Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zan yi muku ne Almustapha? Ita taurin kai, kai kuma baka ya lallashi ba”.



Ya ce, “Wallahi Mami ba zan zauna ina lallasarta ba, ai sai ta raina ni’.



Ta yi dariya ta ce, “Ka daina cika baki



IMAMU-ALMUSTAPHA, ranar rarrashin ba ta zo bane, amma tana nan tafe”.



Ya ce, “To Mami ke ki lallasar min ita man ko ‘yar hira ce ta bari mu yi kafin in tafi? Kin san halin rai......”



Mami ta katse shi da cewa, “Ni nake maka auren da zan je ina maka bambadanci? Tunda ka ce ba za ka yi ba, to ku yi ta zama a yadda kuke, ruwan ku.



Lafiya za ka je ka dawo insha Allahu, ka zo ka same mu cikin alheri da koshin lafiya kamar yadda ka barmu”. Ya tayata da daukar warmers suka

fito. Masallaci ya koma don yin sallar isha’i, inda ya tarar da Daddy suka yi sallar tare sannan suka shigo cikin gidan suka nufi tebir din cin abinci. Daddy ya dago yana kallon su ya ce, “Wai ina Safah ne?”



Shahida ta ce, “Tana dakinsu’’.



Yace, “Kirawo ta”.



Har ta yi shirin barci cikin wasu tausasan nighties bakake wuluk, tana tufke gashin kanta yadda zata ji dadin kwanciya. Shahida ta kwankwasa kofar, daga ciki ta ce, “Waye?”



“Idon matambayi ne”. Shahida tace a kufule.



Ta bude kofar tana dariya ta ce, “Ki zo Daddy ke kiran ki”.



Ta yafa mayafi ta bi bayanta tana kunkuni, ita an dame ta.



Shahida ta ce, “Ki ce ba za ki je ba mana short and simple....”



Ta tura baki ta ce, ““To ban ce ba’”’.



Daddy ya bita da kallo har ta zauna a jikin Mami, gaba daya ta rame ta yi

sanyi, tausayin ta ya kama shi.



Sai dai ta wani fannin ya fi jin tausayin Imam din da ya kallafa burin rayuwarshi da soyayyar shi a kanta tun haihuwarta. Ya rasa mene ne aibun dan shi da ta kasa son shi. Shi kuma ya rantse har bayan ransa ba zai ta da wannan aure ba.



Cikin kulawa ya ce, “Baki da lafiya ne?’



Ta girgiza kai, “Lafiya ta kalau”. Daddy ya ce, “Gobe ne za ki koma makarantar?”



Ta daga mishi kai.



Ya ce, “Ki yi min magana mana, sai daga min kai kike kamar kadangaruwa...”



Ta ce, “Eh, amma ‘hostel’ zan koma, ba zan iya zama ni kadai a gidan ba”. Ya dube ta yana kiyasi ya ce, “To mene ne fa’idar komawar taki tunda barin makarantar za ki yi gaba daya?” Hawayen da take tattali suka kwace, tsoronta Allah, tsoronta kada ace ta bi Imam, ta ce, “Don Allah Daddy a

barni in yi karatuna, na yi nisa kuma ina jin dadin sa....”



Ya ce, “To, mene ne abin kuka a nan? Kin san dai yanzu ba mu da iko dake sai yadda mijin ki ke so”.



Ya juya ga Imam wanda kanshi ke kan wayarshi yana danne-danne kamar bai jin su, ya ce, “Yaushe za ka tashi?”



Ba tareda ya dago daga abinda yake yi cikin wayar ba Ya ce,



““Gobe da asubah insha Allahu”.



Ya ce, “To in zai yiwu ka kara kwana daya don ku samu_ lokaci ku yi shawara a junanku”.



Ya ce, “Ni Daddy duk yadda ka yi daidai ne”.



Ya yi murmushi ya ce, “Saboda kana tsoron ta? To in gaya maka ba a sakarwa mace ragamar kanta, ka zama namijin duniya ma’ abocin gwagwarmaya da rayuwa kala-kala. Kada ka bari soyayyar da ke zuciyarka tasa ka kasa tankwara iyalin ka.



Ku tashi ku je ku yi shawara a tsakanin ku abin da kuka yanke gobe

ku sanar dani”.



