Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata Iyaye. Ina kallo ta baiwa Mamee. Mamee da ƙyar ta karɓa,ni dai na san kunya hana ta karɓa tun farko.

Bai fi na mintuna biyu ba ta miƙawa Mama. Mama ce ta kaiwa Daddyna, inda na ga Daddyna ya karɓa yana dariyar farin ciki, irin wannan dai aka ci gaba da yi har lokacin sallar Magriba ya ƙarato, aka rufe taro da addu'a aka tashi.

**** **** **** **

Gama arba'in ɗina da ƙwana uku, ya yi daidai da hidimar bukukuwan barorin gidanmu,ƴan mata da samari, wanda su Mansura tun da biki ya matso take kukan rabuwa da ni, duk da an ce wa mazajen su mai so zai iya barin matarsa ta yi aiki, ana biyanta kuɗin aikinta.

Bayan ba kuɗin mota za su dinga biya ba, gidaje ne aka gina musu a cikin dajin gidanmu, sai dai na san muna da ɗan nisa da su.

Ana gobe kai amarya ne na taka gidan yari tare da ɗana Ammar, wanda yake ɗauke ga kafaɗar Mansura amaryar Isma'il.

Gaba ɗaya na sa aka jera su layi, na dinga tambayarsu. Yawanci laifi ɗaya gare su, shi ne rashin kunya, wasu kuma sun tarewa Yarima hanyar fita,babu dai wani taƙamaiman mai laifi, sai mutum tara,su ne aka haɗa baki da su za'a sawa Yarima guba a abinci, Allah ya toni asirinsu.

Macen da na samu lokacin da Yarima ya kawo ni gidan yarin, ita kuma laifinta shi ne ta aiko da takarda tana son Yarima, shekarunta ba su wuce ashirin da huɗu ba, sai dai ƴar wahala ce ta mayar da ita baya kaɗan.

Gaba ɗaya mazan na sallame su,ban da taran nan, kowanne daga cikinsu na bashi jarin dubu ashirin da kekunan hawa. Su kuwa matan keken ɗinki da dubu goma-goma. Mubaraka ce kawai na ce a kai mini ita gidana da sauran tambayoyin da zan yi mata. Mazan nan tara kuma na ce a tsare mini su, sai na yi bincike a kansu.

Wata ɗaya na baiwa Mabaraka akan ta fito da miji a yi mata aure,in kuwa ba haka ba duk abin da ya biyo bayan haka, ita ta janyowa kanta. Na kawo dubu biyar na bata ta sayi sabulu kafin ta fito da miji.

An yi bukukuwa lafiya, taro kuma ya tashi lafiya, amma inda Allah ya ba ni sa'a har yau ina tare da yarana na gidana, duk mazansu sun bar su, sai dai wasu biyu da aka kawo mini saboda ƙwana. Ammar kuwa ya zama abin ƙauna ga kowa. Yarima kuwa,ni da shi tamkar amarya da sabon angonta.

**** **** ****

Ƙwanciyar hankali tana neman gagarar mu ni da mijina, da duk wani masoyinmu, sakamakon juya bayan da Sarki ya yi mana,a cikin wata biyu kenan. Dabara, hanyoyin daidaitawa duk mun bi su amma abin ya faskara. Wannan tashin hankali ya hana mini Yarima iya zama gida, kullum yana gidansu neman ko a shirya, amma al'amari sai ma gaba yake yi.

Babu wanda idanuwana ke son gani sai Yarima, saboda tun asuba da ya fita bai dawo ba, sai dai ya yo waya cewa Sarki na son ganinshi, gashi har ƙarfe goma na dare ta kusa. Tun ina hira da mutane har na kai ga komawa falon sama ina zaman jigum ɗin isowar Yarima, amma babu tunanin da nake sai na maganganun da jakadiya ta gaya mini.

