Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya rage ƙoƙarin shawo kan Yarima. Jakadiya ta ce mini babu wata hanyar da zamu bi mushawo kan shi illa mu jira zuwan Mama,idan har muka samu Mama ta gaya masa halin da ake ciki baki da baki,wata ƙila ya amince ya tashi tsaye ya nemawa al'ummar da ke ƙarƙashinsa yanci.

Ikon Allah! Yau kuwa safiyar Laraba sai ga Mama ta zo, ganin ta sake lafiya ƙalau kamar yanda take yi mana kenan, ta nuna ba a cikin wata matsala take ba. Dalili ne ma yasa na ɗan tambaye ta ina su Mansura da jakadiya, sai na ji Mama ta ce.

"Lafiyar su ƙalau." Kan ganin bata da niyyar cewa komai yasa na aiki ɗaya daga cikin masu aikina na ce a kira mini baƙuwar nan.

Shigowar jakadiya za ta yi daidai da ɗaga gwangwanin lemon da Mama ta yi. A madadin ta ci gaba da sha, sai aka samu akasin hakan, saboda firgitar da ta yi.

Gaskiya dai ta bayyana daga bakin Mama, wanda Mama har da kukanta take faɗar wasu abubuwan. Hankalin Yarima kam ya tashi. Cikin sakan ɗaya jinin sarautar sa ya gudanyo jikinsa, saboda har wata rawar jiki na ga yana yi. Sai da ya nisa ya kai sau baƙwai, sannan ya miƙe yana cewa.

"Zan je sai na kashe su."

Mama ta yi saurin riƙe shi tare da zaunar da shi, ta koma ta zauna ita ma. Ya dube ta ya ce, "ina nan zuwa da bindigata, sai na kashe shi."

Mama ta yi murmushi, sannan ta yi kirarinsu na manya, shi ne "Ta yaro ƙyau take yi, amma ba ta ƙarko. Ai Yarima duk yanda ka ke tunanin mutanan nan sun riga sun wuce mu. Abin da ya kamata mu yi kawai shi ne mu ma mu dage da roƙon Allah ba dare ba rana. Na farko jakadiya kin fi mu sanin hanyoyin da za'a bi a karyawa Sarki abin da ke jikinsa."

Nan take na ji Yarima ya ce, "Aƙwai wasu addu'o'i da ayoyi ina da su na karya sammu ko wani mugun baki. Ban da ayoyin da Manzon Allah (S.A.W) ya ce mana, tare da koyar da mu yanda zamu aikata su."

Zan sa a yi saukar Alƙur'ani mai girma,sau sittin da baƙwai, wanda kowanne daga ciki za'a tofa a ruwa a yarfawa wanda ake tunanin an yi masa sammu, ba wata hanya da zamu bi illa wannan. Sannan mu duka mu dinga tashi cikin dare muna gabatar da wannan nafilar, da kuma wacce Allah ya hore mana. In zamu iya kuma mu ma muyi sauka da kanmu. Ga addu'o'in da sallar nafila.

Nafila ce raka'a huɗu, kowacce nafila da Ayatul kursiyu ƙafa baƙwai 7, dukkansu bayan ka yi sujjadar ƙarshe sai ka karanta wannan addu'ar. _Wallahu galibun ala amrih,walakin na akasaran nasi la ya'alamun (7),_ Idan mun sallame sai mu karanta wannan addu'ar.

_Allahumma wahastu nafsi wa irdilaka_ sau baƙwai(7), sai mu karanta Laƙada ja'akum, ita ma sau baƙwai(7).

Manzonmu Annabi Muhammad (S.A.W), ya ce wanda yake karanta waɗannan kalmomi guda goma, Allah zai kare shi daga sharri biyar a duniya,biyar a lahira. Ga su nan kamar haka:---

_1) Hasbunallahu liddini_
_2) Hasbunallahu liman ahamman_
_3) Hasbunallahu liman hasadani_
_4) Hasbunallahu liman kadani bi su'in._
_5) Hasbunallahu indal masala fil ƙabar._
_6) Hasbunallahu indal mizan_
_7) Hasbunallahu indal masala fil ƙabar_
_8) Hasbunallahu la'ila ha'ildalaihi tawakkaltu wahuwa Rabbul Arshir azim._

Allah yasa mu dace.