Da haka taron ya tashi kowa ya nufi dakin sa. Sai dai har zuwa washegari babu wanda ya nemi dan’uwansa tsakanin Safah da Imam.



Ita taurin kai da rashin son duk wata alaka da za ta hada ta da Imam din. Sai ta hadu da wanda ya dame ta ya shanye wajen rashin son wargi da miskilanci.




Imam irin mazan nan ne da duk soyayyar da suke yiwa mace, ba za su lamunci ta raina su ba. Sannan bai taba barin ka gane ‘weakness’ dinsa akan soyayyah. Shi Imam ko yana matukar son abu, da wuya ka gane sabida rashin son raini ya ratsa. Sai a inda yasan za’a yi maraba dashi, da abinda zuciyarsa ta zo dashi ko ta ke kunshe dashi. Mami kadai yake iya gayawa cikinsa. Kamar ba ita ta haifi Safan ba.



Abun duniya ya taru ya yiwa Safah yawa, ga kewar ‘yar’uwarta, ga

hukuncin da Daddy ya yanke mai nuni da cewa, in har tana son karatun ta sai da amincewar mijinta.



To ina ta ganshi balle ta tambaye shi? Shi wani irin mutum ya zame mata yanzun mai wuyar sha’ani ba kamar sanda yake yaro ba. Ta manta shekaru kan canza mutum. Kana girma ne kana kara sanin ciwon kan ka. Ba ya shiga sabgarta, ba ya zuwa inda take tun daga ranar da aka daura musu aure. Harkokin gabansa kawai yake, hankalin sa a kwance



Ga shi ita ko lambar wayar shi bata sani ba. Dole ta tsaga billenta ta tambayi Aunty Shahida, don ta san agogon dake like a bangon dakin ta, dana swatch din dake daure a hannun ta na hagu, ba karya suke gaya mata ba; saura ‘yan awanni kalilan Imam ya bar Nigeria da igiyoyin aurenta, da igiyoyin karatun da ta sha matukar wahala akai. Ba da bata lokaci ba ko tambayar dalili Shahida ta bata.



Ta zuba su cikin wayoyin ta da

Zahraddeen ya bata, wadanda dasu take amfani har yanzu, don ranar daurin aure ta bawa Badar ta ce ta neme shi ko cikin mutane ne ta bashi, amma ya dawowa Badar dasu ya ce ta ce mata ta rike ya bar mata duniya da Jahira.



Karfe hudu na yammacin ranar ta yi zugum rike da wayoyin a hannunta ta rasa ta inda za ta fara mishi magana, kira za ta yi ko tedt za ta yi?



Duk wani tunaninta ya kare ne a kan cewa idan ta yi mishi tedt ko kira, ya tabbata ta dauke shi a matsayin miji kenan.



Bayan ta gama cewa bata son shi a matsayin miji, kuma haka abin yake har gobe a ranta, sannan ba ta san irin karbar da zai yi mata ba, don ta lura green snake ne, ta ruwan sanyi suke ladabtar da zuciyar diya mace, ba ta lallashi da tarairaya kamar Zahraddeen ba.



Da ta ga duk wannan ba zai mata ba, ga lokaci yana ja, kuma ta ji yana

gayawa Mami jirgin “Cathay-Pacific’ zai bi karfe takwas na dare, ga shi yanzu karfe biyar na yamma. Sai ta saduda ta soma yin tedt din fuskarta kamar ta fashe da kuka.



Yana hada kayan shi cikin troller a lokacin da ya ji alamar shigowar sako cikin wayarshi. Mami ta aiko Shahida da kilishi da dambun nama mai yawa ta ce ya hada a kayan.



Hajiya Maama kuma gireba ce bokiti guda ta kawo mishi, don yana son gireba sosai.



Yana murmushi ya karbi sakon Mami ya yi masa mazauni kusa da na Hajiya Mama, ya ce da Shahida, “A ce da Mami, na gode!”’.



Har ta kai bakin kofa ya kira ta, ta dawo ta zauna. Ya ce, “Safah me take yi yanzu?”



Ta ce, ‘“Wallahi ban sani ba, rufe kofar take yi”.