Anya kuwa jakadiya ba nema take ta zura ni hanyar wahala ba? Na tunano yanda ta ce mini,wai in dage da abi...... Shigowar Sa'a ita ta katse mini tunanina,tare da jin kukan Ammar. Tana isowa ta durƙusa ta miƙo min shi. Ban tsaya jiran wani ba'asi ba na raɓa shi a cinyata, domin ba shi abincinsa da ke jikina. Ita kuwa ta yi mini sai da safe ta juya ta koma maƙwancinta.

Wasa irin na ɗa da mahaifi, shi Ammar yake son mu yi, shi ne riƙe bakina da yi mini waƙar yarensu ta yara, amma yau na kasa kula da shi. Yaron da Babansa ya sangarta shi da wasanni kala-kala, ballantana da ya fara girma.

Hankalina kam ya tashi matuƙa, ganin agogon falon ya nuna sha ɗaya har da minti ashirin, amma ban ga Yarima ya dawo ba, wannan ne ya ba ni damar tashi na nufi sashensa, tallabe da Ammar a saman kafaɗata, yaran da ya yi bacci wajen awa ɗaya kenan.

Gabana na ji ya yi wata irin mummunar faɗuwa,jin ƙofar barandar bayan ɗakin Yarima a kulle, na saka nawa mukullin, amma da ɗan makullinsa a jiki.

Me Yarima yake nufi? Ba ya son ganina ko kuwa? Har na ji raina ya yi mugun ɓaci hakan yasa na dawo ɗakina na shinfiɗar da Ammar na zauna na rafka tagumi.

Zuciyata babu abin da bata saƙa mini ba,amma daga ƙarshe duk na ajiye zugar shaiɗan ɗin da ta yi mini,na miƙe na ɗauki alkyabbata na saka, tare da tallabar Ammar. Shiru gidan namu sakamakon kowa ya yi bacci, sai masu gadi da suke yawo.

Ƙofar gidan Yarima a kulle take, amma saboda ina da makullin ƙofar a cikin makullaina yasa na sa na buɗe ta,yau ko ƴar fitilar nan da ake bari ta falo ma babu ita, security light. Cikin ɗan lalubar hanya na iso falon shi na sama, shi ma fitilar wajen a kashe take, na murɗa ƙofar ɗakinsa na shiga.

Nan ma fitilar ɗakin a kashe suke, na sa hannu na dinga laluba inda makunnin wutar yake da ƙyar na samu na gano shi. Haske ya gauraye ɗakin, wanda ya yi daidai da haɗa ido da Yarima, mutumin da na gani a ƙwanciyar rigingine, amma gaba ɗaya ƙafafunsa a ƙasa suke,gangar jikinsa ce kawai ke saman gado. Ya dinga kallona,ni kuwa na yi tsaye ina neman iso. Bai yi mini magana ba, amma ya yi mini magana da kansa, alamar in zo in zauna kusa da shi.

Wata zuciyar ta ce in juya inyi tafiyata, amma sai na yi tunanin hakan ba mafita ba ce. Na isa na zauna kusa da shi, kamar yadda ya umarce ni. Na juya na kalleshi tare da dafa hannunsa ɗaya. Wannan na lura ba ƙaramin daɗi ya yi masa ba, sakamakon tashin da ya yi zaune, tare da ɗauke Ammar daga cinyata,yaro ɗan wata baƙwai da haihuwa.

Ya miƙe tsaye ya kai shi,saman gadonsa ya shinfiɗe shi, sannan ya dawo ya tsugunna gabana, tare da kama hannayena duk biyun. Ganin ya kasa yi mini magana yasa na kama shi ya miƙe tsaye.

Cikin nutsuwa na mayar da shi na ƙwantar a saman gado. Abubuwan da na san za su karkato da hankalinsa zuwa gare ni shi na dinga yi masa cikin salo-salo, hankali ƙwance. Yarima cikin sauri jikinsa ya ɗauki rawa, wacce take ba ni tsoro a duk lokacin da ta zo masa, amma yau zuciyata na ji ta yi mini daɗi, saboda na samu hanyar da zan tambaye shi me ke faruwa.

