main parlour.



Yau kadaran-kadahan Mami ta yiwa Zahraddeen karba ta mutuntawa. Tunda ya zama dolenta.



Ta ce, “Zahraddeen ga Almustapha fa’.



Ya ce, “ai na canka Mami, from the first glance...” (daga kallo na farko)



Ta ce, “Imam. Ga Zahraddeen din Daddy”.



Ya ce, “Nima na canka Mami, ko daga tsagin Mallawan’’.



Duka suka yi dariya. Suka zauna tare cikin kujera, daga nan kuma sai hira rai-rai-rai kamar sun dade da sanin juna.



Cikin dan lokacin Mami ta soma fahimtar Zahraddeen mutum ne mai

dadin mu’amala, kuma dole mutumin da ke alaka da shi ya so shi, saboda saukin kansa. Nutsuwarsa da yadda yake fidda kalamansa a ilmance, duk wata kalma data fito daga bakinsa mai ma’ana ce, daga yadda yake Magana zaka fahimci zurfin ilminsa, ga kyau da kwarjini, gashi mai wayayyen kai. Safah bata yi laifi ba don tayiwa kanta sha’awar auren Zahraddeeen domin ta ko’ina yayi a rayuwa.



Ta tabbatar Daddy na da hujjar shi na son Zahraddeen, kuma bai yiwa diyarta zaben tumun dare ba. Auren gata yake so yayi mata.



Sai ta russunar da kwayar idonta kasa ahankali cikin saduda. Sai azahar Daddy ya_ shigo yana_ baiwa Zahraddeen hakurin bata mishi lokaci da ya yi.



Zahraddeen ya ce babu komi. Saima halayen Alhajin dake kara masa ganin kimarsa. Bai dauki kanshi a bakin komi ba. Suka nufi masallacin Daddy dake wajen gidan suka gabatar da

sallar azuhur.



Kamin su dawo Mami da Marwah sun shirya dining, ita ‘yar mulkin tana daki ko fitowa ba ta yi ba. Tana jiyo muryar Zahraddeeeeeeeen dinta...... ; cikin tausasan lafuzzansa. Ya na yiwa Imam bayanin nasarorin da “‘Dan-Kasa Holdings’ ta cimma a _ wannan shekarar. Bata san cewa hawaye ke zuba tarara daga idanunta ba. Saida ta ji su cikin kunnuwanta, da yake a kwance take.



Bayan sun kammala cin abincin Imam ya yi musu sallama zai je Rabah Road. Zahraddeen ke jan Daddyn _ cikin motarshi ‘buick’ da Imam ya kawo mishi, a kan hanyarsu ta zuwa ofishin Daddy.



Suna tattauna al’amura = masu muhimmanci a garesu. Kamar Uba da dan sa, da yake matukar so. Kamin su gangaro kan muhimmiyar maganar dake cin zuciyar kowannensu.




Daddy ya ce, “Kai nake saurare Zahraddeen, ya ya ka yi shawara da

Inna?’



Yana tukin, amma hakan bai hana shi sunkuyar da kai ba, ya ce, “Na karbi Marwah Daddy, na karbi musayan ka da hannu bibbiyu, ka yi min addu’a Allah Ya sa ta so ni..........27?” Dariya ta kama Daddy saboda yadda Zahraddeen ya yi maganar cikin sanyi? Kamar mai tambaya, kamar kuma mai hasashe. Ya mika hannu ya dafa kafadar Zahraddeen yana bubbugawa ya ce,



“Ta ina Allah ya rage ka da diya mace ba za ta so ka ba?”



Ya cira kyawawan idanunsa ya dubi Daddy. Ya daga mishi kai yana murmushi cikin bada karfin gwiwa, ya ce,



“Kada ka yi haufi kuma kada ka karaya Zahraddeen, you are a genius......



Allah Ya yi maka duk wata falala ta rayuwa, da dan adam ke burin samu. Ba Marwah ba, duk ‘yar wanda kake so za ka aura Zahraddeeni, idan fa har

za ka cire inferiority compled din daka Sanyawa zuciyarka na kasncewar ka karkashi na. Tunda har Safah ta so ka, duk da akidunta da _ baudaddun dabi’unta, a gabana take kuka saboda son da take yi maka. Wanda na tabbata har yau bata daina ba, don tanada_= karfin’ zuciya ne _ da sadaukarwa.