Cikakken bayanin maganin sammu,wato yanda za'a bi a karya sihiri,ko wani mugun Aljani mai taurin kai,ko sanin me mutum ya kamata ya yi,mata ko maza. Ana iya neman littafin nan kantin Al'Ameen Bookshop GUZURIN MATA MUSULMAI IZUWA ƊAKIN AURE. Wanda Malam Bashir Aliyu (Bashir) ya wallafa. Za'a samu duk wani ƙarin bayani a ciki.

Cikin wata ɗaya da ƙwana biyu muka gama duk wani tsarin da muke son muyi. Ta hanyar Mama kuma muka samu ta baiwa Mai Martaba maganin da yarfa masa wannan ruwan sauka. Ban da masallatai da Yarima ya dinga bi yana cewa a tayamu roƙon Allah.

Ba na mantawa da duk zuwa Makka da zan yi,wato aikin Hajji,ko Umarah, sai na yi roƙon Allah ya daidaita tsakanin Yarima da Mai Martaba.

Yau ga shi zan iya cewa Allah ya amsa roƙona,dama kuwa faɗa ce ta malamai, cewa duk muminin ƙwarai ba zai ziyarci ɗakin Allah da buƙatunsa ba face Allah ya biya masa buƙatunsa. Sai dai zasu iya ɗaukar ƴan lokuta, wasu kuma sha yanzu magani yanzu ne. Ko dai ka dawo ka ga alherin abun,ko kuma ma kana can kana dawowa ka samu abin da ka roƙa ya faru.

Mu kanmu ba mu san lokacin da Yarima ya je ga hukumar ƙwantar da tarzoma ta ƙasa ba (Mobile) bayan ya samo taimakon gaggawa, sai dai yau muka wayi gari muka ji an kama Sarkin ƙarya Abdulrahman da mahaifiyarsa, da Yayarsa Hadiza da duk mabiyansu.

Allahu Akbar! Yau ba wanda bai yi wa Mai Martaba kuka ba, shi da ɗan sa Yarima, wanda suka samu shekara ta biyar ba su ga juna ba.

Gaban bainar jama'a Mai Martaba Sarki Jafar ya rungume ɗansa, wanda ya ɗauki sama da mintuna goma, ya ɗagoshi ya kalle shi, sai kuma ya mayar da shi jikinsa ya ƙwantar. Daga baya ne yake tambayar ina jikansa Ammar. Yaro ɗan shekara biyar da wata huɗu ne kawai babu. Amma har ya zama ɗan saurayi saboda girman jiki da yake da shi.

Bayan ya ganshi ne aka miƙa masa Suhailat. Abin ka ga rashin sani, ta ƙi zuwa wajen Sarki. Da yake Allah yasa ta yi saurin tafiya da gudunta, ta iso wajena ta riƙe ni gam tana nuna mini Mai Martaba.

Hankalin Mai Martaba ya dawo jikinsa sosai, saboda duk ya ruɗe wajen neman su Waziri. To aikin da ya ragewa Yarima kenan, neman dattawan da suka rufa mana asiri da yanzu an hallaka mu. Bayan komai ya lafa ne muka ɗauko hanyar dawowa Kaduna. A hanya ne na ji zazzaɓi ya saukar mini,ga shi ko mun isa gida Yarima ba zama zai yi ba, zai tafi yawon neman su Waziri. Wannan shi ne dalilin da yasa muna isowa Kaduna na ce mu biya asibiti in ga Likita, saboda zazzaɓin da ya rufe ni cikin ƙanƙanin lokaci, wanda ni na san hayaniya ce kawai ta yi mini yawa.

Ina zaune a mota da yara da mai rainonsu a baya. Ni kuwa ina mazaunin kusa da direba, ina jiran in ga inda Yarima zai fito, saboda ba zan iya zirga-zirgar cikin asibitin Arewa Clinic ba. Ganin shi ya taho yana washe baki kamar na yi masa albishir ɗin daɗi, duk da na san yau farin ciki yake. Sai da ya iso ya buɗe mota sannan na ga ya ɗaure fuskarshi.

Ni dai ban ce komai ba, amma ina mamakin ganinsa hannu biyu da wata ƴar farar takarda a hannunsa. Abin da ya sa ban yi magana ba, tunanin ko biyawa za mu yi ƙyamus a siyi magani, amma har muka wuce duk inda za'a samu magani ban ga ya tsaya ba.