Tabbas Yarima ya nuna mini farin cikinsa a fili har na tsayin wajen minti arba'in. Fitilar gefen gado ya kunna, sakamakon duhun da ya gauraye ɗakin a ɗan tsayin mintunan da suka wuce. Ina kallo ya miƙe yasa alkyabbarsa,nima ya ɗago ni ya miƙo mini tawa.


######
[2/22, 15:44] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 7


Yanda ki ka san kurame muka koma saboda kamo ni ya yi ya durƙusar da ni gabansa, sannan shi ma ya durƙusa, ma'ana dai mun haɗa gwiwoyin ƙafafun mu waje ɗaya,muna fuskantar juna. Ya kama hannuna duk biyun, sannan na gaya sunkuyar da kansa. Ganin ya ɗan ɗauki lokaci bai yi magana ba,yasa na zame hannuna ɗaya na matsa sosai, na tallabi kumatunsa ɗaya, sannan na ce, "Yarima." Cikin sanyi murya.

Wannan ya ba shi damar yin magana, "Yasmin." Ya yi shiru.

"Yasmin,zaki iya zama da ni ko bani da sarauta? Ko ba ni da komai,ko kowa zaya ƙi ni,ko bani da masu yi miki hidima? Ko ba ni......"

Hannu na sa na rufe bakinsa, "Yarima ka daina shakku a kaina,ni kai nake so,ba wani abin ka ba, ba kuma wani naka ba, zan zauna da kai Yarima a duk halin da ka shiga, ballantana na sanar har abada ba zaka taɓa taɓewa ba,tun da tun farko Allah ya nuna maka ƙauna a kan harkokin rayuwarka. Shin wai taƙamaimai me ya janyo wannan rashin jituwar tsakaninka da Mai Martaba ne? Anya ba ƙulli? Mai Martaba na sonka,son da kowa yake son ya ga iyayensa na yi masa."

"Yasmin,idan na ce miki ga abin da ya haɗa mu nayi ƙarya. Ni dai an wayi gari ranar wata juma'a mun je Masallacin juma'a na ga Mai Martaba bai damu da ni ba, kamar yadda yake yi mini da. Da aka tashi na je gaishe shi, sai bai amsa mini ba. Ban damu ba, saboda na yi tunanin jama'a ce ta yi masa yawa, saboda haka na yanke shawarar bin shi gida domin yi masa gaisuwa ta musamman.

Ina shiga fadar sai cewa ya yi in fita. Amma a lokacin na yi zaton ɗan wasa ne na tsakanin ɗa da mahaifinsa, amma ina kin ga yanda ta kasance mana yanzu, na koma sai dai in hango mahaifina daga nesa. Jama'a sun sa baki, amma lamarin sai ƙara jagulewa ma yake yi." Ya koma ya zauna sosai, tare da janyo ni jikinsa.

"Yau lamarin ya yi zafi Yasmin,saboda yau Mai Martaba ya ce na fitar masa daga gida, komai ke cikin gidan bai ce na ɗauka ba, face sutturun mu, sai kuwa motar da Waziri ya ba ki."

Ya gyara ya janyo mukulli daga aljihunsa.

"Kin ga waɗannan mukullan, Waziri ne ya ba ni su,wai gida ne gare shi a Sultan Road Kaduna, ya ce na je can na zauna.

Yasmin kunyar ki ta hana ni shigowa inda ki ke, da tunanin kada in gaya miki ki guje ni, kema,ni na san hankalina ya tashi matuƙa, koma in ce yana cikin tashi.Amma rabuwata da ke sai ya fi nakasa mini rayuwata, saboda yanzu al'amarin ya zo da ɗan sauƙi, tunda duk ƴan fada na sona, kuma har yanzu ba su goyi bayan Sarki ba,su ma kansu suna mamakin abin da ke faruwa, dukkansu kuma suna iya ƙoƙarinsu, amma al'amarin sai haƙuri."

Ya yi ɗan shiru. "Ni yanzu Mama kawai nake ji, tunda ya ce Allah ya isa idan na shigar masa gida. Yanzu ban san yanda zan yi in dinga ganinta ba, balle in yi sallama da ita a yanzu, saboda plan ɗina in bar ƙasar nan kawai,in koma Greece shi ya fiye mini ƙwanciyar hankali. Ni dai tun da kina tare da ni da sauƙi. Mahaifiyata kawai nake tausayawa."