Don haka count yourself among the luckiest, wanda ake so fiye da Imam dina. (yayi murmushi) Ni na gaya maka Marwah zata so ka fiye da son da Safah take yi maka. Ba duk abinda muke so a rayuwa lallai shi zamu samu ba.



Muna barin wani abu duk son da muke mishi don wani abu muhimmi, wanda ya fi son zuciyar mu muhimmanci. Ba duka mafarkanmu ne suke zama_ gaskiya ba. Su, (mafarkan) kamar ‘ya’ya suke; abin nufi, muna daukar cikinsu, amma ba kowadanne muke yin sa’ar haifewa



ba.

Wasu tun suna ciki suke zubewa. Wasu kuma kuma a haife su a mace. (Zaynab Alkali). Irin wannan auren albarkatacce ne Zahraddeeni, kuma ba’a ganin fa’idarsa sai an zauna da juna, an fahimci juna ciki da waje. Soyayyah ta gaskiya ba lokaci daya take faruwa ba, sai a hankali, idan an zauna tare.



Ni dai fatana da kai shine ka zamo tsayayyen namiji wanda zai fi karfin gidansa, kada ka yi la’akari da kasancewar Marwa diya a gare ni ka kasa lankwasa ta.



Ka lankwasata da duk irin tarbiyyar da kake so ta mike da ita. Sannan auren ka da Marwah, baya nufin shi kenan ba za ka kara aure ba, ka auro duk wadanda kake so ka kara, in har za ka 1ya yin adalci a tsakanin su, nine kuma mai biyan sadakin kowaccensu”. Zahraddeen sai ya yi murmushi yana mamakin halayyar GIRMA irin ta Alhaji Aliko. Ko da_baya_ son Marwah, ya yiwa zuciyarshi alkawarin

rike ta da amana saboda mahaifinta. Sai dai yana shakkar Marwah dinnan, a yadda ya ga takunta da tsarin rayuwarta da kyar in za su daidaita, kwata-kwata halayenta da dabi’unta opposite na ‘yar’uwarta ne, ko ma ya take, ko yaya ne, ya yi alkawarin zai rike ta amana tare da dora ta kan turba sahihiya. Anya???



2K ok 6



R



anar alhamis 9/9 na shekarar alif dari tara da casa’in da tara (1999) Baffannin Zahraddeen da_ kannen mahaifiyarshi suka gabatar da komai na auren dansu da Daddy ya ce sadaki kawai yake so.



Domin shine mai alhakin § yiwa Zahraddeen aure, ko da ba diyarshi zai aura ba. Amma Baffan Zahraddeen ya ce tunda yaro yana da halin yi a barshi ya yi daidai_ karfinsae TUWON GIRMA.......miyar sa nama.



Duk wata dukiya da ake bukata kafin aure da al’ada ta gadar sun gabatar

tare da sadakinsu, sama da yadda Alhajin ya nema. Da lefe saitin jakunkunan lefen zamani_shidda, dankare da sittiru na masu rufin asiri, don dai shi Zahraddeen baisan wasu kayan adon mata ba, Rabi’a bata sani ba, balle kuma Inna. Umma kuwa ai ba’a zancenta, bakauya ce ta a bada labari ko Rabi’a tafita sanin kwalliya, don haka matar Peter ce abokin aikinsa Kafilat ta hado lefen ya biya komai bayan ta ci riba yadda taga dama, don bayerabe baya aikin banza. Itama da taimakon makociyar ta Maryam da yake ita bahaushiya ce kuma mata ga ma’aikacin Zenith ta san yadda ake hada lefe a al’adar hausa. Sun tsaida ranar daurin aure asabar mai zuwa, saboda su Marwah za su koma makaranta litinin, wato kwana biyu bayan daurin aure.



Marwah ba ta san bikin da ake yi ba, ta dai ga Zahraddeen ya daina zuwa wajen Safah, sai ta dauka cewa

Daddy ya ja masa birki ne tunda ga Imam ya dawo.