Ɗaki na nufa kaina tsaye, saboda yanda nake rawar sanyin zazzaɓi. Ina ƙwance Yarima ya shigo ya zauna kusa da ni.

"Tashi ki karɓi takardunki." Gabana kam ya faɗi, amma na yi saurin tashi na karɓa saboda ganewa idanuwana abin da ke ciki.

Positive (Pregnancy test) . Na ga an rubuta a jikin takardar. Na yi saurin dafe cikina.

"Ciki! Haba." Ya harare ni.

"To me kike nufi?"

"Haba Yarima ciki fa?"

"Kina ko ƙwanto ne?"

"Haba gani na yi duka yaushe na haihu?"

"Ko kina nufin ciki ɗaya ya yi kaɗan? Da gaskiyar ki,ƙato kamar ni a ce ciki ɗaya na yi. Tsaya ki gani in dage in yi na biyu yanzu."

Ya taho da sauri zai hayeni, na yi ɗan hanzarin sauka.


######
[2/25, 21:47] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 9


"Na tuba wallahi,ɗayan ma ya isa."

"A'a da sauran Waziri da yake gadin ƙofa, tsaya dai ki ga,ke kin ɗauka abin da wasa ne."

Saboda rashin lafiyar da ke jikina yasa na kasa gudu sosai, har sai da ya kamo ni ya ɗauko ni cak, ya ɗora saman gado.

"Yau Celebration (murna) ɗin shiryawa da Mai Martaba zan yi."

Yana magana yana tuɓe rigar yana cillarwa. Ga shi saman cinyoyina zaune,ni kuwa sai dariyar kukan shagwaɓa nake yi, ina haɗa shi da Allah.

Ya yi saurin sumbatar bakina, ya tsotsa, sannan ya ɗago ni ya tattara gashina da ya baje saman gado, ya riƙe da hannu ɗaya.

"Yasmin na gode miki da ki ka taimaka mini da rayuwa mai ƙyau, ingantacciya. Ga shi kina haifa mini ingantattun yara. Na gode Allah da....."

Muryar Ammar ce ta nufo ɗakin mu. Da ji da gudu yake yana kiran.

"Dady ka yi baƙi masu kayan soja, ga su can a get a tsaye."

Cikin gaggawa ya miƙe tsaye yana kokawar mayar da rigarshi jikinsa. Ni kuwa dariyar ƙeta kawai nake daga ƙwance, har Ammar ya shigo, amma riga ta ƙi sanyuwa,dan ma Allah ya taimaka da wandonsa a jikinshi. Ammar na shigowa sai na ji yana cewa.

"Tsaya Daddy kada ka sa rigar."

Yarima ya yi tsaye da riga a hannu.

"Daddy tsugunna ka gani."

Yarima ya tsugunna, Ammar ya taɓa damtsan cinyar hannun Yarima.

"Wai Daddy ka ajiye chuka,ka fita haka,kai ma sojojin su ji tsoron ka,ka bibbige mana su,nima in na girma zan chuka haka."

"Za kayi amma daga yau tsoka ake cewa."

Ya dafa wajen ƙirjinsa,in tuɓe riga in ga ina da wannan."

"Amma ba yanzu za kayi wannan ba, sai kana cin abinci ka girma,ka zama babba kamar ni."

"Mama wai haka?"

"Kai fita ka barwa mutane waje. Ba na hana ka shigowa ɗaki ba sallama ba da irin wannan surutun naka. Fita mana."

Ya juya tare da cewa, "Ki yi haƙuri Mama." Yana fita na taso na ja kunnan Yarima.

"Kai ma ba na hana ka biyewa surutun Ammar ba? Wata rana sai ya baka kunya a gaban jama'a."

"Sorry Mamo." Na ƙara shan kunu na juya. Ya yi saurin fizgo ni jikinsa.

"Sorry Mamo, ina son in na dawo inga an yi mani fara'a."

"To je ka an yi haƙurin, kada a daɗe a zo a bani magani insha."

"Pracetamol ne kawai za ki sha. Bari in ɗauko miki."

"Ni dai gaskiya mai ƙarfi wanda zai hana komai zama cikina."

"Kada ki damu, ba mantawa na yi ba. Kin ga ko Ammar ya ce zan iya faɗa da sojoji,kin ga kuwa ƙyau na ace ciki bibbiyu nake yi." Na ture shi.