Yanda gabana ke faɗuwa idan har ka saurara kana ji, saboda tashin hankalin maganar da Yarima ke yi mini. Hawaye kuwa da ke fita a idanuwana, duk sun jiƙe gaban rigata. Jin har ya gama amma ban yi magana ba, shi yasa na ga ya ɗago kaina, sai na ga ya yi murmushi mai haɗe da takaici.

"Yasmin,kada ki tayar da hankalinki, komai ki ka ga ya yi tsanani, to sauƙi na tare da shi."

"Yanzu yaushe ya ce ka tashi?"

"Gobe. Yau fa har wajen manyan shi muka je, amma cewa ya yi muddin Azahar ta yi gobe in har ban tashi ba, duk abin da ya faru da ni ni naja."

"Mama ta sani?"

"Eh, na aika mata da Waziri, sannan na yi mata waya, ta ce in tashi kada ya wulaƙanta ni a gaban jama'a. Yasmin na rasa abin da ke yi mini daɗi a rayuwata. Ni yanzu ya ya ma zan yi?"

Cikin ƙarfin hali na tashi zaune na kalleshi sosai, wanda taimakon Innalillahi ya yi min shi tare da tunano abin da Allah (S.W.T) ke cewa cikin littafinsa mai tsarki:

_Fa innama al'usrin usra."_ Ma'ana:--- _Lallai ne tare da tsananin nan da akwai wani sauƙi, lallai ne tare da tsananin nan da akwai wani sauƙi."_ saboda haka idan ka ƙare (ibada) sai ka kadu kana roƙon Allah, kuma zuwa ga ubangijinka ka yi ƙwaɗayi.

"To yanzu ke wacce shawara ki ka ga ta dace da mu? Mu bar ƙasar ko? Saboda ni abin kunya ne...."

"Sam ba ka tare da abin kunya har abada. A shawarata ka bi maganar Waziri, ka zauna Kaduna,kana jin me ke faruwa, sannan duk ranar da mahaifiyarka ta so ganinka za ta zo har inda ka ke. Yanzu tashi za kayi mu ƙwashe duk kayan mu tun yanzu,muna da motoci,a hannunmu kafin gobe a ƙwace. Kada mu gayawa yaranmu abin da ake ciki,mu ce masu tafiya ce ta kama mu, shekara ɗaya za mu je mu dawo kawai. Yanzu kuma ka tado direbobinmu su kai mana kayanmu Kaduna tun cikin daran nan, ina ga shi ne rufin asirinmu."

"Haka za'ayi, tashi ki kirawo jakadiya ki gaya mata komai, ta taimaka miki haɗa kayanki da na Ammar. Kayan sawa kawai, sai kayan ƙwalliyarki, amma na jiki,sarƙoƙinki, daga su kada ki taɓa masu komai. Kafin ku gama nima na gama haɗa nawa."

Na ce, "To."

Na tashi na tafi, wanda har na kai ƙofa na ji ya kira sunana. Ina juyowa ya ce in jira ya rakani dare ya yi.

Jakadiya na kuka tana haɗa kayanmu. Ban da Ammar da ke goye a bayanta,kaɗan-kaɗan kuwa ta ce, "Amma tare zamu tafi ko Gimbiya?" Sai dai in bata amsa da, "Sai abin da Yarima ya ce."

Ƙarfe huɗu na dare mun gama komai, har direbobin sun tafi da kayanmu. Abin da ya rage a hannunmu aƙwatin duniyarmu da ƴan kayan da za mu sa da safe.

Gari na wayewa tun wajen ƙarfe taƙwas gidanmu ya ruɗe da kukan sallama. Mun yi wannan dabarar ne ta barin gida tun safe domin mu samu a kai mu cikin motar gidan nan, tare da tawa motar da Waziri ya ba ni.