A satin duk kafafen yada labarai na radio, talabijin da jarida na_jihar Kaduna, basu da muhimmin kanu sai na yada labaran gayyatar daurin auren ‘ya’yan tsohon Gwamnan, Alh. Aliko Dan Kasa, wanda al’ummar Jihar basu taba mantawa dashi ba. Har gobe cewa suke “baza’a taba yin Gwamnati irin ta Dan-Kasa a Kaduna ba!!!’”’. Yana tuna musu da gwamnatin Janar Murtala Ramat Mohammed ta dan lokaci a kasarmu Najeriya, amma kuma ‘rebolutionary’ a zuciyar al’ummah duk da ta dan takaitaccen lokaci ce; considering his zero



tolerance for corruption...... , for ladity.....,maladministration and nepotism.....



A kuma ranar ne Alh. Aliko ya tara iyalinshi baki daya, ga mahaifiyarshi da kanin mahaifinshi Malam Safiyanu a gefe, ya umarci Hajiya Mama da ta

Missing Some Pages

ajin auren ka? Ai BABBAN GORO...... sai magogin karfe”’.



Ya yi kamar bai ji ta ba, yana ta faman lallatsa wayarshi, amma a_ zahiri obserbing maganganunta yake ji, cikin amfani da hankali da tunani.



Ta kara shaka da kunnen uwar shegun da ya yi da ita, ta yi kwafa ta ce, “Yo ma in ban da wuce gona da iri da kaikai, inda Allah bai kai mutum ba, ina mutum ina Uwargijiyarsa?



Dan aikena ne za a ce mijina saboda a wulakantani, to wallahi sai ka sake ni....” Ta fashe da kuka.



Imam yana ta mamaki, dama yarinyar nan tana da baki haka? Lallai rashin kunyarta ta isa.



Ya ce, “Kai ka bar bakin ‘yar banza yake motsi har yake gasa maka bakar magana. In nine tabdijan, da tuni leben yarinya ya haye ya yi suntum!” Ya ci gaba da tukin shi yana cewa, “To zauna nan ka zama_ gallafiri,



wawa, ‘yar cikinka tana gaya maka magana”’.

Zahraddeen sai ya yi murmushi, “Ina ruwan ka? Mun fi kusa, wai harshe da hakori’”’.



Daidai inda za su zauna Imam ya yi parking, abokai da ‘yan’uwa suka nufo su domin tarar su. A tare suka bude motar, Imam da Zahraddeen suka fito ta kowanne gefe. Sai walkiya suke cikin hasken fitilun da ya haskake wajen.



Suka russuna daidai yadda babu mai ji Sai amaren nasu, “To ya ya? Za ku fito ne ko mu nade hannun riga?”’



Ba shiri suka yunkura suka fito suna ta kumburi. Dariya sosai Imam da Zahraddeen suka yi. Wadda ta jawo hankalin masu daukar hoton bidiyo da talbijin. Sannan suka jera kowanne yana gyarawa amaryarshi gwaggaro, amaren na ta zabga musu _harara, kamar kwayar idanun su ta fado.



Masu daukar hoto da masu bedio na yi, haka kawaye da abokanansu ke ta daukar su da wayoyinsu da ipad saboda kyau da matching din da suka

yl.



Aka fara bude taron da addu’a sannan Engr. Umar Nahaja , babban abokin ango (one) ya soma karanto tarihin Imam.



Ya karanto makarantun da ya yi tun daga kuruciyarsa ta primary da sakandire, da kwalayen da yake dasu a ‘auto-mobile (automotibe) engineering’.



Ya gangaro ga cewa, “Ango one (Imam) da amaryarshi rainon gida daya ne, shine mutum na farko da ya fara sanyawa Safah ‘pampers’, kuma shine mutum na farko da ta fara yiwa tumbudi....”





Aka kyalkyale da dariya. Bai damu da dariyar jama’a ba ya ci gaba da cewa, “Ya gaya min cewa akwai ranar da ya ci kwalliyar sallar shi da farar shadda zai tafi sallar idi, ya dauke ta yana cewa matata me za ki bani goron Sallah?



Ta kuwa feso mishi kashi mai yawa a farar shaddar shi. Ya ce Idin da bai je

ba kenan’’.



Aka sake kwashewa da_ dariya. Takaici kamar ya kashe Safah. Ya ci gaba da cewa, “Ya gaya min cewa, ‘yan biyun, don sun raina mini hankali, idan na yo mata sako (email) sai dayar ce za ta karanta ta bani amsa da sunan daya.