"Ni dai je ka."

Ya yi dariya ya saka riga ya fice. Sai da sha ɗaya na dare ta wuce, sannan ya dawo. Da ganinsa kuwa a gajiye yake. Ya zauna kusa da ni cikin cewa.

"Wash!"

"Sannu."

"Ke dai bari wallahi, na gaji sosai, ta so muje ɗaki,dama dai ni ake jira, bari in ɗan watsa ruwa in ji sanyi."

"Abincin fa?"

"Zan ci, bari dai in samu kaina tukunna."

Bayan ya fito ne yake ba ni labarin cewa wajen su Sarkin ƙarya Abdulrahman ya je, saboda yasa a tuhume shi inda ya kai su Waziri. Da ƙyar ya faɗa, shi ma gani ya yi za'a kashe shi a banza. Kin san inda ya kai su?" Na girgiza kai, tare da matsowa irin na mai ɗokin a gaya masa.

"Suna babban gidan yarin Legos,ƙiri-ƙiri Prison."

"To ya za'ayi yanzu?"

"Sai gobe zamu je mu taho da su. Kai Allah dai ya kusan raba mu da ƙajaga."

Haka dai muka dinga tattaunawa har muka ƙwanta.

N.T.A Kaduna, gidan talabijin na ƙasa, shi muke kallo. Inda muka ga su Yarima na saukowa daga jirgi da su Waziri a bayanshi, sun kai su talatin, dukkansu kamar za su kife ƙasa saboda rama, ga tsufa,ko kuwa in ce yunwa. Amma kaya ne masu ƙyau a jikinsu, ga shi sun sha aski. Jakadiya kuwa, sai kuka take yi,wai tunanin wahalar da ta sha take yi.

**** **** **** **

Wata ɗaya kenan da sati uku da dawowar su Waziri wanda ya yi daidai da yau aka yankewa su Abdulrahman da Yayarsa Hadiza da uwarsu Asabe da sauran muƙarrabansu hukunci a babbar kotu ta jaha, wacce ta yanke masu hukuncin ɗaurin rai da rai, saboda bincike ya nuna Abdulrahman da mabiyansa an kama su da laifin fyaɗe, aikata aikin alfasha da maza, shaye-shaye,kisan kai. Ga shi dama wai sana'ar shi fashi da makami.

Hajiya Asabe uwarsu kuwa an kamata da laifin yin zina kafin ta yi aure, da ta yi kuma tana shigo da wani namiji a cikin gida. Tuhumar ƙarshe kuma ta tabbatar cewa su Abdulrahman ba ƴaƴan Sarki ba ne, sakamakon faɗi da tayi da bakinta cewa ƴaƴan faranta ne.

Hadiza kuwa zaman kanta take yi yanzu haka, ban da gidanta ne matattarar ƴan duniya, ban da bin bokaye da take yi, wanda ya bayar da tabbacin har maƙabarta an taɓa kama ta tana tono wani sashi na jikin matacce. Wa'iyazubillah. Allah ka cikamu da imanin mu,masu yi Allah ya shirye su. Na faɗa a zuciyata.

An yi an gama, sai rigima ta dawo kan Yarima, wanda aka zaɓa a matsayin shi zai hau kujerar sarauta, amma ya ƙiya, ya ce shi da Jos har abada. Wannan al'amari ba ƙaramin tayar da hankalin jama'a ya yi ba. Har ya zama garin Kaduna ƴan garin sun zo, tunda kullum ma samu baƙi ƴan baiwa Yarima haƙuri, da ba shi baki akan ya koma gida. Amma maganar shi ɗaya ce Kaduna ta yi masa, shi hankalin shi a ƙwance yake.

Yau kuwa manyan baƙi ne, wato ƙungiyar su Waziri, amma Yarima ya ƙiya. Da na je gaishe su suka dinga roƙona a kan in ja hankalinsa in nuna masa muhimmancin mutanen da zasu zauna a ƙarƙashinsa. Na bisu da to. Amma na san ba zan iya tunkarar Yarima da wannan maganar ba.