Ƙarfe tara da rabi muna falon Daddyna,yana yi mana nasihohi tare da yi mana alƙawarin za su yi iya ƙoƙarinsu su binciko me ke faruwa. Sannan ya yi mana alƙawarin kai mana ziyara. Ya Kawo addu'o'i ya bamu, ya ce mu dage sosai a kan yin su, Allah zai bayyana ainihin gaskiyar abin da ke faruwa.

Mamee ma haka ta yi mana ita da Aunty Salwa,sannan suka yi mana alƙawarin za su zo cikin sati na sama, domin ganin inda muka koma. Suka yi mana nasiha a kan mu zauna lafiya kada mu kuskura mu baiwa wasu fuska su shiga tsakaninmu, sannan kada mu yarda wannan abun da ya faru ya kawo mana raini a tsakaninmu. Haka dai muka rabu kamar in ce ba zan je ba, amma ganin yanda Yarima ya zama cikin ƙanƙanin lokaci yasa na ji ba zan iya ba.

Sai da muka wuce garin Fambigowa cikin wani ɗan daji, sai muka hango mota jib baƙa da wata ruwan shanshan bale Honda Accord. Wasu mutane suna ɗaga mana hannu. Dalilin ganin mu kuwa direbanmu ne yake faɗa mana shi ne har ya jamu.

Yarima ya ce ya sauke gilasan mu gani, sai da muka iso daidai su, sai na ji Yarima na cewa wai kamar motocin gidan su. Muna dawowa baya Mama na fitowa daga jib ɗin nan baƙa.

Ana cewa tsakanin ɗa da iyaye sai Allah, na amince,yau Mama tamkar zata mayar da Yarima ciki. Tun kuwa da ta karɓi Ammar ba ta miƙo mana shi ba,yana saɓe a kafaɗarta, suka dinga hirarsu ta abin da ke faruwa. Ƙarshe dai Mama ta ce mu dawo motarta mu bayar a mayar wa da Sarki da tashi.

A motar Mama muka isa har Kaduna unguwar Sultan Road,ko awa ɗaya ba mu yi ba da zuwa muka ji ana ta odar mota a get ɗin gidan.

Ɗaya daga cikin direbobin da suka kawo mu ya je ya buɗe ana buɗewa muka ga Jeep Itama baƙa. Joseph wanda direban Daddyna ne, shi muka gani. Ya zo ya durƙusa ya gaishe da Mama da Yarima, sannan ya miƙawa Yarima makullin da ke hannunsa.

"Dama Alhaji ne ya ce in biyo ku a baya in kawo maka wannan. Tirela kuwa kayan ku ne,a juye a bamu ita mu koma da ita, ya ce kuma idan kuna buƙatar masu aiki ku gaya mani a kawo muku."

Anan ne na ji Mama ta yi magana, "Ka ce an gode, amma masu aiki har na tanadar masu su, har da maigadi ma. Motar ma da na tanadar masu, amma tun da ya riga ni kawowa shi kenan, ta shi za'ayi aiki da ita."

Tasa hannu a jaka ta miƙa masa bandir ɗin kuɗi, sannan ta ce su je su sauke kayan.

Nasihohi da nuna mana cewa abin da ke faruwa jarabawa ce daga Allah, duk shi Mama ta yi mana, sannan ta yi sallama da mu tare da cewa duk lokacin da ta so ganinmu za ta zo, sannan duk abin da ya shige mana duhu ga waya nan a buga mata. Ban taɓa ganin kukan Yarima na gaskiya ba sai yau. Yau har sai da na ji hankalina ya yi matuƙar tashi. Da ƙyar na samu na lallashe shi, shi Ammar har da kuka, na ba dalili,a nan ne na nemi kukan Yarima na rasa.

**** **** **** **

Saboda son junanmu da ƙwanciyar hankali ta ƙaru tsakanina da Yarima, babu inda yake zuwa sai gonar kajinshi da shanu da sauran dabbobi da yake kiwo. Daga can kuma ya isa fadamarsa inda yake noman rani, shi ma sai bayan sallar la'asar yake zuwa, kafin magriba kuwa ya dawo gida kullum. Mu kuwa kamar yara muke ga iyayenmu. Sarki ne kawai har yanzu bai yaye mana abin da ya faru ba. Shekaru huɗu kenan har da watanni biyar.