Kamar ba shi ba, saboda yadda muryarsa ta yi kasa sosai, ta nuna wani mutum mai azabtuwa a cikin

soyayyah matuka. Yanayi ne da Shahidah bata taba ganin dan uwanta a ciki ba (rauni) Ya ce,



“Shahidah don Allah, a matsayin ki na mace mai shekaru fiye da kannenki, kuma shakikiya agareni wadda nake da tabbacin bazata gaya min karya don inji dadi ba ta boye gaskiya don na cutu ba, ina da wani aibu ko wani hali mara kyau ne da Safah ta kasa so na?”



Tausayin dan’uwanta ya kama ta, ta ce, “Wallahi-wallahi ka ji rantsuwar musulmi kenan, baka da shi’.



Ya ce, “To a ganin ki mene ne matsalar?”



Ta runtse ido ta ce, “Ya Imam shi SO ba a nan yake ba. Dubi Zahraddeen ai bai kai ka ba, ka fi shi komai, amma ta so shi.



Shi ya sa tun farko na yi fatan a ce ina ma MARWAH ka nema, don ita ce mai yi maka soyayyar aure ta gaskiya........”



Ya bude baki yana kallon ta ya ce,

“who told you?” (Wa ya gaya miki) Dariya ta yi “Na san komai, kada ka manta kannena ne, tare muke rayuwa, kuma na fi su hankali, sannan duk wani takunsu a kan idona suka yi shi tun haihuwar su har girmansu. Abobe all, (sama da komai) I’m far more sociologistic than a political scientist. Marwah ce take yi maka e-mail ba Safah ba. Marwah ce take baka greeting cards da sunan_ Safah, Marwah ce take yi maka asirtacciyar soyayya wadda babu son zuciya a cikinta, domin ta yi juriyar da har yau, ‘yar’ uwarta ba ta taba ganewa ba”.



Ya ce, “Me yasa tun a lokacin baki gaya min ba?”



Ta ce, “Ta yaya zan gaya maka alhalin lokacin idon ka ya rufe da soyayya? Baka ji ba ka gani balle ka gane inda ake maraba da soyayyar taka? Ta yaya zan shiga tsakanin ‘yan’uwa_ biyu? Karewa ma wadanda suka fito duniya tare a lokaci daya?”



Ya yi murmushi kadan ya ce, “Me yasa tun a lokacin baki gaya min ba?”



Ta ce, “Ta yaya zan gaya maka alhalin lokacin idon ka ya rufe da soyayya? Baka ji ba ka gani balle ka gane inda ake maraba da soyayyar taka? Ta yaya zan shiga tsakanin ‘yan’uwa biyu? Karewa ma wadanda suka fito duniya tare a lokaci daya?”



Ya yi murmushi kadan ya ce,



“Ni ban sani ba, kuma ko da na sanin ba abin da zan iya. Safah kawai nasan rai da zuciyata ke so a fadin duniyar nan, kuma ita za su ci gaba da so har duniya ta nade.



Zan yi maneji haka Shahidah, kuma ina ji a jikina watarana na zuwa da zata so nin, musamman idan muka haihu tare, wuyarta mu_ kasance karkashin inuwa daya, shine mai wuyar kuma ya tabbata. Nidai na san bazan tsaya ina lallashin ta ba ta so ni, ai Sai ta raina ni,” Shahida dariya ce ta kama ta tace a ranta “Ya Imam ho! Son girma kamar gyambo. Wane raini

ne kuma ya saura tsakanin miji da mata? Ai da daban, yanzu daban babu zancen discipline sai unity and cooperation. A fili kuma ta ce,



“Yayana!”’.



Ya dago ya dube ta.



“Safah fa ba kai ne ba ta so kwatakwata ba, I’m sorry to say....... kai ma kana da laifi, mutum ne _ kai, tough...... ”



Ya saki rigar da yake ninkewa ya dan fiddo ido ya ce, “Ni din?”



Ta ce, (cikin dariya) “Kwarai, baka lallashi, tarairaya da nuna zahirin soyayyar ka.



Ba haka Zahraddeen yake ba, mutum ne dan soyayya wallahi, wanda ya iya nunawa mace so har ta ji tamkar babu wani da namiji da ya saura a duniya bayan nata.





Da wadannan makamai Zahraddeen ya yaki zuciyar Safah, kuma ya samu. Dalili shine, mu mata muna da indibidual differences a fannin soyayya. Wata tana so a nuna mata kauna a za

hiri da badini, wata tana so amma a boye, wato daga ita sai mijinta.