Su Daddyna sun zo tare da Mamee, amma sai ya ce masu insha Allahu zai yi,su bashi lokacin ya yi tunani. Haka suka tafi suna murna. Amma suna tafiya ya ce ai shi sam,kunyar su tasa ya amsa masu. To ni kuwa dama da na ɗauko hanyar yi masa maganar, kallo ɗaya yake yi mani in yi shiru. Wani lokacin ma har in samu la'adar cewa ba ni da hankali.

Sarki Jafar Sada ne yau da kanshi da Iyalansa gaba ɗaya a gidan mu,Mama, Hajiya Kilishi, Ahmad,Yaya Salimat,Sauda, da Idris,Sarki ya yi gyaran muryar da dukkanmu sai da muka nutsu, sannan ya soma magana.

"Faysal my lovely son. Da farko zan fara da roƙon Allah ya raya maka zuri'arka, ya yi maka sakayya da aljannar fiddausi.

Faysal,sanin kanka ne ba mai raba ni da kai sai Allah, amma akasi ya faru tsakaninmu ta sanadiyyar yaudara da aka fara yi ta hanyar gaya mana aibunka da illolinka. Ban yarda ba da farko, sai da aka kawo mini shaida ta zahiri."

Ya buɗe wata ambulan ya miƙawa Yarima kaset da wasu hotuna.

"Duba!" Ya ajiye.

Ban kawowa raina komai ba. Ta haka ta fara yaudara ta. Ganin raina ya ɓaci matuƙa har na ɗan yi fushin ƙwanaki da kai,ai sai wannan hanyar ta ba shi damar shigo da abubuwan da na san sun daɗe yana tanadar su. Magana dai ni ke son ta wuce,a taƙaice ina neman a yi haƙuri a kan duk abubuwan da suka wuce,a taryi gaba,a kiyaye. Ko kana da magana?"

"Baba ni ban ce kayi mini laifi ba,ni ban riƙe kowa ba,ni dai nayi kokawar ƙwato maku ƴanci ne don kuna iyayena, amma ba don na hau gadon mulki ba. Na gode ƙwarai da ƙyautar da ka yi mini da nuna ƙauna, amma na barwa ɗaya daga cikin ƙannena,ai su ma sun girma. Amma ni Kaduna zan cigaba da zama, saboda hanyoyin cin....."

Ya miƙe ya je ya tsugunna ya kai gaisuwa. "Amma idan na ɓata muku rai ku gafarce ni." Ya miƙe ya shiga ciki.

Falon mu ya yi shiru har tsayin mintuna masu tsayi. Can Sarki ya nisa, "Yasmin, Hajiya Mariya, Hajiya Kilishi, aikin ku ne,kushawo kan ɗanku. Ke kuma mijinki. Koma in ce aikin ki ne. Yasmin ki taimaka ki shawo mana kan mijinki, ya taimaki jama'ar da ba mu san iyakacinta ba."

Ba ni da damar yin gardama, sai dai na bishi da, "To Baba, za'ayi ƙoƙari."

Ni kuwa har hantar cikina sai da ta kaɗa. Daga nan kuwa aka cigaba da ƴar hira, jin falon ya kaure da surutu yasa Yarima ya shigo shi ma ya zauna aka ci gaba da yi dashi.

Sai da suka ci abincin ranar mu, sannan suka tafi,mu kuwa rakiya har mota. Yau an samu shiga, bayan mun dawo hirar mu kawai muka cigaba har ya tafi gona.

Bayan mun shiga ɗaki ne har ma mun yi niyyar ƙwanciya kenan an gama duk wata hira. Na ɗauko Novelle Gelly ina shafawa a jikina, domin jikina ya ɗau ƙamshi gaba ɗayan shi. Gefen gado na zauna, amma gabana ke ta wani irin mummunan faɗuwa, saboda maganar da nake son ta fito daga bakina. Ban kashe fitila ba na hayo gado na zauna kusa da shi tare da robar man ƙamshin jikin nan a hannuna,sai kuwa kaɗawa take yi, da alama jikina ke rawa.

Sai da na karanta addu'a sannan na ambaci sunan shi.

_Ya waliyyan ni'imati,wa mallazi inda kurbati,ij'alni matahu bardan wasalam alayya kama ja'altana barda wassalamun ala Ibrahim (Ƙafa baƙwai).

"Honey." Na kira shi a sanyaye.

"Ina jin ki Sweetyna." Ya faɗa, har da ɗora hannunsa a saman cinyata.

"Magana nake son mu yi da kai mai mahimmanci."