Yanzu haka bai san mun haifi yarinyarmu mace ba, mai sunan Mama, wacce muke kira da Suhailat. Ammar kuwa tuni an sa shi a makaranta. Wani abin mamaki kuma har hutu yake zuwa Jos wajen su Mamee, har kuma ya isa gidan Sarki ya yi ƙwanansa, amma sai dai Mama ta ce ɗan ɗiyar ƙanwarta ne,wato jikanta ne.

Mu kam Kaduna ta karɓe mu,bamu cikin wata matsala,sai ƙaruwa da muke yi. Shi ne yanzu ana zuwa har gida ana koya mana karatun litattafan addini ni da Yarima. Ga shi kuma yanzu ya iya neman na kansa, wanda a da sai dai ya ga kuɗi bai san ta yadda ake samun su ba.

Yau ma Yarima na ƙwance a doguwar kujera daga shi sai singileti fara da dogon wando,ni kuwa ina ƙwance,wato saman jikinsa,muna ta hirarmu ta yaushe zan je Jos, saboda na samu shekara kenan har da wata biyu ban je ba. Na fahimci Yarima yanzu ba ya son ana yi masa hirar Jos, amma ni a wajena ta zama dole. Bai kai ga bani amsa ba muka ji sallama.

Na ɗan yi gaggawar tashi zaune, sannan na ce, "A shigo." Sa'a mai rainon Suhailat ce ta shigo ɗauke da Suhailat yarinyar da ta shekara ɗaya da wata huɗu kenan. Ta durƙusa har ƙasa sannan ta ce, "An yi baƙuwa tana waje. Na tambaye ta sunan ta domin inzo in gaya maku, amma ta ce ace baƙuwa ce daga Jos."

Nan take Yarima ya ɓata rai, "Ki ce mata ta koma can Jos ɗin, nan gidan duk ƴan Kaduna ne ba ƴan Jos."

"A yi haƙuri Yarima." Ya juyo da saurin gaske, ya kira sunana. "A yi haƙuri kuskure ne,je ki kice ta shigo." Ta tashi ta fita.

Kafin ta shigo na yi saurin miƙa masa doguwar rigarsa ta shan iska. Ya karɓa tare da yi mini ƙorafin kada in ƙara kiransa da Yarima, baya so. Na bishi da na daina.

Wata fuska na gani, wacce da gani na san fuskar, sai dai ganin ta yi mini tsufa, ta rame,ko ince ma ba tsoka ko ɗaya a jikin fuskar.

Dattijuwar da ta shigo, ta zauna ƙasa tana gaishe mu.


######
[2/25, 16:04] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 8


"Sannu Inna,ban gane ki ba, na so dai in ga kamar na taɓa ganin ki, amma na kasa tunano a ina na taɓa ganin ki."

Sai na ji ta saka kuka tana cewa, "Ai dama na san da wuya ki gane ni Gimbiya ni ce jakadiya."

Kafin ta ƙarasa daga ni har Yarima mun miƙe tsaye tare da kiran Innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un! Kamar haɗa baki muka ƙara cewa, "Jakadiya me ya same ki haka?"

"Ai Gimbiya Allah ya yi da ragowar shan ruwana gaba, da tuni da sai dai in kun tunano ni ku ce Allah ya ji ƙaina. Yanzu mu ai mulkin kama karya ake yi mana a Jos, saboda azzalumin Sarkin da aka baiwa sarauta."

"Wa aka ba sarautar?" Yarima ya yi tambayar.

"Wani ne wai shi Abdulrahman, wai ɗan Sarki ne, shi ne yanzu duk abin da ake yi sama da shekara uku duk baku da labari?"

"Ba mu da labari, wajen wa zamu ji?"

"Wajen Mama."