Tun bana ganewa har na gane, don abin da ake rubuta min ba shi nake gani a zahiri ba...... Safah da Marwa suka dubi juna. Kowacce idonnan jawur.



Umar ya cigaba da cewa, “amma da yake Allah na son Imam, a yau ga shi ya mallaka mishi abin son shi, ba da tsimi da dabarar shi ba’.



Mutane suka girgiza kai, suna so su tambaya “to ba ta son shi ne? Ita mai bada amsar da sunanta son shi take yi?” Ba’a basu wannan damar ba.



Kutama ya amshe abin maganar ya ce, “Sai ango (two), dan gidan Mallawa_ ne, haifaffun unguwar

Tukur-Tukur. Ya soma karanto tarihin Zahraddeen da makarantun da ya yi har zuwa matakinshi na Engineer a petrochemical. Yana bayyana kwalayenshi da matsayinsa na Manajan gidajen man fetur na ‘DAN KASA HOLDINGS’.



Ya ce, “Zahraddeen uwar dakinshi ce ya aura, saboda kankanba da giggiwa irin tasa, ga shi nan sai yanga take Dariya aka yi (in applause). Ya ci gaba da cewa,



“To amma mu mun san mace ba ta fin karfin NAMIJI in har ya amsa sunan shi NAMIJI. Don haka zan iya cewa abokinaaaa....., ta wani fannin bai yi kankanba ba, tunda shi ma BABBAN GORO ne.......”



Aka sake kwashewa da dariya. Ya ce, “A’a, ku bar dariyar nan, kada ‘yan biyu su ji haushi suyi mana (kofi)”. Umar ya amshe lasifikar ya ce,



“Yo suyi mana kofin man? Sai mu sunkuce su mu goya, mu basu hakuri,

mu lallashi kayanmu, tunda mun ji mun gani muna son _ abinmu ahakan...... kowane iri ne kofine muna maraba da_ shi.....!"’ Kai wadannan Injiniyoyin, idan aka biye musu da nishadin su na yau sai su sa cikin mutum ya yi ciwo. Haka jama’a suke cewa”.



Daga nan aka soma ciye-ciye da shaye-shaye. Taron bai tashi ba sai karfe goma sha biyun dare.



Amare suka nemi angwaye suka



rasa sun bace bat cikin jama’a, ana ta kwashe mutane don duk kawayensu sun tafi. Haushi kamar suyi yaya? Marwah na mamakin yawan ilimin Zahraddeen dinnan, da Engr. Nahaja ya fada, a ‘yan kananan shekarunsa da ajin sa da ta ke rainawa. Ba suyi aune ba sai gani su kai filin yana yashewa sai su kadai cikin tent din, suka tsaya kawai standstill, cike da tsoro da faduwar gaba suna kallon ikon Allah.

Can kuma sai gasu, dukkansu suna gaban motar, wannan karon Zahraddeen ke tuki Imam na gefen sa. Imam ya ce, “Don Allah ku yi hakuri, mun kai ‘yammatan mu gida ne”. Basu ce komi ba don takaici suka bude kofar motar suka shiga, suka ja motar aguje suka harba kan titi.



Sun hau titi sosai Imam ya ce, “Wani zubin shiru ya fi yiwa mutum amfani, amma idan ba tsoro ba yarinya ta bude baki ta sake yin magana mana, ko ta maimaita abinda ta fada dazun’.



Basu tanka ba. Ya ce, “Ango (two) ko za ka dan rage zafi ne? Na ga sai zufa kake, ko mu dan zaga in nema maka ‘Guest Inn?’’



Zahraddeen ya yi murmushi idanun shi na kallon hanya ya ce, “A’a, ni babban Yaya ne ban san wannan ba, in dai kai za ka zaga ne to ku fara sauke min kanwata”’.



Daidai sanda suka shigo layin gidan Alh. Aliko, masu gadi suka bude musu tangamemen gate din suka

shigo.