To Safah tana daga cikin rukunin matan da ke so a nuna musu so da zuciya da gangar jiki a zahiri da badini, idan suna tare, soyayyar da yake yi mata bata boyuwa, amma kai akidarka daban ce. Ban jin ko kalaman soyayyar ka iya.



Ka daina treating dinta kamar sauran matan da ka sani. Ka yi la’akari da bambancin kabila da al’ada, matan Turawa da kuke tare dasu basu san darajar kansu ba balle su san martabar da Allah ya yi musu, shi yasa suke hauka a kan ku, suke binku kamar jakai, su suke nuna muku soyayyar ba ku kuke nuna musu ba.



Unlike namu matan da aka halitta da kunya, kawaici, da _ bin _al’ada. Musamman Safah in kayi duba ga yanayin rayuwarta, za’a iya cewa kanta a duhu yake, banda karatunta batasan komai ba sai wanda aka koyar da ita. Abin nufi, she’s not edposed to

modern society.... not interested to social networkings..... She is just acting according to her edperiences wato yadda aka tafiyar da ita a baya.



Bata wani san cewa yanzu mata ke bin maza ba. Batasan wai mata tarairayar



namiji suke ba...... Safah fa ko talbijin bata kallo...... Ba kawa ba abokiya balle aminiya. ....Bata karance



karance sai wanda ya shafi karatunta. Wannan ce kake cewa bazaka rarrrasa ba sai dai ita ta kwantar da kai ta so ka? To a wane dalili? Rannan fa ina ji kana cewa wai Mami ta rarrasheta haba Ya Imam! Wannan dutse ce mai babban daraja_ like a diamond.....bazaka siye ta da sauki ba!!! Sannan an halicce mu mu mata da juriya fiye da ku, ta yadda ko muna son mutum zamu iya jurewa mu danne. Har sai ya sauke kai ya nemi soyayyar tamu don kashin kansa.



Ta wace hanya ka taba neman soyayyar Safah asanda ta soma mallakar hankalin kanta? Kwanciya fa kayi

kana harkokin cigabanka, sabida tabbacin da kake dashi kawai na cewa taka ce! Babu wanda ya isa ya kwace, anya?



Don haka Ya Imam _ nake baka shawarar ka cire rawanin girman nan ka lallashi matar ka, ka nemi soyayyarta..... (a hankalce), ka mantar da ita Zahraddeeeeni....duk da nasan ta zuciyarta ta Marwah ce bazata kuma darsa mata wani abu akan mijin Marwah ba. Ka ji tausayin ta mana, an rabata da wanda ta mikawa zuciyarta sabida kai, kuma ta yi biyayya, ai ko bata cancanci jin tausayi ba, ta cancanci rarrashi. Babu abinda zai ragu daga jikin ka don ka yi hakan. Ni na gaya maka idan har za ka jure da hakan wallahi za ta sauko”.



Murmushi ya yi yana mamakin a ina Shahida ta san duk wannan? Wannan ba abin mamaki bane domin Shahidah ‘yar Siyasa ce. Sai dai bai tambaye ta ba, bai kuma ce ya karbi shawarar tata ko bai karba ba? Saidai can a

karkashin zuciyarsa ya yarda cewa kowanne irin ilmi da irinnasa amfanin.



A kokarinsa na son kawar da tasirin da zantukan Shahida suka suka soma yi a yanayin sad a zuciyarsa kada ta fahimci hakan sai ya ballo sabon zance. Ya ce, “Ke kuma aure sai yaushe Shahidah? Duk wadannan AIhazan da ke yi mana sintiri a gida kullum ta Allah ina lura dasu fah, me zai hana ki fidda daya ki aura idan hankalinki ya kwanta da shi?”.



Ta ce, “Wallahi Ya Imam duk suna da iyali, ni kuma ba zan auri mai mata ba”.



Ya ce, “Allah ya yi zabin alheri, amma ya kamata ki san cewa kin girma fa (at 26) ya kamata a ce ne a yanzu kina da yara biyu”.



Dariya ta yi ta fita tana cewa, “Tunda kai ga shi ka riga ni yi sai in jira naka ‘ya’ yan mu raba, idan ban samu mara mata ba”.