"In ta zo mu bata gaya mana komai. Ni kuma ko na je Jos ba na zuwa ko'ina sai gidanmu,ni kuwa ban taɓa ji ba,mun san dai ance an yi naɗin sarauta a Jos, amma ba mu san me aka naɗa ba."

"Ai abin ba daɗin faɗa,kin gan mu nan jiya muka gudo daga gidan yari. Wahala ta duniya ba wacce ba mu gani ba...." Tasa kuka.

"Ke har da fyaɗe an yi mini, tsofai-tsofai da ni. Ke yanzu dai Allah ya yaye mana masifa kawai."

"Ina su Mansura." Na tambaya cikin sigar tashin hankali.

"Sun gudu su duka waɗanda ki ka sani, maza da mata, saboda kamo su kawai aka dinga yi ana yi masu fyaɗe kullum. Maza kuma a kaiwa shugaban nasu, shi kuma aikinsa kenan amfani da maza. Gimbiya ƙartin mutane ya zo da su sune dogarawansa, sun kai ɗari biyu, ban da ƴan iskan ƴan mata." Ta sake fashewa da kuka.

"Dole ne in neme ku in sanar daku yanda ƙasarku ta koma. Ku yi mana arziƙi ku je ku taimakawa al'ummarku."

"Ina Mai Martaba yake ne ake yin irin wannan abubuwan kafirci?" Yarima ya tambaya.

"Yana nan,ai ya riga ya tsafe shi, sai yanda ya ga damar yi da shi. Waziri da manyan mabiyansa fa an neme su an rasa."

"Innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un!” muka haɗa baki.

"Yanzu su waye kusa da Sarki?"

"Wasu ne ya kawo ya zuba masa. Kai bacin su Ahmad fa da ƙila ma an gama da su Mama, to su ke tsaye a kan iyayensu, duk sun ajiye karatunsu, sun zama masu gadin iyayensu."

"Yanzu ke ya aka yi kika gane nan gidan?"

"Gidan su Gimbiya na je na samu maigadinsu, shi ne ya yi min ƙwatancen nan gidan. Shi ya gaya mini ma kuna nan garin, da duk abin da ya faru a baya, saboda mu bamu sani ba. An dai taɓa jin labarin kuna ƴar takun saƙa da Sarki, har na cewa Gimbiya ta tashi tsaye,sa hannu aka yi maku kai da mahaifinka."

"Me ye sa hannu kuma?"

"A je mugayen matsafa su shiga tsakanin masoya biyu."

"Allah ya kiyaye. Yanzu ki tashi kiyi tafiyarki,ni yanzu hankalina a ƙwance ya ke ni da iyalina, saboda haka ba na fatan abin da zai zo ya dagula mini lissafi. Sarauta kuma Allah ya tayashi riƙonta. Amma ni yanzu ko ma sha'awarta ba ma yi, ballantana inji ina sonta."

"Amma Allah ya ja da rai kayi kuskure babba, saboda iyayen ka na cikin bala'i, amma sai ka ce ba ruwanka, yanzu haka fa Sarki ya auri matar nan uwarsu shi wanda aka naɗa, sai fa yanda ta yi da shi. Mama kuwa in zata fita sai dai fa ta fita ta ƙofar nan ɓoyayyiya ta je duk inda zata ta dawo."

"Ban yarda ba, saboda da Mama ta gaya mini. Kin ga tashi ki tafi. Honey ba ta dubu goma ta sha ruwa a hanya, kada ki ƙara dawowa gidana,kina jina?"

"Allah ya ja da...." Ya daka mata tsawa. Nan take na ce, "ya isa. Tashi mu je waje,ki jira ni." Na shiga ɗaki, ita kuma ta tafi waje.

Ina fita na ja ta zuwa bayan gida, na tara masu aikinmu na ja masu kunne a kan kada su sake su faɗa cewar akwai baƙuwa a gidan nan . Na ba ta ɗaki na ɗiba mata sabulu, sannan na bayar a sayo mata kayan sawa.

Satin jakadiya shida kenan a gidanmu, ta yi ƙyau, ta mayar da jikinta tamkar ba ita ba. Yanzu abin da

Please Login or Register in order to submit comment