"Ina jin ki. In kuma so ake in ƙara wani cikin, to ban manta ba." Ya faɗa har da ɗan taɓa mini gefen cikina. Na yi murmushin da yake haɗe da fargaba.

"Honey maganar sarau...." Wata tsawa da ya daka mini. Bani ba,na yi imani maigadi ma ya tsorata. Ni kuwa har na kai bakin gado, saboda na yi zaton duka ne zai biyo baya. Tun kuwa da na sauka, na durƙushe nake jin ɗan cikina na mutsulniya, tamkar ɗan kifi a ruwa.

Bai ƙara cewa ƙala ba daga wannan, sai ma ya juya min baya. Gaskiya na san na yi awa ɗaya durƙushen nan, ina saƙa hanyoyin da zan bi. Ganin ba shi da wani alamun motsi ballantana in san hanyar da zan bi, sai na ce, "Wash! Wash!! Wash!!! Cikina." Ina faɗar cikina na ga ya yi saurin saukowa.

Tun daga can na ji yana cewa, "Me ya samu cikin? Da ke nake,me ya samu cikin?"

"Ciwo yake. Marata!"

"Tashi mu gani."

Ya yi saurin isowa ya kama ni. Na lanƙwashe.

"Ba zan iya ba, ina jin ɓari zan yi."

"What? To kin ga ni ga irin ta nan,kin sawa ranki abin da ba ruwanki, ga shi nan za ki janyo mana asarar ƴaƴana. Taso mana mu tafi asibiti." Ya sake ni, ya tafi ya buɗe durowa ya ƙwaso mana kaya. Ya zo ya kama ni.

"Tashi, sannu." Ya yi alamar ɗaga ni. Na riƙe hannunsa.

"Yarima!”

"Ba na ce bana son kina kirana da wannan sunan ba?"

"Na sani,ka yi haƙuri, amma yau ne na ƙarshe, tunda ka nuna mini ba ni da amfanin komai a wajen ka. Yau zan haƙura da auranka,gara ka auro wacce take da muhimmanci da amfani a wajenka." Sannan nasa kuka.

Ina jin sa ya tsugunno. "Yasmin me ya faru? Me na yi miki? Ba ki taɓa gaya mini magana mai ɗaci ba sai yau."

"Yau ma kamawa ta yi." Ya ɗago kumatuna.

"Haba Yasmin, ya zaki tayar da hankalin mijinki...."

"Ba ka son a tayar da hankalin ka, amma kai zaka tayar da na mahaifinka?"

"Ba ruwan ki da maganar mu."

"Kenan ba ruwan ka da ni? Don Allah in tambaye ka?"

"Ina jin ki."

"Yanzu me ye nan cikina?"

"Ɗana ne."

"Kana son shi ko baka so?"


######
[2/28, 08:27] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 10


"Wacce irin magana ce wannan Yasmin?"

"Ka ce mini eh ko a'a."

"Ina son shi mana."

"In ya zube za ka ji ciwo."

"Ƙwarai kuwa."

"To ka yi tunanin irin ciwon da za ka ji,ka ƙwatanta shi ga in ka rasa ɗan da ya girma za ka ji ciwo. To mahaifinka abin da yake ji a zuciyarshi ya linka naka dubu, kuma tunda ba ka jin ban haƙurin shi, to ni ma ba zan ji ban haƙurin ka ba, zan bar maka gidanka da ƴaƴanka, amma zan tafi da cikin jikina,in je Likita ya cire mini...."

"Ki rufa mini asiri Yasmin,duk wata taƙamata taki ce,kin zauna da ni a lokacin da na shiga babban tashin hankali, sai kuma yanzu a kan ƙanƙanin abu ki ce ba zaki zauna da ni ba."

"Kai ka ɗauke shi ƙarami."

"Yasmin ke nake ji, ina son ki,ina son zama da ke, muddin na karɓi sarautar nan sai ya zamo na yi miki amarya."

Ɗan cikina ya sake wajen ƙwanciya da saurin gaske, saboda tashin hankalin da maganar Yarima ta haifar. Jinyar sakan biyar na yi sannan na yi magana.

"Na amince ka yi idan dai har za ka bi maganar iyayenka."

"Yasmin kin kuwa ji abin da na faɗa?"

"Na ji, cewa ka yi zakayi min amarya,ko ba haka ka faɗa ba?"