Shi sam ya mance da wani sako da ya shigo mishi, Shahidah ta tafi da hankalinsa sosai. Sai da ya gama hada kayanshi tsaf, sannan ya dauki wayar, a take kiran shugabansu Mr. Ben ya shigo. Ya tambaye shi har yau bai taso bane?



Ya ce, “Zan taso anjima kadan”’.



Ya zauna bakin gadon shi ya bude sakon, bai san lambar ba. Ya karanta kamar haka:



“Za ka tafi, baka ce da Daddy komai ba”.



Nan take ya gane mai lambar, ya yi murmushi ya koma ya kishingida da pillow a karkashin hakarkarin sa, ya tura mata gajeren sako.



“Ban san mai lambar ba’”’.



“And you want to know waye ne koh?”



Da alama a kufule tayi reply din.

Ya yi murmushi ya kai hannu cikin sumar kanshi yana cakudawa, a yayin da numfashinsa ke racing yake fita da sauri da sauri.



Ya yi kokari ya yi replying amma ya kasa danna alphabet s din, saboda yadda wata irin kasala ta saukar mishi. Wani zazzabi-zazzabi ya soma kokarin rufeshi nan take sabida azabar soyayyar da yake dandana.



Gashi dai fada take yi ba kalaman soyayya ba, amma ji yayi kamar rungumeshi tayi tana blowing kisses on him. Gaskiyar Shahidah ne wannan dutse ce mai babban daraja like a diamond...... bazaka iya sayensa da sauki ba!!! Kowanne ‘acting’? dinta akansa burgeshi yake mai dadi ne ko mara dadi.



Da kyar ya samu ya rubuta kalmar “Eh”,



Ta ga nema yake ya yi yawo da hankalinta, sai ta kashe wayar gaba daya, ta koma gadonta ta kwanta abin tausayi. Ta rasa abin da ke mata dadi.

Sai da ya yi wanka ya zuba orange shirt DKNY product, riga mai dogon hannu da bakin wandon jeans, ya taje sumarshi ta kara kwanciya akansa, ya yi shiri tsaf kai ka ce half-caste ne, wato (ruwa biyu). Duk da duhun kalar fatar jikin sa.



Ko da yake ta wani fannin Imam din ruwa biyun ne, Mamanshi Shuwa Arab, Baban shi Bahaushe.



Yana rataye da wata kyakkyawar bakar jaka wadda su komatsen passport, ID card, wayoyinshi da mukullai ke ciki, ya nufi dakin Hajiya Maama suka yi sallama, sannan ya taho dakin Mami.



Sun jima suna sallama ya kasa tafiya, kuma ya kasa tambayarta abinda idanun shi ke son gani. Gane hakan da Mami ta yi, ya sanya ta ce, “Ka je mana ku yi sallama da kanwar taka”. Ya ce, “Kyale ta Mami, ita ya kamata ta fito ta yi min rakiya amma ban isa ba. Don haka kawai ki gaishe ta, ki gaya mata cewa, na tafi’”.

Mami ta rike hannunshi ta ce, “Idan ita yarinya ce kaima yaron ne da za ka dinga biye mata kuna kunci da juna? Wannan ba ya cikin tsarin musulunci, sam baya ciki, ko da ace ba ma’aurata kuke ba, what is the cause of all these nonesense?”’.



Ya ce, “ita za ki tambaya Mami, ba zan dinga shiga al’amarinta tana harara ta ba, ko ba mijinta bane ni ai gaba nake da ita, amma yarinyar nan ba ta jin kunyar ko a gaban waye ta harare nt”.



Mami ta yi murmushi ta ce, “To ka yi hakuri, babba juji ne”’.




Ya ce, “A’a, wallahi ban da ni Mami, yanzu sai in targada ta kuma in kwana lafiya wallahi’”.



Ta ce, “Je ka ku yi sallamar ka yi hakuri ta ci albarkacina”’.



Tana rike da hannun sa har saman bene, ta murda kofar anyi sa’a ba ta rufe da mukullin ba, suka shiga Imam na bayan ta.



Kudundune take cikin bargo, sai rawar

dari take. Mami ta ce, “Lafiya Safah? Duk uban zafin nan da ake kika shige cikin bargo?”