Tun kafin su daidaita parking Safah da Marwah sun bude sun fice, saura kadan su kifa, suka shige cikin gida da gudu. Dariya suka yi sosai. Kuruciyarsu zallah a fili take Washegari lahadi Mami ta shirya (mothers’ day) a harabar gidanta, ita ta shirya amaren da kanta. Sun yi kyau har sun gaji, cikin wani lallausan leshi (swiss), na Safah blue ne, na Marwah orange, sannan aka kawo goggoro deep colour na leshin kowaccensu. Har daga NTA Abuja an zo daukar labarin shagalin bikin ‘ya’yan Aliko Dan Kasa, ban da gidajen talabijin dake nunawa a ciki da wajen gidajen garin Kaduna. To haka masu daukar



hoton mujallun delight da obasion. 2K OK



Daddy ya yi kiran Zahraddeen da Imam don ya ji ra’ayinsu game da tarewar amaren nasu. Bayan duk wannan ruguntsumi ya lafa. Ga shi za

su koma makaranta gobe.



Imam ya ce, “Safah ta koma makaranta zan koma Glasgow jibi, zan yi mata shirin inda za ta zauna, da sabon gurbin karatu ta dora akan nata, maimakon ta sako daga farko, duk da dai bata yi nisa da wannan din ba”. Daddy ya juya ga Zahraddeen ya ce, “Na ji ra’ayin Imam kai fa?’ Zahraddeen ya sunkuyar da kai ya ce, “Nan Zaria za ta zauna a gidanmu, na yi ginin sassa na daban (flat) ina ganin zai ishe ta”.



Daddy ya ce, “Shikenan”’.



Ya jawo mukullai cikin bounch of keys din sa, ya ware wasu ya mikawa Zahraddeen ya mikawa Imam sauran. Suka dube shi cikin yanayin tambaya, ya ce, “Gidaje ne guda biyu da na yi cinikinsu a Malali na mallaka muku halak-malak a matsayina na Baban ku. Ko da ba za ku zauna a ciki ba, idan kun zo sai ku ke sauka a can. Bana son musu, bana son godiya. Ku tashi ku je, Allah Ya ba da zaman lafiya, ya

bada zurri’a dayyiba.



Ku yi hakuri, kuyi hakuri, kuyi hakuri da iyalanku, namiji abinda ya gada kenan hakuri da iyali, koda a auren inaso kana so ne kuwa. Balle aure irin wannan yadda ya zo muku. Hakurin shine kawai zai sa a cimmawa manufar da aka gina auren akai. Watarana sai labara!!!’.



Fuskar Zahraddeen ta yi jajir, ga dukkan alamu bai ji dadin kyautar ubangidan nashi ba. Bai yi kauron baki ba ya ce.



“Daddy ka yi hakuri ba zan karba ba!”’.



“Alh. Aliko ya ce, “Saboda ba ni na haife ka ba ko?”



Ya girgiza kai da sauri ya ce, “A’a, ba don haka bane. Ina gini a unguwar Rimi kadan ya rage a kammala’. Daddy ya dan zuba mishi ido ya ce, “Na riga na baka, idan baka so ya rage naka ka baiwa wani, amma wannan kyautar babu mai tada ita, ko bayan raina!”’.

Haka taron ya tashi zuciyar Zahraddeen babu dadi, ba don ya san halin Daddy ba, da sai ya ce raina masa ya yl.



Amma shi kansa shaida ne a kan halayen Alh. Aliko, babu raini ga na kasa da shi, sai mutuntawa da darrajawa. Kuma da zuciya daya yake yin kowacce kyauta.



Karfe takwas na dare motocin daukar amarya zuwa Zaria suka iso. Duka rabi abokan Zahraddeen ne da abokan aikinsa.



Marwah ba ta tashi kuka ba, sai da ta ga da gaske raba ta za ai da Mami da ‘yar’ uwarta. Zuwa inda bata sani ba, bata taba rayuwa a ciki ba. Zuwa cikin rukunin rayuwar wasu mutane da bata san irin tasu rayuwar ba. Suka rungume juna suna ta kuka. Mai tsuma zuciyar duk mai imani.



Shahidah ke lallashin su, ita kanta Mamin dauriya takeyi saboda ta shaku da Marwah fiye da Safah, sannan Marwan ta fi taimaka mata a kan

harkokin cikin gida da sabgoginta. Rakiyar unguwa, biki, kasuwa, ziyarar dangi da sauransu.



Da kyar wata daga dangin mahaifin

Please Login or Register in order to submit comment