"Haka na faɗa,kin amince?"

"Eh, amma kai ma in ka amince gobe da safe za mu je Jos,ka gayawa Sarki ka amince da abin da yake so, sannan za ka koma Jos da zama,in ba haka ba,yau ba zan ƙwana gidan ka ba."

"Wannan ma bata taso ba,dama na ga wata yarinya ɗazun da na dawo daga lambu, sai kallona take yi,kin ga shi kenan sai in koma in gani. "Ƴar gayu ce."

Na yi murmushi, "Ƙyan Namiji dama ya auri mace wacce ya gani da idonsa ya ji ta ƙwanta masa a zuciya, ba wai wani ya gane masa ba."

"Yasmin kenan, ba ki san cewa matar daraja da ɗaukaka ta bi bayan zaɓin Iyaye....."

"Ya isa,mu je mu ƙwanta."

"Cikin fa?"

"Ya lafa, zan iya kai wa safe." Ya kama ni muka je muka ƙwanta.


**** **** **** **

Taro kan ya haɗo jama'a, ta ko'ina, sai isowa suke yi. Manyan sarakuna na ƙasa, gwamnoni,kai har da shugabannin kasashe, duk sun iso filin jirgi na garin Jos. Mu kuwa muna gefen mata, wajen su Mama, amma ni ma da tawa gayyar a bayana.

Yarima na can daga sashen su Mai Martaba ya sha alkyabbar alfarma. Abin ka ga farin mutum, ya yi ƙyau, wanda ba ya misaltuwa. Ni kuwa ni da Aunty Salwa daga ni sai ita muna hirar jama'ar da ke wucewa.

Bayan kamar awa biyu kowa ya gama zama aka ce Sarkin Malaman Sarakuna ya zo ya buɗe filin taro da addu'a (Adalin Sarki kenan,Sarkin Musulmai Dr. Usman Nagwaggo) Sarkin Katsina kenan. Dattijo fari tas, mai ruwan matasan yara, jikinsa ba ya tsufa. Shi ya fito ya fara jero addu'o'in buɗe taro tamkar wanda ya girma a tsakiyar Larabawa, saboda harshen da ya karya tamkar na matashin Balarabe.

Tsayawa bayanin abubuwan da aka yi ma mun san ɓatawa kanmu lokaci ne, balle lissafa manyan da suka halarta. Amma mun san Sarkin Sarakuna na Nijeriya, manya ba wani a gabanka, shi ya yi naɗin sarautar,wato Mai Martaba Alhaji.Dr. Ado Bayero, wanda jama'a ke so kenan.


**** **** ****

Wani irin mahaukacin gida ne aka bai wa Yarima, har sai da ya ba ni tsoro. Na kalli gidan, daga ni sai ƴaƴana biyu, sai cikin da ke jikina wanda bai wuce wata baƙwai ba. Masu yi mana hidima kuwa ba su ƙirguwa, amma Mama ta ce in dinga yi wa mijina abinci da kaina. Haka kuwa aka yi, duk na ware ɗaki ɗaya na mayar da shi kicin ɗin kaina, wanda ni kaɗai ke shigarsa, sai kuwa ƴaƴana, amma ko jakadiya shakkun shigarta ciki nake yi.

Tsarin kundin littafin mulkin aka damƙawa Yarima domin ya yi nazarinsa, duk da ba wai shi kenan Mai Martaba ya daina aiki ba, a'a mulkin na ga hannun Mai Martaba, Yarima kamar ɗalibi ne da malami, wato ya koyi yanda ake yi, tun kafin Mai Martaba ya rasu ko kuwa ya yi tsufan da ko ya yi magana ma jama'arsa ba za su saurare shi ba,ko kuwa a dinga cewa ruɗin tsufa ne, amma yanzu da hankalinsa, duk abin da aka yi ba daidai ba zai tsawatar.

Dama su tsarin mulkinsu kenan, shi ne a baiwa wanda ake ganin ya cancanta a baiwa sarauta, tun Sarki na da rai, ba don komai ba sai don ya ga yanda zai tafiyar da nashi tsarin mulkin, saboda in ya yi kuskure a nuna masa hanyar gyara.

Shi kuwa Yarima, sabon tsari muka zauna muka gyarawa littafin nan, saboda

Please Login or Register in order to submit comment