Ta bude idanunta a hankali, sun kankance sunyi ja. Da sauri Imam ya karasa ya janye bargon, ta yi hanzarin dunkule jikinta saboda kananun minis dake jikinta.



Daidai kanta ya zauna ya kai hannu bisa goshinta, zafi rau kamar wuta, sai rawar dari take, hakoranta na karo da



juna kaf-kaf-kaf! Ya ce, “Subhanallahi, Mami ba ta da lafiya...”



Duk ya gigice ya rude, rudewa da gigicewa irin wanda Mami bata taba ganin yayi ba. Tuni ya hullar da jakar hannunsa. Itama Mamin ta karaso ta dauki kanta ta aza a cinyarta, ta ce, “Kashe kanki kike so ki yi Safah, ki dinga kulle kanki kina cuta ke kadai cikin daki?”



Ba ta amsa ba kwayar idanunta ta mayar ta rufe. Zara-zaran gassun idonta suka bi idon suka yi linkif.

Mami ta nuna mishi doguwar riga a sakale jikin ‘hanger’ ta ce dauko ta sa mu tafi asibiti, kai kuma ka tafi kada jirgi ya tashi ya barka”’.



Wani irin kallo ya yiwa Mamin ya ce, ‘In je ina Mami? Alhalin bata da lafiya?” cikin fushi da haushin Safah Mami ta ce,



“To zaman ka ne zai sa ta warke? Ko me ya same ta ai ita ta jawa kanta. Ayi mutum sai taurin kai da_rashin tawakkali? Za ki hada kanki da hawan jini haka kawai? Me aka yi miki? In dai Imam ne tafiya zai yi ya bar miki kasar ma baki dayanta ba garin ba..... Aure kuwa saidai ki mutu, ko kin mutun zamu sa shi ne kawai ya wankeki ya kaiki kabari ya dawo mu shafa fatiharsa da wata, wadda ta fiki da duk abinda kike takama dashi, ni banda kai ma wa zai kwashi wannan mai bakin halin da bakar zuciyar?”



Yayi dariya aransa yace “mami kenan’, a fili ya ce, “Mami ni fa ba inda za ni sai Allah Ya bata lafiya”

Ta ce da shi, “To gwale ni (gwasalewa), ai dama kai ba’a yi ma gwanin ta in dai akan ta ne”.



Ya motsa baki, yana so yayi dariya. Ta taimaka mata ta sa rigar ta rufa mata mayafi, Mamin na rike da ita suka fito.



Mami ta ce, “Ni ba zan je bama, kuje sai kun dawo Allah ya sauwake. In kuma jirgi ya tashi ya barka kai ka jiyo”.



Har jikin mota ta rako su, ta bude mata kofar gaban motar ta shiga ya tada motar masu gadi suka bude get ya ja motar suka fita.



Mami ba ta koma ba sai da ta ga fitarsu daga get din gidan, ta koma cikin gida tana addu’ar Allah Ya nuna mata ranar da za ta ga Safah da Almustapha matsayin mata da mijin dake matukar son junansu, ko yaushe ce wannan ranar? Ko tanada rabon ganinta?? Ko yaushe zata zo??? Ko zata zo din kuwa???? Ko dai mafarkanta na gaya mata gaskiya ne????

Zuciyarta cike take da wani irin



tsoro da firgici mai yawa a dalilin mafarke-mafarkenta a dan tsukin akan Safah da Almustapha, masu nuna mata ko zasu yi zaman aure, to ba yanzu ba. Sai can wani karni mai zuwa a nan gaba. Lokacin da al’amuran rayuwa zasu juye su rikide su chanza da al’amura marassa dadi. Ya kuma sa tana da _ rabon_ ganin ‘ya’yansu da jikokinsu. Har ma da tattaba-kunne in Allah Ya nufa. A lokaci guda kuma tana tunanin halin da Marwah ke ciki da nata angon, ko su kuma wace irin wainar suke soyawa? Tunda wadannan har yanzu sun ki daidaita kansu, su san cewa Annabi ya faku. Ba duk abinda kake so a rayuwa kake samu ba kuma ka zauna lafiya. Amma su sun ki gane hakan da gangan.

MU HADU A LITTAFI NA BIYU. -Takori


*************************⬇**********************
************* Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > [email protected]

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels



Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************






An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani

Please Login or Register in order to submit comment